Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kan jiddah duk ya daga mana hankali shi aure amma lkci daya kinga kuma abinda yyi, ni na haifesa ba shi ya haifeni ba don hka I will fish out what he is up to soon" ita dai Anty Maryam bata ce komai ba sai kallon yayarta take. Sudais na barin gidan ya tafi can gidansa, Khadijah na kitchen tare da Mama suwaiba suka ji an shigo parlorn, fitowa tayi tana ganinsa ta turo baki, ya karaso parlorn ya xauna yana idonsa a kanta, ta sunkuyar da kai ta isa kusa da shi ta xauna a kasa, yace "How are you?" Kin cewa komai tayi, ya d'an yi murmushi ya dau wayarsa yana danna, a hankali tace "Ina yini" ya kalleta yace "Ban yini ba" kamar xata yi kuka tace "Ni ban san me nayi maka ba" yace "Na kawo maki abu kince baki so mana" xaro ido tayi tana kallonsa tace "Ni??" Yace "Ehh" murmushi tayi tace "I don't knw how to thank you that day, that was why...." Hawaye cike idonta ta kare maganar, Kallonta kawai yake bai ce komai ba. Haka nan rayuwa ya ci gaba da kasancewa bayan dawowar sudais Nigeria, duk safiya, rana har da daddare xai xo ganin khadijah, kayan ciye ciye yake xuwa mata shi idan xai xo da daddare wani lkcn shi ma ya ci abinda xai ci a gidan, ita dai Mama suwaiba na son sanin me ya janyo bai kwana gidan amma bata san wa xa ta tambaya ba tunda ba wani hira can suke yi da Khadijah ba, toh ko don tana da ciki ne yake haka, tambayar da ta dinga yi ma kanta kenan har hakan yasa ta d'an fara jin haushin sudais din, rana daddaya ne xai shigo gidan ba tare da kayan baby ba, xuwa yanxu irin siyayyar kayan baby da yyi mata sai ayi xaton yara goma xata haifa, komai ya gani ya Burgesa sai ya daukar mata. A haka har watan haihuwar Khadijah ya tsaya, mama suwaiba bata yi kasa a gwiwa ba wajen bata taimako irin na gargajiya don tausayi take bata, kusan duk yamma sudais sai ya lallaba Yusuf sun je gidan kawai don ya dubata, har ransa yake fargabar kar abu ya sameta, wani sanyi tayi gaba daya a kwanakin ko da yaushe a kwance xaka ganta, idan ya tambayeta ko akwai inda ke mata ciwo sai tace babu ko ina. Ranan Sunday da sassafe ya shirya ya fito parlor yana kallon Mami dake dinning yace "Mami xan fita in dawo" tace "Ranan lahadin ma?" Murmushi yayi yace "Mami it's urgent ne, kuma akan..." Katse sa tayi tace "Aliyu" ya dago da sauri, bata fuska yayi yace "Mami wllh duk kika ce min Aliyu sai gabana ya fadi, cos u always call that name when serious" ta masa wani kallo tace "Toh da meye sunan naka?" Yar dariya yyi yace "Sudais mana" tace "Ni na sa maka sudais?" Dariya yyi sosai yace "Ni na sa ma kaina Mami Aliyun sunan tsoffi ne I...." Ta katse sa tace "What ever.... kaje duk inda xaka ka dawo ka sameni in sha Allah gobe xa a kai kayan can da kasa nayi jere da su a daki" yace "Allah ya kai mu Mami" daga haka ya fice daga parlorn, gidansa ya nufa direct. Mama suwaiba na kitchen tana aiki, bai jira sun gaisa ba ya wuce daki, xaune ya ga khadijah ta takure waje daya, Ya durkusa kusa da ita da sauri yace "Are you okay Amira?" Ta girgixa masa kai da kyar, da damuwa yace "What's wrong? Kina jin ciwo ne jikin ki?" Karfin halin nuna masa bayanta tayi, yace "Yana maki ciwo?" hawayen da ya gani idonta ya rikitar da shi lkci daya ya dagota yace "Let get to the hospital....." Kwace kanta tayi ta koma ta durkushe a wajen tana rintsa ido tace "Ya daina" Allah ma yasan daurewa kawai take, ga ciwon kamar ana kara mata take ji, bata san lkcn da ta sakar masa kuka ba a hankali tace "Wayyo ka taimakeni plss" bai sake saurararta ba suka fita dakin, Mama suwaiba bata ma san sun bar gidan ba tana kitchen, har suka isa asibiti Khadijah bata sani ba duk ta rikice, wani asibiti me tsada ya kai ta banda Wanda Yusuf ke aiki, bbu bata lkci nurses suka amsheta da wani likita, yanda Sudais ya daga hankali sai ka rantse ance masa mutuwa xata yi, khadijah bata yi fatan kara experiencing kwatankwacin irin wahalar da ta sha na labour ba har ta bar duniya, tun da suka je take wahala amma shiru, Sudais ya kira Yusuf ya sanar da shi suna asibiti, Yusuf yace "Me yasa baka kawo ta asibitin mu ba" Sudais yace "Just" Yusuf yace "Toh wani asibitin ku ke?" Sudais ya gaya masa, tabe baki Yusuf yyi yace "Kudi ya ma yawa ne, any way idan ta haihu ka kirani" Sudais ya katse wayar ya jinginar da kansa da kujera yana mai yi ma khadijah addu'a a xuciyarsa, bayan awanni biyu ya sake kiran Yusuf, Yusuf yace "Ya? is she delivered" a hankali Sudais yace "Har yanxu" Yusuf yace "Toh fah, ko dai cs xa ayi mata, dama am thinking it will be difficult ta haihu da kanta, any way bari in taho yanxu" bayan wani lkci Yusuf ya xo, dariya Yusuf ya shiga yi ganin yanayin sudais yace "Kaiiii... To ai ko jiddah ke labour sai haka bawan Allah" Shi dai Sudais bai tanka sa ba, yawanci likitocin asibitin duk Yusuf ya san su, don haka har labour room yaje gun khadijah, ya ji tausayinta ba kadan ba ganin irin dauriyarta, baxa ka taba cewa haihuwar fari xata yi ba tsabar karfin halinta, bayan wani lkci Yusuf ya bar asibitin bayan ya kwantar ma da Sudais hankali yace labour kawai take babu wani matsala, wasa wasa dai shiru ake ji wanda hakan yasa likitocin suka kira Sudais office nan suka nuna masa it's better ayi mata Cs kada yaran da ita kanta su samu matsala, kusan ba da son ransa yyi signing takardar da aka basa ba, bayan wasu yan mintuna aka fitar da Khadijah labour room xuwa Theatre, anan kuma aka yi nasarar ciro mata boys dinta, sai dai sun jigata kamar yanda ita ma ta jigata. Khadijah ta bude ido a hankali ta ganta kwance wani ward, Mama suwaiba dake gefenta ta sakar mata murmushi tace "Sannu Amira, Allah ya baki lafiya" tashi xaune take son yi taji kamar an danneta ta kasa tashin, Mama suwaiba ta mayar da ita ta kwantar tace "Aa kinga ba ki da lafiya ki yi kwanciyar ki kawai kinji" sai a snn taji wani axaba tun daga cikinta har xuwa kafafuwanta, wasu hawaye suka shiga sakko mata cikin rawar murya tace "xafi nake ji" fita Mama suwaiba tayi sai ga ta ta dawo da likita, likitan ya duddubata ya mata Allah ya sauwake sannan ya fita, Nurse ce ta shigo ta mata allura ta fita, bayan fitar ta sai ga Sudais ya shigo khadijah ta bude ido tana kallonsa, ya karaso gefenta cikin sanyin murya yace "Amira...." Bata iya ta amsa sa ba, a hankali ya sa hannunsa cikin nata cikin sanyin murya yace "Be strong Amira, you will get better in sha Allah.." Hawaye ya sakko idonta sai dai bata ce komai ba, ya sakko da fuskarsa dai dai nata yana murmushi a hankali yace "Baki tambayi yaran ki ba ko bakya son su?" Ta gyada masa kai, shiru yyi yana kallonta, can yyi murmushi yace "Toh sai ki bani su" Murya can kasa hawaye na xuba idonta tace "Na baka" ya fadada murmushin fuskarsa yace "Sure?" Throughout ranan Sudais was by her side tare da Mama suwaiba, Yusuf ma ya xo yyi mata barka ya wuce, ba a nuna mata yaran ba kuma bata tambaya ba har ta sa a rai kila ma mutuwa suka yi wanda tunanin hakan yasa mata nutsuwa sosai don har ga Allah bata ma son ganinsu, haka kawai taji bata san su, Sudais dake lura da cewa she was so depressed ya dinga kokarin ganin ya sa ta walwala sai dai ta kirkiri murmushin karfin hali, sallah kadai ke sa shi ya bar gefenta, tun karfe shidda mama suwaiba ta koma gida dauko kaya, duk kiran da aka dinga ma sudais a waya kin dagawa yyi daga karshe ma ya sa wayar a silent, A daren ranan bayan sudais yaje sallar magrib da ya tashi dawowa ya shigo rike da daya daga yaran wata nurse na biye da shi da dayan, tun da suka shigo khadijah ke kallonsu, yana murmushi ya ajiye babyn a gefenta, sosai gabanta ya fadi ta dinga yi ma jaririn wani kallo ganin kamar Aliyu yyi kaki, babu abinda new born din ya mance na ubansa tun daga haske, hanci, kai har bakinsa... Nurse din ta ajiye mata daya carbon copy din yaron dake gefenta kusa da d'an uwansa tana murmushi tace "Congrat mum twins, Allah ya raya su" daga haka ta fita, a hankali Sudais yace "Ain't they cute? I mean the innocent new souls" khadijah bata san lkcn da ta fashe da kukan takaici ba cikin rawar murya tace "Don Allah ka tafi da su, wllh bana son su, ni dai bana son su ka maida masu su" kuka take sosai kamar xata shide, ganin haka Sudais ya mike ya dau yaran gaba daya ya fita da su dakin.

Sudais na dawowa dakin ya dinga kallonta har ya iso kusa da ita yace "Me yaran suka maki da kike cewa baki son su Amira" kin cewa komai tayi, ya ja kujera ya xauna yyi shiru, bayan kusan minti goma wayarsa ya fara ring dauka yyi ya duba yaga Mami ce, yau ta kirasa yyi sau hudu duk bai dauka ba, ya mike yana kallon khadijah da ta lumshe idonta yace "Mama xata dawo yanxu, ni xan je gida Mami na ta kirana, gobe da safe xan xo kin ji?" Bude ido tayi tana kallonsa yace "Be strong, kuma kar ki sake kuka plss" gyada masa kai kawai tayi ya juya ya fita. Bayan fitarsa da yan mintuna mama suwaiba ta shigo, sannu ta dinga yi mata, ta xauna kusa da ita tace "Kin ma ga yaran naki kuwa Amira" Khadijah ta hade rai tace "Ehh" daga haka ta rufe idonta, ana yin isha mama suwaiba tayi sallah a nan ward din da bayan ta shimfida dankwalinta a kasa, bude kofar ward din aka yi nurses biyu suka shigo da babies din Khadijah ta rufe ido da sauri, kan gadon jariran dake kusa da na khadijah suka kwantar da su, daya daga nurse din na kallon Mama suwaiba da ta mike ganin yaran tace "Xa a iya ba su nono yanxu idan suka bukaci haka" daya nurse din na nuna mata babyn kusa da ita tace "Wannan shine Hasan, na kusa da shi kuma Hussain" Mama suwaiba tace "Maa sha Allah, Allah ya raya mana su" nurses din suka amsa da amin sannan suka fita, mama suwaiba sai kallon kyawawan fararen yaran take tana murmushi sai dai abinda ke daure mata kai daga Sudais har Khadijah babu wanda taga yaran suka biyo, a ranta tace "Ikon Allah, to ko wa suka biyo su kuma maa sha Allah" kallon khadijah tayi da ta ki bude ido har lkcn, tausayinta ta dinga ji don idan akwai abinda ta tsana shine ayi ma mace operation. Karfe sha daya da wani abu mama suwaiba ta kwanta a spare bed dake Dakin, har ta fara bacci taji kukan jariri, ta bude ido da sauri taga daya ne ke motsi, ta Mike ta daukesa tana kallon khadijah, Bata san Khadijah na jin yaron ba sai dai idonta a rufe yake har sannan, Mama suwaiba da a tunaninta bacci take ta rungume yaron ta xauna, haka mama suwaiba ta dinga lallaba su tana basu ruwa a feeder ganin yunwa suke ji har Washegari da safe. Karfe tara saura sudais ya shigo ward din,sanye yake da farar shirt da black jean yayi kyau ba kadan ba, direct gun babies dake cikin cot dinsu bayan an masu wanka ya nufa, ya dau daya ya lumshe ido ya daura lips dinsa a soft cheek din babyn, juyawa yayi ya kalli khadijah dake bacci, jikinsa yyi sanyi don da alama mama suwaiba ta je gida dauko abu, daga ita sai yaran ne a ward din, nobody to stay with them, banda tsotson baki bbu abinda yaron dake hannunsa yake alamar yunwa ya kalli d'an uwansa shi ma yaga haka yake da bakin, yana ta tsaye dakin bai tashi Khadijah ba mama suwaiba ta shigo bayan sun gaisa yake tambayarta ko Khadijah ta fara basu abinci ne, Mama suwaiba tace "Aa bata basu ba da nayi mata magana daxu ce min tayi cikin ta na ciwo har na fita na kira wata nurse, tun jiya ruwa kawai nake ba su" Sudais bai ce komai ba ya xauna saman kujera, bayan wani lkci yace "Toh ita ta fara cin abinci ne?" Mama suwaiba tace "A'a ga shi nan dai kunu ma na je gida na dama mata, cewa likitan yyi shi kadai xata iya sha anjima, toh kafin ta tashi shine naje nayo" yace "Toh sannu mama" ya d'an jima a dakin kafin ya bar asibitin kuma har lkcn khadijah bata tashi ba. Wasa wasa yau kwanansu uku a asibiti amma khadijah taki ba yaran nono, da farko cewa take cikinta na mata ciwo baxata iya ba sudais ya siyo masu madara na jarirai mama suwaiba na basu, har abun ya fara daure ma mama suwaiba kai don har sannan khadijah taki daukan yaran ta, tunda tayi kokarin bata su sau daya ta ki amsan su ta kuma ga kamar ranta ya bace bata sake bata su ba. Satinsu daya da kwana daya aka sallamesu asibitin bayan Sudais ya biya bill din, duk yaran na hannun mama suwaiba don khadijah bata amshi ko daya ba, ya bude motar bayan sun isa gida ya amshi dayan yaron hannun Mama suwaiba, ta fito rike da dayan ta nufi cikin gida, kallon khadijah yyi da ta fito ita ma ya mika mata yaron, dauke kai tayi ta bar wajen da sauri tace "Ni dai baxan iya ba" Wani kallo ya mata da mamaki yace "Kee" ta juyo tana kallonsa, mika mata yaron yyi fuskarsa daure yace "Karbesa" kamar xata yi kuka tace "Xai iya faduwa pa" yace "Ya fadi" ganin yanda ya tsare ta da ido ta karbi yaron hawaye har ya kawo idonta ya yi gaba ya bar ta gun tsaye, a hankali ta bi bayansa ba tare da ta bari ta kalli yaron hannunta ba, sudais ya karbi yaron hannun mama suwaiba ya wuce bedroom da shi khadijah ta bi bayansa, gefen gado ta xauna ta ajiye yaron kan gadon, yana kallonta yace "Basu abinci yanxu" da sauri tace "Ai naga sun sha madara fa, ni....." Katse ta yayi yace "Baki son yaran nan koh Amira?" Ta kallesa ta gyada kai a hankali kamar xata yi kuka, yana mata wani kallo yace "Dama kin san baxa ki so su ba kika yarda kika haifo su duniya, me yasa baki amince an raba ki da su tun a ciki ba?" Cikin rawar murya tace "Toh ai babu kyau" yace "Ohk.... abinda kike masu yanxu da kyau kenan" shiru ta yi hawaye na sakko mata, yace "Kin san Allah idan baki basu abincin su ba am leaving here now, kuma wallahi babu ruwana da ke, are you this wicked?" da sauri tace "Kayi hakuri xan basu" tana magana hawaye na xuba idonta don ita har ranta da gaske bata son yaran, Sudais yace "Toh ba su yanxu" tana share hawayen idonta ta fara bude zip din rigarta xata sauke rigar yayi saurin dakatar da ita "Kee haka aka ce maki ake yi?" Kamar xata yi kuka tace "Toh ai ban iya ba" juyawa yyi ya fita sai gashi tare da mama suwaiba, yana tsaye ta gwada mata yanda xata yi tana dariya sudais ya juya ya bar masu dakin, har da kukanta ita wai xafi take ji, Mama suwaiba ta dinga lallaba ta don ita ma tausayin yaran take ganin basu samu gatan shan nonon uwarsu ba tun da suka fito duniya, da kyar ta amince ta ba dayan ma, a ranta kuwa tasan shine farkon shan su kuma shine karshe don ita dai baxata iya ba. Kwanansu biyu da dawowa daga asibiti Sudais ya shigo dakin da Khadijah take da safe, xuwan sa kenan gidan, farar Gezna ce jikinsa dake ta kyalli, waya ne kare kunnensa ya shigo dakin yana magana amma can kasa kasa, ya nufi gun babies dake kwance yana kallonsu kamar yanda Khadijah da ke tsaye gaban madubi ke ta kallonsa tun shigowar sa, Sudais is just the real definition of handsome, duk da wayar da yake gaba daya hankalinsa na kan yaran dake ta tsotson baki yana murmushi, xuwa jikin khadijah yyi kwari sosai don har aikin ya gama warkewa, sosai kirjinta suka ciko har ciwo suke mata amma taki ba ma yara abinci, yanxun ma mama suwaiba ce ta shigo da su ta kwantar ko xata tausaya masu ta basu nono, Sudais ya mayar da wayarsa aljihunsa ya juya ya kalleta tayi saurin dauke kanta, ya xauna gefen gadon yace "I know baki abinci ba yau" ba tare da ta kallesa ba tace "Na basu ka tambayi Anty" bai ce komai ba, bayan wasu mintuna yace "Wani sunan za a sa ma babies din?" Still taki kallon inda yake tace "Nima ban sani ba" yace "Baki sani ba kuma?" Tace "Ko wanne ma ka sa masu" yace "A'a ke xaki xaba da kanki ba yaran ki bane" kin cewa komai tayi, yace "Am talking to you Amira, kuma akwai inda xa ni" ta langwabar da kai a hankali tace "Toh Muhammad da...." Sai kuma tayi shiru, yace "Da wa?" A hankali ta saci kallonsa tace "Kai" ya buda ido sosai yace "Ni kuma?" Tace "Ehh, ur name" murmushin sa mai kyau yyi yace "Aa ki xabi wani sunan dai Amira" hawaye ya kawo idonta tace "Ni kai nake so a sa" Yace "Aliyu kike nufi?" Ta gyada masa kai, wani murnushin ya sake yi yace "Sunan mahaifinsa dai kenan" da sauri khadijah da gabanta yyi mugun faduwa tace "Noo, Brr Aliyu Sudais nake nufi not Dr Aliyu Turab" Shiru Sudais yyi yana kallonta, mikewa yayi bai sake cewa komai ba ya fita yana murmushi. Raguna biyu sudais ya yanka ma 'yan biyun, Hasan aka sa ma Muhammad, Hussain kuma Aliyu, kusan duk sadaka yyi da daya ragon ya bar ma khadijah daya mama suwaiba ta gyara mata, ita dai mama suwaiba kanta ya gama daurewa taga babu me xuwa barka tun dawowarsu, shiru kuma ba xancen taron suna gashi har an gyara rago, Yusuf kadai ya xo gidan a ranan, nan xuciyarta ya fara wani tunanin anya wa en nan ma'aurata ne ma kuwa, don ga dukkan alama wnn dai ba aure bane domin kuwa tun xuwanta bata taba ganin Sudais ya kwana gidan ba, amma meye tsakaninsu? Sudais na bedroom dinsa a can gidan Abbansa da yamma, shigowarsa gidan kenan tun safe da ya fita, Anty Maryam ce ta shigo dakin ya juya yana kallonta sannan ya gaisheta ta amsa da murmushi tace "Kasan an kai ma jiddah kaya kuwa Aliyu, and sati biyu aka sa bikin from today" kasa ce mata komai yyi da farko baki bude, can yace "Amma dai ni babu wanda ya gaya min, sati biyu kuma Anty, what's d rush for, ni Wllh jiddar nan maganar gaskiya ta fitar min a kai, don Allah ni dai Anty...." Dafe kansa yyi yace "Ohh God, sati biyu fa ku ka ce?" Tabe baki Anty Maryam tayi ta juya ta bar masa dakin, zaunawa yyi gefen gado yana rike da kansa, can ya dago ya tashi ya fita, dakin Mami ya shiga ya sameta tana waya ya tsaya ya jira har ta gama sannan ya marairaice yace "Mami Anty Maryam ke ce min...." "Saura sati biyu bikin" Mami ta karasa masa tana masa wani kallo, tsaye yyi yana ta kallonta can ya juya ya fice a dakin, Mami ta fito ita ma ganin dakinsa ya koma ta fita compound, gun drivern gidan ta nufa, ya gaisheta da ladabi ta amsa masa tace "Musa, ina son ka min wani d'an aiki ne don Allah" with respect yace "Toh Hajiya aikin me xan yi" Tace "Ina son idan sudais ya fita gidan nan ka bi sa ka gano min ina xa shi, ko yanxu ko anjima ko da daddare" da mamaki yace "Barrister?" Tace "Shi" yace "Toh in sha Allah Hajiya" Har ta fara tafiya ta juya tace "And be very very careful you knw who you are dealing with"


Sorry it's nt much, long chappy ltr in sha Allah.

Mami na shiga parlor Sudais dake tsaye kusa da window din bedroom dinsa ya sauke curtain din ya bar jikin windan ya rungume hannayensa kamar me naxari, can kuma ya nufi study area dinsa ya ja kujera ya xauna, then... What's Mami telling Musa? Ya kusa minti talatin xaune yana jiran ya ji fitar musa a gidan da mota domin kuwa hakan kadai xai sa ya cire wani xargin da yake a xuciyarsa, amma har kusan magrib shiru Musa bai fita ba, Sudais ya tabe baki ya mike ya tafi ya dauro alwala ya dawo ya xauna, lumshe ido yyi duk jikinsa yyi sanyi "Jiddah? Sure yasan ya so jiddah ba kadan ba a da can, but he just don't knw what came over him all of a sudden yaji kawai ta fice masa a kai, gashi dai babu abinda tayi masa, ko don an takura sai yyi auren ne yake jin hakan, gaba daya ya ma rasa tunanin da xai yi a lkcn, toh shi yanxu ya xai yi da Khadijah da little babies dinta idan aka tilasta sa yin aure yanxu, bude ido yyi ya xauna da kyau yana naxarin idea din da ya xo masa, ya kama mata wani apartment din kenan? Shafa kansa yyi yana kara naxarin shawaran a ransa, jin xa a tada sllh ya mike ya nufi kofa ya fita dakin, ana idar da sllh ya dawo daki ya dau makullin motarsa ya fita, ce ma Mami dake parlor a xaune yyi sai ya dawo ba tare da ta kallesa ba tace "Allah ya kiyaye" yana shiga motarsa ya fita compound din bayan mai gadi ya bude masa gate, sai da ya kusa isa titi ya yaga musa ya danno kan mota xai fito gidan a guje ta madubinsa, Sudais ya hau kan titi driving slowly yana yana kallon musa dake can baya ta madubi, a hankali shi ma musan ke driving din, Sudais yyi murmushi ya kara gudun motar sai yaga shi ma ya kara, gidansu Yusuf ya nufa musa na biye da shi a baya har lkcn yana parking a waje ya fito ya ga musa nesa da shi a motar yyi kamar bai gansa ba ya shiga gidan, bai samu Yusuf a gida ba duk da ba gidan yyi niyyar xuwa ba, ya tsaya har suka d'an yi hira da mahaifiyar Yusuf sannan ya mata sallama ya wuce, gida ya koma yyi parking a waje ya fita ya shiga gidan, tare da mai gadi ya ga musa a xaune yana kallonsa yace "Same ni a waje musa" daga haka ya fita gate din, Musa ya mike ya bi bayansa sai dai fa ya tsorata, Sudais na kallonsa da kyau yace "Hajiya ce ta sa ka bi ni ka ga inda xa ni daxu?" in ina musa ya fara yi, Sudais ya daure fuska yace "Malam amsa min tambayata" gyada kai musa yyi yace "Kayi hakuri barrister umarnin da Hajiya ta bani kenan" Sudais yace "Ohk naga alama, this shud be ur 1st and last, ko da wasa ka kuskura ka sake bin bayana a mota I won't take it likely with you" daga haka ya shiga gida ya bar sa tsaye gun.

Please Login or Register in order to submit comment