Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ka cire mata I will pay what ever amount u request for plss" likitan ya mike ya nufi show glass dake office din ya dauko wani allura da syringe, ya dawo yace "I will give her this injection sauran drugs din kuma xan rubuta maka kaje pharmacy ku siya" Sudais ya sauke ajiyar xuciya yace "Thanks very much Dr, nagode sosai" Lkci daya khadijah t fashe da kuka ta mike tace "Nooo, ni bana son a cire min don Allah ku yi hakuri" bude baki Sudais yyi yana kallonta da mamaki, ta hade hannuwanta tana girgixa masa kai hawaye na sakko mata a hankali tace "Don Allah kayi hakuri, I don't want to abort d pregnancy, Allah will be angry with me plss" Likitan ya ajiye alluran ya rungume hannuwansa yana kallonta yace "Ba mijin ki bane kenan?" Hawaye na ci gaba da sakko mata ta gyada masa kai alamar eh, Sudais dake mata wani irin kallo ya mike yace "Sae ki san inda dare yyi maki kuma daga nan" daga haka ya fice daga office din kamar xae tashi sama, a hankali take kuka tana kallon likitan dake kallonta yana girgixa kai, can ta nufi kofa cikin sanyin jiki ta fita, babu motarsa a parking space, ta fita gate tana share hawayen da ya ki tsaya mata.


Har Khadijah ta isa bakin titi kuka take bata damu da mutanen dake kallonta ba, ta ma rasa inda xata bi gashi ko sisi bata da shi, all this while Sudais na cikin motarsa yyi parking motarsa ya dinga bin ta da kallo har ta d'an yi nisa, ya jinginar da kansa da kujera ya lumshe ido yana kiran Allah a xuciyarsa, he is just confuse, a hankali ya ci gaba ya fara driving motar har ya iso dai dai inda take ya tsaya ya wani hade rai cikin tsawa yace "Ina kika san xaki tafi yanxu?" Ta juyo a tsorace tana kallonsa ta tsaya bata ce komai ba, yace "Shigo mu je" fuska daure yyi maganan, A sanyaye ta xaga ta bude motar tana kallonsa ta shiga, bai ko kalleta ba ya ja motar, har ya isa gidansa bai ce mata komai ba, ita ko tayi nisa cikin tunanin da take ya bude motar ya fita ta bi sa da ido, Juyowa yyi ganin bata fito ba Yace "Should I bring u down?" girgixa kai tayi ta fito ya kulle motar ya nufi entrance din gidan ta bi bayansa, kana ganin yanda yake tafiya kasan a gajiye yake, xaune ta gansa parlor ya jinginar da kansa jikin kujera bayan ya xauna ya lumshe ido, a hankali ta xauna kasa ta takure waje daya sbda sanyin parlon, bude ido yyi bayan wani lokaci ya kalleta, suna hada ido ya dauke kai, khadijah dai sai kallonsa take, yanda ya tsura ma ac dake aiki a parlon ido yasa xaka gane tunani yake, a hankali khadijah tace "Xan yi wanka..." sai a snn ya juya ya kalleta, a takaice yace "In kai ki bayin kenan?" Ta girgixa masa kai, yace "Toh tashi ki tafi" mikewa tayi ta wuce dakin da ya saukar da ita, wanka tayi ta fito ta shirya ta sa Hijab, yana nan yanda ta bar sa, har ta iso kusa da shi kuma bai sani ba, duk jikinta yyi sanyi ta durkusa nan kusa da shi cikin sanyin murya tace "I knw I am a burden, u don't knw where to start from, and u don't want to send me away cos you've got a good heart... You look so responsible to keep me in ur home, you have parent and elders that won't take it likely.... I don't want to be d beginning of ur problems, sbda haka nake rokon ka don Allah ka taimakeni ka kai ni gidan marayu kamar yanda na roka a baya, I will cope there in sha Allah, I will take care of the motherless there, but I want u to do me the favour of coming to see me, even if it's just once in a year plss, I want to feel I have somebody in this world, don Allah kar ka mance ni bani da kowa" tana kai wa nan hawayen dake makale idonta ya sakko, kallonta kawai sudais yake, can ya runtse ido ya bude ya mike ya fice parlorn, hade kai tayi da gwiwowinta tana kuka a hankali tana me tausayin rayuwarta, sai bayan kusan minti talatin sudais ya dawo parlorn, duk da ta ji shigowarsa bata dago kanta ba, muryarsa taji yace "tashi ki shiga daki kiyi kukan da kyau" ba musu ta tashi ta wuce cikin dakin, tayi kukan kamar yanda yace mata har ta gaji ta kwanta ta takure waje daya, bude kofar dakin yyi ya shigo, ta daga kai tana kallon sa har ya iso inda take yana tsaye yace "Good, am hoping all the tears you where planning to shed while in this house kin yi su yau kin gama, cos I am nt gonna tolerate that, clear? Better ki barni in ji da daya" Mikewa xaune tayi ta gyada masa kai tana share guntun hawayen idonta, yace "Me xa ki ci?" Ta girgixa kai tace "Bana jin yunwa" ganin kallonta yake a hankali tace "Toh xan ci apple" yace "Not apple, I mean food" ta d'an yi shiru, can ta dago tana kallonsa a hankali tace "Wainar flawa" wani kallo yake mata yace "Meye shi?" Taace "Da flour, albasa, tarugu, maggi, gishiri and man gyada ake yin sa, Anty Kyauta tayi mana a can gidan" da mamaki yace "A ina xan samo maki shi?" Tayi shiru bata ce komai ba, ya fi minti biyar a tsaye, can ya tabe baki ya fiddo wayarsa a aljihu yayi dialing number ya kai kunne, ba a dau lkci ba ya amsa sallaman da aka yi masa yace "Rabi'ah am on my way now, pls ina son ki min...." Juya ido yyi kamar me son tuno sunan abun, can ya cire wayar a kunne da sauri ya jefa ma khadijah wani kallo yace "Meye sunan ma?" A hankali tace "Wainar flawa" ya mayar da wayar kunne yace "Wainar flawa" Khadijah na jin yarinyar na dariya ya tabe baki ya katse wayarsa ya mayar aljihu ya fice a dakin. Khadijah na nan yanda ya bar ta ya dawo dakin, yana kallonta yace "ermm, ohk let me say Amira, you see xan je gida yanxu, but baxan dade ba xan kawo maki abincin, xa ki iya tsayawa ke kadai ai koh?" Ta gyada masa kai yace "Good, I will be right back now" kashe ac din dakin yyi ya kunna mata kayan kallo daga haka ya nufi kofa khadijah tace "Allah ya tsare" juyowa yyi ya kalleta yace "Amin" daga haka ya fita ya kulle mata kofar. Kwanciya tayi duk da sonta da kallo ta rufe idonta. Tun da sudais ya shiga gidansu yyi parking gabansa ke faduwa ya bude motar a hankali ya fita ya wuce cikin gidan, jin ana soye soye a kitchen ya karasa kitchen din, Rabi'ah ce tsaye tana soya wani abu da bai taba gani ba yace "What's this" wara ido tayi ganinsa tace "Sannu da xuwa yaya, wainar da kace mana" yace "Dama kamar kwai yake?" Ta gyada masa kai tana yar dariya ya tabe baki yace "Mami fa?" Tace "Tana bedroom da su Anty Maryam" bai ce komai ba ya haura sama yyi sallama kofar dakin maminsa, Kanwar mami da kanninsa biyu dake Dakin ne suka amsa masa ya shiga ciki, kallon uban kayan dake jibge a kasa ta ko ina a dakin, ga boxes masu tsada dake ajiye su ma, dukawa yyi ya gaida mami ta amsa da fara'a tana masa tambayar ya hanya, yace "Alhmdllh" sannan ya gaida Anty Maryam ta amsa da murmushi tace "Welcome barrister" sai a sannan ya amsa gaisuwar kanninsa ya mike ya koma can karshen gado ya xauna, Mami tace "Ka ga sai yau Maryam ta karbo sauran akwatunan xa a xuba kayan ciki yanxu" a hankali yace "Ohk" Mami tace "ka gama gyaran da kace a can gidan naka" ya gyada kai yace "Eh Mami" Mami tace "Toh maa sha Allah" Yana ta xaune har suka gama jera gaba daya kayayyakin a akwatunan, kanninsa su Humairah suka fita dakin ya rage daga shi sai Mami da kanwarta, Mami tace "Lkci na ta tafiya sudais yaushe ka ga ya kamata a kai kayan" tasowa yyi a hankali ya dawo kasan carpet ya xauna kansa a kasa murya can kasa yace "Mami..." Mami dake ta kallonsa kamar yanda Anty Maryam ma ke kallonsa tace "Ya aka yi sudais?" Kasa dago kansa yyi yace "Mami ina son a dakatar da kai kayan nan yanxu ne...." Mami dake masa kallon mamaki tace "Ko saboda me Aliyu?" Ya girgixa kai yace "Mami a dai dakata kawai" Anty Maryam tace "Ko Jiddahr ta yi maka wani laifin ne sudais?" Shiru yyi bai ce komai ba, Mami tace "Toh ni dai abinda xan ce maka a nan shine idan dai kasan ba shiririta bane, ba wani concrete laifi bane ka ajiye wannan shashancin da kake fadi aside, idan kuma kaga laifi ne babba to shkkn" Anty Maryam tace "Ka fada mana me tayi, wani laifin ka kama ta da shi Sudais, Kar mu xama kananun mutane" ya girgixa kai a hankali yace "A bar xancen kawai mumy" Mami tace "Toh Allah rufa asiri" yace "Ameen" mikewa yyi yace "Xan fita in dawo yanxu Mami" daga haka ya nufi kofa Mami ta bi sa da ido har ya fita, Anty Maryam tace "Kar ki tilastata masa don Allah Mami tun da kika ga haka ba karamin laifin ya kamata da shi ba, kin dai san halin sudais da xurfin ciki ko xaki shekara kina tambaya ba fada xai yi ba" Mami dai bata ce komai ba. Sudais na fita ya shiga kitchen ya tarar Rabi'ah ta gama wainar ta xuba masa a warmer, ya bude warmer din yana ta kallon abincin kafin ya tabe baki ya dauka ya fito parlor, da mamaki tace "Yaya ba a nan xaka ci ba?" Yace "Ehh ni da frnds dina xa mu ci, sai na dawo" daga haka ya fita gidan ya hau motarsa ya wuce. Sai da Sudais yyi azahar a masallacin layin gidansa sannan ya shiga gidan misalin karfe daya da rabi, jin an bude kofa Khadijah dake bacci ta bude ido da sauri, karasowa yyi yana kallonta ya ajiye warmer din hannunsa yace "Tashi ga abincin" ta xauna ya bude mata warmer din, ba don tsare ta da yyi ba da daya ma baxata cinye ba amma haka ya dinga forcing dinta har ta cinye biyu, sai dai duk she was restless don amai kawai ta dinga ji, ya hade rai sosai yace "Look idan ki ka yi aman nn I will nt bother my self about ur food again am telling you" hawaye cike idonta tace "Kayi hakuri wllh ba ni bace" ya xauna gefen gadon yace "Toh nayi, amma ki daure kar ki yi.... Just try" ta gyada kai ta koma xata kwanta ya ce "Toh ai hakan xai sa ki yi aman" dagowa tayi da sauri ta xauna, toshe baki tayi tana girgixa kai, ya wani hade rai kamar bai taba dariya ba yana kallonta, a hankali tace "Wllh amai xan yi kayi hakuri" daga haka ta mike ya fixgota har sai da ta kusa fadawa kansa, yace "Am serious baxa ki yi ba" bai rufe baki ba ta kwarara masa aman gaba daya a jikinsa da bedsheet, wani kallo ya dinga mata yana yamutse fuska, can ya runtse ido har ta gama aman, Khadijah ta kasa kallonsa sae sauke numfashi take, wani tsaki da bata taba jin irinsa ba ya ja a fusace ya mike ya shige toilet, hawaye ya dinga sakko mata a sanyaye ta hade kai da gado, bayan kusan minti goma ya fito, ita dai tana nn yanda take, taji ya dafa ta ta dago da sauri, singlet da 3qtre ne jikinsa, ya sauke idonsa yace "kije kiyi wanka na sa maki ruwa" ta girgixa masa kai tace "Baxan iya ba ynxu" yace "No ki daure" daga hka ya sa ta tashi ta wuce bayin, Tana fitowa taga har ya shimfida wani bedsheet din ya cire na da, ta kwanta tana rawan sanyi, ya shiga bayi da xanin gadon, bai fito ba sai da ya wanke da shirt dinsa ya fita dakin.

Daga wannan rana Khadijah ta fara laulayi me tsanani kamar baxa ta yi ba, tausayinta Sudais yake har ransa, duk ta rame ba kadan ba ga yawan complain din ciwon kirji da take, idan aka ga yanda sudais ya damu sai a rantse ya taba sanin Khadijah, hakan bai hanasa trying best dinsa gun ganin Maminsa bata d'ago komai a rashin dawowa gida da baya yi da wuri da fitan da yake yi da sassafe ba, yawanci duk khadijah ke cinye masa time dinsa, ya kai ya kawo sai ya fi kwana biyu bai karbi case ba tunda he is always by her side kwana ne kadai bai yi gidan nasa, karfe sha daya idan tayi bacci yake barin gidan ana idar da sllhn asuba kuma kafin ya shiga gida sai ya taho gidansa dubata yaga ya ta tashi, Dr Yusuf ke xuwa bata medication kusan kullum da safe da yamma tun daga allura xuwa drugs duk da biyansa Sudais yake, A haka har Khadijah ta cika sati biyu ciff a gidan. Da safe misalin karfe sha daya Sudais yaje can clinic gun Yusuf, bayan sun gaisa Yusuf ya tambayesa jikin khadijah, ya shafa kai yace "Toh ga ta can dai, am just tired Yusuf, wai why not baxa ka taimaka ka cire mata cikin nan ba frnd, am talking to you about this for the 3rd time don Allah ka cire mata ko nawa ka bukata xan baka, plss Yusuf" Yusuf ya girgixa kai yace "My reply will always be the same, I don't abort pregnancies and I will not, nace ka kai ta wani asibitin ni dai baxan yi ba ka ki ganewa" Sudais ya marairaice yace "Nasan baka cire ciki amma ita wannan case dinta daban ne, she was raped... beside she is too young da ciki dubi fa yarinya ce karama, gashi sai wahala take sha ko don haka ka tausaya mata mana Yusuf" Yusuf dake rubuce rubucensa yace "Ae sai kuma ka yi Barrister" Sudais ya d'an hade rai yace "Haba Dr, ya kke son marainiyar tayi da yaron da xata haifa yanxu, ta ina xata fara rainonsa don ni dai ba dauwama xata yi tare da ni ba na har abada, har ynxu ina tunanin taimakon da xan bata ta tafi ta inganta rayuwarta but nt when she is this sick everyday, dubi fa jiddah gani take kamar na yaudareta ne, but ba hka bane idan aka yi auren ina xan sa ta, kasan it won't make sense ina da gida in kama haya, dole Mami xata so sanin dalili, infact she will be suspicious, Yusuf don girman Allah ka rufa min asiri ka cire mata jaraban nn ta kama gabanta plsss" Yusuf ya tabe baki yace "xa ma ka gama dadin bakin ka" jin Sudais yyi shiru yana kallonsa ya ajiye pen din hannunsa yace "Sae in har in rubuta maka kaje can pharmacy ka siya nasan baxa ka rasa iya allura ba, duk sai kayi mata da kanka" ban da hararansa babu abinda Sudais yake, Yusuf yace "yes, or you buy her just drugs shkkn amma ni dai ba da hannu na ba" Sudais ya dake trying hard to hide his anger yace "Rubuta min" Takarda Yusuf ya jawo yyi rubuce rubucensa ya mika masa Sudais ya fixge ya nufi kofa Yusuf ya bi sa da kallo yana murmushi, Gida ya nufa bayan ya je garage din mota amso sakon Mami da ta aikesa tun safe, Xaune ya same Mami parlor, tun da ya shigo take kallonsa ganin ramar da yyi har ya karaso ya xauna kasa kusa da ita yace "Ina yini Mami" tace "Lafiya lau, sannu da xuwa" ajiye mata ledan hannunsa yyi yace "Ga sakon Mami" Bata ce komai ba ganin haka ya daga kai yana kallonta, tace "Aliyu ni ban fa gane nufin ka ba kayan akwatunan da kasa nayi jere da shi a daki ka hana a kai, toh Abbanku ya sa in xaunar da kai ka sanar da ni ko fasa auren kayi, wannan ai iskanci ne da kokarin mayar da mu kananun mutane da kake, idan ma da matsala ne ai sai ka yi mana bayani, babu mai maka dole tun da kai ka kawo yarinyar nan kana so ba wani ya kawo maka ita ba, yanxu ni ka gaya min ma'anar cewa da kayi kar a kai kayan a dakata" Sudais da har xufa ya fara keto masa ya shafa kai da kyar yace "Mami ba wai na fasa bane, kawai dai akwai matsala... ina son a min alfarmar ce masu su d'aga ko xuwa sabon shekara da xa mu shiga, idan kuma sun ga baxa su iya dagawa ba to gaskiya na hakura, Allah bata wanda ya fi alkhairi a kai na" Mami dake masa wani kallo tace "A daga a kan wani dalili?" Ya kasa dago kai yace "Kiyi hakuri Mami ayi min yanda nace pls, I just want to figure out the problem, Mami kin fa san aure ba don kwana daya ko 'yan watanni ake yin sa ba na har abada ne, Mami I don't want to make marriage mistake in my life don ni bani da burin xama da mace fiye da daya so I want to have the best marriage, ku taimaka ku ce masu a daga har lkcn, idan sun ga yyi masu tsayi to na hakura gaskiya I don't want to cheat my self" Mami tace "Toh shi kenan, Allah sa mu dace, xan yi ma Abban naku bayani" Sudais ya dan yi murmushi a hankali yace "Nagode Mamina, xan je in dawo yanxu" Mami na kallonsa da kyau tace "Wllh ban gane fitar nan da kake kamar me talla ba kwanan nan sudais, da sassafe ka fice baka dawowa sai kusan sha daya, what's wrong with you?" Ya dago yana kallonta a hankali yace "Mami wani case ne ya shige min duhu, so ina bincike ne shi yasa kika ga haka" kallonsa kawai take can ta tabe baki tace "Though I knw when you are saying the truth and when u are lying, and duk da nasan karya kake coz I saw it in ur eyes, ni kam sai dai ince Allah tayi jagora, ya kuma yaye maka abinda ke damun ka, wnn ramar kuma da kayi, kayi kkrin ganin cire ko ma ke damun ka plss, it's better you pray to ur God" Sudais ya dauke kansa daga kallonta da yake ya mike a hankali yace "Toh nagode Mami sai na dawo" tace "Allah ya tsare" daga haka ya fita. Pharmacy ya tsaya ya siya magungunan da Yusuf yyi masa prescribing sannan ya siya fruits kafin ya wuce gidansa, har wani faduwa gabansa ya shiga yi bayan yyi parking cos bai son xuwa ya ga khadijah in pain, ya dai dake ya shiga gidan, kwance ya sameta kamar ko da yaushe a daki idonta a rufe, yawanci duk haka yake xuwa ya sameta kuma ba bacci take ba, yana tsaye a hankali yace "Amira" ta bude idanuwanta a hankali tana kallonsa, yace "Ya jikin" kai ta gyada masa ya durkusa yana bude ledan apples da banana da ya siyo mata yace "Ga Apple nan" ta girgixa kai da sauri tace "Anjima" yace "Toh kin yi sllh?" Gyada masa kai tayi, ya d'an yi shiru sai kuma ya mike yace "Toh tashi ga magani na kawo maki ki sha, you feel more better idan kin sha" kamar xata yi kuka tace "Xan yi amai ni nafi son allura" kallonta ya tsaya yi, can yace "Baxa ki yi ba kawai guda uku ne fa" daga haka ya fiddo magungunan a leda sai kuma ya fita xuwa ya debo mata ruwa, har ya dawo tana kwance ya d'an hade rai yace "Toh tashi mana" mikewa tayi da kyar ya bude maganin gudu uku kamar yanda yace ya bata a hannu ya mika mata ruwa a cup, ta karba tana bata fuska xata yi kuka, ya daure fuska yace "Ki sha Ki ban cup yanxun nan" wayarsa ne ya fara ring ya ciro a aljihu tana ganin haka ta watsa maganin a bayanta tayi saurin kai ruwan baki tana sha dai dai lkcn da ya maido dubansa kanta, da sauri yace "Kin sha?" Ta mika masa cup din tana yamutse fuska, ajiyar xuciya ya sauke a hankali, kokarin amai ta shiga yi da sauri yace "Noooo, don't ko in bata maki rai" ta koma baya a hankali kar ya xagayo ya ga maganin ta jingina da gado yace "Good girl" daga haka ya fita ya kira Yusuf dake kiransa, da sauri ta kwashe magungunan ta watsar a bayan gado tana turo baki, Sudais ya hade rai bayan ya kai wayar kunne yace "Ya aka yi?" Yusuf yace "Ya ta sha?" Sudais yace "It's nt ur concern" dariya Yusuf yyi yace "In dai ka tabbatar ta sha don't leave her alone kar ka kashe yar mutane nan da few hours xata samu miscarriage din in dai magungunan da na rubuta ka siya ka bata" Sudais yace "Ohk" daga haka ya katse wayar ya xauna parlor. Haka Sudais yyi ta xama gidan har magrib amma shiru kke ji, ya duba ta yyi sau ashirin kafin magrib amma banda bacci bbu abinda take hankli kwance, yana fitowa masallaci ya kira Yusuf yace "Kai ni da ina ta xaune gidan har yanxu shiru" Yusuf yace "Bata sha ba toh" Sudais yace "Ya xaka ce haka, a gabana fa ta sha ni ma na bata maganin da ruwa" Yusuf yyi shiru jin haka, sudais yyi tsaki ya katse wayar. har washegari shiru kake ji bbu alamar miscarriage gashi Yusuf yace kar ya kara bata wani, duk ran sudais ya baci, da yammacin washegari Yusuf ya xo gidan, Magungunan ya dauka yana ta kallonsu kamar yanda Sudais ke hararansa shi kuma, can ya balli wasu ya mika ma sudais yace "Bata ta sha" Khadijah dake kwance tana kallonsu kamar xata yi kuka tace "Ni maganin wani iri yake min bana so plss" Sudais ya daure fuska yace "Karba my friend" mikewa tayi hawaye ya cika idonta ta amshi maganin ya mika mata ruwa, daga shi har Yusuf suka kafeta da ido, ta daga gefen Hijab din jikinta tana share hawayen idonta hakan ya bata daman sakin maganin gaba daya a Hijab din cikin dubara sai kuma tayi saurin dage kafarta kamar xata daura kanta bisa kneel dinta, har lkcn kuma hannunta na dunkule kamar tana rike da drugs din, Yusuf yace "Baxa ki sha ba?" Bude baki tayi ta yi kamar ta watsa su ciki sannan tayi saurin xuba ruwa bakin ta tana yamutse fuska har da kokarin amai, da sauri Sudais yace "Don't try that" ta hade kai da gwiwa suna ta tsaye suna kallonta har ta dago a hankali, Yusuf ya juya ya fita sudais ya bi bayansa, Yusuf yace "Toh sai kayi xaman gadi" daga haka ya bar gidan, Sudais na ta xaune har dare amma shiru, mamaki ya dinga yi anya ba yaudararsa Yusuf yyi ba, a fusace yaje har gida ya samesa don jin me yasa yyi masa haka, Yusuf dake dakinsa kwance yace "Toh ka kai ma wani likitan takardar maganin ka tambayesa na menene, I think that's all I can tell you" Bayan kwana biyu sudais ya sake komawa Yusuf office da rana, da damuwa yace "Dr ko xaka canxa wani method din ne, wllh I don't have rest of mind, am afraid kar Mami ta san abinda nake yi, gashi in few weeks time xan je UK, to ya xan yi da yar mutane?" Yusuf yayi dariya yace "Tunda taimakonta kake son yi ka tafi da ita mana" Yusuf ya watsa masa kallo yace

Please Login or Register in order to submit comment