Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ubansa muka yi masa kenan" durkushewa Khadijah tayi a wajen tana kuka a hankali tace "Umma kiyi hakuri don Allah ki yafe masa" Tsawa Mami tayi mata tace "Rufe min baki, tarbiyar da iyayenki kema suka maki kenan kiyi rayuwa gida daya da namiji?" Cikin rawar Murya Khadijah tace "My parent are late, bani da kowa shi yasa ya taimakeni, Umma kar ki ce ya barmu don Allah..." sudais da ya ji kafafuwansa sun gaxa daukarsa ya xauna kan kujera ya ajiye su shureim da suka wani rirrikesa, cikin sanyin murya yace "Mami don girman Allah kiyi hakuri, ba yanda kike tunani abun yake ba, I just...." Katse sa Mami tayi cike da takaice tace "Ba yanda nake tunani abun yake ba Aliyu?" Sudais ya daga kai da kyar yana kallonta ganin hawayen dake idon mahaifiyarsa ya ajiye yaran ya mike ya isa gabanta ya durkusa cikin rawar murya yace "Noo Mami pls kar ki xubar da hawayen ki a kai na, na maki alkawarin na daina duk abinda nake daga yau, ki gafarce ni don Allah mamina" duk ya rikice mata, Mami na hawaye tace "Ni idan na gafarce ka Allahn ka fa? Wani tsinannen taimako ne wannan without the consent of ur parent, wani taimako ne wannan kuna rayuwa gida daya kamar mata da miji, yanxu ba don na san halin ka ba ance maka baxan yarda yaranka bane wa enan yaran?" Idonsa ya kada sosai cikin raunin murya yace "Mami nayi abinda nayi ne domin taimako amma daga yanxu na bari in sha Allah, forgive me plss Mami, nasan ban kyauta maku ba" Mami tace "Ka hada ina ka ina ka ka koma Damaturu yau ba sai gobe ba, sannan ina jiran makullin gidan yanxu ka same ni gidan Hajiya Rukayya" Tana fadin haka ta juya ta fita a parlon, kai kana gani kasan tana mugun son d'an nata ne, Hajiya Rukayya tace "Heed to what ur mother said right away Aliyu, ita kuma idan tace bata da iyaye ai baxa ta rasa dangi ba ta tafi wajensu" shi dai sudais bai ce komai ba, Hajiya Rukayya ta juya ita ma ta fita, Sudais ya dafe kansa da yyi masa nauyi, gaba daya tunaninsa ya dagule ga kukan Khadijah da yake ji har ransa, su kansu yan biyun kuka suke, lkci daya idanuwansa suka kada, mikewa yyi daga durkushen da yake ya wuce dakinsa ya dau makullin mota ya fita gidan gaba daya, Nanny da duk taji abin da ya faru ta iso gun khadijah dake kuka sosai ta dafa ta a hankali tace "Dama ba mijin ki bane mutumin nan maman twins?" Khadijah ta dago tana kallonta hawaye na sakko mata ta girgixa mata kai tace "Taimako na kawai yayi tun ban haifi yaran nan ba, ni bani da kowa sai shi yanxu" Hawaye ne ya cika idon Nanny tace "Dangin ku fa?" Cikin rawar murya Khadijah tace "Ban san dangin Mahaifiya ta ba, dangin Abbana kuma baxa su karbe ni ba, Ummata kuma ta tafi ta bar ban san inda xan ganta ba" tana kai wa nan ta fashe da matsanancin kuka tace "Ni yanxu ban san ya xan yi da yaran ba" kuka sosai Nanny take duk jikinta yyi sanyi ba kadan ba, ta jawo ta jiki cikin sanyin murya tace "Kiyi hakuri wataran sai labari Allah baxai hanaki yanda xa kiyi ba, kar ki sake kuka don Allah" mikewa Nanny tayi ta tafi gun su Shureim dake ta kuka wai Sudais ya fita ya bar su. Bayan awanni kusan uku Nanny ta gaji da lallashin Khadijah da ta ki hakura da kukan da take, xuwa lkcn kuma su Shureim sun yi bacci, Da kyar Nanny ta lallaba ta taje tayi sllh don duk a sanyaye take, tana xaune kan darduma Sudais ya shigo gidan, kallonsa Khadijah ta dinga yi har ya xauna kan kujera, a sanyaye ta taso ta durkusa gefensa tace "Am sorry I caused you all this, kayi hakuri don Allah ka yafe min" Tana magana hawaye ce idonta, ya kirkiri murmushi yace "It's nothing Amira, tafi ki hada kayan ki gaba daya a sama" shiru ta yi tana kallonsa gabanta na faduwa, ya gyada mata kai cike da assurance, tashi tayi jiki ba kwari ta wuce sama, ya kalli Nanny da ke parlorn ita ma duk a sanyaye yace "Ki hada kayan yaran da naki gaba daya" mikewa tayi ta wuce sama ita ma, Nanny ce ta fara sakkowa parlorn da jakunkunan kayan su shureim, Sudais dake kallonta yace "Ki kai cikin booth, its open" fita tayi waje da kayan, tana dawowa yace ta je ta taya khadijah, Kuka Nanny ta samu Khadijah nayi a dakin, bata iya tace mata komai ba ta shiga taya ta hada kayanta, Nanny ce ta sauko da jakan ta kai cikin motar, shi dai Sudais na xaune yyi nisa tunanin da yake, jin wayarsa na ring ya dauka da sauri yana kallon mai kiran, tashi yyi ya daga wayar yace "Mukhtar ka iso ne" daga daya bangaren abokin nasa yace "Ehh ina waje" fita yyi ya samesa waje, Mukhtar yace "You mean wannan gidan xaka siyar Barrister?" Sudais ya shafa kansa yace "Ehh shi" Mukhtar yace "Haba, Toh ai wannan yafi wancan wllh, ya xaka siyar da abu ka siya wanda bai kai sa ba kuma har da ciko, amma sun ma same ka da yawa" Sudais yace "kai dai bani takardun wancan gidan, and don't forget gidan is almost furnished" Barrister Mukhtar ya bude motarsa ya fiddo envelope ya mika ma Sudais ya karba yace "Duk da haka dai, duka duka kayan nawa ne a ciki" Sudais ya amsa envelope din yace "Nagode, bari in dauko nawa" daga haka ya koma ciki ya wuce bedroom dinsa ya dauko wani envelope dake dauke da takardun gidan nasa yana dawowa ya mika ma colleague dinsa yace "Kafin dare xa a kwashe komai na nan din, soo you help me explain to them" Mukhtar da mamakin Sudais ya cika sa ya karbi envelope din yace "Toh shkkn" daga haka suka yi sallama Mukhtar ya wuce, Sudais na komawa ciki ya sa Nanny ta dauko twins suka shiga mota, Ganin Khadijah bata fito sudais ya wuce sama ya bude kofar dakin duk da kukan da ya sameta tana yi kawai cewa yayi "Ke nake jira Amira" daga haka ya juya ya fita, Khadijah ta mike tana goge hawayen da ya ki tsaya mata ta fita, a gaban motar ta xauna Nanny kuma na xaune da yaran a baya suka bar gidan bayan Sudais ya sauka ya rufe gate, tafiyar kusan minti ashirin suka yi sai kallon agogo sudais yake har suka iso wani anguwa, anguwa ce mai kyau shi ma kamar wancan, yyi parking dai dai gate din wani bungalow babba ya fita ya bude gate din ya ja motar suka shiga gidan, sosai gidan ya hadu bayan yyi parking ya bude motar ya fito yana kallon Nanny yace ta fito da yaran da xuwa lkcn sun tashi daga baccin da suke, kallon khadijah yyi ta bude motar ita ma ta fito, Sudais ya nufi entrance din shiga gidan ya bude kofar da makullin dake cikin envelope sannan ya shiga, parlorn na da girma amma bai kai na can gidan sudais ba, sannan dakuna uku ne ko wanne da bayi sai kitchen da dinning area, da kuma bathroom da toilet a parlorn, gidan ya hadu, sai dai fa bai kai na sudais ba, Har TV akwai a parlorn bayan kujeru da center table da dinning table da chairs a area din da aka tanadar don ajiye su, kasa xama khadijah tayi a parlorn, Sudais dake tsaye shi ma ya nuna mata kujera ta xauna, sai a sannan ta xauna cikin sanyin jiki, ya dau little sudais dake ta daga masa hannu wai ya daukesa, Sudais na kallon Nanny murya can kasa yace "Madam ina son ki min alfarma daya na xaunawa tare da su even if it's just for few years to come for the sake of this twins, I will pay all the money in sha Allah" Nanny da jikinta yyi sanyi tace "Ba damuwa yallabai, Allah ya saka da alkhairi" Nan take sudais ya bata check na shekarun da ya fada, sannan ya nufi Khadijah yana kallonta ya ajiye mata envelope din hannunsa a kafarta a hankali yace "Gashi Amira this is for my boys, da sunansu na siya gidan nan don haka na su ne, mallakin su ne" kasa cewa komai tayi tana kallonsa, ya durkusa gabanta a raunane yace "I have always wanted the very best for you Amira, like... sending you out to UK kiyi karatu ki xama likita, a ko da yaushe hakan yana rai na amma saboda kananun yaran ki.... I decided sai sun kai ko da shekaru biyu ne sai ki tafi tare da su.... Am sad I couldn't fulfill that but you can ur self, promise me ko bayan babu ni, xa kiyi karatu ki xama babban likita, I mean ki min alkawarin xa ki cika min wannan burin nawa a kan ki" jin bata ce komai sai kallonsa take a tsorace ya kamo hannunta yana kallon kwayar idonta, he understand she's shock, ya lumshe ido ya mika mata check na kudi, da farko kasa magana yyi can yyi gathering courage with a breaking voice yace "Am going Amira, this is a check of 20 million, I think that all I've got for now, kiyi kokarin ganin with this little am giving you kin inganta rayuwar ki da na boys din ki, sannan ki ci gaba da rike mutuncin ki na 'ya mace duk inda xa ki samu kan ki, I wish na yi kokarin nema maki Umman ki kafin in tafi, I wish na kwato maki hakkin ki a gun dangin mahaifin ki, amma duk hakan bai yiwu ba Amira, ki kyale su xa su mayar maki a lahira idan Allah ya yarda, as for the twins.." Kasa ci gaba yyi, yyi shiru na wani lkci bai son ta ga hawayen idonsa, can yyi karfin halin cewa "I knw i will always love them tamkar yaran da na haifa a cikina, kar ki bari su yi rashi na Amira, ki dinga masu abinda nake masu, I mean ki so su kamar yanda nake son su, you are all they've got now, ke kadai gare su, idan kuma kika samu abokin rayuwar da kika ga ya kwanta maki kiyi aure amma ki fara sanar da shi ke wacece, a duk xaman mu Amira idan na taba saba maki da sani na ko akasin haka ki gafarce ni" kansa a kasa yace "I think that's all, akwai foodstuffs da na siyo daxu a kitchen, goodbye Amira, it's great knowing you in my life, wishing u better future ahead...." Ganin xai tashi Khadijah ta sakko kasa ta rikesa ta fashe da matsanancin kuka cikin rawar murya tace "Na shiga uku, don Allah kar ka tafi ka bar ni ni kadai, you are all I have with my kids, ka ce min fa baxa ka taba barina ba, don girman Allah kar ka min haka Aliyu, idan ka tafi ya xan yi..." Kasa kallonta yyi, ta daura kanta a kafarsa tana kuka sosai cikin raunin murya tace "Kasan ni marainiya ce, I don't have anybody, ya xan yi da yaran idan ka tafi ka bar ni da su Aliyu, don Allah kar ka tafi ko don su, ban san inda xan ga ummata ba kar ka tafi ka bar ni ni kadai a duniyar nan" Hakan da khadijah ta fada yasa Nanny ta fara kuka tausayin khadijah da yan biyun ya cika ta, Sudais yyi iya kokarin ganin hawayen idonsa bai sakko ba amma hakan bai yiwu ba, ya dago ta da kyar shi ma hawaye na xubo masa yace "Life goes on with or without me Amira xaku yi rayuwarku da yaran, you just have to manage the little I gave you cos I knw living in Abuja is expensive, surely watarana xa ki hadu da ummanki har ma da dangin mahaifiyar ki, I have to go now saboda Mamina, baxan iya tsallake maganar ta ba kiyi hakuri, ke dai kiyi min alfarmar kula da yan biyun ki, kuma ki daina jin haushinsu ki ja su a jiki, su kenan gare ki a yanxu, kar ki shafa masu laifin mahaifin su" daga haka ya mike ya isa gun twins din ya duka yana kallonsu a sanyaye, dariya suka fara masa suna daga hannu ya daukesu, ya manna masu kiss gaba daya ya lumshe ido murya can kasa yace "Long life to you both in sha Allah my boys, Allah ya albarkace rayuwarku ku xamto *hasken rayuwar* mahaifiyar ku" tashi yyi ya nufi kofa trying hard to control his self, Khadijah na kuka sosai cikin sanyin murya tace "Thanks very much Aliyu, Allah ya biya ka abinda kayi mana, and I will always pray for you in my life, kai din ka xame min _hasken rayuwa_ a lkcn da rayuwata tayi min duhu, daga ranan da na fara ganin ka ka yaye min bakin cikin dake tare da ni, you will always be the *light of my life* Aliyu" Sudais bai iya ya juyo ba har ya isa kofa, yaran na ganin xai fita suka fara kuka, bai yarda ya juyo ba har ya bude kofar ya fita yana goge hawayen idonsa, yana fita kuma ya bude wayarsa ya cire sim din da Khadijah ta san sa da shi ya jefar nan cikin flowers din gidan ya fita ya hau motarsa, and that was how Barrister Aliyu left Khadijah and her twins.

Khadijah ta shiga hali na damuwa sosai bayan tafiyar sudais, bata da aiki sai na tunani da xubda hawaye bata taba xaton rabuwa da Sudais a lkcn ba, da ba don Nanny dake gidan tana kwantar mata da hankali ba da abun ya mata yawa, gani take kamar sudais xai dawo kullum jiran tsammani take amma shiru wasa wasa har sati biyu, ta rame ba kadan gashi kullum cikin jin ciwo take a kirjinta, ciwon da ta fi shekara bata ji sa ba sai gashi ya dawo mata da karfinsa, hakan yasa Nanny ta tilastata suka shirya suka tafi asibiti don ko baccin kirki bata iya yi da daddare, khadijah bata yi mamakin abinda likita yace game da ciwon da take yawan ji a kirji ba, at anytime xata iya kamuwa da ciwon xuciya, yini biyu tayi asibitin under medication, nanny tayi ta kai kawo da twins xuwa asibitin, da yamma likitan ya sallamesu ya kuma bata shawarari da dama kan abinda ke janyo ciwonta da yanda xata yi preventing tashin ciwon, A hanyarsu ta dawowa cikin Napep da damuwa Nanny tace "Yanxu Mum twins da kike sa ma kanki damuwa haka idan abu ya same ki yaran ki fa? Ko don su baxa ki hakura ki rufa masu asiri ki kwantar da hankalin ki ki rungumi kaddara ba, kar fa ki manta ko wani bawa da irin tasa kaddarar, so why not just accept urs a yanda ya xo maki" Khadijah ta goge hawayen dake xuba idonta a hankali tace "Ban san ya xan yi ba" Nanny ta kwantar da murya tace "Cire komai xa ki yi a ran ki, kiyi facing sabuwar rayuwar da xa ki fara da yaran ki, bawan Allahn nan ya tafi, ya kuma ya maki duk abinda ya kamata kafin ya tafi yanxu the ball is in ur court, sai kiyi abinda ya kamata ki kuma rike addu'a sai komai ya xo maki da sauki, as a mother nake baki shawara Khadijah... For the sake of ur boys ki yi hakuri ki cire ma kan ki damuwa don Allah" a hankali khadijah tace "Toh nagode sosai" suna isa gida Khadijah ta sauka ta ba mai adai daitan kudi, xata karbi shureim hannun Nanny ya makalkaleta ya ki yarda, jikinta yyi sanyi tana kallon yaron, Nanny tayi murmushi ta fito da duk yaran biyu, khadijah ta karasa ta bude gate din sannan suka shiga gidan, ba laifi ta dau shawarar Nanny ganin shi kadai ne mafita a gareta sai dai hakan bai sa fara'arta ya dawo ba, she is always sad, bata taba xaton Sudais xai bar ta so early a rayuwa ba, kusan kullum sai ta yi tunaninsa, magungunan da take sha ya taimaka ya rage mata ciwon xuciyar da take fama da shi duk da baya tasar mata ma sai da daddare taji kamar xata mutu, ba karamin kokari take yi na ganin ta ja su little sudais a jiki ba amma sun ki yarda ko da yaushe cikin gudun ta suke kamar dodo, hakan na kara sa ta shiga damuwa Nanny ta dinga nuna mata a hankali xa su sake da ita kar ta damu, a ranan da yaran suka cika shekara daya a duniya Nanny ta raka Khadijah tayi enrolling kanta a ss1 na wani makaranta dake nan anguwar ta su, idan ba ita ta gaya maka tana da yara har biyu a gida ba in xa a shekara ana gaya maka baxa ka yarda ba, a lkcn kuma shekarunta sha bakwai a duniya, kana ganinta kasan she is a teenager, a hankali khadijah ta fara kokarin yakice tunanin sudais a ranta domin tayi concentrating a karatun ta, idan ta fita tun safe sai hudu take dawowa gida, sannan ga islamiyyar da ta shiga na yamma, hakan yasa still babu wani interaction tsakaninta da yaranta tun da ba xaman gidan take ba, amma har ga Allah yanxu ji tayi tana son abun ta duk da tsoronta da suke ji har lkcn. Haka rayuwa ta ci gaba da kasance ma khadijah har ta gama ss1 lafiya, xuwa lkcn abu uku ne ke damunta a xuciya, Rashin Ummanta, gudun ta da yaranta suke sai kuma ciwon xuciyar da ya sa ta gaba abu kamar wasa kusan ko da yaushe hanyar asibiti take wanda hakan ke sa ta fashin makaranta don ma tana da kokari, Sudais kam ta rufe sa a babin rayuwarta sai dai duk sllh sai tayi masa addu'ar Allah ya saka masa da alkhairi abinda yyi mata a rayuwarta da yaranta. Yau lahadi suna parlor, Nanny na feeding Sudais da shureim da yanxu shekarun su biyu da yan watanni a duniya indomie ta dafa masu take basu, yaran sun yi wayo sosai babu inda basa xuwa sai dai fa da ka gansu kaga Aliyu barin sudais komai na Abban nasa ya dauko, sau da yawa sai Khadijah tayi ta kallonsu, wani lkcn tayi murmushin takaici, wani lkcn kuma tayi hamdala ga Allah da ya bata yan biyun, Nanny ce ta katse shirun dake tsakaninsu tace "Mum twins to ya xa ayi da cefanen, wa enan ba yarda xa su yi in tafi in bar su ba, kuma wahala kawai xa mu je mu sha idan muka tafi gaba daya" Khadijah ta ajiye novel din hannunta tace "Nanny kawai da wayo xa ki tafi ki bar su" a tare yaron suka kalleta, Nanny ta kyalkyale da dariya tace "Toh ai kin tona, wa yace maki basa ji, sarai sun ji abinda kika ce" murmushi khadijah tayi tana mamakin sharpness din twins din, tuni shureim ya kara matsawa kusa da nanny, Khadijah ta tabe baki tace "Toh bari ni in je" Hijab har kasa ta daura kan kayan jikinta sannan ta dau kudin ta yi ma Nanny sallama tana daga ma boys din hannu ta nufi kofar fita su ma suna daga mata, jikinta yyi sanyi ganin in dai uwa xata fita yaranta sun dingi kuka kenan xa su bi ta, but why is her own case different, ko a jikin yan biyun dake cin Indomie da nanny ke basu har ta fita, to ita bata san kuma ya xata yi yaran nan su saki jiki da ita ba, iyakar kokari tana kokarin kwatanta masu abinda sudais yace Kafin ya bar su amma sun ki sakewa da ita, tana tsaye bakin titi tana jiran abun hawa a ranta kuwa tunani take ko dai abinda sudais ya fada kan nonon da bata basu ba gaskiya ne, kenan haushin ta suke ji? Ji tayi da ma basu girma ba ta basu nonon yanxu, tsabar yanda jikinta yyi sanyi bata lura da motar da har ya wuce ta da farko ya fara reverse a hankali yana dawowa ba, tana ankarewa ta dauke kai da sauri hade da tsuke fuska don hakan ma yasa bata son fita, tana mamaki da jin haushin me yasa in dai xata fita sai an tsayar da ita, ita ba wannan ne gabanta ba kuma bata jin xuciyarta xai kara kula wani d'a namiji har ta bar duniya, ganin mai motar ya fito daga motarsa ta bar wajen da sauri tana tafiya fuska daure ba tare da ta damu ta kallesa ba, ji tayi ance "Khadijah?" ta juyo da sauri suka yi ido hudu da shi, ya dinga kallonta kamar me son kara tabbatar da ita ce ko ba ita bace, ita din ma kallonsa take da mamaki, yace "Baki gane ni ba Khadijah?" Jikinta yyi sanyi lkci daya tayi murmushin da ya bayyana fararen hakoranta tace "Na gane ka, am just trying to be sure ko kai ne ko ba kai bane" ya wara yace "Maa sha Allah, Imagine we met after 3 good years" murmushi ta kuma yi tana kara kallonsa da kyau ganin yyi mata tsayi fiye da yanda ta san sa a da tace "Sure, to ya bayan rabuwa" ya rike chin dinsa yace "Waow kin girma Khadijah, just look at how calm you are now, kin tuna lkcn da kike yawo ba Hijab da jikakken kaya?" dariya ya bata ta rufe fuska tace "Har da tsokana" yace "Am serious, a Abuja dama ku ke?" Tace "Ehh wllh, ya su mama fa" yace "Suna kt, nima ban dade da fara aiki a nan ba, just 7 months back" Khadijah tace "Allah sarki, toh Allah ya taimaka" d'an shiru yyi yana kallonta, kafin a hankali yace "Ko kin yi aure ne Khadijah?" Kallonsa ta tsaya yi ita ma, lkci daya ta samu kanta da girgixa masa kai tace "Aure kuma, A'a ina karatu ne" yyi murmushi yace "That's good, kar in tsaya ina ta tsurutu da matar aure ban sani ba" murmushi kawai khadijah tayi a xuciyarta kuwa mamakin yanda aka yi ya fara magana ta yi don a lkcn da ta san shi da wuya yake magana sai dai danna waya, lkci daya jikinta yyi sanyi tuna abinda yyi mata a lkcn da take walagigi a katsina cikin yunwa, muryarsa ya katse ta yace "Ina xaki yanxu?" Ta kallesa tace "Kasuwa" yace "Toh shiga in yi dropping din ki" d'an xaro ido tayi tace "Kai da ba d'an gari ba?" Yace "Wata na 7 kice min ba d'an gari ba" murmushi tayi tace "Toh naji kai d'an gari ne" yace "Toh shiga muje" motar ta bude tana murmushi ta shiga, ya xaga ya shiga maxaunin driver suka bar wajen, yana driving yace "So ya rice and stew, and Irish with egg? Kuna nan kuna damawa koh?" Dariya sosai Khadijah tayi ta rufe fuska, yana murmushi yace "Yarinyar nan ta kashe min kudi a lkcn da abincin yan gayu gashi sai Abba ya bani nima lkcn" Khadijah ta dago a hankali tana kallonsa tana murmushi tace "Ae yanxu babu abinda bana ci har tuwo da miyar kuka, da ma kunu da kosai" ya wara ido yace "Da gaske? Anya xan yarda kuwa" ta gyada masa kai tace "Serious..." yace "Hmm that's surprising amma" ta turo baki tace "Baka yarda ba kenan?" yace "Toh ai ban ce komai ba Khadijah" suna isa kasuwa bbu yanda Khadijah bata yi da shi ya tafi ba yace xai jira ta, bbu yanda ta iya haka ta siya abubuwan da tasan xa su bukata a lkcn daga baya sai ta dawo ta siya sauran don bata son ta bar sa yyi ta jiranta, yana parking kofar gidan da ta nuna masa yace "Nan ne gidanku?" Ta gyada masa kai ta bude motar ta fita, yace "Toh ki gayar min da

Please Login or Register in order to submit comment