Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zata fiddani duhu.

B'at ta ɓace.
Lokacin da Imran yafita kallonshi Sadeeq yayi cikin tsokana yace.
"Dama haka kuma kuke raya luv, ai dole na ɗauki darasi, amma kuma ya akayi kuka rabu da ita me ya haɗaku."

"Ynx babu lokaci bari na nemi dalme shine kaɗai zai taimaka mana."

Yana zaune ya kura dalme shima yazo yace.
"Eh malam gaskiya kurayen nan yaran kabusu ne amna nayi maka alkawari da yarjejeniyar dake tsakaninmu bazasu sake zuwa ba shima kabusun nasa an kama minshi sai kuma bokan da yayi idan babu damuwa zaku iya zuwa ku dakatar dashi."

"Toh bokan yana ina ne ynx." Imran ya tambayeshi.

"Eh toh malan bokan yana bayan dutsen manbila."

"Toh mun gode zaka iya tafiya."

Yana ɓacewa Imran ya kalle sadeeq suka tashi sama rufe sadeeq yayi da hiraminshi take suka lula sama, basu dira ko ina ba sai dutsen manbila.


A kogon dutsen kuwa Nuwarai da Fauza Rusaila,da Fatihiyya suka naɗe boka suna saranshi ya faɗa musu wanda ya saka shi aiki amma fir yaki tunda abin ya faru suka shiga bin didigin al'amarin har suka gano shi da suka zo cikin lumana bai sauraresu ba har sau uku, sukuma suka kafe sau sunji waye ya sakashi aiki, sunyu artabo na wata kusan biyar kafin yau Allah ya basu nasara, inda suka samu yana zubawa wani gunki jini wanda jikknshi duk gashi nan suka mashi fata fata da kayan aiki kafin suka naɗeshi.

Ihun shi Imran yaji suka bazana niman hanya dakyar suka samu, suna shiga suka sami gawarsa Yan mata huɗu na tsaye suna huci. Motsin Imaran da Sadeeq yasa duk suka juya ajiyar zuciya Rusaila tayi me ɗan karfi, tace.
"Ku muje"

Rufe kofar Imran yayi da wani net ɗin karfe, juyawa Fatihiyya tayi kan imran a fusace aikuwa yayi wurgi da ita take yasa sarkan karfe ya ɗaureta, sauran ma haka da suka fusata Rusaila ce bata motsa ba saima kallonshi take tana zabga murmushi, tace.
"Da kyau jarumin maza ka ɗaure min Yan uwana kuma ai dukkanmu abu ɗaya muka zo yi kawai kasake min yan uwa muyi gaba."

Ko kulata baiyi ba ya cigaba da dube dube shida Sadeeq can idanunshi ya sauka akan wannan gunkin da boka yake xuba masa jini, kallon abu yayi yanda gashi ya tsiro ta ko ina yana hango amrah take ya shiga karantu wasu addu'o'i ya saka wuta ya kona abin take wani bakin hayaki yayi sama,

Kuncesu yayi yace.
"Kunga ni bana son damu miye ya haɗu ku da amrah."


Cikin fitsara fauzan tace.
"Mahaifiyarmu ce sai ya-ya"

"Sai naci kaniyarku har da ubanku ina matata ta zama Uwarku" Inji Sadeeq, baya sukayi dan sun hango fusata a idanunshi kuma basu ga tsoro ba.

Cikin sanyi murya Rusaila tace..
"Kuje ku tambayeta zata faɗa muku abinda tasani sauran kuma nayi alkawarin faɗa muku zan taimaka muku, amma don Allah Magajin sarki malamai kabani gurbi nima na shiga sahun matanka."

Zaro ido imran yayi cike da takaici yace.
"Nifa ba sa'an Uwais bane sabida na bashi shekaru ɗari a duniya da furfurana zaki ce."

"Eh nace ina sonka sai me tunranar da ka kawo shi gidansu Umma nake bibiyarka, laifine dan nace ina sonka yeehe."
Har jikin bango ta kaishi tana masifa, tsura mata ido yayi a ranshi yace.
*Masha Allah amma na shiga uku da Zalja*

Sadeeq ne ya shiga tsakaninsu yace.
"Kinga ya isa ai dole ma ya aureki amma ynx muna da abinyi sai wani lokacin"

Fita sukayi yan uwanta sai banka mata harara suke ko ajikinta.

****
Ina kwance nayi duk jikina ya jike buɗe ido nayi naga babu gashin jikina tass, Nanah da Iyayenta na gani a kaina, nuna min yatsa babanta yayi sannan yace.
"Wannan karon kin tsallake rijiya da baya next target ɗina bazakiyi escape bA rantse miki kaman yanda naga bayan Mustapha toh sai naga bayan Sadeeq"

Tsoronsu ne ya hanani cewa kome.

Fuuuu suka bar gidan suna fita Sadeeq da Imran suna shigowa a birkice na fashe da kuka nace.
"Wallahi bazan iya zama da kai ba kawai ka sallame ni,."

Shiru yayi kafin ya kalle imran kallona yayi sannan yace.
"Zan sake ki amma ki fada min kaɗan daga cikin rayuwarki da me yasa macizai ke bibiyarki."

A jiyar zuciya na sauke kafin na zauna na fara da cewa.
Suna na Amrahtu Yusif Jam'are.........


Ku biyo ni dan jin wannan chaqwaqiyyar Kaiii Team Aljanu luv😹👌 Yan mata masu niman haɗeɗɗen gaye ga Imran fa
🌺🌷🌷
*_DA CIWO A RAYUWATA_*
                                  🌹🌸🌸

   Na
  Mai_Dambu
   Wattpad:Mai_Dambu

         Da sunan Allah Mai Rahama Mai Jinkai

```Nagode sosai smart Feena na gode da kyautar page Allah ya kareki da sharrin masu sharri```
*Page L*

 

Mahaifina ɗan karamar hukumar jama'are ne dake jahar bauchi mu goma sha uku ne a gidanmu mata biyar maza takwas, Ya Abbas shine babba sai Aunty MommY, sai ya Ali kafin Aunty Mariya ta rasu, sai Junaid, kabiru, Aunty Adama, Aunty Rahma,Sai ni, sai muttak, Rufa'i,Mubarak,
Duk cikin dukkanmu goma nan bayan Ya Abbas da Ya Ali da Aunty Mariya sune yaran Nenne kishiyar Innarmu, duk sauran ɗakinmu ɗaya dasu Aunty Mommy ce babba a ɗakinmu,

Gidanmu mun taso da tarbiya sosai dan Baffa ɗan bokone yayi aikin gwanati, kafin yayi retire sai ya buɗe kasuwanci abinshi.

Nenne mai suna Hajara yar garin shira ce, tafito daga garin maɗaci, Innarmu kuma yar Alkaleri ce, daga kauyen mainamaji.kusada dajin yankari, duk yan gidanmu manya nice kawai yar karama, dan tun da aka haife ni ake ganin kaman nazo da ciwo shi yasa duk yan gidanmu suka mai da hankalinsu a kaina, rashin girma yana damun kowa amma a gurin baffa ba haka bane, yakance na gado Mamarshi ce itama haka take kamar ni, shi yasa bai wani damu ba,

Ina da shekara huɗu aka cusani a makaranta sabida fitinansu inna da nayi, dake ina da baki amma bana son magana haka na dinga naɗar kome sai lokacin exam ake gane kokarin, ina da shekara goma sha ɗaya na gama primary, nan Baffa ya shiga niman min special schl kafin madaki, ana samun makarantar sai inna tace wa baffa kafin akaini tana son takaini garinsu duk yayuna maza da mata sunsan mainamaji nice kawai ban sani ba, bai ja ba ya amince.

Inna ta shirya min kaya sai mainamaji, inda zamu kwana biyu idan ka kalle ni a lokacin bazaka ɗauka na kai sha ɗaya ba, sabida kankantata,


Tunda muka isa gidansu inna hidima ake mana sosai ga yara sa''o'"ina, haka suke jana zuwa kalle gyaɗa, wake, masara.etc, idan kuma muka gama da yamma su jani zuwa bakin kogi, muyi wanka mu debo ruwa zuwa gida kusan satinmu biyu, dan mukusan dawowa gidan da yammacin jumma'a muka tafi rafin wanka saura sukayi ni kuwa naki wanka, da nagaji na ɗauko tuluna nayo hanya gida,, ina cikin tafiya na hango wani abu kato ya tare hanya gashi yayi gamo, ga kananun macizai suna hayeshi ihu nayi tare da sake tulun daga kaina zuwa kasa, tare da kamewa a gurin fusata abun yayi mike tsaye zai kai mun sura sai kuma ya tsaya cak, yana kallona yanda nake kyarma ga idanuna a rufe, ɓat ya ɓace, bana jin motsin su buɗe ido nayi naga wani mutum a gefe na da kayan saki, yana murmushi hannunshi rike da sarewa, yana tattara macizai yana zubasu a cikin wani gora,

Tafiya yayi rike da goranshi har ya kulle, tun da nadawo gida zazzaɓi ya rufe sai da muka bar garin na samu sauki sai dai mafarkin macixan nan da mai ɗauke dasu ya hanani sakat duk na firgita, wata rana naje hadda muna cikin karatu na hango macizan nan suna tawowa ajinmu ihu nayi ina yarfe hannuna ina nuna gurin babu wanda ya lura da kome, haka na dawo gida,

Tun ina jin tsoro suna firgita na rasa wanda zai faɗawa gashi an rufe min bakina, ana gobe zan tafi kafin madakine, muka shiga kasuwa mukayi sayayyan kayan makaranta da baffa, zamu fito kasuwa naga wani tsoho almajiri na roki baffa ya bani kuɗi na bada sadaka,

Hamsin ya bani ni kuma na bawa tsohon karɓa yayi sannan yace.
"Allah ya karɓa, Lallai mutum baya wuccewa kaddaransa Yarinya Allah ya kareki daga sharrin abin halitta"

Haka muka tafi dake na rike maganar ina zuwa gida na rubuta a book ɗina, dan kalmar tayi min daɗi,

Washi gari muka bar bauchi zuwa kafin madaki, inda aka kaini har ofishin shugaban makaranta ita kuma ta haɗi da Metro, ɗakin da aka kaini aka mika ni hannun wata yar yobe Nazifa,

Shiryawa nayi aka kaini class inda aka haɗani sit da wata yarinya mai suna Princess, yarinyar kyakyawa ce na karshe kome nata me kyau ne sai dai abin mamaki ji nake kaman na kashe yarinya wani tsanarta nake ji,
Ba ita ɗaya ba har da wasu ɗalibai da suke bayanmu, da akayi break mika min wani pack na cake tayi da wasu kayan zaki.

Kallon cikin idanunta nayi sosai naga wani irin wuta na tashi a cikin murmushi nayi na kauda kai take idanuna suka koma fari fat, kallonta nayi ido cikin ido nace.
"Ki rike maitarki ni bana ra'ayi karki kuskura ki shige min domin kasheki zanyi.".

Duk yan class ɗinmu da suke tsoronta sai da suka razana jakata na buɗe take tahango macixai murmushi nayi na rufe,

Na fita break abuna take na sake ina sha'anina Nazifa ce tazo muka je ta class ɗinsu takw nuna ni tayi dota, duk suka tayata murna sai wata can da yan koranta wai nazifa ta kawo ni jikin nazifa na rawa tace.
"Amrah jeki Queen nakiranki.:"
Dariya nayi nace.
"Ba queen ba ko king ne bazani ba idan ta matsu tazo."

Tana jina nima ban damu ba, sabida bana tsoranta,

Kallona tayi ta hango abinda zai dameta sai taki kula abinda nace.

Wato makaranta ya ɓaci da kungiyar asiri na fitan hankali, kuma suna bibiyar kyawawan yara, ina da kyau amma ni baka ce, sai suka takura nazifa da lallai ta kaini ni kuwa naki basu fiska,

Satina biyu kullum nayi sallar la'asar nakanji busan sarewa me daɗi haka zanta bin busan amma bana ganin me buzan, a sati na uku Allah ya nuna min shi kullum sai naje sauraranshi ana haka wata rana ya kamani sai kunya kamani murmushi yayi yace.
"Kamar kece muka taɓa a huɗuwa a mainamaji."

Gyaɗa masakai nayi cike da jin kunya, nan yayi tq jana da hira.

Dana ga duhu yafara rufawa sai nayi masa sai da safe, da muka dawo daga cin abinci muka zauna hira baccine ya ɗauke ni, a mafarkin na kara gani mutumin yana min busa,

A hankali muka saba, har muka tafi hutunmu na farko da muka dawo kuwa su Queen suka saka nazifa a gaba, ni ban sani ba ashe har ce mata sukayi zasu kasheta idan bata basu ni ba,

Mutumin me busa yake faɗa min kallonshi nayi nace.
"Toh mi zanyi musu ynx,"

Zaro zobe yayi yasaka min a hannuna yace.
"Yau ki tabbatar baki bacci ba ki taimaki kawarki.".

Gyaɗa masa kai nayi, da dare kowa ya kwanta duk sunyi bacci sai ni ɗaya, wajen sha biyu naji kiɗa na tashi can naga kwarangwal ɗin mutane na tashi suna fita, can sai gasu da bakaken kaya suka ɗauki nazifa suka fita daita tashi nayi nabisu.


Har gurin naje nasamu sun sanya nazifa akan wani tukunya zasu yanka wuyarta cikin wani irin gudu na bangaje wanda zaiyi yanka ɗagata nayi na riko hannunta muka bar gurin cikin jin haushi suka biyomu, saime wannan katon macijin ne yayi musu katanga, nansuka nime jin dalilinshi na hanasu taɓa ni.
Dariya yayi yace.
"Kuje ku tambayi wanca sake jikin gunkin ku."

Dasuka same shi da maganar shiru yayi sannan yace.
"Matarsa da ta mutu shekara tamanin da tara ce take kama da wanca yarinyar kuma dama tace masa zata dawo amma a duniyar mutane, shi yasa yake mata kallon Samra ce ta dawo masa bashi kaɗai ba har Yaransu, ni ynz ku nemo min yarinyar na zuki jininta."

Shiru sukayi kafin suka mashi alkawarin ɗauko ni,

Koda muka isa ɗaki, zubewa mukayi sai bacci da asuba na tashi mukayi sallah da wanka sannan muka wucce gurin cin abinci.

Abin mamaki baya karewa da muka je gurin cin abinci sai naga ana kallona, ban damu ba naci abincina muka bar gurin.

Haka muka cigaba da gwagwarmayya, har na isa aji uku anan akayi wani tashin hankali wanda ya janyo akayi asaran rayuka, wanda sanadin dai akaina ne,

Karshe koran wasu ɗaliba da malamai akayi na cigaba da karatuna ga shakuwar datashiga tsakaninmu da sarkin busa wanda yace sunansa knn .......


Tun saba da macizan nan bahar muka saba tun a mafarki suke zuwa har na fara ganinsu ido da ido, wani lokaci nagansu suna kirana Umma. ........

Ynx aka fara....

   🌺🌷🌷
*_DA CIWO A RAYUWATA_*
🌹🌸🌸

Na
Mai_Dambu
Wattpad:Mai_Dambu
Sorry for the typing erorr
*My First Kiss with Mr Right💋*
*Page...M*

       Sam babu wanda ya fahimci halin da nake ciki ba, gashi tsakanina da sarkin busa an samin kyakyawan alaka, wanda yakai na tsani ace zan dawo hutu gida, idan na dawo ma bana iya zama cikin mutane sai ɗaki bani da kawa ko aboki asalima tsoron mutane nake, wani komawa na hutu lokacin ina aji huɗu  mun fito daga cin abincin rana, sai naji ihu mutane a can bayan wani hostel dan haka nayi maza naje, ina zuwa gurin nasamu ɗalibai ne suka rutsa wata faran maciji zasu kashe ina zuwa na shiga tsakaninsu na ɗauketa, Ihu suka saka sannan sukayi kaina juyawa nayi na zuba musu harara, sannan na wucce da macijin can fadama na ajiye shi, ina juyawa naga sarki busa dariya yayi min yace.
"Kin ceci rayuwar macijiyata, yau da mutanenku sun kasheta nagode."
     Abinda bai taɓa min ba shi yayi min yau, dan zuwa yayi ya rungume ni, tare da bubuga min bayana,

    Tun daga ranar shakuwarmu ta sauya salo, kuma duk abinda zai min bana jin fargaba daga rike hannuna, rungume ni bana jin kome. Sai ranar da ya furta min yana sona daga nan na fara jin wasu abubuwa a jikina,

            A wani zuwa na hutu ne wata mata tazo daga darazo, tana sallama ina shigewa ɗaki aikuwa ta shiga surfa min masifa inda tacewa.
"Innarmu su cire ni a makarantar na dawo gida in ba haka ba toh wata rana, sai sunyi kuka."

      Dake matar gurin Nenne tazo nan sukayi mata wani irin fahimta ita kuwa matar tace zata nuna musu halin da nake ciki.

               Duk sun ɗauka karya ne sai da dare yayi  kowa ya kwanta, nima ina kwance sai ga macijin ya shigo cikin gidan, ina bauchi fa, suka ga na mike idanuna a rufe na buɗe masa kofa ya shiga, yana shiga ya naɗeni sai dariya nake, haka mukayi ta shirme yana bin jikina, bai bar ɗakina ba sai kusan asuba na buɗe masa kofa yafita,

      Ai washi gari Baffa yace toh na gama bodin, matar ta haɗa musu maganin gargajiya aka fara bani, har na wani lokaci dakyar aka mai dani schl, wannan komawar na haɗu da wani tashin hankali dan kungiyar asirin sun sani a gaba, da kawo hari wata ran nasha wani lokacin ta rutsa dani, gashi lokacin sarkin busa baya nan, koda ya dawo ya sami ni a kwance yake tambayana lafiya nan na faɗa masa wani magani ya ciro a jakarshi ya zuba a kofin ruwana ya bani nasha, fita yayi ban sake ganin shi ba sai can tsakiya yazo ya fita dani,,

              Nuna min irin ɓarnan da yayi musu, gabaki ɗaya ya farfarsa musu kome ya kashe aljanin da yasa akawo ni, duk wani kayqnsu ya rusa na ya zuɓe akan gwawinshi yace.
"Ki amince da soyayyar da muka gina tuntuni, kituna abinda kika ce ko kin tafi zaki dawo gare ni, kin cika alkawari don Allah ki tuna baya haka shi zai sa mukoma inda muka fito."

      Girgiza kai nayi cikin kuka nace.
"Ban tuna kome ba, kuma ni bansan wacce tayi maka alkawari ba,"

         Dariya akayi daga bayanshi idan gunkin da ya fasa yake yace.
"Uwais ka bar damun kanka dukda nima ka gama dani sai dai baza'a sake haihuwar Samra ba, ta mutu kuma na faɗa maka wannan bil 'adam ce ba aljana kamanmu ba,Ko kaso ko karka so ba ita ba ita."

     Maciji ya zama yakoma kan gunkin ya turashi a ramin da ya haka ya rufe gurin sannan ya dawo kaina kafin yayi min magana na juya a guje, ihu ya takarkara tare da kiran Sunan Samra, cak kamar wacce aka samin aya na tsaya bazan iya tuno kome ba, sai dai wasu irin zuɓewa nayi a gurin,

     Ban farka ba sai da nayi sati biyu a kwance dan har an maidani gida, tun daga nan aka cire ni na dawo gida, na cigaba da karatuna,

   Har na gama makaranta, idan ka ganin ni bazaka ɗauka na kai shekaru sha shida zuwa sha bakwai ba, sabida rashin girman jiki kuma a zahirin gaskiya al'adar gidanmu Yarinya zata fara karatu  na jami'a ko na wani makarqntar ta karasa a gidan mijinta, duk yayuna mata haka aka musu, toh gashi ni da na rage mace ɗaya aure ya gaggara,

           Tun ana ganin kaman nice bana son auren har aka fahimci abu guda da zaran saurayi yazo yau toh gobe ba zai kara zuwa ba, duk wanda ya nace kuma toh mutuwa itace makomarsa.

       Har na shiga jami'ar A.t.b.u, lokacin Malam ɗayyabu yana koyar damu yaso ni aka hanashi, min magana sabida labarina ya fara karaɗe ko ina, har nuna ni ake,

          Har na gama shekara biyar a jami'a, na tafi bautar kasa na dawo, a lokacin su baffa suka nime haɗani da wani mutum ɗan sakwa, yana aiki a abuja yana da mata ɗaya da yara huɗu,

      Rimi rimi aka saka aure aka fara hidimar biki an kirashi anyi masa magana ya hakura da aurena yaki, har iyayenshi aka samu fir yaki, ana gobe ɗaurin aure aka sami gawarshi ya rasu, nan danginshi suka makamu a kotu dakyar nasha ni da iyayena, ana cikin haka, Ya Abbas ya sami aiki a canada  ganin ina cikin tashin hankali shine sukayi shawaran tafiya dani, dukka dukka shekaruna ashirin  da uku zuwa da huɗu, muna zuwa can na cigaba da master ɗina dake shekara shida zaiyi sai nima na mai da hankalina gurin karatu na,

     A makotarmu akwai wasu yan africa bansan daga wani yanki suka fito ba, sai dai yanayinsu fulani ne, mutumin yana da matukar girma da kima a canada, ranar na fito zan tari mota zuwa makaranta ashe suna katuwar kuliyarsu ni kuma na tsani kuliya(Kyanwa ko mage,inkiya Catty😻) suna kiranshi da museee  ni bansan cewa rigar da nasaka igiyarta na lilo ba, kawai mi zai faru na tsaya gyara jakata, sai ji nayi an cafke ni tare da cewa.
"Weeeeow "

   Wani gigitaciyar kara na saka itama ganin ina ihu ta burta a guje, a guje Maman Iman tafito matar ya Abbas dashi kanshi da yara, suna tqmbayar lafiya nan na faɗa musu, abinda ke faruwa, yara matasa ne guda biyu tare da mace daya suka fito suna dariya na suna nuna ni,

            Ashe an buɗe gate zasu tafi makaranta shine tafito, mi gadinsu yaje ya faɗa musu abinda ya faru nan sai ga yaran suna min dariya abinda ya kara bani haushi, cikin masifa na kama magani cikin harshen hausa tare da yin Allah ya isa min cak suka tsayi da dariyarsu a lokacin iyayensu suka iso, jin abinda nake fara tare da kuka Uwarsu ta kalle ni cikin sanyi jiki tace.
"Kiyi hakuri Y'a sha'anin yaranmu sai hakuri ku bata hakuri."..

   Sai kuma kunya ya kamani cikin sanyi murya suka ce.
"Adda kiyi hakuri bamu sake miki dariya"

        Goge kwallar da yasake zubo min nayi nace.
"Na yafe."

Ta mace cikinsu wacce bazata fi shekara goma sha ɗaya ba tace.
"Yeeee idan da gaske ne mu kula abota, kinga dama bani da abokiya tunda Meemah tace ke yarta ce shi knn na zams kawarki idan na dawo schl zan zo muje yawo da kuma cinema da...."

  Take ta shiga zuba jan hannunta yayun sukayi Babansu ya bawa Ya Abbas hakuri,

     Wannan shine haɗuwa da Iyalan Arct Muh'd da iyalanshi da matarshi Dr Hadiza.

      Tun bana sakewa dasu har na fara sakewa, sai dai ni ban iya surutunsu ba, Mamansu kejana da hira, ko kuma mu shiga kitchen da ita, muna abinci gargajiya, da kanta ta roki Ya Abbas ina shiga tayata girkin gida nig,  mun saba da ita sosai, abinda ya fara damuna da hidimar gidan shine duk yan gidan babu wanda zaka tambaya su yan ina ne a afrika ya faɗa maka, sai dai kame kame,

          Babban yaronsu me shekara sha biyar Adnan sai me bi masa Adil, da karamarsu Sarah, sun jiku da rayuwar turai dake nima bana son shiga rayuwarsu sai ban taɓa damuwa da saninsu ba,

       Ana haka Adnan ya tsiro min da wani hali na daban, yaro karami dashi sai ya shiga min hidima musaman ranar masoya haka zai sayo min kyaututuka,

           Ban kara sarewa ba har sai ranar da yaron zaiyi birthday

Please Login or Register in order to submit comment