Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zama daga Almu har Hadiza shegen duka zan musu." imran na gama aikinshi ya bar gidan abinshi inda ya nufi kisra.


****
Alhamdulillah jikina yayi dama dama, ina zaune a bakin gado bayan na idar da sallah, cup din tea ne a hannuna wanda yake ɗauke da madara da milo, an sami sugar kaɗan ina sha gashi yayi kauri, toh bana iya cikin kome sai tea ɗin kallon kasa nayi ina nazarin yanda rayuwa tayi min juyin masa,

Kurɓa nayi na cigaba da kallon kasa zuciyata ba daɗi, gefe ɗaya tunanin Sadeeq da Abul ne a raina. Na rasa ta inda zanji motsin ɗana kukane ya kwace min, ajiye kofin nayi na cigaba da kukana, har wani lokaci shigowar Mommy da Rahma shine yasani na haɗiye kukan, dukna rame na fita hayacina, zama sukayi cike ds kulawa Aunty Mommy tace.
"Amratu ki koyi hakuri mana babu daɗi a mutuwar Aure gashi kin rasa cikin dake jikinki, kiyi hkr Allah zai mai damiki wanda yafisu."

Gyaɗa kai nayi tare da share kwallana, nasiha suka min sai dare suka bar asibitin.

Kwana na uku da farkawa aka sallame ni ban taɓa sanin haka mata ke ji, idan aurensu ya mutu a daidai lokacin da kake ganiyarka ba sai yau ahankali labarin mutuwar aurena ya zaga unguwarmu, nan aka kafa gulmana ban damu ba wai dan hankalina ya kwanta Ya Abbas yaje fut yola aka dawo min da aikina nan suka sani a gaba na koma bakin aikina,


Ranar dana koma babu irin gulmar da ba'ayi ba, ban kula kowa ba asalima abinda ke damuna yafi karfin surutun mutane,


A hankali lokaci ya tafi sosai,ranar juma'a na dawo aiki Na gaida baffa knn zan wucce yace min.
"Zo Mamana."

Komawa nayi na zauna cikin nutsuwa, kallona yayi sannan yace.
"Iyayen Sadeeq sun kirani wai suna bikonki ki koma ɗakinki."

D'agowa nayi a sukwane nace.
"A'a baffa aure da zargi baya yuwa da ace babu zargi ne da zan koma kuma baffa idan ka duba ni ɗaya ta zan iya kawo musu wata fitina a cikin iyalinsu ynz suke samun farin ciki idan na koma kaninshi bazai daina bibiyata ba asalima sai dai ya kara kunna min wuta da bazan iya kashewa ba ka duba maganata."

Ajiyar zuciya ya sauke sannan yace min.
"Jeki Allah yayi miki albarka."

"Amin" nace,
Mikewa nayi na shige ɗaki kuma ina da hujjana nakin komawa gidan Sadeeq matukar na koma toh Adnan bazai taɓa barina zaman lafiya ba akaina ace family sun ruguje ina zan iya da wannan alhakin badan Allah ya kare ni ba da fyaɗe zai min kaiii ina na hakura.


Lokacin da Daddy ya koma kira Baffa ya basu hakuri akan naki kuma ina da hujjana ya faɗa musu, amna idan kome ya daidaita zai sake min magana ynx raina a ɓace yake, kuma ina fama da hawan jiki.

Godiya Daddy yayi sukayi sallah.

Lokacin da Sadeeq yaji abinda nace fita yayi a gidan ya tafi can wani lambu ya zauna yayi kuka me cin rai tare da nadamar Abinda ya aikata, sai yamma ya dawo tun daga ranar ya rage walwala,

Zama yake a ɗakinshi ya ɗibo paint yayi ta watsawa a jikin Farin Wall ɗin dake ɗakin zuwa yake yasa hannu yayita zana hotona da hannunshi a hankali ɗakinshi ya cika da zanen hotona,

Idan yaje gurin aiki kuwa, duk abinda zai ce sai ya ambace ni, a cikin maganarshi akwai wata yar India amna tafito yanki south india ce sunanta Amrita,tana aiki a ma'aikatar da zaran zai ce amrita sai ya ɓige da cewa Amratu.

Tun bata saba ba, har ta hakura da amratu. Babu wanda ya fahimci a hankali ciwo ya fara kama shi babu wanda yasani yawan aman jini, da wani irin mura kullum da tari yake kwana da zaran yasha black coffe da Tina take kawo mishi toh haka zai kwana da ciwon kai da tari, tun abin bai ci karfinshi ba har ya kai idan yaje aiki baya iya tsayuwa sai zama,

Idan kuma sanyi Ac yayiwa hancinsa yoyon jini yake, an sami kusan wata bakwai da ciwon ba'a sani ba sai da akaje wani taro anan Canada....

****
Cikina ya cigaba da girma har ynx ina cikin wata bakwai duk wata siyayya nayi, na haɗa kome, jiran haihuwa kawai nake toh ina da kuɗi ga wanda shadow ya taɓa turo min kusan 200m. Toh mi zanyi da kuɗi ga wanda nasamu a gurin Sadeeq Alhamdulillah ins cikin rufin Asiri sai dai har ynx Sadeeq ne a zuciyata dukda raina shekarunshi da nayi a farkon rayuwarmu bai hanani jinshi a jinin jikina ba, dan nayi Imani da Allah rayuwata da kome dake cikinsa dan Sadeeq akayi shi amma dole nayi nesa dashi domin samawa kaina lafiya,


A gajiye nafito aji a hanyar dawowata officer muka haɗu da Aunty Rukayya nan muka gaisa har take min tsiya da Maman 4 dariya nayi nace.
"Na'am faɗi da ihu ki kara da wayyo dan nayi four ɗin nan a haihuwar farko uku sun koma saura ɗaya Almustapha."

Cikin jimami tace.
"Allah ya mai damiki me amfani sannu fa."

Murmushi nayi nace"Amin " nan muka cigaba da hira har ta wucce inda zata ni kuma na nufo office ina saka kaina naji abinda abokan aikina suke faɗa a kaina da cewa.
"Hmmm yaro karami fa ina zai iya da guzuma itama ai budurwan zuciya gareta ina ita ina yaro karami gashi ya sakota ds ciki ai anga kuɗi an saka zallah akai mana."

Murmushi nayi na tura kofar tare da sallama duk sai da suka razana, banji kome ba dan ynz ba da bane da zanyi kuka.


Kayana nashiga haɗawa ina gamawa na kallesu nace.
"Ko yau nabar aiki ina da kuɗin da ya isheni nayi kasuwanci ba tare da na damu da abinda gwanati zata bani ba, kuma da kuke cewa budurwa zuciya gare ni eh nagode wannan ba dani kukayi ba da ubangiji kuke, wallahi yau nace a koreku a aiki toh ko karenku bazai samu aiki balle ku kuje kuji da kanku mana, daɗin abin nayi auren kuma na shiga inda baku taɓa tunanin zuwa ba na mallaki abinda baku da shi, kuyi asarar rayuwa kukan."


Ina gama faɗar haka nayi ficewata, sayau naji zuciyata, koda na dawo gida tsabga gabana ta isheni, wani abinda ya dameni yawwan jin bukatar Sadeeq bansan mike damuna ba da zaran naci na koshi toh fa nan zanji idan ba Oga Sadeeq bana jin kome a jikina idan nayi barci a haka kuwa toh dole ne idan na farka nayi wanka, dan mafarkinshi nake,

Da naje asibiti na faɗawa dr Zakariya murmushi yayi ya rubuta min magani tare da bani shawaran na koma ɗakina jinshi kawai nayi na fito....


A hankali kome ya tafi kamar ban taɓa fuskantar wani matsala ba, ga cikina ya shiga wata takwas yayi wani irin girma na ban mamaki, dan dole na ɗauki hutu a gurin aiki, sabida girmsn cikin da yanda kowa ke maganar cikin Baffa ya hanani zuwa ko ina sai awo.

***
Koda ya faɗi ya tashi dakyar amna dole ya dawo gida Sadeeq farine amma wannan ciwon yasashi yin wani irin fari fat kamar babu jini a jikinshi, kowa ya tambayeshi meke damunshi sai yace ba kome,


A haka ys cigaba da jinya, baya shan magani toh yaki zuwa asibiti, ciwo biyu a tare da shi ba'a san ɗaya ba amma tabbas akwai ciwon zuciya. Dan damuws tayi mishi katutu amms yaki faɗawa kowa Babu abokin shawara babu Matarshi sai ya zauna yasa Abul a gaba suyita kuka, yakancewa yaron.
"Abul na rabaka da Adda Amra ko gashi nima mutuwa zanyi bansan mike damuna ba kaga yanda jini yake fito min a hanci da kunne, ai kasan bazan tashi bs, coffe ɗin da tina ta kawo ya kurɓa aikuwa ya fara tari sosai wanda yajanyo fitar jini a hanci da kunne da baki sosai yake tarin me matukar razanarwa.

***
Ina kwance gurin karfe huɗu nadare, tafiya nake a cikin wani lambu amma ina jin kukan Sadeeq a hankali na isa inda kukan yake, zuwa nayi na ganshi da wasu mutane, sun kewayeshi kowanne da mugayen makami, amma wanda naga fuskarshi Adnan ne, ya ɗauki wuka yana ta soka mishi, da gudu na isa gurin na hankaɗa adnan ya faɗa wuta, na ɗaga Sadeeq muka fara gudu ga ciki ga sadeeq da yasake jikinshi na rasa yanda zanyi ga mutanen suna gab da cin mana, Faran tantabara ce tayi sama damu, sai da mukayi dogon tafiya ta kawomu wani lardi nada ban kwantar dashi mukayi tantabara tana zubda kwalla jijjigashi nayi amma ins baya ko motsin kirki sai kasaka ido xaka ga yana numfashi, muns cikin haka sai ga Adnan yaxo da gudu kamar walkiya ya jefa Sadeeq arami yasa kasa ya rufe tare da wasu mutane dariyarsu ce tafarka dani a firgice. Na tashi ina addu'a ganin Imran yasani dadɗa tsorata kuka yake har kwalla na sauka a jikinshi yace.
"Kece kawai zaki iya tayashi saura kiris akarasa shi sun biyo shi sunci nasara da najikinshi Amratu Sadeeq ke yake bukata ko ya tashi ko ya mutu Yaranki sune abar tausayi shine garkuwa Iyayenshi, ke kuma kece garkuwarshi Amratu kina da karfin zati ki koma ga Abubakar kamar ynd kikayi mafarkin nan haka nima nayi don Allah kodan albarkacin cikin ki je ga Sadeeq."


Yana gama faɗar haka ya ɓace...

Jikina na rawa nayi alola nazo na fara gabatar da nafillah.

****
Tun yanayi da karfinshi har karfinshi ya kare, sai dai motsin da yake haka Abul ya kwana a jikinshi, abinka da yaro dan yayi kuka ya gaji, da safe Meemah bata ga Abul ba gashi lokacin karyawa yayi kowa na zaune banda inna wuro da take ta safa da marwa tace.
"Kee hadiza ban ga Buba ba banga ɗanshi ba."

"Eh inna kinsan baya son zama cikin mutane ynx har ya koyawa yaron ma." bata gama maganar ba inna wuro tayi can kuryan gidan inda ɗakin Sadeeq yake kukan Abul ya shaida mata ba lafiya da sauri ta isa ɗakin tana tura kofar taga yaron yana kuka yana kiran "Amama Amama."

Sai jijjigashi yake ko motsawa bayayi, ganin jini ya ɓata ko ina na ɗakin inna wuro ta fasa ihu......



*_Gaskiya gobe ina da zuwa asibiti ganin likita da kuma awo toh bansan yaushe zan dawo ba dan haka bazaku ga Updater ba sai Jibi Insha Allah ayi hakuri*
🌺🌷🌷
*_DA CIWO A RAYUWATA_*
🌹🌸🌸

Na
Mai_Dambu
Wattpad:Mai_Dambu...
*Ruɗani*

*Page I=INNA WURO*


Cikin mugun tashin hankali Inna wuro tayi waje tana salati da sallame.
Mikewa Daddy yai shida Meemah suka nufeta, a birkice tace.
" Abubakar zai mutu!!!"

Da sauri suka wucce ɗakinsa anan suka sameshi ganin haka Ammih da Adil suka biyosu, cikin firgice Ammih ta ɗauki Abul, Daddy da Adil suka fita da Sadeeq zuwa gurin mota, cikin gaggawa aka kira motar asibiti cikin abinda baifi minti goma ba motar iso, nan suka ɗauke zuwa asibiti komawa ɗakinshi meemah tayi tana kallon hotunan da ya zana min, cup ɗin coffee ɗin da yasha tabi da ido ɗauka tayi tana kallon kafin tafito zuwa kitchen, tana shiga dake shiga bazata tayi a firgice Tina ta sake, ledar garin coffee ɗin a kasa ya zuɓe.

Binta tayi da kallon zargi amma dake tuna halin da Sadeeq yake ciki baisa tabi takanta ba Ajiye cup ɗin tayi tafita.

Sauke ajiyar zuciya tina tayi ta haɗa kayan ta ɓoye a wani loca.

Da sauri ta haɗa abinda zata haɗa tabar gidan, kafin wani abu ya taso.

***
Koda aka suka isa asibitin take aka fara kaikawo akanshi cikin wani irin tashin hankali dan basu taɓs cikin karo da irin wannan ciwon ba asalima, anfi samunshi daga Yanki Asia sosai suka dukufa ceto rayuwarshi inda aka shiga gwaje gwaje, daga ciki kuwa har da gwajin Jini fitsarinshi da bayan garinshi, a gigice Dr Aryan Aslam Khan, ya fito daga ɗakin lab ɗin ya shiga idan Sadeeq yake, ya mikawa saura likitotin sakamakon.


Cikin gaggawa suka fito inda sukawa Meemah magana wacce itama consultant ce a asibitin.

Da ita aka shiga meeting ɗin bayan sun zauna Dr Mark Paul ya mike cikin harshen turanci yace.
"Ina baku hakuri da kiran gaggawa da nayi muku haka ya farune sakamakon case ɗin da aka kawo na mara lafiya! Numfashi ya sauke sannan ya cigaba da cewa.
"Kimani karni biyu xuwa ynx ana haramta amfani da guba dan shayar da wani indai bashi ya shayar da kanshi ba Dr Hadiza mara lafiyarki da kika turo, mun gano ya jima yana shan guba wanda ya haifar mashi da ciwo tari dan gubar ta taɓa huhunshi sai kuma kodarshi wanda itama saura kiris ta taɓa, dan gubar tana lalata brain da huhu, hanta koda. Mafi hatsarin wannan gubar shine yanda take lalata brain ɗin mutu inda zaki ga mutum na zubda jini ta hanci, yanzu abinda muke so a kawo mana asalin gubar da ake sarafa mishi, haka ne kaɗai zamu san ta inda zamu taimaka mishi."

Da gudu meemah tabar ɗakin taron rike da bakinta kuka take sonyi amma tsoro da firgita yasa ta rufe tana fita tayi waje inda motarsu take maza tayi ta faɗa cikin taja da mugun gudu.
Tana anbatar Adnan da sunanshi na asali wato usman, tana shiga gidan ko parking cikin rashin nutsuwa ta faɗa gidan "Tinaaaaa"

Ta kwalla mata kira amma babu alamarta kitchen ɗin ta shiga ta fara bincike har ta samo ledar garin coffee ɗin ta ɗaga tana juyawa, a hankali hawaye suka shiga zubo mata,

Ta juya da niyyar fita Adnan ya fesa mata wani farin hoda a fuska, zata zuɓe ya tareta cikin muryan bugaggu tace.
"Usman mi mukayi maka haka muka amshi wannar sakamakon." Zaunar da ita yayi ya jinginata da jikin firij ya mike ya ɗauko ruwa,

Ya mika mata dakyar tasha sannan ya xauna yana kallonta sosai kafin yace.
"Zaki ɗauki gubar kikai asibiti sannan kuma za'a tsananta bincike toh Meemah baki tunanin Rayuwar Sadeeq ɗin da Yaronshin ne? Zan kyaleshi a haka amma sai kinja bakinki kinyi shiru in ba haka ba zan kashe kowa dan na mallaki amratu, akanta na fara so dan haka babu wanda ya isa rabani da ita."

B'alle rigarshi yayi ya nuna mata katon rubutun sunana daka zana mishi fatar daidai kirjinshi yace.
"Wallahi billahil azim zan kashe Sadeeq har ɗanshi dama aiki aka bani akanshi salin alim ki zuba min ido in ba haka ba toh kome ya biyo baya zaki sami gawar ɗanki da jikanki, ni uwar nake so."

Yana gama faɗar haka ya mike yabar gidan kukane ya kwace mata cikin tashin hankali kwanciya tayi a gurin sabida barci da ya rufeta.

Hankalin Inna wuro da Daddy duk ya tashi haka suka cigaba da zuba ido sai bayan awa biyu sai gata da kunshin ledar nan aka shiga binciken yanda za'a sami makarin, dan sun ga kasar India ne suke samar da maganin, kuɗi Daddy Ya zuba aka tasa Dr Aryan Aslam Khan ya tafi niman makarin sai dai an saka mishi ruwa da alluran da zai rage mashi karfin gubar.


A yanda aka tura Dr Aryan sati biyu zaiyi sai gashi babu shi babu labarinshi,

Ranar da yacika kwana ashirin da tafiya sai ga labarin an tsinci gawarshi a garin Maharachira.

Abin ya kaɗa kowa Meemah kam batayi mamaki ba dan tasan Adnan ne zai aikata haka.


Hankalin likitotin yayi masifar tashi kaii har da iyayenshi, kwana biyu tsakani aka fitar dashi zuwa indian ba tare da sanin kowa ba sai Meemah da Dr Paul,

Sai Inna wuro suka tafi can....

***
Hankalina duk ya tashi narasa wanda zan faɗawa dan dole nayi shiru ina zubawa sarautar Allah ido, bayan sati uku natashi da nakuɗa tun ina ɓoyewa har yaci karfina,
Dakyar na fito nabuga ɗakin Nenne tana fitowa taje ta tashi Baffa,
Muka tafi asibiti wanda nasha gwagwarmayyan dan tun uku nake abu ɗaya har goma nasafe, kafin Allah ya taimaka na sauka lafiya inda nasami yarana biyu mata, ajiyar zuciya na sauke lokacin da takarshen ta diro, kuma dukda mahaifarsu,

Gyarani akayi sannan aka koma kan yaran aka kintsa min su,

Sai da mukayi hutun awa shida aka sallame mu, ina dawowa nashiga niman layin Sadeeq baya shiga gashi tunda Imran ya faɗa min halin da yake ciki duk nashiga damuwa,

Email ɗinshi na turawa sakon haihuwar da kuma hotunan yaran,

Ban damu da jiran reply ba dan ina tunanin ko jikine yaki mishi, bayan ana uku sai ga sakon "toh gani nan zuwa."
Sai na tura mishi da tambayar.
"Kasami lafiya ne aka ce min baka da lafiya"

Sai ga wani sakon ya shigo.
"Waya faɗa miki bani da lafiya."

Shiru nayi kafin nace.
"Abokinka mana Imran"

Shiru yayi na wani lokaci kafin yace.
"Ok ya kyauta amma naji sauki zan zo a maida aurenmu kinji."

Duk sai na rasa tacewa toh knn sai an sake ɗaura wani auren knn eh haka ne faɗa tunda bai mai dani ba har na haihu, ajiyar zuciya na sauke kafin nace.
"Allah ya tabbatar da alkhairi."

Daga haka nayi ofline, tabbas indan nace bana son Abubakar nayi karya dan wani irin so nake mishi me tsarga jinin jikina, aduk lokacin da zan tuna shi sai naji kamar zuciyata zata buga sabida tsananin kaunar da nake mishi.

After six days sai ga Sadeeq a ɗakin baki aka saukeshi nan na kai mishi yaran ya kallesu cikin murmushi yace.
"Nayi farin cikin ganinsu wani suna kike so a saka musu."..

Dake a kujera nake zaune shi kuma yana bakin gadon, nace.
"Duk sunan da kayi ra'ayi."

Kallonshi nayi na wasu lokuta kafin na kauda kaina nace.
"Ai bani da zafi wannan ya wucce naka, kasamu su wanda kaga ya dace."

Daukar Babban yayi ya mika min yace.
"Saka mata sunan Meemah, wannan kuma a saka mata sunan Inna"

A hankali nayi musu huɗuba amma banji daɗin haka ba naso dashi yayiwa Yaranshi amma babu yanda na iya, mikewa nayi zan fita na bashi guri ya ci abinci amna sai naga ya mike, yazo har gabana ya amshi Meemah, ya kwantar da ita sannan ya jingina ni da bango, tare da sumbatar wuyana.

Tureshi nayi na harareshi cikin tsiwa nace.
"Kana son kasancewa dani ka yanke igiyar aurenka dan renin hankali baka taɓa kirana ba amna dake ynx ka ɗibo damuwarka,zaka sauke min."0

Shiru yayi yana kallona dariya yayi wanda nasan ba ɗabi'ar sadeeq bane dashine murmushi zayi ya ɗaga min kafaɗa da nina sanin wannan kuma magana na gaskiya sam bana jin yanda nake ji idan muna tare da Sadeeq,

Amma sai nabar haka da kodan saɓanin da muka samu bama tare ne oho,

Daukar yarana nayi muka fita, naje na zauna ina nazarin Sadeeq, gani nake sabonta min shi akayi, ba Sadeeq ɗina da nasani bane, haka na share zance.

Koda na faɗa sunan da yayiwa yaranshi sai kowa ya hau murna, washi gari bayan an ɗara suna aka maida Aurena da Abubukar Mustapha lamiɗo akan sadakinshi nairai dubu ɗari biyu cif, anyi taro kowa ya watsa da dare ya turo Mubarak na kaimishi yaran na shirya tsaf bayan nayi wanka da turare sabida karnin nono,

Muka nufi ɗakin baki, ina shiga na sameshi da riga da wando na bacci ruwan madara, kallonshi nayi na gaza hakuri nace.
"Abban Abul wani irin ciwo kayi ne naga ka rame haka, kaman ba kaiba."..

Kwantar da Ihsan yayi sannan ya amshi inteesar, ina tsaye fincikoni yayi na faɗo kanshi, maza nayi na mike, yayi juyin duniyan nazo mukwana naki sam bana son haka, karshe da masifa nabar ɗakin.

Washi gari daman ya faɗa min zamu koma tsaf nazo nasame Aunty Rahma sun kintsa mans kayanmu kallona sukayi ina yaran suka ce min,..

Nace.
"Suna gurinshi'
Kwanciyana na gyara suka fara min biki ban kulasu ba sam zuciyata ba daɗi,.

Har kusan

Please Login or Register in order to submit comment