Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yace "Kin tashi?" Kai ta gyada masa, ya karaso yace "How are you feeling now?" A hankali tace "Da sauki" Yace "what did you want to eat?" Murya can kasa tace "Sallah xanyi" yace "Sallah?" Ta gyada masa kai, ya kalli ruwan hannunta, karasowa yyi ya cire mata tube din jikin alluran yace "But be careful kar ruwa ya shiga ciki" ta gyada masa kai, kasa mikewa tsaye tayi da farko don gani take xata iya faduwa, yace "Baxa ki iya ba?" Da kyar ta mike cike da karfin hali ta shiga bayin, ta kama ruwa ta dauro alwala ta fito, taga har ya shimfida mata darduma ya ajiye mata hijab ya fita, tun tana sllhn a tsaye har ta kasa ta fara yi a xaune, sai bayan da ta idar ya shigo dakin yana tsaye daga bakin kofa yace "Me xa ki ci?" Tayi shiru don a lkcn bbu abinda ke ranta bnda danwaken da Kyauta ta taba yi ranan a can gidan, ganin taki cewa komai ya karaso yace "Ki fadi abinda kike so xan je in siyo ynxu" ta kallesa kafin ta sauke idonta a hankali, yace "What did you want" murya can kasa tace "Danwake, amma tunda dare yyi kawai ka bar sa" tsaye yyi na d'an lkci kafin ya juya bai ce komai ba ya nufi kofa, har ya bude kofar xai fita ya juyo yace "But.... I don't knw ur name" tana kallonsa a hankali tace "Khadijah...." Ganin yanda yake kallonta tace "Khadijah Muhammad" ya gyada kai yace "I will call you... Iman.... Cos you have the name of My mum" daga haka ya fita, ji gayi komai ya tsaya mata a lkcn, taji kamar ya fama mata wani ciwo ne a xuciyarta, har ya dawo kuma bata daina kukan da take ba kamar ranta xae fita, lkci daya hankalinsa ya tashi bayan ya ajiye warmer din danwaken, da damuwa yace "Me ya faru, why r u crying" cikin rawar murya tace "Don't call me Iman plss don't bana so" da mugun mamaki yake kallonta, can a hankali yace "Ohk I won't" daga haka ya bude warmer din ya xuba mata danwaken a plate yana kallonta yace "Manja ko Man gyada?" Tayi shiru tana goge hawayen idonta, can a hankali tace "Man gyada" xuba mata yyi kadan, ya ajiye abincin da yajinsa a gabanta, bata iya ta ci da yajin ba, haka ta dinga ci gaya ko maggi bbu, gani take idan ta sa yajin xata yi amai, ba laifi ta ci me yawa, amma ta kasa shan ruwan da ya kawo mata, shi dai yana ta tsaye dakin yana danna waya lkci lkci yana kallonta, ganin bata sha ruwan ba yace "Why didn't you drink d water" a hankali tace "amai, amma kila idan na sha mai xafi baxan yi ba," wani kallo ya fara yi mata kafin ya tabe baki ya fita, ba a dau lkci ba ya dawo da ruwan dumi, cikin ikon Allah kuma bata yi aman ba da ta sha, sai da ya sa ta wanke baki snn ya maida mata drip din, tana kallonsa bata san lkcn da tace "Are you a doctor?" ya girgixa kai ba tare da ya kalleta ba yace "I am nt, but a lot of my frnds are" Komawa baya yyi bayan ya gama yace "Did you need anything, I mean anything?" Ta girgixa masa kai, xai yi magana wayarsa ta fara ring, ya dauka yana kallon screen din da sauri, gefen gado ya koma ya xauna ya daga ya kai kunne a hankali yace "Mami am on my way now, na tsaya yin wani abu ne, but nan da few minutes xan iso, Ki yi hakuri...." Sai bayan da ya mayar da wayar aljihu yace "Am going home now, anjima kadan Yusuf xai turo nurse da xa ta tsaya dake, she's on her way now" a hankali Khadijah tace "Toh na gode" yace "No thanks" daga haka ya fita ya rufo mata kofar. Ko minti sha biyar bai yi da fita ba aka bude kofar dakin wata mata da baxata wuce 30 ba ta shigo dakin, ta karaso kusa da khadijah tace "Sannu ya jikin ki" ta gaisheta don ta gane ta tace da sauki, nurse din tace "Ba kya bukatar komai koh?" Khadijah ta gyada mata kai, tace "Toh ki kwanta kiyi bacci, Allah ya kara lfya" ba musu ta koma ta kwanta, nurse din ta juya ta fita, duk khadijah ta bude ido cikin dare sai ta ganta coincidentally ta shigo duba ruwan dake makale hannunta, duk da drip din kuma hakan bai hanata dinga jin xaxxabi sosai ba, sai kusan asuba ta cire mata drip din bayan ya kare, ta samu da kyar ta shiga bathroom, baki ta wanke tayi wanka ta dauro alwala ta fito, duk yanda ta so yin sllh a tsaye kasawa tayi don jiri ne ke dibanta sosai ga rawan sanyi da take, daga karshe tayi a xaune ta kwanta nan kan darduma, ji tayi ana tada ta ta bude ido da kyar taga nurse din ce, tace "Kin yi wanka ne?" Khadijah ta gyada mata kai, nurse din tace "Da ruwan sanyi?" Girgixa mata kai khadijah tayi tace "Akwai ruwan xafi a heater" nurse din tace "To tashi ki koma kan gado" da taimakonta khadijah ta koma kan gadon ta kwanta ta lullubeta ta fita. Takwas saura taji hannu forehead dinta ta bude ido da sauri, Dr Yusuf ta gani tsaye kanta yace "How are you feeling?" Ta tashi xaune tana gyara hijab dinta tace "Ina kwana" yace "Lafiya lau, ya jikin?" Ta sunkuyar da kai tace "Da sauki" ya kalli nurse din yace "She is having a running temperature" nurse din tace "Eh tun da tayi wanka da asuba" ya kalli khadijah yace "Da ruwan sanyi kika yi wankan?" Ta girgixa masa kai, ya kalli nurse din yace "Je ki bude mota akwai drips da injections da na taho da su daga clinic" tace "Ohk sir" daga haka ta fita, d'aga kai khadijah tayi taga kallonta yake, ya dauke idonsa yana girgixa kai ya nufi window ya dage curtains din yana kallon waje, bude kofa aka yi Sudais ya shigo da sallama, kananun kaya ne jikinsa lkci daya kamshin turarensa ya cika ko ina na dakin, a hankali cikin dubara ta toshe hancinta, Tun da ya kalleta sau daya bai sake kallonta ba ya nufi gun Dr Yusuf, bayan sun gaisa Yusuf yace "Ya su Mami" Sudais yace "They r ol fyn, amma daga clinic kake" Yusuf ya girgixa kai yace "No, yanxu dai xan je clinic din" Sudais yace "ohk how is she feeling now" kafin Yusuf yace komai ya nufo ta yana kallonta yace "Kin tashi lafiya?" Khadijah da har lkcn ta rufe hancinta tace "Ina kwana?" Yace "Lafiya lau, why are you uncomfortable" ta girgixa kai a hankali tana yamutse fuska tace "The perfume" kallon Yusuf yyi ya tabe baki, Nurse ta shigo da abinda Yusuf ya aiketa ta dauko, gaida sudais tayi ya amsa duk da sun gaisa a waje, Sudais ya maida dubansa kan Khadijah yace "Toh me xa ki ci" girgixa masa kai tayi tace "Bana jin yunwa yanxu" Yace "But you need to take something" shayi yasa Nurse ta hado mata mara xafi, ganin Cup din shayin kadai ya dinga tada mata xuciya har da hawayenta, hankali tashe tace "I said am nt hungry plss" Yusuf dai na tsaye kusa da window yana kallon su, Sudais ya karbi shayin ya hade rai ya mika mata yace "Collect it now, ina ruwan wani da rashin jin yunwar ki" Karba tayi ta runtse ido ta rike breath dinta ta kai baki amma ta ki sha, can ta bude ido a hankali tana kallon sa kamar xata yi kuka, taga yanda ya hade rai yana kallonta, kauda fuskarta tayi tace "Don Allah kayi hakuri Allah baxan iya sha ba amai xan yi" yace "Sha kiyi aman" bata ce komai ba kuma bata sha ba, ta kalli Yussuf taga ya rungume hannu yana kallon su kawai, Nurse din tace "Ki daure ki sha kin ji yan mata" runtse ido ta kara yi bata ce mata komai ba, wani tsawa da ya tsorata ta Sudais ya mata yace "Wa kike tunanin xaki dinga ba wahala" bata san lkcn da ta kai shayin baki ba ta kurba, sauka tayi daga kan gadon da sauri jin amai ya taho mata nurse din tayi saurin karban Cup din hannunta ta ajiye, ta shiga bayi tana amai, ita ta taimaka mata ta gyara jikinta ta cire mata hijab ta wanke gun sannan suka fito tana rike da hannunta, bin su Sudais yyi da kallo har ta xaunar da khadijah gefen gado ta kwanta tana maida numfashi, Shi dai Yusuf har lkcn bai ce komai ba, ya karasa gun da nurse din ta ajiye ruwan drip din ya dauka ya fara hadawa, ita ya bar ma ta sa mata sannan ya kalli Sudais yace "Barrister.... I will be on my way now" Sudais ya bi bayansa suka fita. Xa a iya cewa kusan a gidan Sudais ya wuni ranan don da ya fita xai dawo, Nurse din kuma karfe sha biyu ta wuce, duk shigowar da xai yi daki kuma sai Khadijah ta farka daga baccin da take, wani lkcn ya mata sannu, wani lkcn kuma kawai ya juya ya fita. Tun bayan awaran da ta sa ya siyo mata ta samu ta ci kadan bata sake yarda ta ci komai ba don shi dinma damunta yake tayi gashi ta kasa yin aman, Karfe shidda saura ta bude ido jin budewar kofar, shi da Yusuf suka shigo, Yusuf ya mata ya jiki, ta gaishesa, Sudais na kallonta yace "I think Gobe xa mu je can Kaduna..." Sai a snn ta kallesa hnkli tace "Toh" Yusuf yace "Why nt ka bari ta fara samun Lafiya, she's so sick" Sudais ya nufi kofa yace "Noo, she's leaving tomorrow, for how long am I going to keep her here?" sai kuma ya juyo yace "Or is she going to stay here for ever? You knw presently I will be bringing a woman in here...." Daga haka ya fita, Yusuf ya bi sa da ido, can ya kalle Khadijah yace "What's ur name?" A hankali tace "Khadijah" yace "Khadijah are you sure you are nt lying about ur self" hawaye ne ya cika idonta tana girgixa masa kai tace "To God who made me, I didnt lie." Yau din ma nurse din ce ta kwana gidan tare da Khadijah, karfe bakwai da yan mintuna na safe sudais ya shigo gidan, parlor ya xauna bayan ya ajiye flask din hannunsa suka gaisa da nurse din yace "Don Allah ki sa ta shirya anytime soon xa mu kama hanya..." Ruwan xafi nurse din ta sa ma khadijah tayi wanka, ta fito bayan ta yi wankan tana rawan sanyi, nurse din ta ajiye mata daya daga kayan da sudais ya siyo mata dake cikin leda da lotion sannan ta fita, da kyar khadijah ta daure ta tashi ta shirya ta sa Hijab, sai sannan nurse din ta dawo tana kallonta tace "Ki fito yana jiran ki" daga haka ta fita khadijah ta mike a hankali ta bi bayanta, cup din kunun da sudais ya sa aka siyo mata nurse din ta dauka ta bata, amsa tayi tana kallon cikin cup din, can ta dago a hankali ta kalli sudais dake kallonta ta sauke idonta tace "Ina kwana?" Yace "How you feeling?" Ta gyada kai tace "Da sauki." A hankali ta fara shan kunun tana tsoron kar tayi amai, cikin ikon Allah bata ji Aman ba, ta ajiye kusan Rabin cup tace ya isheta, mikewa yyi yace "Ina jiran ku a waje, you help me lock d door pls ga makulli a jiki" ya fadi hakan yana kallon nurse sannan ya juya ya fita, Khadijah ta bi sa da ido yana sanye cikin bakar suit da wando sai farar T-shirt da necktie banda kyalli bbu abinda cover shoe din kafarsa ke yi, nurse din ta kai flask da kunun cup din kitchen sannan ta fito tana kallon khadijah tace "Toh tashi muje" dafa kujera tayi ta mike nurse din na gaba ta bi bayanta har suka fita nurse din ta rufe kofar da makulli ta cire sannan ta tafi gun motarsa Khadijah na bin ta. Yana daga cikin motar ta mika masa ya karba yace "Shigo in rage maki hanya madam" nurse din tace "Toh" ita ta shiga gaban motar khadijah ta shiga baya, sai bayan sun fita gidan ya fito daga motar ya rufe gidan sannan ya koma ya ja motar suka bar layin, dai dai wani junction nurse din ta sauka tana masa godiya, kudin mota ta bata sannan ya ci gaba da tukinsa. Tun da suka fara tafiya khadijah ke jin xuciyarta ke tashi duk ta xama restless, yana lura da ita ta madubi bai dai ce komai ba, bayan wani lkci tace "Amai nake ji plss" yana kallonta ta madubi yace "Amai??" Toshe bakin ta yyi da hannunta da sauri, ya gangara gefen titi ta bude motar da sauri ta sauka ta dinga kwarara amai bakin hanyan, fitowa yyi ya tsaya jikin mota ya rungume hannu yana kallonta, ta gama Aman tana maida numfashi da kyar, bude front seat yyi ya dauko table water ya mika mata ta karba ta wanke bakin ta da fuskarta sannan ta mike kanta a kasa, ya nuna mata front seat yace "Shiga" a hankali ta karasa ta shiga ya rufe motar sannan ya xaga ya shiga, kasa yyi mata da kujerar ya ci gaba da driving dinsa. Har suka yi nisa sosai a tafiyar bacci take, sudais dake kallonta lkci lkci ya gangara gefen titi yyi parking, suit din jikinsa ya cire ya rufa mata ganin sanyi take ji duk da bai kunna ac ba, ta bude ido a hankali tana kallonsa, ya ci gaba da driving dinsa. Sai da suka shigo traffic a kano ta farka, ya kalleta yace "Xa ki ci wani abu ne?" Da sauri ta girgixa masa kai, yace "Ko xa ki ci apple?" Shiru tayi tana kallon mai hawking apple dake tsaye gefen glass dinsa, ya dau suit dake jikinta ya cire kudi sannan ya mayar ya rufa mata ya sauke glass ya siya apples guda shidda ya ajiye kusa da ita, daya ta dauka ta kai baki a hankali gabanta na faduwa, taji bakin ta ba dadi ta dinga taunan Apple din a hankali tana tsoron kar ta ji amai, har ta ci rabi bata ji aman ba kafin su bar kano har ta cinye biyu daga nan kuma bacci ya dauketa. Khadijah bata sake farkawa ba sai da suka shigo garin kaduna kusan karfe uku, ganin ta tashi yace "Wani anguwa ne gidansu Aliyun yake?" A hankali tace "GRA" bai ce komai ba ya dinga driving a hankali sbda traffic, cikin minti ashirin suka shigo Gra, khadijah ta dinga yi masa kwatance har suka iso dai dai kofar gidansu Aliyu Sudais ya juya yana kallonta.

✨ *NOOR-AL-HAYAT* ✨

Bude motar Sudais yyi ya fita yana kallonta yace "Come down" a hankali ta fito gabanta na faduwa, ya nufi gate din gidan ta bi bayansa kamar me tausayin kasa, da farko Usman mai gadi ya tsaya tambayarsa wanda yake nema amma ganin khadijah ya fito da sauri yana kallonta da mamaki yace "Khadijah?" Ta kirkiri murmushi ta gaishesa, tuni Sudais ya shiga gidan, Khadijah ta bi bayansa Usman yace "Duk kika daga ma kowa hankali ana ta neman ki har station Hajiya ta kai report, to Alhmdllh tunda Allah ya bayyana ki, Alhmdllh" ita dai Khadijah bata ce komai ba ta kalli parking space xuciyarta na bugawa ta ga ba motar Aliyu da na Mumy, Sudais ya danna bell din entrance na gidan a hankali, sau uku yana danna bell din kafin a bude kofar, Anty khadijah ce tsaye bakin kofar kana ganinta kasan bacci take, idanuwanta suka bude sosai ganin khadijah dake gefen Sudais a tsaye tsoro dauke fuskarta, Sudais da yana ganin ta yyi guessing ita ce Anty khadijah ganin kallon da take ma khadijah yace "Assalamu alaikum" hade rai Anty khadijah tayi tace "Wa'alaikumus salam" daga haka ta kalli khadijah tace "Lafiya? Daga ina? Wa ku ke nema?" Sudais yace "Aliyu muke nema" daga haka ya shiga parlorn, Khadijah ta kasa shiga saboda tsoro, Wani kallo Sudais yyi mata yace "Come in" a hankali ta daga kafa ta bi gefen Anty khadijah ta shiga cikin parlorn ita ma, tuni Sudais ya isa kan kujera ya xauna, Anty khadijah dake kallonsa da mamaki tace "Malam nan din fa gidan matan aure ne ka shigo, lafiya? wa kake nema?" Yace "Shi yasa nayi sallama kuma kika amsa min kafin in shigo hajiya" Anty khadijah tace "Me kuma ya hada ku da Aliyu ku ke neman sa?" Sudais yace "Xai fi kyau idan ma bai nan ki yi hakuri ki kira mana shi ya dawo, and mahaifiyarsa hope tana nan?" Anty khadijah tayi mitsi mitsi da ido cike da masifa tace "Nima uwarsa ce ae halak malak, sannan Aliyu bai ma kasar gaba daya idan xaka fadi abinda ke tafe da kai malam ka fada don bacci nake ka taso ni..." Shiru Sudais yyi na d'an lkci kafin ya nuna mata khadijah yace "Kin san wannan yarinyar koh?" Ta kalli khadijah ta kara tsuke fuska tamau tace "Kwarai kuwa, yar aikin da muka dauka kwanaki kenan ta lalata mana xumunci ta shisshige ma d'a na, ta raba ni da shi ina ji ina ganin bana iya cewa komai, wannan shari'ar kuma sai a lahira don duk da barin ta gidan har yau abubuwan da ta cakuda bai gyaru ba, Allah ya isa tsakaninmu da ita" Kuka Khadijah ta fara yi a hankali ta durkusa inda take tsaye, Sudais ya ciro handkerchief dinsa ya share fuskarsa yana kallon khadijah yace "Dena wannan kukan xa kiyi ki bude baki da kanki kiyi mata bayani yanxu" Anty khadijah ta dawo tsakiyar parlorn da sauri tana xaro ido tace "Bayanin me?" Khadijah ta dinga goge hawayen da ya ki tsaya mata, kare mata kallo Anty khadijah ta shiga yi, can ta fashe da dariya irin na mugunta lkci daya kuma ta tsayar da dariyar tana ma Sudais wani matsiyacin kallo tace "Xuwa kayi da ita tace mana tana dauke da ciki?" Sudais yace "Alhmdllh fine, unfortunately kin ma san halin d'an naki kenan" Khadijah ta hade kai da gwiwa tana kuka a raunane, Anty khadijah ta fashe da wani shegen dariya kamar bokanniya tayi mai isarta tayi shiru sannan ta nuna masa kofa fuskarta kamar bata taba dariya ba idonta yyi mitsi mitsi tace "Tun muna mu uku a nan bamu fi haka ba ku tashi ku fice mana a gida" a tsawace ta kare maganar, sudais ya tabe baki yace "Tsawar ki ko ihun ki fa baxae razana ni ba malama... Don haka hold it xai maki amfani gaba a wani wajen" Anty khadijah na huci tace "Xan nuna maka a nan ma yana da amfani, har wannan karuwar xata xo ta makala ma d'ana cikin shegen da tayi a wani wajen saboda ita matsiyaciya ce" Sudais yace "Toh abu mai sauki sai mu je asibiti a ga kwanakin cikin nawa, idan yyi dai dai da kwankin da ya koreta ta bar gidan to nasa ne in sha Allah" Anty khadijah tayi shiru jin abinda sudais yace, auuuu wato Aliyun ne ma ya koreta ashe, ita dai ta dawo kauyen da taje bayan kwana biyu da tafiyarta taji wai ba a ga khadijah ba ko sama ko kasa har station an kai report, Ranta yyi mugun baci a lkcn don bata so Khadijah ta tafi haka nan bata walakanta ta ba kmr yanda ta yi alkawari, me yasa xata tafi bata gama cika burin ta a kan ta ba har hawaye sai da tayi sbda bakin cikin kudin mota da kudin magani da tayi asara, suree a lkcn tayi mugun mamakin yanda Aliyu bai wani damu can ba kamar yanda mahaifiyarsa da baby suka damu amma ita bata taba kawo cewar shi ne ma ya koreta ba, Muryar Sudais ya dawo da Anty khadijah "Hajiya kin yi shiru daga nayi xancen asibiti" abinda ya fada kenan yana kallonta, ta yi masa wani shegen kallo tace "Ji gantalalle, to tunanin da nake daban malam, kuma asibitin ya ci kaza kazan sa baxa a je ba, idan ma cikin Aliyu take dauke da, idan ma ba nasa ba... bbu wanda ya isa ya shigo mana da shege cikin xuri'ar mu, I can swear with the Qur'an fasikanci ba halin Aliyu bane idan ma yyi Ita ta koya masa don kullum dakin sa take yini, wa ya sani ma ko har kwana tana yi can, yayata ba mai xama bace don yanxu xancen da nake ma bata kasar, kullum nice ke tare da su, wai hanata shige ma Aliyu da nake har shi ya janyo min bakin jini gun ta, ta janyo d'a na ya daina ganina da gashi a gidan, yanxu tun muna magana irin ta mutane ba mu dawo na mahaukata ba ku tashi ku fice min a gida kar ku ga d other side of me, ku fita nace" a tsawace ta kare maganar, Sudais dake ta kallonta yyi murmushi yace "Toh cikin nasa dake jikinta tayi ya da shi kenan?" a takaice Anty khadijah tace "Ta xubar, don kaf xuri'ar mu ba shege kuma baxa a fara a kan d'a na ba, idan kuma taga xata iya sai ta raini cikin ta haifa ma kanta ajalinta...." Khadijah dai banda kuka babu abinda take, Sudais ya mike yace "Good, I made her brought me here for just 2 reasons, na farko... is to find out how sincere she is, and na karshe... Is just to let you and ur son knw d pains u are about putting the innocent orphan coz ni dai nasan definitely baxa ku taba accepting cikin ba, kun rabata da warce take da ita a duniya, kun goga mata bakin fenti da ba lallai ya gogu ba har karshen rayuwarta, amma Hajiya ina son ku sani, kamar yanda marainiyar nan tayi bankwana da farin ciki to wallahil azeem kuma hakan ne xai same ku a a xuri'ar ku barin shi Aliyun, He will know no peace da hakkin marainiya a kansa, who knows tunda tace likita ne shi signs na pregnancy din ya gani ya koreta, in sha Allahu sai kun yi da kun sanin abinda ku ka aikata ma yarinyar nan" yana kai wa nan ya karasa gabanta ya ciro ID card a gaban rigarsa ya nuna mata yace "Barrister Aliyu Umar, or just sudais.. we might meet some other time in sha Allah.... Or probably not" ya fadi hakan yana gesturing da hannunsa, khadijah da gabanta yayi mugun faduwa ta dago da sauri tana kallonsa wasu hawayen masu xafi na xubo mata, wani dariya Anty khadijah tayi tana tafe hannu tace "Are you threatening us?" Ya girgixa kai yana murmushi yace "Noo, not at all, kilan idan kika gaya masa aika aikan da yyi xai iya biyota, here is my complimentary card..." Ya ajiye card din gefen kujera, dauka tayi ta yayyage ta xubar nan kasa a gabansa tana huci tana kallonsa, yayi murmushi ya kalli khadijah yace "Tashi mu je" khadijah ta mike a hankali ta bi bayan sudais da har ya isa kofa, tana goge hawayen ta har ta iso gun motarsa, shi ya bude mata motar ta shiga ya rufe ya xaga ya shiga maxaunin driver, har suka hau titi bai ce komai ba ta hade kai da gwiwa tana rera kuka ko xata ji saukin tukukin da xuciyarta ke mata, A bakin hanya sudais yyi parking ganin masallaci ya fita don yin sllh da bottle water ya dawo motar, bayan ya sha ruwan ya ci gaba da driving dinsa, ya hade rai yace "Will you stop those tears and start thinking of how to face reality" ba shiri tayi shiru tana shessheka ya ci gaba da tukin sa. Dab da isha suka

Please Login or Register in order to submit comment