Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kyaleka ne sabida girman ka amma now da babu aurenka a kanta am ready to face any challenging."
   Fauce hannunshi yayi na zai ɗauke ni sadeeq ya kai mishi mangari wanda yasa ya faɗi.
      Abu kaman wasa faɗa ta kaure a tsakaninsu har sai da Adil na yashiga tsakaninsu,

   Sannan Ma'aikatan jinya suka ɗauke ni zuwa asibiti. A asibitin ma kasawa Adnan yayi ya tsare, shi yake kokarin dubani amma sadeeq ya tada hatsaniya dole aka fitar dashi yana ji yana gani Adnan yakai hannu zai taɓa ni, sai kuma yajuya ya kalleshi tsam ya ɗaga hannunshi ya bar wani likita ya duba ni,

       Anyi dace na farka amma na koma bacci,  can wajen biyar na asuba na farka ina tashi kome ya shiga dawo min taryan tiryan, mikewa nayi dafe da kaina ban ɗaki nashiga nayi wanka da alola sannan nafito na gabatar da Sallah ina idarwa, na mike fita nayi daga ɗakin nayi waje duk suna gaban ɗakin da aka kwantar da Meemah hankalinsu a tashe haka nazo na wuccesu Adil ne yace.
"Adda Amratu."

   Amna ko juyawa banyi ba Sadeeq kan ko kallona bayi ba ganin haka Adnan ya biyo ni,

     Ina fita taxi na tara, yana kawo ni gida nace ya jirani nafito mishi da kuɗi, ina shiga adnan na zuwa mika mishi kuɗin yayi sannan ya biyo ni ganina da kuɗin a hannu yace.
"Na biya shi."

    Ban kulashi ba na wurga mishi kuɗin nayi ciki abuna, kayana na haɗa tsaf najanyo jakana, ina fitowa falo naganshi a tsaye raɓa gefenshi nayi zan wucce amma ina haka yafincinko ni yana niman haɗa jikinmu tureshi nayi cikinku nace.
"Allah yatsine maka albarka Adnan ka cutar da rayuwata banza jahili dabba jaki kawai kuma Allah sai ya bi min hakkina ɗan iska lalatacce kawai."

        Kankance idanunshi yayi cikin ɓacin rai ya shiga ɓalle rigarshi wani mugun faɗuwar gaba ce ta kamani bansan lokacin da na fashe da kuka ba nace.
"Wai mi nayi maka ne haka da nayi derve wannan hukuncin"..

        Bai kulani ba yayi kaina ɗaukarshi akayi aka makashi da bango ina ganin haka nayi tsigar jikina ya mike  kafin nayi  tunanin waye ya baiyana cikin fararen Imran kaya, ɗaukar jakana yayi yace.
"Muje Malama."

    Jikina a sanyaye na mike haka muka fita muka barshi, har airport ya kawo ni, mika min ticke yayi sannan yace.
"Ina baki hakuri da abinda ya faru sannan ki rage damuwa duba ga yanayinki da kike ciki."
.  Gyaɗa.mishi kai nayi sannan na juya da sauri na shiga tashar ina goge kwallana.

             Ban wani jima ba aka fara kiranmu jirgin zai sauka a abu dhabi ne, daga nan na bi Airline zuwa naija....

               ***
    Lokacin da Sadeeq ga fitarmu shaiɗan ne ta fara mishi huɗubar tsiya bai san lokacin da yabi bayanmu daga nesa ya tsaya yana kallonmu yaga shigar Adnan sai dai fitowarmu da imran yagani bai shiga gidan ba ya biyo mu tashar jirgi, imran na fita suka haɗu tsuke fuska yayi yace.
"Ko nima kafara zargina ne da nimar matanka."
. Rutsa idanunshi yayi ya shiga motar suka bar gurin girgiza kai Imran yayi.

      Komawa gidanshi yayi yasha mamakin ganin motar Adnan har ynx shiga ciki yayi ya ganshi shame shame cikin jini da sauri ya ɗauko ruwa ya watsa mishi a firgice ya farka,
    Haɗa fuska yayi sannan yace..
" kwartancin naka bai isa ba sai kazo min gidana kafara wucce gona da iri maza fitarmu a gidan ɗan iska mara tarbiya."

         Dakyar ya mike yana gyara rigarshi cikin son ya kular da Sadeeq yace.
"Ni da nine da mace kamar Adda Amratu da babu abinda zai rabamu dan ta haɗa kome so sweet muaaaaa ga dadi ga garɗi macen dq zaka jima kana fantamawa da ita wallahi kayiwa kanka ai naso da tabarni munyi irin awa gudan nan muna makeluv."

     Bai kai aya ba Sadeeq yayi waje dashi cike da takaici da bakin ciki suka taru mishi watsashi yayi a waje ranshi na kuna,

Banɗaki ya shiga ya buɗewa kanshi ruwa ko cire kayan baiyi ba,

Koda ya fito cirw kayan yayi ya ɗaura towel, ya kwanta bacci kuwa yace bai sai da haka ba, haka yayi ta juyi a dakin har kusan azhar ya fito zuwa asibiti.


Koda taje Meemah ta farka tana ɗauke da Abul wanda jikinshi yayi zafi ainu jijjigashi tayi tayi har yayi bacci shigowan sadeeq ta kauda kanta ta cigaba da shafa kan Abul, Adnan ne ya shigo da Sallama can kasar makoshi suka amsa mishi, cikin sakalci ya isa gurinta zai daura kanshi a kafadarta tace.
"Usman!!! Karka kuma kusantar inda nake Bazan maka baki ba, amma kaje hakkin Amratu da na ɗan uwanka ya isheka, ba laifinka bane namu ne, tunda haka muka zaba muku yau Sanadinka aka raba aure, sabida aure nabar Iyayena da shi na biyo mahaifinku amma shine yau baka ga girman aure ba karaba shi Usman ka nemi Amratu ta yafe maka,,,"
Numfashi ta sauke sannan taci gaba da cewa.
"Kaii kuma kayiwa kanka amadadin nayi farin cikin shekaru ashirin da bakwai sai gashi ina bakin cikin ganinka tir da mugun zuciyarka da bata da amfani dubi halin da yaron nan yake ciki karabashi da uwarshi kasan ciwon da naji lokacin da nabarka, kasan halin da nashiga kuwa yau da zaka duba yaron ka tuna halin da nabarka da har abada ba zaka so ko makiyinka ya aikata haka ba amna ba damu duk kufita bana son ganinku."

Dakyar suka ja jiki zuwa waje jikinsu a sanyayye...
***
Sai da nasami kwana ɗaya da wuni guda na iso bauchi, dakyar nake ɗaga kafana, ina shiga falo na yanki jiki na suma, Allah ya taimaka dasu Baffa da Inna wuro suna hiranmu ne suka ganni jagwaf.

Da sauri sukayo kaina nan aka shiga min taimakon gaggawa amma ina dole aka wucce dani City clinic.

Kwana na ɗaya na farka Inna wuro na gani, tashi nayi na cire ruwan nayo kanta tana zaune a abin Sallah zuɓewa nayi a jikinta nace.
"Inna wuro, ya sake ni ya rabu dani."

" Amra waye ya sake ki, kar dai Buba amma da anyi mara rabo laifin mi kikayi "0

cikn kuka nake faɗa mata abnd ya faru kafin na kai aya naji an rike min wuya na danne ni Baffa yayi yana kifa min mari, cikin ɓacin rai Inna wuro tace.
"Alhaji ka nuna min Amra yarka ce, shi yasa baka dubi furfurana ba kake niman kasheta nagode."..

Cikin bakin ciki ya sake ni na zube, aikuwa na shiga kwara amai baji ba gani jikina har rawa yake, tun inayi a zaune har na kwanta, likita da nurse inna wuro takira take aka kamani zuwa gado, ruwa da alluran bacci aka saka min.


Sannan likitan ya kalle Ya Abba yace.
"Don Allah ku rangwanta mata wallahi zuciyarta zata iya bugawa any more,da cikin wata ɗaya da kwanaki da wane zata ji ne, plss ku barta hka inba haka ba zakuyi asara biyu daita da baby"

Yana gama faɗar haka yayi waje Hmmm zoku ga yanda Inna wuro take diri kallon Abbas tayi tace.
"Gobe zaka nima min takardan shiga inda yake sai naci kan gwafar malafar uban Buba idan banyi haka ba kafira nake ni zai tozarta ya tozarta min Yarinya kamila wacce Allah ya wanke ya bashi amna Buba yayi asara muje na baka."



Yeeeehoooooooooooooo Chaskalen Inna wuro.....😹
🌺🌷🌷
*_DA CIWO A RAYUWATA_*
🌹🌸🌸

Na
Mai_Dambu
Wattpad:Mai_Dambu...
    *Hajiya Inna Wuro*


Page G=Gauta

Haki take na tsabar masifa haka tasaka Ya Abbas a gaba ta bashi dallolin da Sadeeq ya bata koda bukatar haka ya taso tabawa Ya Abbas ko Mubarak.

Aikuwa yayi mamakin yanda ta ajiye kuɗin me matukar yawa haka, cire wanda zaiyi amfani dashi yayi sannan ya nufi central market inda zaiyi canjin kuɗin a shagon alhaji Haladu me canja,

Ana samu canjin washi gari yabar bauchi zuwa lagos a cikin kwana uku yayo mata biza ya juyo gida,

Yana zuwa ya mika mata yace.
"Inna gashi jibi zaku tashi amma gobe zaki bar bauchi ga sauran canjinki, zan haɗaki da abokin aikina yana lagos zai tsaya har ki tashi ga sauran canjinki dubu arba'in da ɗaya." ɗan birbishi fara'a fuskata ne ya ɗauke cak ta maka mishi harara kafin tace.
" Inyi wata kaniyar da canji a wannan shekaru mi xanyi da kuɗi kasan irin kuɗinda wanca ɗan banza mi wuya kamar markin lema, da shegen idanunshi kaman na budurwan tsaka, zan kama ɗan banza mi kiran arnan farko ja'ire da fuska kamar kosan manja tafi da kuɗin kasayawa mijina da kawata alawa."

Haɗiye dariyanshi yayi dan ya lura inna wuro yar bala'i ce godiya yayi mata sannan ya fito ya faɗawa Baffa da Nenne cikin sanyi murya Nenne tace.
"Wallahi Amratu bata da laifi sharrin shaiɗan ne kawai amma don Allah Alhaji ka sassauta mata irin wannan abinda kayi da wani abu ya sami cikin mi zaka ce."

D'aga mata hannu yayi cikin ɓacin rai yace.
"Bazan sassauta mata ba har sai naji daga mijinta tukun."

Shiru duk sukayi Nenne na zaune shi kuma yana tsaye, farkawa nayi tare da mika haɗi da salati ido biyu nayi da baffa dan kusan kwana na huɗu zuwa biyar bacci nake, jiya ns farka amma da ciwonkai shine suka min allura na koma bacci sai yau na farka sumul sai rashin karfin jiki.

Ganin baffa jikina yaɗauki rawa bansan lokacin da na mike na,zauna ba nace.
"Baffa..."

"Ya isa badai kaso aurenki kikayi ba Amratu toh ga gidan sai kizo ku zauna ai ba wani abu bane" yana gama faɗar haka ya juya ya bar ɗakin kuka nasakawa nenne nace.
"Nenne tuntuni banyi zina ba, sai yanzu da aurena Nenne ya zanyi da kallon da suke min, shin akwai wanda yafine bakin ciki da mutuwar Aurena ne wallahi na tsani kome na duniya shin miye laifina."..

Rarrashina tashiga yi har nayi shiru amma zuwa wani lokaci na shiga faɗa mata wasu abubuwan da basu dace taji ba, jikinta na rawa ta rufe min bakina tace.
"Kiyi hakuri ba ke ɗaya bace akwai ciki a jikinki."

Ji nayi kaman ta watsa min dalma "Bura Uba wallahi sai na zubar bazan zauna da cikin Sadeeq ba."

Aikuwa ta kife ni da mari inda take shiga ba nan take fita ba, sauka nayi daga gadon na faɗa ban ɗaki nayi kwara ruwa nafito, sannan na gabatar da Sallah.


Haushi yasa tafita tabar ni ina zaune Inna wuro tashigo inda take faɗa min tafiyarta bance mata kome ba da dare aka sallame ni,

Ina dawowa na fakaici Idan mutane na fitq cikin gari, ban tsaya ba har bayan gari anan nasami wani shagon a lungun Ibo quaters mutumin Inyamurine, nan na mika mishi 5k na mishi bayani abinda nake so wani irin kallo yake min, tare da lashe baki yace.
"Aboki kazo ciki nasaka maka drugs a cikinka sai kuma nayi aika gane just ten mins we go take ciki zai come out."

Cikin kallon bakada hankali ns mishi nace.
"Kai jakin ina ne magani zaka bani ko ce maka akayi cikin zina ne zan zubar zaka bani magani ko sai na kira maka yan sanda.".

A tsorace ya shiga ya haɗa min kala uku, sannan na juya nabar unguwar dan yanayin shi babu kyau.

Ina isowa gida na ɗauki maganin na shanyesu dukka sannan nayi kwanciyana,.

***
Cikin dare ciwon ciki ya farkar dani ji na nayi cikin ruwa tsundum, ciwon da nake ji ya hanani farin cikin, sosai nake zubda jini na fiton hankali tunda nasamu na shiga ban ɗaki na zuba gwiwana a kasa, ban sake iya fitowa ba dan jini nake zubdawa nafiton hankali.

Tun kusan sha biyu har huɗu nazata zaiyi ya tsaya ne ashe na ɗibo ruwan dafa kaina ne, har huɗu ina kwance cikin jini biyar saura Nenne tashigo tayi min magana taji shiru kutsa kai tayi ta same ni a cikin jini na suma, da sauri tafita nan suka shigo ita da Baffa da Inna wuro, kintsani Inna wuro tayi ta wanke kayan tass sannan su baffa suka dauke ni zuwa asibiti,

Ana kaini cikin gaggawa aka fara dubani tuni Dr Zakariya ya fahimci abinda nayi dan nata binshi yace bazai iya ba tunda cikin ba shege bane asalima ɗan sone.

Bai faɗawa Baffa ba sai ma kokarin tsayi da cikin da yayi inda yasamu suka ɗaure bakin mahaifar, ni kuwa duk wani jigata nayi shi ban masan waye akaina ba,


Na farka amma bana ganin kome sai Imran a cikin ɓacin rai yace.
"Nazata zaki farin ciki da samuwar cikin jikinki ashe har gwara Sadeeq Haba malama Amratu idan hankali ya ɓata ai hankali ke nimowa yanzun miye amfanin haka kinyi yunkurin kashe rai, toh ku cigaba keda Abubakar ɗin tunda haka kuka zaɓawa kanku Allah ya jishemu alkhairi."

Yana gama faɗar haka na fashe da kuka, amma bana ganin kowa sabida jinin da bani dashi, dakyar aka sami jini irin na Sadeeq dan wani mutun ne yazo bada jini sadaka shine aka saka min,


Hmmm wani irin rashin lafiya nayi kaman xan mutu dan suma nake akai akai, hankalin kowa nawa a tashe yake, dakyar Ya Abbas yasak Inna wuro a jirgin ranar lahadi anan bauchi.


Ta isa airport ɗin da yamma washi gari jirginsu ya ɗaga zuwa Addis Ababa na kasar Ethopie, daga can kuma suka mike zuwa Canada.


Hmm sai da na share kwana goma kafin nasan waye akaina, ranar da nafarka Dr Zakariya ne akaina hararata yayi cikin ɓacin rai yace.
"Amma Dr kin bani kunya mi yayi zafi da zaki zubda cikin jikinki kinsan yanda nake niman Allah ya bani haihuwa kuwa ke kin samu kina butulcewa Ubangiji da wani ne ya faɗa min zaki iya haka bazan yarda ba, cikin jikinki bai da laifi laifin wani baya shafan wani wallahi kika sakw gigin zubda ciki toh mutuwa zaki ke ni ɓari ma nake addu'a Allah ya nuna min na gani balle ke da kika sami damar haihuwa zaki yi idan kika kuma zan faɗawa Alhjku yasan matakin da zai ɗauka akanki."

Yana gama faɗar haka ya fita abinshi, kuka nasaka nama rasa mizanyi ne....


*****
Canada zubawa Adnan Ido daddy yayi cikin ɓacin rai yace.
"Ni zata wasu dangin ne masu niman bayan yan uwansu ashe nima nahaifi wanda zai datse aure dubi halin da mahaifiyarku take ciki ka taɓa tambayarmu daga ina muke, ina ne asalinmu."

"Assalamun Alaikum" sallamar Sadeeq ne ya katse abinda Daddy zai faɗa, a hankali ya gaidasu sannan ya mikawa Abul Hannu yaron na,zuwa jikinshi ya fashe da kuka yace.
" Amama adda!!! Adda!!!"
Juyawa yayi yana duba ko ina na har da kofar fita yayi daga jikin Uban yaje bakin kofa yafara "Amama Adda"

Kuka Meemah ta fashe dashi batasan lokacin da ta ɗauki goran ruwa ta makawa adnan ba cikin kuka tace.
"Tir da haihuwarka, tarihi ya maimaita kanshi kafi kona kashe ka wallahi ban yafe maka ba kaje karshenka baza...."

"Hadizaaaaaaaaaaaaaa Ya isa haka so kike ya lalace idan ya ɓaci har dake zai shafa."

Mikewa Sadeeq yayi ya ɗauki ɗanshi zai bar gidan cikin kuka tace.
"Babana Ina zaka da Karami."

Murmushi gefen baki yayi kanshi a sunkuye yace.
"Inna wuro takusan shigowa ne zanje najirata sai na kawota."

Mikewa tayi tace.
"Muje naga mahaifiyata."

Wani irin kallo Adnan yake bin sadeeq dashi har yazo inda zai wucce yace.
"Sai nayi Ajalin soyayyarka da amratu abinda kake gudun kar wani ya lasa sai na bazaje gumina a jikinshi, sai na zuba mata ruwan jikina a mahaifarta yanda zai xamo ɗa naga wanda ya isa ya dakatar da wannan alamarin a shirye nake nayi faɗa dan soyayyar da nagirma da ita, wallahi ina faɗa maka sai nayi sucking inda kake sucking ni dakai ne shege kafasa yanzun za'a fara Love Game."

Rutsa idanu Sadeeq yayi cikin zafin kishi da damuwa ɗan uwanshi kaninshi yau shi yake son matar aurenshi wannan wani irin al'amarine me ruɗarwa haka, dafashi Adil yayi yace.
"Hamma Sadeeq kayi hakuri duk cikinmu shine fitinanne baya jin maganar Meemah da Daddy duk abinda yasaka kanshi sai ya aiwatar, kuma haka ya farune sakamakon son da yakewa Adda Amrah karka ga laifin Iyayenmu suna bakin kokarinsu da zaran Allah ya cire maka zakka a cikin Yaranka toh fa sai addu'a."

Shiru yayi sakamakon hango Meemah da sukayi haka suka fita zuwa tashar jirgi.

Sunyi tsayuwar mintuna ashirin kafin jirgin ya sauko ahankalin mutane suka fara saukowa can Hajiya Inna wuro ta sauko raba idanu take tana niman Buba, har ta iso cikin inda suke jiranta hmmm Inna wuro da masifa ita ko jaka bata ɗauka na kaya ba daga ita sai lalitarta(😹)

Daga nesa ta hangoshi rike da Abul, sauri takara cikin masifa tace.
"Kaii jaja amare da fankan fankan kunne kamar kilishi bani hanya ko na bankaɗe yan banza dubesu a tsuke kamar wanda yunwa ya korosu tirrr da nasara arnan wofi."(😂ko meye matsalarta dasu oho) tana cikin tafiya wani mutun yace mata.
"Madam can i holp you."
Zaro ido tayi cikin masifa tace.
"Mangofaka yaci kotar ubanshi, kundun kaniyarka dan malafar uwata kaga ɗan banza mi zubin ifiritai, nice madan wato ga inyamura, kaga min ɗan kotar uwa, banza da fuska kamar alalen da ya kwana gafara can."

Wucceshi tayi tana masifa tana watsa hannayenta irin na wanda ya fusata, daga nesa Sadeeq ya hangota, cikin azama ya mikawa Ammih Abul yayi gurinta,

Tana hangoshi ta cire hijab ɗinta tasha ɗamara, yana isowa ta tsinka mishi mari wanda yaja duk aka juya sake yarfa mishi tayi daga can Meemah sai murmushi take tana cewa.
"Yes Uwata ce." cike da alfahari abinda suka gazayi idanunsu ya rufe da kaunar ɗansu shine Inna wuro tayi,

Cikin hargagi tace.
"Kaci kwankwalatin kan takalmin ubanka, ɗan banza me kiran adawa sai da kagama lalata musu yarinya ka sassaqe mata duk inda zata nuna ita mace ce, sannan kasake musu ita dan soron gidanku, yo Buba ko zuwa kayi kasami kato akan Amra wallahi bazaka saketa ba wani shegen ne ya raruketa, ina ce da ka addabi yar mutane ko tafiyar sai da ya sauya, har ka mance yanda ka farka musu yar mutane a gomar karshe na ramalana, shine zaka saketata ɗan banza mara mutunci da kunya wani irin wahala ce bata sha akanka ba sama da shekarq guda tayi tana jinyar gadon bayanta dan kwal ubanka shine da kasan zaka sake musu y'a sai da kasake xuba mata wani cikin madallah da cikin ya ɓare ynx idda zatayi ta famtama aurenta mugu munafiki, dan banza kayi asaran macen da zata ɗauke fitinarka bazaka gane haka ba sai Allah ya haɗaka da wacce sai kabiya ka fafuketa"

Duk wannan gurmin akan idanunsu Meemah, Daddy, Ammih da take kukan tausayin ɗan uwanta, sai Adil da ya koma gefe yana kwasan dariya Adnan kan murmushi yayi a ranshi yace
*Sadeeq karasata knn har abada ynz xan tsara kome amma dole sai na nemi inda take Sweet Amrah gani nan zuwa gareki*

A hankali Meemah ta isa gabanta ganin yanda Sadeeq ya zuɓe agaban inna wuro, yana jin faɗarta, sai taji tana alfahari samun ɗa irin Sadeeq dan ma batq san halinshi ba, tana isa tace.
"Inna wuro!!!"
Cike dq masifa tace.
"Kyaleni naci dudduniyar takalmin Uwarshi yaro ya lalata rayuwarshi a cikin ɗan kankanin lokaci, toh ai shiknn "

D'ago kai tayi zata sake banka mishi wata tululiyar ashariyanta sai suka yi ido biyu da Meemah tsabar firgice a take ta zube jikin Sadeeq ............😂



*Zanyi kokarin haddar ashariyar Inna wuro*



🤣🤣🤣🤣🤣🤣😂Inna Wuro Foreve👌🏻😜
🌺🌷🌷
*_DA CIWO A RAYUWATA_*
🌹🌸🌸

Na
Mai_Dambu
Wattpad:Mai_Dambu...
        *Tsaka Mai Wuya*


*Page =Hotiho😂*
     
Kamata sukayi aka sakata a mota nan suka dawo gida da ita suka yayyafa mata ruwa, ajiyar zuciya ta sauke sannan ta mike zuciyarta ba daɗi, kurawa Daddy ido tayi cikin kaɗuwa tace.
"Almu kaine."

Kuka take sosai, sai da duk falon suka matse kwalla, a hankali ta fara magana cikin kuka tace.
" Nayi farin cikin ganinku amma nafi bakin cikin ganinku sabida gashi a sanadinku yau ya rabu da yarinyar da ta,sadaukar da farin cikinta sabida shi, tayi fama da mugayen aljanu sabida Buba ga laluran da tasamu duk sabida shi, wanda har ta koma ga Allah yana tare da ita, mi yasa kuka batar ta dawo gida a she haka zuciyarku ta cika da sonkai, ina ifiritun da ya raba auren babban shaiɗani abokin shaiɗan lamba ɗaya aure kakashe kaima sai ka wulakanta sabida katashi a cikin gata ga uwa da uba, ka girma cikin yahudawa, masu yawo da ɗan kamfe, har ka manta da axabar Allah akan wanda ya nime matar wani niban damu da kai ba nafi damuwa da wanca kafirin."

Hannunta biyu ta dannawa Sadeeq wanda yake zaune rungume da ɗanshi cikin tausayin Sadeeq ɗin tace.
"Buba mi yasa ka gaza hakuri da Amra kome tayi ai kai mi shanyewa ne balle yarinyar nan tayi kokarin hidima da kai, hmmm kayiwa kanka."

Mikewa tayi duk suka bita da ido sai da taje inda Adnan yake ta sake masa dundu a gadon baya sannan tasamo tsakiyar kanshi ta zuba mashi kusa(😂) tsabar ranta ya baci ji kake dundum fau fau tasss,

Duk ya gigice ya tsorata kai Imran da karawa Alamarin zak'i ya shige jikinta yaware karfi ya zuba mata tayi ta jibgarshi kamar jaki tanayi tana fada tana masifa,

Dakyar Sadeeq yaja ta shima kuwa yasami kyautar mari, wanda ya fasa mishi baki Adil komawa gefe yayi yana kyakyatawa, rike da cikinshi Ammih ma haka, zama tayi tana hucci cikin tsananin tsoro Adnan ys mike yabar gidan ranshi a ɓace,

Mikewa tayi dan wani fushi ta kamani, tace.
"Buba kaino ɗakin da,zan zauna dan idan na cigaba da

Please Login or Register in order to submit comment