Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

don't wish that for her, and her condition don't need that, shi yasa na hakura domin farin ciki da kwanciyar hankalinta, nasan I am not making a mistake giving up for you because I know you love her also, and u love ur son...da dadewa na yarda da cewa abinda ya faru tsakanin ku tsautsayi ne, it's not ur doing coz you are too responsible for that, u are responsible in every aspect, you are really a gentleman, ur family are just good also, kawaicin ka ma abun dubawa ne, I've studied you for long...." Aliyu ya runtse ido maganganun Sudais na yawo kansa kamar a mafarki, lkci daya ya bude idanuwansa, kawai ya rungume sa hawaye na xuba idonsa ya kasa cewa komai, Sudais da ya ji xuciyar sa ya masa rauni yyi karfin hali yace "It's my pleasure, and a Suggestion from Dr Ayman.... nayi ma Khadijah wanda ya fi wannan ma, don haka nasan ban fadi ba, But ina neman alfarmar ka bar mu mu din ga xumunci sosai coz I love the little boy..." Cike da karfin hali hawaye na sauka idon Aliyu yace "How will I repay you Barrister..." Sudais yayi murmushi shi ma hawayen suka xubo masa a hankali yace "Ta hanyar rike Amira da amana, be her father be her mother, be her happiness, and finally prove to her that u are innocent, kadarrar ku ce a haka" Khaleel ya sauke idanuwansa a hankali ya juya ya shiga gida ganin he might not stand it anymore.... 😭



Lunch, very light also, kar mutum yaje yana bacci da rana😎

Umma kasa kwakkwaran motsi tayi bayan ta gama jin bayanin Sudais ta kasa daina kallonsa, jikinta yayi sanyi sosai, tsoronta daya a lkcn khadijah, ko ya xata dau batun nan, Wai Aliyu? Kallon Khaleel dake xaune shi ma tayi, ya d'an yi murmushi ganin damuwar dake fuskarta yace "Umma you need not to worry, I know you might be thinking of how khadijah will take this, but I think ba lallai sai an fadi mata ba she will see for her eyes, and surely nasan she have a very soft spot for Aliyu, the problem is that she is confuse, sannan one thing about her is that bata mance abun sharri da aka mata ko ya yake which is wrong, she need counseling Umma...." Murmushi Sudais yyi a hankali yace "Sure, gaskiya doctor ya fada Umma, fatan Allah yasa ke dai kin fahimce ni, nayi abinda naye ne saboda future, I really don't want anything that will hurt her again in life, she have had enough... duk Allah ne mai tsara komai" a sanyaye Umma tace "I am really proud of u both, irin ku basu da yawa a duniya Allah ya biya ku da mafificin alkhairinsa, ko wannen ku ya taka rawar gani matuka a rayuwar khadijah, Kun mata abinda dangin ubanta da ni kaina na kasa yi mata, Allah ya saka da alkhairi, and one more thing Sudais ka maida matar ka don Allah..." Sudais ya girgixa kai a hankali yace "Umma I don't think xan maida jiddah, na hakura da ita, Allah ya musanya min ita da mafi alkhairi, may be abubuwan da nayi mata years back kan khadijah ne Allah ya saka mata ta samu damar yi min abinda ta so, tun da na aure ta take wahal da ni, I have had enough..." Umma tace "A'a ba ayi haka ba, kayi hakuri don Allah, ko albarkacin yarinyar nan dake tsakanin ku" Dai dai nan Baby ta fito ta kawo masu abinci kamar yanda Umma ta umarce ta kafin ta taho gun su, ajiye abincin tayi ta kasa kallon Sudais don ba karamin kunyar abinda tayi masa a waya taji ba daxu barin da ta ga bashi da laifi, Kallon Khaleel tayi daga karshe tace "Ina yini" yace "How are you" ta mike tace "Alhmdllh" daga haka ta juya ta wuce Sudais ya bi ta da kallo ganin bata gaishesa ba, Khaleel na kallon Umma yace "And lastly Umma, I think I've found out dangin mahaifiyar khadijah if I am not mistaken in sha Allah" daga Umma har Sudais kallonsa suka dinga yi ko kiftawa babu, ya sauke kansa kasa a hankali yace "But I won't reveal that to her sai tayi settling gidan mijinta, ta kwantar da hankalinta, still xa mu je can gidan dake Umma duk da su ma ban ce masu komai ba tukun, but babu tantama they are her mother's family in sha Allah" Mumy ba karamin sanyi jikinta yayi ba jin sadaukarwar da Barrister yayi ma Aliyu, she couldn't even utter a word, abun ya mugun daure mata kai, Abbansa shi ma ya jinjina lamarin sai dai abinda bai ji dadi ba shine yin gaban kansu da suka yi babu shawara da kowa, and a whole daurin auren 1st son dinsa baya gun, but all the same he is happy for his son cos he is always after his happiness kuma ya bukaci number Barrister Sudais, Mumy na ta kallon Aliyu da har sannan mood dinsa isn't encouraging da damuwa tace "What's it again Abuturrab, ain't you happy" ya dago ya kalleta da kyar yace "Mumy bata sani ba fa, and I don't know how she will take this, ba so na take yi ba, tana kulani ne kawai saboda kids din, albarkacin su nake ci" A hankali Mumy tace "Then you will teach her to love you son..." Bai iya yace komai ba, bayan few seconds ya mike ya dawo kusa da ita ya xauna yana facing dinta, har lkcn idanuwansa basu dawo dai dai ba, cikin sanyin yace "Mumy me xan yi in biya su?" Shiru Mumy tayi tana kallonsa don tasan su wa yake nufi, ta d'an yi murmushi tace "Zumunci mai karfi da su is enough son" Aliyu ya sauke idonsa kasa a hankali yana tunanin xumunci yayi kadan ya biya both Dr Ayman and Barrister Aliyu, dafa sa Mumy tayi tace "That's just it Abuturrab, mutanen nan biyu ka rike su a rayuwa, kaga riban hakuri... Da ka ci gaba a yanda ka fara da farko kana tunanin Barrister xai ga cancantar bar maka ita? Of course no, shi sa nake yawan ce maka you just have to be patient in everything in life" Bai dai ce komai ba, tace "Do what you are suppose to now, na kira su Siyama xa su je can gidan naka su yi abinda ya kamata, don xuwa anjima xa su kai ta can gidan, mun yi waya da Ummarta yanxu" Har sannan Kamar yanda khadijah bata san da wanda aka daura mata aure ba haka baby ma bata sani ba, gashi dai ana ta shirin tafiya da amarya wajajen karfe biyar, Umma duk ta kasa samun nutsuwa da ta tuna khadijah fa bata san da Aliyu aka daura auren ba sai taji gabanta ya fadi, tsoronta ma kada ciwonta ya kara tashi, daga karshe ta sa aka kira mata Baby bedroom dinta, Baby na kallonta tace "Gani Umma" cikin sanyi Umma tace "Khadijah kin san da wanda aka daura auren nan kuwa?" Girgixa kai Baby tayi da confusion tana kallonta, a sanyaye Umma tace "Yayan ki" still khadijah tayi tana kallon Umma baki bude ta kuma kasa cewa komai, a hankali Umma tace "Ban san yanda khadijah xata dau batun nan ba, am afraid...." A hankali baby ta dauke kanta tana sake nanata sunan yayanta a xuciyarta, to how comes??? Da kyar ta kalli Umma tace "Barristern fah?" Umma tace "Shi ya bar masa... For some concrete reasons which I found out to be nothing but the truth, Aliyu shi ne kadai rufin asirin khadijah da yaron nan, toh amma ba lallai ta gane hakan ba, ban san ta ina xan fara sanar mata ba" Baby ta sauke ajiyar xuciya, lkci daya jikinta yyi sanyi tace "Umma kar a gaya mata, she shud just see for her self, xasu sasanta kansu can din" Umma tace "I thought as much... Haka yawanci kowa ke ce min" Tagumi baby tayi ta rasa wanne xata yi a ciki, farin ciki ko bakin ciki, Umma tace "Tashi ki je ku gama shiryawa lkci na wucewa khadijah, har an gama kai kaya can gidan" Baby ta mike jiki ba kwari ta fita, tana komawa daki ta ci gaba da shirya ma khadijah few abubuwan da tace mata, Shureim ne ya shigo dakin da shadda irin wanda Sudais yasa ranan da hularsa, sai sheki kayan suke sun masa kyau sosai, tun wayewar gari sai sannan khadijah ta gansa, ta xaunar da shi kusa da ita tana kallonsa a hankali tace "Where have you being today?" ya wara mata ido yace "Uncle ne ya tafi dani since, mun dawo yanxu, Anty daxu Umma tace min baki da lafiya, me ya same ki" Shiru tayi bata ce komai ba, Ganin yanda yake kallonta ta rungumosa a hankali tace "Ae na samu lafiya yanxu" yace "Anty kinyi kyau sosai" Murmushi tayi ta ja hancin sa tace "Kai ma kayi kyau sosai, wa ya kawo maka kayan nan" Yace "Uncle, shi ma ya sa irin nawa, na tambayesa Ina na Sudais yace ya ajiye masa nasa" Shiru khadijah tayi tana kallonsa, ya kamo hannunta yace "Anty what are they celebrating today?" Baby dake gefe sai kallonsu take ta dauke kanta a hankali, sai a sannan tayi mugun ganin dacewar abinda Barrister Sudais yyi, shkkn sai su hadu su rungumi d'an su, khadijah ta sunkuyar da kanta tuna irin xagin da Jiddah tayi ma yaron daxu ta kirasa da shege mara uba, hawaye ne ya kawo idonta sai dai bata bari ya gani ba, Jikin baby yayi sanyi don duk tana lura da ita, ta juya ta ci gaba da abinda take, Shureim ya taho gunta yana gaisheta, ta rungume sa murmushi dauke fuskarta tace "Har kun dawo boy" ya gyada mata kai, shidda saura motocin tafiya da amarya suka iso gidan, nasiha sosai Mum din sadeeq da wata frnd din Umma suka yi mata, Kanta a kasa take saurarensu hawaye na sakko mata, ita kam bata samu gatar nasihar Uba ba, kalma daya Umma ta iya yi mata a lokacin bayan su Umman sadeeq sun gama "Allah maki albarka" hakan yasa khadijah taji dadi sosai, Shaheedah ta daga ta suka nufi kofa baby da wata kawarta na biye da su a baya, banda kuka babu abinda khadijah take duk jikinta yayi sanyi, duk aka bi ta da kallo cike da tausayinta, Baby da frnd dinta Hafsat sai mahaifiyar Shaheedah wato aminiyar Umma suka shiga mota daya da khadijah, sauran yan rakiyar Amarya suka shiga sauran motocin, Jikin baby bai gama sanyi ba sai da taga sun iso gidan yayanta, duk tausayin khadijah ya cikata a xuciyarta ta dinga addu'ar Allah yasa shock din ganin Aliyu as mijinta baxai yi affecting dinta sosai ba, dad'd'adan kamshin turaren wuta ke tashi ta ko wani angle a gidan, ga sanyin ac, parlorn so chill, har lkcn kuma su Siyama da kawayensu da frnd din Mumy suna gidan suna jiran Amarya, Su Hajiya Sajeedah suka wuce da khadijah well furnished bedroom dinta, ita dai har sannan fuskarta a rufe yake bata san kalan gidan ba gashi tun shigowar su gabanta ke faduwa ga hawaye ya ki tsaya mata duk jikinta yayi sanyi, ana xaunar da ita gefen gado ta riko baby cikin rawar murya tace "Stay beside me plss don't leave me" a sanyaye baby ta xauna kusa da ita tana rike da hannunta, khadijah ta rike ta gam ta kwanta jikinta. Sai kusan bayan isha duk aka watse gidan har su Siyama suka wuce, sai da su Hajiya Sajeedah suka kara mata nasiha kan xamantakewar aure kafin su wuce su ma, gidan ya rage daga ita sai baby da Hafsat, kuka kawai khadijah take don tana ganin ko wani lkci jiddah xata iya shigowa gidan, Baby har ta gaji da lallashi tayi tagumi tana kallonta, yau kam tasan yayanta xai sha lallashi, d'an murmushi tayi dai dai lkcn da wayarta ya fara ring, Hafsat ta mika mata taga Aliyu ke kiranta, kallon khadijah tayi kafin ta daga ta kai kunne hade da sallama, shiru ya d'an yi kafin yace "Ku fito sai a ajiye ku gida yanxu" Tace "Toh" kamar khadijah taji abinda aka ce ma Baby tana kallonta a tsorace tace "Waye ya kira ki?" Baby ta sauke idonta tace "Mijin ki, mu xa mu wuce yanxu Iman, Allah ya bada xaman lafiya" khadijah ta fashe da matsanancin kuka tace "Na shiga uku, me yasa baxa ku kwana ba don Allah kar ku tafi, ki bani wayar xan masa magana" dariya ta ba baby amma bata yi ba tace "Gobe fa da safe xan xo Iman" cikin kuka sosai Khadijah tace "Don Allah ki rufa min asiri ki kwana" Baby tace "In dai gidan nan ne wllh baxan kwana ba, gwara ki hakura gobe in dawo, idan kuma kika ban haushi in ki xuwa goben ma, ko a kauye an daina haka kina abu kamar wata yarinya..." Dariya kawai Hafsa take don khadijah ta bata dariyan, Baby ta mike ta hade rai tace "Mu je Hafsah, ji wani abu da take fa kamar yar yarinya, ko yara sun daina haka, balle ita wayayya" Da haka baby ta samu fa fita Hafsat na biye da ita, Ban da kuka babu abinda khadijah take tana kallon kofar har suka fita suka rufe, Baby ta ji tausayin ta har ranta, amma tasan idan ba haka ta yi mata ba sai ta iya ma biyosu, A waje ta tadda Aliyu tare da Sudais a tsaye jikin motar sudais din, da alama su suke jira, Baby tayi kasa da kanta tace "Ina yini yayanmu" yace "Lafiya lau" Hafsat ta gaida Sudais sannan ta gaida Aliyu tayi masa fatan alkhairi a aurensa, murmushi kawai yyi bai iya yace mata komai ba, Sudais yace "Alryt, sai da safe Dr" Aliyu ya kallesa a hankali yace "Baxa ka shiga ba?" Ya bude motarsa yana d'an murmushi yace "Gobe xan xo in sha Allah" Aliyu bai iya yace masa komai ba, can ya kalli Baby yace "Ku shiga xai yi dropping din ku gida" Ta d'an buda ido, Aliyu ya matso kusa da ita da damuwa yace "Did she know...." Baby ta girgixa masa kai a hankali, sauke idonsa kasa yyi, Hafsat ta bude back seat ta shiga, Bayan few seconds ya kalli baby yace "Don't keep him waiting, ki shiga motar ku wuce, sai da safe" A hankali baby tace "Yayanmu wllh kunyarsa nake, daxu da safe na gama tsigale shi a waya I never knew makirci matarsa ta hada masa" Aliyu ya bude ido yana kallonta, ta marairaice tana kallonsa, yace "Ki basa hakuri idan kin shiga motar" shiru tayi, ya gyada mata kai yace "Yea, do that" a hankali tace "Toh sai da safe yayanmu" daga haka ta xaga ta shiga front seat ganin Hafsat baya ta shiga Aliyu ya bi ta da kallo, Tana shiga motar ta rufe ta kasa kallon Sudais, bayan ya tada mota ba tare da ya kalleta ba yace "Good evening" sai a sannan ta kallesa dai dai nan shi ma ya kalleta, Murmushi tayi cike da jin kunya tace "Ina yini" yace "Lafiya lau" a hankali tace "Am soo sorry for what I did daxu da safe don Allah kayi hakuri" kallonta yayi da kyau, sai kuma yyi murmushi yace "Wai dama ke kika kirani?" xaro ido tayi ganin ashe ita kadai ke ta haukanta shi bai ma san wa ya kirasa ba, wani murmushin ya kuma yi yana shafa kansa ya ja motar yace "I bet da muna kusa har duka sai kin kai min" sauke kanta kasa tayi bata ce komai ba. Tun da Aliyu ya shiga gidan gabansa ke faduwa, ya kashe wutan parlorn da kyar ya haura sama, ya fi minti daya tsaye kafin ya bude kofar bedroom din da khadijah ke ciki, tana xaune can karshen gado ta hade kanta da gwiwa tana shesshekar kuka, ya kasa karasawa cikin dakin, a hankali ya kai hannunsa kan switch dake jikin bango ya kashe wutan dakin, da sauri ta dago kanta, ya rufe kofar a hankali, cikin rawar murya tace "Barrister ka kunna plss..."

Lumshe ido Aliyu yayi jin sunan da ta kira lkci daya jikinsa yayi sanyi sosai, ya bude idanuwansa ya taka a hankali har ya isa gabanta, ja baya ta dinga yi xuwa lkcn ta daina kukan da take tsoro ne fal xuciyarta, ya xauna dab da ita har suna jiyo numfashin juna xata mike da sauri, yyi hanxarin rikota ta fashe da kuka jikinta na rawa, a hankali ya jawota jikinsa ya rungumeta lkci daya ta hadiye kukan da take, ya dinga jin yanda xuciyarta ke bugawa a kirjinsa kamar xai fito, lumshe ido yyi hawayen idanuwan sa suka xubo, cikin rawar murya tace "Barrister ka kunna wutan bana son duhun plss, switch the light on" Murya can kasa yace "Imannn" Ta fi second talatin muryar da taji na kai kawo a kanta, a hankali ta xame jikinta daga nasa tana kallon fuskarsa cikin duhun dakin kamar yanda shi ma yake kallonta a sanyaye, hannu ta kai fuskarsa tana masa wani kallo da kyar tayi gathering courage din cewa "Aliyu?" Rungume ta yayi kamar xai mayar da ita jikinsa cikin rawar murya yace "Yes Iman, I beg you... don't say no to me plsss, this our fate... na sha wahala kan ki a rayuwa Iman, na sha wahala fiye da tunanin ki, kashe ni ne kadai son ki bai yi ba, for good six years bani da kwanciyar hankali bani da walwala, forgive and forget the past plss, Barrister Aliyu..." Kasa ci gaba yyi bayan wani lkci ya ci gaba voice dinsa na breaking "I owe him... he gave up for me.... Ya bar min ke Iman, don girman Allah ki ji tausayina kar ki bani wahala...." Kamar warce aka yi moulding haka khadijah tayi stiff jikinsa maganganunsa na mata yawo a kai, she's still trying her best to apprehend all what he is saying, Jin tayi shiru ya dago kanta jikinsa na rawa, hawayen dake makale idonta suka xubo tana kallonsa, ta fashe da wani matsanancin kuka kamar warce aka aiko ma wa da sakon mutuwa, sauka yyi saman gadon a rikice ya durkusa kan gwiwowinsa kusa da ita yace "Iman kiyi ma girman Allah kada ki wahal da ni, I have already had enough, don't say no to this marriage, kar ki ce A'a Iman...." Kasa ci gaba yyi.... A hankali tayi baya ta fada saman gadon, ya mike da sauri ya riketa yana kiranta amma tuni idanuwanta suka rufe, ya dago ta ya rungume ta hawaye na sakko masa yace "Why Iman, kin yi saurin mance alkhairin da na maki a rayuwa, sharrin kawai kika bari a ranki, ba laifina bane, ba yin kai na bane, ni ba maxinaci bane, duk xaman ki gidanmu ban taba tunanin akwai ranan da xai xo in cuce ki ba...." Kasa ci gaba yyi ya runtse ido yana rungume da ita har sannan. Sai kusan karfe hudu saura na asuba khadijah ta bude idanuwanta a hankali, Aliyu da ke xaune kan darduma ya mike da sauri ya iso kusa da ita yana kallonta da damuwa, mikewa take kokarin yi tana kallon jikinta, riga ce mara nauyi jikinta maimakon atamfar da ta sa tun a gida, Aliyu ya xauna gefen gadon a sanyaye yana kallonta, kokarin sauka ta shiga yi daga kan gadon yana son riketa amma yana tsoron abinda xai biyo baya, cike da karfin hali yace "Iman you are not strong ina xa ki, Wait..." Bai san lkcn da ya riketa ba ganin tayi baya xata fadi, xai kwantar da ita ta kwace kanta tace "Let me" Dafe kansa yyi, ganin xata sake tashi ya kara rikota, tura hannunsa tayi muryarta na rawa tace "Dole sai ka rike ni ne, nace bana so" ko saurarenta bai yi ba ya ki saketa, ta fashe da kuka tace "I want to use the restroom ka kyalenii...." Tashi tsaye yyi ya dagota ya nufi bayi da ita, suna isa bayin ta kwace kanta ta shiga ta rufe kofar, a hankali ya koma gefen gado ya xauna duk jikinsa a sanyaye, tana fitowa ta nufi kofar fita ya mike da sauri yace "Iman" ganin ko juyowa bata yi ba ya karasa da sauri kafin ta isa kofar ya rufe ya marairaice yana kallonta, Xaunawa tayi nan bakin kofar ta hade kai da gwiwa tana shesshekar kuka xuciyarta yayi rauni ga wani xafi da yake mata, yanxu dama duk yaudararta Sudais yake, me yasa xai ci amanarta ya sa a aura mata Wai Aliyu?? Of all people why Aliyu? The beginning and end of her problem, the person that shattered her life, me yasa xai sa a aura mata shi, ta dinga kuka a raunane taji duk duniyar ya isheta, gaba daya ji tayi haushin kowa take har Umma don tasan ita ma ta sani amma ta boye mata, a hankali Aliyu ya sa key kofar ya cire a jiki, Jin haka ta mike a mugun fusace hawaye na sakko mata xuciyarta na bugawa tace "Malam ka bude min kofa in fita.... Bana son ganin ka, bana so...." Bai bari ta kai karshe ba ya jawota jikinsa ya rungume ta ya lumshe ido, duk iya kokuwan da ta dinga yi xata kwace kanta kasa wa tayi daga karshe ta hakura ta dinga kuka, a hankali murya can kasa yace "Plss, tell me how many days will it take you to finish this drama?" Dago kai tayi tana masa wani kallo xuciyarta na heaving, a sanyaye yace "I just want to get prepared... Just tell me for how long it will take you to finish it? And in sha Allah I will endure" fuskarta daure tace "Sake ni" a hankali ya saketa ta koma baya ta mika masa hannu tace "Bani makullin" ya mika mata makullin hannunsa, ta juya ta bude kofar ta fice tayi banging din kofar, Ya d'an tabe baki ya juya a hankali ya koma kan gado ya kwanta don har wani ciwo kansa ke yi masa baccin da bai yi ba, har aka kira Asuba bai bari bacci ya daukesa ba ya mike ya shiga bayi ya dauro alwala ya fito don wucewa masallaci, kwance ya ganta kan 3 seater a parlor tana bacci ta dunkune waje daya saboda sanyin parlorn, ya kashe A.c sannan ya nufi kofa ya bude ya fita. Ko da ya dawo masallaci bai ganta parlorn ba kuma, ya wuce sama ya bude kofar dakinta a hankali yana leka ciki ya ga bata nan, juyawa yyi da sauri ya bude wani dakin, xaune ya ganta kan darduma ta jinginar da kanta jikin bango, tana ganinsa ta daure fuska ta cinno baki gaba, a hankali ya rufo mata kofar ya shiga nasa dakin ya kwanta, sai a sannan bacci ya daukesa. Sai da gari ya fara wayewa khadijah ta mike jiki ba kwari daga kan darduman da take xaune ta bude kofar dakin ta fito, dakinta ta bude a hankali tana kallon ciki, ganin babu kowa ta shiga ta rufe kofar, bathroom ta shiga tayi wanka ta fito, bayan ta shirya ta kwanta saman gado jin kanta na ciwo sosai, bacci ne ya dauketa daga haka, Bata farka ba sai da aka danna bell a kasa, ta mike xaune da kyar tana kallon agogo, har sannan kanta ciwo yake ba kadan ba, karfe tara saura ta gani, ta sauka daga kan gadon ta dau hijab dinta ta sa ta fita, a hankali ta bude kofar ta ga Baby tsaye rike da basket din abinci tana murmushi tana kallonta, khadijah ta hade rai sosai ta juya ta koma parlor, Baby da ta bi ta da kallo a xuciyarta tace kya yi ki gama ne ma, A nan parlor ta ajiye basket din ta juya xata fita khadijah ta bi ta da kallo har ta fita ta rufe kofar sai a sannan baby ta fara dariya kasa kasa, khadijah da ta bi ta da kallo ta xauna kujera lkci

Please Login or Register in order to submit comment