Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

muni ne ina cikin mafarkin mun faɗa shafin ma'aurata saura kiris mu zama daya sai ji nayi ana shafa min magani a jikina ɓat na nemi mijin mafsrkina da yarana, ina buɗe ido naga sadeeq.

  Bansan lokacin da na fashe da kuka ba, ina ture hannunshi a jikina, ya shigo ɗakin da niyyar ajiye min xuma wanda aka zuba, magani  a ciki sai ya samu ina tura kirjina tare da kamkame jikina, cikin wani irin yanayi shine ya fara shafa min magani dama malamin da yazo dubani ya faɗa masa dole yasaka ido akaina, gefe ɗaya ma abokinshi Imran yana kokarin haɗa min magugguna ina sha ina shafawa ga na wanka nidai nazama Allah sarki.

            Satina uku akace za'a mai dani gidana aikuwa kuka nasaka musu bori,  anyi fama dani kafin na amince dan sai da Baffa ya nuna baccin ranshi na dawo gidan ynx babu tsiwa dan bana kaunar masa magana, dan ina kallonshi kaman yaso kanshi gurin rabani da farin cikina....

#Fiction
#Spirits
#Jinn
#Amsad......Follower Mai_Damb
🌺🌷🌷
*_DA CIWO A RAYUWATA_*
                                  🌹🌸🌸

   Na
  Mai_Dambu
   Wattpad:Mai_Dambu

         Da sunan Allah Mai Rahama Mai Jinkai

     *Nagode masu comments Yaseen masu min thnks ɗin nan kuwa da sticks ban gane muku ba*😛🤒🥰


Page F.
      Sam shi bai damu da sauyin da yaga nayi ba sabida ba damuwarsa bace abinda yasani shine nasha magani, kwana na biyu da dawowa yasani agaba nasha magani amma naki, ko kallonshi balle yasa ran zan sha aikina nake a computer tunda ba makaranta nake zuwa ba,
      Da yagaji da ganin kayan haushi mikewa yayi yazo ya murɗeni har hannunshi na gogan kirjina, ya cusa min magani na shanye sannan ya sake ni ya mika min nashafawa a jiki naki karɓa, mikewa yayi ya shiga kwaɓemin kayan jikina dama ban saka bra ba sai gani tunbur🙈 haka ya gama shafa min magani, cike da masifa nace masa.
"Mara kunya wanda bai san darajar mace ba ince dan ka kalleni ka kirkiro shafa min magani a jikina gashi ba kallo ba har taɓa min boons kanayi wanda bai san ciwon kanshi ba, wawa kawa...."

            Wallahi wani irin mari naji saukarsaa fuskana cike da bacin rai ya matsa min boons ɗin yace.
"Dubesu fa ko cika min hannu basuyi ba har ana cewa sabida su nake kula da jinyarki mi zanyi da kananun nonuwarki wanda ko tokareni min kirji basu isa yi ba, kika kara zagi sai na yagaki gida biyu naga abinda kike takama dashi wacce bata san darajar aurenta ba."

         Tashi yayi ya barni ina kuka sosai fa, kuma naji haushin maganar da yafaɗa min.

          Tun danaji mari sai nake gudun abinda zai haɗani dashi har ya mareni,
          
      Kwatsam wata monday yace na fara zuwa aiki kaman zanyi ihu dan murna haka na fara zuwa aiki abokan aikina maza da mata suka shiga zuwa suna tayani murna.

            Wasu ma yan gulma zuwa suke su ganni, ko a jikina class ɗina naje na gabatar da abinda zan musu sannan na koma office nasaka kai zan shiga naji hiran yan office ɗinmu suna cewa
"Eh ina faɗa muku wanda ya aureta yarone sosai , kuma naji ance baya sonta kawai dai cusa masa ita akayi wallahi dakyar H.O.D yasha dan aljanu take dasu saura kiris sukashe shi."

           Cikin tashin hankali najuya xan bar gurin kawai muka cikaro dashi yazo ɗauka na, dan jimawa zanyi a makarantar ba nuna min gurin mota yayi ba musu na wucce shiga yayi cikin officer ɗin da sallama suka gaisa, sannan ya isa table ɗina ya ɗauki kayana ya zuba a jaka, duk sunyi tsuru tsuru, dakyar wanda yake basu labarin yace.
"Malam lafiya kayan dr Amrah ne kuma ka shigo baka nemi izin kowa ba kana tattara kayan."

         Wani shegen murmushi yayi wanda suka karawa fuskashi haiba da zatti haɗi da kwarjini da muryanshi irinta yara yace.
"Kayan Mata ta nake ɗiba ko akwai matsala ne malam.kaji da rayuwarka karka shiga rayuwar wata yau ya zama na karshe da zanji kana maganar Mata ta idan na kama ka, next hmm zaka iya rasa inda zaka ci abinci kana masinja amma zuciyarka cike ɗa kyashi da hassada,"

    Yana gama faɗan haka ya kwashi kayan yafito ya zuba a bayan mota, ina zaune a gaba kuka nake  kaman idanuna zasu fita taɓe baki yayi dan bai ga abin kuka ba, da zanyiwa kuka.

        Tun daga ranar yan officer ɗinmu suka shiga hankalinsu suna ganinmu zasu nutsu yanzun ya shiga yi min hidima sosai amma a gida kuwa kaman zamu cinye juna dan masifa, wani lokacin idan ina da class 8 - 10/11-1 abinci kake kawo min,  har cikin aji ya katse min karatu yasani a gaba har cikin motarshi sai ya kunna Ac ni kuma, haka ba karamin haushi yake bani ba, dan ko kallon banza nayi masa da murmushi zai mayar min.

        Ranar da nagaji tun amota nake masifa ya dameni sai gulmata ake kowa har son gani na ake suna cewa mijina yarone amma sai rawan kai yake akaina.

       Ina gama fadar haka bai kalle ni ba ya cigaba da tuki, can nace.
"Nidai daga yau na yafe,"
     Dariya yayi kafin nan yace.
"Allah ya baki baiwar rashin kunya da zagi amma baki iya kwatar kanki a gaban mutane ba nonsense kawai."

       "Nice mara hankali." na tambayeshi a harzuke.
      Murmushi yayi sannan ya ɗaga min kafaɗa alamun Eh.

        Aikuwa na zauna nayita masifa, *A ranshi cewa yayi abinda ta iya kenan* har muka isa gida ban daina ba sai sa yaranshi suka zo nayi shiru na shige dan haushi ko girki banyi ba,

  Washi gari da zamu fito ya kalle ni yace.
"Saura muje wata mace ta faɗa miki magana kiyi min shiru Wallahi sai na baki mamaki."

     Koda muka isa department ɗinmu shi ya ɗauka min kayana ina gaba yana take min baya sai magana yake faɗa min sabida kayan da nasaka. Yake nake kawai dan wani zai zata hiran luv ake nan kuwwa magana yake yaɓamin.

         Muna shiga matan gurin suka shiga cewa.
"Eyye Dr kina sha'aninki a tukoki akawoki ɗauko kayan sai ya miki kina shagali fa."

             Satar kallonshi nayi naga shima kallona yake da wutsiyar ido wani kwarin gwiwa naji nasake murmushi kafin nace.
"Eh mana ba dole ba nayi sha'anina Allah ya bani mijin nunawa sa'a ga so ga kulawa, uwa uba hidima yake min kamar dan ni akayi shi, toh duk cikinku wacece ta taki sa'ar dana taka ne, abinfa rabone wai ɗan fari ya koma,"

        Juyawa nayi gurin table ɗina sai jin bakinshi nayi a goshina ya sumbace ni sannan yace.
"Gimbiyata sarauniyata ke ɗaya kike mulkar birnin zuciyata sai nazo ɗaukarki, faɗa min wani abu mana."

            Duk sai na diriri ce murmushi nayi sannan nace.
"Adawo lafiya Half."

   Fita yayi tun daga ranar nasami nutsuwa basu sake min maganar banza ba,

              Nafito daga class kenan na gaji bacci nake ji mata nagani cike a office ɗinmu nan na kutsa kai na shiga, ashe me kayan matace sister Fannah gaisawa mukayi cikin mutunci na nime kujera n zauna na kifa kaina tuni bacci yayi gaba dani, taɓa table ɗin Fannah tayi na farka cikin raha tace.
"Sai kiyi aure ba sanarwa toh ga kayan gyaran gado nan ko zaki ɗiba ga tsumin karya dawo gumbar saki kishiya kuka, turaren Yar gata, ga kuma bani ba kishiya , ga gida ko mota, ga zumar goran tula sa mai gida ihu kenan yashiga ya jiki kamar korama tsabar ni'ima ga daɗin harka, ga matsin gigita mai gida wannan kika saka Hq ai kuka zaki ji yallaɓai na rusawa."

   Tarkace gasu nan kaman hauka, dariya nayi kawai na amshi zumar goran tula ina kallonshi buɗe wani gora tayi ta zuba min wai na gwada naji hmmm karɓa nayi nasha, yayi min daɗi tamvayar kuɗin nayi tace..
"5k take sayrwa."

         Karɓan nomber acc ɗinta nayi na tura mata wallahi nasaya ne kawai sabida yanda abokan aikina suke ta cusa min baki amna sam ban yarda da irin maganin nan ba, haka tayi ciniki a office dinmu dan har bashi tana badawa,

           Lokacin zuwansa nayi sai gashi yazo kayana na haɗa  sannan nayi musu sallama muka fito bayana suka kafa gulma wai da alamun Sadeeq jarababbe ne gashi yana manne dani ba mamaki nima hakan ce,

                Tun a mota naji marana na sukana, can kaman ya kulle sai can ya sake sai naji kaman zuban abune a kasana dan haka muna isa falo na,zube akan kujera tuni jikina ya mutu dakyar na shige ɗakina nayi wanka na duba na zata circle ɗina ne sai ruwa kawai, ban ɗauka wani abu bane ina fitowa wanka nabi gado ina lumshe idanuna,

           Wani irin ciwon mara da bayane ya rufe ni haka nayita juyu dakyar nayi sallah na kwanta,  har dare ban fito ba ganin haka sai gashi ya tawo gurina,  yana shigowa yaga halin da nake ciki take ya ruɗe ya shiga niman magani na, yana fitowa Imran yayi masa sallama, yana murmushi yace.
"Bawan Allah ba ciwonta bane, kawai kaje ku raya daren shine gaskiya dan tasha wani abune ya dameta."

Kallon banza yayi masa sannan yace.
"Taɓ Allah ya tsare ni da yin aikin danasani kawai faɗa min abinda zan bata."
         "Toh ba damuwa kasami jar kanwa ka saka a ruwan ɗumi kaba tasha sai kuma."

     Shiru yayi ya zuba masa ido yana nazarin abinda zai faɗa masa.
"Sai me kuma?"
           Ta tambayeshi, cikin inda inda yace.
"Hmm dama zaka je ne ka tamvayeta inda ke mata ciwo sai kana matsawa Insha Allah zata ji sauki."

      Dakinshi ya shiga yaje ya duba jarkanwa yazo ya jika sai gashi ya shigo tallafe min kai yayi ya bani nasha, sannan ya jingina ni yace min..
"Sannu ko! Ina ke miki ciwo."
   Cizon lips ɗina nayi da hakori na nuna masa marana, kaman wanda na aikeshi kawai sai jin hannunshi nayi yana matsa min gurin yana min tausar gurin katuwar ajiyar zuciya na sauke, a hankali yake murza min gurin, can bayan wani lokaci sai naji saukar abu, a jikina,  ajiyar zuciya na sauke tare da lumshe idanuna kallona yayi, sannan yace.
"Sannu ya kike jin gurin har ynx akwai ciwo ne."..

      Hararanshi nayi cikn borin kunya nace..
"Ka buɗe ni ka duba mana, idan ka damu."

     Aikuwa cike da ɗanye kai ya saka hannunshi tsakanin cinyoyina wai zai buɗe ni, ai bansan lokacin da na hantsilo ba, naga rashin kai da gaske kuma dubani zaiyi dan bai da kunya mikewa nayi naje nayi wanka na haɗa da alola nafito  sallar la'asar na gabatar lokacin yar yayi waje abinshi,

                Bai ce min kome ba sai ranar ina shirin ɗaura nikkaf ɗina yace.
"Wallahi kika kuskura kika shawo wata damu ki nemi mi sauke miki ban da ɗangidan mustapha Lamiɗo."

      Shiru nayi na wucce abuna har  offices ya rakani,.
       
                ***

       Watanmu uku cur da aure ina kwance sai gashi ya shigi zama akan stool yace.
"Zanyi baki Kanen Mamana da kanen Babana sai matar kawuna wacce zan auri yarta nan da wata biyu zuwa Uku, ina bukatar a mutuntasu ai ashe na manta da matar karfe kakata wacce ta haifi  Mamana Hajiyata Innawuro."

        Shiru nayi na kyaleshi, kwana uku tsakani yasani na kwashe komi nawa nakai dakinshi rana na huɗu sai gasu nan, sun iso ranar tare muka wuni a kicin sai karfe huɗu muka fito amma munyi faɗa yafi sau goma har aka gama girkin.......
#Fiction
#Spirits
#Jinn
#Amsad......Follower Mai_Dambu
🌺🌷🌷
*_DA CIWO A RAYUWATA_*
                                  🌹🌸🌸

   Na
  Mai_Dambu
   Wattpad:Mai_Dambu

         Da sunan Allah Mai Rahama Mai Jinkai

*Dominki Maman Muhibba da Maman Surayya Nijar ga Page din nakune*🥰😘



Page.G
Da misalin karfe biyar suka iso gidan kusan mota uku, sai kuma hilux guda ɗaya wanda ke shake da kwatuna har takwas.
Manyan mata bakwai ne da madaidaita masu yara uku, sai Yan mata su uku,

Da ina mita akan yace ayi abinci dayawa sai dai ganin bakin yasa jikina sanyi, tun da suka shigo baka jin kome sai fulatanci kayan shan ruwa nashiga jera musu kafin ya taimaka min muka fara fito da abinci, wata yarinya mai shegen rawan kai a cikin yan mata ta mike tsagal, ta amshi filet ɗin hannunshi bata bar kitchen ɗin ba tasa min a kasa baki ɗaya suka tarwatse a gurin, ko a jikinta sai ma ɓata rai da tayi lokacin da wata mata ta mike da sauri tana tambayarta "Nana lafiya kuwa da fatan baki ji ciwo ba ko waye ya baki filet mai nauyi haka, nifa bama son mugunta ya daga zuwan yarinya za'a bata filet haka ko so ake a kasara min ita kafin ta shigo gidan."

Ina kitchen ina sake fitar da wasu dish ɗin, fitowa yayi daga kitchen ɗin ya zuba musu ido cikin inda inda Nana tace.
"Kai Mama nifa na amsa a hannun Ya Sadeeq kuma bansan da nauyi bane."

Kauda kanshi yayi ya nuna mata parka da broom yace.
"Ga broom nan ɗauka ki share min gurin kafin nayi wasan kura dake wani munafikine ya turoki."

Tsumo tsumo sukayi daga ita har uwarta broom ɗin ta ɗauka ta shiga tattara fassasun filet ɗin shi kuma yq sako uwarta a gaba,

Nidai nawa ido ina gama fito ɗa filet ɗin na wanke na kawo musu ina zuwa naji sun kaurr hayani da fillanci mikewa nayi zan koma kitchen ɗin, fuu nazo wuccewa aikuwa ta bangajeni ta wucce saura kaɗan na faɗi kasa cikin zafin nama ya tare ni dama yana zaune a hannun kujera.

"Keeeeee" Ya buga mata tsawa a tsorace ta mike jikinta na rawa, ɗaya daga cikin matan falon ta juya cikin sanyin murya tace.
"Amrahtu da fatan babu abinda ya sameki."

Gyaɗa mata kai nayi na wucce.
Zama nayi abuna a kitchen ɗin, ina gyara inda ta watsar min da fasasson kwalabe.
Shigowa yayi yaga yanda na sunkuyar da kaina, fita yayi abinshi bai sake shigowa ba har sai da ya turo ɗaya daga cikin yan matan mai suna Zahra taxo ta kirani,

Ina shiga falon na sami guri na zauna a kafet, gaisawa muka sakeyi sannan ys nuna min Yar tsohuwar cikinsu yace.
"Wannan itace kakata Ina wuro,"
Sai na kusa da ita ya nuna min yace.
"Wannan da wanca da me yaron can kannen Mamana ne su Adda Kuluwa sai Adda Mairo, ga Kuma Adda Sadiya, ita adda kuluwa manaje ce a Cbn na yola. Adda mairo kuma Nurse, Adda Sadiya Ita malama ce a state poly."

Daya gefen ya nuna min yace.
"Kinga wayanan kanen babana ne su, Goggo Adama, Goggo safiya, Sai goggo khaira'atu."

Gyaɗa kaina nayi sannan ya nuna min mamar Nana yace.
"Wannan itace Yadiko salma matar kanin Babana ne ita, yarta ce zan aura nan da wata biyu, Nana Khadija kinganta ko"

Cigaba yayi da cewa.
"Zahra da Shukra yaran Adda kuluwa ne. Akwai wasu dan sai kinje can zaki ganewa idanunki amma kinga wancan tsohuwar matar knn karfen ba katakon ba,"

Gabatar dani yayi a gurin iyayenshi, sannan ita Adda Kuluwa ta kalle ni cikin sakin fuska tace.
"Amrahtu matakin karatunki a ina kika tsaya,"

Murmushi nayi kaina a sunkuye ina wasa da yatsun xanyi magana Nana tayi tsagal ta shiga maganar da cewa.
"Mommyn Zahra ai bazai wucce N.C.E ba dan naji ance yan bauchi sunfiyi shi ko Mamah, shi yasa nake kokarin haɗa mai da hankali na haɗa degree na. Kafin nima na zama momis."

Ta fada da rashin kunya dariya uwarta tayi kafin tace.
"Eh wallahi Nanah na, ai N.C.E na y'ayan talakawa ne, ke kinfi karfin n.c.e sai degree a Ati."
Dake sunsan halin Adda Kuluwa ba tada hakuri tuni ta balbaleta da masifa tace.
"Na tambayeki ne toh bana son rashin ɗa'a."
Jikinta a sanyayye ta gyaɗa kanta mai da idanunsu kaina sukayi suna jiran mi zance a hankali nace.
"Nayi Degree na a A.t.b.u, haɗa Masters ɗina a Toronto Canada, sannan na sake komawa nayi Phd na yanzun haka ina koyarwa ne a A.t.b.u, ina koyarwa a course ɗin Microbiology, ina koyar da masu haɗa degree da Master."

Shiru falon yayi ita nanan sai kallona take cike da mamaki Adda mairo tayi murmushi tace.
"Yarona ashe da Dr kake zaune shine dan wulakanci kace min ko sakandiri bata haɗa, Allah ya taimaka ya bada sa'a Amrahtu."

Murmushi nayi aikuwa zahra tace.
"Amrah amma kin girme Ya sadeeq ko dan naga shi tunda ya gama degree ɗin yaki ya maida hankali ya koma master don Allah ki taimaka kiyi ta masa nasiha ko zaiji."

Cikin harshen faransance Adda kuluwa ta daka mata ranta a ɓace mikewa tayi tace.
"Amrah nuna min ɗaki dan matukar na cigaba da zama hannuna zai kai duka."

Mikewa nayi na kaitq ɗakin sannan na juyo zanfito riko hannuna tayi cikin damuwa tace.
"Kiyi hakuri da Family lamiɗo kwana biyu zamuyi mu koma kinji ko."

Karamin murmishi nayi sannan nace.
"Ba damuwa wallahi."
"Yawwa naji kun kusan komawa can ko, dan bikinshi da Nana ya kusa."

Gyaɗa mata kai nayi cikin jin kunya.
Sannan nabar mata ɗakin kwanikan abincin da suka ci na kwashe na kai kitchen shi ya shiga ya fara wankewa kafin na shigo.

Juya maganar komawarmu yola yayi matukar damuna kuma daman ya faɗa min lokacin da yaga zaman kaɗaici ya isheni naje masa da maganar komawa bakin aikina, sai kada kai yace.
"Zaki koma aiki abisa sharaɗi nan da wani lokaci zamu koma Yola zan nima miki sauyin gurin aiki, sai kuma abu na gama bazan yarda kina fita da karamin hijab ba, sai babba har da nikkaf idan bai miki ba ga takarda nan ki ajiyr musu aikinsu ba dole."

Shiru nayi kaina a sunkuye kwalla nazuba daga idanuna na gyaɗa kaina bakina na rawa nace.
"Na amince amma ni bazan iya tafiya nabar Iyayena ba don Allah ka sauwake min mana."

Dago kai yayi ya kalle ni kafin yace.
"Zanyi tunanin haka "

Tun daga ranar bai sake min magana ba, jin komawar mu yola yasa natuna da maganar.

Ina gama shigowa da kayan na fara tayashi muna wanke wanke, jin tsaki mukayi daga bayanmu na juya nanah ce tsirta min yawu tayi sai akan idanunshi, a guje ta fita bai ce min kome ba muka gama aikin na ɗaura girkin dare tare muka gama,

Bayan sallar isha duk sun gama cin abinci na tattara kayan na kai kicin ina wankewa, duk sauran mutane sunci abinci Nana ita wai bazata ci abincin ba indomie zata ci a dafa mata.
Wani irin kallo nabita dashi, ina cikin kicin ɗin sake daga murya tayi cikin gadara tace.
"Ke bazaki dafa min indomie bane."

"Bazata girka ba idan kina son cin ki zo kirakani" ya faɗa mata, sai a lokacin na lura da yarinyar daga ita sai wani karamin riga dakyar ya sauka maranta sai dogon wando pencil
Daga kirjin kuwa kamar zasu fashe kauda kaina nayi sabida mamakin rashin kunyarta ke bani.

Fita sukayi daga gidan, sai da sukayi nisa ya kashe motar ya fincikota ya kifa mata mari guda uku masu kyau yace.
"Mari na farko fasa min kayan matata da kikayi, mari na biyu tsirta mata yawu da kika , na uku rashin kunyar d kika mata wallahi idan baki fita idona ba zan iya fasa aurenki naga Ubanda zai min magana."

Kuka ta fashe dashi ya buga mata tsawa haɗiye kukan tayi suka je har bauchi club suka sayo nama, sannan suka biya sky crown suka sayi ice cream suka juyo gida.

Nikan nagaji dakyar nake iya hira can na tuna inada aiki a computer shima ɗin ganin Adda Kuluwa danata ne tana aiki yasa na shige ɗaki nayi wanka na ɗauko na fara aikima,


Can sai gashi ya shigo Allah ƴasa da hijab a jikina da haka,zai gan ni dan towel ne a ɗaure a kirjina, ban ɗaki ya shiga nima nasaka wata doguwar riga nafito daga ɗakin da systerm ɗina na maida hankali akan aikina munayi ana hira har shima yafito, kura min ido yayi sannan yayi ajiyar zuciya a ɓoye yana me taɓe baki a ranshi yace.
*Na cuci kaina da na auro me matattace idanu duba fa da glss take ganin rubutu.*

Hmm Sadeeq knn.

Karfe goma muka watsa nima ɗakinnmu na shiga na hau gadonshi nayi ɗare ɗare ina maida numfashi yana shigowa yayi tsaki ya ɗauki pillow ya jefa a kujera sai bacci.


A cikin kwana biyu naci kaniyata, suna barin garin na tada masa husuma nace sai ya sakeni.
Dariya yayi yace.
"Ba zaki iya kishi da Nanah ba ko. Toh ba damuwq zan sakeki amma da sharaɗi sai nayi aure tukun zan sakeki."
Bani da zabi haka na hakura, bayan wata guda ya fara shirya mana tafiyq can dan har sun sauya min gurin aiki, sati biyu masu zuwa muka tattara sai yola na ci kuka har nagodewa Allah.


Mun bi jirgin sama ne dan haka. Mun isa da wuri kayanmu ne bai iso ba har ynx, wato gidansu Sadeeq wata duniyq ce dabam ko nace karamin garine na daban, tafiyar mintuna arba'in daga gater ɗin farko zuwa gater ɗin karshe na takwas knn, kuma duk inda zamu wucce Estate ne kafin muka isa asalin gidanshi, wanda yafi sauran haɗuwa koda muka isa cikin gidan ma'aikatan gidan kaman su tashi sama kowa murna ake da dawowarshi.

Cikin gidan muka shiga anan na zama bakauyiya sabida tsarin ciki,nuna min sider ɗina yayi sannan ya nuna min nashi dake kasa, mu kuma namu a sama, kowacce da nata.



Please Login or Register in order to submit comment