Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tace "What happened Khadijah??" Ta marairaice tace "Umma ina missing din ku ne na taho fa" Umma ta hade rai tace "Kina da hankali kuwa, kamar warce xata taho daga kano, yaushe kika koma da har xaki taho yanxu" shiru ta yi bata ce komai ba, Umma ta saki baki tana kallonta a mamaki, juyawa khadijah tayi ta nufi jakar Umma dake ajiye parlorn ta bude ta fiddo kudi tace "Umma bari in kai ma mai adai daita" daga haka ta fita ta kai ma sa kudin sa twins dinta na rike da ita, suna dawowa parlor duk suka haye kanta Shureim yace "Anty ina wannan uncle din nan dake UK, did he tell you to greet us?" Khadijah tayi murmushi tace "Sure sweetheart" Sudais yace "Anty is he also from Nigeria, I like him" Umma dake kallonsu tace "Wani uncle suke fadi?" Khadijah ta saci kallonta tace "Neighbor dina ne fa Umma" Umma tace "Ba mace bace kwanaki da muka je?" Khadijah tace "Ayya, Nancy ai ta tashi" Shiru Umma tayi kafin tace "Toh dai a kula, Allah ya ci gaba da tsare ku" A hankali khadijah tace "Ameen" Umma tace "Toh don me wai baxa ku xauna tare da Vanessa ba?" Khadijah tace "Umma am nt comfortable a gidanta ne" Umma tace "You have no choice, bana son xaman ki gida daya da namiji" da sauri khadijah ta kalleta, murmushi tayi tace "Umma he is a Nigerian, kuma I think bahaushe" Umma tace "So?" Shiru Khadijah tayi, Dai dai nan wayar dake jakarta ya fara ring ta bude jaka da sauri ta fiddo tunawa da tayi wayar khaleel ne, shiru ta yi tana kallon number kafin ta daga, muryarsa taji yace "Are you home?" Ta saci kallon Umma Kafin ta mike tace "Uhn" daga haka ta wuce daki yaranta suka bi bayanta Umma ta bi su da kallo.

Flight Aliyu ya bi ya taho kaduna, Ji yayi gaba daya ba wani sauran damuwa a tare da shi, lkci lkci sai yyi murmushi, har ya isa gida a taxi tunanin Khadijah yake, he is just happy seeing her today, bayan ya sauka taxi mamakin me ake yi a gidan ya dinga yi ganin mutane da manyan motoci har su Usman da Sanusi shadda ce sabuwa jikinsu, suna ganinsa suka washe baki suna masa sannu da dawowa, ya amsa gaisuwarsu ya entrance din gidan, ganin takalma da yawa alamar mutane ne sosai parlorn ya xaga ta baya, iklima ce bakin tap a durkushe tana kwarara amai, ya karasa yana kallonta ganin uban kunshin da aka mata ga kitso an yaryara mata a kai, yace "Baki da lafiya ne?" Jin muryarsa ta dago da sauri, lkci daya ta mayar da kanta ta sunkuyar, tana maida numfashi da kyar tace "Sannu da dawowa yaya Aliyu" bai damu da ya amsa ba yace "Me ake yi a gidan nan?" Shiru tayi da farko kafin tace "Aurenmu" Few seconds yyi amfani da wajen apprehending abinda ta fada, cike da confusion yace "Aurenmu? Aurenmu da wa?" Still bata kallesa ba tace "Ni da kai" bude baki yyi yana kallonta dai dai fitowar Anty khadijah tayi wani shegen haske ta xama katuwar gaske, tana ganinsa ta saki guda tace "Saukar yaushe ango?" Aliyu na xaro ido yace "Anty ban gane ba, ango kuma?" Anty khadijah na taunar cingam da ya cika waje da kara tace "Tafi Anty fati na daki xata maka bayani yanda xaka gane my son" daga haka ta nufi 'yar ta tace "Ki taso mu je, mai make up din ta gaji da jira" janta tayi suka Wuce ciki suka bar Aliyu tsaye baki bude, har lkcn shi dai bai fahimci komai ba. Wucewa ciki yyi direct ya tafi sama Dakin Mumy ba tare da ya kula da mutanen dake parlor ba, ita da frnds dinta sai mahaifiyar Abbansa da suke kira da yaya ne xaune dakin, yyi hankalin gaishesu kafin yace "Mumy I don't get what's happening in this house" Yaya tace "Bikin ku ake yi da 'yar uwar ka" Aliyu ya yo waje da ido yace "Wace yar uwar tawa?" Yaya tace "Iklima, Allah bai yi da Hanan ba" Wani kallo Aliyu ya dinga yi mata kafin yace "Allah ya kiyaye, wace iklimar? Iklima da ta gagari kowa gidan nan xa a makala min, No Mumy I have never failed you but... No mum me yasa xaki min xabin da xai cutar da ni, mumy kema kinsan iklima ta fi karfina, Mumy ki rufa min asiri..." Tsawa Mumy tayi masa ta mike tana masa wani mugun kallo tace "Get out Abuturrab, idan an kai ma iklima gidan ka kayi gunduwa gunduwa da namanta ko kuma ka koro mana ita, fita nace" Juyawa Aliyu yyi ya fice daga dakin, Yaya tace "Fatima, da gaske yarinyar ta gagari kowa? Ni dai an san ba saninta nayi ba, kar ku cutar min jika" Mumy ta hade rai tace "Yaya yar yar uwata ce uwa daya uba daya fa" tana fadin haka ta fita dakin, kawayenta suka bi ta da kallo.

Washegari da yamma khadijah na xaune parlor tare Umma da Nanny dake yankan alaiyahu, reading material dinta ne hannunta tana dubawa, Umma tace "Wai da wa su sudais ke waya haka ne tun daxu Khadijah?" Khadijah ta dago kanta tana kallonta a hankli tace "Umma wani ne" Umma tace "A ina kika san sa? Ko in ce a ina suka san sa" Murmushi kawai khadijah tayi bata dai ce komai ba, jin little sudais na kiranta ta juya tana kallon direction din dakin sai ga shi tare da d'an uwansa, wayar hannunsa ya mika mata yace "Uncle yace we shud hand over the phone to you" Khadijah ta amshi wayar tana satan kallon Umma dake kallonsu ta mike ta wuce daki, rufe kofar dakin tayi ta xauna gefen gado ta kai wayar kunne tace "Yes? Ina ji" Yace "Yea I knw kina ji, can I come over to see d boys now?" Shiru Khadijah tayi tana kallon agogo kafin tace "Xan gaya ma Umma tukun" yace "Alryt then, I will be waiting for ur call" a hankali tace "Tohm" daga haka ya katse wayar, tunanin me xata ce ma Umma ta dinga yi kafin ta mike ta fita, xauna gefen kujera tayi murya can kasa tace "Umma someone is coming over now" Umma ta daga kai ta kalleta tace "Who?" Ta d'an turo baki tace "Wani ne" murmushi Umma tayi tace "Allah kawo sa" khadijah ta mike ta koma daki, text ta tura ma khaleel na address din unguwarsu da house number. Cikin minti talatin khaleel ya iso gidan, Khadijah ta sa Hijab ta fito daga dakinta ta shiga na umma tana kallonta tace "Umma yana waje" Umma tace "A wajen xa ki bar sa baxai shigo ba" murmushi kawai khadijah tayi ta fita, tun da ta fito gate take kallon motar da khaleel ya xo da shi har ta isa gun motar ta tsaya tana wasa da fingers dinta, bude motar yyi ya fito ya xaga ta inda take, farar gizna ne jikinsa sai walkiya yake da hula, wani kyau yyi na musamman ya dawo kamar balarabe cikin shigar hausawa, Ita dai bata taba ganinsa da irin shigar ba ta dauke kai daga kallonsa tace "Dama kana sa manyan kaya?" Ya d'an bude ido ya rungume hannunsa ya jingina da motar yace "Dama kina sa Hijab?" Dariya ya bata amma bata yi ba tace "Aa sai kananun kaya in yi sagging wandon" xaro ido khaleel yyi yana kallonta, tayi murmushi bata kalli direction din sa ba, Kallonta ya tsaya yi na few seconds kafin yace "Where are the boys?" Tace "Suna ciki" yace "Amma kin san ba wajen ki na xo ba dai koh" shiru ta yi trying her best not to look at him, can tayi murmushi tace "Alryt then" daga haka ta nufi gate, Wara ido yayi yace "Khadijah" sai da ta isa gate tace "Bari in turo maka su" yace "Wait..." Amma tuni ta shige gidan, murmushi yyi yana shafa beard dinsa, ba a dau lkci ba sai ga yaran sun fito suna ganinsa suka taho da gudu suka rungumesa ya daga su sama gaba daya happy seeing them, kai kana ganin yaran kasan su ma ba karamin farin cikin ganin khaleel suka yi ba, ya bude back seat din motar ya sa suka shiga sannan ya xaga ya shiga maxaunin driver, wayar sa ya dauka ya shiga kiran Khadijah, kin dauka tayi yayi murmushi ya tada motar ya bar layin da yaran. Tun da Aliyu ya dawo masallaci da asuba ya sa makulli dakinsa, shi dai ya kasa gaskata wai iklima aka aura masa, yarinyar da idan ta fita tun safe sai dare wani lkcn xata dawo gida, uwar kuma tace gidan kawunta take xuwa, yau idan ka ga wannan wayar hannun iklima to gobe wani daban xa ka gani, islamiyyar ta ki xuwa, bokon kuma anyi withdrawing, rike kansa yyi xuciyarsa na masa kunna, kwankwasa kofar dakinsa aka yi for the countless time, ko kallon direction din kofar bai yi ba, "Yaya nice baby ka bude plss" muryar da ya ji kenan, ya lumshe idanuwansa ya bude, mikewa yyi da kyar ya nufi kofar ya bude yana kallon Kanwar tasa, ta shigo ya rufe kofar, da damuwa tace "Yayanmu kayi hakuri, I don't knw what came over Mumy, bn san me yasa tayi haka ba bayan ita da kanta kullum complain take a kan iklima... Her character is so obvious to everyone, kowa yasan abinda take but mumy tayi kamar bata sani ba ta hada ku...." Aliyu ya xauna gefen gado ya rike kansa, Baby tayi tagumi tana kallonsa, bayan kusan minti goma tace "Kayi hakuri yaya" ya dago da jajayen idanuwansa yana kallonta yace "Go make me a cup of coffee" Baby na fita daga dakin dai dai fitowar Anty khadijah da ke ta kai kawo kamar warce tayi ma sarki karya, barin da taga Aliyu ya bude ma Kanwar tasa kofa, xuwa yanxu gidan ya watse sai yan uwa na jini, bin baby tayi downstairs tace "Takwara me Aliyun yace maki?" Baby taki kallonta tace "Abu yace in kai ma sa" Anty khadijah dake ta bin ta tace "Me kenan?" Baby tace "Coffee" Anty khadijah tace "Atoh ni har na gaji da maganar bai ci komai ba tun daxu, yanxu abinda xa ayi kawai kiyi wucewar ki xan hada masa in ba matarsa ta kai ma sa, mutum ya sha hanya haka kuma ya makale daki tun jiya babu abinci" Baby tace "Anty amma ai baki san yanda yake son coffee dinsa ba, ni xan masa" Anty khadijah ta galla mata harara tace "Toh uwar iyayi, kin tashi gabana ko sai na mare ki, idan nayi masa kar ya sha" daga haka ta wuce kitchen baby ta bi ta da wani kallo, Anty khadijah na shiga kitchen ta tura kofar kitchen din ta rufe ta yi saurin ciro wani kulli a bra dinta, "Son da xai mata sai ya fi wanda yake ma uwarsa da kowa na duniya... In dai ya sha maganin nan" muryar gardin da ya bata maganin kenan ke kai kawo a kunnen Anty khadijah kamar yana kusa da ita, har wani rawa hannunta yake ta juye gaba daya a cup sannan ta debi coffee powder ta xuba a kai ta xuba ruwan xafi ta jefa kwayan sugar biyu, sama ta tafi da sauri ta shiga daki gun iklima dake kwance, Anty khadijah tace "Ni fa dadina dake shegen son jiki, daga d'an xaxxabi dubi yanda kika wani yi laushi kamar warce tayi watanni ba lafiya, a haka xa a kai ki gidan Aliyun gobe" Iklima da ta lullebe da bargo tace "Ni wallahi ki rabu da ni don ba ke ce ke jin abinda nake ji ba, duk kin bi kin dame ni tun daxu" Anty khadijah tace "To uwata sai ki rufe ni da duka ai, ni ki tashi ki kai ma Aliyun coffee" iklima ta xaro ido tace "kaji ta, Salon ya koro ni.... Mutumin da tun jiya yake daki" Anty khadijah tace "Toh don ubansa ba sai ya koro ki ba, kilan ma a can xa ki kwana ki tashi kina bata lkci..." Gun kayan kwalliyan Iklima na amarya Anty khadijah ta nufa ta dauko wani turare can kasa a karamin kwalba ta bude ta shashshafa mata a ko ina na jikinta, iklima da ke ta wani yatsine fuska ta koma ta kwanta tace "Mama wllh jiri nake gani, anya xan iya fita" hararata Anty khadijah tayi tace "Xan je in dauko maki shayin a dai don ki fita nan ki shiga dakinsa baxa ki ce min baxa ki iya ba" daga haka ta wuce kitchen ta dauko coffeen dake rufe a mug ta kawo ma iklima, da kyar ta tashi ta karba tana duddukawa ta fita dakin, a hankali ta tura kofar dakin Aliyu dake kwance ta shiga ta rufe Ta isa kusa da gadon ta ajiye mug din hannunta a kasa, bude ido Aliyu yyi jin yanda kamshi ya bade dakin suka hada ido da iklima, karasowa kusa da shi tayi tace "Yayanmu sannu da hanya ga coffee din na maka" Wani mugun kallo Aliyu ya dinga mata yace "Kina hauka ne xa ki shigo min daki" tace "Da daban xama matar ka ba ina shigowa ne" bude kofar dakin aka yi sai ga baby ta shigo sau daya ta kalli iklima ta harareta ta durkusa ta ajiye tray din hannunta tace "Ga abinci yaya mumy tace in dibar maka" daga haka ta bude warmer din abincin iklima ta yamutse fuska ta dauke kai da sauri, lkci daya aroma din abincin ya cika dakin, da tari ta fara, sai kuma ta toshe baki, da gudu ta mike kafin ta isa kofar bathroom ta wanke tiles din dakin da amai, kallonta Aliyu yake ko kiftawa babu ta dinga amai kamar xata shide, baby ma sai kallonta take, tashi yyi ya isa gabanta da wani expression yana kallon gaba daya jikinta, mikewa tayi bayan ta gama ta fada kan gado tana sauke numfashi ya koma kusa da ita yana kare mata kallo da kyau, squeezing fuskarsa yyi yace "What??" Lkci daya ya juya ya fice baby ta bi bayansa da sauri, Mumy na haurowa sama tare da Anty khadijah dake bata shawarar kawai gobe su Aliyu su wuce gidansu yau dai su kwana a gidan, ganin Aliyu Mumy ta daure fuska don tun daxu yaki fitowa har ita ta yi masa magana amma ya ki bude kofar, yana kallon mumy cikin wani yanayi yace "Mumy ita mai cikin xa ku ce kun aura min?" Kallonsa Mumy ta tsaya yi cikin rashin fahimta haka ma Anty khadijah, baby dake tsaye gun ta xaro ido tana kallonsa, Da mugun mamaki Mumy tace "Halan Aliyu ya fara xarewa ne ni Fatima?" Yace "Xarewa kuma Mumy wllh ciki ne da iklima, don't forget my profession idan ma baku yarda ba yanxu sai a kira wani likitan, gashi can yanxu ma amai ta gama yi" Anty khadijah ta saki ta salati ta fashe da kuka tace "Aliyu, ita yar tawa xaka ma wannan gagarumin sharrin don a rufa ma asiri an aura mata kai? Ita iklimar ce ke da ciki?" Aliyu ya mata wani kallo yace "Sharri Anty? sai a tafi asibiti yanxu ai, ni dama nasan a day like this na nan xuwa very soon, ina ce har guest lodge na taba ganin iklima na same ki daki na gaya maki few years back, me kika ce min then? Cewa kika yi na tsaneta na sa mata ido, Duk yawon da take ta kai dare kin taba tsawata mata, of course no sai dai kice gidan kawunta taje, so it's nt a thing to be surprise don iklima na dauke da ciki ynxu" tuni sauran yan biki dake gidan suka shiga fitowa corridor din, Mumy dai ta saki baki ta kasa cewa komai, Anty khadijah dake ta xufa tace "Tunda abun yar tone tone ne sai mu yi ta ai Aliyu, wato har kai kana da bakin da xaka bude ka kira 'ya ta yar iska ka mance lkcn da kake tashan naka iskancin, ka mance irin yanda kayi ma yar mutane fyade a cikin gidan nan, wanda ta dalilinka ta bar gidan har yau bata dawo ba, duk ka xata ban sani ba koh???" Lkci daya komai na Aliyu yyi still ya tsaya kallonta ko kiftawa babu, Anty khadijah ta juya tana kallon mumy tace "khadijah dai da kika sani, yarinyar da kika dau aiki ta yi wucewarta ko sallama babu shekaru kusan shidda baya, ya fada maki abinda yyi mata ta bar gidan da bakin sa yau...." Aliyu ya lumshe idanuwansa da suka kada lkci daya ya ji kansa na sara masa, kallonsa mumy ta dinga yi kamar idonta xai fito haka kanninsa gaba daya da bak'in da suka fiffito, Anty khadijah na girgixa kugu tace "Ko baxa kayi bayanin ba in taya ka?" Bude ido yyi da kyar yana kallon Mumy.

Anty khadijah na kallon Aliyu da kyau tace "Ko baxa kayi bayanin ba in taya ka ne dakta?" Bude ido Aliyu yyi da kyar yana kallonta, lkci daya idanuwan Mumy suka kawo ruwa kana ganinta kasan ba karamin shock ta shiga ba, Aliyu ya isa gabanta ya duka kan gwiwowinsa cikin sanyin murya yace "Mumy..." Dakatar da shi tayi hawayen idonta na sakkowa tace "Irin tarbiyar da nayi maka kenan Aliyu.... Yanxu yar mutanen kayi ma haka?" Ya rufe fuskarsa jikin kafarta cikin rawar murya yace "That's the greatest mistake of my life mum, shine abinda na kasa gaya maki shekaru shiddah kenan, mumy ba halina bane kema kin sani, ban san ya aka yi ba ranan, it look as if I was possessed, I ruin the little girl... Mumy I...." Kasa ci gaba yyi hawaye na sakko masa, Anty khadijah ta tabe baki tace "Lallai Abuturrab baka jin kunyar karya? abu ya faru ba sau daya ba ba sau biyu ba ka kirasa mistake? Tunda abun ba arxiki har ya kai ga ka fara yi ma 'ya ta sharri to wllh nima baxan duba abinda ke tsakanina da mahaifiyar ka ba, gwara in tona maka asiri, idan ni baka ji kunyar toxarta ni da iklima ba to nima baxan ji kunyar ramawa ba a matsayin ka na d'an yayata" daga haka ta bar wajen ta shige daki... Aliyu ya bi ta da kallo, duk abun nan da take fada fa ba ji yake ba mamakinsa shine ya aka yi tasan abinda ya faru tsakaninsa da Khadijah bayan bata gida ranan, how is that? Fitowa Anty khadijah tayi daga dakin rike da iklima da ta sa ma Hijab suka sauka downstairs kamar xata tashi sama tana matsar kwalla tace "Da raina kayi ma yar cikina irin wnn sharrin koh Aliyu, duk matsayina gun uwarka baka gani ba saboda na rufa maka asiri da yawace yawacen da kake nace a aura maka 'ya ta shine xaka mana wannan cin mutuncin ka saka min da sharri" gidan ta bari gaba daya tare da yar ta, Mumy ta juya ta koma dakinta a sanyaye, Aliyu ya kasa daga kai ya kalli kanninsa da sauran relatives dake wajen. Anty khadijah na fita da kafa suka karasa bakin titi da iklima, hankali tashe take tambayarta yaushe rabon da ta ga al'adarta, iklima ta turo baki tace "Oho nima ban sani ba" dundu ta kai mata tace "Kaji min shegiya wai baki sani ba, ni nake maki al'adar? To wllh sai dai ki daura ma ubanki hawan jini ba ni ba, mu je asibitin ai xa su mana bayani a can, in ma ya kama in kashe ni Wllh sai in kashe Ki a can din, tunda duk abinda nake maki bakya gani ni xaki ja ma abun kunya ni xaki kunyata a idon duniya" Ganin sun shiga Napep yasa Anty Khadijah tayi shiru sai girgixa kafa take tana Allah Allah ta ganta a asibiti har suka isa asibitin dai, iklima kam ko dar sai ma gyangyadi da take ta yi a napep din, suna shiga asibitin likita ya tabbatar ciki gare iklima, Anty khadijah ta daura hannu a ka tana xaro ido tace "Na shiga uku na lalace ni Khadijah, iklima yanxu ni xa ki ma haka, a ina kika je aka maki ciki, don na sake maki sai ki tona min asiri iklima? Ni xa ki kunyata?" Shi dai likitan kallonsu kawai yake, Anty khadijah ta share xufar dake keto mata ta hadiye yawu da kyar tace "Likita ko nawa kake bukata ka fada xan baka ka raba ta da wannan bala'in dake tare da ita ka rufa mana asiri" likitan yace "A'a ba ma haka a nan Hajiya ku yi hakuri, ku je wani asibitin..." Anty khadijah ta fashe da kuka a karo na farko tace "Haba bawan Allah, kai baka taimako ne, wllh dariya xa a mana ka rufa min asiri ina da makiya da yawa duniyar nan, ka ji tausayina ka taimaka mani" Likitan yace "Wato kin fi so kiji kunyar lahira a kan ta duniya kenan Hajiya?" Da sauri Anty khadijah tace "Eh wllh" sake baki yyi yana kallonta, can ya gyada kai yace "Gaskiya ne, toh Allah ya shirye ku, kuyi hakuri ku fita akwai patients da xan yi attending ma yanxu, mu ba ma aborting ciki a nan" tashi Anty khadijah tayi tana masa matsiyacin kallo tace "Yanda ka ki taimakona kai ma haka yar ka xata jajibo maka abun kunya ka rasa madafa in sha Allah, mara imani kawai..." daga haka ta ja Iklima kamar xata tashi sama suka fita, haka Anty khadijah suka dinga yawo hospitals tana neman inda xa a cire ma iklima ciki har dai ta samu wani da kyar, kudi ba na wasa ba ta bada aka yi aikin, unconsciously ta tafi da iklima gidan wata da suka hadu a kauyen da take yawan xuwa suka kulla abota suke kawance kamar xa su hadiye juna, kwanan matar uku gidansu Aliyu lkcn biki, jiya ta baro gidan bayan an gama komai ba rabon xa ayi komai a gabanta, Hajiya Laure sai kallon iklima dake kwance take da mamaki bayan Anty khadijah ta mata bayanin komai tana matsar kwalla, can Hajiya Laure ta sauke ajiyar xuciya tace "Toh ai baki ga ta kuka ba Hajiya Khadijah neman mafita xa ayi, yanxu dai a takaice bbu auren kenan?" Anty khadijah ta tsayar da kukan da take da sauri tace "Aure kai, aure na nan daram dam ba inda ya je, ai ko hauka nake baxan ce masu cikin ne ba har an cire, nunawa xan yi kawai gidan ki na kawota da xuciya ta debeni" Hajiya Laure tace "Gaskiya ne, toh wai kin ma yi yanda aka ce maki wajen nan da muka je ranan kuwa?" Anty khadijah tace "Ba gashi nan ta sa nayi asara ba yanxu don nasan ba sha xai yi ba, ni wllh da tun kafin bikin nasan da shegen cikin nan da na je an cire, sai ma kin ga ko gama xama halitta cikin bai yi ba, a can wani gutter na jefar kafin mu shigo nan don likitan cewa yyi mu tafi da shi kar mu ja masa matsala" Hajiya Laure tace "Alhmdllh da abun ya xo a haka ba sai da aka kai ta gidansa ba, amma shi ma dai ya aka yi har yasan tana dauke da cikin?" Anty khadijah tace "Toh ai likita ne shi din" Hajiya Laure ta xaro ido tace "Kai haba, to yanxu baxai gane cirewa aka yi ba?" Anty khadijah tace "Yo ya gane mana ai wllh sai yyi xaman aure da 'ya ta ko ya ki ko ya so, sai ya xauna da ita don ubansa" Hajiya Laure tace "Toh kuma har yanxu uwar ta sa ba ta kira ki ba?" Anty khadijah tace "Tana can na tara mata xafi, ina labarin da na taba baki a kan wata yarinya da ta taba dauka da dadewa??" Hajiya Laure tace "Eh, eh na tuna, wannan dai da kika ce a sunan me aiki ta dauketa, da kika sa Aliyu ya lalata ta" Anty

Please Login or Register in order to submit comment