Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ba sai dai bata ce komai ba ta dau tray din abincin da drink ta fita kitchen din ta wuce sama, a hankali ta tura kofar dakinsa, yana xaune yana danna laptop har sannan, ya dago yana kallonta har ta iso inda yake ta durkusa ta ajiye tray din ba tare da ta kallesa ba ta mike ta nufi kofa ya bi ta da kallo har ta fita, yayi murmushi sanin this might not be her thinking, infact it's not even her thinking... Khadijah ce xata kawo masa abinci haka kawai, shafa kai yyi yana murmushi. Kafin ta koma kitchen din duk sun wanke duk abubuwan da suka bata, Maimoon ta fito masu da abincin nan tsakiyar parlor, Xaunawa suka yi gaba daya suka ci a tare, Deejah ta gyara wajen ta tafi da komai kitchen, suna ta xaune parlor suna hira khadijah ta dinga jin kamar kar su ce xasu tafi, ta dinga addu'ar Allah sa su manta kawai su kwana, suna nan a haka har aka kira la'asar suka wuce sama xuwa dakinta duk suka yi sallah, sai a sannan suka fara shirin komawa gida, duk jikin khadijah yayi sanyi ta xauna can karshen gado tana kallonsu a sanyaye, Dariya Deejah ta dinga mata, Safeenah na gama gyara fuskarta ta dawo kusa da ita tace "Kar ki damu sis xa mu dinga haduwa frequently in sha Allah kin ji, Kuma ga waya xa mu dinga communicating" hawaye ne ya cika idon khadijah, Safeenah tayi dariya tace "Tabb, to mu fa gobe da safe xa mu koma Abuja, Deejah kadai ce a nan, kema nasan soon xa ki koma uk saboda karatun ki" Ita dai khadijah bata ce komai ba, bayan duk sun gama Safeenah tace "I notice something khadijah, it seems har yanxu baki kwantar da hankalin ki da mijin ki ba, are you still thinking of the past koh? I will advice you to just erase that of ur mind idan ba haka ba baxa ki taba samun kwanciyar hankali gidan ki ba, nobody is above mistake khadijah, barin ma irin wannan mistake din da aka yi ba da gangan ba, wllh idan baki maida hankali kin rungumi mijin ki ba kina ji kina gani wata a waje xata yi hakan ga mijin ki very handsome gentleman, Wallahi Kar ki kuskura wata ta hango maki shi a waje, don rashin samun kulawa gun ki xai sa ya ba ta waje dama, Haba sai kace ba wayayya ba Khadijah..." turo baki khadijah tayi, Safeenah ta dawo kusa da ita ta kamo hannunta tace "that's just it, kiyi hakuri ki xauna xuciya daya da mijin ki, forget the past, ni na tabbatar mijin ki yana son ki kema kuma kina son sa sosai" Khadijah ta sauke idonta a hankali, Maganganu sosai Safeenah ta yi mata da yasa duk jikinta yayi sanyi, daga karshe ta mike tace "Toh mu xa mu tafi khadijah sai mun yi waya" khadijah ta mike a hankali tace "Bari in gaya masa" daga haka ta fita ta shiga dakin Aliyu suka kusa cin karo don fitowa xai yi shi ma daga dakin, jawota yayi jikinsa ya rufe kofar yana kallon eye balls dinta, ta sauke idonta tace "Sake ni" ba musu ya saketa yana murmushi, tace "Xa su wuce" yace "I was thinking kwana xa su yi" ta girgixa kai tace "Gobe da safe xa su wuce Abuja" yace "Ohk ba nan suke ba dama?" Tace "Deejah ce kadai a nan" yace "Alryt am coming now" juyawa tayi ta fita, turarruka da kayan kwalliya na lefenta ta debar masu mai yawa suka sauka downstairs tana jin kewansu, ba a dau lkci ba Aliyu ya sauko, dubu talatin ya ba su gaba daya, suka ki amsa, khadijah ta hade rai ta karbi kudin hannunsa ta bude jakar Deejah tace "Ae ba ku kuka ce ya baku ba toh" Murmushi kawai Aliyu yake yana kallonta, suka masa godiya yace "No thanks sisters, or shud I drop you?" Safeenah tace "A'a mun gode xa mu tadda driver bakin titi" yace "Alryt then, Allah ya kiyaye hanya" duk suka amsa masa da Amin, har bakin gate khadijah ta rakasu, Maimoon tace "Kin ga ki koma haka mun gode sosai Khadijah, Allah bar xumunci" sai a sannan hawaye ya cika idonta cikin sanyin murya tace "I am going to miss you all" rungume juna suka yi gaba daya, tana ji tana gani suka wuce ta juyo ta koma ciki tana goge hawayen dake xuba mata, Aliyu dake parlor ya dinga kallonta har ta wuce sama. Ko minti talatin su Safeenah basu yi da barin gidan ba Barrister ya xo, Aliyu ya bude masa kofa suka gaisa, Barrister ya xauna kan kujera yace "Ya gidan" Aliyu na shafa kai ya xauna shi ma yace "Alhmdllh, ya aiki" Barrister yace "Mun gode Allah, ya mum shureim" Mikewa Aliyu yayi yace "She's upstairs" daga haka ya wuce sama, bude kofar dakinta yayi ya ganta kwance ta rufe fuskarta da pillow, ya isa kan gadon ya xauna kusa da ita ya dagota a hankali yace "Ummu Shureim" Bude ido tayi tana kallonsa, ya sakar mata lallausan murmushi yace "Mu je ku gaisa da Barrister" tace "Ya xo?" Yace "Sure" shi ya taimaka mata ta sauko saman gadon bayan ta sauko ta kwace hannunta shi dai bai ce komai ba ta sa hijab dinta suka fita dakin, gaisawa suka yi da Sudais ya mika ma Aliyu takardan hannunsa yace "Bata ta gani, I don't want to do anything without her knowledge" Aliyu ya amsa ya mika mata, karban takardan tayi ta bude tana kallon content din, bayan wani lkci ta Dago a sanyaye tana kallonsa, murmushi yayi yace "Is that okay?" Girgixa masa kai tayi a hankali tace "Barrister ka kyalesa kawai, na yafe masa even for the sake of my dad" Karban takardan Aliyu yyi yana dubawa, Barrister na kallonta yace "Are sure Amira?" Kai ta gyada masa tana murmushi tace "Sure Barrister, na yafe ma kawu na, sai dai kuma tsakaninsa da mahaliccin sa" mikewa Barrister yayi yace "Toh Alhmdllh, Allah ya yafe mana gaba daya, but I don't think ur forgiveness will count, coz dukiyar marayu yyi tampering da" Aliyu na gyada Kai yace "Haka ne" Barrister yace "Alryt xan koma, abinda ya kawo ni kenan dama" tace "Toh nagode sosai Barrister, bari in kawo maka ruwa" yace "Noo Amira, am okay" Tare suka fita da Aliyu, a sanyaye ta wuce sama don ita da gaske take jin ta yafe ma kawun ta. Gyara bedroom dinta tayi ta share ta goge ko ina, ta fito dakin kenan taga Aliyu ma ya fito rike da tray din abincin da ta kai masa da rana, karasawa tayi ta amsa tray din hannunsa, yana kallonta yace "Thank you" bata ce komai ba ta sauka downstairs ta wuce Kitchen. Tana xaune kan darduma bayan ta idar da magrib ya shigo dakin ya xauna gefen gado yace "Mu je ki raka ni" tace "Ina?" Yace "Gida, xan dauko wasu files a can" ta girgixa kai tace "A'a baxan fita ba, ni...." Ya katse ta yace "Ba fa shiga gidan xa ki yi ba" tace "Eh na sani" ya marairaice yace "Plss Ummu Shureim" turo baki tayi kamar xata yi kuka, yayi murmushi ya mike yace "Am waiting for you downstairs" A hankali ta mike ta linke pray mat din ta fita dakin, a kofar gidansu yayi parking yana kallonta yace "Baxan dade ba xan fito yanxu" kasa cewa komai tayi don sai take ga kamar bai dace ta ki shiga ba, can dai tace "Bari in gaida mumy" yace "Noo, ki bari ran Sunday sai mu xo gaisheta, it's already late yanxu" kallonsa ta tsaya yi, ya gyada kai yace "Yea dear" daga haka ya juya ya wuce ciki, kamar yanda ya fada bai dade ba ya fito ya ajiye takardun bayan mota sannan ya shiga maxaunin driver suka bar layin, yace "Me kike son ci in siya maki" ta girgixa kai tace "I am not hungry" yace "Nasan bakya Jin yunwa... abun dadi nake nufi" tace "Baxan ci komai ba" ya kamo hannunta yace "A'a, gwara dai a siya maki ko kaxa ce koh?" tace "Ni nace maka bana ci" parking yayi gun da ake siyar da kaji yace "Ai baki isa ba.." Daga haka ya fita ya siyo masu guda biyu, ya bude bayan mota ya ajiye, yana kallonta yace "Fresh milk kike so ko youghurt?" Tace "Daxu fa na ci abinci me xanyi da yoghurt ko fresh milk" Yar dariya yayi yace "Toh naji ni xan siya in sha" gun da ake siyarwa ya kara parking ya fita ya siyo chill fresh milk ya bude back seat ya ajiye sannan suka dau hanyar gida, da kyar khadijah ta yarda ta xauna parlor tana bata fuska, ta dinga kallon kajin da ya ajiye gabanta sai kamshi yake ga Madara a glass cup a gefe, so mouth watering, a hankali ta kai hannu ta dau cinyar kaxa daya tace "Ni wannan ya isheni" ya kalleta bai ce komai ba ya dau naman shi ma ya kai bakinsa, satan kallonsa tayi bayan ta cinye na hannunta don sosai naman yayi mata dadi, ta turo baki tace "Ashe ma da dadi" ya danne dariyar sa ko kallonta bai yi ba, ta dau wani kaxan ta fara ci, a haka sai da ta kusa cin rabin wanda ya ajiye mata, ta dau madaran glass cup din ta shanye gaba daya, sai a sannan ya dago yana dubanta yace "Amma da muka shigo ne kika fara jin yunwan koh?" Mikewa tayi da sauri ta wuce sama tace "Nima ban sani ba" Murmushi yayi ya bi ta da kallo kamar yanda ita ma take murmushin ta wuce sama, cire kayan jikinta tayi ta linke ta ajiye sannan ta shiga bathroom, wanke bakinta tayi, tayi wankan ta fito, Bata wani jima sosai gaban mirror ba, ta feshe jikinta da turarruka kala kala ta dau kayan baccinta ta sa, sannan ta sa net a dogon gashinta ta kashe wutan dakin ta hau saman gado ta kwanta ta ja duvet ta rufe jikinta ta lumshe ido. Har kusan karfe sha daya ta kasa bacci sabida thirst da take ta ji, ta tashi daga karshe ta sauka kan gadon, ta nufi kofa ta bude a hankali ta fito tana kallon kofar dakinsa dake a rufe, sauka downstairs tayi taga wutan parlorn gaba daya a kashe har kitchen, kunna wutan parlorn tayi ta nufi kitchen ta shiga tana kokarin kunna switch taji an cafkota, ihu ta fasa a mugun tsorace, ya kunna wutan da sauri ganin da gaske ta tsorata ya rungumeta yace "I am sorry iman, I didn't mean to scare the life out of you, wasa nake maki, kiyi hakuri plss" hawaye ya dinga xuba idonta jikinta na bari xuciyarta na bugawa, tausayinta yaji ganin da gaske ta tsorata, ya kasa karasa sauran coffeen da ya rage cup din hannunsa ya ajiye, yana rike da ita ya kashe wutan suka fito yace "I heard ur footsteps shi yasa na kashe wutan, am sorry for scaring you..." ita dai bata ce komai ba har lkcn xuciyarta bai dawo dai dai ba, suna isa stairs ya juyo da sauri yana kallonta yace "Me kika sakko yi" cikin sanyin murya tace "Ruwa xan sha" saketa yayi don xuwa ya dauko mata ruwan ta bi bayansa, yayi murmushi ya bude fridge ya fiddo ruwa ya xuba mata a cup ya mika mata ta amsa ta sha ya karbi cup din ya ajiye, yana rike da ita suka wuce sama bude dakinsa yayi xata kwace hannunta ta wuce nata dakin ya ki saketa ya jawota dakinsa ya rufe kofar, sanyi ne sosai a dakin saboda Ac da ya kure ga fitila kuma a kashe, xata bude kofa ta fita ya riketa murya can kasa yace "Kin san har yanxu ba muyi sallah mun nuna godiya ga Allah.. mu yi addu'ar xaman lafiya da kwanciyar hankali mai dorewa ba Iman?" Da sauri tace "Ni dai nayi, Kai ne dai baka yi ba" yace "Noo kamata yayi muyi tare" tace "I am not clean...." Kallonta ya dinga yi cikin duhun yace "Really??" gabanta na faduwa tace "Ehh" yace "Ban yarda ba" ta hade rai tace "Saboda ni makaryaciya ce?" Yar dariya yayi taji ya dauketa cak sai saman gado, ya kwantar da ita yace "I have to check for my self..." Kara tayi a rikice tace "Nashiga uku, don..." Bai bari ta karasa ba ya rufe bakinta, tun tana turasa tana son kwace kanta har ta gaji, lkci daya kuma jikinta ya mutu, kwata kwata Aliyu bai bata breathing space ba, ya dinga exploring dinta as if his life depend on that... daga karshe ta sakar masa jiki gaba daya, sai dai bakinta bai daina cewa stop it plss idan ma ba kasa kunne kayi sosai ba baxa ka ji me take cewa ba, lkci daya ta rikice masa ganin ba da wasa yake ba, nan ta fara hawaye tana rokonsa, sai take ganin abun kamar na 7 years back, the only difference is that he is not fierce, just romantic and very careful, upon her plea bai iya ya kyaleta ba duk da yayi kokarin ganin yayi hakan amma ya kasa.... Bayan lokaci me tsawo ya dago a hankali ya ga bata gefensa kamar ynda ya bar ta, mikewa xaune yayi da sauri, shesshekar kukanta ya dinga ji can other side of the bed, ya tashi da kyar ya nufi wajen, takurewa tayi waje daya tana kuka a hankali, jikinsa yyi sanyi ya duka gabanta yace "I am very sorry Iman, I...." Rasa abinda xae ce mata yyi ya dagota ta fashe da matsanancin kuka, ya rungume ta xuciyarsa na bugawa yace "I didn't mean to hurt you again" gaba daya tayi laushi, kuka kawai take, ya dagota ya kwantar kan gadon yace "Kiyi hakuri plss Iman, forgive me...." cikin rawar murya tace "Kace min baxan ji xafi ba" Kallonta yake cikin duhun don bai ma san ya fadi hakan ba, ya kwantar da ita kirjinsa a hankali yace "But did you feeling any pain?" Kai ta dinga gyada masa hawaye na xubo mata, yayi shiru bayan wani lkci ya kai bakinsa kunnenta yace "Just like the 1st experience?" Girgixa masa kai tayi, Yana shafa bayanta yana murmushi sanin da ba dan shi yyi deflower dinta ba da bbu abinda xai hanasa cewa budurwa ce ita, kwantar da ita yayi ya mike ya shiga bathroom, ya hada mata ruwan wanka, ya dawo ya kai ta bathroom din, shi ya taimaka tayi wanka tana nonnokewa sannan ya fito tare da ita, babu bata lokaci kuma bacci ya dauketa, sai a sannan ya kunna wutan dakin yana kallon bedsheet din gadon, Bai ga abinda yake xato ba, yayi murmushi ya dawo kusa da ita yana kallonta yana Kara jin wani mugun sonta na fixgarsa, it's just great being with her, and it's the sweetest thing he have ever imagined, tashi yayi daga karshe ya shiga bathroom yayi wanka shi ma ya fito ya shirya sannan ya kashe wutan dakin ya kwanta kusa da ita ta shige jikinsa kamar jira take, ya kankameta hade da lumshe ido.


Da asuba khadijah na jin Aliyu ya fita masallaci ta mike xaune a hankali, gabanta ne ya dinga faduwa from experience, duk da dai wannan karan ko ciwon kai bata ji ba balle na jiki amma tsoro ne fal xuciyarta, ganin lkci na wucewa ta mike cike da karfin hali, the pain wasn't as much as she was expecting... Ta lallaba ta fita dakin ta koma nata ta sa makulli, wanka ta fara yi ta dauro alwala ta fito, tana ta xaune kan darduma tana azkar bayan ta idar taji an murda kofa, kallon kofar tayi sai dai bata motsa daga inda take ba, a hankali yayi knocking yace "Iman, are you alryt..." Shiru tayi bata ce komai ba, tana ji ya bude kofar dakinsa ya shiga, bayan wani lkci ya fito, hade kai tayi da gwiwa jin yana bude kofarta da makulli, bayan ya bude ya tsaya daga bakin kofa yana kallonta, a hankali ya karasa dakin ya duka kusa da ita xai dago kanta ta ki yarda, da damuwa yace "Look at me plss Iman, are you okay..." ganin ba yarda xata yi ta dago ba ya mike ya dagota, ihu ta fasa masa ta boye fuskarta jikinsa tace "Ni dai bana soo" Dariya ta basa yana rungume da ita yace "Meye baki so Ummu Shureim" a hankali tace "Ka fita" murya can kasa yace "Kunya ta kike ji?" Kai ta gyada masa a hankali, sosai ta basa dariya ya nufi gadonta da ita, ya kwantar da ita ta rufe fuskarta da pillow, Xaunawa yayi gefenta yana murmushi yace "Sai ma mun yi wanka tare anjima xaki san meye kunya" Bata san lokacin da ta dago ba ta xaro ido tana kallonsa tace "What???" Sai kuma ta maida kanta da sauri tana murmushi wai ita kunya.... Wani salon soyayya na daban Aliyu ya dinga gwada ma Iman kamar xai maida ta ciki, ko da yaushe suna manne da juna, Khadijah bata taba tunanin haka Aliyu yake ba shi da kunya ko na taro ba, idan aka ce mata xai iya abinda yake mata baxata yarda ba, coz he look so innocent in the face, tun tana kunya tana noke masa har daga karshe tayi give up ita ma a gidan ta sakar masa kanta, gida ya koma kamar na India, kunyan da take ma da daddare shi ma duk ta ajiye sa gefe amma fa cikin duhu, ita kanta bata taba sanin tana da soft spot ma Aliyu ba sai a yanxu, har ranta take jin sa, sannan ko na minti daya bata son ya bar ta duk inda xa su tare suke xuwa. Ranan da suka cika sati biyu gidan tana kwance jikinsa a parlor yana operating laptop, a hankali tace "Abban shureim..." Yana kallonta yayi pecking cheeks dinta yace "Ummu Shureim" ta turo baki tace "kaga mun koma makaranta fa" yace "I thought as much, dama in two days time xa mu koma can ai" Tace "Toh Allah ya kai mu" yana shafa fuskarta yace "Ameen baby" a ranan suka tafi yi ma Mumy sallama da yamma, Khadijah na xaune tare da Baby a dakinta taga Barrister ya kirata yayi sau uku, ita dai bata ce mata komai ba, amma sai suka bata dariya, karfe biyar saura suka shiga dakin Mumy xa su mata sallama don har gidan Umma da umman su jawahir xa su je, Mumy tace "Toh Allah ya kai ku lafiya, ya kiyaye hanya" Khadijah dake durkushe kusa da ita tace "Ameen Mumy" Mumy tace "Toh sai kun dawo biki nan da few months" Aliyu yace "Wani bikin Mumy" sai da Mumy ta fara dariya sannan tace "Na kanwar ka mana" Khadijah tace "Mumy baby?" Mumy tace "Ehh" xaro ido tayi tace "Lahh Mumy ba mu sani ba" Aliyu ya xauna yace "Mumy da Ahmad din?" Mumy tayi murmushi tace "Wannan bada ta kawai Abban ku yayi, ba Ahmad bane, an basa hakuri shi" Aliyu ya d'an hade rai yace "Bada ta kuma? To who?" Mumy tace "Barrister Aliyu" da khadijah ta fara dariya sai da Mumy da Aliyu suka tsaya kallonta, ta mike da sauri ta fita xuwa dakin baby tace "Wato abun har da munafurci koh Baby, ni din ne baxa ki gaya ma ba koh?" Baby tayi murmushi don tasan kwanan xancen, a hankali tace "Shi yace ba sai na gaya maki ba, xai je har gida as a mother ya same ki ya gaya maki" khadijah na murmushi tace "Am soo happy wllh, Allah ya sanya alkhairi, ya nuna mana lokacin lafiya" Har bakin mota baby ta raka su, suka wuce gidan Umma, bayan Umma sun gaisa da Aliyu ta bi bayan khadijah da ta wuce ciki, Ganin yanda tayi kyau ta cicciko Ummu tayi murmushi tace "Ko ke fa da kika kwantar da hankalin ki daughter" murmushi kawai khadijah tayi ta sunkuyar da kanta, Umma ta xauna kusa da ita tace "In ji dai ba matsala?" Khadijah tace "Babu Umma dama sallama muka xo maki xa mu tafi can Uk" Umma tace "Maa Sha Allah, ai hutun ya kare, Allah ya kai ku lafiya my daughter" Khadijah tace "Ameen Ummata" Umma tace "Amma ku je har Umman su jawahir ku yi mata sallama" khadijah tace "Eh dama xa mu je Umma" Umma tace "Toh hakan na da kyau, kin san kawun ki yana yawan kira mu gaisa" Khadijah ta kalleta da sauri tace "Abbansu Safeenah?" Umma tace "A'a ba shi ba, mai bi masa" xaro ido khadijah tayi sai kuma tayi dariya tace "Umma Abban su Maimoon ne, dama umman su ta rasu 3 years back suka gaya min" Umma tace "Toh ya aka yi don Umman su ta rasu, Allah ya ji kanta" Dariya kawai khadijah take, Umma dai sai kallonta take, can ta turo baki tace "Umma ni dai don Allah kar ki ce masa A'a" buda ido Umma tayi, sai tayi dariya tace "Amma baki da kunya yarinyar nan" Khadijah ta mike ta fita tana dariya, minti talatin suka yi a gidan, xa su wuce umma ta ja khadijah xuwa daki tace "Daughter, ya kamata ku je can katsina da Aliyu ki gaida yayan Mahaifin ki" shiru khadijah tayi da farko, sai kuma a hankali tace "Toh Umma xa mu je" Umma tace "Good, Allah ya kiyaye hanya, ki kula da mijin ki fiye da yanda xa ki iya, ki kuma rike tsaftar ki don nasan kina da ita, Allah ya maki albarka" khadijah na murmushi tace "Ameen Umma" da haka suka bar gidan suka dau hanyar gidansu jawahir, can ma basu dade ba bayan sun yi ma Umman jawahir sallama suka koma gida. Da daddare ganin Aliyu xai takurata ta dinga turo baki tana kwace kanta jikinsa, ya kai bakinsa kunnenta murya can kasa yace "Baki son mu tafi da babynmu daga nan Iman" ta marairaice masa tace "Ni dai ka kyaleni bacci nake ji" yace "Plss" kukan shagwaba ta fara masa wanda hakan ya rikita sa, bai kyaleta ba sai da yaga ta fara bacci da gaske, ya fi awa daya kankame da ita, ko da yaushe jin abarsa yake intact, murmushi yayi ya manna mata kiss a lips daga karshe ya kwantar da ita ya shiga bathroom. Washegari suna breakfast tana kallonsa tace "Abban Shureim, Ina son mu je katsina mu gaida Uncle dina" ya kalleta yace "When, Kin san gobe da safe xa mu wuce" Tace "Toh idan mun dawo bikin su baby sai mu je?" Yace "A'a idan kin ce mu je yanxu ma sai mu je ai" ta langwabar da kai a hankali tace "Mu je plss" yace "Alryt then" karfe sha daya suka bar gidan, suka dau flight xuwa kano, daga can yayi masu charter na taxi da xai kai su har kt, tun da suka shigo kt misalin karfe daya da rabi na rana gaban khadijah ke ta faduwa, taxin ya ajiye su dai dai gidan kawunta, ita kanta tayi mamakin yanda ta gane gidan, Aliyu ya fito ita ma ta fito tana kallonsa tace "Mu shiga" Bin bayanta yayi suka shiga gidan, Babu kowa compound din da ya xama wani iri kamar gidan da yayi shekara hamsin, Har parlor ta isa da sallama Aliyu ya tsaya daga bayanta, kallon kawun nata dake xaune k'asa a one side of the parlor yana fama da ciwon kafa sosai tayi, ta kalli Hajiya maimuna da ta fito kitchen jin sallama ta gaisheta a sanyaye, daga ita har yaran dake parlorn kallonta suka dinga yi kamar basu santa ba, ita dai tasan basu gane ta bane, Ta isa har kusa da ita a hankali tace "Mama Khadijah ce" bude baki Hajiya Maimuna tayi tana kallonta da wani irin mamaki, Khadijah ta sauke idonta kasa, ba ita ba har kawu Jibril shi ma bude baki yyi lkci daya hanjin cikinsa ya kada don kullum da threat din Barrister Sudais yake kwana yake tashi, Aliyu ya xauna kusa da

Please Login or Register in order to submit comment