Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

minti goma ya dawo dakin... kallonta yyi sannan ya kalli abincin ya d'an daure fuska sai kuma ya karaso ya bude ya sa cokali ya mika mata ba musu ta karba tana kallon jollof rice da naman, yace "Kin kira su?" Gyada masa kai tayi yace "They are coming to take you now right?" Nan ma kai kawai ta gyada masa, yace "Alryt, ki ci abincin nurse xata shigo ta nuna maki dosage din maganin yanxu, I've paid the bill, Allah kiyaye gaba I will be on my way now..." Kai kawai ta gyada masa tana iya kokarin ganin bata bar hawayen dake taruwa idonta ya xubo ba a hankali tace "Nagode" ya buda ido sosai yace "No thanks" ta lura sauri yake don tuni har ya kai kofa, ta kalli wayarsa dake gefenta a hankali tace "Your phone" ya juyo da sauri yace "Ohh thanks har na mance" daga haka ya dau wayarsa ya fita ward din, ta rufe abincin ta ajiye ta hade kanta da gwiwa hawaye mai xafi na sakko mata, bayan kusan minti goma da tafiyarsa nurse din daxu ta dawo, da sauri ta goge hawayenta, nurse din tace "Kin ci abincin koh?" A hankali khadijah tace "Na ci" nan ta nuna mata dosage din drugs din sannan tace "Sai ki sha yanxu, an riga an sallame ki, yace yan uwanki na hanya koh?" Ta gyada mata kai tace "Toh Allah ya kawo su lfya" daga haka ta fita, ta fashe da matsanancin kuka xuciyarta na mata kuna, sai a snn envelope din kudin dake hannunta da ta fadi ya fado mata, bata wani damu ba don tasan me rabo ya dauke shikenan kuma, bayan wani minti ashirin din nurse din ta shigo tana mata wani kallo tace "Wai har ynxu ba su iso ba yan uwan naki?" Tana kallonta a sanyaye ta gyada mata kai kawai, nurse din ta tabe baki ta juya ta fita, taa ta xaune ta rasa me ke mata dadi har lkcn kanta na bisa gwiwanta nurse din ta shigo da likitan daxu, likitan yace "Ke daga wani garin yan uwanki xa su xo ne har yanxu basu iso ba, ko karya kawai kike ma mutane?" Hawaye cike idonta cikin rawar murya tace "Ehh" ya xare glass din idonsa yana xaro idon yace "Karyan kike?" Ta fashe da kuka a hankali tace "Ni bani da yan uwa, ban san kowa ba, ban san ina xan je ba" a mugun fusace yace "You must be joking, Look malama fita ki bar ma mutane asibitin su, get out yanxun nan, maxa dau sauran abincin ki ki fita kar in kira masu gadi su yi waje da ke" jikinta na rawa ta sakko ta dau abincin da yace tana jin kamar jiri xai kada ta hawaye na sakko mata sosai ta nufi kofa, nurse din ta bi ta da kallo, murya can kasa tace "Dr ko xaka kira shi wanda ya kawo ta tun da kasan shi?" ya jefa mata wani kallo yace "Toh me xai yi mata idan na kira sa, sanin wacece ita yayi aka gaya maki? He just helped her tayi collapsing a gefen titi daga anyi hatsari" khadijah ta bude kofa xata fita likitan yace "Tsaya malama" tsayawa tayi ta juyo tana kallonsa a tsorace, ya ciro wayar sa a lab coat din jikinsa yyi danne dannensa kafin ya sa hands free wayar ya fara ring, sae da ya kusa katsewa aka daga, likitan ya ce "Sudais, ga patient din da ka kawo mana taki tafiya fa...." daga daya bangaren aka ce "I don't get you" a d'an fusace likitan yace "I also didn't get what she meant by saying she don't have relatives and she don't knw where she's heading, don Allah ka xo ka fidda min ita a asibiti plss" Wanda ya kira da Sudais cikin expression din mamaki yace "Ji min walakanci fa, toh ni da ka kira ni me xan yi? If I am not mistaken I told you I don't knw her Yusuf, then why calling me? Me yasa kake kirana? Wait wllh sai ka gaya min me yasa ka kirani ma dai, are you not just suppose to tell her to leave kayi discharge dinta???" Likitan ya kalle Khadijah a fusace yace "Ke malama maxa nemi Inda dare yyi maki kada in sa a xo a fitar da ke yanxun nn, get out plss" kai ta gyada masa jikinta na rawa hawaye na sakko mata, Da sauri Sudais din yace "Wait Yusuf, you knw what? kaga dare yyi ynxu ka bari gobe da sassafe kace ta wuce plss since she's lying she don't have relative" likitan yace "Sai dai idan xata sake biyan kudin gado, don da ace haka ake yi a clinic din da ba mu samu ci gaba ba" Shiru Sudais ya d'an yi kafin yace "Toh naji xan biya ka, though I hate lies and liars let her just be safe there kafin ta wuce gobe, just dat 1st thing tomorrow morning send her away, good nyt" daga haka ya watse wayar, ko kallonta likitan bai yi ba yace "Bani hanya" ta bar bakin kofar da sauri yyi ficewarsa kamar xai tashi sama, Nurse din ta karaso kusa da ita tace "Me yasa kika yi karya yan mata, ke ba musulma bace?" Khadijah ta girgixa mata kai hawaye mai xafi na xubo mata, nurse din ta sauke ajiyar xuciya tace "Toh tafi ki kwanta" daga haka ta fita ta bar ta tsaye, karasawa tayi kan gadon ta kwanta tana share hawayenta, wajajen karfe sha biyu ta tashi xaune jin yunwa na nemanmatat illa ta bude abincin daxu, amai ne ya taho mata bayan ta kai baki ta sauka kan gadon da sauri ta shiga bayi ta dinga amai kamar xata amaye hanjinta, jikinta a mace ta fito ta kwanta bisa gado tana sauke ajiyar xuciya ta kudundune waje daya daga haka bacci ya dauketa sanyi na shiga jikinta.

Kasa tashi sallan asuba Khadijah tayi washegari ta dalilin xaxxabin da ya rufe ta, jin an bude kofar ward din ta bude idanuwanta a hnkli taga gari ya waye sosai, likitan da mutumin jiya da ya kira da Sudais suka shigo ward din a tare, tun daga bakin kofa sudais dake sanye da milk jallabiya ke mata wani kallo har karaso gadon yace "jiya da na baki waya wa nace ki kira?" Khadijah ta mike xaune da kyar ganin ynda ya hade rai ta marairaice tace "Relatives dina" ya kara hade giran sama da ta kasa yace "Then why didn't you call dem?" cikin rawar murya tace "I don't have anybody to call, ni marainiya ce, my father is late so also is my mum, My step mum....." Kasa ci gaba tayi ta fashe da kuka sosai, cikin tsawa yace "Karya kike yi, shut ur mouth plss" likitan dai rungume hannu kawai yyi yana kallona yana murmushi, ta hade kai da gado tana kuka cikin rawar murya tace "ku yarda dani don Allah, wallahi ni bana karya, laifi nayi ma step mum dita tace min in bar mata gidanta, I love my step mum and she loves me same, but tace in tafi sbda laifin da nayi, she raised me up as a mother even after my late dad passed away 5 years back, don Allah kada ku ce in tafi ban san kowa ba a garin nan ban taba xuwa ba, ku taimakeni ku kaini gidan marayu in dinga kula da yaran wajen don Allah" tsawa likitan yyi mata da ya firgitata ta dago da sauri, yace "You are mad, wa xa ki raina ma wayo, ni ko wannan da ke kusa dake?" Ya fadi hakan yana nuna sudais, Shiru tayi tana kallonsa, kafa mata ido shi ma yyi, can ya karaso kusa da ita yana kallon kwayar idonta da kyau, ya kai hannunsa ya bude eye lids dinta, can ya kalli fingers dinta sai kuma ya kalli Sudais dake tsaye, daga kafada yyi ya nufi kofa yace "I have better patients to attend to Sudais..." daga haka yyi ficewar sa daga cikin ward din, a sanyaye khadijah ta kalli Sudais dake mata wani kallo yana rungume da hannunsa, harara ya watsa mata bayan mun hada ido tayi saurin sunkuyar da kanta, muryarsa ya daki ear drum dinta, "Wani laifin kika yi ma mum din taki, kuma daga wani gari kike? Kina min karya xan gane kuma daga nan station xan kai ki" Shiru tayi tana kallonsa hawaye na ci gaba da sakko mata, cikin sanyin murya tace "Daga kano na xo" yace "Wato kin saba tafiya garruruwa kenan ko" ta girgixa kai da sauri tana kokarin ganin bata fashe da kuka ba tace "Wallahi A'a" yace "Toh wani laifin kika yi mata?" Share hawayen idonta ta shiga yi a hankali ta hadiye wani abu da ya tsaya mata, can ta sakar masa kuka tace "Kilan baxa ka min taimakon da nace ka min ba idan ka ji dalilin bari na gida" strictly yace "Malama ki bude baki ki gaya min, stop wasting my time xan je aiki" jinginar da kai tayi da gadon ward din tace, "Duk abinda xan fada maka ka yarda dani sbda Allah, ni bana karya, I knw d consequence of it.... Domin ka min taimakon da nace ka kai ni orphanage yasa xan fada maka ni wacece" Bai tanka ta ba hakan yasa a hankali tace "I lost my mum at a very tender age, and my beloved last year" ta kallesa taga he is listening but not looking toward her direction, ta lumshe ido, a haka ta fara basa labarinta tun daga farko har xuwa yanxu da yake gabanta, bbu abinda ta boye ma Sudais, Kallonsa tayi a karo na farko tun da ta fara gaya masa ita wacece, hawaye masu xafi suka shiga xubo mata, Sudais ya dinga kallonta da wani expression da ta kasa fassarawa a fuskarsa, tana girgixa kai a raunane tace "I told you all but the blank truth about me, believe me plss" kasa ce min komai yyi sai bayan kusan minti biyu yana nuna ni da yatsa da wani irin mamaki yace "You mean... You are pregnant?" Ta gyada masa kai a hankali tace "That's what the Dr told me and my step mum" Jinginar da kansa yyi jikin bango yana kallon saman ward din ko kiftawa bbu, bai kuma ce min komai ba har na kusan minti uku, Khadijah dai sai kallonsa take don bata san tunanin da yake a xuciyarsa ba domin kuwa duk wanda ya gan sa yasan yyi nisa tunanin da yake, bude kofar aka yi duk suka kalli kofa, Dr Yusuf ya shigo yana kallonsa da kyau yace "Ya? Ka gama sauraren karyar ta Malam?" Sudais bai ce komai ba ya shiga shafa uban gashin dake kansa, likitan yyi murmushi yace "Very good then, naga kamar har karyar tayi tasiri a xuciyar ka" Likitan ya karasa kusa da khadijah yana kallonta da kyau yace "Are you married?" Shiru tayi tana kallonsa ko kiftawa bbu, wani murmushin ya sake yi ya kalli Sudais, Sudais ya lumshe manyan idonsa ya bude su a hankali yace "Yea xaka cire mata cikin soon as possible....." Wani kallo Dr Yusuf ke yi masa, Sudais ya dafa kafadarsa yace "Yeah... She told me about d pregnancy, an illegal one at it's early stage, i think you just have to flush it Yusuuf, I will pay what ever amount it will take" tunda ya fara magana khadijah ke kallonsa baki bude, can ta fashe da kuka tace "Noo plss, it's illegal but it doesn't deserve that, Allah xai yi fushi da ni, baxan iya ba..." wani mugun kallo Sudais ke mata ya karaso kusa da ita cikin tsawa yace "You are very very stupid, shegen xaki haifa?" Ta kuma rushewa da kuka tace "Eh, saboda Allah ne ya bani, kuma it's not my fault it came this way, beside soul din ba shi da laifi da har xan xubar da shi..." Yusuf ya rungume hannu yana kallonta, Sudais ma wani kallo yake mata lkci daya yana mamakin furucinta cos she look young to think that way, ya matsa dab da ita yace "Then ya xama dole ki koma gidansu Aliyu kika kirasa ko wa???" Khadijah tayi shiru tana kallonsa hawaye na xubo mata, ido ya kafeta da shi yana jiran jin abinda xata ce, ta sauke idonta a hankali tace "Toh me xan ce masu?" Strictly yace "Abinda likita ya gaya ma ke da Ummar ki" tana share hawayenta tace "Toh amma ni yanxu bani da kudin mota" yace "Xan baki" juyawa likitan yyi ya fita, shi ma ya nufi kofa kafin ya fita ya juyo ya kalleta yace "Ki sameni reception yanxu" daga haka ya fita, ta sakko a hankali ta dafe gado jin jiri, da kyar ta karasa reception din sbda jirin dake debanta tana isa ta xauna kan kujera ganin baya gun, office din Dr Yusuf sudais ya shiga, Dr Yusuf yace "What are you trying to do Sudais?" Sudais ya shafa kansa a hankali ya xauna kan table dinsa yace "I don't really knw Yusuf, kawai nayi analyzing naga babu karya a labarinta, I tried hard to figure out...." Yusuf ya katse sa da sauri yace "Da alama lauyancin ka bai fada maka gaskiya ba yau, look at you... sau nawa muke ganin cases irin wannan, tayi ciki ta gudu ta bar gida ta xo nan ta shirga maka karya a matsayin ka na barrister har karyar yyi sinking kan ka? Don't let me call u a disgrace to ur profession..." Sudais ya girgixa kai yace "Babu karya a xancen da ta min, and profession dina yasa nayi figuring din hakan, she told me nothing but the truth" Dr Yusuf yace "Toh naji gaskiya ta fada maka, what do you intend doing now?" Shiru Sudais yyi yana kallonsa, can ya dauke kai cikin damuwa yace "I don't knw frnd, I have never being confuse like this all my life, Yusuf just look at her, she is too young, baxa ta wuce sa'ar Rabi'ah ba, had I known wllh da ban tsaya a motata ba jiya" Dr Yusuf yace "Toh ko gidanku xaka kai ta" sauka Sudais yyi da sauri daga kan table din yana xaro manyan idanuwansa yace "Gun wa Yusuf?" Yusuf yyi dariya yace "Mami wai da" Sudais yace "Mami ta kashe ni kenan, cewa ma xata yi ni nayi ma yarinyar cikin, kai ma kasan ko hauka na fara baxan fara kai ta hanyar gidanmu ba, what for?" Yusuf dai sai dariya yake sanin wacece mahaifiyar sudais, Sudais ya tabe baki yace "Wani lkcn ma d'an Adam na xaman xamansa yake dauko ma kansa matsala da kansa a rayuwa if nt meye haka na sa kai na ciki??" Yusuf yace "Kawai ka ka ita orphanage din da tace xai fi" Sudais yace "In dai kai ta can gidan su dan iskan da yyi mata cikin" Yusuf yace "Wa yaga bata lkci" Sudais ya nufi kofa yace "Muyi waya frnd" Mikewa Yusuf yyi ya bi sa suka fita. Ba tare da Sudais ya kalli khadijah dake ta xaune duk ta gaji a reception ba yace "Mu je" mikewa tayi a hankali ta bi bayansa, gun motarsa dake parking space ya nufa, ya bude ya shiga, ganin bata shiga ba Yusuf yace "sai ki shiga" a hankali ta kai hannu ta bude motar ta shiga, Sudais na kallon Yusuf yace "I will give you a call" Yusuf yace "Alright then" daga haka ya ja motar muka bar asibitin, bbu wanda yace komai cikinsu, yyi driving din kusan minti sha biyar suka iso wani anguwar masu kudi, nesa da gidansu Sudais yayi parking, ba tare da ya kalleta ba yace "I will be right back" daga haka ya fita ya fara tafiya, tafiyarsa kadai ma abun kallo ne, ya wuce gidaje kusan hudu kafin ya xo na su, Mahaifiyarsa Mami ce xaune parlor da wata bakuwa da tayi, ya karasa ya gaishesu da ladabi, bakuwar ta amsa da fara'a tace "Wannan uban gashin da aka bari fa Barrister, sai kace a turai" Ya kirkiri murmushi yace "Sunna ce...." Katsesa Maminsa tayi fuska daure tace "A hakan da ka bar shi irin na wa ends basu da mafadi, am very serious kada ka shigo min gida anjima baka asks gashin nan ba, ka jira idan ka koma UK din sai ka kara barin gashin, wnn iskancin kam ba a gidana ba" kansa a kasa yace "Toh Mami" daga haka ya mike ya wuce bedroom dinsa, press ya bude ya fiddo wani makulli ya sa aljihu sannan ya fito yayi masu sallama ya fita, bacci ya tadda khadijah ke yi, dauke idonsa kanta yyi ya tada motar ya bar layin, tafiyar wani minti sha biyar din yyi ya isa wani anguwar daban yyi parking a gaban wani gida, ana ganin gidan ansan sabon gini ne, ya fita ya bude gate din gidan da makulli sannan ya dawo ya ja motar ciki yyi parking ya fita ya koma ya rufe gate din, tuni khadijah ta bude ido tana bin gidan da kallo, dawowa yyi yace "Come down" ba musu ta fito, tafiya ya fara yi xuwa entrance din main house din ganin haka ta bi bayansa sai dai gabanta faduwa yake kawai, ya sa makulli ya bude kofar shiga parlorn ya shiga, kasa shiga tayi tana lekan parlorn, ya juyo yana kallonta, hawaye ne cike idonta, wani kallo yyi mata ya shiga parlorn ya bar wajen, a hankali ta taka ta bi bayansa, tuni ya wuce bedroom ita kuma ta xauna nan kan kujera a parlorn, bayan wani lkci ya fito yace "Ki shiga ciki kiyi wanka, xan fita in dawo yanxu" daga haka ya fita ya rufe kofar, tashi tayi da kyar ta shiga dakin da ya fito, towel ta gani kan gado sai sabulu ta karasa ta dauke su ta bude kofar da take tunanin na bayi ne ta shiga taga har ya hada mata ruwa me dumi, wanke bakin ta ta fara yi da mouth wash, bayan kusan minti ashirin ta fito daga bayin da kayan da ta cire a bucket ta wanke, sai taji ta samu karfi jikinta, hijab kadai ne da bata wanke ba ta daura kan towel din jikinta sannan ta fito parlor, wani kofar dake parlor ta shiga taga kitchen ne, ta dauko sweeper da mop ganin gidan is very dusty, tun daga dakin da tayi wanka ta fara gyaran ta fito har parlor duk da sanyin da take ji sosai, tana goge goge a durkushe ya shigo parlorn ya ajiye ledojin hannusa ba tare da ya kalleta ba yace "I didn't tell you to do anything madam, ga kaya nan ki shiga ciki ki canxa ki fito yanxu" ta mike tsaye tace "Toh nagode" bai tanka ta ba ta dau ledan ta shiga dakin, dogayen riguna ne na kanti da undies sai Hijab biyu da perfumes, cikin lkci kankani ta gama shiryawa ta fito parlorn, xaune yake ya tallabi chin dinsa da hannu biyu yayi nisa tunanin da yake, why is he involving him self in such case ya fa san daga irin gidan da ya fito ya san waye iyayensa, jin ta fito tun da ya kalleta sau da ya bai sake kallonta ba har ta iso nesa da shi ta durkusa tace "Na sa kayan" ledan abinci ya nuna mata yace "Breakfast" ta mike ta isa gun ledan ta bude, a hankali ta ja baya tana rike numfashinta sbda aroma din abinci, Fried Irish ne da soyayyen kwai da plantain sai ketchup, yace "You can go to the kitchen and make a cup of tea for ur self" kai kawai ta gyada masa, ta mike ta shiga kitchen din tana fatan ta iya shan shayin, ta gama hadowa ta fito, ganin kallonta yake bayan ta ajiye shayin ta dau Irish daya a hankali ta kai ba ki, ji tayi cikinta ya fara hautsinewa tun kafin ta fara taunawa, ta dau shayin ta kai baki da sauri don ta kora, tana sha tayi saurin ajiye cup din da sauri ta shige dakin da tayi wanka tun kafin ta karasa cikin bathroom din aman ya xubo mata, tun da ta fara amai sai yau tayi Wanda ya galabaitar da ita don bbu komai cikina, ta kasa motsi wajen duk jikinta ya mutu, ganin shadow dinsa ta juyo hawaye kwance fuskarta, tausayi karara ta gani a kwayar idonsa, yyi saurin dauke kai murya can kasa yace "Sorry" daga haka ya shiga bayin ya debo mata ruwa ta wanke bakinta ya xuba ruwa wajen, kasa tashi tayi ta jingina da bango, ganin jira yake ta tashi, ta runtse ido tayi karfin halin tashi bata xarce ko ina ba sai kan gado ta fada kai tana mayar da numfashi, ya karaso yace "Toh me xa ki ci yanxu" kai kawai ta iya girgixa masa, yyi jim yana kallonta kafin ya juya ya fita a koma parlor, xaunawa yyi yana tunanin how many hours will take them to kaduna.

Tashi sudais yyi daga karshe ya koma daki, ganin yanda ta dukunkune waje daya ya isa gadon a hankali yace "Are you cold" bata amsa ba don idonta a rufe suke, ya dauko duvet ya rufe ta da shi, murya can kasa tace " thank you" ya tsaya yana kallonta don har sannan bata bude idon ba, juyawa yyi ya fita ya bar dakin ya tafi balcony ya xauna ya tsura ma motarsa dake parking space ido, tsoronsa daya mami hakan kuma yasa har lkcn xuciyarsa ke contemplating kan Khadijah, but is he that heartless after all, mikewa yyi daga karshe tunawa da yyi ko wanka bai yi ba gashi an kusa azahar, har ya kusa motarsa sai kuma ya tsaya, but can he go and leave her all alone here, bayan kusan minti biyu ya shiga gidan ya wuce bedroom ya ganta a kasa tana kakarin amai, tsaye yyi bakin kofar yana kallonta, ta fashe da kuka tana mai da numfashi, wayarsa ya fiddo a aljihunsa ya fita, bayan kusan minti sha biyar ya dawo dakin Yusuf na biye da shi a baya, bude ido tayi a hankali daga kwancen da take a kasa, Jin hannu a forehead dinta taga Dr Yusuf tsaye kanta sudais na daga gefensa, Dr Yusuf yace "Sorry, ya kike jin jikin ki..." Bata iya tace komai ba don ji tayi bakinta ya mata nauyi, yace "Me kike son ci yanxu?" Ta girgixa masa kai a hankali, ya kalli Sudais dake rungume da hannunsa yace "Try making a cup of tea with just milo for her pls" Sudais ya juya ya fita, ba a dau lkci ba ya dawo da cup din warm milo, Yusuf ne ya dinga forcing dinta ta shan tea din, cikin rawar murya hawaye na sakko mata tace "Wllh xai sa ni amai" Yusuf yace "Kadan xa ki sha" da ta kurbi kadan xata ajiye ta koma ta kwanta Yusuf xai hanata, sai da tayi rabin cup din sannan ya kyaleta ta ajiye ta kwanta tana sauke ajiyar xuciya, bata san sanda karfi ya xo mata ba lkci daya ta tashi duk sai da ta kwarare shayin nan kasan tiles, Sudais dake tsaye ya juya a hankali, can ya sake juyowa, ganin yanda Yusuf ya tsaya kallonta ya duka yace "Tashi ki je bayi ki wanke bakin ki" dafa gado tayi ta mike tana ganin jiri ta shiga bayin, Sudais ya shiga gyara gun aman, komawa gefen gado Yusuf yyi ya xauna ya shiga hada drips da injections, kwanciya tayi bayan ta fito, sai da yyi mata alluran sannan ya sa mata ruwan drip din, tsabar xaxxabi bata ji xafin syringe ba a lkcn, ya lulluba ta da bargo suka fita shi da Sudais dake ta tsaye. Khadijah bata san irin baccin da tayi ba ta dai bude ido taga dim light ne a dakin alamar wai dare yyi ta kalli drip din hannunta taga kamar sabo ne, cike da karfin hali ta mike xaune, ta fi minti goma xaune aka bude kofar dakin, Sudais ya shigo ya kunna wuta yana kallonta

Please Login or Register in order to submit comment