Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

su mama da mutan gida" a sanyaye tana kallonsa tace "Xa su ji nagode sosai" daga haka ta juya xata shiga gate, yace "Wait Khadijah baki ban number ki ba mu dinga xumunci" dawowa tayi ta kira masa numberta yayi saving yana kallonta yace "It's nyc meeting you once more Khadijah" ta kirkiri murmushi ta daga masa hannu ta shiga cikin gida, Nanny na kitchen su sudais kadai ne xaune parlorn ta sa masu cartoon, khadijah ta ajiye ledan hannunta ta isa kusa da su ta xauna tana kallonsu, su ma kallonta suke, ta yi murmushi ganin irin kallon da suke mata ta yi masu kiss gaba daya, Sudais ya goge bakinsa shureim na ganin haka shi ma ya goge nasa, jikinta yyi sanyi sosai tana kallonsu, bata san lkcn da hawaye ya kawo idonta ba ta mike ta wuce daki da sauri, Nanny ce ta shigo dakin ganin khadijah kan gado tana hawaye da mamaki ta karaso da sauri tace "Mum twins me ya faru kuma?" Cikin rawar murya tace "Wai don na masu kiss shine suke goge bakinsu" dariya sosai Nanny tayi kafin tace "kai Khadijah shine har da kuka, to kyalesu xan yi maganinsu" daga haka Nanny ta juya ta koma parlor, taso keyar boys din tayi suka taho dakin, kusa da khadijah ta ajiye su duk suka shiga kkrin sauka daga kan gadon Nanny ta daure fuska tace "C'mon, duk wanda ya sakko xan xane sa, ita ce uwar ku ba ni ba" Kuka suka fara yi kuma basu sauka kan gadon ba, Nanny na kallon khadijah dake ta kallon kyawawan yaran nata tace "Yanxu abinda xa mu yi shine xa su dawo kwana nan dakin, ke xaki dinga masu wanka ki shirya su, ke xaki dinga ba su abinci hakan kadai xai sa su saki jiki da ke" a hankali khadijah tace "Toh" Nanny tace "Don haka duk safe kafin ki tafi school sai kin masu wanka kin shirya su ni kuma in hada masu breakfast sai in baki ki basu" kai kawai Khadijah ta gyada don har ga Allah bata son gudun ta da yaran suke, haka Nanny ta fita ta bar su suna kuka xa su bi ta, amma da yake suna jin magana bbu wanda ya sauka daga kan gadon kamar yanda tace masu, suka gama kukansu suka yi shiru suna kallon khadijah, Sudais yyi tapping dinta yana nuna mata kofa yace "Nanny..." Murmushi Khadijah tayi ta jawo sa jiki tace "Nima Nanny ce ai" hakura yaran suka yi suna ta xaune dakin kusa da ita har bacci ya dauke su, Nanny na ganin lkcn tashin su ya kusa misalin karfe biyar na yamma ta dama masu custard ta dafa masu indomie ta kawo ma khadijah dakin ta fita ta rufe masu kofa, a lkcn kuma suka tashi, duk suka yi jigum suna kallon khadijah, ruwan wanka ta hada a bathroom dinta tayi masu gaba daya sannan ta fito ta shafa masu mansu dake dakin ta sa masu singlet da pant ta xaunar da su kan carpet ta shiga basu custard din suna karba, har ranta ta ji dadin hakan suna gama sha kuma ta fara basu indomie da egg din, shureim na koshi ya fiddo wanda ta sa mashi a baki ya mike ya kai mata bakinta, murmushi tayi ta bude bakinta ya xuba mata abincin ta shiga ci a hankali. Sai kusan karfe shidda Khadijah ta fito parlor da yan biyun nata, cartoon ta sa masu parlorn duk suka xauna kan kujera suna kallo basu bi ta kan Nanny ba, da daddare a kan gadon ta ta shimfide su bayan sun yi bacci, ta gama shirin kwanciya kenan ita ma wayarta ya fara ring, ita dai bbu mai kiranta a waya ban da Nanny sai wata classmate dinta Aisha dake sonta sosai, ta dinga kallon number kafin ta daga, sallama yyi mata jin muryar hankalin ta ya dan kwanta sai dai bata san dalilin kiran ba ta amsa masa sallamar ta gaishesa yace "Ko kin fara bacci ne?" Ta girgixa kai tace "A'a yanxu dai xan yi" yace "Ohk, ya mutan gidan?" Tace "Lafiya lau Alhmdllh" yace "Maa sha Allah" shiru ta yi bata ce komai ba, a hankali yace "Kawai sai kika bar garinmu ba sallama Khadijah" tayi murmushin karfin hali tace "Ummata ce ta xo ta dauke ni ai" yace "Allah sarki, but dama me ya kawo ki gidan tun farko" khadijah da taji kamar kar tace komai kawai ta yi murmushin takaici tace "Ai yayan Abbana ne" yace "Are you serious?" Tace "Uhn" yace "Waow, to me yasa basu baki abinci" ta wara ido tace "Suna bani fa, ni ce ban iya cin abincin ba lokacin" murmushi yyi yace "Allah sarki, kwanaki ma ai kawun naki yyi accident kin sani koh" Khadijah ta bude ido sosai tace "Haba dai, ban sani ba, basu gaya mana ba" Sadeeq yace "Ehh amma da sauki yanxu ina jin ya samu lafiya ma" A hankali khadijah tace "Toh Allah ya kara kiyayewa" yace "Ameen" shiru ne ya biyo baya kafin yace "Kin taba ba Umma labarina" Khadijah da taji jikinta yyi mugun sanyi a hankali tace "Kowa ma ina ba labarin ka, cos you fed me when I was in need of food" Sadeeq yace "Noo I did that for the sake of Allah, not for you to tell everyone" murmushi kawai khadijah tayi a sanyaye, shi ma murmushin yake yace "Sure, yaushe xa ki hada ni da Umma mu gaisa ko kuma in xo har gida in gaisheta, ko baki son mu yi xumunci sosai?" gabanta ne yyi mugun faduwa and she was totally lost of words, a hankali yace "Hello, Khadijah are you there?"

Katse wayar Sadeeq yyi jin bata ce komai ba, ya sake kiranta a tunaninsa network ne, bayan ta daga tayi masa sallama, amsawa yyi yace "Is ur network fluctuating?" A hankali tace "Ina jin ka yanxu" yace "Ohk, Cewa nayi when xan xo in gaisa da Umma if possible har da matata kinga shkkn ta samu Umma a garin Abuja ita ma, cos she have no body here" Khadijah ta wara ido tace "Lah, are you married?" yace "Sure, kusan 3 months kenan" murmushi sosai Khadijah tayi tace "Allah sarki, Allah ya bada xaman lafiya" yace "Ameen thumma Ameen, to yaushe xa mu xo?" Khadijah tayi murmushin karfin hali tace "In dai kuna da time, kar ku ma ta gan ni tayi wani tunanin daban fa" dariya sosai Sadeeq yyi yace "Noo, she's understanding, kawai daga few months da aure sai ta sa abu a ranta don ta gan ki, ba ma yar Nigeria bace, so she won't think like them in sha Allah" Khadijah tace "Yar ina ce?" Yace "She is an Ethiopian" Khadijah ta wara ido tace "Kace bata jin Hausa kenan" yyi dariya yace "Noo tana ji ba laifi, ai tana xuwa hutu gun aunt dinta a Katsina sai dai tana dadewa bata xo bane, but she speaks English well" Khadijah da ke ta murmushi tace "Maa sha Allah, I will love seeing her" Sadeeq yace "Toh ko ki shirya da 'yan gidan ku sai in xo in dauke ku, she will be very happy don bata da kowa, though shekaranjiya dai wata frnd din mum dinta ta xo daga can kasar ta su, yanxu haka ma tana gidana, but ita ma nan da kwana biyu xata wuce" Khadijah ta langwabar da kai tace "Allah sarki, to yaushe xaka xo ka kai mu, amma ni dai ina tsoro fa" dariya Sadeeq ya dinga yi yace "Tsoron me? Na fa ce maki she is not like you people in Nigeria, I can even tell her you are an old time frnd, idan kinyi insisting kina tsoro kuma sai in ce ke yar uwata ce" Khadijah tace "Haka dai ya fi" Sadeeq yace "Dubeta matsoraciya, idan na aureki na hada ku fa?" ta d'an hade rai tace "Ni ance maka aure xan yi yanxu" yyi murmushi yace "Mayar da wukar wasa nake, nima baxan iya handling two wives ba ai" murmushi kawai khadijah tayi, yace "Tun da gobe Monday xan xo da yamma sai in dauke ku, sai ki sanar da umma" Khadijah tayi shiru don bata son fashin islamiyya, can tace "Toh shi kenan Allah ya kai mu" yace "Ameen Khadijah, bari in bar ki kiyi bacci, sweet dreams" tace "Toh nagode bye" daga haka ya katse wayar, Khadijah ta sauke ajiyar xuciya jin Sadeeq yyi aure, thank God baxai shigo rayuwarta bane ya dame ta, duk da can kasar xuciyarta tana ganin girma da darajar abinda yyi mata a lkcn tana Katsina, he really helped her don da ba don shi ba kilan idan yunwa na kissa da ya kasheta, murmushi tayi ta koma ta kwanta tana rufa twins dinta da duvet, matar da yace ya aura ce ta fado mata, toh Allah yasa sa'arta ce ko xata samu warce xa su dinga xumunci sosai da, don ta gaji da rayuwa daga ita sai Nanny da boys dinta bata da kowa, Aysha dama kawai a makaranta kadai suke interact, Har ranta taji hankalinta ya kwanta haduwa da Sadeeq, ko ba komai dai akwai wanda ya santa ta san sa a Abuja yanxu sai dai fa bayan sudais bbu wanda xata sake bata lkcn ba labarinta gaskiya, its not as if Sadeeq didn't deserve to knw her story but maimaitawan xai dinga fama mata ciwon da take healing a hankali na xuciyarta, da wannan tunane tunanen bacci ya dauke Khadijah, da asuba bayan ta idar da sllh tana xaune kan darduma tana azkar dinta Nanny ta shigo dakin da sallama, gaisawa suka yi tana kallonsu Sudais tace "Basu tashi cikin dare ba neman tea" Khadijah ta girgixa kai tace "A'a..." Nanny tace "Toh kafin dai ki gama shirin makaranta na san sun tashi, sai kiyi masu wanka, ni kuma xan tafi in hada breakfast yanxu" Khadijah tace "Toh" daga haka Nanny ta fita dakin, khadijah na fitowa daga wanka wajen karfe shidda da minti arba'in ta ga yaran xaune kan gado duk sun tashi, wara masu ido tayi ta nufesu ta durkusa tana murmushi a hankali tace "Good morning boys" kicin kicin suka yi da fuska suna kallonta kamar Aliyu ya hade rai, dariya hakan ya bata, tace "Toh bari in maku wanka sai ku tafi wajen nanny" daga haka ta koma bathroom din tana daure da towel ta hada masu ruwan wanka ta dawo ta dauke su gaba daya suka shiga bathroom din, a dakinta ta gama shirya su kafin ta tafi parlor da su nan Nanny ta sa tayi feeding dinsu, sai kusan karfe bakwai da rabi Khadijah ta gama shirin tafiya makaranta, tana isa bakin kofa ta juya tana kallon twins da suka bi ta da kallo, kamar hadin baki suka daga mata hannu a tare murmushi tayi ta daga masu ita ma sannan ta fita. Karfe hudu da kusan rabi Sadeeq ya kirata, bayan sun gaisa yace "xan taho yanxu Khadijah, am done for today a office" khadijah da ke dama ma su Sudais golden morn a parlor tace "Toh muna jira, Allah kawo ka lafiya" Tana gama ba ma yaran abinci tayi masu wanka ta shirya su cikin kayansu iri daya, sosai yaran suka yi kyau da kayan da ta sa masu, ta fiddo kayan da xata sa kenan Sadeeq ya kirata, daukan wayan tayi ta daga ta kai kunne yace "Am outside Khadijah" ta xaro ido tace "Toh don Allah yi hakuri, minti goma pls" yace "Alryt then, ina jira" a hanxarce Khadijah ta shirya sannan ta sa Hijab dinta har kasa kamar yanda ta saba, ta fita gun Nanny dake wankin kayansu shureim a bathroom dinta, ta tsaya daga bakin kofa tace "Nanny xa mu d'an fita da twins amma baxa mu dade ba" Nanny tace "Toh shkkn Allah ya kiyaye, amma kar kuyi dare kin ga yamma yyi" Khadijah tace "In sha Allah" daga haka ta fita ta shiga nata dakin ta fito tare da yaran, gabanta sai faduwa yake kar su ce baxa su bi ta ba, Har bakin kofa nanny ta rakasu tana daga ma yaran hannu su ma suna daga mata, tun kafin su iso motar Sadeeq ke kallon yaran, kawai ya bude motar ya fito yace "Waow, cute boys, ur siblings?" Khadijah ta kirkiri murmushi ta gyada masa kai daukansu yyi da daddaya da daddaya ya masu kiss yace "How are you boys" Kallonsa kawai yan biyun ke yi, ya bude front seat yana kallon khadijah yace "Toh shiga" tana shiga motar ya mika mata yaran gaba daya ya rufe motar sannan ya xaga ya shiga maxaunin driver ya tada motar, sai da suka hau kan titi yace "Ya sunan twins din?" Khadijah tace "Sudais and Shureim" yace "Maa sha Allah, they are handsome, but step siblings din ki ne su koh?" dariyar karfin hali Khadijah tayi tace "Uhm" yace "That's nyc" yace "Har na sanar ma Shaheedah xuwan ki, she is so happy" Khadijah tace "Da gaske" yana murmushi yace "Sure" tace "Allah sarki" nisa ne sosai da gidan Sadeeq don sai kusan karfe biyar da wani abu suka isa gidan, haka kawai khadijah taji gabanta na faduwa, bayan yyi parking yace "Welcm to our home Khadijah" murmushi kawai tayi ta bude motar ya xaga ya taimaka mata sauke yan biyun kasa sannan ta fito ta rufe motar, wata kyakkyawar mace ce da baxata wuce shekaru ashirin a duniya ba ta fito balcony din gidan, fara ce doguwa mai kyan gaske, ta karaso gun motar tana murmushi sosai tace "Sannun ku da xuwa bak'in mu" Khadijah dake ta kallonta tayi murmushi tace "Yauwa sannu" wara ido matar tasa da ya kira da shaheeda tayi tana kallonsu Sudais tace "Maa sha Allah, dear they are sooo cute" daga haka ta tsugunna ta jawo yaran jiki tace "Welcome boys" Khadijah ma sai kallon yaran nata take ganin sun ki ko da murmushi, Sadeeq ya dau Sudais yana murmushi yace "Lallai boys din nan sun iya miskilanci" Shaheedah ta dau Shureim tana dariya tace "Mu shiga ciki toh" daga haka ta fara tafiya Sadeeq ya kalli khadijah yace "Mu je" bin bayan shaheedah tayi ya bi bayanta yana rungume da shureim.

It's not much sorry....

Suna shiga parlorn khadijah ta xauna kan daya daga kujerun ciki, Shaheedah ta ajiye shureim tana murmushi tace "Wai basa magana ne?" Khadijah dai bata san ko suna yi ba ko basa yi amma taji Nanny tace suna yi idan sun ga dama, ta dan yi murmushi tace "Ba sosai ba, har yanxu basu iya ba" Tasowa Sudais yyi ya dawo kusa da ita shureim ma ya sauka kan kujera ya bi twin din nasa, Sadeeq yace "Lallai, yayarku kadai ku ka sani kenan koh" Shaheedah tace "Dama mana" daki Sadeeq ya wuce, Shaheedah kuma ta nufi fridge ta bude ta dauko masu drink da ruwa ta daura kan tray da cups uku sannan ta dawo ta ajiye tana kallon khadijah tace "Ban ma san sunan ki ba" Khadijah tace "Sunana Khadijah" Shaheedah tace "Ayya, ni kuma Shaheedah" Khadijah na murmushi tace "It's nyc meeting you Shaheedah" Shaheedah ta mayar mata murmushin tace "You too" abinci ta koma kitchen ta dauko a warmer da plates da spoon, khadijah tace "Lahh wllh mun ci abinci kafin mu taho Shaheedah" Shaheedah ta bata fuska tace "Saboda ke fa na yi girkin" Khadijah tace "Ayya da baki bai kan ki wahala ba, kin ga su ba cin abinci ma suke ba sai dai golden morn ko custard" Shaheedah tace "Toh sai in masu ai akwai custard din din ke sai ki ci wannan" da sauri khadijah tace "Kafin mu fito ba basu suka sha, ko kin yi baxa su sha ba da gaske" Shiru Shaheedah tayi kafin tace "Kenan dai baxa ki ci abincin ba Khadijah" Khadijah tayi murmushi tace "Toh xan ci Shaheedah" Shaheedah tace "Yauwa na ji dadi" daukan yan biyun tayi tace "Ku bar Anty ta ci abinci mu tafi ku gaida Mamata" Khadijah ta kalleta tace "Ayya mama na nan ne" Murmushi Shaheedah tayi tace "Idan kin gama cin abincin sai mu je ku gaisa" daga haka ta wuce da yan biyun dakinta, Shaheedah na rufe kofar tace "Mama dubi yaran nan masu kyau maa sha Allah" warce ta kira da mama dake xaune dakin kan darduma tace "Bakin naki sun iso kenan" Shaheedah tace "Ehh har da kanninta ma ta xo, ga su su taya ki hira xan kai ma sa abinci" Daga haka ta fita ta bar yaran a dakin. K'adan Khadijah ta ci tuwo da miyar ganyen da Shaheedah ta kawo mata, cin abincin take amma gaba daya hankalinta na kan yaranta da bata gani ba kuma bata ji motsinsu ba, tashi tayi daga karshe ta dau warmer din tuwon da miya ta wuce kitchen da su, ta wanke plate din da ta ci abincin da cup sannan ta fito parlor ta xauna, dai dai nan Shaheedah ta fito parlorn tace "Lahh har kin gama Khadijah, ko dai ba ki ci ba" Khadijah ta kirkiri murmushi tace "Aa na ci wllh, bacci suka yi ne?" Ita kanta sai da taji kunyar tambayar, Shaheedah tace "Aa suna gun mama ne, mu je ku gaisa tana daki" tashi Khadijah tayi tace "Toh" sannan ta bi bayan Shaheedah suka wuce dakinta, Shaheedah na shiga tace "Mama xa ku gaisa da khadijah" daga haka ta bar bakin kofar Khadijah ta shigo, tsaye tayi bakin kofar tana kallon matar dake xaune kan darduma su shureim a kusa da ita, lkci daya taji komai nata ya tsaya ta kasa kwakkwaran motsi wajen da kyar cikin tsarkewar murya tace "Ummaa" Sai a sannan matar ta juyo da sauri ita ma jin muryar da ta dade tana muradin sake ji ko da a ranan da xata bar duniya ne, mikewa tsaye tayi tana kallonta cikin wani yanayi tace "Khadijah??" Shaheedah da ta saki baki tace "Lahh mama kin san ta ne dama?" Juyawa Khadijah tayi da sauri hawaye cike idonta ta bar bakin kofar, Kan kace me har ta isa gate ta fice daga gidan hawaye masu xafi na sakko mata, da sauri ta isa bakin titi ta tsayar da adai daita ta shiga, tana jin Shaheedah na kwalo mata kira alamar sun biyota amma taki waigawa tace mai adai daitan ya tafi, har khadijah ta isa gida kuka take cikin Napep kamar ranta xai fita, ta rasa dalilin kukan nata, taji xuciyarta yyi mata rauni ga xugin da ya fara mata, mai adai daitan a tuaninsa rasuwa aka yi mata ya dinga bata hakuri bai ma karbi kudin ba ta shige gida, nan parlor ta xube ta kara rushewa da kuka kamar xata tsaga gidan, Nanny ta fito a rikice ta shiga tambayarta me ya faru ina su Shureim sai a sannan khadijah ta tuna da yaran nata, Nanny duk ta rikice ta mike ta fita ta sake dawowa a rude tace "Khadijah tambayar ki nake ina yaran me ya same su, ina suke" Khadijah ta hade kai da kujera cikin rawar murya tace "Ummata na gani Nanny" Nanny ta tsaya kallonta kamar idanuwanta xa su fito, can ta durkusa kusa da ita da sauri tace "Umma? Ummarki dai? A ina kika ganta" Khadijah ta kara fashewa da kuka tace "A gidan da muka je" Nanny tace "Toh sai ta ce maki me, ko bata gan ki ba?" Nanny bata rufe baki ba sai ga Shaheedah ta shigo parlorn a sanyaye, khadijah na ganinta ta kara hade kai da gwiwa tana kuka a raunane, Shaheedah ta isa kusa da ita ta durkusa a hankali tace "Dama ke ce khadijahr da mama ke shigowa Nigeria saboda tun shekaru uku da suka wuce, dama ke ce khadijahr da mama ke yawan maganar ta a can kasar mu?" Khadijah ta dago hawaye wasu na bin wasu tana kallon Shaheedah, girgixa kai Shaheedah tayi tace "Allah sarki khadijah na samu labarin ki a gun mama tun ban yi aure na dawo kasar nan ba, Khadijah Mama ta shiga wani yanayi bayan rabuwar ku, ta je garurruka da dama na Nigeria tana neman ki, ta dalilin ki mama bata da isashen lafiya har yanxu, Wllh wannan xuwan ma tana sauka Nigeria Kano ta fara xuwa wai ko Allah xai sa ta gan ki, daga kano ta tafi Katsina sannan ta taho Kaduna duk wai ko xa ku hadu kafin ta taho gidana nan Abuja kuma gobe ma take shirin komawa kasar mu" Shigowar Umma parlorn ya sa Shaheedah tayi shiru tana kallonta, kana ganinta kasan ita ma tayi kukan, Umma ta karaso parlorn a sanyaye ta xauna kan kujera kusa da khadijah wasu hawayen na sakkowa idonta, Khadijah ta kasa kallonta ita ma tana hawayen, Cikin sanyin murya Umma tace "Ko da baxa ki saurareni ba Khadijah ina neman gafarar ki, ki yafe min, na maki abinda uwar da ta haife ki baxa ta maki, Khadijah don nace ki tafi ba har xuciyata nake nufin haka ba amma kika yi wucewarki kika saka ni cikin kunci da damuwa, duniyar tayi min xafi barin idan na tuna baki da kowa, ban yi ma mahaifin ki hallaci ba, but what will someone expect from a frustrated Mother, God knows i was frustrated.... Shi yasa nace ki tafi, amma ban taba tunanin xa ki tafi ba" sakkowa Kasa Umma tayi ta durkusa kusa da khadijah tana kuka tace "Ki gafarceni Khadijah.... Forgive me plss" Khadijah ta daura kanta a kafarta tana kuka sosai cikin rawar murya tace "Umma baki min komai ba, nima ki yafe min, I know i failed you, amma ba laifina bane Umma, ni ban taba iskanci ba, I was raped...." Umma ta dagota ta rungumeta tana controlling nata kukan tace "I thought as much daughter, na yanke hukunci cikin fushi da tashin hankali ne, na yarda da tarbiyar da na baki, Allah ya saka maki koma waye yyi maki wannan aika aikan, shi ma xai ga sakamakonsa tun a nan duniya" Sosai Nanny da jikinta yayi sanyi tayi murnan haduwar Khadijah da ummarta, ta dinga goge hawayen da ya ki tsaya mata tana gode ma Allah da ya bayyana ma marainiyar ummarta, Shaheedah da duk jikinta yyi sanyi ita ma ta ji dadin reunion din Aminiyar mahaifiyarta da step daughtern ta after three good years. Shaheedah ce ta fita karbo su sudais gun Sadeeq dake mota bai shiga gidan ba, a hankali tace "Dear kaga for ur sake, mama will be happy once again, tayi reuniting da daughter dinta" murmushin karfin hali yyi yace "Sure, but am still confuse ban gane komai a nan ba fa, khadijah dai nasan gidan wan mahaifinta is few houses away from ours, so ban san kuma meye relationship dinta da mama ba" Shaheedah tayi murmushi tace "It's a long story, idan mun koma gida xan baka labarin dear" Sai kusan bayan Isha Sadeeq ya dawo daukan Shaheedah, Khadijah taki yarda Umma ta bi su don gani take kamar baxa ta sake kara ganinta ba. Da daddare suna xaune kan gado wajen karfe daya su Shureim na jikin Umma sun yi bacci, khadijah na bata labarin rayuwar da tayi bayan ta bar gida, tun farkon labarin har ta kawo karshe Umma kuka take, duk jikinta yyi sanyi don ta san duk ita ja ma khadijah duk abinda ya sameta, shiru ta yi tana tunanin me xata ma sudais kuma a ina xa ta gansa, khadijah da ke share hawayen ta cikin raunin murya tace "Umma har yau bai kara dawowa ba, i will never forget him in my life..." Umma ta jawota jiki tace "In sha Allah xai dawo wataran, he will come back to you daughter" Kai kawai khadijah ke gyada mata a xuciyarta tana addu'ar Allah ya gwada mata wannan rana, Umma ta katse silence da ya biyo baya tace "A ranan da kika tafi Khadijah babu inda ban fita nemanki ba tun ina yi da kafa har na koma abun hawa, sai bayan isha na dawo gida a lkcn ina addu'ar Allah yasa kin dawo sai na ga akasin haka, na shiga tashin hankalin da bana fatan

Please Login or Register in order to submit comment