Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

matan gidan da yaransu a xaune babu mai bata hakuri sai ma xugata da suke, khadijah kuma na tsaye bakin xaure duk tayi wani duhu ta rame sosai, idonta duk ya kumbura don kuka ga shatin bulala a jikinta, Ladi tace "Yo da kinsan haka ne tun farko kema ai baxa ki fara daukarta ba, meye amfanin yaron da baxa ka amfana da shi ba sai shegen son jiki da iyayi, ai kadan ma kika mata da kin hada kin fasa shegen bakin turancin da take xagin mutane da shi a gidan nan" Yakumbo na huci tace "Ai Amina ta cuce ni, ta yaudare ni... Tasan haka shegiyar yar take xata kawo min ita tun farko, gode gode da yarinya bata iya komai ba wanke wanke duk ta jika kayan jikinta tayi awa da awanni a bakin kwararo, shara duk a gantale, gyaran daki gwara ka da fauziyya mai shekara biyar, aike sai kayi yyi sau uku, har yau ta kasa iya hura icce, girki dama ba a maganar sa, wa ennan yan mitsimitsi yaran idan na sa ta tayi masu wanka ta shaka masu sabulu a hanci ko a ido, ni dama tun farko abinda ya sa na karbeta na yi xatan xan amfana da ita ne, banda haka me xai kai ni kowa na ta kansa a rayuwar nan gashi gobe ko jibi xa a xo a fitar mana da kaya har ynxu ban kama wani gidan ba, ni wllh wllh da nasan gidan Amina sai in yi kudin mota in mayar da ita ta bani kudi na don baxan iya kayan tsiya ba, dama can Aminar ma ba wani kyautata min take ba uba ne kadai ya hada mu" Salamatu tace "Ai irin yaran nan kyansu aikatu wllh, a can xa a horasu su ladabtu...." Katse ta yakumbo tayi tace "Yar da har yanxu bata iya shara ba xan kai aikatau, ai koramu xa ayi daga ni har ita" Ladi tace "Yo ke nuna masu xa ki yi bbu abinda bata iya ba ai, a can xa su gyara mata xama ta iya komai, mutanen da basu san darajar d'an Adam ba, ai tuni wahalar da xa su dinga mata xai sa ta xage a nan kuma xata koyi komai, wannan d'an abincin da kike bata ma take kin ci take yawo da yunwa can nema xata yi ta rasa, hakan xai ladabtar da ita wllh" Yakumbo ta ja kujerar tsugunno ta xauna tace "Kai amma fa kun kawo shawara, amma...." Sai kuma tayi shiru ta kalli khadijah dake kallonsu, tsawa tayi mata ta ce "Fita ki ban waje kije gun mai kanti da hamsin di ta dake gunsa ki amso min barkonu" juyawa khadijah tayi da sauri ta fita gidan, Yakumbo ta mayar da dubanta gun su Ladi tace "Toh Amina fa? Kunsan baxa ta yarda ba" dariya Ladi tayi tace "Ka ji ki, sai ki gaya mata, barin ma yanxu tashi xa ku yi Ku bar anguwar, shawara a nan shine kada ki kuskura ki gaya ma ko inda kika koma a anguwar nan, kawai cewa xa ki yi ba ki ma samu gidan ba gidan wata yar uwarki xa ki kafin ki samu, ke kuwa kije shanono abun ki ki kama ko daki daya ne bbu wanda yasan inda kike, dama ba waya gare ki ba, har ki tara kudin da xa ki tara da yarinyar daga nan idan ma mayar da ita gun Aminan xa ki yi sai ki ja mata kunne ki mayar da ita" Yakumbo tayi murmushi tace "Dadina da ku akwai shawara mai ma'ana, amma fa har da kudin da xan sa yarinyar a makarantar gwamnati ta bani, yanxu haka ma da kudin xan je kama haya a shanonon, dubu hamsin kuma jari xan ja na su omo da sabulu ina siyarwa, ita can na kai ta gun aiki ana biyanta dubu uku misali, kun ga ni ban ma kai da nisa ba...." Ladi tace "Toh gaskiya sai kin ba mu dubu dai dai mu da muka kawo shawarar Ashe ma kudi gare ki har haka" yakumbo ta hade rai tana da ta sanin gaya masu, rai a bace tace "Dari bibbiyu dai" daga haka ta mike ta shiga cikin akurkin dakinta, sai ga ta ta fito da sauri tace "Toh yanxu wa xai min hanya in kai ta gidan aikin, don ni gaskiya baxan tare da ita a sabon gidana ba, ko yau aka samu gun aikin ba don yamma yyi ba kai ta xan yi, don haka gobe da safe xan kai ta...." Ladi tace "Akwai wata kawata Habiba dillaliyarsu ce, xan baki lambarta... Ko kuma ki sa katin dari a wayata mu kirata, in sha Allah nasan baxata rasa inda xata kai maki ita ba" hakan ko aka yi Yakumbo ta sa kati ladi ta kira Habiba, suka ci sa'a number ya shiga, bayan ladi ta gaisa da kawartata tace "Bibalo dama wata yarinya ce da ake son kai ta gidan aiki to shine muke son ki yi taimako" Bibalo tace "Kai yanxu haka Ina hanyar dawowa daga kauye na mayar da wasu yara, amma gobe da safe xa ki gan ni duk da bani da wa enda ke son masu aiki yanxu, amma nasan kawata Abu baxata rasa ba don ta ma fi ni sanin gidajen manya" daga haka suka yi sallama ladi ta katse wayar tana kallon Yakumbo don ba sai ta mata bayani ba tunda a handsfree tasa ita ma ta ji komai, Yakumbo tace "Toh Allah ya sa a dace, ni wllh ko dubu biyu ma xa a dinga biyanta na yarda" tagumi tayi tace "Allah gani gare ka, kasa a karbi yarinyar nan ni kuluwa" Washegari da safe kuwa sai ga Bibalo tare da kawarta da ta fada Abu, Yakumbo dake ta washe hakora ta gaishesu suka amsa aka xaxxauna kan tabarma ladi ma ta fito akurkin ta tana masu sannu da xuwa, bayan sun gaisa Bibalo tace "Toh kinga ni bni da inda xan kai ta amma Abu tace kawarta ta taba hadata da wata Hajiya mai neman mai aiki, da xata dinga share share da goge goge sannan wanke wanke, akwai ma wata babbar mai aiki dake girki a gidan, to Abu taje gidan ya fi sau uku ba a bude mata gate, yanxu ma gwada sa'a xa ayi kuje har da ke kika wajen, idan sun dauketa to, idan kuma sun ce A'a sai ki jira har a bukaci mai aiki a wani gidan sai in kai ta" Yakumbo tace "A'a mu je kawai mu gwada sa'ar mu" Bibalo tace "Toh ki sallame ni ni xan wuce" Yakumbo ta hade rai tace "In sallame ki? Me kika min da xan sallame ki" Bibalo ta bude baki tace "Au haka ma xa ki ce, shi kudin motar da nayi da kuma bata lokacina da na yi na xo nan tare da kawata har xa ki ce min me na maki" mikewa Yakumbo tayi rai a bace ta shiga ciki ta fito da dari biyu tana cewa "Ko daukar yarinya ba ayi ba xaki wani ce in sallame ki idan ba hadama ba" dungura mata dari biyun tayi a gabanta rai a bace, Bibalo ta dauka ta mike tace "Ya fi babu ai" daga haka ta yi ma Ladi sallama da Abu tayi ficewarta, Abu tace "Toh inji kinsan mu dubu daya ce sallamar mu?" Yakumbo ta hade rai tace "Idan an dauki yarinya ba" Abu tace "Toh gwara da kika san haka don ni baxan tsaya cacar baki ba, yanxu Ina yarinyar take?" Yakumbo ta nuna mata khadijah dake ta fama da wanke wanke, kwalalo ido tayi tace "Warcen da ta fi minti ashirin tana d'an wanke wanken can, tun shigowar mu fa take wanke wanken kamar ayi kamar baxa ayi ba" yakumbo ta marairaice tace "Haka take Abu, akwai iya aiki amma ba sauri ne kawai, amma tana xuwa can nasan xa su gyara mata xama ta xama mai hanxari" Abu ta tabe baki tace "Toh unguwar da nisa, don can Gra ne, kuma wllh gidan babban mutane ne, ni dai Allah ya sa su dauketa, yanxu sai ki tashi ku shirya ta hada kayanta ina jiran ku mu kama hanya" Yakumbo ta mike da sauri ta shiga ciki tana cewa "Toh bamu minti biyar kacal" tana shiga dakin ta kwalo ma khadijah kira, khadijah ta mike ta shiga da sauri. Yakumbo ta jawota tayi kasa da murya tace "Dijangala ta mai gari, ba auren talaka ba" tana washe hakora ta fadi haka, ita dai khadijah kallon ta kawai take, Yakumbo tace "Kinsan inda xa mu yanxu kuwa?" Girgixa kai khadijah tayi, Yakumbo tace "Gidan da xa a dinga biyanki kudi mai yawa in tara maki in sa ki a boko, kai har in maki aure ma" khadijah tayi shiru bata ce komai ba, yakumbo ta marairaice tace "Don haka muna xuwa kice kin iya aikin komai, sai ki bada himma idan an saki aiki ki yi da sauri da sauri, sannan don Allah Idan mun je gidan khadijah kar ki masu wannan yaran naki na turanci kin ji koh? Kawai Hausa xa ki masu, idan kuma baki san Kalmar da xa ki fada da hausa ba sai kiyi shiru abun ki ba sai kin yi turancin ba" yanxu maxa canxa kayan Ki bari in tusa maki wa encan a jaka tunda basu samu wanki ba idan kin je can ko ba ki iya wankin ba ki tsoma su a ruwa ki xuba omo ki shanya" daga haka Yakumbo ta shiga tusa kayanta a wani karamin Ghana must go, don har ta siyar da jakar da Umma ta kawo mata kayanta ciki, karfe tara da kusan rabi su yakumbo suka bar gidan tare da Abu bayan ta yi ma yan gidan sallama suka dinga yi mata Allah ya bada sa'a, tana rike da hannun khadijah suka isa bakin titi, Abu tace "Amma kinsan ke xa ki biya kudin abun hawa dai koh?" Yakumbo ta tsuke fuska tace "A kan me?" Abu tace "A'a mayar da wukar ae dai naga ba xuwan kai na xan yi ba gidan don hka idan kinsan gidan ke sai ki kai ta, yakumbo ta rikota da sauri tace "Naji, mu je ya na iya, daga yau ai babu wanda xai xo yace in biya masa kudin napep dai koh?" Ko tanka ta Abu bata yi ba ta shiga napep din da ta tsayar, Yakumbo ta shiga ta daura khadijah a cinya. Tafiya ce mai nisa kamar yanda Abu tace masu, tun da suka bar hayi dama Yakumbo ke addu'ar Allah ya sa a dau khadijah gidan aikin idan ba haka ba asirinta ya tonu don ta sa rai da kudin da xa a dinga biyan khadijah, tun da suka shigo anguwan Yakumbo ta saki baki kamar yawu xai dalalo tana kallon gidaje na alfarma, Abu ta dinga nuna ma Mai napep din inda xai bai, har suka iso wani cool silent anguwa mai cike da shuke shuke a ko wani gate, ga bakin kwalta a shimfide daga farkon layin har inda yakumbo ke tunani karshe ne, bakin wani gate Abu ta sa mai napep din ya tsaya, yakumbo ta wage baki tana kallon jibgegen gidan da aka yi ma ginin xamani kamar ta sure ta gudu, gidan ya hadu ne kawai don ita a ganinta duk ya fi sauran gidajen dake layin haduwa, suka sauka sai kuma Yakumbo aka tsuke fuska da ta tuna kudi xata bada yanxu, ta dungura ma mai napep din kudin da yace lkci daya kuma tana hararan Abu, Abu da ko lura da ita bata yi ba tace "Toh Allah ka bamu sa'a don kwanaki da na xo haka na sha xamana bakin gate rana yayi maganina ban samu shiga gidan ba... Yakumbo tace "Yana da kyau mutum ya dinga fadin alkhairi ko yayi shiru, yanxu me ya kawo wannan xancen, in sha Allahu ma sai mun shiga don haka ki mana shiru" daga haka Yakumbo bta kwankwasa gate din a hankali kamar me tsoron kada ya fashe don ita fa gani take kamar glass ne a kauyancinta, ta kwankwasa ya kai sau hudu kafin wani da alamar mai gadi ne ya bude yana kallonsu, Yakumbo ta durkusa har kasa ta gaishesa, yace "Wa ku ke nema?" Yakumbo ta mike tace "Matar gidan muke nema ce mana tayi mu samo mata mai aiki yarinya karama, to cikin ikon Allah gashi mun samo mai haxaka, shine muke hadaka da Allah yaro ka bar mu mu shiga, mu gabatar mata da aiken da ta mana" ya girgixa kai yace "Ai akwai mai aiki yanxu haka a gidan don haka ban ji xa a bukaci warce xa ku kawo" Bakin yakumbo ya fara rawa tace "Wllh xa su bukata dubeta fa kaga bbu abinda bata iya ba, sannan Hajiyar da kanta ta sa mu ko daxu mun yi waya da ita tace sai mun xo, haba yarona ka duba tsufana mana gashi daga hayin rigasa muke wllh" Mai gadin yace "Toh yanxu ma ku kirata idan tace ku shiga toh shkkn" daga yakumbo har Abu aka hadiye yawu da kyar don babu mai waya cikinsu, Yakumbo tayi karfin halin cewa "Wallahi wallahi na mance wayar a gida kaji rantsuwar musulmi" Abu ta saki baki jin rantsuwar da Yakumbo tayi alhalin taji Bibalo tace bata da waya.


Not edited.

Mai gadin ya girgixa kai yace "Toh ku yi hakuri gobe sai ku je ku dawo, amma ku tabbatar kun taho da wayar da xa ku yi communicating da ita" xai rufe gate Yakumbo tayi saurin saka kafarta daya ciki tace "Don girman Allah kayi hakuri ka bar mu mu shiga, wllh mun kashe kudin mota yayi dubu daya, kuma ni na biya, ka ji tausayina d'an nan" kamar xata rushe masa da kuka ta kai karshe, ya tsaya kallonsu da mamaki, can yace "Toh shkkn, amma har ni nasan sai kun janyo min fada wllh, amma bakomai akwai Allah, ku shigo" Yakumbo ta durkusa har kasa tana masa godiya suka shiga cikin makeken compound din gidan, uwa idonta xai fito yyi magana ta dinga bin gidan da kallo da motocin dake parking lot, Abuu ko idan da sabo ta saba shiga gidaje haka kai yara masu aiki, don haka ita ke biye da mai gadin yakumbo kuwa nata kalle kalle, bbu abinda khadijah tayi ma kallo biyu a compound din, don bbu bakonta a ciki. Karkashin wani artificial tree mai gadin ya nuna masu su jira sa, ya isa main entrance din shiga gidan, ya kusa minti biyar tsaye bakin kofar bayan ya danna bell aka bude kofar, Mai aikin gidan ce warce baxata wuce shekara ashirin da bakwai ba tana sanye da apron da hularsa alamar daga kitchen take, ganin warce ta fito yayi murmushi yace "Kyauta mun tashi lafiya?" Tace "Lafiya lau Usman, Ashe kai ne ma, ya aka yi?" Ya d'an sosa kai yace "Hajiya ce tayi bak'i ina fatan dai ta tashi bacci?" Kyauta tayi kasa da murya tace "Gata can parlor xaune ma" Muryar Hajiyar gidan suka ji tace "Waye kyauta?" Kyauta ta yi saurin barin bakin kofar tace "Hajiya, Usman mai gadi ne wai kin yi baki" Hajiyar dake gyara farcenta da nail cutter ta kalli agogo tace "Baki kuma?" Kyauta tace "Eh Hajiya" tace "Toh su shigo, amma ni bani da wasu baki da nake expecting da safen nan, da akwai ai da na gaya masa" Usman da ya ji abinda ta fada ya nufi gun da yakumbo suke yace "Allah ku daina karya bashi da amfani a rayuwa, yanxu gashi tace ita bata da wasu baki da take expecting da safen nan ku kuma har da ce min kun yi waya" yakumbo ta yi kasa da murya tace "Mu dai don Allah tunda har muka samu muka shigo gidan nan ka rufa mana asiri mu karasa idan ma ta kore mu shi kenan sai mu fita haka Allah yayi" ya nuna masu kofar shiga ya koma can bakin gate yana mamakin wasu 'yan Adam. Da yake a bude kyauta ta bar masu kofar, da sallama Yakumbo ta kutsa kai cikin parlorn tana dudduke kai ga wani daddadan kamshi dake tashi ta ko wani angle... Abuu na biye da ita a baya, Sai da duk suka shiga khadijah ta tura kofar a hankali ta rufe sannan ta bi bayansu, Hajiya Fatima matar gidan ta dinga kallonsu da mamaki har suka xauna kasan lallausan carpet din tsakar makeken parlorn, sanyin Ac yasa yakumbo ta fara rawan Dari, Hajiya tace "Sannun ku da xuwa" Yakumbo tayi saurin cewa "Yauwa ina kwana shugaba?" Ba Hajiyar kadai bace xaune parlorn ita da wata ce wanda ga dukkan alama kanwarta ce tsabar kamanninsu, matar xa kuma ta yi shekaru talatin da 'yan kai a duniya, Hajiya ta kalli kanwarta kamar yanda ita ma take kallonta, Amsa gaisuwar yakumbo Hajiyar tayi tace "Daga ina?" Yakumbo tayi gyaran murya kafin Abuu tace komai tace "Dama Hajiya da daddewa mun ji kina neman mai taimakon ki, shine ga yarinyata ganin irin haxakarta da hanxari yasa nace in rako Abuu dillaliya mu kawo maki" Hajiyar tace "Ayya ai kam ina da mai aiki bayin Allah gata can ita ta bude kofar ma...." Yakumbo ta katse ta tace "Ayya wannan d'an share share da goge goge xata ke maki Hajiya, wancan naga ai babba ce, ni ko baxa ki biya kudi mai yawa ba ki dauketa Hajiya don wllh daga waje me nisa muke ga uban kudin mota da muka kashe, ki taimaka fisabillilahi Hajiya" Abuu ta kara da cewa "Ki taimaka Hajiya wllh takanas saboda ke muka kawo yarinyar" Hajiya da tayi shiru tana kallonsu tace "Toh wacece mai aikin?" Da sauri Yakumbo ta nuna khadijah dake kallo so engrossed a katon plazma dake parlorn tana murmushi, Yakumbo ko lura da hakan ba ta yi ba, sai kallon Hajiya take ta kara jin abinda xata ce kan khadijah xuciyarta na bugawa, Hajiyar na duban khadijah tace "Ke ya sunan ki?" Inaa khadijah ana can duniyar kallo wannan karan har da dariyarta don film din ya mata dadi, yakumbo ta hadiye abu da kyar ganin irin kallon da Hajiyar ke mata, ta wani mitsileta a boye da sauri khadijah ta dawo, a fusace Abuu tace "Ba ke ake ma magana ba" khadijah ta kalli Hajiyar dake kallonta har lkcn tayi kasa da murya tace "Sorry ma'am, pardon?" Daga Hajiyar har kanwarta dake xaune kusa da ita bude ido suka yi suna kallonta sosai, Khadijah tayi kasa da manyan idanuwanta tace "I am sorry" Mikewa Yakumbo tayi jin fitsari ya taho mata, shi kenan khadijah ta cuce ta sai da ta buga masu turancin, ta nufi kofa da sauri tana cewa "Bari in d'an xaga Hajiya ku yi hakuri" Abuu ma sai kallon khadijah take baki sake jin fa kamar wani yare ta yi maimakon Hausa, Hajiya dake ta kallon khadijah tace "Alright, what's ur name!" Khadijah ta kalleta tace "My name is khadijah Muhd" Hajiyar tace "From where" khadijah tace "I am from kano, I lost my mum and dad... My step mum brought me to Kaduna 4 days ago and she left me...." Tana magana ne har hawaye ya kawo idonta, Hajiya dake kallonta keenly tace "And... Who is this woman that left to ease her self now?" Khadijah tace "My stepmum told me she is her senior sister.." Shigowar yakumbo yasa khadijah tayi shiru, Yakumbo ta shiga kalle kalle kamar munafuka ta xauna amma kuma ta kasa cewa komai tana jiran jin hukuncin Hajiya, ta ma san kawai Hajiya fasa daukar khadijah xata yi don ita tunda take bata taba jin an dauki mai aiki yar boko ba, sai ayi tunanin wani mission ya kawo ta gidan, Hajiyar na kallon Yakumbo tace "Nawa ne kudin aikin?" Xuciyar Yakumbo yyi mugun sanyi ta gyara zama tace "Wallahi ko nawa Hajiya, ko nawa Allah ya hore maki babu damuwa barin yanxu da kudi yyi wahala" Hajiya tace "Dubu uku xan bayar, yanxu kuma xan ba da na wata uku kamar yanda nake ma duk mai aiki idan na dauka" Yakumbo dake ta godiya kamar marokiya tace "Wallahi ba damuwa Allah ya bi ya maki bukatunki na alkhairi, nagode nagode nagode" Kanwar Hajiya mai sunan Khadijah dake gefenta ce tace "Why House maid again bayan kyauta Mumy? Beside I don't think this little girl will be capable, you just look at how engross she is with the TV...." Ko kadan khadijah bata ma san abinda ake cewa ba don gaskiya ne gaba daya hankalinta ta mayar kan kallo, yakumbo da babu abinda taji baya ga kyauta a xancen da Anty khadijah tayi ta marairaice tace "Kiyi hakuri baiwar Allah bbu abinda yarinyar nan ba ta iya ba wllh" Hajiya tace "Toh idan naga bbu abun kirki in sha Allah nan da kwana uku xa ku dawo ku dauki yarinyar, idan ya so sai ki mayar min da dubu shidda nah, ki rike dubu uku" Yakumbo tace "In sha Allah Hajiya, nagode nagode nagode" Hajiya ta katse ta daga godiyar da take yi tace "Toh ta wani number xa a same ki?" Yakumbo tace "ni ki ban naki idan na koma gida sai in kira ki Hajiya, na bar wayar a gida kuma ban san number ba" Hajiya ta sa kyauta ta kawo takarda da Biro tana cikin rubuta number aka bude kofar, duk suka juya kallon bakin kofar banda ita dake rubuta number, dogo ne tamkar dai khaleel din wasu can Lol... Irinsa shi ma ake kira da gentlemen, sanye yake da farar T-shirt da bakin wando, shigar ya kara haska farin fatarsa, iyakar kyau dai kam Alhmdllh Allah ya masa, tuni turarensa ya gauraye ko ina na gidan, har ya iso cikin parlorn idanuwansa na kan mahaifiyarsa dake rubuta sunanta kan number da ta rubuta a takardan hannunta, ya xauna gefenta yana murmushi ya mata side hug a hankali yace "Good morning mum" Sai a sannan ta kallesa hade da turasa tace "Morning...tashi kusa da ni sai warin asibiti kake dalla" Xaro ido yayi yana shinshina kayansa yace "Kai mum warin asibiti kuma duk kamshin nan da nake" tace "Ae kamshin daban warin asibitin daban" ya d'an yi murmushi yace "Ba dai warin asibiti ba sai dai kice kamshin magunguna mum..." Ya kalli Small mum dinsa yana shafa kai yace "Good morning small mum" tabe baki tayi tace "Allah ya kara.... ina ce nan ka tsallakeni ka tafi can gashi an gwaleka" rike kansa yyi yana d'an murmushi can ya dago a hankali yace "Mum kin ji koh" Sai a sannan ya kalli su Yakumbo, tayi saurin cewa "Ina kwana Alhaji" yace "Lafiya Alhmdllh" Hajiya da har ta bata paper din tace "Toh shkkn, yanxu saura in baku kudin ina sauraren kiran ku" kallon D'an ta dake xaune har lkcn a gefenta tayi tace "Aliyu akwai cash tare da kai yanxu?" Ya sa hannu aljihun sa, tace "10k xaka ban" dubu goman ya fiddo ya mika mata ta karba ta ba Yakumbo, Hannu bibbiyu ta karba tana jero godiya, Aliyu yyi saurin dauke kai yana kallon small mum dinsa da wani expression yace "Who are they?" Anty khadijah ta tabe baki tace "Wai house help" yace "House help kuma, did mum dismissed the one available?" Anty khadijah tace "Ina fa, duk biyun xata hada ina ga" ya yatsine fuska yace "Which means ta ba ma su Siyama daman su kara relaxing kenan" Anty khadijah ta tabe baki bata ce komai ba, yace "Which among them is the house help" Anty khadijah ta nuna masa khadijah dake rakube gu daya ana ta kallo happily, lekata ya dinga yi baki bude, can ya dago da sauri yace "Which help will this little girl render?" Anty khadijah tace "Kai ma dai ka gani" bai sake cewa komai ba ya fiddo wayarsa dake vibrate a aljihu, Su Yakumbo suka tashi xa su tafi har lkcn tana ma Hajiya godiya ko bin ta kan Khadijah bata yi ba ta fita tana kara dunkule kudin hannunta Abuu na biye da ita, Hajiya ta kalli Khadijah tace "Tashi ki dau cups din nan

Please Login or Register in order to submit comment