Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

abincinta, kyauta ta bi khadijah kitchen ta jawota fuskarta daure tace "Ke fa ba ruwanki da yaran gidan nan naga har kin fara masu fetsara, ki tsaya a matsayin ki idan ba haka ba baxawara ta ishe ki"

Karfe hudu duk yaran gidan suka gama shirin tafiya islamiyya, kyauta ta hada socks dinsu gaba daya da Uniform din autar Mumy da ake kira da Baby saboda sunan Anty khadijah gareta xata wanke, kallon khadijah dake tsaye kanta tayi tace "Toh ni dai kin tsaya min kamar soldier ki tafi can dinning area ki kwaso duk plates din wajen, saura kar kiyi a hankali" khadijah tace "Toh" sannan ta wuce ciki, bbu kowa dinning area din sai plates da shinkafa da aka yi littering a wajen, Khadijah na ganin Anty khadijah a parlor xaune tana gyara ma Baby Hijab tayi saurin dauke kanta ta shiga hade plates din waje daya, muryar daya daga yan matan parlorn taji tana cewa "Anty wacece wancan yarinyar wai?" Anty khadijah ta tabe baki tace "The new housemaid" Baby ta xaro ido tace "Anty is kyauta going?" Anty khadijah tace "Noo she is not" Baby ta sauke ajiyar xuciya tace "Better... coz I don't think i like that girl, she can look for Africa as a whole" horn da driver yake yasa Siyama da Aneesah suka mike rike da jakar islamiyyarsu suka ma Anty khadijah sallama suka fita, Anty khadijah tace "She's not even worth talking to, don hka bbu ruwanki da ita yar aikin gidan ce kin ji takwara" baby tace "Sure" khadijah ta turo baki tana kallonsu, baby ta harareta ta fice daga parlorn, khadijah ta ki daukan komai a dinning din ta fita gun kyauta da gudu tana kumbure kumbure, kyauta tace "Ina kwanukan?" Ta fashe da kuka tace "Anty mai girki kinga yarinyar nan har da neman tsokanana koh, shine har da ce min I can look for Africa where as she was the one looking at me, kuma Anty mai ihu tace mata ni house girl ce" Kyauta ta tabe baki ta nuna mata wani dakali tace "Tafi can ki xauna, ni dai ba ruwana idan kina kallon yan gidan nan sai su dake ki ma su daki banxa nima ba kyaleni suka yi ba gwara babyn ma a cikinsu, idan ba iskanci ba... Ba aikin aka kawo ki kiyi ba har xa ki ji haushi don an ce maki house girl?" Khadijah ta turo baki bata ce komai ba, kyauta ta gama wankin ta tafi ta kwaso plates din ta gyara dinning din, khadijah ta hada ma kayan wanke wanken can bakin tap kar ta jika kitchen din ita kuma ta shiga girka dinner, da ta leka sai ta ga kamar ba a wanke wanken, daga karshe fixgota tayi bakin tap din ta turata waje daya ta shiga wanke wanken tana bala'i, khadijah ta toshe baki kar tayi dariya jin har da kiranta lazy ass, har kusan magrib khadijah na kusa da kyauta a kitchen komai kyauta ta sauke kan wuta sai ta ba buda mata hannu xata d'an d'ana tun kyauta na mata da mugunta tana konata da cokalin miya har ta gaji ta kyaleta sai ta xuba mata a d'an karamin plate, kyauta ta samu wani roba ta xuba duk pepper soup din da tayi mai yawa a ciki bata yi gigin ba khadijah ba tace "Tafi ki leka su waye a parlor" khadijah ta dawo tace "Ba kowa Anty mai girki" kyauta ta fita da sauri ta bude dakinsu ta ajiye masu bayan kofa sannan ta dawo ta jera komai kan dinning bayan ta ba khadijah na su Usman mai gadi ta kai masu, Kyauta na gama tsaftace kitchen suka wuce daki da Khadijah, sai a sannan ta xauna ta fixgo khadijah tace "Ke bakya sallah ne hala?" Khadijah tace "Ina yi amma bani da Hijab yanxu" turata bayi kyauta tayi tace "Ni ina da shi ai" Khadijah na xaune kan dankwalin da kyauta ta shimfida mata ta yi sllh tana ta kallon kyauta dake addu'a ta idar da sallahn ita ma, Muryar Mumy kyauta taji ta shafe addu'ar ta mike da sauri ta fita khadijah ma ta bi bayanta da sauri, Mumy tace "Ki xuba ma Aliyu abincin xai wuce aiki yanxu, ku kun ci abincin?" Kyauta tayi kasa da kai tace "Xan xuba masa yanxu Hajiya, mu kuma yanxu xa mu xuba" Mumy tace "Toh sai ki debar maku har da farfesun" Kyauta tace "Toh mun gode Hajiya" Mumy tace "Toh ya tana kokarin aiki kuwa ita?" Mumy ta fada tana nuna khadijah, kyauta tace "Ehh ba laifi Hajiya" Mumy ta juya tace "Toh shkkn" A dinning kyauta ta dibar ma Aliyu nasa abincin a plate ta xuba masa farfesun kaji sanin bai cin sauran, sama ta tafi kai masa khadijah ta biye da ita, ta kwankwasa masa kofa ba a dau lkci ba ya bude yana buttoning din shirt din jikinsa, kyauta tace "Ga abinci yallabai" kallo daya yyi masu ya karbi tray da kyauta ke mika masa yace "Nagode" khadijah tace "Nan ne dakin ka" bai ce komai ba ya rufe kofarsa, kyauta ta ja khadijah suka sauka ta shiga daki da ita ta hade hannayenta biyu tace "Ke wai dan gidanku ina ruwan ki da likitan gidan nan, kin taba sanin sa ne idan ba shisshigi ba?" A hankali tace "Kiyi hakuri" kyauta ta ja bakinta da karfi hade da dungurinta tace "Sai na cire maki wannan mayun idon naki wllh idan kika sake yi ma kowa magana a gidan nan" khadijah ta gyada mata kai hawaye cike idonta, kyauta ta fita ta bar jin alamar su baby sun shigo gidan daga makaranta. Ko kafin kyauta ta sallamesu ta dawo ciki har khadijah tayi bacci, tashin ta ta shiga yi ta ci abinci cikin magagin bacci take cewa Umma na koshi, kyauta ta debo ruwa ta yarfa mata a fuska, da sauri ta farka gaba daya kyauta ta ajiye mata abincin a gabanta ta shiga bayi don yin alwala, ko da ta fito Khadijah bata ci abincin ba ta koma bacci, hakan yasa tace "Ke kika sani" dagata tayi ta kwantar ta xauna cin abincin ita kafin tayi sallahn. Washegari kyauta na idar da sallah ta fita daura breakfast, ta gama fere dankalin turawa Anty khadijah ta shigo kitchen din, kalle kalle ta shiga yi kafin tace "ina wannan yarinyar take?" Kyauta tace "Ina kwana Anty?" Anty khadijah tace "Lafiya, ina yarinyar nace?" Kyauta tace "Na aiketa daki shiru shiru" fita Anty khadijah tayi ta bude kofar dakin kyauta tana yatsine fuska, kwance ta tadda khadijah shame shame kan gado, karasawa tayi ta maka mata duka har sau biyu a baya, khadijah ta farka a rikice, Anty khadijah ta fixgota tace "Ko yan gidan gaba daya ma sun tashi bare ke shegiya, a hakan xa ki iya aiki a gidan nan, a kirga har dubu goma a bai ma iyayenki jiya ki yi ma mutane shame shame kina bacci kan gado har yanxu?" Khadijah ta sauka kan gadon hawaye cike idonta tace "Anty kiyi hakuri" fixota Anty khadijah tayi ta turata waje da karfi tace "Fita kije ki kama ma kyauta aiki, ko ita din baiwar ki ce, ina ce yanda ake biyanta haka ake biyan ki kema" khadijah ta wuce kitchen da sauri tana hawaye, Anty khadijah ta biyota har kitchen din tace "Maxa hada wanke wanke ki fita ki yi" da sauri ta dinga fita da plates waje hawaye na sakko mata, ita dai kyauta bata ce komai ba har Anty khadijah ta fita kitchen din, khadijah ta dau cups uku xata fita da su, kyauta tayi tsaki tace "Mata ta ki xaman aure duk ta xo ta addabe mutane a gida tirrr, ke kuma ai kinga result din bacci kamar matatcciya" khadijah dai bata ce komai ba ta fita, Kyauta ce tayi wanke wanken bayan ta sallami yan makaranta khadijah na mata dauraya, karfe tara da rabi mumy ta sakko xata fita aiki, bayan sun gaisa da kyauta dake hada mata breakfast a dinning mumy tace "Ina khadijah" Kyauta tace "Tana can tana shara Hajiya" Mumy tace "Ohk" kyauta ta koma kitchen bayan ta gama hada ma mumy shayi sanin gimbiya na can sama tana ta bacci yanxu haka, Kallon khadijah tayi da tasa dankali da kwai da shayi a gabanta ta ki ci, Kyauta tace "Au baxa ki ci ba?" Khadijah ta kalleta tace "Ina ci" sai kuma ta fara kuka, Kyauta tace "Samun waje, wato duk da lafiyayyen abincin nan dake gaban ki har kuka kika samu daman yi koh? Kila ma a gidan da kika baro baki samun irin haka" khadijah ta mike tana kuka ta daga rigarta tana nuna ma kyauta bayan ta tace "Anty mai girki har yanxu fa xafi wajen da ta dokeni yake min" kyauta ta buda baki ganin shatin hannun Anty khadijah a bayanta, can tace "Tabdi, toh Allah ya isan ki, kuma in sha Allahu a baxawara xata Karachi rayuwarta, ni kam ko yanxu na bar gidan nan nasan xan samu mijin aure, ita kuwa wllh sai dai taga ana yi, kuma ina jin ita ma ta bar 'ya yanta a wani gidan to haka xa ayi ta cin ubansu ana gallaza masu in sha Allahu" Kyauta ta sauke rigar tace "Maganinki kenan kema dai, gobe ba sai kin jira an tashe ki ba" daga haka kyauta ta ci gaba da aikinta, da sauri kyauta ta fita jin mumy xata wuce gun aiki, ta gama sauraren abinda mumy ke ce mata ta risina tace "In sha Allah Hajiya, Allah ya tsare hanya" tsaye jikin kofa Mumy ta hango khadijah tace "How are you" a hankali khadijah tace "Good morning maa" mumy ta kalli kyauta tace "Anya baki cika ma yarinyar nan aiki kuwa kyauta?" Da sauri kyauta tace "Wallahi ko daya Hajiya, ki tambayeta bana cika ta da aiki" Mumy tace "Ohk" sannan ta mayar da dubanta kan khadijah tace "Am off to work, hope kin yi breakfast?" Ta gyada kai tace "Nayi Anty" Mumy tace "Good" daga haka ta nufi kofa, kyauta ta rakata tana mata Allah ya kiyaye, Mumy na fita da motar ta kyauta ta koma kitchen ta kwashi sauran kayan wanke wanke ta tafi wankewa a waje, khadijah na ta tsaye bakin kofar kitchen din Aliyu ya shigo gidan, tun da ta kallesa bata sake kallonsa ba har ya wuce sama, bayan kusan minti ashirin sai ga shi ya sakko, har lkcn khadijah na gun da take a tsaye, ya shiga kitchen din ya hada abinda xai hada a cup ya fito har ya wuce ya juyo ya daure fuska yace "Baki iya gaisuwa ba koh?" Ta turo baki tace "Good morning" daga haka ta juya ta wuce gun kyauta a waje, ya kusa second ashirin a tsaye kafin ya juya ya wuce sama. Ruwan wanka kyauta ta hada mata bayan sun koma daki, khadijah tace "Anty mai girki ni fa ban yi brush ba kika bani abinci" kyauta tace "Ni na hanaki brush?" Khadijah ta langwabar da kanta tace "Toh su fauxiyya sunyi lost din min brush dina a gidansu" kyauta tace "Oho dai tafi kinyi wanka ga ruwa can" khadijah na fitowa daga wanka kyauta ta bata Vaseline ta shafa sannan ta fiddo mata da daya daga kayan ta da ta linke bayan ta kwaso mata su jiya, khadijah tace "Anty mai girki kinsan wa ya siyo min new pants din nan" kyauta tace "Oho" khadijah tace "My lovely Umma" kyauta bata sake kula ta ba ta fixgota ta lafta mata uban kwalli a ido ta shafa mata farin powder a fuska sannan tace "Wuce can baya ki xauna kar ki shigo gidan nan sai na kira ki na gaji da surutun ki" khadijah tace "Toh" sannan ta fita, dakalin da ta saba xama ta xauna bayan ta tsinka flowers da yawa ta dinga yin jakar hannu da su kamar yanda aka koya masu a schl da dadewa, kamar ance ta daga kai suka hada ido da Aliyu dake kallonta, ta dauke idonta ta ci gaba da abinda take, bayan wani lkci ta daga kai bata sake ganinsa xaune balcony din ba, gajiya da xama tayi ta shiga ciki ta bude kofar kyauta a hankali ta ganta kwance tana bacci, shiga tayi ita ma ta kwanta gefenta nan da nan bacci ya dauketa. Da yamma Mumy na xaune parlor da Anty khadijah da ita ma dawowarta gidan kenan tun daxu da ta fita, khadijah ta fito daga daki bayan ta ajiye kayan kyauta da ta bata, mumy ta kirata ta karasa parlorn ta durkusa tace "Anty gani" mumy tace "Meye da meye bbu a kayan ki?" Khadijah tayi shiru tana naxari, can ta fara lissafo su da fingers dinta tace "I don't have toothbrush and toothpaste, I don't have towel, I only have six pants da ummata ta siya min sauran fauxiyya ta sace min, even ves bani da shi, kuma bani da mai da xan shafa, Anty har da na gashina" murmushi kawai Mumy take, Anty khadijah kuwa ta hade rai kamar bata taba dariya ba, Aliyu dake dinning yana cin abinci tabe baki kawai yyi, mumy tace "Toh in ga kan naki" khadijah ta xame hular kanta Anty khadijah ta saci kallon dogon gashin, mumy tace "Kai maa sha Allah ran Saturday sai ki bi su Siyama kema a gyara maki koh" da sauri khadijah ta xauna a tsorace tace "Anty ummata ta gyara min ai, it's just of recent ta kai ni saloon" Mumy tace "Anjima driver xai kawo maki duk abinda baki da, kina da takalmi koh?" Ta gyada kai tace "Amma ya kusa tsinkewa su fauxiyya suke sa min" mumy tace "Toh tashi kije xa a siya maki" khadijah tayi murmushi tace "Toh Anty I like you" daga haka ta wuce kitchen gun kyauta da sauri. Mumy na kallon Anty khadijah da har lkcn ranta a bace yake tace "Khadijah am thinking ko in sa yarinyar nan a islamiyya su dinga xuwa tare da su baby da yamma, kowa ya ganta yasan she is from a wealthy home, it's just condition...." Katse ta Anty khadijah tayi tace "Anty fatima ki raba kanki, Anty Fatima ki raba kanki ki kyale mutum yanda kika gansa na sha gaya maki times without number, su wa enda suka kawo ta gun aikin sun fa pi ki sanin akwai islamiyya, me yasa kike son sa ma kanki matsala ne wai, tsinannun masu aikin nan da kiris suke jira su tura wanda ya kyautata masu cikin rana, meye hadin ki da yarinyar idan ba shisshigi ba da neman wajen xama??" Mumy ta kalli Aliyu dake ta kallonsu tace "Abuturrab yanxu don nace ayi enrolling din baiwar Allahn nan a islamiyya laifine don Allah?" Ya mike yace "Noo, ba laifi bane mum, sai ma lada da xa ki samu in sha Allah" daga haka yayi wucewarsa sama, Anty khadijah ta bi sa da wani mugun kallo, mumy tace "Atoh, baka san yanda Allah xai yi da naka ba gobe, baka kuma san ina reward din ka yake ba, yarinyar nan tare da ke take gaya mana ita marainiya ce, to don me baxa a ji tausayinta ba, kika san kudin iyayenta a da, don duk wanda yaga yarinyar nan yasan ba daga karamin gida ta fito ba, just put little baby in her shoes... Kin dai ga sa'anni ne su din daga ganin, to da baby ce ta shiga irin halin nan yaya xa ki ji, Allah ya rufa min asiri don dai kudin islamiyya xan iya biya mata, toh ni ban san meye damuwarki ba khadijah" Tsaki Anty khadijah tayi ta mike ta nufi stairs tana cewa "Muna nan da ke sai kin yi da kin sani Anty, shi kuma Aliyu ya ci gaba da daure ma karya kugu, daga ganin yarinya shegiya ku hakikance ku ce a sa ta a Islamiyya for what reason, shi aka aikota yi gidan nan" Mumy tace "Aniyar ki ta bi ki khadijah, shi yasa kike samun matsala da kowa a rayuwa ni dai baki yo halin mahaifanmu ba Allah ya ji kansu, nima ba halin mu daya ba, tirr"

Washegari thursday Kyauta xa ta kasuwa tare da Khadijah bayan Mumy ta fita aiki, Anty khadijah kuma ta fita anguwa, Aliyu kadai suka bari gidan kasancewar night duty yake yanxu, da ido ya bi su har suka fita parlorn, Driver da xai kai su kasuwar ya tada motar ganin sun fito, Daya daga dogayen riguna Umma ta siya ma khadijah ne jikinta sai hula da Kyauta ta sa mata ta bata karamin mayafi ta daura a kan, Khadijah ta karbi list din abubuwan da xa su siyo ta dinga karanta su kyauta na jifanta da hararan wa ya sa ta? Driver Sanusi yace "Wai wannan yarinyar madam tace mu je tare da ke ayi ma siyayya?" Kyauta tace "Ehh ita ce" Drivern yace "Kin ga shi kenan sai ayi mata gaba daya koh? Daxu ta bani dubu ashirin da biyar kafin ta fita" kyauta tace "Ka ji sanusi da wani xance, cefane fa xa mu je yi ba kasuwar kaya ba" Sanusi yace "Toh shkkn, gobe sai mu je kasuwar kayan" sai kusan karfe daya Kyauta ta gama duk siyayyar da xata yi suka dawo gida, babu kowa gidan har Aliyu ma ya fita, nan ta daura girki a gurguje Khadijah kuma ta tafi yin sallah kamar yanda tace mata tana idarwa taki fita tayi kwanciyarta. Karfe Uku da rabi su Siyama suka dawo gida, kyauta ta xuba masu abinci gaba daya ta kwashi uniform dinsu ta kai gun wanki, baby kadai ce parlor ta sa cartoon tana kallo da plate din abincin a hannunta da yake bbu islamiyya, su Siyama kuma suna can kan dining, khadijah ta fito daga daki tashinta daga bacci knn ta makale jikin bango tana kallon Cartoon din da baby ke kallo, Baby na ganinta ta kashe tvn da remote ta hade rai, shiru khadijah tayi bata ce mata komai ba, su Siyama suka fara dariya suna kallon khadijah dake tsaye, bude kofa aka yi duk suka juya Aliyu ya shigo parlorn Baby ta kallesa tace "Yayanmu sannu da xuwa" ya karaso parlor ya ajiye makullin motarsa saman table ya xauna tare da jinginar da kansa da kujera yace "Ya school, yau ba islamiyya sai kallo koh" baby bata ce komai ba ta kai fork dake dauke da taliya bakinta, ya kalli TV yace "Wa ya kashe television din" Baby ta nuna masa khadijah tace "Ko ba ita bace take kallon cartoon din da nasa, tell her to get away" kwace remote din yyi ya kunna tvn yana hararanta, Tayi shiru bata ce komai ba, yace "Wawiya kawai" daga haka ya mike yyi wucewarsa sama, baby ta hade kai da gwiwa xata yi kuka, juyawa khadijah tayi ta wuce kitchen, su Siyama suka bi ta da harara. Khadijah na ta tsaye kitchen tana kallon naman da kyauta ta daura yana ta soyuwa a cikin mai kyauta kuma na can waje, jin an shigo kitchen din ta juya da sauri taga Aliyu ne, cup ya dauka ba tare da ya kalleta ba yace "Have you eaten?" Kai ta gyada masa ita ma bata kallesa ba, sai ga kyauta ta shigo kitchen din, ganin Aliyu tayi saurin cewa "Sannu da xuwa yallabai, in kai maka abinci" ya juya ya nufi kofa yace "A'a nagode" khadijah tayi narai narai da ido tace "Wallahi anty mai girki ni ban kulasa ba shi ne yyi mun magana ki tambayesa ma ki ji" da sauri kyauta ta tura kofar kitchen din ta rufe ta daura hannu a ka tana xaro ido tace "Na shiga uku ni kyautar Allah, yanxu 'yar nan me nace maki xaki ja min salalan tsiya?" Khadijah tayi shiru tana kallonta, kyauta ta bude kofar kitchen din ta turata waje tace "Tafi ki ban waje ni dai" turo baki tayi ta juyo taga Aliyu xaune parlor da baby dake sulking har lkcn, ta wuce daki tana ci gaba da turo baki. Da daddare khadijah ta fito wanka tana daure da xanin da kyauta ta bata ta dinga wanka, kyautar kuma na tsaftace kitchen aka bude kofar dakin, Anty khadijah ce ta shigo baby na biye da ita a baya, kana ganin Khadijah kasan ba karamin tsorata tayi ba ganinta, Anty khadijah ta riko duk hannayenta biyu da hannu daya fuskarta kamar bai taba ganin ruwan alwala ba tace "Don kaza kazan ki kinsan matsayin yarinyar nan a gidan nan?" Ta fada hakan tana nuna mata baby, Khadijah da ta gama tsorata gaba daya cikin rawar murya tace "Anty kiyi hakuri" mari Anty khadijah ta sauke mata, lkci daya tayi saurin daura hannunta a lebbenta alamar kar tayi kara, hawaye ya shiga sakko mata ta dinga girgixa mata kai, kalle kallen dakin Anty khadijah ta dinga yi ko xata samu wayar wuta amma bbu, hakan yasa ta kuma kai mata wani mari, Cikin kuka khadijah tace "Anty don Allah kiyi hakuri ban mata komai ba" da hannu Anty khadijah ta dinga dukan bare skin dinta tana mintsilinta ta ko ina tana cewa "Toh wllh ko kallon baby kika sake yi a bisa kuskure cikin gidan nan sai na sumar da ke shegiya balle ki mata kallon banxa, gayyar tsiya arna a idi, kuma daga yau kika sake tsayawa cikin parlor ba kitchen ba koh cikin dakin nan sai na kashe ki in kashe banxa" wani Marin tayi mata ta rankwasheta ta hankadeta sannan ta kama hannun baby suka nufi kofa tana cewa "Banda Anty fati hau ya fada mata ina ita ina dinga yi ma shegun mutane abinda take yi yanxu, ai sai dai idan bana gidan nan amma duk sai na sa an sallameki har tsinanniyar kyautar, ni kadai raina ma xan iya aikin gidan nan gaba daya idan Allah ya yarda, shegu kwadayayyu yan maula" Kuka kawai khadijah take har da shessheka rabonta da irin wannan kukan tun tana gidan kawunta, fita tayi dakin ta wuce kitchen gun kyauta tana kuka sosai, nan taga kyauta bata kitchen ta bude kofa ta fita can gun da kyauta ke cewa ta xauna ta xauna nan ta dinga kuka kamar ranta xai fita, Aliyu ya mike daga xaunen da yake yana aiki a laptop ya leka kasa, juyawa yyi ya bude kofa ya fita, tsaye yyi kanta yana kallonta, ganinsa ta hade kai da gwiwa tana ci gaba da kukanta, ya durkusa yace "What happened?" Dagowa tayi tana kallonsa amma ta kasa cewa komai saboda kukan da ya ci karfinta, yyi shiru bai ce komai ba, ya kyaleta don kanta ta daina kukan a hankali sai ajiyar xuciya da take, yace "Me aka maki?" Cikin rawar murya ta nuna masa cikin gidan wasu hawayen na sakko mata tace "Wannan Antyn nan ce ta min duka" shiru yyi yana kallon tafin hannun dake kwance saman fuskarta da yyi ja, yace "Wace Anty?" Kasa cewa komai tayi saboda wani sabon kuka da ya taho mata, yace "Don't cry again, ki fada min wace Anty ce ta doke ki" ta buda masa hannu muryarta na rawa tace "Ban san sunanta ba" Fiddo wayarsa yyi a aljihu ya shiga gallery ya nuna mata hoton kusan yan gidan gaba daya yace "Wacce a ciki?" Ta goge hawayen idonta tana kallon hoton da yake nuna mata da kyau, a hankali tace "The one wearing blue" sake kallon hoton yyi yaga Anty khadijah ce, yace "Me kika mata" wasu sabon hawayen suka taho mata tace "May be wannan yarinyar ce tace mata ina kallo a parlor....." yace "wacce yarinya?" Shiru ta yi bata ce komai ba hawaye na taruwa idonta, Ya sake shiga gallery ya nuna mata hoton daxu ta nuna masa baby, dauke kai yyi bai ce komai ba can ya kalleta yace "Toh ina kayan ki?" A hankali tace "I just took my bath shine ta shigo daki" rushewa ta kuma yi da kuka yace "Don't cry, ki jira ni a nan" daga haka ya mike ya wuce ciki, ba a wani dau lkci ba ya dawo rike da hannun baby dake kallonsa a tsorace,

Please Login or Register in order to submit comment