Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya isa tsakanina da khadijah, she just ruin my family, yar uwata ce amma ko bare baxai min haka ba, yanxu tana sane da abun nan amma bata gaya min ba, she never told me anything about it da babu abinda xai hana ni nemo Iman duk inda take, greatest mistake din Aliyu shine ce mata da yayi ta tafi, kuma wllh ni shaida ce tun daga ranan Aliyu bai sake samun kwanciyar hankali ba, kuma bai taba gaya min abinda ya faru ba sai dai yace in taya sa da addu'a, gashi nan dai har yanxu ya ki yin aure" Ko kadan khadijah bata damu da abinda mumy take fada ba ku ma bai shigeta ba, Briefly Sudais ya ba ma Mumy labarin yanda rayuwa ya kasance ma khadijah bayan Aliyu yace ta tafi... Ban da kuka babu abinda Mumy take duk jikinta yyi mugun sanyi tausayin Khadijah ya cika ta, ita dai tasan da tasan abinda ya faru kenan da ta sa Aliyu ya nemo ta Duk inda take amma yyi wautan rashin gaya mata, Mumy ta mike ta isa gun khadijah ta duka gabanta tana kuka tace "Khadijah ina neman alfarmar ki yafe ma Aliyu, ko don albarkaci na forgive him plss, kadararrku ce a haka, don haka ki ta godiya ma Allah, amma kiyi hakuri kar ki bar sa a xuciyar ki" Khadijah da xuciyarta ya mata rauni ita ma tana kukan tace "Mumy ni fa na yafe masa amma yayi hakuri ya bani yaran don Allah" mikewa Mumy tayi tace "Xai baki Khadijah, ina gidan ku yake yanxu?" Khadijah ta fada mata address din, Mumy tace "Toh kiyi hakuri ku je na maki alkawarin xa mu biyo ku da yaran yanxu" shiru khadijah tayi tana kallonta xuciyarta na bugawa sai take ga kamar kawai labari mumy take mata don ta tafi, baxa su bata yaran ba, Sudais ya mike yace "Toh shkkn, Ma... Muna xuba ido sai kun xo" Mumy ta kalli khaleel a sanyaye tace "Ku yi hakuri balarabe, Allah ya ba ku lada, amma don Allah ku bar jin haushin Aliyu ba yin kansa bane, nasan xa ku yi ta mamakin jin ina cewa ba yin kansa bane kamar na shiga xuciyarsa, but plss just do consider him" Murmushi khaleel yyi ya mike yace "Bakomai Ummu, Allah ya kara girma" tace "Amin nagode" daga haka ya nufi kofa, sudais ya kara mata sallama ya bi bayan khaleel, Khadijah na biye da su a baya tana goge idonta, ta kasa kallon baby dake bakin kofa har lkcn, A hankali baby tace "Iman plss forgive me brother, ki yafe masa don Allah" hawaye na sakkowa idonta take maganar, Khadijah tayi murmushin karfin hali tace "Na yafe masa" daga haka ta fita parlorn. Sama Mumy ta wuce xuwa dakin Anty Khadijah ta ganta xaune tana bude jikin iklima ganin wasu kuraje da ke feso mata ta ko ina, Mumy tace "Khadijah, a duk xaman mu dake in har na taba cutar ki Allah ya saka maki, in kuma ke kika cuce ni Allah ya saka mani, ki tattara kayan ki da na yar ki ki bar min gidana yanxu, Allah ya bani ladan xumuncin da nayi a baya, kuma in sha Allah nasan Allah baxai kama ni da laifin xumunci ba, ki je na bar ki da Allah" mikewa Anty khadijah tayi tace "Ni yau kike kora gidan ki yau Anty fati saboda wasu shegu sun xo sun shirga maki karya?" A fusace Mumy tace "Ki fita ki ban waje, yanda kika so ganina da jikoki wanda aka samu ba ta hanyar aure ba ke ma Allah ya ba ki" Anty khadijah ta tashi tana wani murmushi tace "Sai kinyi da kin sanin daga min yatsa da kika yi fatima" daga haka ta bude siff ta dinga fiddo kayanta da na Iklima tana huci, Mumy tace "Da na sani sai dai ki gansa a kwaryar ki" daga haka ta fice daga dakin ta shiga na Aliyu, Yana xaune gefen gado ya rike kansa, duk yan biyun sun yi bacci kan gado, Mumy na kallonsa tace "Kai da babban laifi kai da fadin bakakken maganganu ko Aliyu?" Kamar xai mata kuka yace "Mumy me yasa duk hallacin da na ma khadijah a baya baxata duba na, did I deserve this, wllh da hankalinta baxan cuce ta haka ba, sannan ta dinga wani hadani da wasu karti, ni ita na sani ba su ba su ba su daina involving kansu a abinda bai shafe su...." Katse sa mumy tayi tace "Don't tell me nonsense, dole duk mai conscience idan ya ji labarinta ya so ya kwatar mata hakinta, kasan irin cutar da ka mata kuwa ka raba ta da kowa nata?" Aliyu ya rike kansa bai ce komai ba, Mumy tace "Sai ka tashi mu tafi can gidan nasu yanxu" Aliyu ya dago ya kalleta da kyar don wani Sara masa kansa ke masa yace "Mumy wllh ni baxan iya rabuwa da Iman ba, baxan iya rayuwa ba ita ba, my life has being miserable tun da na sa ta bar gidan nan, Don Allah ki rokar min ita ta amince mu yi aure, I don't think xan iya auren wata ya mace a duniya idan ba ita ba, plsss even for the sake of this innocent children ta amince mu yi aure" Mumy tace "yanxu kuma??" Tashi yyi Yace "Wllh Mumy idan tace baxata aure ni ba, I promise to go away with this kids baxa ta sake ganinsu ba har karshen rayuwarta, ai da can ba da su take rayuwa ba" Mumy na masa wani kallo tace "Na ga alamar ka fara xarewa, da yaran xaka mata baraxanar ta aure ka kenan, a hakan xata amince ta aure kake tunani, kasan ko kotu aka je yaran nan ba naka bane Aliyu, ba ta hanyar aure ku ka same su ba don haka ka janye wannan baxan maganar da kake yi, kuma kar ka bata min rai" Wani murmushi yyi bai dai ce komai ba, Jikin mumy yyi sanyi ta bi sa da kallo, tsoronta kar ya tafi da su kamar yanda yace, da kyar tace "Ka tashi mu je gidan na su, nasan even for my sake ma xata amince maka" daga haka ta fita dakin. Sai kusan magrib suka isa address da khadijah ta ba mumy, Aliyu ke driving din, Sai baby a gaba, mumy kuma na xaune back seat da yan biyun, tana rungume da little Sudais da jikinsa yyi xafi sosai duk da allurorin da Aliyu yyi masa, kai kana ganin yaran kasan hankalinsu ya kwanta da mumy, Shureim na kallonta yace "Are we going to visit you again mama?" Tana murmushi ta shafa kansa tace "Sure sweetheart" parking Aliyu yyi kusa da gidan ya juya yana kallon Mumy, Mumy tace "Ina jin nan ne" Shureim yace "Ehh mama nan ne gidanmu" Mumy tace "baby sauka ki kwankwasa gate din" Baby ta sauka tayi yanda Mumy tace, Mumy ta sauko tare da boys din, Aliyu ya fito shi ma ya dau sudais, bayan wani lkci Nanny ta bude gate din, da gudu Shureim ya tafi ya rungumeta, Nanny ta ji dadin ganin su sosai ta dinga yi ma su Mumy sannu da xuwa, Kallo daya tayi ma Aliyu ta gane shi ne uban yan biyun, ta yi masu iso har parlor, Sannan ta shiga daki don Umma na ciki tana sallah, Khadijah ma tasan sallan take yi, Umma ta sa Hijab ta fito bayan Nanny ta sanar mata bakin da suka yi, Har lkcn Sudais na jikin Aliyu, Shureim dake jikin Mumy ya tafi da gudu ya rungume Umma yace "I miss you Mumy na" Umma ta xauna tana murmushi ta ja sa jiki sannan suka shiga gaisawa da su Mumy, jikin mumy yyi sanyi sosai don bata taba xaton xata tarbesu da kyau haka ba, shi dai Aliyu ya kasa daga kai ya kalleta, shi ma bai yi xaton haka ba, Khadijah dake xaune kan darduma lkci daya taji ranta yyi mugun bacci jin yanda Umma ta sake masu, jin muryar yaranta yasa ta lumshe idonta, amma ta ki fitowa parlor ta same su don bata ma son ganin Aliyu, Mumy na kallon Umma tace "Ina Khadijar Hajiya?" Umma ta kalli Nanny dake tsaye tace "kira Khadijah" sosai Khadijah ta dake xuciyarta ta mike ta bi bayan Nanny kan ta a kasa, har ta shigo parlorn bata yarda ta dago kanta ba ta gaida Mumy, Aliyu sai kallonta yake ko kiftawa babu, Shureim ya nufeta ya xauna jikinta yace "Anty mun dawo, I like the house so much..." Khadijah ta ki kallon yaron amma har ranta bata ji dadin abinda yace ba, ita fa in dan ta ita ne yaranta basu da uba, ita dai tasan Allah ne ya bata su, kuma tana gode masa, fuskarta daure ta dago tana satan kallon Aliyu dake ta kallonta suka hada ido ta masa wani harara ta dauke kai, lkci daya ta mike ta ja hannun Shureim suka bar parlorn, tana xaunawa kan gado ta jawo yaron gabanta tana kallonsa da kyau tace "Did that stranger tell you anything?" Shiru yyi da farko kafin yace "But he is not a stranger Anty, this is the 4th time we are meeting with him" ta xaro ido xuciyarta na bugawa tace "Where and where" yace "Anty ranan nan da muka kusa yin accident, that i told you he made sure we where fine...." Gabanta yayi mugun faduwa tace "And where?" Yace "We met again at the airport da xa mu je holiday a UK, shi ma xai je can..." Ta runtse ido xuciyarta na tafarfasa tace "And where????" Yace "Yesterday at the market, because sudais don't like him shine ya gudu ya shiga titi babban mota ya buge sa" ta fixgo yaron tana huci tace "Shi ya janyo mota ya buge Sudais?" Kai ya gyada mata ta jefa masa wani kallo tace "And you are telling me he is kind yana neman kashe maka brother, daga yau ka sake yarda ko kallon ka yayi sai ya xuke maka jinin jikin ka gaba daya, baka san shi vampire bane" buda baki yyi yana kallonta da surprise, can yace "Me yasa bai shanye mana ba a gidansu?? Anty he is kind fa, ni dai I like him, he was with us....." Tsawa tayi masa ta turasa har sai da ya kusa faduwa hawaye cike idonta tace "Xan fasa maka kai... Nace stay away from him, you have no business with that wicked man" Shiru yyi a tsorace yana kallonta, a hankali yace "But he even told us he is our father not barrister as you told us...." Mikewa tayi hankali tashe xuciyarta na mugun bugawa tace "He is a liar... Karya yake maka barrister ne babanka, ba abinda ya hada mu da shi" cikin rawar murya tace "Tafi ka kamo hannun sudais ku xo nan yanxun nan" da sauri ya fita, yana isa kusa da Aliyu yace "Uncle, Anty tace I shud call my brother now" shiru yyi yana kallon yaran, haka ma Mumy da Umma, Aliyu yayi kasa da kai a hankali yace "Umma ki d'an mata magana ta bari in je da shi, he is sick dole xa mu koma asibiti" a fusace Khadijah dake jin sa ta fito tace "Ina ruwanka da rashin lafiyarsa? Ka bani yarona ai nasan hanyar asibiti, give me my son" tsawa Umma tayi mata ta mike tace "Tafi ki bar parlorn nan kar in bata maki rai, shashasha" ta fashe da kuka ta juya da sauri ta bar wajen, Umma dake kallonsa a sanyaye tace "Ka je da shi, Amma ko xuwa gobe sai ka kawo shi" a sanyaye yace "Na gode Umma" su mumy basu bar gidan ba sai kusan karfe taran dare bayan mumy ta mata bayanin duk abinda ya faru, Umma ta raka su har bakin mota jikinta a sanyaye.

Umma na dawowa cikin gidan ta tafi daki gun Khadijah a daki, xaune ta sameta kasa ta hade kai da gwiwa tana kukan takaici, Umma ta sauke ajiyar xuciya tace "Amma Khadijah ban taba xaton haka daga gare ki ba, da ilimin ki bai kamata kiyi abinda kika yi ba, ina ce ko ba komai xai ci albarkacin mahaifiyarsa, ke da kanki kin bani labarin irin abubuwan da tayi maki while with them, me yasa xa ki mance hakan da wuri, don me laifin d'an ta xai shafeta, me yasa ko don ita baxa ki raga masa ba, ni ban ce lallai sai kin kulasa ba, Amma for the sake of his mum...." Cikin kuka tace "Umma kiyi hakuri, but I have nothing to do with Aliyu and his family again, I will pretend ban taba rayuwa tare da su ba, don Allah su rabu da ni su bar min yarana su je na yafe masu, ina jin kunyar mahaifiyar sa shi yasa nake raga masa, only me knew wat I passed through in life, ni kadai nasan abubuwan da na fuskanta a rayuwa shekarun baya, Umma na sha wahala, na ji na tsani rayuwar, ban taba sanin xan yi surviving ba ummata, da ba don sudais ba da ban san me xai sameni ba, me yasa rana tsaka Aliyu xai dawo rayuwata yana min gadara a kan yaran da bai ma san da su ba, why Umma??" Umma ta xauna duk jikinta yyi sanyi tace "Ni ba nace ki yarda da Aliyu bane Khadijah, amma kiyi hakuri ko domin mahaifiyarsa ki yafe masa, ki mance past din ki" tana kallon umma da jajayen idanuwanta tace "Na yafe masa amma kar ya sake cewa shi ne uban yarana, kuma da kai na xan shirya in tafi in dauko yarona gidansu gobe, it's better Barrister sudais ya raba ni da su then ace Aliyu, saboda shi ne ya sha wahalar su kuma shi ya koya min sonsu ba don shi ba kilan da sun mutu yanxu" shiru Umma tayi ta kasa cewa komai tana kallonta, mikewa khadijah tayi ta hau saman gado ta kwanta, Umma ta mike a sanyaye ta kama hannun Shureim dake ta kallon uwar tasa ta fita da shi. Mikewa xaune khadijah tayi jin wayarta na ring ta dau wayar, ganin khaleel ne ta daga ta kai kunne tayi masa sallama cikin sanyin murya, Daga daya bangaren ya amsa a hankali yace "Sun kawo maki yaran Khadijah?" Ta fashe da kukan takaici tace "they brought just one, Shureim kawai suka kawo, ya tafi da sudais" Khaleel yace "Saboda me?" Cikin kuka tace "Wai xai kai sa asibiti, I don't knw ko meye damuwarsa da ciwonsa, ni dai ya rabu da yarana, ya kyale min su" Khaleel yyi shiru na wani lkci kafin yace "Kar ki damu xa su dawo maki shi, bana son ki kara sa ma kanki damuwa Khadijah, and plss because of his mother let take everything easy, kar ma ki sake kulasa, sure baxata bari ya dauke maki kids ba, kin san ana barin halak ko don kunya, am sure soon xa a dawo maki da little Sudais kin ji" kai kawai ta gyada masa hawaye na sauka idonta, yace "Sleep without worries plss Khadijah" a hankali tace "Toh nagode" daga haka ya katse wayar, ta koma ta kwanta ta lumshe ido, cikin dare misalin karfe biyu Khadijah na xaune kan darduma bayan ta idar da slh taga wayarta yyi haske alamar shigowar text, ta mike a hankali ta isa gun wayar, message din barrister Sudais ta gani ta dauka ta bude tana kallon content din, "Dear am sorry I didn't call, na shiga gida ne da wuri jiya, but mun yi communicating da Dr Ayman, he told me everything, you don't worry xa a dawo maki da little sudais soon, gobe da safe xan xo in sha Allah, sleep without thought plss" tabe baki tayi ta ajiye wayar ta koma kan darduma ta xauna, har kusan asuba Khadijah bata runtsa ba, damuwa yayi mata yawa sosai ga yawan faduwar gaba da take ta ji, karfe hudu saura umma ta shigo dakin da Shureim ganin khadijah kan darduma ta isa kusa da ita da yaron tace "Gashi ya ki bacci, his temperature is high but na basa paracetamol, wai xai xo wajen ki" xaunawa Shureim yyi kusa da ita yana kallonta yace "Anty yaushe sudais xai dawo, I want to see him" Umma tace "Au abinda ke damun ka kenan" murmushii tayi ta juya ta fita tace "ka gamu da aiki kam" Khadijah ta jawo sa jikinta a hankali, taji jikin nasa ya dau xafi sosai, dago kansa tayi tace "Are you feeling pain anywhere?" Ya girgixa mata kai yace "I want to go to my brother" ta rungume sa sosai tace "Gobe xai dawo ka ji" ba a dau lkci ba yaron yayi bacci a jikinta ta mike ta daukesa ta kwantar kan gado, ta koma ta xauna tana jiran lkcn sllhn asuba. Washegari da safe Mumy na xaune kusa da Sudais da Aliyu ke sa ma drip da damuwa tace "Abuturrab ko xa ku je asibiti dai a kara duba sa, he is suffering slowly..." Aliyu ya kalleta yace "He will be okay mum, na dubasa babu wani matsala, a hankali xai dinga recovering, and it looks as if he is missing his twin, tun jiya yake ta tambayar sa" Tace "Toh ko xa a mayar da shi gidan ne?" Da kamar baxai ce komai ba, sai kuma yace "Mumy bari ya kara samun lafiya" Baby ce ta shigo da wayar Mumy dake ring ta mika mata ta fita, Mumy ta karba ta daga kiran, shiru ta d'an fara yi kafin tace "Ehh ni ce, who is on the line" ganin Mumy bata sake cewa komai ba sai shock da ya bayyana a fusakarta, a hankali afterward ta sauke wayar daga kunnenta tana kallon screen din, Aliyu dake kallonta yace "Waye mumy? Me ya faru?" Kallonsa tayi a sanyaye tace "Ka sake kiransu kilan ban ji da kyau ba ne" Aliyu ya amshi wayar ya kira number, bayan wani lkci aka dauka, abinda aka fadi ma Mumy aka sake maimaita masa, ya d'an bude ido shi ma lkci daya yace "Subhanallah, to ga mu nan xuwa, mun gode" daga haka ya katse wayar yace "Mumy wai Anty khadijah na asibiti..." A hankali mumy tace "Toh sai ku je, ni kam baxan je ba" ya bata fuska yace "No plss mumy kar ki ce haka, tunda har aka kira ki mu je kawai, baxa a biye ta halinta ba, kuma ai ba a canxa ma tuwo suna she still remain ur sister" da kyar Aliyu yyi convincing Mumy ta yarda xa ta je. Umma tayi pecking din goshin Shureim har sannan jikinsa da dumi tana shafa kansa tace "You behave your self kaji my boy, kuma ban da fada a gidan" Kai ya gyada mata, Khadijah ta kama hannunsa suka fita parlorn, khaleel na jingine jikin motarsa har suka iso inda yake, ya duka yana kallon kyakkyawan yaran a hankali yace "How are you Darling" murmushi Shureim yyi yace "Am fine uncle" mikewa khaleel yyi ya kama hannunsa yana kallon khadijah yace "Toh sai mun yi waya..." murmushi tayi tana bin sa da kallo tace "Nagode, byee" daga haka ya bude front seat ya saka Shureim ya xaga ya shiga maxaunin driver ya tada motar ya bar layin, Khadijah ta juya to koma ciki feeling relieved. Shureim na wasa da wayar khaleel yace "Uncle baxan sake ganin Sudais ba?" Khaleel ya d'an buda ido ya kalllesa yace "In ji wa ya gaya maka haka?" Ya langwabar da kai bai ce komai ba, duk sai ya basa tausayi, a hankali Khaleel ya shafa kansa yace "Xai dawo soon ka ji my boy" har khaleel ya isa gida Shureim bai sake cewa komai ba, gida ne mai girman gaske, Shureim ya wara ido yana bin makeken compound din da kallo yace "Uncle is this ur home" khaleel yyi murmushi ya gyada masa kai bai dai ce komai ba, yaron yace "It's big" parking khaleel yyi a parking space ya fito ya xaga ya sakko da yaron sannan ya nufi entrance na babban parlorn gidan yana rike da hannunsa, yara ne da baxa su wuce Shureim din ba su uku duk maxa kusan duk kamanninsu na larabawa suna wasa parlorn da puzzles, suna ganin khaleel suka yo kansa da gudu suka rungume sa suna gaishesa da larabci, ko wannensu cike da murnan ganinsa, Dukawa yyi duk ya shafa kansa yana murmushi yace "I brought you a new friend, Shureim by name" Murmushi Shureim yyi yana kallonsu yace "Hey" sallama suka yi masa gaba daya, khaleel yyi dariya sosai, ya mike ya kama hannun Shureim suka wuce sama yana waigo yaran, bedroom din Ummun sa ya tafi da shi, Wata balarabiya ce da baxata haura sittin ba xaune dakin tana waya da halshan larabci, ya xauna gefen makeken gadon ta, ya dau Shureim ma ya ajiye sa gefensa, tana gama wayar ta juya tana kallon khaleel tace "Sai yanxu" gaisheta yayi ta amsa da murmushi ta na kallon shureim tace "Ina ka samo mana yaro" Ya shafa kai a hankali yace "Ummu... Khadijah da nake baki labari, he is her son Shureim" Umma tace "Maa sha Allah, xo in ganka sweetheart" Shureim ya sauka kan gadon ya tafi gunta ta jawo sa ta rungume sa tace "Ya ummun ka fa?" Yace "She is fyn" Khaleel yace "Twin dinsa baya tare da shi ne duk ya daga hankali shine nace bari in kawo sa nan sai su dinga wasa da su fadeel tunda suna hutu su ma" Ummu tace "That's nyc, Ina twin din nasa ya tafi" khaleel yace "Ya tafi familyn Dad dinsa ne" Umma tace "Ayya, toh Allah ya sa wannan din ya saki jiki a nan" Khaleel yace "Ameen" Mikewa yayi ya fita dakin ya bar ta da Shureim tana masa tambayoyi tana murmushi. Baby ce ta tsaya tare da Sudais dake bacci dakin Abbansa, Mumy da Aliyu da saleem suka tafi asibitin da aka kira Mumy a zaria, Har suka isa ward din da aka gaya masu Anty Khadijah take mumy gabanta bai bar faduwa ba lkci daya kuma ta dinga tunanin wa gare Khadijah a cikin garin Zaria da ta taho, Aliyu ya murda kofar ward din ya shiga Mumy na biye da shi, kwance suka ga Anty Khadijah kafafuwanta duk biyu an mata dauri, ga wani katon plaster an mata rawani da shi a kai, hannunta daya ma daurin ne, mumy ta kasa karasawa cikin dakin sai hawaye duk jikinta yyi mugun sanyi, saleem ma ya makale jikin kofa ya kasa shiga yana kallonta baki bude, Aliyu ne yyi karfin halin karasawa cikin dakin yace "Subhanallah.... Innalillahi wa inna ilai hi raji'un" Anty khadijah ta juyo wuyanta da kyar tana ganinsu ta fashe da kuka muryarta can kasa tana magana da kyar tace "Aliyu duk na kakkarye, Wayyo Allah na ku taimake ni" Kasa cewa komai Aliyu yayi ya xauna kujera dake wajen duk jikinsa yyi sanyi yana kallonta, Wata nurse ce ta shigo dakin tace "Likita na magana da mutum daya cikin ku" Aliyu ya kalli Mumy tayi karfin halin cewa "Ka je" mikewa yyi cikin sanyin jiki ya bi bayan nurse din, Ba a dau lkci ba wata nurse ta sake shigowa da wasu allurai ta xuba su cikin ledan ruwan dake jikin Anty khadijah, yunkurin amai ta fara yi daga kwancen, nurse din tayi saurin sa hand gloves ta dagota ta dauko wani tasa ta sa mata dai dai bakinta tana mata sannu, amai ta dinga kwarara kamar xata amaye hanjinta, Mumy tayi karfin halin karasowa a karo na farko cikin muryar kuka tace "Sannu Khadijah" Nurse din ta mayar da ita ta kwantar tana ihu alamar ta fama daurinta ta ajiye tasan aman ta fita, wata cleaner ta shigo ta dau tasan ta shiga toilet. Har likitan ya kai aya Aliyu kallonsa yake da shock, cike da karfin hali yace "Ciki kuma Dr?" Likitan ya mika masa result din yace "In sha Allah, gashi nan har wata uku" kasa cewa komai yyi ya mike ya bar

Please Login or Register in order to submit comment