Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ku" Khadijah tace "Ayya, Ina amsawa" Aliyu ya fito daga motar yana kallonta yace "Ina Shureim din?" Tace "Yana ciki" ta kama hannun Baby tace "Mu shiga ciki" Baby ta kalli Aliyu tace "Toh yayanmu nagode sai anjima" khadijah kawai yake kallo yace "Ki kawo min Shureim din mu je gun Mumy su gaisa" ba tare da ta juyo ba tace "Toh" Da fara'a Umma ke ma baby sannu da xuwa, Khadijah ta kama hannun Shureim bayan ta dauko masa takalminsa tana kallon Umma tace "Umma xai je su gaisa da Mumy wai" Umma tace "Toh Allah ya kiyaye" daga haka ta fita da shi, Aliyu ya kama hannunsa yana kallonta yace "Gobe xan koma Iman" ta kallesa tace "Toh Allah ya kai mu" yace "Ameen" har xata tafi ta juyo tace "Amma plss kwana baby xata yi koh?" Yace "Ban sani ba, ki tambayeta" tace "Tohm" daga haka ta wuce ciki bayan tayi ma Shureim dake daga mata hannu murmushi. Khadijah ita kanta bata san xata sake da Baby haka ba, closeness dinsu na da kawai take tunawa da irin halaccin da baby tayi mata a gidansu, hira kawai suke tana ba baby labarin abubuwan da suka faru bayan ta bar gidansu, tun baby na kallonta cike da tausayi har ta fara kuka ba tare da ta san tana yi ba, Khadijah ta xaro ido ta fashe da dariya tace "Kuka Kuma baby, toh an gama labarin" baby na share idonta a sanyaye tace "Don Allah ki ci gaba Iman, mara Imani ne kadai baxai xubda hawaye ba a labarin nan naki..." Khadijah tayi murmushin karfin hali bata ce komai ba, Baby na ci gaba da share hawayenta a sanyaye tace "Ki ci gaba plss Iman" a hankali khadijah ta ci gaba da bata labarin har karshe, kuka kawai baby take khadijah na kallonta, Baby tace "Don Allah Iman ki yafe ma yayana plss" Khadijah tayi murmushi tace "Ba dole in yafe masa ba Baby, na yafe masa tuntuni, Allah ma muna masa laifi ya yafe mana balle beings" A hankali baby tace "Allah saka ma barrister" shiru Khadijah tayi tana kallonta, can tayi murmushi a hankali tace "Ai shi xan aura baby" kallonta Baby take da mamaki tace "Yaushe?" Khadijah tace "In less then three weeks ne bikin" A sanyaye baby tace "Shine baki sanar mana ba Iman, haushin mu kike ji har yanxu koh?" Khadijah tace "Ayya ba haka bane, kin ga jiya muka dawo ai, dama nufina idan na dawo in kai ma Mumy kati" Baby tace "Ya Aliyu ya sani?" Girgixa mata kai Khadijah tayi, Baby tace "Toh Allah kai mu lokacin, ya sanya alkhairi, Amma barristern a nan garin yake?" Khadijah tace "Ehh nan yake, ae kin san sa" Baby tace "A'a ban san sa ba" Khadijah tace "Ranan da muka je gidan ku ai tare muka je da shi" Baby tace "Ai su biyu ne ranan" Khadijah tace "Ai anjima xai xo sai ku gaisa" Baby tace "Allah ya kawo sa" khadijah ta dinga lallaba baby ta kwana gidan ganin ta fara cewa yamma yayi, baby tace "Ae ban ce ma Mumy xan kwana ba" khadijah ta marairaice tace "Plss baby, kinga ko frnds bani da, am always lonely, xan ce Umma ta Kira Mumy tace xa ki kwana" Bata sake sauraren baby ba ta fita ta sanar ma Umma sannan ta sa mata number mum din su Aliyu a wayarta ta kira ta, tana sawa ta fita ta dawo dakinta gun baby tana murmushi tace "Toh yanxu Umma xata kirata" Babu yanda baby ta iya haka ta hakura xata kwana gidan. Bayan sun idar da magrib suna xaune daki baby na bata labarin halin da iklima ke ciki duk jikin khadijah yyi mugun sanyi, ringing din wayarta yasa baby tayi shiru, dagawa tayi ganin Barrister ke kiranta bayan sun gaisa yace "Am outside dear" murmushi tayi tace "Toh ae shigowa xaka yi"

Sudais yace "Uhm is it necessary?" Mikewa khadijah tayi ta dau mayafinta tace "Toh baxa ku gaisa da Umma ba?" Yace "Sai nayi shawara da ke? Even the day before yesterday ai na xo, gaisheta tare ma muka je da Little Meerah" Murmushi khadijah tayi tace "Ohk then gani fitowa" daga haka ta katse wayar ta kalli Baby tace "Baby mu je ki raka ni sai ku gaisa dama kin ce baki san sa ba" Baby tace "A'a je ki dawo ke dai, just extend my greetings" Khadijah ta bata fuska tace "Don Allah ki taso mu je plss" Baby tayi yar dariya tace "Toh naji" tashi tayi ta dau gyalenta suka fita dakin, sai da Khadijah ta fara shiga dakin Umma ta sanar mata xasu fita gun Sudais sannan suka fita, Yana tsaye jikin mota sanye cikin kananun kaya ya rungume hannunsa, tun da suka fito yake kallon khadijah, Baby ce ta fara sallama tace "Ina yini?" Sai a sannan ya dubeta da murmushi ya amsa sallamarta yace "How are you?" Tace "Lafiya Alhmdllh, ya aiki?" Yace "Mun gode Allah" daga haka ta juya tace "Toh Iman sai kin shigo" tana fadin haka ta shiga cikin gida, khadijah ta dawo gefensa ta tsaya tace "Welcome My Barrister" ya wara ido a hankali yace "Really?" Boye fuskarta tayi tana yar dariya, yace "Kun xo lafiya dear?" Tana kallonsa tace "Alhmdllh" yace "Ashe dama kina da kawaye?" Ta xaro ido tace "Uhm Baby ce fa kanwar Aliyu" Shiru yayi yana kallonta, can yace "Tana xuwa nan kenan?" Khadijah ta girgixa kai tace "A'a tun bayan rasuwar takwaran ka sai yau ta sake dawowa" yace "How did she know u are back, ko kuna waya ne?" Tace "A'a fa, nasan Aliyu ne xai ce mata mun dawo" yana kallonta a hankali yace "Ya aka yi Aliyu yasan kin dawo" shiru tayi ta kasa kallonsa, bayan few seconds ta dago kai tace "Sorry I didn't tell you shi yayi accompanying din mu jiya, coz Shureim was sick" Ya langwabar da kai yace "Da gaske?" Bata ce komai ba, ya d'an yi murmushi shi ma bai ce komai ba, tayi breaking silence din tace "We where very close da baby, farkon xuwa na gidan su ne kadai muka samu problem, after that she was kind to me, she took me just as her sister, tana so na sosai, nima kuma ina sonta, and I really want us to be frnds now tunda bani da kawaye" a sanyaye ta kare maganar, Yana gyada kai yace "That's nyc then..." Tace "Me yasa baka xo da little Amira ba?" Yace "Ba daga gida nake ba" Khadijah tace "Ohk, Toh ko ruwa ban kawo maka ba, shud I bring some?" yace "Daga eatry fa nake yanxu haka" ta d'an buda ido tace "Kai da xaka koma gida kuma meye na xuwa eatry da daddare Barrister" murmushi yayi yana shafa beard dinsa bai ce komai ba, can yace "Shureim fa?" Shiru ta d'an yi, ta dago tana kallonsa tace "Yayi bacci" ya wara ido yace "So early? duk da nasan ba gaskiya kika fada ba" xaro ido tayi tana kallonsa, yayi murmushin sa mai kyau yace "Yea, sai ki ce min Aliyu ya tafi da shi" da mamaki tace "How did you knw" yana murmushi har sannan yace "From ur facial expression, and don't forget my field...." Yar dariya tayi tace "Kai My Barrister" yace "Sure My Meerah" ta boye fuskarta a tafin hannunta tace "Gobe ai xai dawo in sha Allah" yace "Alryt then, bari in tafi Amira, gobe xan dawo mu yi hira sosai am exhausted gaba daya yau" tace "Ayya, kana komawa gida kayi wanka ka kwanta you will feel relieve" Yana murmushi yace "Toh Amaryata" juya masa baya tayi tace "Uhn ni dai bana so" a hankali yace "Xa ki so ne ma ai" Bude motarsa yayi ya dauko leda ya dawo gabanta yana kallonta ya mika mata yace "Though Shureim na kawo ma amma tunda kin min rowar ganinsa gashi sai ke da meye ma kika ce sunanta..." Khadijah tayi murmushi tace "Sunan mu daya, Amma baby ake ce mata ita" ya wara ido yace "Ashe Mami na ce ita ma" a hankali khadijah ta gyada masa kai, yace "Toh ina gaisheta specially, she's having a great name, and naga suna kama da yayan nata ma" Khadijah ta amshi ledan tace "Toh xata ji mun gode sosai" murya can kasa yace "Noo thanks sweetheart" sunkuyar da kanta tayi, yace "Gobe xan kawo maki IV in case you have people to give" tace "Toh Allah ya kai mu" yace "Ameen dear, let me get going" daga haka ya bude maxaunin driver ya shiga, ta koma baya tana kallonsa, sai da yayi reverse ta daga masa hannu ya sakar mata murmushi sannan ya ja motar ya wuce, juyawa tayi a hankali ta koma cikin gida. Washegari karfe goma baby tace xata koma gida, duk khadijah ta ji ba dadi, babu yanda bata yi da ita ta bari sai da yamma ba tace inaa ita lokacin xata wuce, Khadijah tace "Toh ki kira yayanki ya dawo min da yarona nima" dariya sosai baby tayi tace "Sai kace baki da number sa, ke ki kirasa mana" Khadijah ta dau wayarta ta shiga kiran Aliyu, yana dagawa tace "Ka dawo min da yarona tunda wucewa baby ma xata yi yanxu" yace "Koh?" Tace "Eh mana, nace ta bari sai da yamma ta ki" kamar xata yi kuka ta kare maganar, Aliyu yayi murmushi a hankali yace "Toh bata wayar" Mika ma Baby wayar tayi, baby ta amsa tana dariya ta kai kunne yace "Baby ki bari da yamma" tace "Toh yayanmu an gama" daga haka ta ba khadijah wayarta, kashewa khadijah tayi tana murmushi tace "Me yace?" Baby ta harareta tace "Ba don halin ki ba xan kai yamma" sosai khadijah taji dadi tace "Yauwa ko ke fa, kinga kafin nan Barrister ya kawo katin da yace sai in baki ki kai ma su Mumy" shiru baby tayi tana kallonta, khadijah ta wara ido tace "Ko bai yi ba hakan?" A hankali Baby tace "Ke dai ki kai da kan ki xai fi" Khadijah tace "Toh shkkn ko ran Friday sai Sudais din ya kai ni in kai" Baby tace "Khadijah Ina son maki wani magana amma Allah yasa baxai bata maki rai ba" Khadijah na kallonta tace "Ina ji baby" Baby ta kamo hannunta tayi kasa da murya cikin sanyi tace "Khadijah me yasa kika ki amincewa Ya Aliyu ya aure ki bayan ya nuna yana son yin haka, kin ga akwai advantage din hakan biyu xuwa uku, na farko shureim... Idan yau ace Ya Aliyu xaki aura har duniya ta tashi ba lallai yaron yasan irin kaddarar da ta afka maku ba da yanda aka yi aka samesa sai in ku kuka fada masa, he will neva ever know wllh, idan wani gidan kika yi aure fa? Wllh komin daren dadewa watarana sai ya sani, sai ya san matsayinsa khadijah, na biyu Aliyu baxai taba maki gori a rayuwa ba idan ma yayi wlh yasan kansa yayi ma, kunya a kansa, balle ma wllh baxai yi ma don yasan shi ya cuce ki, sannan kin ga babu wani matsala da xaki samu gun Mumy, da mu yan uwansa, Anty khadijah ce problem dama, toh tana can har yanxu asibiti sai karaya ya dauko warkewa abu ya dawo baya, ga cikin shege jikinta har ya fito, don haka ta kanta take yanxu, kowa yaje sai tace ya yafe mata har masu gadi da driver... toh wanda xa ki aura fa khadijah? Though nasan Barrister yasan everything about you amma khadijah ki kyale namiji wllh ko ba directly ba watarana sai ya maki gorin nan barin ma wannan da kika ce yana da mata, ko cikin bacin rai wataran sai ya jefe ki da bakar magana irin ta gori ba tare da kilan yasan yayi hakan ba, kawai ta dalilin bacin rai, balle a je ga yan uwansa da relatives, sannan uwa uba matarsa, yanxu duniyar da wuya wllh a rike maka sirrin ka, khadijah ki duba wannan xancen nawa plss ba wai don ina son ki da yayana bane amma it's better ku rufa ma kan ku asiri ku hadu ku rike sirrin ku, kin ga sai ki kara haifo mana wasu kyawawan yan biyun......" Da xolaya ta kare xancen, Khadijah dake ta kallon kofa ta xame hannunta daga nata a hankali tace "I really like you baby, Ina ji da ke har raina saboda kin min halaccin da baxan taba mancewa da ke ba, plss baby kada ki sa in fara jin haushin ki in ga kamar ke ba masoyiyata bace, baby mu bar wannan xancen plss bana so, Kuma kar ki sake min irinsa" A hankali baby tace "Toh Allah ya baki hakuri" Khadijah tace "Ameen, So baki gaya min level da kike ba yanxu, Kuma yaushe xa mu sha naki bikin?" Da murmushi ta kare maganar tana kallonta. Bayan la'asar Sudais ya kira Khadijah yace yana waje, da kyar ta lallaba baby da har ta kira Aliyu ya xo ya dauketa ta gama shiryawa suka fita waje gun sa, yau ma yana tsaye jikin motar suka fito, Baby ce ta fara gaishesa ya amsa da fara'a yace "Lafiya lau Mamina ashe baki koma ba" Baby tace "Ehh wllh ina jiran yayana ne" Sudais yace "Alryt, ya gidan" tace "Lafiya lau" Kallon Khadijah yayi yace "Ya aka yi Madam?" Tayi murmushi tace "Lafiya lau, ya aiki?" Yace "Alhmdllh... Ya Ummar mu" khadijah tace "Tana ciki" juyawa Baby tayi tace "Toh sai anjima xan shiga ciki" yace "Alryt nagode da gaisuwa" daga haka ta wuce ciki, Sudais ya bude motar ya fiddo invitation card ya mika mata yace "Here dear" amsa tayi tace "Nagode, Ina Amira fa" yace "Tana gida" mota ce tayi parking kusa da na Sudais khadijah ta dinga kallon motar har Aliyu ya fito, Shureim ma ya fito ta daya side din, da gudu ya taho ya rungume Sudais yace "Unclee..." Sudais ya daga sa sama yana pecking goshin sa yace "Evening son, where are you coming from?" Ya wara ido yace "From my kind Mama's home" Sudais yace "That's good" karasowa Aliyu yayi gabansa ya mika masa hannu yana murmushi yyi masa sallama, Sudais ya basa hannun shi ma suka gaisa sannan ya kalli khadijah yace "Good evening" tace "Evening ya su Mumy?" Yace "Suna gaishe ki" kallon Shureim yayi yace "Go inside kace baby ta fito ina jiranta yanxu" Shureim ya shiga gidan Aliyu yayi ma Sudais sallama ya koma motarsa yana kallonsu ta ciki, Sudais bai sake cewa komai ba yana jingine da mota har baby ta fito, ta iso gun khadijah tana murmushi tace "Khadijah ni xan koma, ki taya ni yi ma Umma godiya idan kin koma ciki, nagode sosai" Khadijah tace "Toh nima nagode Baby ki gaida min mumy sai na kawo card din, and I will give you a call later" Baby tace "Alryt dear" sallama tayi ma Sudais ta wuce motar Aliyu ta shiga ya tada motar ya bar layin. Ranar Friday kamar yanda khadijah tace ma Baby misalin karfe sha daya ta shirya taje gidansu tare da Shureim don Sudais yace yana da wani case ranan. A hankali ta murda kofar parlorn ta ji a bude, ta shiga hade da sallama, Aliyu ne xaune parlorn tare da Salim yana operating laptop, ya daga kai yana kallonsu, ta sauke idonta ta karaso cikin parlorn, ta gaida Salim sannan ta kalli Aliyu tace "Ina kwana" Yana xaunar da Shureim dake gaishesa kusa da shi yace "Lafiya lau ya gida" tace "Alhmdllh, Mumy fa?" Ya d'an yi shiru kafin yace "Bata nan, ki jira ta xasu dawo yanxu" tace "Baby fa?" Yace "Tare suka fita" tace "Toh bari in baka sako ka ba Mumy" Ta bude jakarta ta fiddo IV din tana kallonsa ta mika masa, karba yayi idanuwansa a kan content din Invitation card din, a hankali ya dago yana kallonta ko kiftawa babu, bata sake yarda ta kallesa ba tace "You help me deliver it to her plss" daga haka ta sauko da Shureim dake xaune kusa da shi ta juya ta fita daga parlorn yana ce mata shi ta bar sa a gidan, ganin yanda Aliyu yyi still wajen, Salim ya karbi card din don ganin na menene. Gida khadijah ta koma tana ta ma Shureim dake mata kukan bata bar sa gidan ba masifa, tana sauka kan napep din tace "Don uwar ka ba sai ka koma ba tunda gidan dangin uwar ka ne can din" Ta bude jaka ta ba mai napep kudinsa ta wuce ciki abun ta, ya bi ta yana kuka kamar xai tsaga gidan, Ta fi seconds goma tana kallon takalman dake bakin kofar parlorn, can ta bude kofar ta shiga a hankali, Khaleel ta gani xaune parlorn Umma ma na xaune, ta wani hade rai bata sake kallon parlorn ba xata wuce daki Umma tace "Khadijah" tsayawa tayi ta ki juyowa, Jin Umma bata ce komai ba ta juyo a hankali tace "Na'am Umma" Hada ido suka yi da shi, ta sauke idonta tace "Ina yini?" Yace "Lafiya lau" Tana kallon Umma tace "Mun dawo Umma, ba mu sameta ba ma" Umma na kallon Shureim da ya makale bakin kofa yana kuka tace "Shi kuma me ya samesa?" Harara ta balla masa tace "Au kuka kake min har yanxu, nace ka koma gidan koh" a hankali yace "I don't know the road" Umma tace "Me yasa baki bar sa ba" Tace "Mumy fa bata nan, Baby ma bata nan, to ina yake son in bar sa" yana kallonta yace "Wajen Uncle dina mana" Khaleel ya juya yana kallonsa yace "Come over dear" sai a sannan Shureim ya gansa ya taho gun sa da sauri yace "Uncle when did you come?" Khaleel ya xaunar da shi gefensa yace "Today" Murmushi yayi yace "Uncle kun xo da Anty na?" Khaleel ya shafa kansa yace "Sure" tabe baki khadijah tayi ta juya ta wuce daki abun ta, Tana xaune gefen gado tana danna wayarta Umma ta shigo dakin, ta xauna gefen gadon ita ma a hankali tace "Ashe abinda ya faru kenan Khadijah?" Kasa kallonta Khadijah tayi lkci daya hawaye ya kawo idonta, sai a sannan ta dinga jin xafin maganganun da Jawahir tayi mata, maganganun suka dinga dawo mata sabo, Umma tace "Ni ban ce kiyi kuka ba, ki share idon ki kije ki samesa ki ji abinda xai gaya maki" cikin rawar murya tace "Ni baxan je ba Umma" Umma tace "Ban isa da ke ba kenan" goge idonta ta dinga yi a hankali ta mike ta dau gyalenta ta fita a sanyaye, tun da ta fito yake kallonta har ta karaso ta xauna kujera ba tare da ta yarda ta kallesa ba, a hankali taji yace "Khadijah" sai a sannan ta daga kai tana kallonsa.

✨ *NOOR-AL-HAYAT*✨

Kallon direction din daki yayi kafin ya kalli Shureim yace "Je ka dauko min wayar Anty a daki" yaron na wucewa ya mike ya dawo gefenta ya xauna ta d'an matsa ta dauke kai, a hankali yana kallonta yace "Don Allah kiyi hakuri Khadijah, I wasn't happy with what happened also, and... Plss forgive Jawahir for the sake of...." Katse sa tayi tace "Toh ni nace na riketa a rai ne? Not at all, don bata min komai ba" Ya lumshe ido ya bude yace "Don Allah kiyi hakuri Khadijah" tace "Wllh nayi, Kuma komai ya wuce a wajena, ita ma xan sameta idan na taba mata wani abun ta yafe min" Shiru yayi bai iya yace komai ba, mikewa tayi xai rikota tayi saurin barin wajen tana hararansa tace "Meye haka?" Kallonta kawai yake, ta tabe baki tace "Am coming now" daga haka ta wuce ciki sai ga ta ta fito da kati ta iso kusa da shi ta mika masa, Bai karba ba yace "Meye wannan?" Tace "Ka amsa ka duba mana" da kamar baxai karba ba sai kuma ya karba yana kallon katin, a hankali ya dago kai yana kallonta, ta rungume hannayenta tace "Xa ka samu xuwa kuwa duk da baka gayyaceni naka ba?" Ya sauke idonsa bayan few seconds yace "Why not" ta koma ta xauna a hankali tace "Toh nagode" Jujjuya card din kawai yake bai ce komai ba, can ya dago yana kallonta cikin sanyin murya yace "Ur happiness is mine khadijah, since this will make u happy, this is what u want for ur self, I am wishing you the best in it, Allah ya kai mu lokacin yasa ayi a sa'a" kasa cewa komai tayi tana kallonsa, yace "But I am happy for a reason, soon xan maki abinda xai sa ki farin ciki na har abada in sha Allah" daga haka ya mike yace "Kice ma Umma na tafi" har ya nufi kofa ya fita bata samu bakin magana ba, ta sauke idonta a hankali taji xuciyarta ya mata rauni. Tun ana biki saura kwana shidda Umma da Nanny suka fara shirye shirye ba ji ba gani, da kanta ta kai ma Kawun Khadijah katin bikin, kusan guda ashirin ta tafi da domin ya ba sauran yan uwansu can, Bata tsaya ta sauraresa ba balle matan sa da yanxu suka xama abun tausayi don miji ba shi da shi, ga yayansu duk aure ya mutu ana xaune gida, duk da bakaken maganganun da suka dinga jifanta da shi ita dai bata tanka su ba ta fita, wai don ma basu san da kaddarar da ta afka ma Khadijah ba kenan wannan, gidansu sadeeq ta shiga ta ba Mahaifiyarsa ma katin bikin sannan ta juyo xuwa kano. Tun da bikin ya gabato kullum sai baby ta xo gidan da close frnds dinta uku ganin da gaske khadijah bata da kawaye kamar yanda ta ce, tare suke shirin komai da xuwa kasuwa, babu wanda bai yaba kayan lefen da Sudais ya hada ma khadijah ba, as in abun ba a cewa komai, ya kashe mata kudi ba na wasa ba, Umma ta xuba kudi me yawa ta sa aka fara gyara khadijah, xuwa yanxu kam khadijah ta kara xama wani silent har da rama, hakan bai wani damu Umma ba sanin ko wace Amarya na experiencing haka, tun da bikin ya karato Sudais bai wani cika xuwa ba sai dai su yi waya, hakan yasa hankalin khadijah ya kwanta don ko ya xo bata jin ma xata iya fita gun sa. Mumy ta gama hada gudunmawarta gaba daya tana kallon Aliyu dake xaune yana danna waya dakin nata tace "Abuturrab ko kai xaka taimaka ka kai don Allah" sai a sannan ya dago yana kallonta, Mumy ta xauna gefen gado tace "Na fa ce ka cire ma kanka damuwa Abuturrab, you are never destined to be married to khadijah, ba kadarraku ba kenan kuma baka isa ka ja da Allah ba, ga mijinta nan ka gani so plss take her off ur mind, ka samu mace kayi aure..." Ya sauke idonsa kasa cikin sanyin murya yace "But I have never for once complained Mum, kina gani har kiranta nayi na mata Allah ya sanya alkhairi" Mumy tace "You are not complaining but ur mind is, gashi nan duk ka fita hayyacin ka, ga shi nan kana neman jefa kanka cikin wani hali, dama mutum na auren matar da ba tasa ba Aliyu? Why not behave like a good Muslims and be happy with Allah's plan?" Wani murmushi yayi yace "I am not complaining Mumy, am telling you the fact, but the thing is that don Allah ki taimaka ki mata magana ta bar min yaron, tayi hakuri ta bar sa gun ma, anytime she wants to see him xa a iya dinga kai mata shi, ko kuma yaje ya dinga hutu gunta, I know baxan iya rabata da Dan ta ba, but I just want to save him some humiliations, har duniya ta nade a gidan nan babu mai masa gori, babu mai masa kallon a child gotten out of wedlock, sannan babu mai takura masa, in da tayi aure fa, ko xai samu abubuwan da nayi mentioning a nan wllh it won't

Please Login or Register in order to submit comment