Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

abinda ya faru, yayinda mutane suka watsa abun a kafar sadarwa, ana yayyatawa, Adda kuluwa tana bank wani abokin aikinta ya kawo mata take ta birkice dan sunce bazata fita ba, kallonsu tayi ta ja takarda tayi dogon Rubutun barin aiki, ajiyewa ogansu tayi tace.
"Dani da Mahaifiyar Sadeeq Uwa ɗaya Uba ɗaya ne, kuma da mijina Aminu da Baban Sadeeq uwa ɗaya Uba ɗaya ne, kenan babu amfanin zama da aikinku indai bazan je naga halin da marayan ɗana yake ciki ba."

"Ok Mrs Aminu lamiɗo karki damu zaki iya tafi amma batun barin aiki bai taso ba sabida muna matukar amfana dake kiyi hakuri mun baki hutu sati ɗaya."
Inji ogansu da sauri tayi godiya ta fita,

Sai asibiti duk yanda suka so ganinshi abu yaci tura, hankalin kowa a tashe da zaran likita yazo zasu mike ko nurse,

***
Ina zaune a ɗaki jikina yayi sanyi dan tun ɗazun banga shigowarsa ba, sai kallon computers ɗin nake tsigar jikina ne ya mike, a hankali naji ance.
"Assalamun Alaikumun."

Zuciyata kamar zata buga nadago kaina nace.
"Amin Waaalaikumun Salam,"
D'ago kaina nayi na kalleshi sanye yake da fararren kaya, mika min hijab yayi yace.
"Taso muje."

Jikina na rawa nasaka take muka bayyana a wajen asibiti, yace min.
"Kisa idanunki akan kome Sadeeq bayi da lafiya, sannan nima zan bibiyaku ki nutsu bazan cutar da dake ba, dan shi aminina ne jeki suna emergence zaki ga sauran mutane,"

Gyaɗa kai nayi nashige ciki da sauri har na faran nisa sai na gqnshi kusadani "Kiyi hakuri kar wani ko wata tace miki zata maidaki gida ki bisu kice a gurinshi zaki zauna nima zan san abinyi kinji sannan ki nutsu akwai da zaki iya tsinta zuwa anjima keep watching."

Gyaɗa kai nayi ya tafi nima, na shiga ciki.

Adda Kuluwa na hango tanawa Su Adda Sadeeya faɗa bayan itama goge kwalla take, jiki a sanyayye na raɓe a can nisa ina kallonsu.

Duk yan uwansune da abokan arziki, ni ɗaya ce bare, sai naji na muzanta ainun dan sun ganni amma babu wacce tayi min karan jana a jiki, duk sai kuka suke, ina tsaye na dukar da kaina kasa, sai ji nayi an bangaje ni, "Yar iska tsohuwar kilaki, ai munga kiranki ne yaja aka buge shi mayya kawai me mugun nufi Allah sai ya wulakantaki, kuma ku jiya kibar mana asibitin."

Haka kawai sai naji sanyi na ratsa jikina, tare da karkarwa, duk cikin mutanen babu wanda ya hana nanah cinmu mutunci asalima kaman haushina suke ji,
Rufe idona nayi na jingina da bango, nafi mintuna goma kafin na buɗe na sunkuyar da kaina, tabbas an dawo da hannun agogo baya mikewa nayi zan shige ɗakin da aka hana shiga inda ake dubashi,
Ji nayi ansha gabana tare da ɗaga hannu zata mare ni ɗago kai nayi muka haɗa ido, cikin firgici tayi baya, sauran watsa musu harara nayi na shige, drs ɗin suna ganina wai nafita suma kallo ɗaya nayi musu, suka koma bakin aiki, bansan iya adadin lokaci da na ɗauka bana hayacina ba har sai da wata nurse ta riko hannuna taji jikina sanyi ta kalleni sake ni tayi bayan anfita da shi wani ɗaki, sake riko hannuna tayi ta fito dani takaini ɗakin da yake wanda aka hana kowa shiga, fita tayi sai gata da ruwaa gora addu'a tayi min ta tofa a cikin ruwan , sanan tabani nasha, can nayi ajiyar zuciya take zazzabi ya nime rufeni magani ta kawon nasha sannan naje inda yake zaune karamin kujeran naja na zauna, juyawa nayi nace mats.
"Nagode."

Murmushi tayi min tafita, ganin tafito suka mata caaa(Irin wanda fans suke min idan ban turo cigaba ba)😂

Banza tayi dasu ta wucce, shigowan CP yola tare da wasu manya yasa aka barsu suka shiga ɗakin tabbas Sadeeq yana da jama'a wanda wasu ma zaka sha mamaki idan ka ganshi dasu, bayan fitarsu wasu kusoshin gwanati suka shigo suma, badan kome ba sai dai suna aikin kwangila dashi, kuma ko baka bashi kuɗin aiki ba zai maka aiki ka biyashi hakkinshi haka yasama mishi farin jini a gurin manyan mutane sosai, *(Toh ya za'ayi kainuwa knn murucin kan dutse, ɗan marayan zaki ɗan tsakon da uwarsa takasa, ciwon ido sai hakuri turmin tsakatmr gida shalugudan mahassada, farin wata shakallo nakiyan kan kabari, babban gamji rurun tsakar gida, Giwa babbar Dabba Sarki kake adawa sarki kake a mutane, Karamin mutum Sai babban Kasada)* haka suke shigowa ɗakin mu gaisa dasu, suce ya miye jiki nace da sauki.

Har dare bai farka ba haka Nanah tashigo tare da Sauran Iyayensu dake akwai sauran abin basu tafi dukka ba, tana zuwa inda nake tasa kafa ta takani, murmushi nayi nace.
"Kina takani fa"
Wani mugun kallo Adda Kuluwa tayi min kafin tace.
"Ta taka ɗin zaki wani abune? Yar iska mara kunya, wahalalliya kawao,kinyi asara."

Murmushi nayi kaina a sunkuye nace.
"Aiku iyayenshine kuma ko ba kome kunci darajarshi."

Kallonta nayi cikin ɗaga gira nace.
"Sometime bana iya tuna kome amna idan da cin mutunci nakan rike abun a raina wallahi na rantse da Allah sai kinyi kuka yanda kika cigaba da takamin kafa."

A fusace Adda kuluwa tayo kaina Adda mairo tace.
"Wallahi kika mata wani abu duniya zata ji mu, Keee Khadija ɗaga takalminki akan kafarta, wato kune y'ay'an dangi ita bare ko Adda kuluwa wannan zafin na shekarun ya ci a manta dashi duk lalacewa Hammah Mustapha mijin Adda Dejane, kar zafin ya koma kan Amrah kina da Zahra da Khairat ba laifi idan kika bashi ɗaya a cikinsu haka zai goge ciwon baya."

Tana gama faɗin haka ta kama hannun Yusrah da Naufal, suka fita,

Duk sai jikin kowa yayi sanyi sai nanah wai nafito na tafi gida ita ta zauna, wani kallo na bata a guje tabi bayansu, zuciyata na zafi tabbas akwai tashin hankali a cikin family Sadeeq, har kusan sha ɗaya ina zaune ina kallonshi yanda yake sauke numfashin wahala ga karaya a kafaɗa zuwa hannunshi ga kuma kananun ciwo.

Mikewa nayi na fito niman ruwa, ban samu ba sai da nafita wajen asibitin nasayo, wasu maza nagani a gabana , bansan suwaye ba amna abinda naji ya bani tsoro da sauri na wuce su, abinda na lura kaman basu gani na, kafin su iso narigasu har ɗakin suka shigo ina kallonsu, ganin bana ciki basu ganin ba sai ɗaya yace.
"Kashe shi babu amfani, dan ina da yaki nin Mustapha yabar takardan da yake ɗauke da makudan kuɗaɗɗenshi a belin kuma akwai yuwar mark dohga zai sake zuwa niman a mishi irin wanca Estate ɗin a Rasha, kasan a belin Mustapha yayi toh kimanin shekaru talatin knn, ɗan iskan yaron nan bansan inda ya samu baiwar zane wanda har yafi na ubanshi kaga abin takaici duk yaranmu mun turasu manyan jami'o'in duniya dan su iya zane kaman mustapha amma abin takaici ɗanshi da bamu barshi yayi karatun bama ko cikin mutane bai shiga ba wai shine mai baiwar, ynx mufita tunda munga yanda yake zuwa gobe idan ya farka sai munemi saka hannunshi, jibi kuma.."

Jan hanunshi yayi a wuyarshi, fita sukayi har zasu rufe kofar sai ɗayan yace.
"Ba ance da Matarshi a gurinshi ba,ina take muganta naji yarana suna yaba kyanta amma sunce baka ce."

Ta jikin bango Imran ya fitar dani yace.
"Zasu jiraki kishiga,asibitin yanzu nan ina biye dake."

Cikin mugun sauri na zagayo cikin asibitin har ɗakin da yake ganinsu nayi, dagske jirana suke a kunyan ce na gaishesu sannan suka kura min ido, ɗayan da yayi dogon magana yace.
"Ya jikin sadeeq "
Nace..
"Sauki"
Bina sukayi da kallo har na shiga ɗakin na zauna, fita sukayi ɗayan yace.
"Nifa na yaba da yarinyar daga ganinta, zatayi kyau da harka."

"Toh idan muka kashe shi ba sai ka aureta ba."
"Eh ka kawo shawara"

Bayyana Imran yayi cikin murmushi, yace.
"Ynx ba lokacin tunani bane na haɗa miki kayanki tsaf zaku wucce Jimeta babu wanda zaiyi tunanin wai kuna can, ynx kin fahimci kaɗan daga cikin halin mutane gidan ko? Toh wannan ba kome bane a cikin halinsu bazaka taɓa sanin waye mugu a cikinsu sabida duk sun mutu da son abinda ba mallakinsu ba, kowa kokuwa yake ya tare arzikin ɗan uwansa, kuma har ynx basu tara rabin abinda mazani mustapha ya tara ba, dukkqnsu Allah ya nuna musu bazasu yi irin arzikinshi ba kowani mutum yana da arziki amma na mustapha wannan daga cikin taskar Ubangiji ne shi yasa ya nuna musu bazasu yi nakansu ba sai dai suci a a cikin wanda ya bashi kinga tashi muje."

Mikewa nayi ina jin mugun tashin hankali a raina dafa Sadeeq yayi sukq isa mota nice na fita, ina zuwa nasamu ya tada motar shiga nayi muka bar asibitin bamu isa jimeta ba sai karfe ɗaya saura,

Shi ya buga kofar gidan Malam jauro ya buɗe, mika masa hannu yayi suka gaisa sannan ya masa maganar tare muke, take ya fito ya tare da buɗe kofar gidan Imran ya shiga da Sadeeq har Wani flat ginin zamani amma idan ka ganshi sai ka rantse ba a gari yake ba,

Kayanmu Malam ya kwaso, baifaɗawa kowa ba sai gashi da flas na ruwan zafi da kayan tea fita sukayi da imran suka min sai da safe,, duk wani abun da aka masa a asibitu, kama daga karin ruwan da sauransu duk munzo da shi,kusa Imran yasaka ya kafa ruwa da jinin da aka sa mishi kwanciya nayi a gefenshi ina kallonshi,

Sarkin ɓarayi ne yayi gaba dani,😒 ina cikin bacci naji ana hura min iska, a hankali na buɗe idona tar akanshi zubur na mike na zauna, karamin murmushi ya sakar min, yace.
"Sallah kin ma kara sannan duba idan wani ya shigo fa kinzo kin naɗe min a jikina sai fama min ciwo kike da ni ne da kin fara ruwa hawaye."..

Leka window nayi naga haske da sauri na shiga toilet nayi alola sannan na fito da ruwa a buta, da karamin roba na fara zuba mashi har ya gama dan yaki na masa yace zai dakanshi,
Kallon jikinshi yayi babu riga, "Kiyi salla tukun kar ɓata lokacin yayi yawa.".
Sallar nayi ina idarwa na koma gurin jakunan mu na duba kayanshi wani shirt na ɗauko masa ya saka hannu ɗaya ɗaya hannun ɗaure da bandaji da aka sakala a wuya, rigar ya saka, yayi sallah yana idarwa aka buga kofar zuwa nayi na buɗe, cikin girmama na buɗe musu kofa, suka shigo kwansu da kwarkwatansu, mata da maza har da yaransu matasa da magidanta,

Gaisawa mukayi sannan suka shiga tambayar ya mi jiki da sauki nace musu yana jingine, da jikin gadon, komawa gefe nayi na shiga haɗa mashi tea, ina idarwa zan mikia masa sai gani nayi an ɗauki kofin a shiga ɗaga tea ɗin, sannan ta haura har gadon ta mika masa, karɓa yayi da ɗayan hannun, dakyar yake sha,

Fita sukayi ni kuwa na koma gefe ina kallonsu kallona yayi cikin damuwa yace.
"Zoki taimaka min."

Kaman nayi banza dashi sai naga yarinya ce zata iya ɗaukar haka a jin haushi, zama nayi a kusa dashi ina bashi yana sha, tsaki tayi tafita daga ɗakin inda tayi karo da inna wuro, wacce tayiwa jikanta mafi soyuwa a zuciyarta farfesun zabuwa.
Da sallama tashigi ɗakin ajiye cup ɗin nayi naje na amsa, cikin kulawa tace.
"Amra ya mi jikin dai."
Zan bata amsa yace.
"Matar karfe zo nan gani nan ras."

Zama tayi ta kalle shi kafin tqce.
"Har sai yaushe wannan al'amarin zai tsaya na gaji da zullumi, kai ɗaya ka zame musu kalagaren bakin tulu,"

"Toh matar ina zan sani jiya fa bayan naga barinku tasha abin ya faru, wannan bashine farko ba dan haka ba shine karshe ba zasu cigaba da shiri, amma wannan karan sunyiwa kansu muguwar asara, dan yau zanyi baki daga rasha kuma abinda zan zana musu bani ɗaya zan amfana ba har dasu,"

"Kallonshi tayi kafin tace.
"Kana nufin basu san da zuwan bakin ba."
"Eh basu sani ba amna zasu iso yau kuma rashina asara ne babba a gurin Lamiɗo groups."

Sun jima suna tattaunawa kafin wasu malaman jiyan har su biyu suka shigo dubashu sukayi sannan, suka saka masa ruwa suka fita ita ɗayar idanunta kur akanshi,

Muna zaune har aka kawo abin karyawa, tunda muka sha farfesun Inna wuro ban sake cin wani abu ba, har karfe ɗaya Yan matan suka shigo suka gama abinda zasuyi suka fita,


***
Da asuba likita yazo duba Sadeeq aka samu munyi gaba take aka fara bincike duk yanda aka so ganowa babu wanda yaga fitarmu, abinda ya fusata familynshi knn,

A ranar suka bada cigiya da kome aka kuma saka jami'a suna bincike,

Wajen karfe ɗaya bakinshi suka iso, suna zuwa suka sami muguwan labari, bakik ciki yasa suka koma ko faɗan kome basu yi ba sai Bayan tafiyarsu suka duba sakon da suka bari, da kuma yawan kuɗin dq zasu biya take cutar hauka ta kamasu....

Nanah kuwa ai suna komawa gidansu macizai suka hanata sakat, kamar mahaukaciya haka tayi ta ihu har asuba

Adda kuluwa kashedi aka mata bayan tasha matsa😂.


***
Sati biyu da zuwanmu na fahimci matsalar Yarinyar gidan, Mi suna Aunty Amma asalin sunan khadija ne, masifar son Sadeeq take abin dariya a wnna shekaran zata gama skull,

Ina zaune a falo shi kuma yana ɗaki faɗa mukayi na fito na bar mashi ɗakiin ba kome bane ya haɗa mu sai yanda yarinyar dake masa dress ciwo take, shafa shi , bai mata mgn ba shine da nayi magana wai aikinta take gashi tayi ta janshi da hira tana iyayi, duba lokaci nayi naga ta kusan zuwa, gyara kwanciyana nayi dama nike goge masa jiki, kuma na haɗa masa ruwa yayi wnk, amma yar banta uba wai ni zata kawowa bariki,

Ina jin shigowarta ko sannu bata min ba, jikinta har rawa yake, sai da nabari ta shiga ciki nima na bibayanta, karɓan kayan aikin nayi cikin wani irin fushi nace.
"Ya isa haka ni matarshi ce kije ki rike aikin ki bana son iyayi kar nasake ganin kafarki, "

Wardrob na buɗe na ciro kuɗi na mika mata sai kallonshi take, ni kuwa tana fita na zauna, nayi masa gyara ko kallonshi banyi ba, zan miki ya finciko ni da hannunshi me lafiyan ya matsa ni a jikinshi yace.
"Kin kyauta da kika kore min me kula dani"
Shiru nayi ina jin yanda yake sunsunar wuyana, saka hannu me ciwon yayi ya zare hijab ɗin, ɗauke wuta yayi, sakamakon ganin rigar jikina, toh zafi ake shine saka haf vest da wando pencil, take ya ɗauke gangaro da kanshi yayi wuyana, har zuwa kirjina yana shakar kamshin turarena,

Goga kanshi yake tare da sumbatar ko ina, karshe janyo fuskana yayi ya haɗa bakinmu, jikina ne ya ɗauki rawa, bam muka ji an buɗe kofa,

Aunty ce, cikin masifa na juya nace.
"Ke jakar ina ce da baki iya sallama ba fitar min a ɗaki kafin nazo inda.."
Da gudu tafita tana kuka aikuwa ta haɗu da Inna wuro tambayarta tayi tace mata dan tashiga ɗakin Hammah Sadeeq shine na koreta Babban budurwa fa, aikuwa ta haɗu da masifar inna wuro ta sakata a gaba har gaban Uwarta ta faɗa mata kome da kuma abinda hansatu ta faɗa mata na wai ita Aunty san Sadeeq take shi yasa take min gani gani, aikuwa mahaifiyarta ta surfeta tass, tace bakin rijiya ba gurin wasan makawo bane ta shiga hankalinta Sadeeq ba sa'antq bane balle ni,




Tanq fita ya kalle ni cikin dariya yace.
"You're jealous"

Tsaki nayi NA juya masa baya nace.
"Allah ya yayye min kishi akanka kana Y...."

Finciko yayi yana hucci yace.
"Mi kika Ce yaro zaki Ce min."
"A'a Ya Sadeeq zance fa." NA kai karshen maganar tare da tura masa baki, ganin tsakanina da Allah na kore masa yan mata sai ya shiga tsokana Aunty ban kara ganinta ba sai da na shigq cikin gida muka gaisa Mamarta ta bani hakuri tare da sauran matan cikin gidan,, nuna musu nayi bata min kome ba, kawai sallama nayi mata magana tayi inzata shiga keɓaɓɓiyar guri.


Zama nayi da sauran matan muna hira jefi jefi, ganin yanda suke fura ya ban sha'awa da,zasu daga nima na karɓa, akayi dani.


****
Bayan wata guda, dake an fara damina, kuma yaran gidan suna zuwa mkrnt sai matan surukai Jummala matar Takwaran Sadeeq ana kiranshi da buba, sai Matar Hayatu, Sakina sai matar Adamu, Tabawa, yar carafke suke, nima na shiga cikinsu anayi dani , fitowa yayi ya zauna ya tsaya kallona nima dai van sani ba, can muka mike muka fara siwe, wani zane ake a kasa babban box da kafa ɗaya kana tsalle, abin ya tuna min da kuruciyata, karan jigidan sakina naji nace.
"Yawwa matar ina son wannan abun dake kara,"

Aikuwa jimmala tace.
"Hajiya mi zakiyi dasu ina dashi,".. Aikuwq tajamu muka shige ɗakinta ta kwaso ta dan tA zuba a zaren lilo, tayani ɗaura sukayi ina dariya, har aka gama, ɗan tsallenayi suka jiyo karanshi, hiranmu muka cigaba can naji murya inna wuro da sauri nafito,

Rike haɓa tayi ni kuwa nasa mata dariya, tsiya tayi min wai sai ta kwace mijinta,

Dariya kawai nayi bansan yana falo ba nashiga da ɗan tsalle na na zare hijab ɗin ina sga jigidan, can kasa kasa yace.
"Ya isa haka Am....ra..h"

Da sauri na juya, idanunshi a rufe ya yafito ni, a hankalin na isa gurinshi ynx kan nasaba da kwanciya a jikinshi bana cika jin tsoron shi kaman da, shafa jigidan yayi wanda sukamin ɗibi sha biyu, jin yanayinshi na sauyawa yasa na mike na koma gefenshi a hankali yace.
"Yaushe zaki ɗauke ni a mijinki nagaji ina niman a gajin mace wacce zata ɗauki nauyina, idan zan matsa miki toh zan hakura dake, nayi wani auren."


Washhhh Shafin yau ya min daɗi fa😂 typing nake baji ba gani...
🌺🌷🌷
*_DA CIWO A RAYUWATA_*
🌹🌸🌸

Na
Mai_Dambu
Wattpad:Mai_Dambu
            * Can I Accetpt You*

        
*Page Q👈*

     Tsoron abinda zai shiga tsakaninmu nake ai ni ban ɗauki shi a matsayin miji ba kawai ina masa kallon kanina ne, girgiza masa kai nayi cikin rawan murya na manta gargaɗinmu dashi, kawai na shiga magana nace.
"Wallahi ban karɓan kanin bayana a miji ba Allah ya gani ni bana son wannan kaddarriyar auren mi zancewa duniya mi zan nuna musu, ko wacce mace alfahari take da mijin da zata aura ya girmeta ko sa'anta ni kuma sai na nuna masu yaro karami haba kayi nazari da 6 ɗinka mana nooo."

                 Mikewa nayi na shige kitchen na cigaba da ɗaura
Mana abincin rana, ɗan wake da kayan lambu ne, sai yankakken kwai,

          Koda na kawo masa girgiza kai yayi yace.
"Jeki na gode da abincinki."
           Haka kafin na bashi magani ya kira Aunty Ta bashi magani.
      Wasa wasa Sadeeq ya yanke alakar dake tsakaninmu, a dakin da muke yana da rest chair akai yake kwanciya ko a falo, haka na zuba masa ido dan bani da tacewa,

   Yanzun kam yana fita cikin gari har gidan gonarshi yaje yaga ya dabbobinshi suke dake,
   Wani irin shakuwa ce ta shiga tsakaninshi da Aunty wanda yasa na kauda kai sosai idan tashigo gidan toh dole fita zasuyi,

    Inna wuro tana kallonmu tsaf ta fahimci muna rikici amma bata san miye ya haɗa mu ba, sai tasa mana ido, na gaji da zaman gida, dan haka Ranar juma'a ana cin kasuwa naga Hansatu da Jimmala da Tabawa tare da Sakina zasu kasuwa, ban tambaye shi ba nabisu inda na kwashi kuɗi muka je, nayi sayayya sannan suma na kara musu muka fito, dake babban gyale nasaka ban sa Hijab ba, muna hanyar dawowa, wani mutum yasani a gaba da magana, har muka shigo inda Sadeeq yake zama da matasa bina yake,

    Lokacin da Sadeeq ya dawo yaga bana nan gurin Inna wuro yaje ya tambayeta ina na je.
Ɓantaran goronta tayi sannan tace.
"Ta shiga kasuwa ka ɗauko mutum ba dabba ka ajiyeshi guri guda sannan ka tsiro masa miskilanci kana ɗaukar wata daban kana fita da ita, dama ita Amra yarinya ce me fahimta in nice tuni ban ɗagawa kowa hankali ba,."

          Maganar zuwa kasuwa ya daki Sadeeq fatanshi guda Allah yasa da hijab da Nikkaf na fita ba da wani gyale ba,

            Kin kulata yayi ya fito majalasa, inda ya zauna aka kawo soyayye namar kaza ya juyewa matasan yace sauran akai cikin gida, duk abinda ya gani sai ya saya musu shi kuma bai ci.
   
    Mun yanko kwana kenan dama ya zubawa gurin ido, mutumin yafito daga mota yace.
"Haba ranki shi daɗe ki kula ni mana"

           Hango Sadeeq yasa jikina ɗaukar rawa, wani irin kallo yake bina dashi, da sauri na wucce mutumin nayi hanyar gida, har kofar gidan ya biyo ni zuciyata kaman xata yo waje, ina shiga bansan mi ya faru ba, sai jin Salatin Inna wuro nake da sauri na fito,
.    Hannun Sadeeq me ciwon ne ya sake famawa, take aka kira mi ɗauri yana zuwa ya shiga dubawa, mikewa yayi yace.
"Inna wuro ai karayan ta koma dai danta, kuma babu wani ciwo dan motsata da yayi da karfi ta haɗe da bata haɗe ba nan da yan kwanaki zai iya amfani

Please Login or Register in order to submit comment