Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

"Ko matata ce ke wannan laulayin ina xa ni da ita balle wannan" Yusuf yace "In baka shawara Barrister?" Sudais yyi shiru yana kallonsa, Yusuf ya mike tsaye yace "Wllh ka kyale mata cikinta tunda ka ga haka, Allah kadai yasan me xata haifa, there is power in the baby, banda haka ban ga dalilin da xai sa ta sha drugs din nan har sau biyu ba amma shiru ake ji, just let her pls and idan son samu ne ka taho da ita clinic ko gobe da safe ayi mata scan cos this is almost a miracle" kasa cewa komai Sudais yyi can ya juya ya fita. Washegari kamar yarda Yusuf yace haka Sudais ya sa khadijah ta shirya suka je asibiti don a mata scan, gaba daya jikinsa yyi mugun sanyi bayan result ya fito, shi kadai da Yusuf ne a office din Yusuf din, ita kuma tana reception, Yusuf yace "You see, da haka xaka sa ayi wasting bayin Allahn da basu san komai ba, 2 souls barrister" Sudais bai iya yace komai ba. A hakan dai Sudais ya ci gaba da ba Khadijah kulawa yanda ya kamata, bai rage ta da komai ba a gidan sa, damuwarsa daya yanda ta ki kwantar da hankali har lkcn ga yawan koke koke, idan ya sa ta gaba ta fadi me ke sa ta kuka sai ta ce masa ita bata da kowa yanxu, hakan nasa jikinsa yyi sanyi, sannan hakan ke kara masa kwarin gwiwan ci gaba da taimaka mata, ganin saura yan kwanaki ya fita kasar ya sa ya shiga tunanin wanda xai bar ta da a gidan, idea ne ya xo masa yasa aka nema masa wata dattijuwar da xa su xauna tare da Khadijah a gidan nasa, hakan aka yi bayan matar da baxata haura shekaru hamsin ba ta amince duk wata xai dinga bata dubu arba'in. A yau Khadijah na daki xaune kasan carpet tana shan kunun da dattijuwar da ta dama mata, dattijuwar matar da a ranan tayi kwana uku a gidan duk tunaninta Khadijah matar Sudais ce, su biyu ne dakin Sudais yayi sallama bakin kofa, ta mike da sauri ta iso kofa ta bude tana cewa "Sannu da xuwa yallabai" Gaisheta yyi ta amsa cike da jin dadin yanda yake girmamata sannan ta fita, Sudais ya karasa cikin dakin yana kallon khadijah, wani mugun haske tayi da kyau sai kyalli take, lips dinta yyi pink colour, dauke kai yyi ya isa gefen gado ya xauna, a hankali tace "Ina yini?" Yace "Lafiya lau, ya jiki?" Tace "Da sauki" shiru yyi na wasu yan mintuna kafin yace "Am traveling Amira" ta dago tana kallonsa, ya gyada kai yace "Yeah, gobe xan tafi" sauke idonta kasa tayi, lkci daya hawaye ya kawo idonta cikin sanyin murya tace "Tafiya xaka yi ba bar ni" ya tsura mata ido kafin yyi murmushi yace "Aiki xan tafi yi can, in sha Allah xan dawo when am done" ta kallesa hawayen idonta ya sakko tace "Toh yaushe ne xaka gama" ya wara Manyan idonsa yace "Nima ban sani ba, but da na gama xan dawo ai" kai kawai ta gyada masa amma kana ganinta kasan jikinta yyi sanyi, murmushi ya sake yi yace "Ba ga mama ba xata dinga kula da ke xan bar mata kudi ta dinga siya maki duk abinda kike so, just promise me baxa ki dinga damuwa ba that's all" murya can kasa tace "I promise, amma yaushe xaka dawo?" Dariya ta basa ganin ta yi tambayar daxu yace "Duk sanda kika samu lafiya kika fara cin abinci sosai sannan bakya damuwa xan dawo" xaro ido tayi tana kallonsa, yace "Yes" murmushi tayi ta sunkuyar da kanta, sae ranan ya fara ganin murmushinta ya dinga kallonta ganin xata dago kanta yyi saurin dauke kai, tana wasa da dogayen yatsun ta tace "Toh naji" yace "Yauwa ko ke fa" wayarsa daya ya Ciro ya mika mata yace "Xan dinga kiran ki in sha Allah" karba tayi a hankali tace "Toh" yace "to tashi ki raka ni" Ba musu ta mike shi ma ya tashi ya nufi kofa sannan ta bi bayansa, a parlor ya tsaya yyi sallama da Dattijuwar ya kuma sanar da ita xai yi tafiya ta dinga masa addu'ar Allah ya tsare yace "Ameen Ngd mama, don Allah ki dinga sa mata ido bata son cin abinci" tace "In sha Allah kar ka samu damuwa" Dubu hamsin ya ba matar ta dinga siya ma khadijah duk abinda ta bukata, ya kuma sanar da ita komai babu gidan Dr Yusuf xai kawo masu, daga haka ya juya yana kallon khadijah dake ta kokarin ganin bata yi kuka ba yace "Toh mu je" har bakin mota ta rakasa kanta a kasa ya kara mata sallama ta kasa daurewa ta fara kuka, duk jikinsa yyi sanyi, a hankali yace "Look Amira ba dadewa xan yi xan dawo ba, ki daina kuka pls" kai ta gyada masa cikin sanyin murya tace "Toh Allah ya tsare hanya" daga haka ta juya ta koma cikin gida ya bi ta da ido. Kamar kar Sudais ya bar kasar Khadijah ta fara samun lafiya sosai dattijuwar me kirki komai take so shi take mata kafin wani lkci duk babu ramar da tayi sai cikinta da ya fara fitowa, kullum a rana sudais xai kirata kusan sau biyar just to check if she is fine, idan bai kirata ba kuwa ta dinga damuwa kenan, a haka har watanni suka shude.

5 months later.

Yau tun da Khadijah ta tashi take ta murna ta rasa dalili, har hirarta ya fi na ko wani rana yawa har da dariyarta wanda da wuya ka ga tayi dariya, Dattijuwar mama suwaiba da take kira da Anty har ta lura da hakan tace "Wannan murnar yayi yawa khadijah ko dai mai gidan ne xai dawo yau" Khadijah dake hada fruits salad xata sha ta daga kai tana kallon mama suwaiba tayi shiru don kuwa gaskiya ne jiya da daddare da suka yi waya da Sudais yace mata yau xai dawo, murmushi tayi ta sunkuyar da kanta ta ci gaba da abinda take a hankali, mama suwaiba tace "Toh gwara a tashi a san me xa a girka masa, ki fadi duk abinda kika San yafi so sai in shirya in tafi kasuwa yanxu" Khadijah tayi shiru don har lkcn bata san komai game da Sudais ba balle ta san abinda ya fi so da wanda bai so, hakan yasa jikinta yyi sanyi sosai. A cikin watanni biyar din nan khadijah ta warware jikinta yyi kwari, babu abinda bata ci har da wanda bata ci a da can, wato wake, taliya kai har da tuwo da miyar kuka, wani kyau na musamman tayi don hatta fatar jikinta har wani glittering yake yayi taushi, yanxu kam cikinta ya fito sosai don sai ayi tunanin at anytime xata iya haihuwa don da kyar take yin komai nan ko watannin cikin bakwai, tausayi take ba mama suwaiba ganin yarinya ce sosai wa ya sani ko xata iya haihuwa da kanta ma, hakan yasa in dai ta fita cefane ko siyo wani abun bata rabo da dawowa da magunguna irin na gargajiya da tasan mai ciki na bukata, duk ranakun alhamis kuma tare da mama suwaiba suke xuwa can clinic dinsu Yusuf domin Antenatal a bisa umarnin sudais, damuwar Khadijah daya a lkcn ummarta don ko cikin dake jikinta baya damunta ta kuma rasa dalili, gaba daya tayi kokarin ganin ta mance ta taba rayuwa gidansu Aliyu, amma duk sanda cikinta yayi motsi sai ta tuna shi Aliyun, duk wannan difficulties na rayuwa da ta shiga ko sau daya bata taba jin haushin Aliyu ba kuma har ranta take jin ta yafe masa a lkcn... ko don tana tare da yarinta har sannan ne oho. Khadijah ta kasa hakuri ganin har yamma bata ga sudais ba alhalin yace mata in sha Allah yau yana Nigerian duk jikinta yayi sanyi ta tafi daki ta kwanta, Mama suwaiba kuma ta ki hakura tana ta girke girke a kitchen ita kadai. Sudais na sauka taxin da ya kawo sa har kofar gida ya shiga gidan yana rike da daya daga travelling bag dinsa guda uku da mai taxin ya dire masa a bakin gate, kai kana ganinsa kasan daga turai yake don wani fresh na musamman yyi da haske sai dai ya rame sai idanuwa da hancinsa da suka fito, sosai ya rage bak'in gashin kansa, yyi murmushi ya na amsa gaisuwar da mai gadi ke masa da fara'a yana masa sannu da dawowa sannan yace "Ka shigo min da sauran kayana bilyamin" tun a bakin kofa kanninsa suka rungumesa ko wacce na murnar dawowarsa bayan kusan watanni biyar, Mami dake parlor da Anty Maryam ma sai murmushi suke, lkci daya murmushin Sudais yyi fading ganin Jiddah da yayi xaune parlorn, ya karaso a sanyaye ya duka kasa ya gaida mami ta amsa tana murmushi tace "Sannu da xuwa Aliyu ya hanya?" Yace "Alhmdllh Mami, fatan mun same ku lafiya?" Tace "Alhmdllh" gaisawa suka yi da Anty Maryam sannan ya kalli jiddah yana kirkiran murmushi ta sunkuyar da kai tace "Sannu da xuwa ya hanya?" Yace "Alhmdllh mun same ku lafiya?" Tace "Sure" Rabi'ah da Humairah suka dau bags dinsa xa su kai daki yace "Noo don't worry sisters wancan kadai xaku dauka ku bar wa ennan, xan d'an fita yanxu" da mamaki Mami tace "Ka fita kaje ina daga dawowa, idan ma fitan xaka yi ina xaka da jaka kuma?" Ya sunkuyar da kai yace "Sakon wani abokina ne xan kai gidansu Mami" Mami tace "Ohk, to amma sai ka huta ka ci abinci koh?" D'an shiru yyi sai kuma yace "Mami baxan dade ba xan dawo yanxu" daga haka yasa kanninsa suka dau jakunkunan suka kai masa bakin motarsa sanin ko baya nan ana amfani da motar, ya mike yace "Toh sai na dawo Mami" tace "Toh don Allah kar ka jima ka dawo ka ci abinci ka huta" yace "In sha Allah" yana barin gidan bayan ya hau titi ya dau wayarsa ya shiga kiran khadijah, Khadijah dake kwance har lkcn a daki ta mike da sauri kamar jira take jin ring din wayar ta jawo ganin Sudais ne ta daga ta kai kunne, daga daya bangaren yyi sallama yace "Amira" turo baki tayi tace "Uhn" yace "How are you" a hankali tace "Fine baka dawo ba kuma" d'an murmushi yyi yace "I postponed the trip xuwa next month in sha Allah" wani irin faduwa gabanta yyi da har sai da ta ji a kirjinta da ya mata sauki kwana biyu sbda magungunan da Yusuf ke bata, hawaye ne ya shiga sakkowa idonta, yace "Hello are you there?" Kasa amsawa tayi ya dinga hello ta katse wayar ta hade kai da gado ta fara rera kuka, sake kiranta yyi ta ki dauka har ya katse ya kara kira, sai a snn ta dauka ta kai kunne taki cewa komai, murya can kasa yace "Amira" ta fashe masa da kuka a hankali, wara ido yyi hade da murmushi yace "Har da kuka kuma?" Ta ki cewa komai, murya can kasa yace "Cry no more, tunda kina son ganina kawai fito gate ki tsaya ni kuma xan taso daga UK yanxu, har kofar gida jirgin xai ajiye ni" mikewa tayi xaune da sauri tace "Don Allah ka bari, ka dawo pls?" yace "Da gaske fa just wait me outside xa ki ganni yanxun nan" katse wayar tayi ta tashi da sauri ta dau Hijab har Kasa ta sa sannan ta fita dakin, Ganin xata fita waje Mama suwaiba da fitowarta kitchen kenan tace "Ya iso halan" Khadijah bata iya ta ce komai ba ta kirkiri murmushi ta fita, a hankali take tafiyar har ta isa gate ta tsaya gabanta na bugawa, tsaye ta ga motarsa bakin gate din suna hada ido ya bude motar ya fito yana murmushi, tsabar farin ciki ta kasa cewa komai amma kana ganin ta kasan she is just happy, ita dai tasan yau da ace mace ce Sudais da ta tafi da gudu ta rungumesa, ya wara mata ido ganin kallon da take masa yace "Toh ko dai in koma tunda kallona xa ki tsaya yi" tahowa tayi ta tsaya gabansa ta sunkuyar da kai tana murmushi, murmushin yayi shi ma murya can kasa yace "How are you Amira" ta kasa dago kai cikin sanyin murya tace "Am fyn, sannu da dawowa" yace "Sannu, ya babies dinmu" dagowa tayi ta kallesa da sauri sai kuma ta juya masa baya, dariya yayi yana kallonta, tayi murmushi tana jan hannunta, yace "Toh mu shiga" tafiya ta fara yi ya bi bayanta bayan ya rufe motar har suka shigo parlor. Xaunawa yayi parlorn suna gaisawa da mama suwaiba dake tayi masa sannu da xuwa, khadijah ma ta xauna kasan parlorn tana kallonsa ko kiftawa bbu, mama suwaiba ta koma kitchen ya maida dubansa kan Khadijah, sauke idonta tayi kasa da sauri, yace "Are you now happy" murmushi tayi tana gyada kai a hankali shi ma yyi murmushin yana kallonta, Kirar ta Mama Suwaiba tayi ta mike ta nufi kitchen ya bi ta da ido, Mama suwaiba tace "Toh ke haka ake yi, sai ki je bayi ki hada masa ruwan wanka, idan kuma abinci xai fara ci sai ki kai masa daki" murmushi khadijah tayi bata ce komai ba, mama suwaiba tace "Toh kin yi shiru kuma" a hankali khadijah tace "Toh bari in tambayesa" daga haka ta juya ta koma parlor, Wayarsa yake dannawa ta duka gefensa ya kalleta yace "Xauna kujera mana, you are stressing ur self and the babies" sauke idonta tayi kasa tace "Dama Anty ce ta ce in tambayeka ko xaka ci abinci a kai maka daki" shiru yyi na wani lkci kafin yace "She is thinking something different, and Mamina ta min abinci a can gida but... Ohk toh kai abincin daki" Tashi Khadijah tayi ta koma kitchen ta karbi abincin da Mama suwaiba ta hada a tray ta wuce can bedroom da shi, Sudais ya mike ya bi bayanta, karban abincin yyi a hannunta ya ajiye kan rug sannan ya xauna yace "Ke kin ci abincin" tace "Na ci daxu" yace "Daxu daban, yanxu daban, so xauna mu ci" dafa gado tayi xata xauna a kasa yace "No ki xauna saman gado" xaunawa tayi gefen gado ya debi abincin a plate ya sa spoon sannan ya mika mata ta amsa a hankali tace "Nagode" ya debi kadan a wani plate din dai dai nan wayarsa yyi ring dubawa yyi da sauri ya ga Mami ce, ya d'an bude ido sannan ya daga, daga daya bangaren Mami tace "Wai daga dawowa ina ka tafi haka Aliyu? Are you even okay" a hankali yace "Gani nan tahowa Mami am sorry" katse wayarta tayi, ya ajiye wayar yana kallon abincin, samun kansa yyi da Kasa cin abincin, ya rufe yace "Amira xan je gida Mami na jirana idan kin cinye wannan sai ki kara da nawa" Bata ce komai ba sai wasa da cokalin hannunta take, ya mike yace "Kilan xan xo gobe da safe, take care of ur self" daga haka ya juya ya fita, hawaye ne ya cika idonta ta rasa dalili abincin duk ya fita ranta ta kasa ci ta ajiye tana goge hawayen dake xubo mata, Sudais na fita ya tuna bai shiga da kayan da ya taho mata da su daga UK ba, ganin xai kara bata lkci kawai yyi deciding ya bar sa a motar sai gobe idan ya xo. Ko da ya koma gida kawai yana cin abincin da Mami tayi masa ne amma gaba daya hankalinsa na kan Khadijah don bai san ko ta ci abincin da ya debar mata ko bata ci ba, Mami dake xaune ta sa shi gaba da jira har ya gama cin abincin sannan tace "Kun yi waya da jiddah xaka dawo yau ne?" Girgixa kai yyi duk da faduwar da gabansa yyi a hankali yace "Aa mun ma kwana biyu ba mu yi magana ba, fushi take ai da ni" Mami tace "Toh wasa wasa gashi har watanni kusan shidda da kace a daga biki yyi, yanxu kuma ya ake ci" kasa kallonta yayi ya fara kame kamen rufe warmers din abinci, strictly tace "Magana nake ma ka Aliyu" da kyar ya dago ya kalleta yace "Toh Mami a sa bikin nan da wata daya xuwa biyu in sha Allah" wani kallo ta watsa masa tace "Me sati biyu ko uku yayi da har sai an kai wata biyu kuma?" Ya shafa kai yace "Dai dai wannan lkcn xan koma UK kuma xan jima sosai kafin in dawo kinga kawai ana bikin a lkcn sai mu tafi tare da ita" Mami tace "Allah ya kai mu, xan ma Abbanku bayani" yace "Nagode Mami" daga haka ya mike yace mata xai kwanta ya wuce bedroom dinsa. Yana shiga dakinsa khadijah ya kira, tana dagawa yace "Kin gama cin abincin?" Turo baki tayi tace "Na koshi" yace "Baki ci ba kenan?" Shiru tayi bata ce komai ba, yace "Me kike yanxu?" Tace "Na kwanta" yace "Tashi ki je ki dau abincin ki ci idan ba haka ba baxa ki ganni gidan nan ba for plenty days" tashi tayi xaune da sauri tace "Ni ban ce baxan ci ba" yace "Toh je ki ci" ta mike da kyar tace "Toh" yace "Idan kin gama ki kirani" gyada masa kai tayi kamar yana ganinta ya katse wayar. Sosai ta ci abincin ta hada har da wanda ya dibar ma kansa, tana gama ci ta dau wayar ta kirasa, sai da ya kusa katsewa ya daga, jin muryarsa tace "Bacci kake" a hankali yace "Yea, kin gama cin abincin?" Tace "ehh na cinye" yace "Good Mami" murmushi tayi tace "Toh kayi baccin, byee" murmushin shi ma yyi ya katse wayar. Xuwan Yusuf gidansu da daddare ne saving grace dinsa don da shi da fita kuma sai gobe, bayan Yusuf ya gaisa da Mami suka tafi dakin Sudais yana tambayar sa ko yayi ciwo a UK ne don ya rame sosai, bayan kusan minti talatin Yusuf yace xai tafi suka fito tare da sudais da yace ma Mami xai rakasa, sai da suka shiga mota Yusuf yace "Kaje ka duba mai cikin ka?" Sudais ya hade rai yace "Mai cikina kuma" dariya Yusuf yyi yace "Toh ai kusan baka da banbanci da uban yaran, kai ma uba kake a gare su kama fi sa xama masu uba kan ubansu" tsaki Sudais yyi bai ce komai ba, Yusuf yace "But don Allah Sudais da yau ko watarana xaka ga uban unborn babies din nan me xaka masa?" Sudais yyi wani murmushi da kamar baxai ce komai ba sai kuma yace "I won't even look at him twice yaran da xata haifa sun ishesa" Yusuf yace "What if ya xo wataran yayi claiming yaran fa?" Wani kallo Sudais yyi masa baki bude, can yyi wani dariya yace "Wllh wllh I will sue him, sai na sa yyi shekaru da dama a gidan yari" Yusuf dake driving ya wara ido yace "Tohhh, kenan yaran ka ne ba nasa ba" Yusuf na dariya ya kare maganar, Sudais yyi banxa da shi, Yusuf yace "Toh why not bayan ta haihu ka aureta kawai Sudais" juyawa Sudais yyi yana kallonsa da wani expression, can ya dake yace "Ko saboda me?" Yusuf yyi murmushi yace "Saboda ka ji dadin ci gaba da kula da ita da yaran da xata Haifa kwanan nan, kasan a yanxu kai ne ubanta kai ne uwarta, i mean kai ne gatan ta, don haka sai ka ci gaba da xama gatan nata har karshen rayuwarta, nan da shekaru biyu kai ma ta haifa maka naka yan biyun ba na wani ba"

Girgixa kai Sudais yyi bayan ya dauke idonsa daga kallon da yyi ta ma Yusuf yace "I didn't blame you Dr, why?? Because am very sure kafin ka xo gidanmu yanxu daga club din da ka saba xuwa kake, and definitely idan ka je club dole sai ka sha ruwan can na sani, soo no offense, u are drunk...." Dariya kawai Yusuf yake yace "Kai kuma tun bayan haduwarka da marainiyar nan ka daina xuwa can koh? Thank God we where both drunkards before" Sudais da yyi mugun hade rai yace "Drop me here my frnd" Yusuf yyi parking yace "Ji dan iska kamar wani driver din sa wai drop me here my frnd" Bude motar Sudais yyi ya fice ya juya yana masa wani kallo, da yatsarsa yyi masa xagin turawa yayi wucewarsa, dariya kawai Yusuf yake ya ja motarsa ya wuce gida, Da kafa Sudais ya karasa gidansa, Mama suwaiba kadai ce parlor tana cin abinci TV a kunne, tana ganinsa ta mike da sauri tana masa sannu da xuwa yace "A'a yi xaman ki mama" Mama suwaiba ta koma ta xauna tace "Toh nagode" yana son tambayarta khadijah amma yyi shiru, can ya mike ya wuce bedroom, kwance ya ganta tayi bacci tana rufe da bargo, ya karasa kusa da gadon yana kallonta, dukawa yyi dai dai fuskarta murya can kasa yace "So early?" Ko motsi bata yi ba alamar ta jima da yin baccin, a hankali yyi murmushi ya kai hannu dogon hancinta ko mai ya tuna yyi saurin withdrawing din hannunsa ya mike ya kashe mata wuta ya fita daga dakin, Sallama yyi ma Mama suwaiba ya nufi kofa ta bi sa da kallon mamaki, yau ma da ya dawo baxai kwana gidansa tare da matarsa ba, wannan wani irin aure ne a gantale, har ya rufe kofa kallonsa take baki sake. Washegari lahadu Khadijah na xaune parlor da tuwo da miyar kuka da mama suwaiba tayi mata, da cokali take cin tuwon mama suwaiba kuma na kitchen tana wanke wanke, bude kofa aka yi ta daga kai da sauri sudais ya shigo parlorn rike da babban jaka, ajiye jakar yyi yana wara ido yace "Kaiiii yanxu xa ki iya cinye wannan tuwon Amira?" Rufe fuskarta tayi da kujera da sauri tace "A'a fa xan rage in ci anjima" dariya yyi ya juya ya fita ya shigo da daya jakar ya ajiye sannan ya xauna kan lallausan carpet da take xaune yace "Ci da yawa abin ki kin ji, sai ki haifo mana yara masu karfi" bata dago kanta ba har lkcn yyi murmushi ya bude zip din jakar ya fara fiddo kayan ciki, sai bayan da ya Ciro kayan jakunkunan gaba daya sannan yace "Here... you like them?" sai a sannan khadijah ta dago a hankali tana kallon kayan, kayan babies ne masu tsada ko wanne set biyu, shiru ta yi tana kallon kayan, ya ware nata dogayen riguna masu kyau gudu hudu yace "Wannan kuma naki" sauke idonta da ya kawo ruwa tayi a hankali, ya hade rai yace "Baki so ne xa ki min kuka" bata san lkcn da ta fashe da kuka ba ta hade kanta da kujera, yyi shiru yana kallonta, can ya fara mayar da kayan gaba daya jaka yana gamawa ya kai jakunkunan daki sannan ya nufi kofa ya fice daga gidan ya shiga motarsa ya wuce. Har bayan kwana biyu Sudais bai je gidan ba duk da he is just trying not to go amma hankalinsa gaba daya na can, sosai hankalin khadijah ya tashi don tasan kilan fushi yake ne ya sa, tana son kiransa amma ta kasa, ganin baxata iya jurewa ba kuma ta kira sa, a lokacin yana gida bedroom din Mami suna hira da Anty Maryam, ganin kiran yyi ta kallon screen din kafin yyi silencing wayar ya mike yace "Mami bari in tafi in shirya xan fita yanxu" daga haka ya bar dakin bayan yayi ma Anty Maryam ma sallama, Mami ta tabe baki tace "Kwata kwata Aliyu ba shi da gaskiya yanxu, I really don't knw what he is up to, tun ma kafin ya bar kasar months back na lura da haka kuma gashi ya dawo ya ci gaba da behavior din, there is something big he is hiding kuma shi ya hanasa auren ma, dubi fa yanda ya axalxalemu a

Please Login or Register in order to submit comment