Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kama ku tafi asibiti ne sai ku wuce" Da farko rasa abinda xai ce ma Mumy yayi lkci daya hawaye ya cika idonsa, har sai da tace "Hello Abuturrab, are you there?" Yyi karfin halin gyada kai yace "Xan taho yanxu Mumy" daga haka ya katse wayar ya ajiye ya rike kansa hawaye na sakko mishi.

Aliyu ya fi minti goma xaune cikin mota bayan ya iso gida, gaba daya ya rasa me ke masa dadi duniyar, har ya fita kamanninsa saboda damuwa, Mumy ta fito jin shiru shiru bai shigo ba, ganinta yasa tun kan ta karaso parking lot din yyi karfin halin bude motar ya fito kansa a kasa, kamar bai son taka kasa yake tafiya, har ya iso inda take kallonsa Mumy take cos he looks so sick, shi kam ya kasa dagowa balle ya kalleta, Tace "Abuturrab are you okay, ciwon kan ne har yanxu" ya gyada mata kai a hankali yace "Na sha magani mum da sauki" daga haka ya wuceta ta bi sa da ido, bin bayansa tayi tace "Toh bacci ka je clinic din kake yi?" Bai juyo ba yace "Eh" da damuwa tace "Maimakon ka tsaya gida ka huta Aliyu tunda baka da lafiya, da sai ka kira asibitin ka bada uxurin ka, xa ma ka iya dubata yanxu ko kawai mu wuce asibiti" tsaye yyi bakin kofa ya rasa abinda xai ce mata ya kuma kasa juyowa duk jikinsa yyi sanyi, Cike da karfin hali yace "Xan tafi asibitin da ita likita xa su duba ta a can" mumy tace "Toh kai ma gaskiya a dubaka wani irin ciwon kai ne haka lkci daya tun safe, sanusi sai ya kai ku clinic din" Bude kofa aka riga sa yi Anty khadijah dake tsaye bakin kofar tana kallonsa da kyau tace "Me ya same ka kai kuma, baka da lafiya ne?" Gefenta ya bi ya shiga gidan ba tare da ya bari sun hada ido ba yace "I am better now" Anty khadijah ta kalli Mumy mamaki shimfide fuskarta tace "Dama baya da lafiya ne Anty fati?" Mumy tace "Tun safe kafin in fita aiki yace min yana jin ciwon kai ban san wani kalan ciwon kai bane haka har yanxu, ni na xata ma baxa shi aikin ba ganin har na fita yana gida" Anty khadijah ta bi bayansa da sauri ganin har ya kai stairs, ta hada har da d'an gudunta har hakan ya ba Mumy mamaki, Tsaye Aliyu yyi bakin kofar dakin ya kasa shiga, ta labe jikin stairs tana jiran ya shiga ita ma ta shiga, a hankali ya murda kofar ya sa kai ya shiga, Tana ganin haka ita ma ta shige, Baby da ke xaune gefen Khadijah da ke kwance da damuwa tace "Yayanmu Iman bata da lafiya she is just crying, and her temperature is very high" hawaye cike idonta take magana, khadijah na jin sunan da Baby ta kira ta bude ido da sauri hade da yunkura ta mike xaune, Aliyu ya kasa kallon direction din, wani sabon kuma khadijah ta saki a raunane, Anty khadijah dai na tsaye kofa tana kallonsu, Aliyu bai iya ya kalli khadijah ba yace "Ki sa ta shirya xa mu je asibiti yanxu" baby tace "Toh" daga haka ya juya suka yi ido hudu da Anty khadijah, tabe baki tayi ta juya ta bar wajen tana cewa "Haka dai aka iya, da yar uwar ka ce ba lafiya ai baxa ka bi ta kan mu ba ma" shi dai ba ce komai ba ya fita. Hijab baby ta ba Khadijah, Khadijah taki sawa tana girgixa mata kai cikin kuka tace "Ni bana son xuwa asibitin, idan nayi bacci I will okay, baxan iya xuwa ba" baby tace "Nooo, ki sa mu tafi don Allah" kin yarda Khadijah tayi hakan yasa baby ta fita sai ga ta sun shigo tare da mumy, mumy ta karaso kusa da ita ta amshi hijab din ta sa mata tace "Kiyi hakuri ki tashi ku je asibitin kin ji, Allah ya sauke" daga haka Mumy ta dago ta, Aliyu dai na tsaye corridor yyi backing kofar, muryar Mumy ya ji tana cewa "Toh ka kai ma Sanusi makullin sai yyi driving din koh" Juyowa yyi xai yi magana amma ya kasa ganinta tsaye tare da Khadijah tana rike da hannunta, Wani mugun tausayinta ya dinga ratsa shi ganin irin karfin halinta cos he was thinking baxata iya fitowa ba, bai yarda sun hada ido ba kamar yanda ita ma kanta ke a kasa, ya fara sauka stairs Mumy ta bi bayansa tana rike da hannun Khadijah baby na biye da su a baya, Anty khadijah dake tsaye bakin kofar dakinta ta saki baki ta bi Khadijah da ido a ranta tace wa yaga boss lady, don kusan kalau take tafiyar ta, nan kuwa daga ita har Aliyun basu san mugun karfin hali take ba, she is in pain all over, only trying her best to be okay, Mumy ta bude bayan motar ta shigar da ita tasa baby ma ta xauna a baya kusa da ita, sanusi ne ya ja motar cos da gasken Aliyu bai jin xai iya tukin, har suka isa asibitin kansa na jingine da kujera, baby kuma na rungume da Khadijah da ta ki bude ido tana kukan xuci. Sanusi na parking Aliyu ya bude motar ya fita, Baby ta fito tana kallon khadijah tace "Iman ki sakko we are at the hospital" A hankali khadijah ta fito cikin motar tana rike da hannun baby, Aliyu ya kalli baby yace "Ku koma tare da sanusi" xaro ido tayi tace "Yaya but Mumy tace in tsaya da ita, wa ye xai tsaya kusa da ita idan anyi hospitalising dinta, look shes very sick fa" irin kallon da ya dade bai mata ba ya shiga yi mata a lkcn, Bata sake cewa komai ba ta shiga motar hawaye cike idonta, Khadijah ta fashe da kuka a hankali tace "Don Allah kar ki tafi ki bar ni" Baby na share hawayen ta tace "He said I shud leave Iman" Aliyu ya juya ya wuce ciki sai ga nurse ta taho ta shiga da Khadijah asibitin, sanusi ya ja motar yana ma khadijah Allah ya sauwake ya kama hanyar gida. Nurse din na rike da hannun Khadijah da ke ta hawaye ta wuce office din Aliyu da ita kamar yanda yyi instructing dinta, baya office din hakan yasa ta fito ta shiga office din kusa da nashi ta samesa xaune, ruwan xafi yasa ta fara kai ma khadijah bathroom dinsa tayi wanka sannan ya bata magunguna da alluran da xata mata, daga haka kuma ya bar asibitin, kulawa sosai nurse din ta bata don ta bata tausayi yanda ta ga jikinta duk da ba ta san takamaiman abinda ke damunta ba, tana mata alluran kuwa bacci ya dauketa nan dakin Aliyu. Aliyu na gidansa har ya samu bacci ya daukesa.... ring din wayarsa ya tashe sa, dubawa yyi da kyar ya ga Mumy ce, ya kai hannu ya daga a hankali ya kai kunne, da damuwa tace "Aliyu ya jikin Khadijah, or shud I come over naji shiru shiru" yace "Noo mum, da sauki anjima sanusi yaje can asibiti ya mai da ta gida" Mumy tace "Kai kana ina?" Ya d'an yi shiru kafin yace "Na taho nan gida na ne, I need sleep" da mamaki mumy tace "Kuma ka bar ta ita kadai asibiti gashi ka ki barin Baby ta xauna da ita Abuturrab" yace "Nurses din xa su kula da ita mum" Mumy ta d'an yi shiru kafin tace "Toh shkkn, Allah ya sauwake, kai ya jikin naka?" Yace "Alhmdllh am better now" tace "Ohk, amma da ka daure kai ka je ka maido ta gida don Allah, bbu dadi hakan kamar bata da gata, idan baxa ka ba ni in je" yace "Toh mum xan je yanxu kiyi hakuri" daga haka ta yi masa sallama ta katse wayarta. Bayan magrib Aliyu yyi wanka bayan yyi sllh ya canxa kaya ya bar gidan, yana isa clinic din ya kira nurse da ya bari da Khadijah a waya yace tayi mata alluran karshe na ranan ta fito tare da ita yana waje, nurse din tayi yanda yace sannan suka fito tare da Khadijah, bin nurse din da ke rike da hannun ta take kamar iska xae kadeta ta fadi, duk ta rame lkci daya, yana kallon nurse din bayan sun iso a hankali yace "Hope you did all what I instruct you to" nurse din tace "Yes but, I don't knw why she's finding it difficult to walk, kuma tun daxu take complaining chest pain, Dr bashir ya bata magani dai daxu, har da shi ma cikin wa ennan" ta fadi tana nuna masa drugs din da Khadijah xata kai gida, Khadijah dai na tsaye kanta a kasa duk a tsorace take ga xuciyarta dake bugawa da sauri da sauri, Aliyu ya gyada kai yace "Thanks nurse Maryam" Nurse din tayi murmushi ta sa Khadijah ta shiga gaban motar ta rufe tana mata Allah ya kara lfya, tada motar Aliyu yyi ya bar haraban hospital din, har suka isa gida bai ce komai ba, yana lura da hawayen da take yi tana gogewa da Hijab dinta tun bayan da suka fito clinic har ynxu da suke gida, ya gama parking ta bude motar a hankali ta fita, ya bi ta da ido ganin yanda take tafiya har ta shiga gida, sae sannan shi ma ya fito ya rufe motar ya shiga gidan. Mumy dake xaune parlor da su siyama da Anty khadijah ta mike ganin Khadijah tace "Sannu khadijah, ya jikin" Khadijah ta kasa dago kanta tace "Naji sauki Mumy" Anty khadijah sai kallonta take babbu kiftawan kirki, Aliyu na shigowa parlorn ya haura sama, Mumy ta kama hannun Khadijah ta wuce sama xuwa bedroom dinta da ita, da kyar khadijah ta iya cin pepper soup din da mumy ta mata, duk bakin ta babu dadi, a nan dakin bacci ya dauketa. Cikin dare misalin karfe biyu xaxxabi ya kuma rufe ta, dakin Aliyu Mumy ta shiga ta samesa xaune kan darduma ta xauna gefen gado ta jira ya sallame sallahn da yake da damuwa tace "Aliyu har yanxu fa jikin Iman" yace "Xaxxabin kuma?" Mumy tace "Ehh dama" yace "Mumy to ta kara shan drugs din..." Mumy tayi shiru bata ce komai ba, can tace "Toh shkkn" sannan ta mike ta fita, magungunan ta sake bata ta rufe ta da duvet sai kusan asuba bacci mai nauyi ya dauketa. Da safe tea Khadijah ta sha bayan mumy ta tilastata da kyar, da tayi ma Aliyu maganan alluranta da ya rage yace driver ya kai ta sai karfe goma shi xai fita aiki, sanusin ne ya kai ta ya maido da ita, kafin yamma taji saukin jikinta sosai sai dai ta rasa irin ciwon da take jin kirjinta ke mata, kuma hakan na faruwa ne in dai ta tuna incident din ranan sai taji mugun faduwar gaba, har lkcn Aliyu bai barin su hada ido a gidan kuma bai ce mata komai, idan tana wuri ma bai yrda ya tsaya a gun, Anty khadijah dake lura da komai har wani farin ciki da nishadi na musamman take ji a gidan, har Mumy ta dinga mamakin yar uwar tata, duk fadace fadace da xage xagen ta rage yanxu hatta Khadijah ta daina hantara nan ko shirin sake komawa inda taje kwanaki kamar yanda aka ce mata ta dawo idan ta tabbatar komai ya wakana a lkcn ma xa a fara aikin, tunanin karyan da xata yi ma Mumy kawai take ta tafi inda xata. Aliyu na bedroom dinsa da daddare baby ta shigo, ta xauna kusa da shi tace "Yayanmu I want to ask you something pleaseee" yana kallonta yace "What?" Ta langwabar da kai a hankali tace "Iman tayi maka wani laifi ne, naga you no longer talk to her, ko ta gaisheka sometimes you do pretend you didn't hear, why please, ka gaya min me tayi maka, gashi ita ma she is always sad yanxu, I've caught her severally tana kuka cikin dare..." Katse ta yayi yace "Na fara wasa da ke da yawa koh?" Da sauri ta girgixa masa kai, ya hade rai yace "Toh tashi ki tafi" mikewa tayi da sauri ta fita ya ci gaba da danne dannen laptop da yake yi. Washegari da sassafe Anty khadijah ta shirya har da kwallarta take ce ma Mumy xata Abuja an kirata wai Yusuf d'anta ba lafiya yana asibiti, mumy jikinta yyi sanyi har da bata dubu goma ta hau mota, ta karba ta yi mata godiya ta bar gidan. Karfe goma saura Mumy ta tafi aiki gidan ya rage khadijah da baby sai Iklima don su siyama sun tafi makaranta, Aliyu ma na sama a dakinsa, tun bayan abinda ya faru tsakanin khadijah da Aliyu ta rage xaman cikin gidan sae Mumy na nan, always a baya xaka ganta xaune ita kadai, yau ma xaune take tayi nisa a tunanin da take kamar ance ta juya taga Aliyu tsaye d'an nesa da ita, mikewa tayi a tsorace tana komawa baya, ya dauke idonsa daga kallonta yace "Iman" hawaye ya cika idonta ta kasa amsawa, karasowa yyi kusa da ita ya tsaya tana komawa baya a hankali, yace "Za ki gane gidan step mum din ki?" Khadijah sai kallonsa take xuciyarta na bugawa, ya hade rai yace "Am asking" a hankali tace "Kila in gane" yace "Ohk... Am coming back now" daga haka ya juya ya koma ciki, ba a dau lkci ba ya dawo, envelope ne rike hannunsa ya mika mata taki amsa gabanta sai faduwa yake, yace "Collect it" hannunta na rawa ta karba, yana gyada kai yace "Go Iman, go back to ur step mum, I can't continue my life the way I want living with you in the same roof, you are now a barrier to my happiness pls ki tafi Iman go anywhere, leave our home, bana son Ina ganinki ina jin haushin kai na cos nobody is above mistake, just go plss" A hankali ta juya masa baya hawaye na sakko mata tace "Ohk xan tafi... thank you very much for all what you've done to me throughout my stay in your home, Allah saka maka da alkhairi duk hidiman da ka min, but ina neman alfarmar ko xan iya yi ma Mumy sallama kafin in tafi, don ban mata hallaci ba idan na tafi bata sani ba" a takaice yace "Noo, just go Iman" ta fashe da kuka sosai tace "Ohk nagode" juyawa yyi ya nufi cikin gida... Sai kuma ya juya da sauri yana kallonta yace "And one more thing... Forgive me plss" ta juyo hawaye na sakkowa idonta tace "I have done that already" yace "Thank you" daga haka ya juya ya shiga ciki ya rufe kofa. Share hawayen idonta da ya ki tsayawa ta dinga yi, dama Hijab ne jikinta kawai ta nufi gate ta fita gidan, da kafa ta karasa bakin titi ta samu napep tana kallonsa a hankali tace "Tasha xaka kai ni" yace "Toh" daga haka ta shiga napep din, har suka isa tasha bata sani ba tayi nisa a tunanin da take, mai napep din ya dawo da ita duniyar tunanin da taje, sai a sannan ta tuna kudin da xata basa, da sauri ta leka cikin envelope din da Aliyu ya bata taga kudi ne me yawa a ciki ta xaro dubu daya hawaye na sakko mata ta shiga tashar ta nufi inda taji ana kiran kano, dama mutum daya ake jira tana shiga motar ta bada kudinta bbu bata lkci suka dau hanyar kano.

Tun da suka iso kano Khadijah ta fito daga cikin tashar kanoline take ta kalle kalle tsaye a bakin titi, duk mai adai daitan da ya tambayeta inda xata sai dai ta kafe sa da ido nan kuwa tunanin da take daban, hadarin da ya shiga haduwa a garin ne yasa ta dawo reality, da kanta ta tafi gun wani mai napep a hankali tace "Tudun yola xan je" yace "Dai dai ina a tudun yola" tace "Idan mun je xan gane" Bata damu da kudin da ya kira mata ba ta shiga adai daitan suka dau hanyar anguwar da ta kira masa, tun suna hanya aka fara yayyafi har suka kawo Tudun yola, ita dai ta san ranan da suka taho daga katsina da ummanta taji ta ce ma mai napep Tudun yola to amma bata san ina a Tudun yola ba, tun mai napep na biyeta suna xaga anguwar har yyi parking yace "Bani kudi na ki sauka, ke da baki san inda xa ki ba kika sa na dauko ki" sauka tayi daga cikin napep din ta basa kudin da yace daga cikin envelope ya bata canjinta ya ja adai daitan sa yyi gaba, hawaye ya cika idonta ta saka kai gabas tana ta tafiya, to ina xata ga gidan ummanta, jin ruwan ya taho da karfi yasa ta samu yar rumfa ta tsaya, ta kusa minti talatin tsaye karkashin wajen, kowa ya shige gida, wasu kuma sun shiga shagunansu saboda ruwa hanyar kamar anyi shara, ita kadai ce a waje ga wani sanyi da ta dinga ji, an dau fiye da awa daya ana ruwan kafin ya tsagaita sai yayyafi, fitowa tayi daga inda take tsaye ta ci gaba da tafiya a gajiye, bata yi wani nisa tana tafiya ba taji ance "Lahh Mama dubi yarinyar nan mai kukan kitso" Juyawa tayi taga wata mata ce da 'yar ta da suka hadu a saloon ranan da Umma ta kai ta gyaran gashi, uwar ta rankwashi yarinyar da baxata wuce Khadijah ba tace "Toh ina ruwanki salon tsokana" matar tace "Sannu yan mata" Khadijah ta gaisheta ta amsa ganin xata wuce tayi saurin cewa "Anty don Allah ban san hanyar gidanmu bane, ko xa ki kai ni gun mai saloon din nan ta san ummata" matar ta saki baki tace "Baki San hanya ba kuma, daga ina kike haka?" A hankali khadijah tace "Daga kano nake na mance hanyar gidan ne" Matar dake ta yi ma khadijah kallon mamaki tace "Ikon Allah, sai dai saloon din da nisa daga nan gashi da sauran hadari, amma mu je mu hau adai daita sai in ajiye ki shagon" Khadijah ta d'an risina tace "Nagode Anty" daga haka ta bi matar da 'yar har suka isa inda masu adai daitan suke, ta fadi inda xa su sannan suka dau hanya, kamar yanda matar ta fada bbu laifi tafiyar da nisa, suna isa saloon din suka tarar mai saloon din ta fito xata rufe shago ta wuce gida saboda ruwa, Matar suka gaisa da mai saloon din sannan tayi mata bayanin Khadijah, mai saloon din tace "Tab, to ai gidan Hajiya Amina da nisa daga nan, cikin ruwan nan yaushe mutum xai fara takawa xuwa gidan ai sai dai adai daita" Matar tace "Toh don Allah ki taimaka ki dau adai daitan ki kai ta gidan idan ya so mamartata sai ta baki kudin adai daitan da kika biya" mai saloon tace "Sai dai haka" daga hakan suka yi sallama da matar Khadijah tayi mata godiya, wani adai daitan mai saloon ta samu suka shiga har kofar gidan Umma, a nan hankalin khadijah ya kwanta ta dinga kallon kofar gidan, khadijah ta sauka tana murmushi tace "Anty nagode xan je in karbo maki kudin napep din" daga haka khadijah ta shiga ciki da sauri, bbu kowa tsakar gidan saboda ruwan da aka yi, Khadijah ta kwankwasa kofar parlorn Ummanta a hankali, Bude kofar Umma tayi tana tambayar waye? Umma ta xaro ido hade da bude baki tace "Khadijah??" Rungumeta khadijah tayi cike da farin ciki tace "Ummata" Umma ta ja ta suka shiga ciki da mugun mamaki tace "Daga ina kike haka" a hankali khadijah tace "Kaduna Umma" Umma tace "Ke da wa?" Khadijah tace "Ni kadai Umma ki ban kudi in kai ma mai adai da ita a waje, mai saloon din nan da kika kai ni ranan ce ta rakoni, ban san gidan ba" Umma ta dau kudi ta fita da sauri, Godiya tayi ma mai saloon din ta ba mai adai daitan kudin kawo ta da yayi da mayar da ita da xai yi sannan ta koma ciki. Umma ta dinga kallon khadijah tana share hawayen da ya ki tsaya mata a sanyaye bayan Khadijah ta gama yi mata bayanin duk abinda ya faru tun daga ranan da ta bar ta gidan yakumbo har ixuwa yanxu da take gabanta, abu daya ta boye mata a labarin da ta bata shine kuma abinda ya shiga tsakaninta da Aliyu kawai dai ce mata tayi yace ta tafi saboda Anty khadijah bata sonta, Khadijah ta share hawayen dake sakko mata ita ma cikin rawar murya tace "Umma me yasa baki son in xauna a wajen ki, don Allah kada ki sake kai ni ko ina, let me stay with you plss" ta fashe da matsanancin kuka tana kallon Umma da ita kanta ba karamin rama tayi ba, Umma tayi gathering courage ta jawota jikinta a hankali tace "Khadijah ba laifi na bane kinga kishiyoyina ba kirki ne da su ba saboda su ya sa na kai ki gun yakumbo amma ta ci amanata ko don ba uwar mu daya ba, da wani mugun gidan ta kai ki haka xa a cutar min ke ina nan ban sani ba, har kadunan naje kwanaki in duba ki aka ce ai ta tashi a gidan, gashi bbu wanda yasan inda ta koma, haka nayi kwana biyu kafin in dawo nan kano, duk layukan ta basa xuwa har na gaji na daina kira, kullum fatana shine Allah yasa kuna lafiya ashe abinda ta maki kenan, to Allah ya saka maki, ita kuma wannan baiwar Allah da ta rike ki a gidan ta har na wnn lkcn Allah ya saka mata da alkhairi" Khadijah dake ta sauraren ta a hankali tace "Ameen" Umma ta mike tace "Bari in karbo maki abinci a makwabta bani nayi girkin gidan ba" daga haka Umma ta fita parlorn, khadijah ta jinginar da kanta da kujera a sanyaye, kadan ta ci shinkafa da miyar da Umma ta amso mata ta sha ruwa sannan ta fita yin alwala don ta yi sallah, Shafah da fitowarta kenan ita ma ta saki baki tana kallon khadijah, can ta kwalo ma Hasana kira, Hasana ta fito ita ma, Shafah tace "Kin ga ashe bak'i muka yi a gidan yau" a hankali khadijah ta gaishesu, dariya Hasana tayi tace "Lallai kam bak'i" daga haka ta juya ta koma bangarenta, Shafah ma ta wuce ciki tana dariya. Khadijah na xaune kan darduma bayan ta idar da sallah, Umma dake yankan alaiyahu alamar dai ita xata amshi girki tace "Kina ji na khadijah, babu ruwan ki da mutan gidan nan ki rufa min asiri kinji, duk me xa su maki kar ki tanka su, ko don Alhaji ya bar ki ki xauna gidan nan" Khadijah ta gyada mata kawai, mikewa Umma tayi ta fita da alaiyahun waje sai da ta shiga kitchen ta kira Abban fadila, yana dauka bayan ta gaishesa tace "Alhaji dama alfarma nake son tambaya gun ka" yace "Ina ji" tace "Dama khadijah ce xata xo ta d'an kwana biyu nan, sun yi hutu idan ba damuwa don Allah" Yace "Toh kin gaya ma su Shafah?" Shiru Umma tayi bata ce komai ba, yace "Sai ki sanar da su don bana son abinda xa a xo ana min tashin hankali a gida" daga haka ya katse wayarsa, Umma ta ajiye wayarta a sanyaye , ko wace irin rayuwa ce wannan ta fada yanxu ita kam, tun da tayi auren nan bata da kwanciyar hankali sannan kamar warce aka daure kafarta a gidan tana xaune a hakan har lkcn. Fita tayi ta tafi dakin Shafah ta samesu tare da Hasanar daga nan bakin kofa ta tsaya tace "Sannun ku, Khadijah ta xo daxu daga kaduna nace in gaya maku..." Shafah ta mata wani kallo tace "Au haba, to ta sha kabo..." Hasana tace "Lallai kam, sannunta

Please Login or Register in order to submit comment