Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


Downloaded from GNOVELS.COM.NG




This Novel is downloaded from https://GNOVELS.COM.NG
to download more hausa novels visits our site at www.GNOVELS.COM.NG

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/gnovels

Twitter : https://twitter.com/gnovels

Telegram : https://t.me/gnovels

Compiled By Umar Dalha Funtua.




*_DA CIWO A RAYUWATA_*

Page A

   Na 🔷 Wawa shi ke fadin abin da zai aikata, mai kuri shi ke bayyana abinda ya aikata. mai natsuwa aikinsa ne ke bayyana matsayinsa.

*
*

  Mai_Dambu
   Wattpad:Mai_Dambu

         Da sunan Allah Mai Rahama Mai Jinkai

Adamawa State....

Jumeta, kwance yake a cikin lambu kanshi akan cinyata wanda yake lulluɓe da mayafi so yake yasaka hannunshi cikin ya yayye mayafin dake masa shamaki da ni, abin mamaki sai yaga hannunshi yaki kaiwa dole ya ɗago daga cinyarta gani yayi wani mutum da wasu yan mata uku da yar karamarsu suna janta koda ya mike take yaji tana cewa.
"Kazo ka taimakeni  Sadeeq kchvvvvarka bari su tafi dani Sadeeeeeeeeeeeeeeq.."

    A firgice ya farka daga mugun mafarkin da yake akaina wanda inda sabo yasaba ganin dattijon dake kusada shi yasa ya gyara zamanshi addu'a yayi sannan yacigaba da kallon kasa kamar mai nazari,
   "Assalamun Alaikumun" akayi sallama a bakin kofar ɗakin, sanin wanda yayi sallama ba bakonsu bane yasa Dattijon yace.
"Waalaikumun Salam, Imran kashigo mana ai gidan ba bakonka bane kota jikin bango zaka iya shigowa balle kuma ta koina nagidan."

      Bayyana yayi a gabansu cikin jin kunya ya dukar da kanshi yace.
"Malam jauro ina wuni, dukda
       Karfe sha biyu saura na rana,"

          "Lafiya lau Imran ya gida ya iyayenka, da sauran mutanenku." Inji Malam jauro yace masa.
    Murmusawa yayi kafin yace.
"Suna lafiya, kakatace ma ta aiko ni gurin wanca miskili bansan yanda zai ɗauki maganar ba dan nasan a halin ynx tsoron mutane yake, taya kuma zai iya kawo karshen wasu matsalolin."

      Shirune ya gifta tsakanin duk maganar da suke baisa ya ɗago ya kallesu ba, yasan daga Imran har kakanshi bazasu taɓa cutar da shi ba, sake cusa kanshi yayi cikin tsakankanin cinyoyinshi ya rufe idanunshi bayan ya zagaye hannunwanshi akafarshi, yayi musu shiru

    Gyara zama  malam jauro yayi kafin yace.
"Malam Imran da fatan lafiya dai wannan aikan."

Girgizai kai yayi kafin yace.
"Nidai tace min nazo na ɗaukeshi zuwa bauchi yayi wani aiki na taimako bayan haka bansan mi take nufi ba, naso nasan mi yasa ta turashi can sai tace min yaje zai ga abinda idanunshi"

        Bai ɗago ba kuma basuyi tsamanin zai ce wani abu ba yace.
"Kaka yau ma nasake tana ihu da niman taimakona Ya Allah kusani a addu'arku mana."
       A raunane ya kai ayar maganarshi, kusadashi Imrah ya isa ya dafashi kafin yace.
"Babu lokaci kazo muje ana jiranmu fa, sai dai kayi hakuri dan zaka zama bawa a wani gurine dan bayan bukatar wasu,"

         D'ago kanshi yayi cike ds ɓaccin rai ya ture hannun imrah sannan ya zabga masa harara kaman bazai magana ba nan kuwa a hasale yake da masifa.
Yace
"Wato ku aljannu kuna da matsala tunda kuka taimakeni shi knn kuka mai dani bawanku wallahi zan iya zabga maka naushi sannan naje har inda Kak....."

     Ji yayi a rike masa wuyarshi  ba tare da ya karasa batunsa ba, murmushi Imrah yayi sannan yace.
"Kaine kake da matsala bamu ba. Inda zaka domin kanka aka tura ka, matukar kace baxaka ba toh tabbas akwai matsala akan rayuwarku malam tashi muje babu lokaci."

          Sake masa wuya akayi  jikinshi ba kwari ya mike ya shiga haɗa kayanshi bawai baida yanda zaiyi bane sai dai bazai iya bijirewa ImraN da Family shi ba, sun gama masa kome a rayuwa sunyiwa Rayuwarsa hidima musamam Imran da Kakarsa mace.

     Yana gama haɗa kayanshi Imran ya kalli Malam jauro yace.
"Duk halin da yake ciki zai faɗa maka zamu haɗa karfi da karfe mu taimaka musu, amma dole sai yaje Bauchi tukun yaga muna maka sallama irinta addinin musulunci."

        Jinjina kai Malam jauro yayi sannan ya mika masa hannun sukayi musabaha, haka ma Sadeeq ɗin suna fitowa tsakar gida sukayi kiciɓis da Innawuro kallonta Sadeeq yayi sannan yace.
"Tsohuwar karfena zanyi balaguro nawani lokaci."

     Tsaki tayi ciki ciki, sannan ta kunce goron bakinta ta ɓantara cike da masifa take taunawa sannan ta ɗago manyan idanunta ta banka masa harara tace.
"Wallahi ka kwalta tuzurun banza tuzurun wofi a haka dai zaka zauna kana bacci a ɗaki idan ka isheni auro maka Bintalo zanyi."
       Murmushi yayi ya juya suka bar cikin gidan har yakai bakin kofa ta kwala masa kira dole ya tsaya cak tana zuwa ta mika masa farin langa bokiti tace.
"Gashi nan sadiquna dambu zabine." karɓa yayi sannan ya mata godiya, juyawa tayi tana shafce hawayenta cike da bakin ciki komawar jikarta haka, koda suka shiga mota basu ɓata lokacu ba dan motar Imran ce.

          *Bauchi State*

   At A.T.B.U......

A hankali nafito daga cikin aji ina tafiya a gajiye sabida tsayuwar danayi na koyar da ɗalibaina yan matakin masters duk jikina yaga mutuwa gida kawai nake bukatar zuwa, ofishina naje nagama abinda zanyi nasa kai nafito ko bakin kofan ban bari naji suna min dariya ɗaya daga cikinsu nace.
"Eh nafaɗa maku budurwace bata taɓa aure ba, wallahi."

     Can wani a cikinsu yace.
"Ina budurwa a talatin da ɗaya budurci yayi gaba abinshi yaushe zata zauna babu namiji bazawara dai ko,"

          Haka sukayita faɗar maganganu akaina, da sauri na isa gurin motata na tada ita a guje ina tuki amma zuciyata cike yake da kunci haka nafigi motata raina a ɓace wai shin nizan iya sauya kaddarata ce, da mutane suke kalubalantata, dakyar Allah ya nufa na isa gida, ko parking me kyau banyi ba na fita daga motar aguje ina kuka, yana zaune shida Baba maigadi, wanda yq buɗe min kofa, da kishiyar Inna nafara cin karo inda na zube a jikinta tare da fashewa da wani irin kuka, jikina na rawa na ɗago kai ina kallonta cikin kuka nace.
" Nenne shin laifina ne da banyi aure ba, ko wani yana wucce kaddaransane."
   Girgiza kai tayi a tsanake sannan tayi murmushi sannan tace.
"Kome yayi farko zaiyi karshe Amrahtu hakuri da kikayi na shekaru yakusan zuwa karshe kiyi hakuri kinji"

        "Nenne Da ciwo a rayuwata fa, tun kuruciya nake kuka Nenne har yau kuka nake, duk wanda yazo gurina yau gobe bazai sake dawowa ba idan kuma ya dage da  niman aurena karshe mutuwa yake."

     Shafa kaina tayi tana kallon fuskana da yayi ja, itama goge kwallarta tayi sannan tace.
"Tashi ki shiga ciki,"

     Haka na mike jikina bakwari na shige ɗakina da aka ware min, sai da nayi kuka mai isata sannan na rage kayan jikina na ɗaura towel na shiga wanka, ina fitowa nayi sallar la'asar na dan kishingiɗa sai barci  sosai nayi, sai gurin karfe biyar da kwata na mike shima sabida mafarkin da nayine wanda ina tashi na manta kome wanka nashiga da alola sannan nasaka doguwar riga mai karamin hannun nafito zuwa falo, muryan Ya Abbas da Baffanmu yasa na karaso fuska ɗauke da murmushi na zauna a cikinsu, nan kuwa hira yasake ɓarkewa har muka gangaro maganar, ɗaukar min drive da akayi shiru nayi kaman ruwa ya cinyenk, kiran sunana Baffanmu yayi.
"Amratuuuuu, shin drvn bai miki bane naga kinyi jum."
   Girgiza kai nayi cikin sanyi jiki nace.
"Baffa ba haka bane kawai gani nayi ai nima zan kula da kaina ko?."
     Kaina a sunkuye na bashi amsa
"A'a Amrahtu ina gudun kar wani ya sake yunkurin cutar dake ne, shi yasa na daukar miki shi kuma naganshi yana da kamala da nutsuwa!!!" nufashinsa ya sauke kafin ya cigaba da cewa.
"Gashi yana da ɗan ilimi dan har N.c.e yayi zanga takardunsa sai na nima masa aiki kinga bazai kare a tukaki ba kafin Allah ya kawo miki miji na gari, yawwa ɗazun suwaye suka saki kuka."

          Murmushi nayi sannan nace.
"Ai ya wucce a manta dasu kawai."

     Sai naji zaman falon ya gundireni, dan bana son tukani da wani zaiyi, koda yake banga laifin Baffa kwana uku da suka wucce ina fitowa daga yelwa zan yanko kwanar governmen house wasu yan dabba suka tare ni har suka fasa min glass ɗin motata,  dakyar Yan sanda da suke gurin suka koresu parking nayi na kira Ya Abbas wanda yake aikin a Cid office yazo ya daukeni cike da tsoro anyi bincike ba agano ko suwaye ba shi yasa aka ɗan saka min matakan tsaro wanda Aikin Ya Abbas ne,

    Dakina na koma cike da jin haushi, buɗe wayata nayi na duba naga babu data, tsaki nayi na ɗauki gyalena zuwa waje kafana sanye da yar silifas taroba mai pink da blue, a hankali na fito harabar gidan suna zaune da ma'aikatan gidan, idan suke hira cikin nishaɗi shi kuwa yana zaune murmushine kawai akan fuskarshi, kallo ɗaya nayi musu na kauda kaina Nura me yiwa flower gidanmu ban ruwa nakira na bashi 3k nace ya sayo min da sauri yafita, ina tsaye a gurin ina kallon motata da naga an gyara mata zama, tunawa nayi da akwai abubuwa a cikin motar, a hankali na isa gurin motar nasa hannuna na buɗe, ban lura ba sabida hankalina na kan Nura da ya shigo cikin gidan nakai hannuna knn zan ɗauki kayana, kamar ance kalle, hmmm macizai guda huɗu nagani a cikin motar tsananin tsoro da firgici bansan lokacin da na daka tsalle ba, sannan na akwala ihu tare da rufe motar zaman dirshan nayi a can gefe guda jikina na rawa,

     Kafin ace wani abu duk masu aikin gidanmu da Baffanmu da Ya Abbas haɗi da Iyayena mata son kawo min ɗauki har da shi a ciki suka iso kaina kowa na tambayana lfy kamar wacce ta tashi daga barci na mike zubur jikina na rawa nace musu.
"Wallahi wasu irin macizai nagani a cikin motata, ni na hakura da motar,"

    Buɗe motar sukayi aka duba ba'aga kome ba yana jingine da motar Ya Abbas.

              Haka sukai ta niman macizan nan babu su babu dalilinsu, asalima kamar babu alamarsu, haka suka hakura suka ɗibo min kayana zuwa cikin gida jikina a sanyayye na shige ɗakina ina jinjina wannan al'amarin
         
         ***
Washi gari.....
  
Karfe goma da rabi nafito ina fitowa nasame shi a cikin motar, taɓe nayi sannan na shiga motar a hankali yaja motar, wayarshi ya ciro ya duba map ɗin bauchi A.t.b.u yayi searche nan hanyan ya fito masa, jinjina girman kanshi nayi ace mutum ga wanda zaka tambaya, hmm.
      
          Har cikin makrnt ya shiga dani nan ne kuma yayi parking yana kallon wayar can yasake figar motar har department ɗinmu ko cikan ka bance ba nafita tare da ɗibar kayana zuwa ciki, bai tambaye ni yaushe zai dawo ba nima ban damu da na faɗa masa ba......

#Fiction
#Spirits
#Jinn
#Amsad......By Mai_Dambu

*_DA CIWO A RAYUWATA_*

Page B

   Na
  Mai_Dambu
   Wattpad:Mai_Dambu

         Da sunan Allah Mai Rahama Mai Jinkai

      Karfe ɗaya narana ina fita anan na same shi yana jirana, buɗewa nayi na zuba kayana na zauna sannan muka bar makrnt a gajiye liɓis sai ajiyar zuciya nake sabida gajiya,

          A titin Ahamdu bello way muka tsaya gurin traffic muna jira wasu yan mata guda huɗu suka zo ta inda nake kaina a sunkuye, ina duba wayata, dukda glass ɗin a rufe yake amma abin mamaki sai jin muryansu nayi suna cewa.
"Umma abamu sadaka sabida Allah"

      Cike da mamaki na ɗago kaina ashe a waje suke, kallonsu nayi kafin na shiga kiciniyar zuge glass ɗin yaki buɗuwa daga gaban motar yace.
"Koda wasa karki basu kome na faɗa miki."

    Mamakine ya sake turnike ni na zuge glass ɗin motar na mika musu 1k kuwa garin kiciniyar karɓa naji sun karceni da wani abu kamar farce da sauri na maida hannuna ina yarfewa, ɗago kaina nayi da niyyar kallonsu wayam nagani babu su babu dalilinsu, sake duba hannun nawa nayi naga yayi wani irin ja.....

          Inda babu ciwon na fitar da wani irin zufa, shiru nayi har muka bar gurin jikina yayi sanyi  koda muka isa gida yana fakin na kwashi kayana zuwa cikin gida abin mamaki hannuna kara kumburi yake, har na shige ɗakina babu kowa ina shiga  zubar da kayan nayi na faɗa ban ɗaki ina kwara ruwa ko kayan jikina banyi ba sabida mugun zafin da nake ji, ina fitowa na yanki jiki na faɗi.....

                ****
"Koma Yaya ne dole kasaka ido akanta dan sabida ita kazo gidan nan kayi kokarin gano inda matsalar take, ynx haka tana can ɗakinta ta suma sabida gubar macijin da ke jikinta, kasan abinyi kafin lkc ya kure maka." Inji Imran knn,
          "Toh ya kake so nayi mata sam babu ɗa'a afuskarta mutanen gidan basu da matsala amna ita tana da matsala dan na lura  bata da kunya kodan kananun kuɗin da take ɗaukane suka ɗaga mata hankali shi yasa take hura hanci ranar da ta ɗauki manyan kuɗi ai ba'a magana ni babu abinda zan iya mata."

          Da imran yaga bashi da niyyar zuwa sai ya ɓace a ɗakin ya rikiɗe zuwa sufar Sadeeq ya shiga cikin gidanmu yayi sallama a kofr falo Badi'atu ta amsa masa sallqmar, tare da ɗaga labule "sannu dai kana son wani abune?"
   Ta tambayeshi tare da kafa masa idanu, girgixa mata kai yayi sannan ya mika mata wayata, yace.
"Hmm ɗazun nazo karkaɗe motar naga ashe Hajiya ta manta wayarta a motar."

    Karɓa tayi tare da sake masa murmushi dan sadeeq Allah yayi masa baiwar kyau kamar mace, fari tasss.

   Kaman yash, haka yake kunga dole badi'atu ta sussuce, niko a jikina dan kyanshi bai burgeni ba asalima ni baka ce  dan duk yan gidanmu farare ne nice baƙa , yana mika mata ya juya da sauri yabar kofar falon,

       Itama kuma ta komo ciki ɗakina halin da tasame ina kwance malala akasa, kamar mara numfashi, ihu ta fasa sannan tafita da mugun gudu tayi ɗakin Nenne ta faɗa mata kasancewar Innarmu ta rasu, nenne ita ta zame mana uwa, kuma,da itace uwar gidan baffa. Tun auren saurayi da budurwa, ita tahaifi Ya Abbas sai aunty Mariya sai....

   Da sauri mutanen gidanmu suka shigo ɗakina suna zuwa suka shiga kiciniyar ɗaukata basu ajiye ni a ko ina ba sai asibitin  City clinic dake titin bank road da gaggawa aka amshe ni kusan babu bincike da basu yi ba haka suka cigaba da zuba min allura har bayan kwana uku,

     Karshe wancan yaron dasuka kawo a drv na shi yakawo maganin da aka shiga bani ina sha, sai gashi nayi aman wani farin ruwa kamar madara mai shegen wari. Kwana shida aka sallameni.

                 ***
Abinda na lura yaron yana da girman kai, dan dakyar ya shigo gaishe ni ko kallon inda yake banyi ba nace lafiya.
             Daga haka ban kuma kallon inda yake ba, asalima ɗan banzan yaro kwarjini yake min bansan dalili ba...

                 ****
    Kusan satina biyu a gidan na fara zuwa a.t.b.u. ranar da zan fara zuwa ban faɗa masa ba sai ganina yayi a shirye aikuwa ya taso yazo ya buɗe motan ya shiga abinshi yusha'u ne yazo da sauri ya buɗe min kofa motar nasaka kayana raina aɓace nacewa.
"Yusha'u nagode sosai."

    Tsaki nayi kasa kasa nace.
"Yaro karami sai tsabar iskanci da rashin kunya idan mutum bazai iya aikin ba ya bari mana."

       Murmushi yayi da gefen baki yaja motar zuwa makaranta.

Ina gama koyarwa na shigo officer din sai ga H.O.D mun ya shigo nan muka gaisa dashi hankalina na kan aiki ashe shi nashi hankalin akaina yake ban ji haka nayi a jikina ana kallona ina dago kai sai ya shiga sosa kanshi yace.
"Dama ina son magana dake maybe zan shigo unguwarku da yamma."

A hankali na saci kallon yan ofishinmu sai naga kowa harkan gabanshi yake dan haka na gyaɗa masa kai kawai dan babban mutune ya manyanta sosai dan haka da girmamawa a tsakaninmu.

       Ina tashi nafito har gurin parking nazo babu yaron nan babu dalilinshi haushine ya kamani na tsaya jiranshi can sai gashi yana zuwa na buɗe nasaka kayana na shiga ciki na zauna.
Nace.
"Wannan wani iskanci ne daza tafi yawon banzan ka, ko kamanta da ina jiranka ne, eyye ni bana son shashancinku irin na yaran nan."

     Juyowa yayi ya kalle ni sosai kafin ya juya ya fara tafiya ranshi ya ɓaci sai tauna bakinshi yake har muka isa gida.

      Bayan sallar magarib sai ga h.o.d mu yazo iso nayi masa har falon baki anan dai muka gaisa na ajiye masa abin taɓawa, yasha ruwa sannan ya zuba min ido kafin yace.
"Amrah dama nazo ne ina niman damar aurenki da fatan ba matsala kinga dai mu ba yara bane ya kamata mu tsayi da magana ko ya kika ce, dan nasan akalla shekarunki bazasu haura talatin da ɗaya zuwa dabiyu kinga ni kuma next month nake da hamsin da huɗu da fatan ban tsofa miki ba"

    Kunya ce tasa na rufe fuskana ina dariya tare da gyaɗa masa kai mun dan zanta kaɗan sannan muka rabu jibi zai turo magabatanshi,

      Ko Nenne ban fadawa ba sabida nasan ba lallai bane yasake dawowa, washi gari har ofishina ya biyo ni inda muka ɗan taɓa hira har yake tambayata a ina nayi master da phd nace masa a Canada munyi hira sosai sannan muka rabu abinka da jami'a sai gashi ana gulmarmu..

                Kaman yanda yace haka kuwa takasance sai ga manyanshi sukazo har gida, dake sun shirya har da sadaki suka bada,
     Sati uku tsakanin sai ga kayan aurenshi soyayya ba kama hannun yaro, sai wani rawan kai nake amma duk da haka lokaci zuwa lokaci jikina na sanyi da al'amarin,

     Ansa bikin wata biyu masu zuwa dan haka kowani shashi shiri ake sosai musaman ta shashinmu anfi shi,

    Lokaci na tafiya yanayi nakara kitsu kai har binki ya rage saura satittika a hankali ya sauko yan kwana ki.

      Ana saura kwana biyu anyi kamu washi gari juma'a akayi walima, bayan an watse yazo gidanmu nafito har motanshi na shiga muka gaisa, fitar da ɗaya kafarshi yayi waje mukq cigaba da hira can yaji kamar cizon kwaro yana dubawa yaga babu kome dan haka ya share muka cigaba da hiranmu can yaji kafar tadameshi dan haka mukayi sallama, ya tafi yana isa gida yasa kai zai cire kafar sai yaji tayi masa wani irin nauyi kamar dutse tayi fari fat, ga wani irin farin ruwa na zuba ,

  Dakyar ya shiga cikin gida dake gidansu family house ne amma kowa da side ɗinshi,

                    Dakyar ya shga babban falo yana,zuwa ya yanki jiki yana zubda wani farin ruwa irin wanda yake fita akafarshi.......

Toh fa

#Fiction
#Spirits
#Jinn
#Amsad......By Mai_Dambu
Pls share nd Comments🥰
🌺🌷🌷
*_DA CIWO A RAYUWATA_*
                                  🌹🌸🌸
Page C

   Na
  Mai_Dambu
   Wattpad:Mai_Dambu

         Da sunan Allah Mai Rahama Mai Jinkai

Page C.

    Salati duk matan falon suka saka tare da mikewa suna kiran sunanshi "Alhaji Yusif"
Yaranshi kuwa har sun fara kuka shigowar ɗaya daga cikin Yaranshi da gudu ta zuɓe a gurin tace.
"Ku kyale min Babana karku kuskura musa kafar wando ɗaya daku ku kyale shi naceeee"

              "Hahaha Zabba'u kenn zamu kyale shi sai ya janye daga niman auren Uwarmu in ba haka ba sai dai ya mutu dan alkawari muka ɗaukawa Babanmu sai mun kashe duk wanda yace zai aureta kuma duk kashedin da muka..."

       "Keee Fauzn ban tambayeki ba ku fita min a jikin babana" Zabba'u ta buga mata tsawa,

     Abin kamar almara haka idanunshi suka koma fari fat kamar yanda jikinshi ya koma dan har gashin kansa yayi kaman hazo.

      Tun goma na dare ake abu ɗaya har karfe biyar na asuba a dare aka nemo wni malamin yazo suka sakasu a gaba ana abu ɗaya sun kafe sai ya fasa auren matukar aka fasa ko hanyar da yake bi bazasu sake bi ba.

          Suka je masalaci suka dawo da kanenshi maza da wasu yan uwan babanshi da Mahaifiyarshi suka tsayida magana a janye auren an fasa sun tsayida shawara misalin goma nasafe,   gurinshi suka zo sukayi sallama dakyar suka amsa,
    "Toh mun janye auren ya fasa Insha Allah ya rabu da ita knn."

    Kafin malamin ya gama magana har sun fita abinsu kafar dake ruwa ya koma kamar bashi ba dama ta nan suka shigeshi, ya jima yana bacci kafin ya farka nan mahaifiyarshi tace.
"Toh dama ai ba yau akafaɗa min kome akan yarinyar da kake nima ba dan haka indai nice na haifeka na haramta maka aurenta har duniya ta tashi."

     Shiru yayi yana kallon mahaifiyarshi kafin ya gyaɗa kai, nan aka shiga niman mutanen da zasu gidanmu suce an janye aurena.

              :::
     Yana kwance tun da nayi sallar asuba zazzaɓi ya rufe nu,dakyar nasamu nayi wanka nasha farfesun da aka haɗa min waina gyara, ina sha ina sake murmushi sabida son da nake alhji a shirye nake na bada kome nawa kuma ai dama ni nafi son auren babba wanda ya manyanta zaifi sanin darajata akan na auri sa'ana ko wanda bai fini ba, ko wanda yafini da kaɗan dan dukkanmu sai a hankali.
         Key motata ce faɗo min arai na mike da sauri ina jin hayaniyar yan shirin ɗaurin auren karfe sha ɗaya sai kaiwa da komowa suke,   ta kofar kitchen na bi naje har inda wanca yaron yake yana ɗakinsu ganin Yusha'u nace.
"Yusha'u ina wannan yaron yake?"

     Kallona yayi da mamaki yace.
"Wani yaro hajiya kuma."
    Taɓe baki nayi nace.
"Sabon drvn nan mana"
           "Ai Sadeeq"
      Nayi masa shiru nuna min ɗakinsu yayi yace.
"Yana jinki ai dan yana ciki."

     Haushine ya kamani na bankaɗe labule, yana sanye da farar dakakkiyar shadda kamar shine angon. Tsaki nayi a madadin sallama na mika masa hannuna nace.
"Bani key"

   Kamar da dutse nake magana idan kuka ganni dashi sai kun jinjina min rashin kunyata Eh nasan na girmeshi but baxai wucce irin 2yr to 3yr bafa amma ji nake kaman na haifeshi, sabida ina koyarda wanda suka fishi da sa'o'inshi a jami'a gani yar karama dan idan ban faɗa maka shekaruna ba bazaka yarda ba,sabida ni yar mitsila ce, kome nawa karamine shi yasa mutane suke raina girmana, amma duk da haka inada cikar halitta daga sama har kasa, sake nanata masa nayi nace.
"Ɓazaka bani key ɗin bane ko sai na maka ihun ɓarawo ishashe mara kunya"

            Ɗago idonshi ɗaya yayi ya kalleni daga haka bai kuma cewa kome ba, fusata nayi na shigo ɗakin na tsaya masa kerere a tsakar kanshi ina masa rashin mutunci.
      Mikewa yayi tsaye Wallahi basan lokacin da na ɗaga kaina ina kallon basumudan gaba ba, kutt nace a raina, dama haka yake da tsawo sai gani a gabanshi kamar lomar tuwo, saka hannunshi yayi a aljuhunshi ya wurga min key ɗin, tsabar raine kin ɗauka nayi nace.
"Zaka ɗauko kabani ko sai na falla maka mari"  
     Zama zaiyi amna baisan lokacin da dariya ta,suɓuce masa ba,
         Gyara zama yayi irin bismillah nan haushi yasa na ɗauki key na nayi gaba ina masa gorin yazo cin arziki yanawa mutane gadara. Bai damu kallon Imran yayi yace.
"Kaii Wannan matar akwai masifa na tausayawa mijinta."

       Dariya imran ɗin yayi yace.
"Idan kuma Allah ya nufa kaine

Please Login or Register in order to submit comment