Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Ban ɓoye musu ba na faɗa musu,
Kallon Sadeeq nayi wanda shima ya kalle Imran yace.
"Dole zata je gurin knn.?"
Shima ya jefa mishi tambaya,
"Eh sai taje gurin, amma nimanta zasuyi." Ya faɗa mana.

Haka sukayita tattaunawa har rana sannan suka fita nima na shige ɗakin da Sadeeq ya nuna min,

Can wajen karfe biyu bayan na gama abincin rana, muna kwance nida Nur ba bacci nake ba dan ina krnt Hisnul muslum ne, tana kwance a jikina, kaman ance na kalle window, wata nur na gani akan window zata faɗa bazata faɗa ba ga wacce take kwance jikina, a hankali na shiga karanta addu'ar nimam tsari take ta ɓace.

****
A cikin sati ɗaya naga abinda saura kiris da na haukace sabida tsoro da firgici, amma dake ina tare da Allah sai bana tsorata da al'amarinsu, kwatsam na fara samun sako, a wayata.

Abinda ya fara kawo haka wani fitar da mukayi da yamma nida Nur, zamu gidan Adda Sadiya dan yafi kusadamu wata katuwar sharon ce tazo da gudu zata hayemu Kawu Junaida ya turemu gefe muka faɗi karshe sai da motar ta take, mishi kafa sosai.

Ihu na fasa wanda yayi sanadin fitowar mutane gurin, da gudu aka ɗauke shi zuwa asibiti tare damu.


Sakon da aka turo shine ya girgizani.
*Ki mika mana wasu sirrin mijinki zaki rayu, ai kinga abinda ya faru toh duk wnd yashiga gabanmu kasheshi muke zaki bamu ko sai mun fara akan Yar kishiyanki*

Abin ya bani mamaki bayan kwana biyu Nanah taje gidansu akace yarta ta ɓace, sakon aka sake turo min da cewa.
*_Kice musu a duba bayan gidanku ta windownki za'a sami gawar Yarinyar._*"

Lokacin muna tare a gidansu kallon mutanen gurin nayi jikina narawa nace.
"Abban Abul."

Juyawa yayi yana kallona a tsora ce nace.
"Gawar Baby yana..."

"Wayyo Allah ta kashe min Yarinyata."
Da gudu tayo kaina zata shakeni sadeeq ya riketa, yace.
"Amaratu gawar tana ina."
Kuka ne ya ci karfina daka min tsawa yayi wanda yasa na birkice,
Cikin ɗaga murya yace.
"Gawar na ina?"

Tsabar tashin hankali nace.
"Yana bayan windowna."

Salati duk yan gurin suka ɗauka, tare da fita suka barni a gidan, suna fita sakon nasake shigowa kamar haka.
*_Zaki bamu haɗinka ko sai kinga sakon gawa na gaba._*

Rungume Nur nayi ina kuka me taɓa zuciya,
"Kiyi hakuri Malama dole sai in fuskanci haka, amma gaskiya ta kusan bayana."

Inji Imran da yazo gurin knn, can sai gasu da gawar yarinyar abar tausayi suna zuwa da gawar sukayo kaina zasu taɓani amma tsoron da Imran ya saka musu akaina yasa suka koma....


Bayan kwana biyu da faruwan haka ina zaune kawai naji ina son fita, daukar nur nayi na runguma muka fara tafiya bamu tsaya ba sai a get six, kamar wacce ke umarta haka ajiye nur nayi ina mata murmushi na shiga cire kayana na isa gaban ruwan ina kallonshi, ji nayi an hankaɗa ni, na nutsu sosai ina son fitowa amma an danne kaina,

Duk wani addu'ar bakina yi nake dakyar na ɗago hannuna zuwa wuyana na janyo wanda yake shakeni a ruwan na turashi ciki, sama akayi dani zuwa inda na ajiye nur, matse min cikina ya shiga yi yana cewa.
"Amratu sannu na sakaki a damuwa, ko?"

Buɗe idanuna nayi wanda suka koma fari nace.
"A'a taimakon kai ne."

Kayana yasaka min, sannan imran ya mika mishi kofin ruwa, ya bani ina sha na fara amai can idanuna suka dawo dai dai, kwanciya nayi a jikinshi nace.
"Na gaji."

Mota ya kaini imran ya ɗauki nur, muka dawo gida har lokacin nanah haushina take ji.



Duk wani abun rikitarwa ina gani, ga sako ba adadi.

Kusan wata biyu muna cikin niman mafita kwatsam aka ɗauke kawu Aminu, ina chart da yan gidanmu aka turo min, sakon videon, ina buɗewa naga Kawu aminu an ɗaureshi kamar rago,

Gefe Adnan ne da wasu mutane, suna dariya, wuka suke wasawa, a hankali aka hasko bayan wani mutum yana magana yace.
"Zan baki nan da mintuna arba'in ki kawo min Sadeeq ko kuma na kashe Aminu da kuma Yarki."

A gurin vedion ya kare karɓan wayar yayi yasake kunnawa ya gani dariya yayi sannan ya fara bin cike wayar ya kalleni yace.
"Nasa an janye wancan ruwan da kika faɗa, kuma na saka an hako min, abinda suka binne, Alhamdulillah kome ya fara zuwa karshe, sai dai zan baki hakuri dan nine na fitar da Nur dan ta haka zasu faɗa tarkonmu,"

"Ynx baka tunanin halin da zata faɗa."
Na zuba mishi ido.
"Babu abinda zai sameta amma tabbas dole sai naje gurin."


Shiru duk muka sannan ya koma ɗakinshi ya sauya kaya, ya fito mika min key yayi a nutse ya kalle ni yace.
"Idan baki manta ba, tun abauchi mun faɗa miki haka zai faru, daga ranar da muka dawo dake zamu fara samun saɓani su kuma zasuyi amfani dake dan ganin sun sami nasara akaina, kuma ai Imran yace miki, zasuyi ta razanaki, ko kin manta abubuwsn da gani ne, Don Allah Amratu badan niba kodan abin cikinki ki taimaka min mu karasa wannan abun ai mun gama."


Shiru nayi ina tunanin kasadar da,zan faɗa ciki.

****
Aminu ya fito masalaci zai dawo gida, d gudu motarnan tazo ta buge shi.

Yana faɗuwa Adnan ya fito da wasu maza suka ɗauke shi, zuwa cikin motar suka bar gurin a guje inda suka nufi dajin ta wani hanya daban, Sadeeq yana biye dasu shi da Imran har cikin dajin can karshen dajin suka a wani gida suka tsaya sannan suka fito da Aminu suka shiga dashi ciki.

Suma kutsawa ciki sukayi, Adda Kuluwa ce a zaune sanye da jajjayen kaya, Gefenta kuwa wani kujerane a juye, kallon juya Sadeeq da Imran sukayi gefe guda Alhaji bilya ne zaune suna shan abu a kofi kunce Aminu, watsa mishi ruwa sukayi ya farka, kallon Alhaji bilya da Kuluwa yayi sai, ya fashe da dariya yace.
" Amma kunyi asara, mi kuke nima a duniya."

Kwaɗe mishi kai akayi ya faɗi kasa, ɗago kai yayi yana kallon wanda ke kan kujeran da yake juyowa.
Nuna shi yayi da ya tsaya yace.
"Dama kaine Shadow."
A tsorace Sadeeq yace.
"Uncle......."

Wallahi nagama juye kwalkwalwata a buk Allah idan banga voter da comments ba, toh sai bayan Sallah Insha Allah.....💁


A cikin mutane uku waye ne shadow,😂
🌺🌷🌷
*_DA CIWO A RAYUWATA_*
🌹🌸🌸

Na
Mai_Dambu
Wattpad:Mai_Dambu
*HAZAK'A WRITER'S ASSOCIATION*
(HWA)
Da sunan Allah Mai Rahama Mai Jinkai

_Pagen nakune Sis Aishat Magaji, tare da Deejerh, Maman Surayya hannun Damar Inna wuro, tare da sauran fans ɗin da ciwo a rayuwata na all websit_

~*Yabonku ya zama dole Yan azare musaman Yan grp ɗin Matan quart ga shafin nan nakune sukutun da guda nabaku, kowa yasan Azare da bauchi duk yanki ɗayane toh suma Yan bauchin ban manta dasu ba*~



                    *Don Allah Marubuta manyan da Kananu irina a duk lokacin da zamu faɗi halin mutum, ka tuna da Yardan da Yayi dakai da kuma amanar da Yayi da kai karka ɓata shi suna dan kaga yayi maka nisa*

*Page=V..Van*


    "Bawa kaii ina bashi bane haka ma bazai faru ba, Aboki taya haka zai faru mutumin da babu ruwanshi shine kuma wanda yake niman rayuwata." Inji Sadeeq.

        "Bawa kaine Dama Shadow amma Allah ya tsine maka albar.."

     Kifeshi da mari Adda kuluwa tayi, cikin ɓacin rai tace.
"Waye ya faɗa maka shine shadow ainice zan faɗa muku, kuma bazan faɗa ba."

        "Kuluwa kema har dake? A cikin azalumai,"
dariya ta saka sai da tayi ya isheta sannan ta iso gabanshi tace.
"Aminu ka dauka ni ɗin sonka nake ai ko kaɗan bana kaunarka dan Almu nake so, kuma bawa da kake gani bashi bane wanda kuke zargi, dukda kasan sirrinmu bazamu barka kafita ba sai dai gawarka, ynz munsa Adnan yasa Almu yazo kuma anan zamu sakashi ya kashe mana ɗanshi da Matarshi."

              Tana gama faɗar haka ta mike tare da bada Umarnin akai Aminu wani ɗaki,

          Barin gurin Sadeeq sukayi, shiru Imran yayi sannan yace.
"Ka ɗauki Nur mu kai musu."

                     Kallon Imran yayi sannan ya sauke a jiyar zuciya yace.
"Amma kuma naji sunce Iyayena na hanya."
     
       "Eh koda suna hanya aikin da akayi musu nan ne ya karye tunda mun kwashe ruwan min cire akwatin da kurwansu yake ciki, zasu iya zuwa ko wani lokaci, kawai ka mika musu Yarinyar sai mu bar garin dan nasan can lagos zasu sauka kafin su biyo jirgin yola."

         Koda suka zo nur suka ɗauka wacce take barci, Imran yayi mata addu'a sosai tare da saka mata wani awarwaron azurfa a hannunta na dama sannan suka zo kofar gidan suka ajiyeta, komawa can sukayi suna kallonta ganin yanda take ta waige waige. Duk tausayin yarinyar ya cika zuciyar Sadeeq juya baya yayi yana share kwallar da zuba daga idanunshi,

   Kuka ta fasa wanda yaja hankalinsu, daga ciki suka ɗauketa.

          *Wnnan knn*

        ****
     Rike hannuna yayi yana kallon fuskana cikin nutsuwa ya janyoni jikinshi, ya rungume ni yace.
"Ki kaimu Airport zan tafi lagos ne."
       D'ago kai nayi ina kallonshi zuciyata kamar zata kwace nace.
"Tafiya zakayi kabar min Y'ata a gurin mugayen can."

     "A'a Amratu karki cire min tsimanin da nayi mana, ki bani kwarin gwiwa akan aikin da na fara."
   D'ago kaina yayi yace.
"Ina niman fatan alkhairinki ne ba raunanani zaki yi ba, matukar kika karya min gwiwa toh ba makawa bazan iya moruwa ba."

      Kallonshi nake narasa mi zance mishi, sunkyar da kaina nayi ina jan shasheka ɗago kaina yayi yana share min kwalla,
         Tsuramin ido yayi zuciyarshi ba daɗi, "Domin fitar da xinari dole sai an narka da karfenshi, ki kula da kanki sai na dawo."
Juyawa yayi yabarni a gurin ina kuka, sosai ina jin tashin motarshi naji kamar na fasa ihu.

Tsakin Nanah yasa na ɗago kai, cike da tsabar rashin kunya ta shiga zagina har da kirana Mayya.

Mik'ewa nayi nabar mata falon dan bana son rigima.....

****
*Canada*
Tun da mukabar garin Meemah take zazzaɓi da ciwo a tsatsaye har yakai ta kwanta, sun kirashi sun faɗa mishi amma nice ban sani ba, haka tayi ta fama har taji sauki, ranar da Sadeeq suka kwashe ruwan nan suka kona akwatin, a ranar Daddy na Officee ɗinshi, sai yankan jiki yayi ya faɗi wani hayaki nafita a jikinshi, dake babu kowa a cikin office ɗin sai shi, har aka tashi bai farka ba, sai da Amrita ta lura da bai fito ba shine tashiga ta duba shi tasamu yana sume, da gudu tafito tana faɗawa sauran abokan aikitanta.


Ai basu ɓata lokaci ba, suka kira motar asibiti akazo aka tafi dashi, kiran iyalinshi sukayi suka je itama Meemah tana aiki a kitchen ta faɗi, dole aka kaita asibitin itama, haka abubuwa suka rincaɓe musu,

Kwanansu huɗu suka farka, tun da suka tashi hankalinsu ya dawo gida koda aka sallamesu, suke ta shirin dawowa yola, suna cikin haka ne Adnan ya kirasu ya faɗa musu an Sadeeq yasa an kamashi a kashe shi.

Shine hankalinsu ya tashi, sosai suka shiga tattaro kayansu zasu dawo gida Har da Inna wuro.

***
Koda suka isa airport shi da imran sun samu jirgin farko ya tashi, dan haka suka bi na abuja, daga can zasu bi, na lagos abin haushi suna zuwa suka samu jar jirigin ya sauka tuntuni, duba meemah yayi bai gansu ba,

***
Abinda ya faru kuwa Mutane da aka tura su ɗauko, sun riga su Sadeeq zuwa, koda su Meemah da Daddy, Adil, Ammih da Inna wuro da yara suka sauko sai suka ɗaukesu zuwa tashan jirgin kasa har yola.

Dan haka koda su sadeeq suka iso, su sun bar Filin jirgin.

Idan hankalin Sadeeq yayi dubu ya tashi, cikin ɗimauta ya shiga tambayar mutane babu amsa karshe janshi imran yayi suka fita, karan wayarshi yasa ya saka hannunshi a aljuhu ya ɗauko, sako ya gani.

*Yanzun haka Iyayenka suna hanyar yola ta jirgin kasa, sannan shima kaninka da yazo min kashe shi, suma suna zuwa abu ɗaya zamu musu.*

Dafe goshinsa yayi cikin damuwa ya shiga duba nomber Cp na yola, nan ya sanar mishi da kome, shi kuma yayi mishi alkawarin kula da abubuwan kafin ya iso.

Zama sukayi har aka sami jirgin yola kai tsaye, suka bar lagos, suna sauka suka sami jami'an tsaro na jiransu daga nan railway station suka nufa, jirgin kasan bai iso ba, suna gurin har dare basu jiran isowarsu.

Misalin karfe biyar na asuba, jirgin ya iso, koda su Meemah suka fito babu Daddy, da sauri ya isa garesu, cikin tashin hankali yace.
"Inna Wuro ina Daddyna yake?"

Waigawa suka shigayi babu shi babu alamarshi, cikin tashin hankali yace.
"Shit aiki ya ɓaci sun ɗauke shi."

Fita yayi gurin da gudu, dake akwai cunkoso, sai da yayita ratsa mutane, yana wuccesu zafin da yaji a daidai cikinshi yasa shi shafa gurin yanka shi akayi, a cikinshi abin mamaki baiga wanda yayi wannan aikin ba, sake jin zafi yayi a gadon bayanshi yayi, wanda yasashi dukawa.

Ga jinin dake fita a ciwon.
Karan wayarshi ya dawo dashi daga duniyar zafi, ɗaukar wayar yayi ya kara a kunne,

......
Kuka meemah dasu Ammih suke, wacce take rike da, Ihsan Adil yana rike da Abul, Mataimakin Cp ne ya fito dasu ta ɗaya kofar, dan Imran na tare dasu har ofishin yan sanda aka kawosu dan tsiratar da lafiyarsu.

****
Ina kwance bacci nake ganin mutum nayi akaina kaman dodon kamam skeleton jini ke zuba a bakinshi, matsoni yake yana murmushi tare da lashe bakinshi afirgice na tashi.

Murmushi yayi min tare da matsowa inda nake, zama yayi a gabana cikin nutsuwa yace.
"Duk cikin Estate ɗin nan babu wanda yake min taurin kai irinki, ban taɓa haɗuwa da mutum me jin kai irinki ba, haka kuma ban taɓa haɗuwa da mutum mara tsoro Irinki ba."

Yana wannan maganar ne, hannunshi yana kokarin zare min Hijab ɗina, rike hijab ɗin nayi.
Dariya yayi sannan yace.
"Nasha razanaki amma baki tsorata ba, kinsan ma me? Mijinki nacan nasa a kashe minshi koda yake yana jinki dan nakirashi shigowana. Mi zaki ce mishi dan nayi nasara akanshi."

Dariya nayi sosai nace.
"Jaiiii kana jina kuwa tashi namijin duniya, waima kasan mi ake nufi da *Jaiii* hmmmm tashu sa maza gudu, Jaiii Namijin duniya Jaiii Jarumina, Jaii Jan namiji, Jaiii Jan wuya tashi dodon makiya, idan da gaske kaiiii Jarumin Amratune tashi kazo ka amshi Uwar Yaranka, Jaiiiii Kana jina kuwa ko Mazajen sun faɗine tashi Uban Hadiza da Aishatu, Tashi ɗan Mustapha Uban Mustapha, idan da Gaske Mustapha ne fitar numfashinka naji sautin numfashin tawaya...."

Ajiyar Zuciya ya sauke nakuwa fashe da dariya Nace.
"Junaidu kayi Asara kafara gudu dan namiji na hanya, Ka ɗauka ya mutu ne?.."

Tasssss ya tsinkeni da mari yana Hucci yace.
"Nine Ninuuuuuu kuma Nine Shadow...."

Yaseen na gaji😹😹😹😹 Heyyyy Ku bani kujeran aikin hajj bana, dan nasan na haɗa muku tafkekken Chakwakiyya, Ina masu cewa Hamidu, Aminu, Bilya, Bawa, Adnan, Toh ga shadow da ya baku ciwon kaiiii ya bayyana, ga kuma *jaiii ɗin amratu a cikin wani hali*

Kuyi hkr ina busy ne, yau da gobe ma haka.

Sumayya da Brst saura naji kunyi copy catty😱


Love you Zauren Mai_Dambu.....💋💜
🌺🌷🌷
*_DA CIWO A RAYUWATA_*
🌹🌸🌸

Na
Mai_Dambu
Wattpad:Mai_Dambu...



*Page=W..Wurgi*


"Eh nine! Ninu sabida bai Iya kiran Junaidu ba yasa yake kirana da Ninu, kinsan mi yasa ban kashe kiba?."
Bina yayi da kallo tare da zare min hijab ɗina, kare jikina nayi na durkusa kasa tare da fashewa da kuka.
"Sabida ina muradin jikinki dake kanki, zan kyaleki amma shi da kike masa kirari zan kashe zan kashe Ubanshi da yafi kowa Sa'a"

Cikin kuka Nace....
"Sadeeeq kazo mana zaka kyaleshi ne ya keta min haddi."

"Nayi amfani da Yan uwana baki ɗaya na baya nan shine Hamidu, inda na tura mishi mugayen aljanu wanda da zaran kinganshi zaki fara razana, amma dake kanki yana da tauri haka kika tsallake, hmmmm ni bazan iya cutar dake ba sabida ina sonki!!! Dalilin haka nasa a kashe min wancan yaron dan aikinshi ya kare." Numfashi ya sauke tare da matsowa gabana yana jan zaren jikin rigana, buge hannunshi nayi cikin kuka nace.
"Azzalumi mara imani wallahi karshenka bazai yi kyau ba. Mugu kawai."

Zuba min ido yayi yana son ya taɓa ni nayi baya ina kuka, kashe wayarshi yayi ya saka aljuhu, kafin nayi wani motsi ya watsa min wani farin abu a gurin na zuɓe sai bacci.

****
Babu wanda ya lura da halin da Sadeeq ke ciki sabida cunkoso ɗagashi akayi aka fita dashi lokacin jinin dake zuba a jikinshi yayi yawa, jin yana yawo a iska amma bai kawo wani tsamani ba, dan yacire rai ta tashi,

Bai farka ba sai a gadon Asibiti, kallon ɗakin yayi ya mike a take Tunaninmu yazo mishi, sauka a gadon yayi yaga wani farin shirt ya ɗauka ya saka, kallon agogon da yayi kara a ɗakin yayi yaga karfe biyu daidai na rana, ban ɗaki yashi yayi alola yana fitowa yaji wayarshi tayi tsiwa.

Bai ɗauka ba ya tada sallah dan ɗakin akewaye yake da kafet. Ya jima yana addu'a kafin ya mike zuwa buɗe ɗakin yayi zai fita Fathiyya tashigo itama komawa yayi yana kallonta, cike da jin kunya tace.
"Nazo dubaka ne ko ka farka."

Gyaɗa mata kaii yayi, sannan yace.
"Ina son tafiyane."

"Amma kuma ai jikinka bai warke ba." ta faɗa kanta na kasa,
"Eh zafin da nake ji bai kai zafindake zuciyata ba Mahaifina da Matata kanina da kuma Y'ata babu amfanin barinsu a hannunsu." Yana gama faɗar haka ya mike zai fita,
"Hmm idan bazaka damu ba ko zamu iya taimaka?"
Girgiza mata kai yayi yace.
"Nagode karki damu Allah zai taimaka min, bana son sabida matsalata ya shafi wani nagode sosai."

Yana gama faɗar haka yafita daga ɗakin, wajen gidan ya fita yana kallon ta inda zai fara, barin cikin dajin dan a cikin dajin dake yankarine.

"Malam Sadeeq har katashi sannu bari nazo na maidaka gida."
Uwais ya gani cikin siffar rabinshi Maciji rabinshi mutum. Murmushi ya sakarwa Sadeeq, sannan yaja jiki zuwa gurin Sadeeq,

"Daka rufe idanunka sai ka faɗa min inda zan kai ka."
Inji Uwais,

"Ofishin Yan sanda zaka kaini dake cikin garin Yola"
Yana faɗar haka ya rufe idanunshi, take Uwais yayi sama dashi, bai direshi ko ina ba sai bakin ofishin yana shiga ya hangosu Inna wuro bai bi takansu ba ya nime iso da Cp.

Har ciki aka kaishi mikawa Sadeeq hannu Cp yayi, sukayi musabaha.

Zama sadeeq yayi sannan ya fara magana, yace.
"Yallaɓai kamar yanda muka taɓa magana da kai watanin baya yau ma nasake zuwa maka da maganar."

Mikawa Cp wayar yayi ya fara nuna mishi, abubuwan da suka turo mishi, har wanda basu jima da turowa, sannan yace.
"Yallaɓai wannan na farko shine autarsu babana kuma shine wanda yake niman rayuwata. Wandannan da kake ganin aiki yayi dasu daga kan Aminu Lamiɗo zuwa kan Abubakar lamiɗo, sai Wannar matar itama kanwar Mama ce."

Shiru yayi yana kallon Cp kafin yacigaba da Cewa.
"Akwai me gidansu amna shi nasami labarin ya jima da mutuwa, sai dai matsalar da nake ciki matata da Y'ata

Please Login or Register in order to submit comment