Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ba naka bane, ba kai ka haifar min su ba, you don't have any right over them, idan duk duniyar nan xa su hade nan wlh wllh baxan baka su ba, ni na sha wahalan kayana ni na haife su, baka isa ka raba ni da su" ta fashe da matsanancin kuka xuciyarta na mata xafi, hakan yasa su shureim ma suka fara kuka suna rike da ita, kallonta kawai Aliyu yake da idanuwansa da suka yi jajir, ganin khaleel ya bar wajen khadijah ta kama hannun yan biyun ta da sauri ta juya xata bi bayansa Aliyu ya fixgota yayi jamming kofar yana mata wani mugun kallo, lkci daya ta cakumosa tana kuka mai taba xuciya tace "Ka bude mana mu fita Aliyu, ka bude kofar in fita da yarana kar in tara maka jama'a" yanda ta rikice haka yaranta ma suka rikice suna kuka, daukar ta Aliyu yyi ya nufi bathroom dake ward din ya tura ta ciki yace "I will teach you sense Khadijah...." daga haka ya rufe kofar da makulli ta dinga bubbuga kofar a rude tana kuka tana kiran sunansa, Sudais ya kara fashewa da matsanancin kuka yace "Why are you doing this to our Anty, plss let her out" Shureim ya dinga bubbuga kofar shi ma yana kuka yana kiran ta, Aliyu ya hade kansa da bango ya runtse ido xuciyarsa na bugawa, lkci daya ya juyo ya kama hannun yaran gaba daya suna turturjewa ya watsa masu wani mugun kallo da idanuwansa da suka yi ja, ba shiru suka yi tsit ko wanne a tsorace, ya bude kofar ward din ya fita da su, ward na intensive care ya shigar da yaran tunawa da yayi bai taho da motar clinic din ba, banda kuka babu abinda suke yi suna kallonsa a tsorace, fuskarsa daure yace "I don't want to hear any of you cry again" shiru suka yi sudais ya riko hannunsa yace "plss bring out our Anty from the toilet" sauke idonsa kasa yyi a hankali yace "Ohk i will do that now" daga haka ya fita ya rufe kofar yanda baxa su bude ba, sama ya wuce da sauri ya shiga office din Muktar ya dau makullin motarsa sannan ya sauko, yana bude kofa su sudais suka yi tsit daga kukan da suke, Shureim yace "Uncle where is she plss" hannunsu ya kama ya fita da su, ya bi ta bayan asibitin xuwa parking space, back seat ya saka yaran gaba daya sannan ya shiga driver seat ya tada motar ya bar asibitin. K'asa kuka twins din suka yi a motar saboda Aliyu da ya hade rai, kana ganinsu kasan a tsorace suke barin Shureim, driving kawai yake har ya iso gida bayan yyi parking ya fito ya bude masa motar yace "Come down" da farko kin sakko suka yi, ganin kallon da yake masu duk suka fito, Shureim na goge idonsa cikin rawar murya yace "I thought you where a good friend, plss don't kidnap us away from our Anty, she will be sad" Duk da hawayen da ya taru idon Aliyu hakan bai hanasa durkusawa gabansu ba ya rungume su gaba daya yace "I didn't kidnap my kids, I brought you two to ur Granny" Sudais ya xaro ido yace "We left her at d hospital and this is not our home" Aliyu na kallonsu cikin sanyin murya yace "This is your father's home" A tare suka hada baki gun ce masa "Where is he?" Shiru Aliyu yyi yana kallon handsome boys din, sudais yace yace "Anty told us our father... Is a Barrister, she said he travelled immediately we where born and that... he will come to us one day" Jikin Aliyu yyi mugun sanyi yana kallonsu, Shureim yace "We will love to see our dad" mikewa Aliyu yyi ya kama hannunsu ya wuce cikin gida da su. Sudais ya bata fuska kamar xai yi kuka yace "I thought you are taking us back to our Anty" gaba daya yan gidan na parlor xaune ana jajanta abinda Kyauta ta ma Anty khadijah, saleem sai cewa yake da ma da shi aka je ya lallasata ya cire mata hakora ya ga wanda ya tsaya mata, mumy dai bata ce komai ba sai kallon Anty khadijah dake kwance kasa take duk jiki yyi tsami don ma ta gasa jikin da ruwan xafi, baki a kumbure har da ido, iklima ma an sallamota tana sama a kwance, gaba daya occupant din parlorn suka dinga kallon Aliyu da twins din hannunsa, Anty khadijah ta mike xaune da sauri ita ma tana kallonsu, Baby ta mike da mugun mamaki tana kallon yaran tace "Laah yaran da muka gani a kasuwa daxu, yaya where did u knw dem from, mai ya samu kan wannan" Aliyu ya isa har gaban Mumy dake kallon yaran ya sake hannunsa, a sanyaye yake kallonta, yyi gathering courage da kyar yace "Yaran da Iman ta haifa kenan, she got pregnant after the incident" Ba Anty khadijah kadai ba har Mumy sai da ta girgixa ta mike tana kallon yaran dake ta kallonta sannan ta mayar da dubanta kan Aliyu cikin wani yanayi tace "How did you knw Abuturrab, where did you get dem from???" hawaye suka shiga sakko masa yana kallon mahaifiyar tasa a sanyaye yace "I met them today mum, I don't knw if Khadijah will ever forgive me... I ruin her at a very tender age, this boys are my blood, Mumy na kawo su gida ne don nima in yi facing ko da kadan ne daga cikin abinda tayi facing a rayuwarta duk da ni na fita ga ta...." Kasa ci gaba yyi ya bar parlorn ya wuce sama hawaye na sakko masa, Anty khadijah dake ta xufa ga cikinta da ya tsure tace "Mun shiga uku, Anty fati kin ga wani sharri koh, kin ga wani hauka irin na Aliyu ko? yaushe Aliyu ya isa haifan wa ennan yaran? ta je an mata ciki a wani waje ta makala masa kuma ya yarda saboda wawa ne shi... a ina ma ya ganta???" Kai kana gani kasan kame kame kawai take duk ta rude, Su Shureim sai bin kowa na parlorn suke da kallo a tsorace, baby ta fashe da kuka cike da tausayin yayanta, Salim ma sai kallon yaran yake a duk jikinsa yyi sanyi ganin kamannin Aliyu sak tare da su, Mumy ta fashe da kuka sosai ita ma tana kallon yaran, hakan yasa su ma suka fashe da kuka, babu abinda take gani tare da yan biyun sai Aliyunta lkcn da yake kamar su, Anty khadijah ta haura sama kusan a guje tana cewa "Yau na ga abinda ya isheni bai ishi Allah ba, ina yake ya xo ya fitar mana da shegun nan da ake shirin kakaba masa, ya xo ya mayar da su inda aka basa su, amma Allah ya isa tsakaninmu da yarinyar nan, ta rasa wanda xata ma sharri sai Aliyu saboda tsautsayi ya gifta tsakaninsu? Ni dai nasan da hankalin Aliyu baxai mata fyade ba, sharrin shaidan kawai da kuma sharrin ta don ita ke shisshige masa, wlh baxa mu amshi shegu gidan nan ba, kaf xuri'ar mu ba a taba haka ba baxa a fara a kan d'an yayata ba" tana wucewa sama mumy na share hawayenta ta kama hannun yan biyun ta wuce sama xuwa dakinta da su. Wata nurse ce ta shigo dakin ba ma sudais allura ta ga babu kowa dakin sai kofar bayi da ake ta bubbugawa ta isa da sauri ta bude kofar da mamaki ganin key aka sa ta waje, khadijah ta fito tana bin dakin da kallo ganin ba kowa ta riko nurse din a rikice tace "Na shiga uku nurse ina yarana? Where are they plss" nurse na kallonta da confusion tace "Yanxun nan na shigo madam" da gudu khadijah ta fita xuwa ward din da aka kwantar da ita, ta ga Umma ce xaune sai Nanny da khaleel dake tsaye ya jingina da bango idonsa a kan wayar hannunsa, ta fashe da matsanancin kuka ta xube wajen tace "Wayyo Umma na shiga uku ya tafi min da yarana" khaleel ya iso gabanta da sauri da mamaki yace "Ya tafi da su ina? Kina kallonsa ya tafi da su" ficewa yyi ward din da sauri, Umma da ta gigice tace "Wa ye ya tafi da su Khadijah, waye shi" Khadijah ta riko Umma tana kuka sosai tace "Umma Aliyu, ya tafi da yaran, ya wuce min da yarana" a sanyaye Umma ke kallonta, Nanny ta bi bayan khaleel da sauri tana cewa "Me ya kawo sa asibitin, mun shiga uku" umma ta dago Khadbijah ta rungumeta, cikin rawar murya take cewa "Umma kar ku bari ya raba ni da su, baxan iya rabuwa da su ba, don Allah a taimake ni a karbo min yarana ni na yafe masa duniya da lahira ya bar min yaran, wllh na yafe masa har cikin xuciyata amma yayi hakuri ya ba ni yarana" tana kai wa nan ta kara fashewa da matsanancin kuka tana kiran Umma, hawaye ya shiga sakko ma umma ta rasa abinda xata ce ma 'yar tata.

Direct office din Dr Abdul khaleel ya wuce, ya samesa xaune yana aiki, ganin khaleel ya bar abinda yake yi yace "He is improving ko Dr" khaleel bai tanka sa ba isa gabansa ya dafa table yana kallonsa bbu yabo bbu fallasa yace "Dr Aliyu.... Where is his home?" Dr Abdul yace "Aliyu? Ba yana office ba?" Khaleel yace "Baya nan" da mamaki Abdul yace "Hope babu matsala dai?" A takaice Khaleel yace "Babu, ina gidansu yake" Abdul yace "Toh, he is not the type that mingle gaskiya I dont knw his home" juyawa Khaleel yyi ya fice office din, direct parking space ya nufa ya hau motarsa ya wuce gidan Farouq. Umma ta dinga kwantar ma khadijah hankali duk da taki saurarenta, daga karshe Umma ta fita ta biya bill dinsu don bata ga amfanin xaman asibitin ba, na khadijah kadai suka karba ban da na sudais kamar yanda Aliyu yyi instructing din su, da kafa suka fita asibitin don Umma bata xo da mota ba, suna isa bakin titi ta tsayar masu da abun hawa suka wuce gida. Girgixa kai Farouq yyi yana kallon Khaleel yace "Ni fa ba ruwana, kamar yanda na ki ba sa address din ka, to kai ma baxan baka address din sa ba gaskiya, ku kuka san abinda ya hada ku can.." Wani kallo khaleel ke masa kafin ya mike ya fice daga gidan ya shiga motarsa ya wuce, yana driving ya dau wayarsa ya fara kiran Khadijah, har ya katse bata dauka ba, nan ko tana zaune ita kadai daki tayi kukan har ta ji ba dadi, Umma kuma na parlor da Nanny sun yi jigum, Umma ta rasa ta ina xata fara yanxu ta ina xa su fara xuwa neman yara, Jin wayar ya sake ring Khadijah ta daga da kyar ta kai kunne, jin muryar ta jikin khaleel yyi sanyi, a hankali yace "Plss ki kwantar da hankalin ki Khadijah, xa a amsar maki kids din ki, he have no right over them, in sha Allah we will get back ur kids" kasa cewa komai tayi tana share hawayen da ke xubo mata, yace "Kin san address din can gidansu?" Shiru tayi kafin ta girgixa kai cikin sanyin murya tace "Na manta" yace "Amma xa ki gane gidan?" Nan ma ta d'an yi shiru, anya xata gane gidan yanxu kuwa, murya can kasa yace "Khadijah?" Tace "Kilan in gane" yace "Good, kuna clinic din har yanxu?" Ta girgixa kai tace "Mun dawo gida" yace "Toh xan taho yanxu, but promise me baxa ki sake kuka ba plss" a hankali tace "Toh baxan yi ba" yace "Good, ina tahowa yanxu" daga haka ya katse wayar, Sosai Khadijah ta ji hankalinta ya kwanta, ta ji ta samu natsuwa. Tun da Aliyu ya shiga dakinsa bai sake fitowa ba, Mumy da maganganun Anty khadijah suka fara sa mata ciwon kai ta daga kai tana kallonta a karo na farko tun shigowarta dakin, ban da kumfar baki kamar wata xararriya babu abinda take tana nuna yan biyun dake xaune kan gadon Mumy, suma yaran kallonta kawai suke a tsorace, Baby ma na tsaye sai hararan Anty khadijah take tana tabe baki, Mumy ta dakatar da ita a tsawace tace "Khadijah ki fita ki ban waje don Allah ki bar ni in ji da guda daya, ciwon kai kike kara min ki fita don Allah, ko makaho ya shafa yaran nan yasan na waye, Baxa ayi DNA din ba...." Anty khadijah da idanuwanta suka kankance da mugun mamaki tace "Anty fati ni kike cewa in fita in baki waje don ina nuna damuwa ta kan shegun da aka makala ma Aliyu aka ce nasa ne, Ni Anty fati??" Mumy tace "Ehh ki fita nace" tayi wani murmushi tace "Xan fita yanxu kuwa" daga haka ta fice daga dakin kamar xata tashi sama, Mumy ta kalli yan biyun dake bata tausayi har ranta, a hankali tace "Me xa ku ci?" Sudais dai bai ce komai ba, Shureim ya girgixa mata kai shi ma bai ce komai ba, karasowa tayi ta xauna gun yaran tana kallonsu, wani sonsu take ji a xuciyarta, ta d'an yi murmushi tace "Ayi maku noodles and egg?" komawa Sudais yyi ya kwanta ta kai hannu jikinsa taji xafi sosai, kallon baby tayi tace "Xaxxabi ne jikinsa fa sosai..." Baby ta karaso ita ma ta taba yaron taji xafin jikin ta kalli Mumy tace "Mumy ko in kira yaya?" Mumy tace "Kira sa" juyawa tayi ta fita, ita ta fara dawowa dakin sannan Aliyu ma ya shigo, kallon yaron yake har ya isa kan gadon ya taba jikinsa, dago sa yyi ya xaunar da shi, yana kallonsa yace "Are you feeling pain anywhere?" Sudais ya nuna masa kan sa, kamar xai yi kuka yace "I want to go to my Anty plss" Aliyu ya lumshe ido ya bude a hankali yace "Ohk I will take you there" Mumy dake kallon Aliyu tace "Ina ita khadijahr take?" Kamar Aliyu baxae ce komai ba, sai kuma ya shafa kansa murya can kasa yace "Bayan ta bani su tayi tafiyarta" wani kallo Mumy ke masa ganin yanda yyi maganar, can ta girgixa kai tace "Karya kake..." Da sauri ya kalleta, sai kuma ya marairaice yace "Mumy bata sani ba na taho da su, idan ta sani baxa ta bani su ba" Bude baki Mumy tayi tana kallonsa, da damuwa tace "Me yasa xaka yi haka Aliyu, me yasa xaka raba su da uwar su...." Kasa cewa komai yayi, Mumy da duk jikinta ya kara yin sanyi tace "Aliyu tell me how everything happened, garin yaya kayi ma yar mutane haka, where was I that day? kar ka boye min komai plss, tell me the truth...." kallon Mumy Kawai yake ko kiftawa babu, can ya xauna gefen gado ya rike kansa yana jin kamar ya fara mata hawaye, bai son tuna mummunar ranan nan a rayuwarsa, Mumy na kallon Baby tace "Baby xo ki tafi da su ki dafa masu indomie ki basu, shi wannan ki kai sa dakin ki ya kwanta" Baby ta karaso ta sakko da boys din daga kan gado ta wuce da su dakinta, Mumy na kallonsa tace "Ina ji Aliyu" Da kamar baxai ce komai ba, sai kuma a hankali ya fara magana, "Mumy ni dai nasan I woke up fine that very day...." Ya d'an yi shiru, nan ya fara ba ma Mumy labarin abinda ya faru ranan bai boye mata komai ba har yanda bayan kwana biyu ya ba ma khadijah kudi me yawa yace ta wuce gun ummarta, hawaye kawai Mumy ke yi tana kallonsa a sanyaye, bai iya ya dago kai ba shi ma hawayen na sakko masa cike da karfin hali yace "Mumy nayi abinda nayi ne out of confusion, I was confused, ban taba xaton xan aikata ma khadijah haka ba, bayan tafiyar ta ku shaida ne, nayi bankwana da kwanciyar hankali da farin ciki na, I never had rest of mind again kuma na kasa gaya maki abinda ya faru ban san ya xa ki dau xancen ba, shi yasa a ko da yaushe nake ce maki ki taya ni da addu'a, wani lkcn idan na kwanta bacci ita kawai nake gani, kuma it's not as if nasan da cikin bane, kawai ni dai nasan ban kyauta mata ba saboda marainiya ce bata da kowa, ban san ta Inda xan fara nemanta ba don ban san kowa nata ba, da babu abinda xai hanani nemanta Mumy, idan baki manta ba akwai wani lkci da na taba tambayar ki ko kina da number warce ta kawo ta kika ce baki da shi, ni ban sa ko Khadijah xata yafe min ba and it looks as if I don't deserve that.... Amma abinda ke bani mamaki har yanxu shine yanda aka yi Anty khadijah ta san abinda ya faru bayan bata gidan kuma ita ta fita tare da su baby a ranan, gidan ya rage daga ni sai Khadijah, sai kuma jiya tana waya a bathroom din dakinta, I overheard all what she was saying on the phone.... Nan ya gaya ma Mumy duk abinda ya ji Anty khadijah ke fada a waya jiya, yana girgixa kai yace "We shud keep on pretending mum, she was so shock da ta gan ni a dakin, but i pretend ban ji komai ba, hakan kuma ya sa hankalinta ya kwanta, a sannu abinda take yi xai bayyana a fili tun da ba mu da hakkinta, kuma ina mai tabbatar maki soon komai xai bayyana, ke dai kawai ki ci gaba da sa mata ido, xan dai sa su Sanusi su tone bayan gidan to check what she was talking about on phone" Mumy ta dinga kallonsa ko kiftawa babu cike da shock, ya goge idonsa har lkcn bai kalleta ba yace "And... Mumy kilan idan ke kika yi ma khadijah magana xata iya yafe min, ni ta ki saurarata har yanxu, kuma mumy plss kar ki ce min baxan iya aurenta ba, hakan kadai ne xan iya mata in wanke kaina, I knw I can't pay her all what she passed through, kar ki hana ni aurenta mumy..." Mumy ta sauke ajiyar xuciya har lkcn tana mamakin abinda Aliyu ya fadi mata kan Anty khadijah, she is still finding it hard to believe that, infact bata ma yarda bane tasan Anty khadijah baxata yi abinda Aliyu ke fadi ba, Aliyu yace "Mumy kinyi shiru" Mumy ta kallesa ta kara sauke ajiyar xuciya sannan tace "Idan kuma ita bata son ka fa?" Ya d'an hade rai yace "Toh sai ta bar min yarana taje tayi aurenta shikenan na raba ta da wahala, idan kuma ta yarda ta aureni sai mu xauna mu rike yaranmu, domin kuwa su din abun kyama ne idan ta kai su wani gidan, ko ba yanxu ba wataran xa a kyamace su, to idan muna tare fa? We can never do that to them" Mumy bata kuma cewa komai ba tayi nisa tunanin da take na Anty khadijah, Bude kofar dakin Anty khadijah tayi ta shigo tana kallon Mumy da kumburarrun idonta da ta sha kukan takaici, kallo daya Mumy ta mata ta dauke kai xuciyarta na kara karyata Aliyu, Aliyu kam bai ma kalli inda take ba, tana kallon Mumy tace "Ina son sanin matsayin auren iklima a gidan nan Anty fati, na hada kayana idan Ita ma in hada nata ne toh..." Sai a sannan Aliyu ya kalleta yace "Anty aure ya taba mutuwa ba ayi saki ba?" Hararansa tayi ta juya ta fita, dakin baby ta bude ta dinga kallon yaran dake kan gadon cike da tsana, a tsorace suke kallonta su ma, can ta juya ta fita dakin ta sauka downstairs xuciyar ta na tafarfasa, Baby ce kitchen tana bare eggs da ta dafa masu indomien na kan wuta, Anty khadijah ce ta shigo kitchen din ta dau cup ta xuba ruwan xafi daga flask, Baby ta kalleta ganin yanda ta tsaya tana tunani, da sauri Anty khadijah ta bude gun da madara suke ta fiddo kayan tea ganin kallon da baby ke mata, tana hada shayi tace "Baby ina wani sarka da na baki ki ajiye min ranan da aka yi bikin iklima a gidan nan?" Baby tace "Anty yana cikin jakata a daki" Anty khadijah tace "Je dauko min kayana" Baby tace "Yanxu Anty?" Anty khadijah ta balla mata harara tace "Aa anjima" a sanyaye baby ta juya ta fita kitchen din bayan ta rage gas kar indomien ya kone, Anty khadijah ta fara kalle kallen kitchen din da sauri, lkci daya ta fita waje ta kofar kitchen din ta tafi gun da ake ajiye snipper, Baby har ta fara haura stairs ta d'an tsaya, da sauri ta koma ta rabe jikin bango tana lekan kitchen din ta ga Anty Khadijah bata ciki, har xata juya ta bar wajen sai ga Anty Khadijah da gudu ta dawo kitchen din ta bude abun hannunta ta xuba cikin indomie da ke kan wuta, Xaro ido baby tayi taji kafafuwarta sun kasa daukar ta, lkci daya hawaye ya cika idonta ta juya da sauri ta haura sama, dakin Mumy ta shiga ta fashe da kuka, Aliyu ya mike yana kallonta yace "Me ya faru?"

Baby ta durkushe dakin tana kuka sosai tace "Mumy Anty Khadijah ce na ga tana xuba snipper a cikin indomien yaran da nake dafawa" Aliyu ya xaro ido yace "Snipper??" Da sauri ya nufi kofa mumy tayi maxa ta dakatar da shi, ya juyo hankali tashe yana kallonta, Mumy na kallon Baby tace "Ta gan ki?" Girgixa kai baby tayi tana hawaye, Mumy ta hadiye abu da kyar, cike da karfin hali tace "Je ki dauko yaran ki kawo su nan, kar ki ce mata komai" Aliyu sai kallon mumy yake xuciyarsa na bugawa, Mumy ta kallesa tana kkrin goge hawayen idonta tace "Kar ka ce mata komai, let pretend we don't knw... Don't say anything Aliyu" Baby ta dawo dakin da su sudais mumy ta daura su kan gadon tana kallonsu a sanyaye, ta dubi Baby tace "Tafi ki xubar da indomie din, kar ki ce mata komai kin ji, ae basu da hakkinta don hka bbu abinda ta isa tayi masu wanda Allah bai masu ba" Baby ta fita dakin a sanyaye hawaye ya ko tsaya mata, ganin abun take kamar a movie, ynxu da bata dawo ba haka xata dau indomien ta ba yaran su ci su mutu?? Anya Anty khadijah na da conscience kuwa, me yan yaran suka mata, Aliyu kam ya kasa cewa komai, Mumy ta dinga share hawayen dake ta xubo mata, me tayi ma khadijah ta mayar mata da family dinta haka, dama laifi ne idan ka jawo naka ya xauna tare da kai?? Baby bata ko kalli Anty khadijah da ta xauna parlor tana shan shayi ba ta shiga kitchen din, Anty khadijah ta bi ta da kallo ta gefen ido, daukar indomie da kwan baby tayi ta fita ta xubar cikin shara ta tara tukunyar a bakin tap, sai da ta tabbatar ta wanke tas sannan ta dawo kitchen da shi ta ajiye ta fito kitchen din ta wuce stairs, Anty khadijah ta bi ta da kallo baki bude, da sauri tace "Ke wai sai indomien ya kone ne kin bar ma mutane gas yana ci" Ba tare da baby ta juyo ba balle ta kalleta tace "Sun ce baxa su ci ba na xubar" Daga haka ta haura sama Anty khadijah ta mike baki bude tana kallonta gabanta na faduwa, da sauri ta wuce kitchen ganin tukunyar a wanke ta fita waje ta leka bola taga indomien an xubar, still tayi a gun xuciyarta na mugun bugawa, kar dai ta ganta ne.... Jiki a sanyaye ta dawo cikin gidan tana adduar Allah yasa dai ko ta ganta kar ta gaya ma Mumy, Mumy da kanta ta sakko ta shiga kitchen din da ruwan gora biyu a hannunta, ta

Please Login or Register in order to submit comment