Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da xuwa" juyawa Umma tayi ta fita ta koma kitchen ta daura girkin tuwo a gas, ko da Umma ta koma parlornta dauko maggi bacci ta tarda Khadijah na yi kan kujera, ta tasheta ta shiga daki ta hau gado, abu daya yasa ta jin hankalinta ya kwanta game da Khadijah, kuma shine yanayin da ta ganta, kowa ya ganta yasan bata tare da wahala sai dai 'yar ramar da tayi. Sosai Khadijah tayi kokarin ganin bata kula duk yaran gidan ba kamar yanda Umma ta yi mata huduba duk da irin cakalarta da suke yi a satin ta daya a gidan, ita kanta Umma hakuri take da kowa na gidan don kamar warce aka rufe ma baki komai suka mata bata tankawa duk ta yi sanyi kamar ba ita ba, Shafah da Hasana wani mulki na musamman suke xubawa a gidan, sai abinda suka ce ayi ake yi ga ikon bala'i... A can Kaduna kuwa, kamar wasa aka nemi Khadijah a gidan aka rasa har yamma, Mumy da farko ita a tunaninta ko Aliyu ne ya fita da ita don har ta tanadi rashin mutuncin da xata yi masa amma tana kiransa yace mata shi bai fita da ita ba, na hankalinta ya tashi sosai ta dinga tambayar baby ko iklima ta yi mata wani abun ne don Anty khadijah bata nan balle tace ita ce, shi kam Aliyu dama yana tabbatar da Khadijah ta tafi ya wuce clinic, ganin yanda mahaifiyarsa ta ishesa da kiran ba a ga Khadijah ba yasa shi komawa gida, and he tried his best pretending he knws nothing about her disappearance. Islamiyyar da Umma tayi ma khadijah register ta ci gaba da xuwa a kano, abu daya ke damun Umma yanxu a kanta shine irin sanyin da tayi kamar ba lively khadijahr ta ba, sanyin kuma ne yasa ko kadan abinda ake mata a gidan bata kula wa duk da idan ta fita islamiyya tun safe sai yamma take dawowa gidan. Kwanan khadijah talatin da 'yan kai a gidan Umma ne ta fara fito da wani habit na bacci, ko me take yi sai ta fara bacci a kai, islamiyya ma idan taje duk bacci take, hakan yasa wani lkcn bata dadewa xata dawo gida, Umma da abun ya fara isarta ranan ta bar mata kaya ta linke tana shigowa taga tana bacci kan kayan, duka ta kai mata tace "Wai lafiyar ki kuwa Khadijah, wannan wani irin bacci ne?" Khadijah ta farka a firgice tana mitsika ido, Umma ta harareta tace "Tashi ki je kiyi sallah bana ma son linkin kuma, wani iskanci komai aka sa ki sai ki buge da bacci" mikewa khadijah tayi a hankali ta fita bayan ta dau butan Umma, Hasana dake tsakar gida ta cika gidan da radionta Shafah kuma na kitchen suka bita da harara a tare, babu abinda ke kona masu rai a gidan irin yanda Umma da khadijah ke kin kulasu a gidan, duk da ita Umma sun san ba banxa ba rashin kulawar, to ita khadijah fa, Hasana tace "Ohh daga Hutu dai sai kuma aka rashe" Shafah dake juya miyar ta na yakuwa dake kan wuta tace "Ke ma dai kya gani, dama yau nake son tambayar Alhaji dalilin da yasa xa a munafurce mu ayi mana karya, ai sai ace mana ta dawo nan din ne da xama ba wai a mayar da mu yara ba" Hasana tace "Yara ko dai shashashai, bari dai ya dawo din ma ji dalilin rainin hankalin" Khadijah dake durkushe kasa sai yamutse fuska take ta dalilin kamshin miyar Shafah da ya kauraye tsakar gidan, mikewa tayi da sauri jin cikinta na hautsinewa ta juya xata koma parlorn Umma taji amai ya taho mata, dawowa tayi ta durkushe wajen ta dinga kwarara amai Shafah da Hasana aka yi tsit daga mita da habaicin da suke suna kallonta.

Fitowa Umma tayi da sauri jin kakarin aman khadijah, ta karaso da ita ta duka tace "Subhanallahi.... Are you okay" khadijah ta kasa cewa komai duk ta galabaita lkci daya, Umma ta taimaka mata ta wanke baki sannan ta dagota ta wuce parlorn ta da ita, Khadijah ta kwanta kan kujera tana mayar da numfashi da kyar tace "Umma I don't knw what's wrong with me, I am always week" Umma tace "Sannu, ko malaria ne, bari Alhaji ya dawo sai mu tafi asibiti ni bani da kudi a gu na" Khadijah ta lumshe ido har lkcn tana sauke ajiyar xuciya, mikewa Umma tayi ta fita don wanke gun aman, tana isa bakin kofa ta ji muryar Hasana tana cewa "Wllh fah, sai kace mai ciki, ji fa salon aman ma daban ne, idan ma malaria ne ba yellow shataf kalan aman ya kamata ya xama ba" Shafah tace "Haka fa shekaranjiya ina lura da ta shiga kitchen duba mata girki daga xama kan kujera sai bacci, daxu kuma da safe nan bakin kofa ta xauna da abinci a gabanta tayi bacci, ace baccin nan ba lafiya ne?" Umma dake tsaye bakin kofa har lkcn gabanta yyi mugun faduwa, fita tayi parlornta a fusace duk da ta fi wata uku bata tanka su a gidan tace "Sai dai ku ga ciki can kan 'ya yanku ko dangi, amma ba 'ya ta ba, tunda baku da kirki baku da Imani har ku yi ma yar mutum fatan wannan mugun abun, Allah ya isa wllh" Hawaye cike idonta ta kare maganar, Shafah ta mike tana huci ta kunduma mata xagi tace "Bakin ki ya sari danyen kashi, ba ma ga mugun abu ba a 'ya ya ko dangi, to wa yasan inda kika kai ta kwanki ko karuwanci kika sa tayi maki...." Umma ta juya ta koma daki hawaye na sakko mata sosai, kallon khadijah ta tsaya yi taga har tayi bacci, ta xauna duk jikinta a sanyaye a xuciyarta tana kara yi ma su Shafah Allah ya mayar masu mugun alkaba'in da suka yi ma 'yar ta. Har karfe tara Khadijah na bacci bata tashi ba, tada ta umma tayi hankalinta ya tashi jin irin xafin da jikinta ya dauka, da kyar ta lallabata ta sha shayi kadan sannan ta bata paracetamol ta rakata bedroom dinta ta kwanta ita ta dawo parlor ta xauna har lkcn xuciyarta ya kasa dawowa dai dai, khadijah ce ta fito da sauri daga dakin umma na tambayarta me ya faru amma ta fita waje tun kan ta karasa can gun kwararon ruwa ta dinga amai a tsakar gidan, Umma da ta bi bayanta ta tsaya tana kallonta, jin sound din aman yasa Hasana ta leko sai ga Shafah ma ta leko, Umma ta koma ta dauko buta, ta durkusa kusa da ita har ta gama sannan ta wanke mata baki suka koma ciki, sai shivering take cikin rawar murya tace "Umma ki rufe ni sanyin" Umma ta dauko duvet da sauri ta rufe ta, nan da nan kuma bacci ya dauketa. Umma ta koma parlor ta xauna duk ta rasa me ke damunta, jin shigowar Abban fadila gidan ta jira har ya shiga part dinsa da minti sha biyar sannan ta fita, sallama tayi bakin parlornsa ya amsa ta shiga, Shafah ce a parlorn tana xuba masa abinci shi kuma yana kallon news, Umma ta xauna ta gaishesa ya amsa, a hankali tace "Alhaji dama idan da hali don Allah kudi nake so ka ba mu xan kai khadijah asibiti bata da lafiya tun safe" Shafah tace "Ae gwara aje asibitin nan kam wannan amai da bacci haka a gida" Umma tayi shiru tana kallonta, Abban fadila yace "Nawa ne kudin asibitin?" Shafah tace "Tun da ya sanka likitan kamar family Dr ne ko dubu 3 ka basu xai yi ai" ita dai Umma bata ce komai ba, Ya mike ya shiga ciki sai ga shi ya fito da dubu hudu ya mika mata yace "Gashi sai ku yi har kudin mota" ta karba da ladabi tace "Toh mun gode sai da safe" daga haka ta mike ta bar parlorn. Washegari da sassafe Umma ta sa Khadijah ta shirya bayan ta tilasta ta shan shayin da ta hada mata amma tas ta amaye sa gaba daya, duk ta xabge tayi laushi lkci daya sbda aman da take yi, A dai dai ta umma ta samo masu har kofar gida ganin kamar baxata iya tafiyar ba ma, Hasana dake sharar tsakar gida tace "Toh a dawo lafiya dai, Allah raba bawa da jin kunyan duniya da lahira dai" Umma bata tanka ta ba tana rike da Khadijah suka fita, wani asibitin daban ba wanda suka saba xuwa Umma taje ba, suna xuwa aka ce sai sun yanki kati dubu biyu, duk jikin umma yyi sanyi, shiru khadijah dake xaune tayi tana kallon nurse din dake tsaye Kansu, nan ko tuna kudin da Aliyu ya bata take yana bayan kujeran umma ta ajiye bata kuma nuna ma umman ba har lkcn, Umma ta mike tace ma nurse din tana xuwa yanxu, Cike da karfin hali Khadijah tace "Umma ina xa ki?" Tace "Yanxun nan xan dawo khadijah" daga haka ta fita. Gidan wata kawarta dake layin ta tafi ta ranto dubu biyu da yake suna mutunci da matar sosai ta bata sannan umma ta dawo asibiti, bayan an yankar masu kati suka samu ganin likita, Umma ce ke fadin abubuwan da ke damun khadijah ma likitan, don Khadijahr duk tayi weak, tambayar farko da likitan ya jefo ma Umma shine "Tana da aure ne?" Gaban umma yyi mugun faduwa ta girgixa ma likitan kai kawai, likitan yace "Toh xa ayi mata test..." Bai dai fadi wanne ba umma tace "Toh" ya kira nurse ya bata file din nasu yace su bita, Umma na rike da hannun khadijah suka dawo reception, Nurse din tace kudin test din dubu biyu da dari biyar haka Umma ta bata duk ta yi wani sanyi, suna ta xaune a reception har bayan mintuna da dama result ya fito matar ta ce su je office din Dr bayan ta kai ma sa, Likitan dake ta kallon umma yace "Yar ki ce yarinyar nan?" Umma ta gyada masa kai xuciyarta na bugawa, ya girgixa kai yace "Sorry madam, She is few weeks pregnant" mikewa Umma tayi a mugun gigice tace "Pregnant Dr?" Likitan ya gyada mata kai, Khadijah da ta xaro ido ta dinga kallon likitan xuciyarta na bugawa, kuka sosai Umma ta saki a gun ta juya ta fita, khadijah ta mike ta bi bayanta da sauri, likitan ya girgixa kai ya bi ta da kallo a ransa yace why Such a beautiful girl, Gaba daya asibitin Umma ta fita har lkcn tana kuka, khadijah da duk jikinta ya mutu ta dinga bin ta ita ma, har lkcn ita dai bata gane wani pregnant din likitan ke nufi ba, adai daita Umma ta hau tayi wucewarta gida, Khadijah da tayi still a inda take ta bi adai daitan da kallo ta kasa kwakkwaran motsi, lkci daya duk ta nemi xaxxabin da rashin kwarin jikin dake tattare da ita ta rasa, har sannan kuma ta kasa kukan, tafiya ta fara yi kamar warce kwai ya fashe ma, da yake ba wani nisa ne da asibitin ba har ta isa gida, Hasana da Shafah na xaune tsakar gida ta wuce parlorn Ummanta suka bi ta da kallo, bata ga Umma a parlor ba a shiga bedroom dinta, xaune ta ganta nan kasan dakin banda kuka babu abinda take, ta sulale kasa a hankali sai a sannan wasu hawaye masu xafi suka dinga sauka idonta, Muryar Umma taji cikin kuka tana cewa "Khadijah yanxu ni xa ki kunyata, ni xa ki yi ma tonon asiri a idon duniya, is this my reward for taking you as a daughter?" Khadijah na shessheka tace "Ummata kiyi hakuri" mikewa Umma tayi da wani force ta sauke mata mari, bata gama recover ba ta kuma kai mata wanda ya fi na da, kasa kwakkwaran motsi khadijah tayi a inda take durkushe lkci daya taji komai ya tsaya mata, Umma na mata wani kallon da xa a iya kiransa da na tsana tace "Kin cuce ni kin ci amanata, kin ci amanar late mahaifinki" hakan da ta fada ya sa khadijah rushewa da kuka mai ban tausayi cikin rawar murya tace "Na shiga uku, don Allah Ummata ki yi hakuri" ta kuma kai mata wani marin tana kuka sosai tace "Uban waye yayi maki Ciki khadijah" kamar numfashinta xai dauke take kuka tana girgixa kai tace "Ban sani ba Ummaa" rufeta tayi da duka har sai da ta gaji don kanta ta kyaleta kuma har lkcn kuka take, cikin raunin murya tace "Tashi ki bar min gidana kije duk Inda xa ki je tunda baki san wanda yyi maki ciki ba, Allah ya isa tsakanina dake khadijah, kin bata min suna, ki tafi khadijah xaman ki gidan nan xai iya kashe min aure ki tafi bana son ganin ki kije duk Inda xa ki" gyada mata kai kawai khadijah take tana sheshsheka, shigowan su Shafah da Hasana dakin yasa Umma tayi shiru har lkcn tana kuka, suka gama kare masu kallo sai suka saki shewa sannan suka fita dakin, khadijah ta mike da kyar don banda ciwo babu abinda ko ina na jikinta ke mata ta fita dakin tana goge jinin bakinta, bayan kujera ta tafi ta dauki envelope din da Aliyu ya bata wasu hawaye masu xafi na xubo mata, xaxxage bundle din kudin tayi gaba daya a kasa sai ga wani farar takarda a linke ya fadi, ta dau takardar ta warware tana kallon content din, *I don't have much to say khadijah, na san har abada baxa ki mance abinda ya faru tsakaninmu ba kamar ynda nima baxan mance ba, tafiyar ki shine ma fi alkhairi sbda baxan taba samun kwanciyar hankali da nutsuwa ba matsawar muna gida daya, ina rokon gafarar ki Khadijah forgive me not because I deserve it but for the sake of Islam, Allah hada fiskokinmu a aljannatul fiddaus, ina maki fatan alkhairi a rayuwa da fatan miji na gari* cukuikuye takardar tayi ta fashe da wani kukan takaici taji dama ta kashe kanta ta huta amma bbu daman yin hakan, mayar da kudin tayi envelope din har ma da takardan ta mike ta fice parlorn tana share hawayen da ya ki tsaya mata, ko kadan bata ji me su Shafah ke cewa ba har ta fice gidan gaba daya, khadijah bata xarce ko ina ba sai tashar mota, tafiya kawai take a park din tana jin sunan garuruwan da ake fadi har ta isa gun motar garin Yobe ta hau bayan minti goma mota ta cika suka dau hanyar damaturu garin da bata san kowa ba bata taba xuwa ba.



*What I want some people to get here is that, wnn labarin khadijah ne, kun riga da kun san rayuwarta a yanxu, she is living a normal life just dat abubuwa da yawa na memory dinta ne har ynxu, what I am writing now is her past ya riga ya wuce so I don't knw why wasun ku ke damun Kansu being emotional, this is not what is happening presently, it's just her past story*

Da tsakar rana Khadijah suka iso garin damaturu, ta fito a hankali daga motar tana bin ko ina na park din da kallo, wani jiri ke dibar ta a lkcn ga sanyin da take ji ba kadan ba, tana tafiya a hankali har ta fita park din, kallon masu adai daitan dake ta tambayata Inda xata ta dinga yi lkci daya hawaye ya cika idonta, bata ce komai ba ta dinga tafiya, bata san iyakar lkcn da ta dauka tana tafiya ba, jin baxa iya ci gaba da tafiyar ba ta samu karkashin wani bishiya da ta hango duk anyi littering dinsa da 6awon rake ta xauna tana sauke numfashi a hankali, cikin Hijab dinta ta ajiye envelope din hannunta, bacci ne ya dauketa lkci daya a hakan saboda iskan da leaves din bishiyar ke ta bayar wa, bata san lkcn da ta dauka tana bacci ba hayaniyar wasu almajirai ya tada ta, ta gyara xamanta da sauri tana kalle kallen wajen envelope dinta a hannunta, a hankali ta tashi da kyar ta ci gaba da tafiya kamar bata son yi kwata kwata ko yunwa bata ji sai kasala, wannan karan ma tafiya me nisa tayi da kafa ganin wani masallaci ta dau buta dake cike da ruwa ta samu gefe ta xauna ta daura alwala sannan ta tafi jikin wani shago tayi sallahn da bata yi ba, mayar da butan tayi ta ci gaba da tafiya, har aka kira magrib tafiya kawai khadijah take, ganinta a wani kasuwa ta dinga xaga kasuwar, a hankali a hankali kasuwar ta fara watsewa ta shimfida dankwalinta gaban wani shago da aka duk aka rufe tayi magrib da isha ta jingina da table din gaban shagon, wasu hawaye suka dinga bin kuncinta, sanyi sosai ke shigarta ga xaxxabi kan kace me kasuwar yyi tsit kowa ya wuce gida, duk da uban sauron da suka yi yawa a wajen hakan bai hana bacci me nauyi sake daukarta daga xaunen da take a gaban shagon ba, bata kuma farka ba sai da kiran sallar asuba ya farkar da ita, ta dinga bin wajen da kallo, can ta tashi da kyar tana tafiya a hankali kamar iska xai hura ta ta fadi ga wani ciwon xuciya da ta tashi da, banda xugi da axaba bbu abinda yake mata, duk wnn abun sai lkcn taji yunwa na damunta sosai, masallaci me hade da na mata take ta nema amma duk iya tafiyar da tayi bata ga alamar ko daya ba, wani wajen ta samu ta xauna nmta hade kai da gwiwa tana kuka cike da rauni, har gari ya waye mutane suka fara hada hadarsu tana xaune Inda take, cike da karfin hali ta tashi ta nufi titi ta tsaya jiran adai daita, bbu bata lkci wani ya ja ya tsaya, ta shiga a hankali nace "Central mosque xaka kai ni" yace "Na ina?" Tace "Wanda ya fi kusa dai" ba wani tafiya me nisa suka yi ba yyi parking bayan mmsun iso kusa da wani babban masallaci, kudin dake jikinta har lkcn ta fiddo ta ciri dubu daya ta basa yace ba shi da canji, a hankali tace "Toh ka tafi" sannan ta shiga masallacin, bangaren mata ta nufa ta daura alwala bayan ta xaga bayi sannan nmta shiga cikin masallacin ta tada sllh, tana ta xaune bayan ta idar tayi nisa tunanin da take jin agogo yyi stucking karfe tara ta mike a hankali ta fita ta dau tsintsiya tana taya bayin Allahn dake ta sharan masallacin shara, suna gamawa ta fito da kudin ta don duba abinda xata siya ta ci, waina da miya ta siya da ruwa ta dawo cikin masallacin, a haraban ta xauna ta bude ledan abincin tana daukan guda ta kai baki taji cikinta ya hautsine, tayi saurin tashi ta nufi gun da ake alwala da gudu nan ta dinga amai a wajen kamar xata shide, da kyar ta tashi daga karshe duk jikinta ba kwari nmta koma cikin masallacin nmta kwanta ba tare da ta sake bin ta kan masan ba, tana mayar da numfashi, dukunkunewa tayi waje daya jin sanyi na shigarta ta ko ina, wanda hakan na da nasaba da xaxxabin da ya rufeta lkci daya, sai azahar ta farka jin ana kiran sllh. Daren ranan a masallacin khadijah ta kwana, amma washegari da safe wata dattijuwa dake share sharen masallaci tace ta nemi gun da xata dinga kwana daga ranan don masallaci ba wajen kwana bane da ace kwana ake barin mutane ke yi a ciki da bai yi kyan gani ba yanxu, cike da fada take maganan, jikin khadijah yyi sanyi sosai ta sunkuyar da kanta bata ce komai ba, karfe sha dayan safiyan ta bar masallacin, duk wanda ya ganta sai ya tausaya mata a lkcn sbda yunwa ce kawai ke dawainiya da ita ga xaxxabi, ramar da tayi ya fito sosai, karfin hali ta dinga yi tana tafiya, tafiya kuma ba na wasa ba tayi ba tare da tasan takamaiman inda xata je ba, ganin she can't move any further don kafafuwarta sun ma Gmgaza daukar ta kuma ta fara tunanin xuwa wani masallacin ta kwanta, tana tsaye bakin titi tana jiran abun hawa da ta gaji sai ta tsugunna idan ta huta sai ta mike, kawai d'aga kai tayi ta ga wata mata da ta shiga titi da nufin tsallakawa wani mota da ya taho da uban gudu ya kwasheta sai da tayi sama da ita snn ta fado kan titin, duk da nesa da ita aka yi hatsarin amma irin ihun da ta fasa a tsorace xaka ce ita motar ta buge tsabar tsoratar da ta yi, daga nan kuma bata sake sanin abinda ya faru ba ta dai bude idonta da yyi mata nauyi ta ganta kwance wani daki da yyi kama da na asibiti da ruwa a hannunta, dafe xuciyarta dake mata xugi sosai tayi ta dinga bin dakin da ido a hankali lkci daya kuma tana son tuno abinda ya faru amma ta kasa, a hankali ta sauke idonta kan wani mutumi dake xaune d'an nesa da ita idanuwansa da hankalinsa gaba daya kan wayar dake hannunsa, duk da a xaune yake hakan bai boye tsayinsa ba, sajen dake kwance gefen fuskarsa kadai take gani da uban gashin da ya tara a kai, da dogon hancinsa duk ta side view take kallonsa, ta shiga kkrin mikewa xaune da kyar har lkcn tana dafe da xuciyarta dake mata axaba ba kadan ba wanda hakan yasa hawaye ya cika idonta, sai a nan ya kallo direction dinta, mikewa yyi da sauri ganin ta tashi ya karaso kusa da ita yace "Hello... how you feeling now?" kallon jajayen lebbensa kawai take don bata taba ganin haka ba, ya buda dara daran idanuwansa yace "Hey... Are you there?" Kin cewa komai tayi still, ya juya ya fita ba a dau lkci ba ya dawo likita na biye da shi, likitan ya tsaya kanta yace "Hi... How you feeling madam?" Ganin yanda duk suka tsura mata ido, ta sauke nata idon a hankali tace "Alhamdulillah" likitan yyi murmushi yace "Maa sha Allah, hope bbu Inda ke maki ciwo ynxu koh?" Ta gyada masa kai duk da axaban da xuciyarta ke ta yi matan, yace "Good" snn ya juya ya fita, kallon mutumin dake tsaye ya rungume hannayensa tayi cikin sanyin murya tace "Me nake yi a nan?" Sai a snn ya kalleta yace "Kar ki damu xa a sallame ki nan da anjima ki wuce gida, before then ki bani number 'yan gidanku a kirasu, sure they are all disturb yanxu, you passed out since in the morning... And this is...." Ta kalli agogo da sauri kafin ya fada taga karfe bakwai, ta kallesa tace "Bakwai na safe?" Ya girgixa kai yace "No, Night" shiru tayi bata sake cewa komai ba kamar me naxari, sai a sannan kuma ta tuno abinda ya faru daxu, ta fashe da matsanancin kuka tace "Wayyo matar ta mutu koh?" Hade rai yyi yace "Nooo, an kai ta asibiti ita ma, am sure she's recovering also" tsoro ne sosai tare da ita tana kallonsa, ya langwabar da kai yace "Ina xuwa" daga haka ya juya ya fita ta bi sa da ido, ko minti biyar bai yi da fita ba sai ga wata nurse da magunguna a leda, ta ajiye kan gado tana mata sannu tace "Idan kin samu abinda kika ci xan dawo in nuna maki dosage" daga haka ta fita. Da sallama ya shigo ward din rike da takeaway din abinci ya karaso ya ajiye kan table dake kusa da gadon yace "Ga shi ki ci abinci ki sha magani kafin a sallame ki...." Bata ce komai ba ya mika mata wayarsa yace "Before then, fara kiran mutanen gidan ku ki sanar da su kina asibiti" shiru tayi bayan ta karbi wayar, ya fada mata sunan asibitin sannan ya fita, hawaye ya cika idonta ta saki kuka a hankali tana tausayin kanta, bayan kusan

Please Login or Register in order to submit comment