Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

duwatsu da azurfar yar asali, an kawata kirjin rigar da karfen azurfan da kuma duwatsu murjani. D'aga idanuna nayi na kalleshi take na tuna lokacin da yasaya mana nida nanah a saudiya amadadin nayi godiya sai na bige da nimana cire rigar ina hucci.

Takowa yayi gabana yace.
"Wallahi Amratuh karki kure ni dan zan baki mamaki dan ba'a kanki aka fara kishi ba kuma ba'a kanki aka fara ciki ba idan zaki nutsu ki nutsu ki bar ni naji da abinda ke damuna ko kuma na miki shegen duka dan tsaf zan iya aikatawa, kuma mu zuba ni dake."

Wani abu me kama da jaka ya mika min na karba dakyar ina sauke kwallar da suke idona bai kula ni ba, yafita waje abinshi, buɗe laidar nayi nafito da takalmi da jaka, ɗaukar wayata nayi nasaka sannan na ciro takalmin nasaka nafito,

Yana bakin kofa ya jingina da jikin bango, kallona yayi har zai mana sai yaji kamshin humra da Soft turarena kenan dukda ina amfani da Oud amma ina son soft da pure love, shima haka ba laifi.

A hankali yake bin baya yana kare min kallo girgiza yayi a ranshi yace.
*Kishi da masifar ciki duk ya maida ita wata iri mace har mace.*

Haka muka fito har zuwa gidan sunan a nan naga iyayi yan matan family sai cusa masa kai yake shi kuwa yana rike da hannuna har falon me jegon, kowa yaga rigar jikina sai yayi magana, babu hassada nayi ne shi yasa ko ina na shiga ake bani ido....

Inna hari ce ta gasa boye damuwarta tace.
"Yo ɗan farka ba ance min bazaka iya haihuwa ba ita wannan a gidan wani shege ɗa ɗauko cikin."

"Matar knn akwai wani shegen bayan ni ne, ai cikin nawa ne jikarki ce dai banyi niyar mata ciki ba kuma naga ɗan banza da ya isa ya sani ko ance miki bansan zuwa da cire abin hana ɗaukar ciki zai saka asami cikin karki damu ga magajin Almu nan."
Nikan tunda na sunkuyar da kaina ban kuma ɗagawa ba,

Tsaki tayi cikin jin haushi tace.
"Aikin banza zani ya mutu yabar ɗuwawu, daɗin abin waye almu da abin...."

Haɗiye maganar tayi tare da kwafa...

Kai naga damuwa a cikin gidan nan kowa so yake ya fitar da ciwon dake ranshi daga Sadeeq harsu ɗin sai bayan isha muka bar gidan.


A hankali Sadeeq da Nanah suka jone aka mai dani gefe ko nace gashin da Sadeeq yake min nakan zauna a ɗaki nayita kuka na rasa inda zan tsuma raina,

Gashi abinda na fahimta shine baya zaman gida kuma baya dawowa sai dare, inda zai shigo yasame ni ina kuka bai taɓa ce min lafiya ba, ni duk na fada asibiti ya kaini na fara awo,

Tunda Shadow ya turo min sako na karshe bai kuma turowa ba.

Wata talata na koma asibiti aka gama min kome toh ina fama da cinyoyina suna ciwo, sai na faɗa suka haɗani da likita koda na shiga na zauna na sameshi da wank mutum ya juya mana baya,

Kallona likitan yayi cikin kulawa ya tambaye ni nai masa bayani,

Rubuta min magani yayi da cream na man zafin kashi, zan fita naji an kira sunana na zata likitane a'a ashe wanca mutumin ne yace.
"Amratu Yusif Jama'ar, dr in microbiology degree kuka gareki shekaru talatin da biyu a duniya mijinki ɗan shekara ashirin da tara, wow abu yayi kyau an turo miki miliyan ɗari biyu dan kirabu da Sadeeq amma kinki toh ai badamuwa muga takardanta wow cikin seven month an two wks lallai zaki haifi yaron a cikin kabari knn zan baki nan dawata biyu ki yanke shawara in ba haka ba, wallahi kinji na rantse zaki sha mamaki dan Me gidanmu ya wucce saninki."

Da sauri nafita har muna cin karo da Sadeeq a razane na buɗe murya zan kwalla ihu ya ce.
"Kee nine"

Faɗawa jikinshi nayi tare da sake kuka, nace.
"Muje gida ina jin tsoro."

Jana yayi muka tafi gida kuka nake yana rungume dani nan ya tambaye ni dakyar na faɗa mishi.

Tsaki yayi yace.
"Toh Allah ya kyauta.".
Bai damu ba har muka dawo gida.

****
Da dare zaune Sadeeq yake a gaban likitan yana kallonshi yace.
"A duk lokacin da ciwo ta kamaka asibiti ake nufa kuma gurin likita, sai gashi kai kana amfani da iliminka ana razana mace me ɗauke da juna biyu wacce bata san kome ba, Dr Sa'id kasani zan iya cutar da kai kuma na kwana lafiya koda wani irin...."..

Mikewa yayi yaje dai dai gurin da likitan yake ya saka hannunshi kasar table ɗin da likita ke zaune ya zaro wayar da yakira nomber Shadow,

Murmushi yayi ya ajiye mishi wayar yace.
"Ni bazan maka kome ba amma kasani su abin dogaranka zasu maka..."

Yana gama faɗar haka ya nufo gida abinshi.

Aikuwa washi gari sai ga labarin an kashe dr Sa'id na asibitin lamiɗo hospital wanda aka kashe shi bayan anyi masa dukar kawo wuka.

Murmushi Sadeeq yayi dan yasan haka zai faru Allah yasa, yasami wani abu a gurin likitan dan bayan yafito officer ɗinshi ya tura masa da sakon....



Tun daga wannan ranar bamu sake jin ɗuriyar Shadow ba har na shiga wata tara, ina fama da cikin.

Izuwa wannan lokacin hakurina ya kare, da kaina naje har ɗakinshi na bashi hakuru har da kuka,shiru yayi yana kallona kafin yatako har gabana ya kallon yatsun kafana da suka ɗan fara hawa sabida tsayuwar da nayi, zaunar dani yayi yace.
"Aini ba fushi nayi dake ba kawai na baki dama ne kiyi yanda kike so, tunda prince ko princess mulki suke ji ai badamuwa mu cigaba a haka."
Rike fuskar shi nayi ina niman goge laifina janye fuskanshi yayi dukda yana cikin bukatuwa da ni amma ya danne haka yayi hakuri dan kar nan gaba nace mishi ya cika damuna da halinshi murmushi yayi yace.
"Mi zaki min kar dai sassaqe ni zakiyi, ko ce miki akayi ni tuwon laushine."

Duka nakai mishi yana karewa tare da sake dariya, haɗe fuskarmu yayi cikin wani irin yanayi yace.
"Kince kinyi hater ɗina yake nan."..

Bakinshi na kama cikin wani irin sumbata nake aika mishi dakyaer ya kwaci kanshi yana dariya yace.
"Kiyi hakuri ba ynz ba"

Kuka nasaka mishi amma tsakaninshi da Allah yaki amincewa har da rarrashina dan dole na hakura da niman Sadeeq dan tsakaninshi da Allah yake guduna kuma zasuyi kome da Nanah nice dai yake gasani.

Sai na hakura na cigaba da kallonshi duk ranar girkina sama zai hauro har sai na fita, Sadeeq na min wani irin horone wanda ake amfani da emotion ɗinka kuma yayi nasara dan nayi laushi na daina binshi sai dai kullum ina kokarin gyara alakarmu dashi har izuwa lokacin da cikina ya fara tsufa.

Dake cikin ya kumbura min kafafuna, dan na kumbura sosai ban cika xaman sama ba, sai na dawo kasa da zama nanah kam bana ma jin ɗuriyarta dan bama haɗuwa,
..

Tun safe na tashi da mutuwar jiki ina kwance a kan doguwar kujera shi kuma yana kitchen wayarshi aka kira ya ɗauka dan yaga ɓoyayyen nomber, nima jin karan wayana naji a sama ashe ban fito da shi ba,

Dakyar na mike ina ɓata fuska, duba wayar yayi yasaka a kunne ce masa akayi.
"Abu ɗaya zakayi kasallama mana kome na dukiyarka in ba haka ba, matarka da take hawa sama da ita da abin cikin Allah ya gafarta musu....."

"Kaiiiiiiii."
Ina haurawa naji dummm akan cikina, dukawa nayi a tsoroce na ɗago wani mutum na gani da bakakke kaya, wani dukan yayi niyyar sake min a cikin na duka, nayi maza na bashi bayana ya maka min sandar ihun da na kuma a karo da nakira "Hamma Sadeeeeeeeeeeeeeeeq" nabiyu shi ya ankarar da Sadeeq, turoni mutumin yayi daga step na shiga fadowa.
"Amratuuuuuuuuuuuuuu"Da mugun gudu ya iso amna ina tuni na faɗi akan cikin ga jinin dake zuba kaman am buɗe magudanar ruwa Allah sarki yayi shirinsa na,zuwa aiki ganin halin da nake ciki na wahalar ciki yace na zauna yayii aiki, da ace nanah tana gida ne itacw zatayi toh sun tafi manbila bikin yar kanwar Mamanta nice kawai sai shi.......

😭😭😭😭😭😭 Allah Wahidun Ahaddu Makiya kuma na cikin gida...
🌺🌷🌷
*_DA CIWO A RAYUWATA_*
🌹🌸🌸

Na
Mai_Dambu
Wattpad:Mai_Dambu
        *Gudun ceton rai...*


*Page B=📕*


Koda na iso dakyar na iya mika
Mika mishi hannuna a raunanne nace.
"H...a...m...m..a..n..a z..a..n m..u.t..u kaxo"
Numfashi naja wanda ya sa na fitar da jini ta hancina, mai da hannuna nayi tare rufe idanuna, gigice ya iso dariyar mutumin muka tsinkayo yana cewa.
"Wannan fa gargaɗi ne fa kayi ɗauki wayarka kaji mi zasu ce, sai ka ɗauketa zuwa asibiti in ba haka ba daga ita har abin ciki feeeyu" ya shata wuyarshi a ta barandar waje ya dira abinshi.

A gigice Sadeeq ya ɗauki wayar dariya aka masa, jikinshi yana rawa yace.
"Mi kuke bukata dani toh toh zan kawo muku amma kubarni na kai mata na asibiti."

A ruɗe yazo ya sungume ni zuwa waje ganin halin damuke ciki yasa masu tsaronshi suka buɗe mishi motar ya sakani zasu ja motar yace.
"Kubar shi."

Cikin gidan ya koma can yafito da wasu ducomentry ya zuɓe muka bar gidan sai asibiti, yana shiga ya fito dr Ya'u michika yasa nurse suka fito da gadon majinyata aka sakani a ciki, inda akayi dani cikin ɗakin haihuwa, fitowar dr Amnah Buba Yaro da kuma dr Ya'u suka mika mishi takarda yasa hannun Dr Amnah tace.
"Mr Lamiɗo kasa hannu mushiga da ita tiyata, sannan muna bukatar jini."


Da sauri ya karɓa ya cika,"Mr Lamiɗo saura jini."

"Ok jinina grp o nagitive ne zaku iya ɗiba."

Nuna mashi lab sukayi yaje ya kwanta aka ɗiba, har laida biyu, ana gama ɗiba wayar shi nakara, ɗauka yayi ya kara a kunne runtsa idanunshi yayi ya mike dukda hutun da akace yayi haka ya fito kanshi na sarawa,

Dakyar yafito ganin wasu kaman likitoti sun tawo ayari guda yasa ya matsa gefen wani mutum, jin sukar allura yayi a gefen wuyarshi, an cika an cire shafa gurin yayi yaji damshin jini, juyawa yayi babu wanda ya nuna alamunshine, da sauri yafito.

Gurin motarshi ya shiga ya tadda ita, ya bar asibitin baki ɗaya, jirine ya fara ɗaukarshi a hankali ya koma gefen hanya, ɗigan abu yaji a hancinshi ya shafa jini ya gani na zuba ga wayarshi na kara, duk lokaci guda ya farq ganin duhu lalubar wayarshi yayi yayi swip ɗinshi ya kara a kunne dariya aka mishi. Sanan aka ce mashi.
"Ga yara na nan sun zo ɗaukarka."

D'aga kanshi yayi dakyar ya kalli side ɗin da yake, kafin yayi wani abu sun buɗe motar sun kwashi takardun sun watsashi, a motarsu suka bar gurin a guje.

***
A asibiti kuwa anyi nasaran cire yara huɗu amma biyu sun mutu mace da namiji, sai maza biyun ɗaya ya karye a hannu ɗaya kuma toh sai abinda Ubangiji yayi, ana cikin ɗinkeni ɗayan ya cika, saura ɗaya wanda ya karye cikin sauri aka shiga duba karayar sai da suka kai shi aka mishi Xray aka gano gocewa ne,, sai buguwar da nayi a gadon bayana wanda shima ya haifar min da gocewar kashin bayan har ya matse lakana, anyi aikin ciki nasara,

Haka aka fito damu da gawarwakin yaran uku, nikan koda nasami lafiya bazan iya kome ba sai an kaini Germany.

***
Watsa mishi ruwa sukayi mi masifan sanyi tare da sake mishi duka da itace a gefen fuskanshi faɗuwa yayi da kujeran, yana mai rutsa idanunshi, dago shi sukayi Alhaji bilya ya shiga kifa mishi mari har sai da idanunshi suka buɗe,

Kunce shi sukayi sannan suka watsa mishi takardun da biro ya shiga saka musu hannu ko uffan bai ce musu ba,.

Yana gamawa suka kece da dariya Alhaji bilya yace.
"Daga kai har manta bazaku rayu ba, dan Shadow yace a kasheku dan mun sami labarin duk abin cikin sun mutu sai shaiɗani irinka da yaki mutuwa toh ai badamuwa nan da awa biyu duk allura zaiyi aiki akansu.."

D'ago kai yayi cikin mutuwar jiki yace.
"Idan kuka bar min iyalina zan bar muku kome kamar yanda mahaifina yayi na shiga duniya ko ɗuriyata bazaku ji ba, amma wani abu yasami iyalina daga Nanah har Badariyya bazu rayuwa ba, kaiii kun ɗauka ku kaɗai kuka iya abin ne idan nace zanyi nawa wasan bazai muku kyau ba tunda na baku kome ku barni na tafi."
.

A tsorace Alhaji bilya ya kalleshi dariya sadeeq yayi sannan yace.

"Badariyya tana hanyarta na dawowa daga abuja ta shiga jirgi yanxun haka, saidai kash tasha gubar makarin gubar shine abarni na fita salim alim in ba haka ba, toh ai ba damuwa dan ynx haka Ita khadija har tasha madaran Admiral, wanda shima gauraye yake da wata guba ta musaman saika zaɓa yaranka ko migidanka shadow."..

A gigice ya ɗauki itace ya makawa Sadeeq sai da yaranshi suka rike shi, suka jashi gefe sukayi yar kuskus sannan suka dawo nan suka dawo, suka sunce Sadeeq, dakyar ya mike m amma a haka sai da yazube a kasa, sake mikewa yayi sai kawai ganinsu yayi sun rufe mishi fuska da wani kyalle, aka jasu suka fita watsa shi sukayi a mota sannan suka bar cikin dajin a fusace.

Inda motarshi yake suka ajiyeshi sannan suka bar gurin, da rarrafe ya shiga motarshi ya bar gurin, asibiti ya nufa, koda ya fito mikewa yayi rass ya shiga ciki,, da tambaya yaje har ɗakin da nake, kiran wata nurse yayi ya faɗa mata abinda yake bukata, a lokacin sannan ya shiga ciki, ya fito gurin biyan kuɗi yaje, ya biya kome sannan ya samu nurse ɗin ta fito mashi da yaran har mota ta taimaka mashi ya kwantar dani sannan ya ɗaura min yaro me lafiyar gefena, gawarwakin ya sakasu a gaban motar ya shiga,

Wuta ya bawa motar, muka fita a cikin asibitin da masifar gudu dan yasan zasu biyo bayanshi tunda takardun da yabasu ba na asali bane haka duk labarin da ya basu karya ce,

Yana barin asibitin suna zuwa, gudu yake tsakaninshi da Allah har ya fara hango su dan suna duva inda muke akace ya fita dani shine suka biyomu,

Sosai suke tsire da motarshi a yankar wani daji yayi me mugun duhuwa, ya cigaba da gudu.

....
Jikin Alhaji bilya na rawa ya ɗauki kiran shadow yace.
"A..Yallaɓe kayi hakuri an samu akasi ba takardun bane ashe na bugine kum...."

Hakuri ya cigaba da bayarwa har aka kashe wayar abin mamaki shine sunyanki dajin amma basu hango shi ba asalima kamar ɓace musu yayi, duk yanda suka so nimanshi basu ganshi ba ga dare yayi.

Ga kuma sawun motarshi amna babu alamarshi fita sukayi suka shiga nimanmu, wayarsu suka kunna da niyyar shiga dajin amma abin mamakin yanda wasu kwari suka shiga binsu suna cizonsu dan dole suka koma, ihu suke sabida zafin cizon kwarin kamar harbin kunama, kana susawa wajen zai ɗaye kamar an zuba maka wuta,

Dole suka fito da gudu suna ihu, Alhaji bilya kan anan yabar babbar rigarshi da takalminshi,....

Asalin wannan dajin, mugun dajine me fama da muyagun aljanu da namun musu hatsari, dan a kusurwan gombe yake, kasantuwar gudun da yayi wanda yashi barin garin yola baki ɗaya, garin bin yanke ya faɗa wannan dajin wanda babu mai fiddashi sai kudiran Ubangiji,

Kuma mugayen aljanu suka hanasu Alhaji Bilya shiga, tafiya muke hanyar na dadda rufewa har ya daki wani icce.

Take motar tayi wani irin kara, gefe guda aljanun na bin bayanmu.

****
Birnin kisra......
Cikin fararen kaya Ummul Khair ta bayana hannunta rike da farin calbi ta kalle imran da yake lazumi tace.
"Sadauki tashi maza Amininka yana bukatar taimako maza dan yana cikin muguwar dajin nan na iyakar gombe da yola maza ka isa cikin izinin ubangiji ka taimaka mishi dan a ruɗe yake,."..

Da wani irin azama ya mike tare da kiran daumakarshi da cewa.
"Huruz."..

Kafin ya rufe baki ya baiyana hawa bayanshi yayi suka lula gajimare, shafa wuyar daumakar yayi yace.
"Kayi gudun da baka taba yi a cikin mintuna goma."

......
Fita Sadeeq yayi yana me jin tsigar jikinshi na mikewa sunayen Allah ya fara ambata yaje ya buɗe motar yana dubawa, ya kai mintuna goma zuwa sama, a lokacin har sun zagayeshi cikin mugun suffa.

Zasu daka wawa akanshi aka ce musu.
"Kaiiiiiiiiiiiiiiiiiiii" cikin wani irin tsawa a firgice ya juya Imran ya watsa mashi ruwa take yazube a gurin dan yasan matukar ya ga shi tog zai ga sauran, tun karosu ya fara suna ja da baya, har ya ɗaga Imran zuwa cikin motarshi, sannan ya shafa Huruz yace..
"Jarumina jeka abinka Allah ya albarkaci barde huruz."

Haniniya yayi sannan ya tashi sama.
Kallon aljanun yayi cikin maɗaukakiyar murya yace
"Kimanin shekara ɗari biyu kuka hana mutane shigowa wannan yanki ni kuma yau zan karya wannan abun dan zanfita dashi duk wanda yake son uwarshi ta haifi wani ko matarshi tayi takaba ko yaranshi su zama marayu bismillah."7

Ai a guje suka juya cikin tsawa yace.
"Ku bude min hanya kafin na shafe tarihinku."

Ai a guje suka buɗe mishi hanya har bakin hanya, yace.
"Koda gigin wasa wani yabi bayin Allah nan sunanshi gawa..."


Hurawa Sadeeq iska yayi take ya farka, yace.
"Maza jimeta.".
"Aboki kaja motar bani da karfi."

Fita yayi ya maida Sadeeq baya inda ya ɗaga kaina Sadeeq ya zauna sannan ya ɗaura kaina a cinyar Sadeeq ya mika mishi baby ya kallemu cikin tausayi yace.
"Kayi hakurin rashin da kayi amma na dawo Insha Allah ynxu zamu fara da ikon Allah, rufe kofar yayi sannan ya koma ma zaunin drv yana kallon jariran da suka rasu. Girgiza kai yayi ranshi na kuna alwashi yaci a ranshi dole akawo karshen wannan wasar.....





***
Birnin Toronto na Canada, an sami ɓollowar annobar muran tsintsiye shi yasa aka fara kokarin zubawa tsintsayen magani.


A guje ta isa gidan tana kiranshi da karamin murya dakyar ya ɗago kai cikin dariya ya.mike ya ɗagata sama, yace.
"Baby Diana barka da zuwa."

Karewa fuskarshi kallo tayi kafin tace.
"Idan aka cire Glass ɗinka da aka saka maka gashin fuskarka babu abinda zai ban bantaku sai sai shi cikin idanunshi ashe colour ne kuma yana tara gashi Ya ma sunanshi something Lamiɗo.".. F
Faɗuwar tangaran a hannun......

*Nima nace haka kuyi min afuwa na tafi hidimar gabana, dan haka no more complain....*
🌺🌷🌷
*_DA CIWO A RAYUWATA_*
🌹🌸🌸

Na
Mai_Dambu
Wattpad:Mai_Dambu


     Kuyi hkr jiya gabaki ɗaya na fitane.....

   
*Page C=🐈*

      Cikin wani irin gudu yafitar damu a wannan dajin, bai wata wata ba sai jimeta har gidan Inna wuro wacce take zaune a kan abin sallah zuciyarta ba daɗi, a hankali taji iska na busa labulenta, mikewa tayi zatayi sallama yace mata.
"Assalamun Alaikumun Malama Aishatu, ga jikarki da matarshi a cikin mugun Yanayi na kawo miki sune dan nan da kwana uku zaku bar kasar baki ɗaya."

    Jikinta na rawa ta buɗe mashi labulen, ya shigo dani  ya kwantar akan gadonta sannan yafita ya shigo da Sadeeq ya kwantar dashi akan kujeran,

     Jariran ya kwaso ya mika mata mai ran sannan ya zuba mata gawarwakin a kasa yace.
"Malama Aishatu kinga kyautar Allah ko, ba ɗaya ba biyu, ba uku ba har huɗu Allah sarki azaliman can sun kashesu baki ɗaya ya kamata a suturtasu bari na taimaka miki da likaffani."

    Fita yayi ita kuma inna wuro ta shiga juye ruwan xafi ta surka, tayiwa yaran wanka a tana kan mace knn yayi sallama bashi izin shigowa tayi yana shigowa ya fara suturta maxan tsaf sannan ya jira ta mika mishi mace kallon Yarinyar yayi yace.
"Wannan kamarta sak da Aminina, sauran ma haka amma basu kaita ba,."

   Goge kwallarta tayi tace.
"Mazan da Almustpha suke kama, ita wannan Hadiza ce dan Buba yafi kama da Hadiza akan Almu."

     Yana gama kintsa yaran yace.
"Wannan naga da ciwo a hannunshi ga wannan zuwa gobe karku masa wanka a shafa sai bayan awa ɗaya ayi masa wanka, Takwaran Almustapha kenan dan nasan burin Aminina knn sannan uwar bazata farka nan kusa ba ki bani hotonki zuwa jibi zasu bar kasan sabida akwai abinda zanyi"

         

  Mikewa tayi ta ɗauko kananun hotunanta ta mika mishi, ya karɓa sannan yayi mata saida safe.

   Yana fita bai zame ko ina ba sai Tsibirin Pakistan inda yaje ya sakasu Rusaila da babansu, kunce musu sassarin sallama yayi musu sannan yace.
"Idan da gaske Kuna kaunar Amratu toh kufita a rayuwarta sannan idan son gaskiya kuke mata ku tayasu kwatar hakkinsu."

         Shiru sukayi sannan suka gyaɗa kai, da cewa.
"Mun amince zamuyi haka zamu tayaka amma da sharaɗi zaka auri Y'ata?"


Harara Imran ya jefa ma Uwais sannan yace.
"Kuje zan nimeku zuwa kwana biyu batun yarka kuwa ajiyeshi a gefe dan Matata yagalgalata zatayi dan masifar kishine da ita."

"Wannan tunaninka ne amma ina mace babu macen da zata razanani kawai kace min bazaka aureni ba shine maganar kuma koda rikici sai na aureka." tana kai aya tafita hankalinta kwance,

Bin bayanta yayi yana murmushi, yana son macen da bata ɓoye abinda ke ranta kamar Zulja amma ina zai iya da wannan dan har ya fara hango gidanshi ya koma sansanin Yakin kishi.

****
A razane suka juya dire Diana Adnan yayi ya isa ga Mamanshi cikin rawan murya yace.
"Meemah

Please Login or Register in order to submit comment