Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ɗaya na naɗe ina zaune akai tura mishi baki nayi na mike,zan shiga ban ɗaki dawo dani yayi  ya zaunar dani jakarshi ya buɗe ya ɗauko shirt da boxes, ya fessa musu turare Black Man, sannan ya shiga kokuwar saka min duk ina jinshi yasa min wando rigar ce da yazo, sakata duk hannuna suna dake da kirjinshi kaina na jingina da damtsen shi ina bacci, har ya gams saka min, ya mikar dani zuwa bayin, janye wando yayi yace.
"Don Allah buɗe ido kiyi tsarki."

     Dakyar nayi sayi ina gyangyaɗi ganin zan ɓata masa lokaci yasa hannunshi da ruwa ya tsaftace min jikina, a gurin alola sai da ya watsa min ruwa nayi niyya, nafara kafar ce ya wanke min ya raɓoni muka fito a nan ne yace.
"Wallahi ki buɗe idanuwanki kiyi sallah."

          After dress na saka buɗe jakarshi yayi yace.
"Gudun ɓacin rana."

      Hijab ɗina ne, nan natada sallah, a hankali nake karatu dan a baiyane take, jin yanda nake karanta aya goma na suratul maryam sai da tsigar jikinshi ya mike, yana kallona sabida kowani harafi ina bashi hakkinshi tare da fitar da tajiweedinshi. Har na idar  dakyar nayi addu'a tare ds azkar ɗin safe.
     Ban idar ba bacci yayi gaba dani.
Cak ya sureni sai gado ya gyara min kwanciyana, sannan ya kintsa kayanshi ya zauna ya rubuta short not, yazo dai dai fuskana ya sumbace ni yace.
"I with miss u, My Pinky Durling."

            Mikewa yayi ya fita juyawa yayi yana kallona, cike da damuwa ji yake kaman zuciyarsa ce ya ajiye a gurin, sam sai yaji ba daɗi for the first time.

    Haka ya dawo yayi min addu'a sannan yafita da kwarin gwiwa.,
          Ta kofar waje yafita ya bada ecort ɗinshi kayanshi ya koma ciki yayi musu sallama inda yacewa Baffa.
"Na barta tayi kwana biyu nan da wata guda zan dawo ɗaukarta."
               
     Kin yarda baffa yayi amma sadeeq din ya nuna masa ai zaiyi tafiya ne, shi yasa gidan da muke ba kowa ga yanayinda nake ciki,, haka suka amince.

            Godiya yayi musu sannsn ya fita,

     Kofar ɗakin bakin ya kalla sannan ya sauke ajiyar zuciya ya shiga motar da suka buɗe, sannan suka bar gidan.

             .......
    Karfe sha biyu da rabi naji ana taɓa fillow na buɗe ido nayi a hankali da yayuna mata Aunty Mommy da Aunty Adama sai Aunty Rahama, tura musu baki nayi nace.
"Wai miye haka mutum ba baza'a barshi yayi bacci cikin sallama ba."

Kallon juna sukayi suna mamakin yaushe nayi bakin magana haka, cikin bacci na tuna ina yake take na buɗe idona tare da warewa akansu, zubur na mike na zauna ina raba ido nace.
"Ina Hamma Sadeeq yake?"

Sake mutuwa sukayi da mamaki musaman da suka ga kayan jikina, Aunty Mommy da bata da hakuri kamar Haihuwar Inna wuro ta shiga tafa hannunta idanuntq kur akan kirjina tace.
"Amratuh Yaushe kika lalace haka wato daɗi miji shine har da saka rigarshi da wandonshi, idan na fahimta anan ɗakin kika kwana,"

Ai ban saurari me zata ce ba nayi hanyar ban ɗaki na duba baya nan, kuma a gigice nake fa, ai waje suka ga zan nufa Aunty Adama ta rikoni, tace.
"Baki da hankaline haka zaki fita."
Kukan da ban tsamanci zuwan shi ba shina ji nace.
"Eh bani da hankali akan shi na haukace kinsa mi yasamin ɗan ɗani hauka nake ji mi yasa kuka barshi ya tafi na shiga uku na lalace zasu kashe min ɗan marayan miji."

Duk sai jikinsu yayi sanyi afterna Aunty Rahama tasami, ina kuka duk sai na basu tausayi rungumeni Aunty Mommy tayi muka fito falon Baffa inda duk yan uwana suke da matansu da yaransu, kasancewa ranar lahadine,

Da sarsarfa na isa jikin Baffa ina wani irin kuka nace.
"Baffa kace ya dawo basu imani wallahi zasu cuta min dashi baffa bai da kowa sai kakanshi Yaro karami ya girma cikin makiya baffa idan wani abu yasame shi mutuwa zanyi kakarshi amanarshi ta bar min nikam Bazaku kira min shi baneeeeeee. kodan Uwata Bata Raye neeeee Wayyo Allah Na mutu na lalaceeeee."
"Hello My Baby doll." abinda ya doki dodon kunena kenan,
Cikin kuka na rike wayar. Nace.
"Abubakarrrrr, Sadeeq ɗina ne Hammana ne kayi min Magana."

Allah sarki ta faɗa tarkon Yan maxa🏇🏇🏇🏇
🌺🌷🌷
*_DA CIWO A RAYUWATA_*
🌹🌸🌸

Na
Mai_Dambu
Wattpad:Mai_Dambu

*Back to Yola*

_Oho dai ana idan yarana suka dawo daga school, idan ana tambayarsu karatun da akayi basu faɗa ba an dinga talle keyarsu kenan ana cewa nan Abbanka yake biyan kuɗin Islamiyya da haka, ga schl fee amma kullum baka kome sai wasa ta dage tana masifa shi yasa nima na ramawa Yarana suma su ɗana😎😜😂😹 oho dai kullum sai kunyi bita😂_

*Page X👈*

Kuka nasake saka mishi kaman wata karamar yarinya, "Ok kiyi shiru kinji zan zo na ɗauke ki wata guda kawai zaki yi."

"What!!! Kana da lafiya kuwa har wata wallahi bazai yu ba ni nan da sati biyu zan dawo haka kawai kala kaje su baka guba kaci plss ka dawo min ni bana son tafiyar kan nan"
Ji nayi ana ɗaga ni daga durkushe da nake kallon Aunty Mommy nayi cikin niman rigima turani tayi ɗakin Nenne ina shiga nayiwa ɗakin key,
Na zuɓe a saman gadonta na cusa kaina cikin fillow kuka na saka masa, shiru yayi yana saurarona a cikin nutsuwa yace.
"Idan da zaki ji yanda kukanki nan yake taɓani da wallahi bazaki yi min ba, amma sam baki lura da haka ni na isa Estate tun sha biyu saura, sannan ni ynx bana bukatar kukanki just addu'a kawai zaki tayani da shi shine gatar da zaki min kinji ko."

"Ina kewarka kuma Insha Allah zan maka i miss ur body nd arms urs smooth nd soft skin, hmm nd.....ahhh"
"Amratuh!!! Don Allah ki barni haka karki lalata min rayuwa wanda kikayi ya isa zaki kasheni da wannan nishin naki."

"Ai wallahi baka ji kome ba dan sai na hanaka sukuno."

"Wayyo Allah sai na faɗawa Inna wuro kin tsotseni baki ɗaya babu ruwa a jikina."
Wani irin nishi na sauke, nace.
"Hmmm.".

"Mi kike so Hotmilk."
"Kai mana, idan ba kai ba wazan so My lollipop kayi tunanin a haɗa hot milk da lollipo a guri guda mi zai bada."

"Mmmm don Allah barni nayi aiki dan ina office ɗina estate kuma akwai jama'a a waje suna jirana"
"Ahhhhh shhhhhhhhhh."

Iska ya huro min ta cikin waya, take nasake wani irin dariya wanda ya ke ɗauke da tsantsar kirsa da kisisina nace.
"Lollipop baka ce kome ba mi kake nazarine."
"Hmmm bana nazarin kome Yar mutane bauchi zata sani hauka a office kinsan abinda kike min nan yana ɗaga min hankali kuma kina da zara dani, balle nazo na rarukeki."

"Kansan me?"
"A'a sai kin faɗa."
"Wai so nake na ganka dan nayi miss wannan farin idnunka."

"Ji min zagi a kafaice, ai na ajiye miki sakonki a ɗakin da muka kwana."

Tun bansan mi ya ajiye min ba na fara masa godiya tare da addu'a katse ni yayi yace.
"Ya isa haka hakkine na miki more, sannan kiyi sitting whatsp zan dubaki an jima."..

"Ni bana son Whatsp amma tunda zamuyi Video cal ya isa ma nagode zanyi miss ɗinka koda yake nice nake haukana ni ɗaya amma kai baka damu dani ba."
Ajiyar zuciya ya sauke yace.
"Wa yace miki ban damu dake ba aike ynx kin zama half ɗina key ɗin zuciyata na hannunki kece kawai zaki iya sarafashi cikin ruwan sanyi."

Mun jima muna musayan kalamai masu daɗi har na ɓingire da bacci, a ajiye wayar jin na ɓata shiru yasa shi kashe wayar, wanda nukayi kimanin awa ɗaya da rabi,

Ban tashi ba sai karfe biyu na rana, mika nayi haɗe da salati na shige ban ɗaki nayi wanka sosai ina fitowa naga wayar tana kara.
Duba kiran nayi A.M.Lamiɗo na gani cikin sauri na ɗauka na kara kunnena tare da sallah nace.
"Kayi hakuri yanzun na tashi daga bacci, kuma ina son yin sallah sai naci abinci."

"A hankali yace.
"Yayi kyau ina ta surutu sai naji shiru."
Dariya tare da katse kiran na fara shirya jikina, Riga da skirt na saka tare da shafa mai a bakina sallah na gabatar ina idarwa, nafito falo cikin matsanacin kunya na gaida Baffa da Nenne sai yayuna duk nabisu da gaisuwa, nan kanena suka gaisheni cillawa Sadeeq wayarshi nayi, tare da kwanciya a kan tumtum ɗin da Baffa ya ɗaura hannunshi, idanuna a lumshe nace.
"Mubarak ina son Burger da kuma smooth shaka banana idan bashi ba toh ka had'a min da ice cream, me chocolet plss kayi sauri ina jiranka karka ɓata lokaci amma ka shiga ɗakin bakin nan akwai tarkace na ka kawo min nan."

Kafin na gama maganar har bacci yayi gaba dani kallon mamaki suke min rashin hakuri irin na Aunty Mommy ta kai min duka cikin masifa tace...
"Kaniyar ki.".
Mikewa zaune nayi raurau nayi da fuska na kalle Ya Abbas nace.
"Babban Yaya kaganta ko".
Duk suka kwashe min da dariya, cikin sauri Mubarak yq mika min wayarda ya ɗauko min kiran Iphone +8 ɗaga ta nayi nasaka a kunne nace.
"Nagode Allah ya biya maka bukatarka na alkhairi"
Tambayana yayi da naci abinci na girgiza kai nace..
"Nama fasa cin burger ɗin Zansa a min alalen gwangwani,da kunun tsamiya yayi maka."

"Gud gal"
Sallama mukayi da shi sannan na kafe Aunty Mommy ido ina kallonta nace.
"Ni dai kusan yanda zakuyi dani dan alalar gwangwani zan ci da kunun tsamiya."

Tsura min ido sukayi duk suka ɗauke wuta, kallon Nenne nayi cikin ɓata fuska nace.
"Nenne yunwa nake ji."

Mi aikinta takira me suna zulai akan tayi min alale da kunun tsamiya.

Kwanciya nayi bacci na ɗaukana a hankali hirana suka fara, cikin nuna sauyawar da nayi can cikin bacci na fara jin murɗa a hankali na soma yunkurin amai kafin ace wani abu na fara amai,

Sosai duk yan uwana suka rufo akaina sosai nayi kuma babu kome a cikina, dakyar ya tsaya, Allah yasa ba'a jikina nayi ba, duk suka ruɗe, kunun tsamiyar aka kawo, kafa kai nayi sai da naga babu kome a cup ɗin duk da zafin da yake dashi jingina nayi,

"Amma kunje asibiti ko." tambayar da ya abbas yayi min kenan, gyaɗa kai nayi,
Aunty Mommy ce take share kwalla tana kallona tace.
"Sannun Amratuh Allah ya raba lafiya sannu."
Mikewa tayi tabar falonmu kowa yasan ba kome bane yasata wannan kukan sai tuna Innarmu tunda nasha kunu na nasa Mubarak ya fitar min da jakuna duk na raba musu tsarabarsu muka buɗe hira, sai da aka kira sallar la'asar muka yi sallah a falo,

Bayan mun idar muka kafa hira nikam na zama ɗurau dan zamanmu kafin sallar magarib naci abinci yafi akirga har suka watse zuwa gidansu. Da dare kuwa muka sha hira a video cal, inda nake sanye da boxes ɗinshi da kuma haf vest na jika gashina ruwan nabin jikina girgiza kai yayi tare da cizon lips ɗinshi yana kallona, dariya nake masa wanda ina yi jikina na ɗan girgiza, inda hankalinshi yafi raja'a,
"Mukwana lafiya."
Yace min, kashe wayar yayi,

***
*Yola*
Lokacin da ya bar bauchi to gombe tare da imran, kiran gaggawa akayiwa Imran wanda yasa sukayi bankwana yace.
"Ka cigaba da addu'a ka kuma kauda kanka ga duk abinda zaka gani kayi hakuri."

Yana gama faɗar haka yafita tasamar motar, sun isa gombe goma na safe, bayan mintuna talatin jirgin yolq ya ɗaga inda suka sauka a birnin kyawawa,

Katsaye motar suka wuce dashi, kamfanin lamiɗo anan yasamu bakin da suka zo niman ya musu aiki, lokacin da aka buɗe masa motar ya fito sanye yake da wani whiter suit, mai masifar ɗaukar ido, ya kara cika da haiba ga wani uban gwarjinin da ya kara, sanyo kafarshi yayi ya fito ya manna farin glass ɗimshi a fuska, da yawa mutanen da suka zo dominshi suna zaune bakin ciki ya ishesu na suna ji suna gani, zasu rasa aikinsu dan yan kwangilane, ganinshi ya fito a mota take duk suka mike,

Cikin kamfanin ya kusa kai sai gashi ina faɗin ga COE ya dawo,

Alhaji bilya da su Uncle Aminu da sauran Iyayenshi duk suka fito, yayinda wasu dawowarshi yayi musu daɗi wasu kuwa bakin cikine gwara Alhaji bilya nashi ido da ido yace masa.
"Kafiri baka mutu ba?"

Dariya yayi sannan yace.
"Surukina idan na mutu kai ma rayuwar bazata maka daɗi ba kawai mu cigaba da faffatawa, gwara kai fuska ɗaya nake ganinka da shi sauran wanda suke fatar mutuwata kan ai su fuska uku garesu, kawai manta zan cigaba da niman kariyar Allah sirikina, banda abinka ko asaran billiya ɗari uku da ɓata ta yaja muku ai bazakayi fatar mutuwata ba amma ba damuwa da ne nake tsoron mutuwa a ynx kuwa ai gudun mutuwa banawa bane, Almustapha lamiɗo ya tafi ya bar baya bayan ma zai tafi yabar baya kaga babu batun rub da ciki akan dukiyar ɗan marayan zaki."

Yana gama faɗin haka ya wucce office ɗinshi, anan ya samu tulin files zama yayi aka shirya meeting, kafin shiga meeting ɗin ne na kirashi muka sha luv ɗinmu,

A gurin meeting ɗine Aminu ke mitan yasan yana raye shine bai dawo gida ba.

Saka hannunshi yayi duk biyu a fuska yace.
"Eh toh idan na dawo suka karasani fa."

"Au dama kace baka shirya Yaki ba Yaro bayan kuma su ɗin suna shirye a koda yaushe Yarona" Inji Aminu,
"Uncle kenan ai ja da baya a gurin rago ba tsoro bane shirin yakine sosai."

Dake an gama meeting dan bakin har sun fita, mikewa Aminu yayi ya daga kafaɗar Sadeeq yace.
"Gaskiya Yarona kasake shiri dan zasu iya dawowa fatana koda zasu dawo kar Ayi biyu babu dan bana son rasaka kaman yanda na rasa ɗan uwana.".
Yana gama faɗar haka yafita abinshi, wayar Alhaji bilya ne ya ɗauki kara garin ya mike wayar ta faɗi screen ɗin wayar tana sama, Sadeeq ya saka hannu xai ɗauka masa, yayi maza ya ɗauki abinshi,
Ya fita abinda yake kan wayar shine ya bashi mamaki.
*Shadow*

Shiru yayi har Bawa da Hamidu suka kalle shi cikin mutuwar jiki suka ce.
"Allah yana tare da mai gaskiya."

Murmushii yayi musu suka fita yana zaune sai ga Uncle Aminu yashigo cikin sanyin jiki ya zauna kaman xaiyi kuka can ya fashe kuka da kukan yace.
"Sadeeq na damu da kaine kuma raina ya ɓaci da kasan kana raye mi yasa baka dawo gida ba kasan irin asaran da muka tafka kuwa, amna ba damuwa tunda Allah ya kawo ka, kasa ido akan bilya da Bawa dan ina zarginsu."
Yana gama faɗin haka yayi waje, da wutsiyar ido Sadeeq ya rakashi yana nazarin maganarshi.

Karfe huɗu aka tashi kai tsaye gida ya wucce inda ya samu gidan makil da iyayenshi mata zama yayi suka gaisa, sunyi masa jaje kafin suka bar gidan ɗakinshi ya shiga ya sauya kayanshi, sannan yafi shigowar Nanah ɗakine yasashi ɗaga kanshi,

Jinginawa tayi da kofar ɗakin tare da jan igiyar rigarta, a hankali ya sauka kasa, zubs mata ido yayi take hiranmu ya dawo masa, tsigar jikinshine ya mike,

Cikin ko in kula ya kauda kanshi ya cigaba da abinda yake gabanshi taje ya juya mata baya, (Ita ya dace tayi fushi amma sai ga Sadeeq har da juya baya.)

Rungume shi tayi, tana goga mishi kirjinta, juyota yayi cikin fusata amma ganinta cassss yasashi ya haɗiye fushinsa yace.
"Kinga my sister ba lallai banena iya gamsar dake dan bani da lafiyar gamsar da iyali idan kuma makin gamsu ba lallai bane kisamu ciki dani dan kwayoyin halittana sun mutu bazasu iya bada ɗa ba,".

Bata fahimci maganar ba ita dai kawai a ɗaurata network, ganin tana kamo kasa inda bai aiketa dole yabi yarima yasha kiɗa, rabin hankalinshi da nutsuwarshi na can gurin zuciyarshi, ba karya yau a karon farko da yayi tunanin Yar guzumarshi, ita kam tasamu yanda take so dan ya gurjeta an dade ba'a haɗu ba , shima ba laifi....

Sadeeq da wulakacin yana gama moreta yace.
"Maza ki kwashe wannan kayan kazantar kiyi waje kuma ki ciro wani zanin gadon ki shimfiɗa min,"

Kaman zatayi kuka haka take ji,

Da dare rufe kofarshi yayi inda yasha hira dani, bayan kashe wayar ne ya shiga juya wani abin wasa puzzle wanda yake ɗauke da kaloli daban daba, karshe ajiyewa yayi ya ɗauko Tap ɗinshi ya shiga games.

Dakyar yayi bacci washi gari.
Ya tashi shi da kanshi yayi abin karyawa yafita.


****
A cikin sati biyu ya zama busy dan aiyuka yake samu baji ba gani, ga tafiye tafiye babu ji babu gani,

Ina da sati uku har na kusan shiga na huɗu ya shirya tafiyar kwana biyar cikin nutsuwa yace.
"Zan tafi zurich akwai wani ajiyar da Papana ya bar min a can toh Files ɗin na gurina gobe zan tafi.".

"Munafukin yaro dama nasan zamanka na 20yrs a cikin wanca gidan kasan kome toh ynx kuɗine ko me." Inji Alh Bilya

"Eh toh ina tunanin kaman kuɗine" yana faɗar haka ya mike yabar ɗakin meeting ɗin,..


Take Alhj bilya ya ruɗe yafito, sauran ma duk mike.

A mota alhaji bilya ya amsa kiran Shadow, jikinshi na rawa yace.
"Eh amma ynz kar ayi gaggawa a jira ya dawo.

Duk wayar da suke sadeeq najinsu, A hankali Yace.

"............WAYE SHADOW........."




🏃🏃🏃🏃🏇🏄🏂
🌺🌷🌷
*_DA CIWO A RAYUWATA_*
🌹🌸🌸

Na
Mai_Dambu
Wattpad:Mai_Dambu

       *Rashin Fahimta*

*Page Y👈*
   Washi gari wajen karfe biyu ya kirani ɗaukar wayar nayi lokacin muna cikin kasuwar central market, na kanga wayar a kunena cikin jin haushin nakirashi wayar a kashe bayan sallamar da nayi masa, ban sake cewa kome ba dan haushin nake ji sabida idan nakira wayarshi always busy, idan kuma da dare ne, kashewa yake, kusan sati uku dakyar muke waya dashi, cikin sanyi murya yace.
"Da fatan kuna lfy ke da little Papa, ko Momma."..
     
  Cikin jin haushi da kishi nace.
"Eh muna lfy so what tunda kasami wacce tafimu a gurinka ina zaka san muna lafiya, sau nawa ina kiranka ka kashe sannan da rana busy nagode da yanzu ina gaban iyayena da a can nake bansan iya adadin bakin cikin da zan gani ba, kuma kaje Allah sai ya saka min dan kaga ina sonka shi yasa kake raina min hankali bana son ganin fuskarka am really Hate U kuma karka kuskura kazo ka zauna idan na haihu kazo ka amshi abarka."

Kuka na saka mishi tare da kashe wayar baki ɗaya, Aunty Rahama da mubarak wnd daman fitar sabida shi mukayi matarsa ta haihu munje sayan kayan suna, ina baya su suna gaban mota, kallon juna suka,

   Ganin yanda nake rare kuka wanda tsabar kishine ke addabata dan hango Sadeeq nake da Nana a cikin wani irin yanayi.
Kwanciya nayi akan seat ɗin ina sauke wasu irin kuka me haɗe da shasheka,, kuma duk suna jina asalima tsoron rigimata suke, dan tsakani da Allah nake sakasu a gaba da rigima,

      Wayar mubarak ce tayi kara ɗauka yayi Yace.
"Mr Lamiɗo barka dai,ok muna tare da ita,"
  
Aunty Rahama ya mikawa wayar ta miko min, naki karɓa sai da ta daka min tsawa da cewa.
"Zaki karɓa ne ko sai na ballaki, waye sa'anki ni ko mijin naki yar iska mara hankali kin sami miji kina juya masa hankali da wata yarinyar ce ko tari bazata mashi,"
"Amna Aunty Rahma sati uku rabona dashi."
"Sai me dan bai kiraki ba, Ehhe nace sai miye wallahi ki shiga hankalinki lalura ce dake kina ɗaurawa kanki damuwa sabida kishin banza "
      Karɓan wayar nayi ina kuka, kashe kiran yayi,.
     Daga kasuwa shagon Gwaram nd son muka je, anan naga kayan Baby, cikin fitar hankali nayita ɗiban kayan, bamu koma gida ba sai karfe takwas dan mun wucce gidan mubarak ɗin.

          Tunda naga jerin gwanon manyan motoci nasan Sadeeq ne tsaki nayi na fito daga motar cikin gida na nufa, ina shiga falon Baffa kamshin turaren Armania ya daki hancina, a hankali na shaka,

            Da sallama abakima na shige falon, gaida Baffa nayi da kuma nenne ban kalli inda yake ba, nasa kai na wucce abuna, sunkuyar da kai yayi cikin matsanacin damuwa yana wasa da kafet ɗin falon duk sai yaba su tausayi niko wuccewa nayi ina hura hancina, irin gani nan am ɓata min rai(😂)

Kallon Nenne baffa yayi cikin ɓacin rai yace.
"Ki turo min wancar kafaffiyar."
Tashi tayi tare da cewa.
"Toh Alhaji.".

Kallon Sadeeq

Please Login or Register in order to submit comment