Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

bude motarsa, Shureim na ganinsa ya nufe sa da gudu cike da murnar ganinsa Aliyu ya daga sa ya rungume sa ya lumshe ido, cike jin dadi shureim yace "Uncle ka kai ni wajen mama plss" Aliyu ya dago kansa yana kallonsa yayi pecking goshinsa yace "Mama tana Nigeria ai, idan kun yi hutu sai in kai ka" Shureim yace "Uncle plss ka tafi da ni" Aliyu ya kalli Khadijah dake wasa da ring din hannunta, a hankali yace "Thanks for coming out Khadijah" Sai a sannan ta daga kai tana kallonsa, jin bata ce komai ba ya bude bayan motar ya fiddo babban leda, Shureim yace "Uncle Anty ta bani irin wannan chocolate da kake bani da Sudais..." Aliyu ya wara ido yace "Da gaske?" Yace "Yes uncle" ya kalli Khadijah ya langwabar da kai yace "Toh Anty ki bari muje in siyo masa irin chocolates din, sai mu dawo yanxu" Khadijah bata ce komai ba, Aliyu yayi kasa da murya yace "Ko xa ki raka mu?" Girgixa kai tayi tace "No way" daga haka ta tsallaka ta wuce ciki abun ta, Aliyu ya bi ta da kallo kafin yayi murmushi ya xaga ya bude front seat ya xaunar da Shureim, ya dawo ya shiga driver seat ya tada motar ya bar street din. Khadijah na dai dai apartment dinta khaleel ya bude motar ya fito rike da makulin motarsa, ganinta yace "Let me go pick Shureim, na sha'afa wllh" a takaice tace "You don't worry na dauko sa, Ni ban sha'afa ba" daga haka ta Shiga ta rufe kofarta, ya fi minti daya a tsaye kafin ya koma nasa apartment din. Shopping mall din da Aliyu ya kai Shureim kusa da gidan kanwar Abbansa yake, don haka yana gama masa shopping ya shiga gidan tare da Shureim, Tasowa Maryam dake xaune parlor da Deejah tayi ganinsa ta tafi da sauri dau yaron ta rungumesa tace "Waow yau ga Shureim a gidanmu, Yaya Aliyu a ina ka samo mana shi? Jiya kuwa muka hadu da mum dinsa a cafteria a schl" Maryam ta kalli Deejah dake parlorn tana kallon Shureim da expression na Waow a fuskarta tace "Kin tuna warce muka gani a cafteria jiya?" Deejah ta xaro ido tace "Wai Khadijahr nan da nace maki suna kama da Safeenah??" Maryam tace "Yauwa ita" da mamaki Deejah tace "Kar ki ce min ita ta haifi yaron nan?" Maryam tayi dariya tace "Yaronta ne mana, yan biyu ne ma, daya ya rasu" lkci daya jikin Deejah yayi sanyi ta mike tace "Allah sarki" Aliyu dai bai tanka su ba ya wuce sama bayan ya amshi Shureim hannun Maryam don kai ma Antyn sa shi, Deejah ta bi su da kallo murya can kasa tace "but naga yaron na kama da cousin din naki ai, I mean sosai fa" Murmushi kawai Maryam tayi sai dai bata ce komai ba, bude kofa aka yi sai ga jawahir ta shigo, wurgar da takalman kafar tayi, ta jefar da jakar hannunta kan kujera ta xauna, Deejah dake ta kallonta tace "Ke kuma meye haka? me ya faru?" A fusace ta fara magana tace "Wllh Anty deejah na gaji da Ayman, abinda yake min ya fara isata, am just tired" Maryam ta xauna kusa da ita tace "Toh fah, me kuma ya hada ku?" Mikewa Jawahir tayi rai bace tace "Don rainin hankali sai yayi ta wani hada ni da yarinya da ban san meye tsakaninsu ba, I really want to know wacece yarinyar nan, sanann ta wani dinga daga min hanci tana amsa min da kyar kamar dole.... Da yaje Nigeria gaba daya lkcn sa ita yayi dedicating ma, ashe ma gidansu daya a nan ban sani ba sai daxu da ya fita yake gaya min, Ni kuma abinda yasa ma na sake ma yarinyar fuska tun farkon da muka hadu a Nigeria naga tana min yanayi da Safeenah ne, ban da haka tayi kadan in ganta da saurayina in raga mata, sannan ni a tunani na matar aure ce don ina ganin yaran nan nasan nata ne but now I am totally confuse...."
Deejah ta kamo hannunta a hankali tace "Kilan it's not what u are thinking lil sis, may be they are just frnds and neighbors, Kar ki bari shaidan ya ci galaba a kan ki, na kuma san ki da hakuri sosai jawahir so meye nasa wannan a ran ki?" Kamar xata yi kuka tace "Anty da kyar fa take amsa min magana idan na mata, kamar ma haushi na take ji shi kuma sai yayi ta sa ni in mata magana, to idan ba budurwarsa bace ita me yasa xata dinga haka" Deejah ta sauke ajiyar xuciya tace "But ni dai she was very free with me da muka hadu a cafteria jiya" Jawahir ta jinginar da kanta jikin kujera cike da damuwa bata ce komai ba, tausayinta Deejah ta dinga ji, Maryam dai na tsaye tana kallonsu ta kasa cewa komai, mikewa Jawahir tayi ta dau jakarta ta wuce sama, Xaunawa Maryam tayi, Deejah na kallonta tace "Maryam ko dai budurwar Ayman ce Khadijah kar ki boye min?" Maryam ta bude ido tace "A'a gaskiya ban sani ba, ni ban ma taba ganinsu tare ba ko a schl" Tare Aliyu ya sakko da Hajiya Mariya dake rike da Shureim, shi kuma yana rike da ledan na lotion da turaren yara da small mum din tasa ta ba Shureim, Maryam na kallonsu tace "Ya Aliyu dama ba kwana xai yi ba" Aliyu ya kalleta yace "Aa" Hajiya Mariya ta xauna kan kujera tana kallon Shureim dake gabanta tace "Ka gaida mumy ka ji boy?" Ya wara idanuwansa irin na Aliyu yace "Mumy ai tana can Nigeria, Anty xan gaida maki" Murmushi Hajiya Mariya tayi tana shafa kansa tace "Toh ka gayar min da Anty son" Aliyu ta kalla tace "Toh yaushe Antyn xata xo ta gaisheni" Aliyu yyi yar dariya yace "Ai Antyn nan sai a hankali ba xuwa xata yi ba" a hankali Hajiya Mariya tace "Kar ka damu, Allah xai dai dai ta ku ko don albarkacin yaron nan" murmushi kawai Aliyu yyi bai ce komai ba ya kama hannun Shureim xa su fita yace "Toh bari in mayar da shi mum, it's getting late" Shureim ya daga ma Hajiya Mariya da ta bi sa da kallo ganin sak mahaifinsa yana daga mata hannu, mikewa Maryam tayi ta bi bayansu, sai da suka fita waje ta kamo hannun Shureim ta durkusa tana gyara masa hular sweater dinsa tace "Darling ni baxa kace min bye bye ba" Dariya yayi yana kallonta ya daga mata hannu yace "Byee" mikewa tayi tana murmushi ta daga masa hannun ita ma sannan ta ce ma Aliyu sai ya dawo ta juya ta koma ciki, Aliyu ya sa Shureim mota sannan ya xaga ya Shiga ya tada motar ya nufi gida da shi, sai da suka kusa isa gidan ya juya yana kallonsa yace "Wani school kake xuwa Boy?" Shureim ya fada masa sunan makarantar, yace "Did you like the schl?" Gyada masa kai Shureim yayi, Aliyu yyi parking dai dai gidan yana kallonsa a hankali yace "Anty ce ta kai ka schl din?" Shureim yace "A'a uncle dina ne ya kai ni" Shiru Aliyu yayi bai ce komai ba, can ya dauko wayarsa ya shiga kiran Khadijah, Tana xaune parlor tana karatu kiran ya shigo wayarta, tana ganin number ta gane ta daga ta kai kunne, Aliyu yace "ki d'an fito ki dau Shureim" Katse wayar tayi ta mike ta shiga daki ta sa hijab ta fito, kamar mai tausayin kasa take tafiya har ta isa inda motar Aliyu yake, fitowa yyi daga motar ya xagaya ya bude side din Shureim ya sauko da shi, Khadijah ta karaso ta kama hannun yaronta ba tare da ta kalli Aliyu ba tace "Sai da safe" Riko Hijab dinta yayi yana kallonta, ta juya suna hada ido gabanta ya fadi tayi saurin sunkuyar da kanta, murya can kasa yace "Sai da safe kuma? baki amshi sakon sa ba" Bata ce komai ba ya saketa ya bude bayan motar ya dauko babban leda ya dau ledan da Hajiya Mariya ta ba Shureim ya sa a ciki da ledan da yayi masa shopping duk ya hada su waje daya ya mika mata, karba tayi yace "Xa ki iya" Bata ce komai ba ta kama hannun Shureim ta fara tafiya, ya bi su da kallo, Shureim ya juya yana daga masa hannu, murmushi yayi ya daga masa hannun shi ma a sanyaye har suka wuce ciki. Manyan sweaters da head warmer ke cikin ledar da Aliyu ya bata na Shureim sai kaya kala hudu, ta bude daya ledan taga chocolates, biscuits sweets da dai abubuwan ci na yara, ta bude ledan da Hajiya Mariya ta basa taga lotions masu tsada da turare, tabe baki tayi ta mike ta wuce ciki da kayan, sai da ta ajiye kayan inda ya kamata a daki sannan ta fito da ledan chocolates din parlor, turus ta tsaya ganin khaleel xaune parlorn, ta dinga bin parlorn da kallo ganin bata ga Shureim ba, Mikewa khaleel yayi yana kallonta, sake ledan hannunta tayi ta juya da sauri xata koma ciki yace "Khadijah" tsayawa tayi amma ta ki juyowa, kawai ganinsa tayi gabanta yana kallonta, tayi saurin juyo masa baya, a hankali yace "Gaya min me na maki?" Ta turo baki tace "Toh ni na ce ka min wani abu ne?" D'an murmushi yayi yace "Saboda Aliyu kika canxa min Khadijah?" Shiru tayi ta rasa ma abinda xata ce masa, lkci daya jikinta yayi sanyi, jin shi ma bai ce komai ba ta juyo a hankali tana kallonsa, hawaye ya cika idonta tace "Me yasa xan canxa maka saboda Aliyu?" A sanyaye yace "Nima ban sani ba Khadijah" hawaye idonta ya xubo tace "Ko dai kai ne ka canxa min saboda budurwar ka" tana fadin haka ta fashe da kuka, kallonta ya dinga yi shi ma jikinsa yayi sanyi, da wani expression fuskarsa yace "Why? Why will I change because of Jawahir?" tana hararensa cikin kuka tace "Toh nima me yasa xan canxa saboda Aliyu?" Ya lumshe ido ya bude a hankali yana kallonta, rasa abin fadi yayi, har ransa yake jin kukanta, ya bude hannayensa cikin sanyin murya yace "Can... I console you?" Make kafada tayi ta juya masa baya, ya lumshe idanuwansa a hankali ya rungumota, cikin sanyayyan muryar sa yace "You know I love you Khadijah, and... I want you to be the mother of my kids, i want to marry you Khadijah, but you met me with Jawahir, I was with her before you, kin ga baxan mata walakanci ba saboda ke, jawahir na da saukin kai sosai, she don't have problem, and I don't want to betray her... Beside ita daban a rai na haka ke ma, Give me a chance to show you how much I love you plss Khadijah" kasa cewa komai Khadijah tayi, duk gaba daya jikinta yayi sanyi, jin tayi shiru ya juyo da ita a hankali yana kallonta, Bata yarda sun hada ido ba ta sulale nan kasa ta xauna, dukawa yayi gabanta yana kallonta murya can kasa yace "Say something plss Khadijah... Nace Ina son auren ki baki ce komai ba" Ta hade kai da gwiwa jin hawaye ya kawo idonta cikin rawar murya tace "But Barrister Sudais...." Sai kuma ta fashe da kuka, ya dago kanta gabansa na faduwa, da kyar ya iya cewa "what about him Khadijah?" Tace "He proposed before you..." Shiru yayi yana kallonta ko kiftawa babu, a sanyaye tace "He said he want to marry me, and you know I can't tell him no Doctor, aure ma bai isa na biyasa abinda ya min a rayuwa ba, he deserves more than that from me, though nasan 6 years back I will confess I was in love with him, but yanxu I only respect him as someone that brought light to my life after my Lord, sai gashi ya dawo yace yana son aure na, baxan iya cewa bana son Sudais ba, baxan iya cewa baxan auresa ba, but I am afraid of his wife" shi dai khaleel bai ce komai ba, kana ganinsa kasan jikinsa yayi sanyi sosai, mikewa yayi a hankali bayan few seconds yace "Ohk then, Khadijah, Allah yasa hakan yafi alkhairi, wishing you all the best" daga haka ya juya xai fita ta tashi da sauri hawaye na sakko mata tace "But I know I love you so much Dr, bayan Sudais you are the next in my life, da ba don kai ba da ban san abinda xai sameni ba few months back, you made me lively once more in life, may be...." sai da ya isa bakin kofa ya juyo yana kallonta ya katse ta yace "Forget I did that to you Khadijah" daga haka ya fita, ta bi sa da ido xuciyarta na bugawa.

Duk yanda Khadijah ta so yin kuka ko xata samu saukin xafin da take ji a xuciyarta kasa yin hakan tayi, ita ta dai san ta fadi ma khaleel haka ne don ta wanke kanta ko da wani abun xai faru gaba wanda bata ma fatan hakan but she never expect such harsh reply from him, why will he just decide to leave? Sai a sannan ta fashe da matsanancin kuka, ashe dama ba sonta yake ba, ashe dama playing dinta kawai yake, gaba daya ta rasa abinda ke mata dadi a ranta, tayi kukan har ta ji babu dadi, duk jikinta yayi sanyi. Tana kwance bayan Isha ita kadai a daki, xuwa sannan ta daina kukan da take kuma ta samu relieve amma banda xafi babu abinda xuciyarta yake mata, ji tayi an bude kofar parlor, duk da wutan bedroom dinta a kashe yake hakan bai hanata dinga kallon kofar dakin ba, lkci daya kuma aka bude kofar Shureim ya shigo dakin, bai kunna wuta ba ya karaso ya hau saman gadon ya kwanta kusa da ita a hankali yace "Anty are you sleeping?" Shiru tayi bata ce komai ba idonta a lumshe, tana ji yayi addu'ar bacci yayi lamo jikinta, a hankali tace "Ka ci abinci?" Ya dago kai yana kallonta yace "Uncle ya bani na ci" Jawo sa tayi jikinta bata ce komai ba, sai da taji yayi bacci sannan ta kwantar da shi ta mike da kyar ta sakko kan gadon tana jin kanta na sara mata ta fita parlor don rufe kofa, a kan centre table ta ga Key a ajiye ta karasa gun kofa ta murda taji a rufe, alamar ya rufe ta waje ga Key a ajiye kan centre table, Dawowa parlorn tayi a sanyaye ta dau books din Shureim ta duba taga yayi assignment dinsa ta ajiye cikin jakarsa sannan kashe wutan parlorn ta koma daki ta kwanta ta lumshe ido. Har kusan karfe goma na dare ta kasa bacci, bude ido tayi da sauri jin wayar ta na ring ta mike xaune ta dau wayar tana kallon mai kiranta, A hankali ta daga ta kai kunne tayi sallama, daga daya bangaren ya amsa yace "Hope ban tashe ki bacci ba Amira" ta lumshe ido a sanyaye tace "Ba bacci nake ba" Shiru ya d'an yi na wani lkci kafin yace "Gaya min me ya faru, what's wrong with you" Ta bude ido da sauri cike da mamaki tace "A'a ba komai, am just tired, me ka ga?" Sudais ya girgixa kai yace "Noo, I know you well Amira, we stayed together for two years, from ur voice, there is something wrong, ki gaya min meye plss" Tace "Lahh da gaske ba komai barrister, today was very hectic shi yasa" D'an murmushi yayi yace "Ohk then" trying to brighten up tace "Ya Namecy na fa?" Yace "Ga ta tayi bacci" Khadijah tace "Toh a shafa min kanta" Sudais yace "Alryt, Shureim yayi bacci?" Khadijah ta gyada kai tace "Uhm" yace "Ya kamata ya ci gaba da karatun sa a nan, I think I will be coming over next week sai inyi enrolling dinsa" A hankali Khadijah tace "Ai ya fara ma" Yace "School din?" Tace "Ehh" yace "Shine baki fadi min ba Amira?" Ta langwabar da kai tace "Kayi hakuri" yace "Ke kika sa shi schl din" ta girgixa kai tace "Dr Ayman ya sa shi" Sudais ya d'an yi shiru sannan yace "That's nyc" Khadijah tace "Next week din xaka taho?" Yace "Sure, Akwai abinda xan yi, but few days xan yi, so do you need anything?" tace "A'a bana bukatar komai, Allah ya kawo ka lafiya" yace "Ameen, let me leave you dear, it's late and kilan xa ki lectures gobe koh?" Murmushi kawai tayi bata ce komai ba, yayi mata sallama bayan ya tunasar da ita tayi addu'a sannan ya katse wayar, ajiye wayar tayi ta kwanta ta ja masu duvet da Shureim. Washegari kafin karfe bakwai ta gama komai, ta ba Shureim indomie da ta girka masu a baki don kar ya bata uniform dinsa, Yana gamawa ta mike ta basa jakarsa ya goya ta dau nata jakar tana rike da hannunsa ta nufi kofa, tana gama rufe kofarta Shureim yace "Anty yau ma tafiya xa mu yi mu bar uncle?" Ta kallesa kamar baxa tace komai ba sai kuma a hankali tace "He is still sleeping dear" daga haka ta ja sa suka fita gidan, cab ta samar masu kamar jiya tayi dropping dinsa a schl sannan ta wuce nata makarantar duk da bata da lectures din safe, Wani waje ta samu ita kadai ta xauna, har ga Allah mai lallashinta take nema a lkcin, she need someone to console her, ta share hawayen da ya cika idonta trying hard to control her self, bata samu courage din kiran Umma ba har lkcn, tana ta xaune har lkcn lectures yayi bata tashi ba sai da ta ga kiran Vanessa, ta mike jiki ba kwari ta bar wajen. Bayan sun fito daga lectures sha biyu saura, Khadijah ta wuce cafteria ba tare da ta bari su Vanessa sun lura da ita ba, tana ta xaune nan tayi tagumi kamar ance ta daga kai ta ga Aliyu xaune yana kallonta, a hankali ta sauke kanta kasa, bayan kusan minti biyar ta sake daga kai tana kallonsa taga wayarsa yake dannawa, mikewa tayi ta dau wayarta dake ajiye kan table da jakarta xata fita taji a hankali yace "Iman" kasa kallonsa tayi tana tsaye, ya mike ya iso kusa da ita yace "Gida xa ki wuce?" Tana kokarin ganin bai ga hawayen idonta ba ta gyada masa kai, daga haka ta fita cafterian ya bi bayanta, har suka yi nisa bata ce masa ba shi ma bai ce mata ba, kuma kusan a tare suke tafiyar Daga karshe yayi breaking silence din a hankali yace "What's wrong Iman?" bata san lkcn da ta fashe da kuka ba kamar jira take, nan da nan ya rikice mata yace "Subhanallah, me ya faru Iman, plss ki gaya min, wani abu ya faru ne" ta kasa ce masa komai sai kuka take xuciyarta na mata xafi, Har ransa ya dinga jin kukan nata, bai san lkcn da cikin tsawa yace "Plss I don't like this Iman, ki daina wannan kukan" Tsayar da kukan nata tayi amma hawaye na ci gaba da sakko mata, wuri Aliyu ya samu ya xauna jin kafafuwarsa sun masa nauyi ya rike kansa, lkci daya jikinsa yayi sanyi xuciyarsa yayi masa rauni don kukan nata bashi da maraba da irin wanda tayi a ranar da kaddara ta afka masu six years back, A hankali ta nufi inda ya xauna ta xauna kusa da shi tana goge hawayen da yaki tsaya mata, Bayan kusan minti daya ya dago, cikin sanyin murya yace "What happened Khadijah?" Ta hadiye abu da kyar tace "Should I confide in you plss?" Kallonta yake ko kiftawa babu, a hankali yace "Sure Iman, you won't regret doing so" Ta gyada kai cikin sanyi tace "Ohk, tnx" Shiru ne ya biyo baya na 'ya dakiku.....


😦Seriously I don't like this short chapters da nake yi yanxu wllh, but dai ya fi babu d'an agwai da bak'in d'a....🙄
Gobe xa ku samu 5 read more😅

Khadijah ta hade kanta da gwiwa a hankali ta ki cewa komai, ya fi minti biyu yana kallonta, can ya shafa kansa murya can kasa yace "Talk Iman..." lkci daya ta dago kanta ya dinga kallon jajayen idanuwanta, ta hadiye abu da kyar ta make kafada tace "I think I've changed my mind" muryar ta na rawa ta fadi haka, ya dinga kallonta a sanyaye yace "Why Iman??" k'in cewa komai tayi, wasu sabbin hawayen suka shiga xubo mata, da damuwa sosai yace "Why did u change ur mind Iman, am I not trustworthy" goge idonta tayi tana kallonsa, ya jinginar da kansa da kujera ya lumshe idanuwansa, murya can kasa ya ji tace "Ina son xan wuce gida yanxu" Ya bude ido ya kalli agogon wrist dinsa a sanyaye yace "To mu je in kai ki" shi ya fara mikewa sannan ita ma ta tashi a hankali tana share idonta, har suka iso gun motarsa bai ce komai ba, sai da ya bude motar ya shiga sannan ita ma ta shiga, gaba daya she was absent-minded during the ride, idonta ne ya sauka kan wani karamin agogo mai kyau na yara cikin a cikin motar, ta kai hannu ta dauka tana kallon agogon ko kiftawa babu, agogon da khaleel ya taba siya ma su Shureim ne lkcn da suka xo hutu wajenta da xa su koma, ita dai ta san na Shureim na nan don da shi ma suka xo, Aliyu dai bai ce komai ba yana driving a nutse, ganin ta kallesa kafin tace komai murya can kasa yace "For little Aliyu...." Kasa cewa komai tayi da farko, a sanyaye tace "Where did you get it from?" Ya d'an yi murmushi kamar baxai ce komai ba shi ma, sai kuma yace "When he had an accident that very day agogon na aljihunsa, da muka tafi asibiti na cire" Khadijah ta sauke idonta bata ce komai ba, a hankali ta xuge zip din jakarta xata sa a ciki ya karba a hannunta, da mamaki take kallonsa, yace "Nima ina so, shi yasa na bar shi ma a mota" ta hade rai tace "Toh nima ai ina so" A hankali yace "But ai Shureim ma na da shi" bata sake saurarensa ba ta kai hannu xata karbe, bai san lkcn da ya sake steering ba ta fasa ihu a tsorace, parking yayi daga karshe inda ya dace yayi, ta dinga kallonsa xuciyarta na bugawa, yayi kokarin ganin bai yi dariya ba, dauke hannunsa yyi wajen ganin xata kwace agogon, Tace "Bana so ka bani abun yarona" a hankali yace "Nima ai yarona ne Iman" wani kallo tayi masa tace "A tunanin ka??" Murmushi kawai yayi yana kara kallon agogon, Mika mata yayi yana kallonta a hankali yace "Toh na hakura" kasa amsa tayi, ya dinga kallonta yana mika mata, dauke kai tayi ta turo baki tace "Toh na ara maka, xaka ban watarana" Murmushin sa yayi mai kyau murya can kasa yace "Toh ina godiya Iman" Ya mayar da agogon inda yake ya ajiye, ya juya yana facing dinta yace "But why did you change ur mind Iman?" kallonsa tayi sai kuma ta dauke kai, kamar baxata ce komai ba bayan few minutes a sanyaye tace "It's Dr Ayman, and it looks as if it's of no use telling you...." sai da gabansa ya fadi sosai, ya dake cike da karfin hali yace "What about him" ta jinginar da kanta da kujerar da take xaune, ji tayi abun ya dawo mata sabo, muryar ta na rawa tace "Kawai don nayi masa magana shine ya min walakanci" Aliyu ya ji komai nasa ya tsaya, a hankali yace "May be.... may be he misunderstood you Iman...." Ta fashe da kuka tuna abinda Dr Khaleel yace mata, ya lumshe ido ya bude yace "Toh wani maganr kika masa?" Babu abinda ta boye masa a maganarsu da khaleel na jiya, jin yanda take kuka Aliyu ya lumshe ido yace "Look....

Please Login or Register in order to submit comment