Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da hannun,"

    Kuɗi Sadeeq ya ciro xai bashi mutumin yace.
"A'a Alhaji wallahi nagode abin arzikin da kaimana ya ishemu ma mungode."

      Mutumin yana fita shima ya mike yayo ɗaki ciki na koma shi kuma ya shigo, masifa ce ke cin ranshi ya finciki hannuns muka shige ɗaki, a gado ya wurgani ya zuba min ido yana hucci haka bai isheshi ba yace.
"Da izinin wa kika fita? Shi wacce dole da kika fita tsirara ya biyo ki na karya masa haɓa, da aurena kika fita min da wannar abar Amrah na zuba miki ido na gaji yau zamu raba raini."

          Yana gama magana har zai fita zuciya ta ciwo shi ya dawo cikin zafin rai ya shiga rabani da kayana dake nasan abinda na taka ko kula masifarshi banyi ba, har ya shiga niman mafita, turus ya tsaya yana kallona, ranshi yayi kwaloluwar ɓaci, kaman zai yi kuka yace.
"Kinyi min laifi amma baki san bada hakuri ba, sannan kinga ina shirin yin abu baki dakatar dani ba Wai shin mi nayi miki ne da zafi Amrahtu, miye laifina da kike  azabtar dani. Insha Allah bazan sake ba nagode Amma kisa  ranki Zan auri Aunty a cikin wata ɗaya zuwa biyu."

   
             Kuka ne ya kwace min nace.
"Toh ni dole ne sai ka xauna dani kawai ka rabu dani tunda ba tilasa maka ni akayi ba, ni na faɗa maka gaskiya ba zan karɓe ka ba a matsayin miji dan banga abin gile a gurin ba ka sake ni nace ka.."
     Tasss ya sauke min mari a fuskana rike fuskana nayi cikin kuka nace.
"Wannan shine a binda bazan ɗauka ba duka, ai ko ba kome xaka bani girmata na wacce ta girmeka ba sa'arka, ko kanwar bayanka, Sadeeq marina kayi a karo na biyu, dan kaga ina karkashin ka shine kake dukana toh Allah ya isa min ban yafe ba dan nasan ko nace zan rama nice da wahala kasauka a kaina mugu azzalume wanda bai da abinda ya saka a ranshi sai sex kaje ka auri jinjira ma, mayyen mata kawai idan kai ɗan halak ne."

   Sake daga hannu yayi zai kai min mari aka rike hannun, juyawa yayi yaga inna wuro girgixa masa kai tayi tace.
"Har mustapha ya bar duniya bai taɓa dukann hadiza ba, asalima kaman sarauniya ya maida ta, dik da anyi auren bata sonshi amma haka ya shanye halayarta har suka haife ka, karka sake dukan Matarka dan yana zubda kiman na miji a idanunta."

     Gyara rigarshi yayi da wandonshi ita kuma tafita, jan bargo yayi ya lulluɓa min ya fita, dunkulewa nayi na cigaba da kuka mi cin rai shigowa tayi ta zauna a bakin gadon tace.
"Kin bani mamaki wallahi Allah ya kashe ya baki namija ɗaya kwal tankar da dubu, wanda mata suke kawowa hari dn ya auresu kinsan kuwa daga zuwanku nan Iyayen yan mata nawa suka kawo masa tallar yarqnsu sabida nagartanshi Sadeeq ya wahaltu a cikin hannun dangin uwa da na uba, yaro ne da bai san so ko kiyayya ba Amra idan kika ji rayuwar Sadeeq sai kin zubda kwalla, ni ce nahaifi Uwar Sadeeq sannan Kakqn Sadeeq Hammah Buba Yayana ne cikinmu ɗaya, Kakar Sadeeq Uwani yar Baffana ce..."

    Ajiyar zuciya ta sauke kafin ta gyara zama tace.
"Madibbo Almu shine mahaifinmu, yana da kanne Aminu Hammadadda, sai Hamidu Ja'e Sai Rukayya Sumaye, wannan jerin Iyayenmu ne, Madibbo Almu ɗan nan garin Jimeta ne amma shi ma zaunin Yola inda wanca gidan yake, Mahaifinmu ya kasance mutum me fikran zane a jikin kori, amma iyayenshi suka ki kula da wannan baiwar tashi abisa al'ada a zuri'a Malam Buba  Lamiɗo shine sunan kakanmu, auren zumunta ake a zuri'armu, Lamiɗo nada Kane Malam datti lamiɗo, Sai Malam Junaidu lamiɗo da Kuma Hadiza lamiɗo, sai Hauwa u lamiɗo.

    Kuma dukkansu sun hayayyafa dan haka sai aka Dauki Yar gidan Inna Hauwa, Binto mahaifiyata aka bawa Madibbo Almu wato Almustapha,, ka haɗa Hammadda da Safindo yar Datti lamiɗo, Ja'e hamidu aka bashi Jabu Yar gurin Hadiza, Shaban ɗann Junaidu aka bashi karamar Yar Ta annabi yar Hauwa lamiɗo, Rukayya Sumaye aka haɗata da Wada ɗan kawunsu

        Toh yanda suka tsara haɗinsu babu wanda ya isa ya sanja, duk abinda zakuyi kuyi amma auren an kammala shi,

    Koda akayi wannan haɗin sai kwalliya tabiya kuɗin Sabulu, Innata tana shiga tasami cikin Buba, wanda aka dawo da ita gida ta zauna kusan shekara uku ta haihu har ta yaye, Haka ma matar Hammadadda Aminu itama an kawota gida bayan innarmu ta haihu da shekara biyu inda ta sami namiji itama, aka saka masa Junaidu amma yaron kwananshi ashirin ya koma.

      A hankali aka cigaba da haihuwa a zuri'a bayan shekara uku Innarmu tahaife ni, sai kuma haihuwar ta tsaya, Inda akace ya kara aure yace baisan wannan batu ba dole aka kyaleshi,

     Bayan shekara goma sha uku Inna tasami cikin Da gori usman,

   Muka zama mu uku a ɗakinmu,

        A lokacin Hamma buba shima ya gaji baiwar babanmu inda yake zane sosai har turawa suka zo suka nemi a barshi su tafi dashi iyayenmu suka ki, sai Atta ya jefashi a makaranta boko, Hamma yasha tsangwama agun mutane, har Allah ya nufa yayi karatu mi zurfi.

     Ana haka kafara shirin haɗa aure, Nan aka  sai aka ɗauki Yar Sumaye, wacce take aure a jade, Kabawa Buba, ni kuma ɗan Ja'e hamidu, Yar gidan Aminu akabawa D'an gidan shaban Yusif,

    Take aka sakamu lalle, aka kayi mu gidanjemu dake abisa al'ada mace tana gudun namiji toh haka ce ta faru damu mune fadama mune kan kamfa. Kuma a haka muke ta guje guje , ko shekara bamu rufa ba Binto ta fara laulayi dole aka maida ita gida mukuwa da Karime muka cigaba da gudu har Matar Hammah buba tahaifi namiji aka saka masa sunan Attanmu, wato Almustapha , sai da almu yayi shekara uku nasami cikiN  Aminu, na haifi aminu shekara biyu ya koma Karime itama ta sami cikin inda ta haifi ya mace.
           Watana uku da rasuwa Aminu nasami cikin uwar mijinki, wanda nayi fama da mugun laulayi, lokacin kuma matar Hamma buba tana goyon Aminu kanin mustapha dan nawa aminun na komawa ita ta haifi namiji sai akq mai da mata sunan aminu,  watan aminu goma na haifi Hadiza,   tana shekara biyu da rabi na haifi Hauwa u, lokacin kuma Binto tana da cikin Hamidu,
              Karime ce dai har lokacin bata haihu ba, bintoa goyon Junaidu ta rasu lokacin ina goyon sai aka bawa ɗan gidan Harira, toh tun da tashigo gidan ta shiga kunna mana wuta, har dai muka yi magana, cikin ikon Allah tanq,zuwa ta haifi Bilyaminu, shekaranshi guda tasami cikin Adama, lokacin ina goyon maryam,,, tana haihuwa ita kuma binto ta Haifi Safiya, ni kuma na haifi Sadeeya, ana haka mijin Harira ya kara aure inda ya auro wata bafulatana tana zuwa ta haifi Abubakar ana kiranshi bawa,

Yaranmu sun taso sai ya zamana tsakanin Hadiza da Almu akwai rashin jituwa, sunfi shiri da Hauwa, dake lokacin ilimi ya wadata, duk aka sa yaran amakrnt,

Tsakanin Aminu da Hadiza kaman tagwye dukda ta girmeshi da watanin, haka sukayi karatu har aka samawa Almu makaranta, a kasar jamus, inda zaiyi karqtu a gini gine,


Sauran yaran kowa ya zaɓi abinda yake so, haka kawai tsans da mugun kishi ya shiga tsakaninmu da hari, babu wanda ta tsana sama da Almu, haka take jan sauran yaran tana cusa musu mugun abu,


Almu nada shekara takwas ya dawo daga karatun inda ya dawo da dukiya masu yawa yace shekaransa shida ya gama karatu, shine suka rike shi, yana zuwa da dukiyarshi yabawa mahaifinshi, nan Hamma buba ya ɗauke shu ya nuna masa, wannan filin yace.
"Almu na turaka kayi karatune dan na haɗa kan zuri'armu baki ɗaya anan duk yan uwanka sun gama karatu na nuna musu bukatata amma basu kulani ba karshe guduna suke shin zaka iya gina min gida inda zamu zauna kaf iyalina da yan uwana,."

Cikin biyayya ya amince ds kudirin mahaifinshi,

Dukiyar da ya dawo da ita ya zuba ya zauna kusan wata uku yana zane, wannan gidan da yanda za'a fitar da kowani unguwa dani kawai muke zama a ɗakina yana zane,

Watanshi huɗu da dawowa aka fara haɗi, mu bamu sani ba ashe tsakanin Aminu da Hadiza akwai soyayya,, ita kuma kuluwa Almu take so, Hamidu kuma Adama, sai iyayensu maxa suka ce tsarin bai musu ba aka ɗauki kuluwa aka bawa Aminu, ita kuma Hadiza aka bawa Almu, Sadeeya aka bawa junaida, Bawa kuma aka haɗashi da Safiya,ashe wannan haɗin baiwa kowa daɗi , Bilyaminu kuma yar kanwar Uwarshi Salma,


Shine silan kiyayyar da aka kulashi, dan sun tsani almu, duk yan uwan suka juya masa baya idan aka cire Hamidu da Bawa, sune kawai suke tare dashi.


Ginin da Almu ya ɗauka sai da ya kwashi shekara uku, har lokacin tsakaninshi da Hadiza cin mutunci da nuna masa kiyayya kiriri tace itace ajalinshi ranar da naji haka sai da nayi mata dukan da bantaɓa yiwa kowani ɗana ba, ina kuka nace matq.
"Daga yau nazareki a cikin yarana kije ki zauna da masu zugaki."

Nasan aikin hari ce, hankqlinta ya tashi dan haka taje gurin Hamma buba tana kuka ta faɗa masa, tasota yayi a gaba har gurina yayin faɗa sosai,

A dalilin wannan abinda nayiwa Hadiza binto ta daina min magana, dakyar muka shirya,

A shekara na huɗu Muka ga hadiza da ciki, kowa yayi murna amma sai muka boye dan karta ɓalle mana,........
Chaiiiiiiiii wallahi abin da rikitarwa yake😥 Kaina har ciwo yake wallahi ynx sai wata tace bata fahimci kome ba
🌺🌷🌷
*_DA CIWO A RAYUWATA_*
🌹🌸🌸

Na
Mai_Dambu
Wattpad:Mai_Dambu
            *Luv&Caring*

       *Wannan shafin sadaukar ga Fans Ɗin Da ciwo a rayuwata a duk inda kuke na sadaukar muku wannan shafin musaman Masu tilawan A.B.C.D.....Nagode da Kauna😹😂👌 Ana tare*

Ku nutsu ku karanta book ɗin a nutsu babu ruɗani a ciki.
*Page R👈*

        
Take muka ɗauki son duniya muka ɗaurawa cikin jikinta, cikin nasara Almu ya gama ginin gidan wanda yake ɗauke da unguwanni takwas, kuma a kuwani unguwa akwai gidaje huɗu gidan sama, can ta unguwa ta uku aka ware gidan ma'aikata,

Dama a cikin dukiyar da Almu yaxo da shi Hamma Buba ya ware wasu aka fara masa kasuwanci da ita inda ake ɗibar dabobbi daga nan ana kaiwa kudu, aikuwa Allah ya sanya albarka a ciki, nan Aminu ya fara ikirarin ai dukiyar da Babansu yake juyawa ai sabida su yakeyi dan ya mutu yabar musu baya,

Abin an ɗauka wasa ne sai da maganar tazo kunne Hammah anan ya kirasu kaf ya tarasu har dani da sauran yan uwanshi yace.
"Na taraku ne anan dan na sanar muku wani abu guda."

Shiru yayi sannan ya cigaba da cewa.
"Wato dukiyar da nake juyawa bana kowa bane sai na Almu dan na fara jin aminu yana wasu magana toh kaji da kunnenka wannan kayan mallakin Almu ne."

Nan ya faɗa musu kome, dangane da dukiyar aikuwa ran Aminu ɓaci, amma sai ya nuna cewa ai bai sani bane amma ba damuwa,

Haka aka watse bayan munyi musu nasiha,

Bayan kwana biyu da haka Almu yazo daga yola ya sanar mana da Ya gama ginin gidan, banda Hamidu da Bawa babu wanda yaje yaga gidan, lokacin da aka kawo mota muka je ganin gidan sai da muka kaɗu, dan haka aka tara malamai akayi sauka a gidan, wasu suka dawo suka tattara nasu ya nasu suka koma, lokacin da almu ya gama gidan cikin Hadiza ya tsufa sosai dan haka muka ce ta zauna sai ta haihu ta koma,sati uku da tarewa su Hammahna Hadiza ta haifi ɗa namiji,

Tun kafin uban ɗan yazo tasawa yaron Sadeeq sabida rashin kara irin na hadiza sai da na make mata baki, lokacin da Almu yazo ko ɗakin yaki shiga, yana zaune a bakin kofa, ya kalleni ina aiki a tsakar gida yace.
"Gwaggo wani suna kikayiwa mijin naki."

Murmushi nayi nace.
"A duniya ai bani da sama da Hammahna sai Kuma da gori kaga shi yatafi yabarmu, amma kasa masa hammahna idan Allah ya baku wani kusa mishi Da gori Usmanu knn."

Daga ɗaki, Hadiza tayi masa gwalo tace.
"Sunan Yarona Sadeeq yana faɗowa duniya nabishi da sunanshi,"

Danaji abinda take sai na shige madafi dan asani na Hadiza mai kunya ce amma ynz ta zama mara kunya matukar almu zai zo toh shirinta na daban ne, tun ina mata faɗa har na zuba mata ido sam barinta da mukayi tayi boko ya buɗe mata ido.

Haka akayi suna almu nan bayan suna ya koma, yanw komawa ya sami bakin turawa sunzo nasu hidiman suka ga gidan gidan da yayi shine suka nime ya musu, da fari xana musu gidan yayi, suka biya shi kuɗi me yawa, bayan wata shida sai gasu nan lokacin har sadeeq ya fara sama dan sun koma yola, nan suka ɗaukeshi yace yana da mata da yaro suka kwasu su sai Belin, na kasar jamus, ya zauna yayi musu aiki dake akwai kayan aiki take a cikin shekara guda suka gama ginin nan suka shiga bashi kwangiloli, haka yana aikin yana zuwa gida ya fara buɗe kamfanin gini gini na zamani da kuma wasu kananun kamfani kamar wanda yasan zai tafi duk ya cike sunayen Sadeeq akan takardunshi.

Shekaransu ɗaya da rabi a can ya dawo gida, inda ya sauka a nan Jimeta, shida Hadiza da Sadeeq ɗin a gaskiya duk cikin Jikokina nafin son Sadeeq, sun kwana suka wuni,

Wani abin mamaki duk yan uwanshi banda Hamidu da Bawa sune suke da abin kansu duk sauran basu da wata sana"a an nima musu aikin sunkiyi sai dai su jira Almu ya turo musu kuɗaɗɗe,

Ranar da abun zai faru wanda yayi dai dai da ranar ds zasu bar jimeta zuwa yola zama hadiza tayi taita kuka nima kuka nake wanda bamu san dalili ba, dakyar ta bi minta dan tana da shiga wani cikin karami,

Wanda har ina ce mata da alamu tasami Da gori ko Binto, dariya tayi kawai suka tafi.

A cikin yanayin damina muke har suka isa gidan aka buɗe masa kofan farko sannan suka wucce sauran har zuwa kofa na shida anan aka samu motarsu babu su babu labarinsu , har da Sadeeq ɗin,

Munga tashin hankali dalilin faruwan wannan Al'amarin Mijina Saminu ya faɗi ba'a ɗagashi ba sai gawarshi, Hammahna yayi kokarin bincike inda yaxo da kanshi ya faɗa min yayi Istahara sharrin cikin gidane har da jininshi da nawa da kuma na wasu agefe guda akayi aikin amna Sadeeq bai tafi dasu ba yana kusa, koda ya koma ya tsananta bincike hmm karshe sai samun gawarsu akayi an rataye su,......

Naga tashin hankali na rasa ɗan uwana da matarshi na rasa Yata da mijinta, na jijjiga sosai, kafin wani lokaci mun manta da batun sai dai na gaza cire Sadeeq a raina addu'a nake ba dare ba rana,

*** Bazan ce miki ga yanda kayi Sadeeq ya tsira ba sai da wani abu ya taso naje wani kauye biki anan wata mata aljanunta suka tashi tana ganina tace.
"Inna Wuro jikanki na nan a raye da ya faɗa hannun mugayen aljanu wanda suka faraka shi da iyayenshi toh ynx yana hannun Ummul Aimana, tana rike dashi, duk yanda kika so zuwa gareshi ba zayu ba za'akawo miki shi sai shaiɗanun sun buɗe masa idanu yana rayuwan kaɗai ci, cike da tsoro zamanshi a hannunki hatsarine sabida shaiɗanun mutane suna bibiyar bugun zuciyarshi karki damu dan ba haka suka so ba sunso su salwantar dashi amma sun barshi raye ne dan ya cika musu kudirinsu sai dai sunyi kuskuren barin baya da kura barinshi a raye barazana ce ga rayuwarshi Inna wuro, kun haifi namiji a cikin zuri'arku wanda zai tashi bai san tsoro ko fargaba ba, ni kam zan tafi amma zan iya dawowa bayan shekaru masu yawa, sun so kasheshi Allah ya nufa rayayye ne sai ya basu mamaki,"..

Daga haka matan ta yanki jiki ta faɗi, ina gajarce miki kusan sau uku mutane da aljanu suna faɗa min Sadeeq yana hannu me kyau amma zagaye yake da makiya , a duk lokacin da naso zuwa sai na kasa zuwa ko na manta haka muka cigaba da zama.
Ashe lokacin da abin ya faru Ita Umnul Aimana tazo wuccewa sai taga yaron a cikin gida shi ɗaya sai wasu shaiɗanun aljanu suna razana shi har sai ya suma,shine ta tafi birnin Kisra ea faɗawa kakanta ita kuma ta rubutawa Imran wasika shine yazo suka tawo tare, sun zo suɓ samu aljanu sun shige jikinshi dakyar da taimakon Zalja suka cire su sai ya zamana baya uhhu ko hnmm yana zaune zai ta zanen fuskar Iyayenshi ko na mutanen da suka cutar dasu.

A haka ya zauna shiɗaya a gidan sai Imran yana da shekara uku imran yafita dashi, madina gurin Malam Huzaf shi ɗan adam ne kuma yasan imran ya faɗa masa kome akan Sadeeq, bai ce kome ba ya ɗauki sadeeq ya kaishi mkrnta amma fir yaki zama karshe gida ya dawo imran ya cigaba da koya masa karatu, yana cika shekara goma ya haɗa alkur'ani, a gaban Imran ɗin tare da wasu littafan Addini, anan imran ya kai shi makarnta ya kammal primary, a madina yayi scndry, jami'a kuma yace. Shi a china zayi inda ya samu shaidan doplma a computer dakyar Imran yasashi yayi degree a zane zane dan ya iya zane amma gefe guda na'ura na tsoron Sadeeq.

Shekaranshi ashirin da ɗaya ina zaune a tsakar gida naga mutum a kaina, ɗaga kai nayi saurayi akaina, kallon tsoro na masa, nace.
"Sau...."
. Ban kai iya ba sai ka Talatu makociyarmu ta shigo da gudu tana guda tace.
"Inn Wuro zaki ya tashi daga baccin da yake yanzun lokacin farauta ne, dan haka hankali namun dawa zai tashi mun faɗa miki zai zo da kafarshi, ai kariyan Ubangiji ne bana kowa ba Inna wuro barka muna.miki murna, duk tsanani shine da nasara."

Tana gama faɗin haka tafita tabar gurin taburma na ɗauko zan shimfiɗa masa ya karɓa ya shimfuɗa, sunkuyar da kanshi yayi a hankali na tqɓa shi nace.
"Abubakar ne"
Gyaɗa kanshi yayi shafa kanshi nayi ina kuka shima kuka yake nima haka shigowa Malam jauro da wani mutum wanda ganinshi sai da tsigar jikina ya tashi nan ya nemi guri ya zauna, sallama yayi mana muka amsa,

Yace.
"Da faru ina me baku hakuri da abinda ya faru shekaru baya, Allah shine masani amma kanwata Ummul Aimana tazo wuccewa taga yanda Mugayen aljunu yan uwamu suke gana masa azaba sakamakon biyansu da akayi da jini na,su kashe shi ko su haukatashi,

Daga nan kasar zuwa tamu kasar tafiya ce me nisan zango dan haka sai da mukayi wata guda muka iso, lokacin sun ɓuɗe masa ido, babu abinda yake sai ya boye kanshi suna zuwa zasuyita wasan kura dashi, muna zuwa tare da kakarmu muka fatattakesu suka tafi, sai mukayi kokarin cire masa tsoron mutane har da aljanu, dan Sadeeq zai iya zama a kofar gida har gari ya waye batare da ya jitsoron kome ba, munsha ɗaukarshi mu kaishi cikin dajin dake cikin gidan badan kome ba sai dan ya saba da gurin kuma Alhamdulillqh haka ya bamu abinda muke nima, tashi cikin kaɗai ci yasa ba lallai bane ya saki jiki da kowa amna ke da Malam zai zauna a gurunku idan akwana biyu ya koma cikin gidansu inda zai cigaba da fuskantar abokan gaba, kuyi hakuri haka da mukayi shine mafi alkhairi sabida da mun kawo miki shi da keba babu amma ynx zuwan shi zai samar da masalaha."

Mika min takardu yayi yace.
"Duk wannan tashin hankalin sabida wannan takardun ne Ummul Aimana ce tasamu a kasar kujeran motar, bayan ta tsinci karamin takardan da akayi rubutu da jamansi akan a ɗauki takardu akasan kujeran mota, da kuma wani wanda aka ajiye a belin shi kan yana hannuna bazan bashi ba sai ranar da ya zama cikakke mutum na barku lafiya."

Godiya muka masa sannan ya tafi, duba takardun yayi ɗaya bayan ɗaya duk sunayenshi ne daga na bankuna guda uku Union bank da UbA da Kuma Fisrt bank, duk kuma akwai kuɗi a cikinsu, wanda suke mallakinshi,

Mika min yayi na ajiye ina faɗa miki yaron nan sai ds yayi shekara biyar yana haɗa kan kome nashi wanda yake nashi, sannan ya zuba kuɗi ya a kamfaninshi da mahaifinshi ya bar masa ya farfaɗo dashi, duk basu sani ba, kafin ya cika shekara ashirin da bakwai ya tsara kome nashi a kamfani , sai lokacin suka farga yana raye, nan aka shiga kai mada hari yana faɗawa ko ya tsira da kar, gashi Sana'ar zane ya zame masa abinci dan ma baya so, amma haka nake sashi dole, sai yayi ga dangin da suka shige masa jiki dole ya saki jiki dasu amma yana takan tsantsan, sabida yasan dukiyar suke bibiyarshi har yaran da na haifa nasan wasu sabida nasan badan Allah suke binshi ba, dan tun da abinda ya faru suka min jaje basu kara magana ba ko nayi musu magana basu kulawa,

Amra aurenki da Sadeeq haɗin Allah ne, dan yasha yin mafarkinki kina niman yazo ya ɗaukeki, amma bai san ta inda kike ba, kwatsam abokinshi Imran yazo ya tafi dashi dan ya taimaka miki, kuma akayi dace aurenki ya faɗa kanshi shin Sadeeq ya cancanci wulakantar wanki wallahi nasan duk cikin zuri'armu nice kawai da mutanen wannan gidan muke kaunarki Wancan gidan na yola yafi karfinki sabida aka'ida yar gida ake son ya aura kafin bare sai akayi rashin dace ke ya fara aurowa, tashi na nuna miki abinda baki sani ba."..

Rike hannuna tayi har cikin wani ɗaki dake kusada namu inq shiga zanen hotunane a ɗakin

Please Login or Register in order to submit comment