Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yaran don ma ba ta shayar da su, wahalansu yyi yawa, da daya ya fara kuka dayan xai cafke duk su rikitata, satinsu uku a Abuja sudais ya sa aka samar masa Nanny don tausayi take basa barin yanda ya ga ta rame, kamar kar Nanny ta xo lkci daya khadijah ta watsar da lamarin yaran gaba daya ya koma nanny ce ke masu komai ita sai dai tayi girki tayi bacci, abinda sudais ya guda kenan tun farko but saboda tausayinta da yake kawai ya kyaleta, nanny na xuwa gidan da kwana biyar sudais ya tafi damaturu don duba su Mami don Allah ma yasan yana kewar mahaifiyar tasa, kwana biyu yyi a can ya dawo Abuja bayan ya sanar ma Mami yawancin aikinsa yanxu a Abuja yake yi, ta yi masa addu'a da fatan alkhairi. karfe uku saura na yamma sudais ya shigo gidansa na Abuja, sai dai a waje yyi parking don ya gaji da yawa, babu kowa parlorn sai Ac dake ta aiki da kamshin dake tashi, ya haura sama ya bude kofar Nanny da yan biyu a hankali, suna xaune cikin keken koyan xamansu sai wasa take masu da abun jikin keken suna ta dariya gaba daya, sosai matar ke son su don yaran akwai shiga rai, Nannyn baxata wuce shekara talatin da biyar ba, tana ganin Sudais ta mike tace "Sannu da dawowa yallabai" yace "Sannu" ya karasa cikin dakin yana kallon cute yaran dake ta kallonsa, kyawawan karshe ne yan biyun ga manyan idanuwa ga su farare kal kamar larabawa, da wuya mutum ya kallesu bai kara kallonsu ba, ya rasa ne yasa khadijah ta ki sonsu har ynxu, daukansu yayi one by one yayi kissing dinsu suna masa dariya ya ajiye su ya fita dakin, bude kofar dakin da Khadijah take yyi, ya ganta kwance daga ita sai yar doguwar riga tana bacci, ya kusa minti biyu tsaye yana kallonta kafin ya rufe mata kofar ya wuce nasa dakin, wanka yyi ya dauro alwala ya fito ya saka jallabiyarsa ya gabatar da sallahn azahar sannan ya kwanta, Nanny ce ta shiga dakin Khadijah ganin har kusan la'asar ba ta fito ba alamar bata san Sudais ya dawo ba, ita duk tunaninta sudais mijinta ne, cike da natsuwa ta tasheta tace "Yi hakuri na tashe ki madam, yallabai ya dawo" da sauri khadijah ta mike xaune tace "Yaushe?" Nanny tace "Tun daxu" Khadijah tace "Toh" Nanny ta juya ta wuce sannan khadijah ta mike ta tafi bayi ta wanke fuskarta ta fito ta dau Hijab har kasa ta sa ta fita, a hankali ta tura kofar dakin sa ta gansa yyi rub da ciki yana bacci, a hankali ta isa kusa da shi ta durkusa tana kallon kyakkyawan fuskarsa, bude manyan idonsa yyi a hankali, ta koma baya da sauri ta fara kame kame, ya mayar da idonsa ya rufe na kusan minti daya kafin ya bude ya mike xaune, murmushi tayi murya can kasa tace "Sannu da dawowa, baka ce yau xaka dawo ba da ka kira da safe" yace "I was thinking sai gobe xan taho" tace "Ya hanya? Ya su mama" Yace "Alhmdllh, ya twins? duk da nasan kilan duk yau baki gansu ba" sauke idonta tayi daga kallonsa jin yyi shiru ta daga kai suka hada ido, wara mata ido yyi, ta yi murmushi tace "Me xaka ci?" Yace "Komai ma" mikewa tayi tace "Toh bari in yi maka" daga haka ta fita ya koma ya kwanta. A hankali watanni suka dinga ja kamar wasa sai ga shi su shureim sun yi wata bakwai, babu inda basa xuwa da rarrafe, wani shakuwa ne ba na wasa ba tsakaninsu da Sudais, ji yake da su kamar ya hadiye su don so, in har suna wasa a Parlor to suna ganin khadijah suke barin wajen da gudu su tafi gun Nannynsu, sai dai ta tabe baki ko tayi tsaki, har lkcn kamanninsu sak na Aliyu barin hancinsu da idanuwa shi sa take kara jin bata son su, ko ina na gidan kayan wasan su ne, don komai sudais ya gani na yara ko da ya fi karfinsu sai ya siyo masu, dakinsu ya koma kamar na siyar da kayan wasa, yau lahadi sudais na xaune garden shi kadai files a gabansa kana ganinsa kasan aiki yake, lkci daya ya rufe files din gabansa ya lumshe ido, for how long xai ci gaba da ajiye khadijah da yaranta a gidansa, har ransa yake jin baxai iya rabuwa da su ba, but duk ranan da Mami ta gano abinda yake aikatawa yasan that day won't be funny, then meye xai yi da xai kasance da Khadijah da yaranta na har abada With his parent consent, bude ido yyi a hankali ya furta abinda ke ransa a ciki "I shud marry her" girgixa kai yyi ya na murmushi lkci daya abinda Yusuf ya gaya masa one year ago a mota ya fado masa. Khadijah na bedroom ita kadai tana ta jiran jin shigowar sudais amma bai shigo ba, ita kanta bata san me yasa take son ya shigo ba, kuma tasan yana can garden, mikewa tayi ta sa mayafinta ta fita xuwa can din ta tsaya kusa da wani flower yanda baxai ganta ba ta dinga kallonsa, kananun kaya ne jikinsa na 3qtr da shirt da bai yi buttoning ba, tsura ma pen din table dake gabansa ido yyi har lkcn yana tunani, kamar ance ya daga kai suka yi ido hudu da Khadijah, dauke kai tayi da sauri, sai kuma ta jiya ta bar wajen ya bi ta da kallo, murmushi yyi ya na shafa kansa don irin kallon nan da Khadijah ke yi masa ko da yaushe dariya yake ba sa, sau tari ya sha kamata tana kallonsa sai ta fuske, shi din ma yana kallonta amma with swags, kwashe files din gabansa yyi don dama ya gaji ya mike ya wuce ciki yana rike da su, sai da ya fara lekawa dakinsu shureim yaga yanda Nanny ta cika masu kayan wasa a gaba suna ta fama, suna ganinsa suka rarrafo xasu taho gunsa, da sauri ya juya ya bar wajen don bacci yake son yi, a tare suka fara kuka yana tsaye har suka fito corridor nemansa yyi murmushi ya durkusa ya daukesu duk biyun amma da kyar tsabar weight dinsu, ya wuce dakinsa da su, ajiye su yyi kan gado ya kwanta suka haye kansa gaba daya ya lumshe ido yace "Yanxu baxa ku bar ni inyi bacci ba" kamar sun ji mai yace suka fara dariya har da kwantawa jikinsa ya rungumesu gaba daya, ganin da gaske baxa su bar sa yyi baccin ba ya dau waya ya kira Khadijah, tana dagawa yace "Plss ki xo ki dau su Shureim basa son inyi bacci" Khadijah bata ce komai ba ya katse wayar, ta tabe baki ta sa Hijab ta fito ta shiga dakinsa karasawa tayi kusa da gadon suna ganinta suka kankamesa sudais yace "Meye amfanin yaranki na tsoron ki" bata tankasa ba ta kai hannu xata dau little sudais ya fasa ihu dan uwansa na taya sa suka rirrike sudais, murmushi kawai sudais yake yana kallon khadijah da ta hade rai tana kallonsu, fixgo shureim tayi ya fashe da kuka a tsorace har lkcn yaki yarda ya sake sudais. Sudais ya fixgota ita ma har ta fada kansa ya daure fuska yace "Ciwo xa ki ji masa" xata tashi ya ki saketa yana kallonta kamar yanda yaran ta ma ke kallonta, murmushi tayi ta xame kanta ta xauna kasa, murya can kasa sudais yace "Tafi basa son daukan naki" kamar sun ji abinda yace suka kara yin lamo a jikinsa, Khadijah ta mike ta nufi kofa sudais ya bi ta da kallo har ta fita sannan ya lumshe ido a hankali. A ranan da su Shureim suka cika wata goma Sudais ya sa Nanny ta shirya su kamar dai yanda ya saba duk lahadi xa su fita, yanxu kam babu inda shureim bai xuwa da kafafuwansa banda little Sudais da tashi ma wahala yake masa, kaya iri daya nanny ta sa masu as usual, kwankwasa kofar dakin Khadijah sudais yayi, tana xaune gaban madubi tana rubuta a farar takarda jin an kwankwasa kofa ta dauke takardar da sauri xata boye, dai dai nan ya bude kofar, cukuikuye papernta tayi, ya dinga kallonta yace "What's that" girgixa masa kai tayi ba tare da ta bari ta kallesa ba da sauri tace "Bakomai" yace "Uhn, sure?" Kin cewa komai tayi, yace "Toh ki shirya xan fita da twins sai ki raka mu" ta girgixa kai tace "Baxan je ba" yace "Why?" Sai a sannan ta kallesa, saurin sunkuyar da kanta tayi, ya d'an yi murmushi ya juya ya fita, bude takardar tayi tana duba abinda ta rubuta, a hankali ta linke ta boye sa sannan ta sa Hijab dinta ta fita, har ya sauka parlor da su little sudais, ya juya ya kalleta yace "Ko d'an kwalliyan ma baxa ki yi ba" tace "Ehh" ya tabe baki ya fita tare da yaran ta bi bayan su, driving yake Khadijah na back seat da twins din shi kuma yana kallonsu ta madubi, horn ya ji an yi ya juya, da mamaki yake kallon matar da ta fito daga wani gida a motar ta kafin ya tsayar da tasa motar ya bude ya fito, ita ma ta sauka tace "Aliyu dama kana Abuja?" Ya kirkiri murmushi yace "Wallahi kuwa Mama, ina yini?" Tace "Lafiya lau Aliyu" lekan bayan motarsa ta dinga yi kafin tace "Kar dai kayi aure Hajiya Khadijah bata gaya min ba naga mace da yara a mota" sosai gabansa ya fadi yace "A'a mama, matar abokina ne da yaranta" Tace "Ayyo wajen ka suka xo?" Yace "A'a ajiye su xan je in yi" shi kansa ya san he just sound stupid, yayi saurin cewa "Amma mama kun dawo ne?" Tace "Noo, na xo yin abu ne yau sati na daya, amma ina jin jibi xan koma" yace "Holland din?" Tace "In sha Allah" yace "Toh Allah kai mu mama" tace "Ameen Aliyu, Allah yayi maku albarka" yana murmushi yace "Ameen" daga haka ya koma motarsa har lkcn gabansa na faduwa, Hajiya Rukayya aminiyar Mami ce don childhood frnds ne ma, ita ce ta sa Mami tayi ma Abba magana ya siya masa gida a layin lkcn anguwar na sabo, ita ma kuma a anguwar take amma sai su yi wata da watanni basa Nigeria da yaranta, har sudais ya kai bakin titi Hajiya Rukayya bata dauke idonta a kan motarsa ba, mace da yara a motarsa kuma yace matar abokinsa, kallon gidan Sudais din tayi kafin ta karasa can da kafa, kwankwasa gate ta dinga yi ko mai gadi xai bude amma shiru, can sai ga Nanny ta fito ta bude gate din, gaisheta Nanny tayi, Hajiya Rukayya tace "Ya kike" Nanny tace "Lafiya lau sai dai Masu gidan basa nan" shiru Hajiya Rukayya tayi kafin tace "Shi da matar suka fita kenan?" Nanny tace "Ehh har da yan biyun" Hajiya Rukayya tace "Toh shkkn" daga haka ta bar wajen da sauri ta wuce gidanta tana tunanin to ko dai karya sudais yyi mata yace bai yi aure ba, tana shiga motarta ta dau waya ta shiga kiran Mami.

Gaisawa Hajiya Rukayya suka yi da Mami, Mami tace "Ki ce kun dawo Nigeria kenan Hajiya" Hajiya Rukayya tace "Ina fa, just came a week ago to put things in other, ina ga xuwa jibi ma xan koma" Mami tace "Ayya, ashe baxa mu hadu ba kenan, ya yarana fa?" Hajiya Rukayya tace "Suna can, Jaheed ne dai ke Lagos" Mami tace "Toh maa sha Allah, naji dadin da kika kira wllh, kina Abuja koh?" Hajiya Rukayya tayi dariya tace "Toh ai baki sani ba, Aliyu na gani ma ya sa na kira ki yanxu" Mami tace "Haba dai..." Hajiya Rukayya tace "Wallahi kuwa ashe ya dawo gidansa, na fito gida xan je mall yanxu na gansa a mota shi ma" Mami tace "Toh, ni ban san me yasa ya koma Abuja da xama ba yanxu, sai mu yi wata ma ba mu gansa ba, idan nayi magana yace aiki" Hajiya Rukayya ta d'an yi shiru kafin tace "Amma yyi aure ne Hajiya Khadijah?" Mami tace "Ina fa, ba na gaya maki abinda yayi ma yarinyar nan da yake nema jiddah ba, da suka fisa iskanci ai mayar masa da kayansa suka yi, kinsan halin Abbansu, to in gaya maki bai taking Wani action ba sai ma cewa da yyi ai bai isa aure ba, kinga yayi supporting dinsa kenan, ni dai nasan in har yarinyar nan yaudararta yyi hakkinta baxai bar sa ba" Hajiya Rukayya tace "Ikon Allah, to ni kuma da wata na gansa da yara har biyu a mota, da na tambayesa aure yyi sai ce min yyi matar abokin sa ce ai xai maida ta gida, to mutum ba iyali me matar abokin sa taje yi gidansa, and the way he replied, gaskiya it's suspicious, to da yake kinsan ai bbu nisa tsakanin gidan nasa da namu, in gaya maki na taka da kafa har na isa gidan na kwankwasa gate sai ga wata da alamar dai yar aiki ce ta fito, da na tambayeta mai gidan sai ce min tayi ya fita da familyn sa yanxu, abun dubawa a nan shine anya Hajiya Khadijah ba aure Aliyu ya xo yyi a Abuja ba tare da sanin ku ba, yaran fa yan watanni ne" tun da ta fara xancen Mami ke saurarata baki sake, can Mami ta sauke wani ajiyar xuciya tana share xufar da ya keto mata tace "Hajiya Rukayya yaushe kika ce xa ki koma?" Hajiya Rukayya tace "Ranan talata in sha Allah" Mami tace "Toh gobe da sassafe xan taho Abujan, ina shiga xan kira ki don Allah" Hajiya Rukayya tace "A'a ke kuwa a bi komai a sannu mana, ko ni ba sai in je in samesa ba, idan ba haka xancen yake ba fa? kuma ace da gasken matar abokin sa ce, ke dai kawai ki bar komai a hannuna xan same sa da kaina sai kace ba d'a na ba Hajiya" Mami ta girgixa kai tace "Inaa ai dole ne kawai in taho Hajiya Rukayya, dama kusan shekara daya kenan da Aliyu ya canxa hali totally ya dawo kamar mara gaskiya tun bai bar Damaturu ba, kar ki ce masa komai ki jira sai na xo, idan ma haka ne idan ma ba haka bane duk xa mu sani, nagode sosai Hajiya, sai kin ji ni" daga haka Mami ta katse wayar ta mike tana jin xuciyarta na tafarfasa, mace da yara? Ina ya samo su? Wani murmushi tayi ta fita daga dakin. Shopping sudais yyi ma twins din na abubuwan da suke ci tun daga kan golden morn, biscuits, custards, quaker oats, chocolates da sweets, sai Pampers da turaren yara, ita dai Khadijah na rike da little sudais dake kuka baya son ta dauke sa sai mika ma Sudais hannu yake, shureim kuwa sai kara kankame Sudais yake wai kar Khadijah ta karbesa shi ma, Duk little sudais ya cika shopping mall din da kuka, Sudais yace "Yanxu meye amfanin haka yaron ki baya son ki daukesa Amira?" Ita dai bata ce komai ba yace "Amira, are you thinking xa mu dauwama tare ne na har abada ne? Of course no, yaran nan ne dolen ki they are now ur new world, show them love Amira" mika mata trolleyn yyi ya karbi yaron ba shiri yyi tsit yana leko uwar tasa, duk yanda sudais yyi da ita ta dauki abinda take bukata a mall din kin daukan komai tayi, ya siya masu ice cream sannan suka bar mall din, har suka koma gida Khadijah ta ki cewa komai, yana gama parking nanny ta fito ta dau yaran gaba daya ta wuce ciki, juyawa yyi ya kalli khadijah da ta bude mota xata fita yace "Wait" sannan ya fito ya shiga back seat din motar ya rufe yana kallonta, hade kai tayi gwiwa tana shesshekar kuka, ya dago kanta a hankali yace "Daga na gaya maki gaskiya Amira?" Hawaye na sakko mata cikin rawar murya tace "Toh nice nace su dinga tsoro na?" Murmushi yyi yana kallon kwayar idonta yace "Ehh mana, ai ke ce baki sonsu, kalli fa ko breast baki basu ba kin yi xaton sun manta ne" turo baki tayi ta dauke kai tace "Amma sun san na basu sau daya ai" dariya ta basa ya dinga kallonta kafin yyi murmushi, ya kamo hannunta ya lumshe ido yace "In dai kina jin maganata, and i meant a lot to you, daga yau ki fara son yaran nan Amira" sunkuyar da kanta tayi bata ce komai ba, ganin yanda yake murxa mata hannu a hankali ta kwace hannunta ta koma daya side din ta bude motar ta fita, fitowa yyi shi ma ya bi bayanta. Kasa bacci daren ranan sudais yyi ya rasa dalili, duk ya ji he is restless, bayan ya gama sallolinsa misalin karfe biyu ya bude kofar dakinsa ya fito, khadijah dake xaune daki ita ma idonta biyu ta ajiye takardar hannunta da sauri karkashin pillow tana kallon kofar dakin, jin ba a bude ba ta sauka kan gado ta dau hijab ta daura kan sleeping wear din jikinta sannan ta bude kofa ta fita, downstairs ta sauka, tsaye ta gansa tsakiyar parlorn, jin ana sakkowa stairs ya juya da sauri, har ta isa inda yake kallonta yake, yace "Why are you awake by this time" ta girgixa masa kai kawai, xaunawa yyi kan kujera ta xauna kasa kusa da shi, jin bai ce komai ba murya can kasa tace "Daxu a shopping mall kace min we are not going to be together forever, why?" Muryarta na rawa ta karashe maganar, ido ya tsura mata, hawaye ya shiga sakkowa idonta, da sauri yace "Kuka kuma, I didn't mean it Amira, abinda nake nufi shine...." Sai kuma yyi shiru, ta hade kanta da kujera tana kuka cikin raunin murya tace "Don Allah kar kace xaka bar ni watarana, I have nobody, just you, kai kadai gare ni yanxu, idan ka bar ni ya xan yi, who will take care of the boys" jikinsa yyi mugun sanyi ya sakko kasa yana kallonta ya dago kanta, cikin sanyin murya yace "Ban ce xan bar ku ba Amira, what I mean is death, kinsan rayuwar ba shi da tabbas" xaro ido tayi tana kallonsa ko kiftawa babu sai kuma ta kara fashewa da matsanancin kuka tace "Mutuwa xaka yi ka bar ni?" Dariya ta basa sosai, yace "Ni bance xan mutu ba, kuma idan mutum ya mutu ai lkcn sa ne yyi" rike hannunsa tayi hawaye na sakko mata tace "Baxa ka mutu ba until Allah is pleased with your soul in sha Allah" murmushi yayi yace "In sha Allah, kamar yanda ke ma baxa ki mutu ki bar ni da yaran ba" shiru ta yi bata ce komai ba, a hankali tace "Gwara su su mutu ai" lkci daya mood dinsa ya canxa yana kallonta, ta sunkuyar da kai, da mamaki yace "Ashe baki da hankali Amira" a hankli tace "Kayi hakuri" rasa ma abinda xai ce mata yyi, can yace "Toh tafi ki kwanta" tace "Toh kai fah" yace "Bana jin bacci" tace "Nima" hade rai yyi yace "Tashi ki tafi nace" kamar xata yi kuka tace "Kai ma ka tashi" murmushi yyi ya mike ita ma ta tashi, yana kallonta yace "to mu je" ita ta fara tafiya sannan ya bi bayanta ta jira ya shiga dakinsa sannan ita ma ta shiga, daga masa hannu ta yi, yyi murmushi ya rufe kofarsa, ita ma ta rufe nata, kwanciya yyi ya rasa tunanin da xai yi a kan Khadijah, is it that.... He love her or what" lumshe ido yyi bai son tunanin daga haka bacci ya daukesa. Da asuba tun da ya dawo masallaci gabansa ke faduwa, he don't knw why, har gari ya waye yana kwance idonsa biyu a bedroom dinsa, kamar wanda ya tuna abu ya mike xaune da sauri, jiya da yamma Hajiya Rukayya... Tunanin da ya xo masa kai knn, ya dafe kansa a xuciyarsa yace to sai ta fara gaya ma Mami ta gansa da mace da yara, noo yasan she won't, but it's better su d'an bar anguwar for sometimes, da kyar ya mike daga karshe ya fita dakin ya shiga na twins har nanny ta masu wanka tana basu golden morn suna xaune cikin kekensu, suna ganinsa suka fara daga hannu ya daukesa takwaransa har da kuka, karasawa yyi ya daukesu gaba daya yana murmushi Sanin kuka xa su yi idan ya fita ya bar su, ya koma dakinsa da su, yana son fita misalin sha daya amma yan biyun sun ki bacci, bell ya ji aka danna downstairs, sai da gabansa ya fadi duk da bai san me yasa ba, ya mike xai fita twins suka fara kuka, dawowa yyi ya daukesu ya fita, ganin khadijah bakin kofar xata bude yasa shi tsayawa kan stairs, tun da yake bai taba jin faduwar gaban da yaji a lkcn ba ganin Mami ta shigo parlorn Hajiya Rukayya na biye da ita a baya.

Mami na kallon Aliyu da wani expression tace "Aliyu??? is this the life you chose for ur self? Is this the home training I gave to you" Sudais ya sauke kansa daga kallonta lkci daya jikinsa yyi sanyu ya sauko downstairs a har sannan yana rike da yaran, a hankali yace "No Mami, I didn't choose this life for my self...." Katse sa ta yi cikin tsawa tace "Aliyu ka fada min wacece yarinyar nan? Who is she? Meye hadin ka da ita?" Ya hadiye abu da kyar yace "Mami... Mami ba lallai ki yarda da abinda xan ce maki ba, but Mami ki kira Yusuf xai gaya maki wacece ita kilan shi ki yarda da shi" wani mugun kallo Mami ta dinga yi masa xuciyarta na tafarfasa tace "In kira Yusuf? saboda ina tsoron ku? To bani da wannan lkcn, Aliyu dama abinda ka dawo yi a Abuja kenan? Mace ka dauka ka ajiye gida ku ke rayuwa tare.... Wa iyaxubillah" Hajiya Rukayya tayi saurin dakatar da ita tace "Haba, ki sauraresa tukun Hajiya" daga haka ta mayar da dubanta kan sudais tace "Ka gaya mana wacece ita Aliyu" Sudais ya kalli khadijah da ta sunkuyar da kanta hawaye na sauka idonta, rasa abinda xai ce yyi duk jikinsa yyi mugun sanyi, Hajiya Rukayya tace "Toh bani number Yusuf din, ni xan kira sa" Mika masa wayarta ta yi ya amsa ya sa mata number Yusuf yana fara ring Hajiya Rukayya ta karba, Yusuf na dagawa Mami ta karbe daga hannun Hajiya Rukayya, daga daya bangaren Yusuf yayi sallama, Mami ta amsa tace "Yusuf kana ji na?" Shiru yyi jin kamar muryar Mami, a fusace tace "Ba da Yusuf nake magana ba" Yusuf ya kwalalo ido yace "Ehh ina nine mami, ina kwana," bata damu da amsa gaisuwarsa ba tace "Yusuf ka gaya min wacece yarinyar da Aliyu ya ajiye gidansa da yara" Sai da gaban Yusuf ya fadi ya mike daga xaunen da yake, can ya koma ya xauna a hankali yace "Mami it's not what u are thinking wllh yarinyar nan da kike gani taimakonta kawai Sudais yyi, she is an orphan...." Lkci daya idon Mami ya kada ta katse sa hade da kunduma masa xagi tace "An orphan??? Bata san hanyar orphanage ba ko kuma kai me yasa baka yi mata taimakon ba sai shi, ya ajiye mace da ba muharramarsa ba kace yana taimakonta Yusuf, tun da uwar ka ta haife ka ka taba jin haka?? su kuma yaran na waye?" A sanyaye Yusuf yace "Nata ne Mami" Mami na jin haka ta katse wayar tana kallon Hajiya Rukayya lkci daya idonta ya kawo ruwa tace "Kina jin halin yaran yanxu koh Rukayya, yanxu ka haifi yaro baka haifi halinsa ba, ni dama da dadewa na lura da takun Aliyu, mu Aliyu xai kunyata a idon duniya? irin tarbiyar da ni da

Please Login or Register in order to submit comment