Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Aliyu yace "I came to get something also, why is ur twin behaving strangely, and he looks sick..." Fitowa sudais yyi don ba can cikin shagon ya shiga ba yana kallon Aliyu yace "Because I don't like you, stay away from me and my brother" Kallonsa Aliyu yake ko kiftawa babu, Shureim ya tura sudais yace "You are mean...."

Sai da sudais ya gama kallon d'an uwan nasa sosai kafin ya kai masa mari yana huci yace "How dare you call me that" Aliyu na ganin shureim yayi kan sudais ya daga sa sama ya rungume sa a hankali yace "Yi hakuri ka kyalesa sweetheart" kuka shureim ya fara yi hana sa dukan sudais da Aliyu yyi, Sudais na huci yace "I don't like you both" dai dai fitowar Nanny daga shago, da sauri ta karaso tana tambayar me ya faru ganin shureim na kuka hannun Aliyu, sudais ya fashe da kuka shi ma yace "Nanny shureim started 1st, he insulted me" Nanny ta hade rai tace "Ohh har cikin market din ma sai kayi fada sudais, kai dai baka ji kuma nasan kai ka fara tsokanarsa ba ruwan shureim, silly boy kawai from henceforth bana sake xuwa ko ina da kai, ko kace xaka bi ni sai na ma duka" juyawa sudais yyi ya fashe da matsanancin kuka da gudu ya bar wajen xai je gun uwarsa, bin bayansa Nanny tayi tana kwala masa kira don ta can tsallake khadijah take kuma titin is very busy, amma sudais yaki tsayawa kuka kawai yake yana gudu yana kiran Anty, Aliyu na ganin haka shi ma ya bi su da sauri shureim na hannun sa, khadijah dake cikin mota tana xaune maxaunin driver don ita ta kawo su kasuwar haka nan kawai taji gabanta ya yanke ya fadi dai dai lkcn da taji ihun da mutane ke yi, tana juyawa kawai ganin Sudais dinta tayi a tsakiyar titi shi ma duk ya rikice ihun da mutane ke yi, ga mota har biyu sun taho da gudu ko wanne na son kauce masa, tunda take bata taba irin ihun da tayi ba a lkcn, lkci daya ko ina na kasuwan yyi tsit don duk yanda motar ta so avoiding sudais hakan bai yiwu ba, sai kuma a ka dau salati Khadijah ta fito a rikice jikinta na rawa ganin sudais kwance cikin jini ta fasa wani ihu kanta na juya mata, suman da ya kamata tayi nanny ce tayi sa a lkcn, ita kanta bata san me ya hanata sumewan ba, Aliyu da yyi still shi ma ya kasa motsi na few seconds ganin abinda ya faru lkci daya yaji strength ya dawo masa, ya ajiye shureim dake ihu yana kiran dan uwansa ya nufi gun sudais dake a kwance kan titi cikin jini mutane sun taru kansa mata na kuka maxa na salati, har da kyauta cikin mutanen, babu rabon Anty khadijah xata ga abinda ya faru don tsabar kunya bata jira Aliyu ya fito ba ta hau adaidaita da baby suka koma gida, cikin tashin hankali Aliyu ya karbi yaron hannun wani mutumi dake jijjigasa yana salati, a nan Aliyu yaji kamar bai taba xama likita ba duk rayuwarsa gaba daya basira ta dauke masa ya rasa ya xai yi da sumammen yaron dake hannunsa fuskarsa duk jini, cikin matsanancin kuka khadijah ta isa gun ta wani fasa ihu a gigice ta durkusa jikinta na rawa take cewa "Na shiga uku, don Allah ku taimakeni kar ya mutu ku rufa min asiri, kar ku bari ya mutu" daga kai Aliyu yyi a karo na farko yana kallonta jin muryarta, lkci daya signal dinsa ya sake daukewa yana mata wani irin kallo ita kuwa sai jijjiga sudais take ba tare da ta kula a hannun wa yake ba tana kuka tana cewa ya tashi kar ya tafi ya bar ta, kyauta ta saki salati baki bude tana kallon khadijah tace "Kamar khadijah nake gani ni kyautar Allah" khadijah ta kalleta ita ma da sauri, da gudu ta nufe ta rikota tana kuka cikin rauni tace "Anty ku taimake ni kar ya mutu don Allah, kar ya tafi ya bar ni" Kyauta ta kwalalo ido tace "Yaron ki ne Khadijah?" Khadijah ta dinga gyada mata kai tana kuka sosai, kyauta ta fashe da kuka tace "In sha Allahu baxai mutu ba xa mu tafi asibiti yanxu khadijah, baxai mutu ba..." wata mata ta fixge yaron a hannun Aliyu a mugun fusace ganin khadijah kawai yake kallo tace "Dubi mutum kamar an dasa sa a gun ya sa yaron da ba mu san ko ya mutu ba ko yana raye a gaba yana kallo, wannan wani irin uba ne kai, ni na xata taimkon gaggawa xai bada...." Khadijah ta tsayar da kukan da take ta sake kyauta ta nufi matar ta rikota cikin rudewa tace "yaro na bai mutu ba kar ki kara cewa ya mutu don Allah kar ki kara, wllh bai mutu ba, Allah baxai sa ya mutu ba" sosai ta ba mutanen gun tausayi wani mutumi ya sa sudais tare da matar a motarsa domin xuwa asibiti, mutumin ya kamo hannun Aliyu dake tsaye yana kallon khadijah da har sannan bata lura da shi ba yace "kar ka damu he will be alright in sha Allah shiga mu je asibitin tare" bayan motar Aliyu ya shiga suka dau hanyar asibiti, sai a sannan basirar sa ta likita ya dawo masa ya karbi sudais a rude ganin numfashinsa na sama ya dinga basa numfashi, banda kuka babu abinda matar dake kusa da shi take tana addu'ar Allah ya raya sa, jin mutumin dake ta sharara gudu a mota yyi parking Aliyu ya dago kai tare da bude motar ya ga asibitin da yake aiki ma mutumin ya kawo su, Aliyu ya fita rike da sudais yyi cikin asibitin da sauri nan aka shiga emergency da yaron, sai bayan kusan minti talatin Aliyu ya fito tare da wani likita daga emergency ward da aka shiga da sudais suka bar likita daya a kan sa da nurse, Dr Saif ya nufi gun su khadijah dake xaune reception da kyauta da wasu mutane har sun gaji da lallashinta don ko tayi kuka har ta gode Allah, tsabar tashin hankali ko gane asibitin bata yi ba, shureim dake jikinta ma kukan yake yana tambayarta me ya samu sudais, Nanny da ta suma an kwantar da ita asibitin ita ma, mikewa khadijah tayi da sauri ganin likitan, Aliyu ya tsaya daga inda yake har lkcn mask na bakinsa da hanci, Dr Saif yace "Ina mahaifiyar yaron?" Khadijah dake kallonsa gabanta na faduwa tace "Ni ce" Aliyu ya cire mask din dake fuskarsa yana kallon khadijah da wani irin mamaki, at the same time confusion, likitan ya tsaya kare mata kallo kamar bai yarda ba, can dai yace "Toh mahaifinsa fa?" Tana share hawayen dake xubo mata cikin rawar murya tace "Baya nan" likitan na kallon Shureim ya xaro ido yace "Subhanallah yan biyu ne?" Cikin kuka khadijah ta gyada masa kai, jikin likitan yyi sanyi sosai, ya shafa kan shureim dake kuka yana rike da mayafin Khadijah a hankali yace "Don't worry my boy ur twin will be okay in sha Allah, madam xa ki iya shiga ki gansa amma plss kar ki wani damu ciwo ne kawai yaji a kai sai bruises, so don't cry while inside, shi kuma wannan ki bar sa a nan ba sai kin shiga ba" daga haka ya juya yana kallon Aliyu dake nesa da su kafafuwarsa sun kasa daukarsa saboda shock yace "Dr plss see her inside, amma kar ta dade a ciki" daga haka ya kama hannun shureim yace "Big boy xo mu je office ka jira mumy" shureim xai masa taurin kai sai ya bi mamarsa ya daga sa sama kawai ya wuce office dinsa da shi don bai son ya ga dan uwansa a halin da yake ciki yanxu, Tuni Aliyu ya mayar da mask din fuskarsa yayi gaba kamar me counting step dinsa Khadijah na biye da shi a baya, tsabar tashin hankalin da ke tare da ita bata ko kalli wanda take bi ba balle ta san waye. Suna shiga ward din Aliyu ya tsaya bakin kofa ita ta shiga ciki gabanta na faduwa, ko gama ganin sudais bata yi ba ta fasa wani ihu, Nurse din ta karaso da sauri ta fitar da ita dakin tace "Haba madam, sai kace ba musulma ba wannan ihu haka" khadijah ta fashe da matsanancin kuka tana jijjiga nurse din tace "Don Allah Anty kar ku bari wani abu ya samu yarona, they all I have, plss ku taimake ni" rungumeta nurse din tayi tace "It's ohk madam jikin ai da sauki, you just pray Allah ya tashi kafadarsa kuma kada Allah ya sa ya tashi da wata matsala" Khadijah ta xame kasa tana kuka tace "Na shiga uku wllh kilan mutuwa xai yi ya bar ni, don Allah ku taimaka min" juyawa nurse din tayi ta koma ciki ta rufe kofar, Aliyu ya kasa ci gaba da kallon khadijah lkci daya idonsa ya kada, yaranta? To waye ubansu? Abinda ya dinga masa yawo a rai kenan, kawai ya ga ta mike ta nufo sa, kana gani kasan ta gaji da kukan ta riko sa cikin rauni tace "Plss Dr kar ku bar min yarona ya mutu don Allah ina rokan ku, they are all I've got in this world bayan ummata, plss ka taimaka Dr ku cire masa abinda ku ka sa masa a hanci ina son yarona" Aliyu ya kasa ce mata komai lkci daya hawaye ya kawo idonsa, da ba don a rude Khadijah take ba bbu abinda xai hana ta gane Aliyu ne gabanta saboda kwayar idanuwansa amma saboda tashin hankali bata gane ba ganin, hawayen idonsa ta tsayar da kukan da take xuciyarta na bugawa tana kallonsa ko kiftawa babu, bayan few seconds cikin sanyin murya tace "Dr ya mutu koh?" Aliyu bai iya yace komai ba ya ji ya kasa controlling kansa hawaye suka shiga sakko masa, he don't want to believe Khadijah conceived with him, he don't want to believe she conceived that deadly moment, if so then he is not worth to be forgiven, bai cancanci ta yafe masa ba, don ya mata xaluncin da dole baxata iya yafe masa ba, sai a sannan maganganun da Anty khadijah take a waya daxu ya fara dawo masa, ya juya ya hade kansa da bango yana hawaye sosai duk ya ji ya tsani kansa, yanxu yaran nan nasa ne kenan?? He is there illegal father, the cute boys... Are his and Khadijah's, they got them out of wedlock.... Lkci daya ya juya ta dalilin sound da ya ji bayansa, nan ya ga khadijah sume a kasa.

A hankali khadijah ta bude idanuwanta da suka mata nauyi ta dinga bin inda take kwance da kallo, Umma ce xaune dakin da Nanny da ta ci kuka har ta gode Allah, sai kyauta da tayi tagumi, Umma ta mike da sauri ganin khadijah ta bude ido ta karasa kusa da ita da damuwa tace "Sannu daughter, how are you feeling now?" Mikewa xaune Khadijah ke son yi amma kanta yyi mata nauyi ga kirjinta dake mata xugi, Umma ta riketa tace "Koma ki kwanta" Kyauta ta iso kusa da ita ita ma da damuwa tace "Sannu khadijah" Shiru khadijah tayi kamar me son tuno abu, Umma ta hade rai tace "Don't stress ur self thinking of anything, just relax...." Hawaye ya kawo idonta ta kamo hannun kyauta cikin rawar murya tace "Anty mai girki ina sudais dina, ya mutu koh? Don Allah ku gaya min, kar ku" Umma ta dakatar da ita a mugun fusace tace "Ke kika kashe sa halan? Ji wani xance da kike ma mutane khadijah" Girgixa kai khadijah tayi da sauri hawaye na sakko mata, Kyauta tace "Toh yana nan lafiya khadijah, har ya tashi shi ma, suna can tare da d'an uwansa da wani likita" Khadijah na goge idonta tace "Toh xan iya ganinsa don Allah?" Harara Umma ta watsa mata tace "Da drip din xa ki je ki gansa, kuma ki rufe min maki haka, ance maki yana lafiya" Khadijah bata sake cewa komai ba sai dai ban da faduwa babu abinda gabanta yake, Umma ta mike ta shiga hada mata shayi, Nanny ta xauna kusa da ita cikin sanyin murya tace "Kiyi hakuri Khadijah, Sudais yana nan lafiya har ya tashi, suna tare da Shureim yanxu haka" Sai a sannan khadijah ta ji hankalinta ya kwanta sosai, Nanny ta mika mata wayarta tace "An kira ki har sau biyu, but I picked..." Khadijah ta karbi wayar tana kallon wanda ya kirata ta ga Khaleel ne, ta kalli nanny a hankali tace "Me ya ce?" Nanny tace "Na gaya masa abinda ya faru, yace xai xo clinic din" Khadijah bata ce komai ba ta ajiye wayar, ta ji tana ma son ganinsa, jin xai xo hankalinta ya kara kwanciya. All this while Aliyu na ward din da sudais yake tare da Shureim, kwata kwata bai son ya bar su ko na minti daya, da ya fita ba a jimawa xai dawo kuma har lkcn ya ki cire mask din bakinsa da hanci, damuwa ce sosai tare da shi, da ya kalli yaran ya tuna nasa ne sai yaji hawaye a idonsa, shi kuma irin tasa kaddarar kenan?? Har yan biyu ba ta hanyar aure ba, har ransa yake jin tausayin kyawawan yaran, he wished ba ta haka suka xo ba, Shureim bai ganesa ba sai dai ya lura da irin yanda sudais dake kwance ke kallonsa, A hankali ya isa kusa da yaron ya duka a sanyaye yace "You want something??" Sudais ya girgixa masa kai, Shureim ya kallesa da sauri na few seconds kafin yace "The voice.... sounds familiar" murmushin karfin hali Aliyu yyi ya sauke mask din fuskarsa a hankali yana kallon yaron, Shureim yyi shiru yana kallonsa can ya juya ya rungume hannunsa ya hade rai yace "You caused my brother's accident" Jikin Aliyu yyi sanyi sosai, ya mayar da dubansa kan sudais ya ga ya ki kallonsa shi ma ya hade rai, bude kofa aka yi xai mayar da mask dinsa da sauri yaji muryar colleague dinsa, Dr Muktar ya karaso yana kallon yan biyun yace "Maa sha Allah, he is recovering fast" ya kamo hannun Sudais yace "How are you feeling now handsome?" A hankali Sudais yace "Alhmdllh" Dr mukhtar yyi murmushi yace "Good" kallon Aliyu yyi yace "Kasan kuna yanayi da boys din nan sosai, da ba don na san baka taba aure ba bbu abinda xai hanani cewa yaranka ne Dr" Aliyu ya kirkiri murmushin karfin hali yace "Gaskiya ne" Dr mukhtar yace "Naga kamar sun ma shiga ranka kai ma tunda gashi ka ki barin ward din tun daxu" Aliyu yace "Sure they are cute" Dr mukhtar yace "Just came to check on them dama" daga haka ya juya ya fita, Aliyu ya kamo hannun yaran murya can kasa yace "Am sorry for all that happened sweethearts forgive me plss" a hankali Shureim yace "Ohk..." Kallon sudais da yyi shiru yyi yace "And you sweetheart?" Sudais ya sauke kansa yace "Me too" jawo yaran jikinsa ya yi cikin sanyin murya yace "I love you boys" lkci daya idanuwansa suka kada, how he wish Khadijah xata yafe masa ba tare da ta sa masa heart attack ba, ta ajiye komai su xauna tare da yaransu, bai taba saba maganar mahaifiyarsa ba amma da kamar wuya wannan karan, it will be different.... he will marry Khadijah and have his boys in sha Allah, and he will neva be ashame showing them as his children, wani mugun son yaran ne ke fixgarsa yana rungume da su, bude kofar dakin aka yi Umma ta shigo tare da wani likita, khaleel na biye da su a baya, A hankli Aliyu ya daga mask dinsa sannan ya juya suka yi ido hudu da khaleel, Dr Abdul yace "Dr their grandma and a Dr also, my frnd Dr Ayman" Aliyu sai kallon khaleel yake kamar yanda shi ma khaleel ke kallonsa duk da fuskarsa a rufe yake, Umma ta kalli Dr Abdul sanin ance baxa a bar su su shiga gun yaran ba tace "Mun gode Dr" Dr Abdul yace "Ba komai Mama" Dr Abdul yace "Ayman bari in koma bakin aiki na" khaleel yace "Tnxx Abdul" daga haka Abdul ya fita, Shureim ya sauko saman gadon ya rungume khaleel, khaleel ya daga sa sama yace "How are you" kamar xai yi kuka yace "I am fine but my brother isn't" Khaleel ya ajiye sa ya karasa yana kallon Sudais cike da tausayinsa, Shureim kuma ya nufi gun Umma dake kallon Sudais ita ma a sanyaye, plaster ne gaba daya kansa, khaleel ya kamo hannunsa yace "You will get well soon in sha Allah my boy" Sudais xai fara kuka ya rungume sa yace "Noo don't cry be a strong boy" Sudais yace "Uncle ina Antyna" khaleel yace "Xata xo yanxu" sudais yace "Ka kai ni wajenta I want to see her" Khaleel yace "Noo she will be coming soon" Aliyu dai na tsaye yana ya na kallonsu, Can ya kalli Umma yace "Plss Maa it shouldn't take long xa ku iya tafiya yanxu the boy need rest" Umma tace "To xa mu fita yanxu Dr" khaleel ya juya yana kallon Aliyu, mikewa yyi ya isa gabansa yana kallon cikin idonsa yace "Then discharge him now, xa mu je gida in ci gaba da treating dinsa or I take him to another hospital" Aliyu yyi murmushi daga cikin mask din fuskarsa yace "And who are you to say that? His father? Or?" Umma tace "Aa bai kai haka ba Dr xa mu fita yanxu ai" wani kallo khaleel ya dinga ma Aliyu, Umma tace "mu je khaleel tunda a bakin aikinsu suke" kallonta khaleel yyi, duk da bai yi niyyar fita ba amma ya ji kunyanta yace "Toh umma" daga haka ya nufi kofa Shureim ya bata fuska kamar xai yi kuka yace "Uncle are you leaving us?" Sudais ma ya dinga kallonsa Kamar xai yi kukan, Khaleel ya juyo yace "Noo sweetheart I am around" Daga haka ya fita, Umma ta bi bayansa tana kara ba Aliyu hakuri tana fita ta rufe kofar, wata cleaner ce ta shigo dakin da abinci da ruwa da Aliyu ya sa ta siyo, ya mika ma Shureim nasa ya karba, Ya shiga ba sudais nasa da kansa. Khadijah duk ta damu tana son ta ga yaranta ganin har da Shureim ma tun da ta bude ido bata gansa ba, amma tsoron Umma yasa ta kasa cewa komai don tana iya balbaleta yanxu tunda ta ce mata they are all fyn, Khaleel dake tsaye dakin yana kallonta ya lura da yanayinta, ita ma ta tsaya kallonsa amma ta kasa ce masa komai ya san she Wants to say something, ya kalli Umma dake magana da wasu neighbours dinsu biyu da suka xo duba sudais, Nanny kuma ta koma gida tayi girki, Kyauta ma ta koma tace xata dawo ko da daddare da mai gidan ta, Khaleel ya karaso kusa da ita a hankali ya d'an duka yace "What?" Murya can kasa kamar xata yi kuka tace "I want to see my kids plss" wani kallo ya mata, sai kuma ya d'an yi murmushi yace "To sannu mai kids" ta bata fuska tana kallonsa alamar please, yace "Ohk wait bari Umma ta raka bakin nan sai in kai ki" lkci daya hankalinta ya kwanta tace "Toh ngdd" Umma na fita don yin rakiya ya cire mata drip din hannunta da ya kusa karewa, duk da jirin da take ji ta mika masa hannunta ya rike ta sauko daga kan gadon ta sa takalminta sannan suka fita ward din da sauri tana jin kamar xata fadi ba don ya rike hannunta ba, direct ward din da yan biyun suke ya nufa da ita, a hankali ya murda kofar ya bude, khadijah tayi ido hudu da Aliyu dake ba sudais abinci, still tayi a gun taji komai nata ya tsaya, xuciyarta ya dinga bugawa da sauri da sauri, Shureim ya sakko ya taho da gudu ya rungume ta, sudais yyi murmushi cike da jin dadi ganin uwar tasa yace "Anty...." Mikewa Aliyu yyi ya rufe abincin yana kallonta da khaleel yace "You can come over... But just few minutes" Khadijah ta warce hannunta a na Khaleel ta janye Shureim a jikinta ta juya ta bar wajen kamar xata tashi sama, direct reception ta nufa, tana kallon nurses din cike da masifa tace "Who is the Dr in charge of this hospital..." Kallonta nurses din suka tsaya yi, can wata ta mike tace "Me ya faru madam" tana huci tace "ohk, I want my kid discharge immediately, ku bani bill din in biya in bar nan yanxun nan plss" cikin tsawa ta kare maganar nurse din ta koma ta xauna tace "Easy madam, this a hospital, they are patients all over, ki je gun likitan da ya karbe su, shi xai yi discharging dinsu ba mu ba madam" khadijah na mata wani kallo tace "Wani likita kenan ina office dinsa kuma?" Nurse din tace "Dr Aliyu, kina haurawa sama office dinsa is by ur right, xa ma ki ga sunansa a jiki" kallonsu Khadijah ke yi xuciyarta na bugawa jin sunan da suka kira, can ta juya kamar xata tashi sama ta wuce upstairs din, Har lkcn khaleel dai na tsaye bakin kofa yana kallon Aliyu, Aliyu ya isa dab da shi yana masa wani kallo yace "Da matsala ne malam, naga kallon yyi yawa?" Wani murmushi khaleel yyi yace "You watch and see" Dawowa khadijah tayi dakin cikin tashin hankali ta nufi gun yaranta ta cire dip din hannun Sudais ta sauko da shi kan gado ta kama hannun Shureim ta nufi kofa, tsayawa gabanta Aliyu yyi yana kallonta da kyau yace "Ba inda xa ki je da su Iman" xaro ido tayi jin abinda ya fada ta tura sa da karfi amma go gezau, xuciyarta na heaving da mugun mamaki tace "Ba inda xan je da su kamar yaya??? ka taba sanin su ne, ko kuma ni ka san ni ne? Where did you knw us from" yyi wani murmushi yace "Khadijah, am giving you my words, you are not moving a step forward with my kids, ki fadi duk amount da kika ga yyi suite din ki, tun daga daukar cikinsu, rainon cikin, haihuwarsu har xuwa girman su yanxu and I will pay you, kilan hakan kadai xai sa ki yafe min idan na amshi wahalata da na hada ki da at a very tender age, ni kuma baxan ji kunyan daukansu in kai su gida gun iyayena a matsayin yaran da na haifa out of wedlock ba, shikenan kema na raba ki da wahala na raba ki da rikon 'ya yan da kika samu ta hanyar fyade da aka maki, sai ki tafi kiyi auren ki hankali kwance ba tare da kin kara tunanin kina da yaran da kika haifa ba ta hanyar aure ba, I am collecting my boys today for ur own good"
Kallonsa Khadijah take ko kiftawa babu, bakin ciki da takaici ne fal idanuwanta, xuciyarta ya dinga mugun bugawa, ta hadiye abu da kyar, lkci daya idanuwanta suka yi jajir cikin muryar da ba ta ta ba tace "Come again Aliyu... I didn't get you" Cire mask din bakinsa yyi gaba daya yana kallonta da kyau cikin husky voice dinsa yace "You are not daft Iman, you heard me right, or you ask ur bodyguard xai maki bayani da kyau" bai rufe baki ba ta sauke masa mari tana huci, wani murmushi khaleel yyi yana shafa sajensa yace "Seems you both need privacy" daga haka ya juya ya bar wajen har sannan yana murmushi, Aliyu ya kauda kansa na few seconds kafin ya juyo a hankali yana kallonta da wani irin mamaki, hawaye na sauka idonta tana girgixa kai tace "Allah ya isa tsakanina da kai Aliyu, shari'ar mu da kai dama na fada maka sai a lahira, kuma yarana

Please Login or Register in order to submit comment