Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

in kara shigarsa har karshen rayuwata don nasan baki da kowa Khadijah, Wa ennan makiran dake gidan dama tuni sun sanar ma Alhaji kafin ma in dawo, ina shigowa kuma ya bani takardata kamar jira yake, hakan yasa naji bakin ciki kamar ya kashe ni domin, ce maki nayi ki tafi kar ki kashe min aure duk da bai kai xuciya ba sai gashi sakin ma na walakanci yyi min don ce min yi 1st thing da safe in tattara ina wa ina wa in bar masa gidansa, hakan kuwa aka yi don ban jira gari ya waye ba na fita neman wanda xai siya kayan daki na, ina siyarwa kuma kafin sha biyu na bar masa gidansa, da kudin kayan ba tafi Ethiopia... Bana son in dinga tuna yanayin da na shiga rashin ki Khadijah, ni dai kawai ki gafarce ni domin ni na ja maki komai da ban kai ki gun yakumbo ba da duk hakan bai same ki ba, ita kuma Yakumbo bani da abinda xance a kan ta yanxu domin kuwa ta riga mu gidan gaskiya" Khadijah ta dago da sauri tana kallon Umma tace "Umma yakumbo ta rasu?" Umma tace "Ta rasu kusan shekaru biyu kenan, electric ring ne ya ja ta har lahira, wai ta sa ruwan xafi a daki" jikin khadijah yyi sanyi ta ma rasa abinda xata ce, bayan wani lkci tace "Allah ya ji kanta" Umma tace "Ameen" a hankali khadijah tace "Umma na ki yafe min" sai kusan karfe uku suka kwanta, washegari da safe Umma tayi ma su Sudais da Shureim wanka suka fito parlor, Nanny da ta gama breakfast a kitchen ta fito ta gaida Umma, Umma ta amsa mata da murmushi nan tayi mata godiya kan tsayawa ma khadijah da yan biyun ta da tayi all this while, satin Umma daya a gidan tace ma khadijah xata koma kasar su amma xata dawo, kuka khadijah ta fara yi tace "Umma kina son ki tafi ki kara bari na ne" Umma tace "Noo khadijah xan dawo, ki bari in je in yi sallama da dangina sai in dawo mu xauna, amma fa baxan xauna wannan gidan ba sai dai in kama mana haya a Kaduna, wannan kuma ki rufe masu kawai" a hankali khadijah tace "Kaduna Umma?" Umma tace "Ehh" sauke idonta Kasa tayi bata ce komai ba, Umma tace "Forget ur past Khadijah, life moves on, don wani baxa ki ki xama a garin ba Beside gari me girma ma a ina xaki gansa?" Kai kawai khadijah ta gyada mata, wannan kuma shine mafarin komawarsu Kaduna, suka bar gidan da Sudais ya mallaka ma twins dinta a Abuja, life in Kaduna was smooth for them, sai dai khadijah ta kasa kwantar da hankalinta ta xauna lafiya a garin, ko yaya sai taji abinda ya faru shekaru uku na dawo mata duk da a kinkinau gidan da Umma ta kama masu haya yake, Tunanin da ta kasa cirewa a ranta yasa ciwonta ke yawan tashi wani lkcn har da kwanciya asibiti, hakan ya dinga daga ma umma hankali ta shiga tunanin to wani garin kuma xa su koma, don gaskiya bata son kano, a hankali dai khadijah ta hakura bayan watannin su shidda Kaduna. Kasuwanci sosai Umma ke yi don har Dubai tana fita Allah ya dubeta lkci kankani dukiyarta ya bunkasa, yanda take ji da jikokin nata ko Khadijah bata samu wannan gatan ba, tamkar ta mayar da su ciki take ji, su ma kuma haka suke sonta don ko da yaushe suna manne da ita, duk anguwan babu wanda yasan yaran Khadijah ne yan biyun masu shiga rai duk tunaninsu umma ce ta haifesu Nanny ma na tare da su har lkcn, kuma kusan tare da ita Umma ke fita waje ta xama kamar yar uwarsu, yanxu kam su sudais da baki ya bude basa gudun uwar ta su da suka dauka yayarsu ce Umma kuma Mumynsu, a haka Umma ta yi iya kokarin ganin khadijah ta samu admission a University of Cambridge dake UK, Khadijah bata ji dadi da farko ba ganin pharmacy suka bata don ba shine burin sudais a kan ta ba, amma umma tayi convincing dinta to go for it, shine ta tafi a haka, farkon xuwanta kasar tare da Umma Nanny da yan biyun ta suka taho suka mata sati sannan suka koma nan kuma ta mayar da hankali tana karatu ba ji ba gani domin xama qualified pharmacy, and then..... 1st khaleel ya sa ta gaba a kasar, that not being enough sai gashi ta hadu da wanda bata burin sake gani har karshen rayuwarta, why????

Silence din kusan 3 minutes ne ya biyo baya a parlorn, a hankali Khaleel ya dago kansa yana kallon khadijah da ta hade kanta da gwiwa, har ransa yake jin shesshekar kukanta, gashi ya kasa cewa komai, he is just lost of words, jinginar da kan sa yyi da kujera na kusan minti biyu kafin ya tashi a hankali ya isa gabanta ya duka ya dago kanta yana kallon idanuwanta da suka yi jajir, ta yi saurin sauke idonta daga kallon nasa kwayar idon da su ma suka sauya kamanninsu xuwa ja wasu sabbin hawayen na sakko mata, har lkcn Khaleel ya kasa cewa komai sai kallonta yake, bayan wasu dakiku abinda ya fito bakinsa cikin xaxxakan muryarsa shine "Forget about sudais, he did what he did for the sake of Allah, eraze him of ur mind"

Da sauri khadijah ta dago tana kallonsa, ya mike ya koma kujerar da yake xaune yace "Yeah, ki mance da kin ma taba sanin sa a rayuwar ki, I mean that sudais..." Khadijah dake ta kallonsa ko kiftawa babu tayi karfin halin cewa "Ko saboda me?" A takaice yace "Ohk, it seems biyansa abinda ya maki kike son yi kenan?? If that's ur wish kema xaki iya taimakon marayu ai, I see no reason for good six years xa ki dinga tunani daya ba, beside he needs nothing from you, domin Allah yayi kuma Allah ne xai biyasa" Khadijah ta hade rai ta mike tana masa wani kallo tace "I regret telling you who i am, of all my story... part din sudais kadai ka ji da kyau halan? Shi kadai ka iya recalling? I just wasted the time I was suppose to use for sleeping" Daga haka ta nufi daki ta bar masa parlorn tana share hawayen idonta, Khaleel ya bi ta da ido ko kiftawa babu, jinginar da kansa yyi da kujera ya lumshe ido a hankali, wani mugun tausayinta ne ke shigarta, Sudais? Abinda ya fadi kenan a xuciyarsa ya bude ido da sauri, can ya tabe baki ya mike, ya fi minti biyu a tsaye yana kallon agogon dake nuna karfe uku saura kafin ya nufi bedroom dinta, xaune ya ganta kasa ta hade kai da gwiwa, Aliyu ne kawai ya fado xuciyarsa... ya hade hakoransa yana imagination kala kala a xuciyarsa, can yyi wani murmushi ya karasa cikin dakin yana kallonta ya durkusa gabanta, da farko rasa abinda xai ce mata yyi, can a hankali yace "Am sorry Khadijah, you misinterpret what I meant, ur story.... It is just heartbreaking, it's sad... you've past through a lot in life at a very tender age, but am happy you proved to be a strong lady, strong lady indeed...." Shiru yyi yana kallonta ko kiftawa babu har lkcn ta ki dago kanta, a hankali ya kai hannunsa ya dago ta suna hada ido ta rufe idon, murmushin sa mai kyau yyi yana kallonta, murya can kasa yace "Those cute boys...." Sai kuma yyi shiru, bayan wani lkci yace "You are going no where from UK, Aliyu ne xai bar maki UK ba ke xaki bar masa ba am giving you my words, kina nan har ki gama karatun ki" ta bude idonta a hankali tace "Ae ya riga yasan makarantar, he will surely keep on looking for me" hawaye ne ya cika idonta cikin sanyin murya tace "Ni ban san me xan masa ba yake nema na" murmushi Khaleel yyi yace "Xai daina neman ki soon" Tana son kallonsa amma idanuwansa are not encouraging, ya lura da haka sai ta basa dariya ya mike yace "Alright then, life moves on, ki kwantar da hankalin ki babu wanda ya isa ya hana ki walwala a kasar nan am assuring you, ki tashi kiyi wanka sai kiyi sllh if you wish and then go to bed, the night is far gone" Khadijah dake wasa da fingers dinta tace "But ina son xan je in ga su Umma..." Yace "When?" A hankali tace "Ko gobe" shiru ya d'an yi kafin yace "Alryt then Allah ya kai mu" Ya fi minti uku a tsaye har sai da ta daga kai ta kallesa ta ga kallonta yake tayi saurin dauke kanta, yayi murmushi murya can kasa yace "Good nyt" kai ta gyada masa daga haka ya juya ya fita duk jikinsa a sanyaye, she is really a strong lady, yana fita ya kulle mata kofar, haka kawai khadijah taji ta samu relieve sosai don kusan ji tayi babu abinda ke damunta a ranta kuma, tashi tayi a hankali tayi yanda Khaleel ya ce mata, sai kusan karfe uku da rabi bacci me nauyi ya dauketa.

Tun da ya fito daki Kanwar Abbansa Hajiya Mariya ke bin sa da kallo, kitchen ya shiga ya fito ya sake shiga ya fito kamar xai koma daki sai kuma ya sake shiga kitchen din sai gashi ya kara fitowa Hajiya Mariya tace "Aliyu" juyawa yyi da sauri yana kallon direction din da take don bai ma san tana wajen ba, har ya iso inda take kallonsa take, ya xauna gefen kujera yace "Na'am mum" da damuwa tace "Aliyu what's wrong with you pls, meye matsalar ka dubi yanda ka lalace, abun har ya kai ya kawo ka fara behaving kamar mara hankali, yanxu meye ma'anar shiga da ficen da kake a kitchen kamar wanda ya xauce" k'asa kallonta yyi ya sunkuyar da kansa, wanda hakan yasa jikinta yyi mugun sanyi, tasowa tayi ta dawo kusa da shi tace "Gaya min abinda ke damun ka Aliyu, you Neva knw if I can be of help, ko baka dauke ni kamar Anty fatima bane" Hawayen da ta gani idonsa ya kara daga mata hankali duk ta rikice tace "Subhanallahi, Aliyu, why the tears, don girman Allah ka gaya min meye ya faru, or have you gone wrong somewhere? Tel me son.." damuwa ce karara dauke fuskarta, ya girgixa kai yace "Just keep on praying for me mum, and... I will be going to Nigeria tomorrow, amma baxan jima ba xan dawo" daga haka ya mike ya bar ta gun xaune ta bi sa da kallo baki bude, tashi tayi ta wuce dakinta ta dau waya ta shiga kiran Mumy, ba a dau lkci ba ta daga bayan sun gaisa da damuwa tace "Anty fatima ni dai ko xa ki kira Aliyu ki ji me ke faruwa wllh gaba daya na rasa gane kansa yana cikin damuwa sosai, yanxu ma da na sa shi gaba sai ya fada min damuwarsa hawaye fa ya fara min kuma ya ki fada, I really don't knw his problem, wllh ko abincin kirki bai ci sai kinga yanda ya rame..." Mumy ta tabe baki tace "Ina ga ke ce baki taba lura ba sai wannan xuwan da yyi maki, amma Aliyu ai ko da yaushe cikin damuwa xa ki gansa, ni na saba ma ganinsa a hakan, ni dai bani da xurfin ciki haka ma mahaifinsa so I don't knw... Shi ya sani, na sha ce masa idan ma wani laifin ya aikata ma Allah yayi ta istigifari, or may be ya ji labarin auren da Abbansa ke shirin masa ne shi yasa hankalinsa ya kara tashi" da mamaki Hajiya Mariya tace "Aure kuma?? Yaushe?" Mumy tace "Yanxu ma shirye shiryen da ake ta yi kenan, idan ya dawo sai ya dau matar su yi ta yawon da yake yi tare, amma kar ki gaya ma sa, shi yasa ma yayan ki bai gaya maki ba, just let him... Kila idan aka yi auren xai dawo hankalinsa" Hajiya Mariya tace "Toh ai ya ma ce min gobe xai tafi Nigeria" Mumy tace "Toh dai dai kenan goben juma'ah dama xa a daura auren ke dai kar ki ma ce masa komai, sai ya xo muna jiransa" jikin Hajiya Mariya yyi sanyi sosai don har ga Allah bata ji dadin jin hakan ba duk da ita ma rashin aurensa na damunta amma aure without his knowledge kuma?? Sallama mumy tayi mata ta katse wayar.Tun da Khadijah ta fito rike da karamar jakarta daga cikin apartment dinta khaleel dake tsaye ya rungume hannunsa ke kallonta cikin bakin glass din idonsa kuma saboda ita ya sa glass din, abaya baki ne jikinta da mayafinsa, sosai kayan ya haska ta daga nisa kamar balarabiya, tana isowa gun da yake ya dauke kansa ya fara tafiya xuwa waje, taxi ya tsayar masu don motarsa na gun wani abokinsa, ya bude mata ta shiga sannan shi ma ya shiga, sai da suka dau hanya yace "Have you call home? I mean kin gaya masu kina tahowa?" Girgixa masa kai tayi, yace "Why?" Kamar xata yi kuka tace "Umma xata iya cewa kar in taho" khaleel ya hade rai yace "Toh tunda haka ne meye amfanin xuwan? Kawai ki fasa, da kin gaya min haka tun a gida ma ni baxan fito ba" Hararansa tayi daga sama har Kasa bata ce komai ba, ya xaro ido daga cikin glass dinsa, kamar me counting words din yace "Did... you... just... eye me?" ta sake juyawa ta maka masa wani hararan tace "You check for your self, kuma ni ban ce dole ka rakani airport ba, xaka iya komawa gida" lkci daya ya xare glass din idonsa suka hada ido, tayi saurin boye fuskarta a kafarta kamar xata yi kuka tace "Bana so" murmushi yyi bai ce komai ba ya mayar da glass din ya shiga danna wayarsa, har suka iso airport bbu wanda yace komai cikinsu sai dai lkci lkci yake satan kallonta, Khadijah ta bude cab din ta fita shima ya fita ta daya side din ya ba mai taxin kudinsa, kallon agogo yayi kafin su shiga airport din, khaleel ne yyi mata komai a airport din tana xaune ya dawo ya xauna gefenta ya mika mata ticket, xaro ido tayi tace "Noo, give me ur account details pls" wani kallo yyi mata yace "Toh Hajiya" daga haka ya dauke kansa, jikinta yyi sanyi bata iya tace komai ba, Wayarta ta ciro a jaka xata tura ma Vanessa text don bata ce mata xata yi tafiya ba, kamar ance ta kalli side dinta ta ga Aliyu xaune though nesa da su yana danna wayarsa, gabanta yyi mugun faduwa.... Lkci daya kuma babu abinda ya fado mata rai sai yan biyunta kamanninsu ya baci ne kawai, xuciyarta ya dinga bugawa ta dauke kai da sauri tana addu'ar Allah yasa ba jirgi daya xa su yi boarding ba, kallonta Khaleel yyi ganin yanda ta matso kusa da shi ba tare da tasan tayi hakan ba, suna hada ido tayi saurin sunkuyar da kai trying to control her self, da wani expression khaleel dake kallonta yace "What?" Ta girgixa masa kai da sauri kuma har lkcn ta ki dago kanta, bata kuma matsa daga kusa da shi ba, duk iya kallon khaleel a wajajen bai ga komai ba sai turawa da few bakaken fata dake wajen, a hankali yace "Khadijah" ta dago da sauri tana kallonsa, yace "What happened?" Girgixa masa kai tayi da sauri, a tsorace tace "I don't knw why I am afraid" ya d'an bude ido yace "Afraid? Of what" ta buda masa hannu kamar xata yi kuka, shiru yyi na few seconds, a hankali taji yace "Ohk shud I accompany you?" Ta dago tana kallonsa, dogon hancinsa da bakinsa kadai take gani banda idanuwansa, samun kanta tayi da gyada masa kai, yace "Ohk then" mikewa yyi ta bi sa da kallo tana boye fuskarta da mayafin jikinta ta saci kallon direction din Aliyu, yanxu ba danna waya yake ba ya dai jinginar da kansa da kujera yana kallon yaran turawa dake tare da uwarsu suna tafiya, da sauri ta dauke kanta. Har suka shiga jirgi Khadijah bata daina shisshge ma Khaleel ba, tayi sa'a kuma seat dinsa kusa da ita, suna keta haxo ta dinga bin jirgin da kallo cikin dubara amma ba ta ga alamar Aliyu ba, bacci ne ya dauketa daga karshe sai dai ta rufe rabin fuskarta da veil dinta, khaleel ya dinga kallonta, ya rasa gane irin tausayin da yake ma khadijah, ya san har ransa kuma he don't knw why, a hankali ta jinginar da kanta a shoulder dinsa, jawota yyi jikinsa ya lumshe idanuwansa, bayan awanni da dama Khadijah ta bude idonta a hankali, kallonsa tayi ta janye jikinta da sauri daga nasa, ya buda manyan idanuwansa yace "Are you hungry?" Ta girgixa masa kai, kamar ance ta kalli gefensu taga Aliyu xaune ya makala earpiece a kunnensa idonsa a lumshe, boye fuskarta tayi jikin khaleel jikinta na bari, khaleel ya riketa da mamaki yace "Are you okay?" Girgixa masa kai tayi a tsorace, bin jirgin ya dinga yi da kallo shi ma, lkci daya idonsa ya sauka kan Aliyu, haka kawai yaji gabansa ya fadi... Ya dinga kallonsa ko kiftawa babu don ko ba a fada ba kawai ya ga shureim da sudais a tattare da shi, lkci daya ya dauke kai, Khadijah da ta rufe fuska ta ki yarda ta kallesa, sauran journey din gaba daya daga ita har khaleel they where uncomfortable, khaleel ya kalli direction din Aliyu ya fi a kirga, gwara Khadijah tayi kokarin ganin bata sake kallon direction din ba, few hours kafin jirginsu ya sauka Abuja Khadijah ta d'an saci kallon gefensu dai dai lkcn da Aliyu ya juyo, hada ido suka yi sai dai fuskarta dama a rufe yake, ji tayi kamar an soka mata mashi a xuciya tayi saurin kauda kanta, shi ko yana ta kallonta bayan wani lkci ya dauke kansa. Har suka yi set down Khadijah ko da wasa ba ta juya kanta ba. Khaleel ya jira mutane suka fara sauka kafin ya mike, ita ma ta tashi da sauri, kamar xata shige jikinsa haka ta dinga bin sa har suka sauka matakalan jirgin, tsaye ta hango Aliyu nesa da jirgin yana kallonsu bayan shi ya sauka, taji kafafuwarta sun kasa daukar ta don tasan kila ya ganeta ne, har suka sauka Khaleel bai gansa ba don wani abokin sa bature ya dauke hankalinsa suna gaisawa, Aliyu dake ta kallon idanuwan khadijah da su kadai yake iya gani ya nufo ta, dai dai gabanta ya tsaya lkci daya ya fixge veil din fuskarta yana kallonta, rikicewa tayi, khaleel ya juya da sauri, ganin abinda Aliyu yyi ya cakumosa cikin tsawa yana masa wani mugun kallo yace "How dare you?"

Daga sama har kasa Aliyu ke kallon Khaleel da ya ki sake sa, Aliyu ya dake yace "Who are you?" khadijah na ganin haka a rikice ta ajiye jakar hannunta tace "Noo plss Dr ka kyale shi..." Khaleel na kallon kwayar idon Aliyu strictly yace "Stay away from her or else you regret it...." Yana fadin haka ya sakesa, Aliyu yyi wani murmushi yace "And who are you to tell me that? Her boyfriend? Husband or??" Juyowa khaleel yyi a mugun fusace ya sake cakumosa Aliyu ma ya cakumesa yana mayar masa da irin kallon da yake masa, khaleel yace "Both! Husband and boyfriend" dariya Aliyu yyi yace "You are very very stupid, idan ma mijinta ne kai ka shirya rabuwa da ita domin kuwa she is not meant for you" Khadijah na ganin abun ya kai haka ta shiga tsakaninsu da sauri cikin kuka tace "Wayyo na shiga uku, don Allah don annabi ku rufa min asiri ku yi hakuri" tayi facing din khaleel dake hade fist dinsa yana ma Aliyu wani irin kallo ta rikesa hawaye na sakko mata tace "Plss am begging you ka kyale sa don Allah Dr" lkci daya khaleel ya sake Aliyu ya kama hannunta ya dau jakarta, Aliyu ya fiddo complimentary card dinsa a aljihu ya saka a na Khaleel yana kallon kwayar idonsa yace "I will be waiting for ur call young man" still khaleel yyi kamar xai cire ya jefar sai kuma ya bari ya juya kamar xai tashi sama ya bar wajen Khadijah ta dinga bin sa xuciyarta na bugawa, Aliyu ya bi su da kallo yana murmushi a hankali yace "I will surely get you soon Iman, not when I have set my eyes on you" ta waigo ta kallesa tayi saurin dauke kai, har suka shiga cab Khadijah waigawa take taga ko ya biyo su, sai dai ta kasa ganewa don mutane ne da yawa ko ganinsa bata sake yi ba, duk ta kasa samun nutsuwa, tana kallon Khaleel da har sannan fuskarsa ke a daure kamar xata yi kuka tace "Plss Dr kar ka sake kulasa" Kallonta khaleel yyi a fusace xuciyarsa na heaving yace "That's idan bai shiga rayuwar ki ba, Billah xan iya yi masa komai, I don't care... Ina da wanda ya tsaya min a kasar nan, look... my father...." Sai kuma yyi shiru, lkci daya idanuwansa suka canxa kamanni, Khadijah jikinta yyi sanyi sosai, muryar khaleel ne ya dawo da ita tunanin da ta tafi, cikin sanyayyan muryarsa yace "Don't forget this is Abuja, ina xa mu? Thinking Kaduna kika ce min Umma take" A hankali tace "Dole sai mun bi train xuwa Kaduna" yace "Why not flight" ta hararesa tace "Bayan mun baro airport din, kawai kaje xaka tara mana crowd a airport ko meye na kulasa" bai ce komai ba sai kallon tagar taxin yake, khadijah ta sanar ma mai taxin train station xai kai su, Tsaki taji khaleel ya ja yace "Seriously It's being long aka ba ta min rai haka... Da ba don airport bane we ought have teach each other a lesson da guy din nan, I don't even care about d securities there..." Khadijah dai sai kallonsa take ganin how serious he was, Juyowa yyi ya kalleta tayi saurin dauke kanta, murya can kasa yace "It's because of you khadijah, don ke na kyalesa da mun yi karamin exercise a wajen nan" ta tabe baki tace "Ni dai babu ruwana" yayi murmushi da ya bayyana dimples dinsa yace "Billah ke kuwa ke da ruwa baby" kallonsa tayi da sauri, ya tsuke fuska kamar ba shi ya fada ba ya fiddo wayarsa yana dannawa, tayi murmushi tana ci gaba da kallon waje, suna isa station suka samu jirgin kasa mai xuwa Kaduna, Khaleel ya yankar masu ticket, sai da jirgin ya tashi khadijah ta kallesa tace "Are you a Nigerian" kallonta yyi, ta sauke idonta, yyi murmushi yace "Sure, A Nigerian... From Kaduna also, why do you ask, ko ban yi kama da ku ba ne" bata ce komai ba, shima bai ce komai ba, bayan few hours suka isa station din train dake kaduna, Napep suka dauka da xai kai su har gida, Yace "Do I have to accompany you har kofar gida" Khadijah ta kallesa sannan ta sa mai Napep ya tsaya tace "Sauka toh ka hau wani adai daitan ka tafi gidan ku" wara ido yyi yace "Like serious??" Ta langwabar da kai tace "Sure" murmushi yyi ya sauka yace "Ohk then" tace "Yeah, thanks" daga haka ta sa mai Napep din ya wuce khaleel ya bi su da kallo. Khadijah na isa gida ta sauka ta bude Jakarta, tunawa tayi ba kudi wajenta ta basa hakuri tace bari ta amso a ciki sannan ta shiga gida, sudais da shureim ne parlor suna kallon cartoon, suna ganinta suka mike a guje suka yi kanta suna mata oyoyo ta rungumesu gaba daya cike da murnan ganin yan biyunta, Umma dake kitchen ta fito da mamaki tana kallonta, da kyar ta yakice yaran a jikinta ta nufi Umma ta rungumeta tace "Ummata na dawo" Umma na kallonta

Please Login or Register in order to submit comment