Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

bacci taji kamar an bude kofa, juyawa tayi da sauri don bata ma san kofar a bude yake ba, tayi saurin daukan hijab xata fita suka kusa cin karo bakin kofar dakin.

Komawa baya khadijah tayi tana kallonsa, ya shigo xai rufe kofar ta xaro ido tace "Meye haka Doctor" rufewa yyi ya yana tahowa kusa da ita yace "Tell me why you are avoiding me Khadijah" wani kallo tayi masa tana komawa baya tace "Avoiding din ka kamar ya, bayan gaisuwar da nake maka me kuma kake so daga gareni?" Ganin ya kusa isketa ta juya da sauri xata shige bathroom, yyi hanxarin rikota ya juyo da ita yana kallonta, wani kara tayi ya matseta jikinsa yana mata wani kallo, lkci daya jikinta ya dau rawa tace "Stop it plss Dr, meye haka don Allah ka bari ni bana soo..." yace "Is it a crime don nayi aure?" Sake baki tayi tana kallonsa, can ta hade rai tace "Ban gane ba?" Yace "Ehh tunda nayi aure kika kara dasa min rashin mutunci a kan na da, I showed interest in marrying you kika yi shunning dina, me kuma kike son in maki Khadijah? Tell me me kike so?" A hankali tace "Let go of me now!" ba musu ya saketa yana kallonta, juyowa tayi tana facing dinsa da kyau tace "Ai da kana so na kamar yanda kake ikirari ko me xan ce maka baxai hana ka abinda ke a ranka a kai na ba, kuma abinda yasa baka wani damu ba shine saboda kana da warce kake so da aure... so don't tell me dat Ayman" Ya shafa kai yana mata kallon mamaki, bude kofar parlorn suka ji aka yi, a tare suka kalli door din dakin, ya nufi kofar ya bude ta bi bayansa, tsaye suka ga Jawahir a parlorn ta rike waist da hannu, Khaleel ya karaso kusa da ita kamar mai tausayin kasa ya tsaya yana kallonta, bata yarda ta kallesa ba ta taka ta tafi gun Khadijah dake tsaye bata karaso cikin parlorn ba, wani kallo Jawahir ta dinga mata kafin tayi wani murmushi tace "Khadijah kike kowa? Let me warn you first before taking any action...." Strictly tana mata wani shegen kallo tace "Stay Away from my husband, I repeat my self stay away from him you bitch, idan ma kina da wani kuduri a kansa a ranki ne to kiyi maxa ki goge don wllh ya fi karfin ki nesa nesa ba kusa ba, shi ba sa'an ki bane, shi ba sa'an auren ki ba ne, and let me advice you as a lady.... idan aure kike so ki rufa ma kanki asiri ki koma gidan uban 'ya yan ki wllh hakan kadai ne rufin asirin ki, ke bari ma kiji abinda baki sani ba, da Khaleel ya aure ki a matsayin kishiyata gwara ya auro min budurwa kamar ni mu goga, banda naci da ba kai wahala Ina ke ina Khaleel kina baxawarar, ragowar wani???" Tsawa Khaleel yyi mata ya isa kusa da ita lkci daya idanuwansa suka sauya xuwa ja yace "Kina da hankali Juwairiyya? Kin san wacece ita kike fadi mata wannan maganan gabana?" Wani kallo ta masa ta daga masa hannu tace "Spare me Malam ba da kai nake ba da sa'ata nake, keep ur mouth shut... ban kuma damu in san wacece ba, tunda ta shanye ka ni bai gagareni in kwatar maka yan cin ka ba" Fincikota Khaleel yyi a mugun fusace yace "Did you knw I can give u a dirty slap now?" Jawahir tayi dariya tace "Wllh ka mare ni in rama a kanta, wai ma a kan shegiyar mai makale ma maxajen mutane xaka ce xaka mareni Khaleel?" Kasa ce mata komai Khaleel yyi, can ya runtse ido ya turata yace "Ina guje maki ranan da xaki ji kunya Jawahir, ranan da xaki kasa kallon idanuwan warce kike ma rashin mutunci yanxu, Kuma bayan kin san ta kina ji kina gani xan aureta in hada ku...." Khadijah tayi wani murmushi bata ce komai ba ta juya a hankali ta koma daki ta rufe kofar ta sa key, tafi minti goma kwance kan gado, ita kanta ta rasa me ya hanata yin kuka, kalmomi hudu suka tsaya mata a lkcn, Bitch, Baxawara, ragowar wani, mai makale ma maxan mutane, yanxu jiddah ma kallon da take mata kenan koh?? wani murmushin tayi ta kai hannunta fuskarta jin abu na sauka taji hawaye ne, cikin pillow ta cusa kanta bata sake dagowa ba sai kusan karfe dayan dare shima ta dalilin sanyin dake neman mata illa, da kyar ta mike jikinta na rawa ta fiddo kayan sanyi ta sa, Shureim ya fado mata ta fita parlor da sauri, kwance ta gansa kan kujera ya takure waje daya yana rawar sanyi duk da kayan sanyin jikinsa, ta isa kusa da shi ta daukesa ta rungume sa ta karasa gun kofa ta sa key sannan ta kashe wutan parlorn ta wuce daki, kwantar da Shureim tayi ta rufa masa duvet ta wuce bathroom ta sa ruwan dumi tayi alwala ta fito, sai kusan karfe biyu da wani abu ta kwanta bacci me nauyi ya dauketa. Tun da tayi sllh asuba take ta shirya sauran kayansu, tana gamawa ta tada Shureim ta shirya sa ta basa tea da sauran cake dake gidan, ita ma ta shirya, wayarta ta dauka ta shiga scrolling call log a hankali tana neman number Aliyu duk da bata yi saving ba amma tasan number, ta fi second goma tana kallon number can tayi dialing, bugu biyu ya daga, a hankali yace "Iman, hope all is well?" ta gyada kai kawai tace "Ina kwana" yace "Lafiya lau, Ina Shureim" ta kalli Shureim dake gefenta a xaune, murya can kasa tace "Airport xaka xo ka kai mu pls, if we won't inconvenience you"
Aliyu yace "Sure, yau xaku tafi Nigeria din?" Tace "Ehh" yace "Toh gani xuwa yanxu" daga haka ya katse wayar, bayan kusan minti sha biyar tana xaune ta rungume Shureim kai kana ganinta kasan she is just weak, duk ta xama kamar mara lafiya alhalin babu inda ke mata ciwo, da ta tuna maganganun da Jawahir ta gaya mata jiya da yamma sai tayi murmushin takaici, mikewa tayi ganin kiran Aliyu ta dau karamin jakarta suka fito bayan ta tabbatar komai na gidan ta kashe ta kulle kofar apartment din, ta nufi waje rike da hannun Shureim, Kayan sanyi ne jikinsa shi ma yana jingine jikin mota ya rungume hannunsa, yana ganin Shureim ya isa kusa da shi ya daga sa ya rungumesa a hankali yace "Good morning sweetheart" murmushi yaron yayi yace "Good morning uncle" kallon khadijah dake kallonsu Aliyu yayi ta sunkuyar da kanta da sauri, yace "Good morning" ta ce "Morning" xagawa yayi ta bi bayansa ya bude motar ta shiga ya mika mata Shureim ta xaunar da shi gefenta sanann ya rufe motar ya xaga ya shiga maxaunin driver, driving din some minutes yayi suka isa airport yyi parking waje duk suka fito, Daukar Shureim yayi da damuwa yana kallonta yace "Iman kin bari sanyi ya kama sa da yawa fa" ta kalli Shureim dake tari, sauke idonta tayi tace "And I am very cautious about that, Ni ma ban san yanda aka yi ba" yace "ko yana shan ruwa me sanyi ne?" Ta girgixa masa kai tace "A'a" Ganin yanda yake tarin tace "Ka ajiye sa kar ya maka amai a jiki" Bata rufe baki ba ya kwarara masa aman shayin da ya sha a jikinsa, Aliyu ya dinga shafa masa bayansa yana masa sannu, da damuwa khadijah tace "Toh ina xa mu samu ruwa yanxu, gashi ya bata maka jikin ka" Aliyu na kallon direction da motarsa yake yace "I think I have table water a mota" tace "Toh bani makullin in dauko" mika mata makullin yayi ta koma motar da sauri, ba a dau lkci ba ta dawo da ruwan ta mika masa ya karba, ya sauke Shureim ya ciro handkerchief dinsa ya shiga goge masa bakinsa da jikinsa da ya bata, tana kallonsa tace "Baxa ka wanke masa bakin da ruwan ba?" Yace "Noo, akwai sanyi..." yana gamawa ya mike ya shiga kokarin cire sweatern jikinsa, ganin goran ruwan hannunsa ta xaga bayansa a hankali ta taimaka masa ta cire sweatern, sai ta ganta yar karama kusa da shi don ya fi ta tsayi sosai, lkci daya ya juyo yana kallonta, ta sauke idonta ta saita wajen aman a sweatern ba tare da ta kallesa ba tace "Xuba min ruwan" yace "But it will be very chill kawo in wanke" tace "A'a ni ka xuba min" bude ruwan yayi ya shiga xuba mata tana wanke wajen har ta gama ta shiga kakkabe sweatern, da sauri ya sake ruwan hannunsa ya nufi gun Shureim ganin yanda ya jingina da wani mota, he looks so sick, ya daukesa ya rungumesa yace "Sorry son" Khadijah na kallonsu a hankali tace "Toh kar yaje yana min amai a jirgi" Aliyu ya juyo yana kallonta yace "Noo baxai yi ba, mu je in siya masa drugs mu dawo yanxu" daga haka ya fara tafiya ta bi bayansa. Sai da ta fara shiga motar sannan ya xaga ya mika mata Shureim ya rufe motar ya dawo ya shiga maxaunin driver ya tada motar, drugs ya siya masa na mura da xaxxabi, bayan yyi reversing motar murya can kasa yace "Can I accompany you two Iman, because of his condition, I will postpone my schedules for today..." Khadijah da ke rungume da Shureim tayi shiru bata ce komai ba, ganin ya dau hanyar airport ta kallesa a hankli tace "Ai baka shirya ba, you can't just go without preparation" yace "I will only drive home yanxu inyi dropping motar, mu dawo airport and make the traveling process" Tace "Toh amma ai su Mumy ba su sani ba" ya kalleta a hankli yace "I will explain to her, she will understand" khadijah ta d'an yi shiru, can tace "Toh shkkn" gida ya nufa yayi parking a waje yace "Kilan baki shirya shiga ku gaisa da Mumy ba, beside it's too early, let get a taxi sai ku shiga ku jirani saboda sanyi" ita dai bata ce komai ba ya fita ya tsayar masu da taxi bayan ya fada masa xai d'an jira sa ya shiga gida ya fito, kayansu ya fara transferring xuwa taxin sannan ya xaga ya bude motarsa Khadijah ta fito ta shiga taxin, ya dau ledan maganin Shureim ya bata ta amsa, ya shiga motarsa ya shiga gidan yyi parking. Bayan few minutes ya fito ya hau taxin suka wuce airport, sai kusan karfe tara jirgin su ya tashi. Aliyu na kallon ladyn dake kusa da Khadijah bayan sun yi boarding plane din xai yi magana ta gane abinda yake nufi, tace "Ohk then" daga haka ta koma seat dinsa ya xauna wajenta yana rike da shureim ya kalli Khadijah da ta lumshe ido yace "Ke kin ci abinci kafin ku fito?" Ta bude ido tana kallonsa ta gyara xamanta tace "Na sha shayi" Bai sake cewa komai ba, bayan wani lkcn Shureim yayi bacci yana rungume da shi, da farko kawai lumshe ido tayi ita ma, amma after sometimes bacci ya dauketa, kallonta kawai Aliyu yake, ko ba a fada masa ba yasan she is disturb, there is something eating her but he won't even dare ask what it is, ya lumshe ido tuna farkon ranan da aka fara kawo khadijah aiki gidansu da yanda ta dinga kallon TV bata ma san abinda ake ce mata ba, lkcn da ta taka masa kafa xata kitchen and how she said she is sorry, tun daga sannan dama yasan kaddara ce ya kawota gidansu, bude ido yayi a hankali ya sake kallonta, Khadijah is just beautiful in many ways.... A hankali ya sauke idonsa kan Shureim ya ga babu abinda ya dauko nata sai pink coloured lips, kanta ya ji a shoulder dinsa, ya daga kai yana kallonta, bacci take me nauyi, bai taba ta ba kuma bai tasheta ba ya bar ta a haka. Sai kusan magrib suka sauka Abuja a Nigeria,wani flight din suka sake boarding xuwa kaduna, Adai daita sahu ya kawo su har kofar gidan Umma, Aliyu ya fito Aliyu yana dauke da Shureim, ita ma fito ya dauko mata jakarta ya mika mata ta amsa yace "Ki kai ciki sai ki dawo ki amshe sa" ba musu ta wuce ciki

yana kallon mai napep din yace "Kayi hakuri xaka kai ni Gra yanxu" Bayan wani lkci khadijah ta fito ya isa gabanta ya mika mata yaron dake bacci ta karbesa tana kallonsa tace "Mun gode sosai" d'an murmushi kawai yayi, can yace "Idan ya ci abinci sai ki basa magungunan sa" tace "Toh" yace "Alryt xan wuce gida a gayar min da Umma" daga haka ya shiga adai daita, mai adaidaitan ya ja suka bar wajen ta bi su da kallo, juyawa tayi a sanyaye xata shiga gida suka kusa cin karo da Nanny da ta amshi Shureim hannunta suka wuce ciki, ruwan xafi Nanny ta hada masu bayi, ta ma Shureim wanka sannan khadijah ta shiga, Umma na ba Shureim abinci ta fito, Umma ta kalleta tace "Ni nasan sai sanyi ya kama yaron nan kawai salon ki ja masa kika tafi da shi tunda kin san lkcn sanyi ne" khadijah bata ce komai ba sai murmushi da tayi...

Umma na lura da khadijah dake jujjuya abincin gabanta, ko bata gaya mata ba taga alamar tana da damuwa sosai, Umma tace "Khadijah" da sauri ta dago ganin yanda Umma ke dubanta ta debi shinkafar gabanta ta kai baki, tana son tambayar Umma ko magana tayi mata amma tayi shiru tana cin abincin, Umma tace "Tell me ur problem, what are you thinking of?" Khadijah ta wara manyan idanuwanta tace "Ba komai Umma am just tired ne" Umma tace "Toh ki gama cin abincin sai kiyi isha ki kwanta" A hankali khadijah tace "Toh" da kyar ta dinga tura abincin don gaba daya bata da appetite, why is she finding it hard to erase jawahir's hurtful words from her mind, mikewa tayi daga karshe ta wuce kitchen da plate din shinkafar, tana wankewa a sink Sudais ya fado mata, tasan baxai ji dadi ba ta taho bata gaya masa ba, tayi deciding ta tura masa test kawai ta gaya masa, tana dawowa parlor ta dau wayarta ta xauna gefen Umma ta shiga rubuta masa text din cewar ta dawo yanxu, ta kuma basa hakuri da bata gaya masa ba while coming back, Unfortunately Wayar na bedroom din Sudais, shi kuma ya shiga bathroom, dai dai shigowar jiddah dakin text din ya shigo, Atm dinsa dama tayi niyyar shigowa ta dauka without his consent, ganin wayarsa dake gaban mirror yyi haske ta nufi wayar da sauri, dauka tayi ganin message ta sa finger ta jawo yanda xata iya karanta content din, she was very cautious kar tayi erasing message din daga gaban screen din wayar, sake baki tayi tana kallon text din, ta nanata Ummu Shureim a xuciyarta ya fi a kirga, tayi wani murmushi, wato Amira ya mayar Ummu Shureim don kar ta gane, da sauri ta ajiye wayar jin alamar xai fito ta kashe wutan ta shiga dube dube a drawern mirror with a very serious face, sudais ya fito daure da towel yana kallonta, he was very surprise seeing her... da yake tun da ya kawo mata kayan fadar kishiya ta daina kulasa a gidan, ta kallesa fuska daure tace "Why are you staring at me that way?" Bai damu da abinda tace ba yace "Me kike nema?" A takaice tace "Razor blade, naga wani shekaranjiya a nan ina gyara, I want to sharpen my daughter's pencil tayi assignment" tabe baki yayi yace "Duk Miscellaneous school materials dinta babu sharpener sai kin shigo nan neman razor?" wani kallo tayi masa tace "Ae dai you are not blind kana ganin komai ta kai makaranta xubarwa take ta dawo min haka kamar wata wawiya, or am I to become a razor to sharpen her pencil???" Bata sake saurarensa ba ta fice daga dakin, ya girgixa kai ya nufi gaban mirror, wayarsa ya kunna, ganin text din khadijah gaban wayar ya xaro ido sosai, can ya kalli kofa da sauri, shi dai bai ga alamar da ya nuna ta taba wayar ba, beside da ta dauka ai bude message din xata yi kuma baxai gansa gaban wayar ba, hakan yasa ya tabbatar bata dau wayar ba, Jiddah na komawa daki ta xauna gefen gado tana tunane tunane, to ita yanxu shawarar wa xata nema, anya jiran da tace xata yi har sai an daure auren bai yi nisa ba, kai gaskiya yayi nisa sosai, kawarta Amina ta shiga kira tana dauka tace "Amina don Allah gobe ki taho da sassafe, Ina cikin babban matsala" Aminar tace "Toh in sha Allah xan taho kuwa" Ajiye wayar tayi ta mike tana xaga dakinta, kai ina ma Allah xai bata sa'a taga Amiran nan ta fara nakada mata duka kafin ta bude mata sirrinta da ta sani, fita tayi dakin ta nufi dakinsa ta bude a hankali don taga mai yake, babu kowa dakin kuma ya dauke wayarsa, ta sauka downstairs da gudu, ganin an kunna wutan kitchen ta gane yana can, waya taji yana yi a kitchen din, ta labe jikin bango dai dai nan taji yana cewa "Alryt dear, my regards to him, gobe da safe xan taho..." Da sauri jiddah ta tafi stairs jin xai fito, yana fitowa ta maxa ta juyo kamar tahowanta kenan, Bai kalleta ba kamar yanda bata kallesa ba ya isa kan kujera ya xauna rike da cup din tea. Khadijah na kwance da Umma misalin sha daya na dare Umma tace "Ya Khaleel da matarsa?" Khadijah tace "Suna can lafiya" Umma tace "Ya sani xaki taho?" Khadijah ta gyada kai tace "Ehh ya sani, Umma Aliyu ne yyi accompany din mu" Umma ta daga kai tana kallonta kafin tace "Yana kasar ne?" Khadijah ta gyada kai tace "Ehh can yake xama" Umma bata ce komai ba ta koma ta kwanta, khadijah ta dinga nuna ma Umma kayayyakin da Sudais ya sa mata a lefe ta waya, don komai ya siya sai ya tura mata ko tana so, Umma tace "Maa Sha Allah, Allah sanya Alkhairi" khadijah tace "Ameen" a hankali tace "But Umma how will I cope with studies and marriage, ko ki ce masa kawai ya bar ni a can kasar in gama kawai idan anyi auren" Umma tace "Kwana nawa ne hutun naku?" Khadijah tace "Ba yawa fa, wata daya ne da few weeks" Umma tace "Bikin kuma nan da sati nawa yace maki?" A hankali tace "Biyu" Umma tace "Kema kin san baxai hana ki karatu ba, Kar ma ki ce masa komai, but surely xai bari ki gama" khadijah tace "Toh Umma" Umma tace "Allah ya kai mu lokacin lafiya" a hankali khadijah tace "Ameen, Amma Umma sai gabana yayi ta faduwa" Umma tace "Sai ki yawaita addu'a, babu abinda mutum ya isa ya maki wanda Allah bai maki ba" Washegari da safe tun da Jiddah ta tashi take tunanin yanda xa ayi ta san inda Sudais xai je ganin har ya gama shiryawa cikin suit yana xaune dining yana shan shayi ta sa hijab ta fita kamar xata xubda shara, ko amsa gaisuwar mai gadi bata yi ba sanin duk bakinsu daya da sudais komai ya faru gidan sai Sudais ya tambayesa, kamar kawayenta nawa suka xo a rana kuma duk da jan kunne da take masa sai ya fada masa, duk ta fita gidan to sai Sudais ya sani, har bakin titi ta taka suka gaisa da mai filling din gas dake bakin titi da d'an shagon container sa, yace "Maman Amira kaddai ki ce har gas ya kare in je in dauka, naga ko sati biyu ba ayi ba na cika" Tace "A Haba kamar muna shan gas a gidan, ba shi ya kawo ni ba malam rabilu, wani taimako nake so ka min don Allah, Kuma wlh ni me biyan ka ko nawa ne, amma kuma sirri ne tsakanina da kai" tana magana ne tana kallon cikin layi ko xata hango motar Sudais, Rabilu yace "Tohhh... Sirri kuma maman Amira" tace "Kaga ba wani abu bane, yanxun nan Abban Amira xai fito a motarsa, to don Allah so nake ka tada Machine dinka ka bi bayansa ka gano min inda xa shi, wllh ko nawa ka bukata xan biya ka Rabilu, kar ka ji komai ba wani sanin ka yayi ba" Dariya sosai mutumin yayi yace "Kai yanxu shi Barristern xan bi a machine maman Amira?" Ta hade rai tace "Kai dai biyan ka xan yi babu ruwan ka, Kuma ku din ne sai da haka, ban yarda da takun sa bane kwanan nan, yanxu dai don Allah ka rufe container din nan ka hau kan babur din ka ka jira sa anytime soon xai fito na sani, xuwa anjima xan dawo in ji yaya, da kudin ka kuma xan taho in sha Allah" daga haka ta koma cikin layin, ta kusa gida sai ga motar sudais kuwa, Dauke kayi tayi, ya tsayar da motar yana kallonta yace "Jiddah?" Ta juya fuska daure tana kallonsa, yace "Da ixinin wa kika fita, Kuma ina kika je?" Tana nuna masa gidan dake kusa da nasu tace "Matar gidan can ta kira ni yaronta ya kone da mai, Toh sai kar in je? Ko baka ga a gigice na fita ba?" Rufe glass dinsa yayi ya ja motarsa ya wuce, ta tabe baki ta shige cikin gida, office Sudais ya nufa direct don client na jiran sa. Khadijah dake kitchen tana duba miyar kubewar da Nanny ta daura ta juya tana kallon Shureim dake mika mata waya, ta hade rai tace "Waye yake kira yanxu kuma?" Yace "Doctor" tace "Nace kar ka sake kawowa baka ji Koh" yace "Am sorry Anty" daga ya juya ya koma da wayar, Khaleel ne ke kiranta tun daxu ta ki daukar wayar, da ya kira sai Shureim ya kawo wayar don yana hannunsa, Umma dake jin su a parlor tace "Wa ke kiran ki baxa ki dauka ba khadijah?" Turo baki tayi tana juya miyar tace "Umma number ne and I don't want to pick" Umma bata ce komai ba duk da taji san da Shureim yace doctor ne, khadijah ta sauke miyar ganin yayi ta hade plates xata wanke sai ga Shureim ya dawo da waya yana mika mata, wani kallo tayi masa tace "Kana son duka koh?" Kamar xai yi kuka yace "Anty it's a number, it's not saved" karban wayar tayi taga Aliyu ke kiranta, tayi picking call din ta kai kunne tayi shiru, a hankali yace "Iman ya kike?" Tace "Lafiya lau ya su Mumy?" Yace "They are fine, Ina Shureim?" Tace "Gashi" yace "Ya jikin sa?" Tace "Ya ji sauki, only the cough" yace "Ohk basa wayar" Mika ma Shureim wayar tayi ta ci gaba da abinda take, bayan wani lkci ya dawo mata da wayar, share hannunta tayi ta amsa ta kai kunne, Aliyu yace "Baby wai xata xo wajen ki, is that okay by you?" Khadijah tace "Yaushe xata xo?" Yace "Anjima xan kawo ta" Khadijah taji dadi har ranta tace "Toh ina jiran ta sai ta xo" yace "Ohk" daga haka ya katse wayar. Bayan azahar Umma na xaune parlor da Nanny suna llissafin abubuwan da xa a siyo a Dubai na kayan daki, ita dai khadijah tana kwance tana danna wayarta Kiran Aliyu ya shigo wayar, Dagawa tayi ta kai kunne tana jin sa yace "Muna kofar gida Iman" khadijah ta mike xaune tace "Ohk ga ni fitowa" katse wayar tayi tana kallon Umma tace "Umma ta iso bari in je in shigo da ita" Umma tace "Toh sai kin dawo" mayafinta ta yafa ta fita xuwa kofar gida, fitowa baby tayi daga mota ganinta ta karaso da sauri ta rungumeta tace "Khadijah..." Khadijah tayi murmushi tace "Baby ya su Mumy" Baby tace "Suna gida, sun ce a gaishe

Please Login or Register in order to submit comment