Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dan yau kece mai rike da linzamin Sadeeq lamiɗo Allah yarabaki da jarabar Inna wuro."
Cak na tsaya ina murmushine amna sai da ya ɗauke a fuskans agogon falon na kalla naga mun ci lokaci ashe juyawa nayi na ɗauki fillow kujeran falon na wurga mishi na fita abuna, duk na rasa yanda zan ɓoye inne wear ɗina ba, kamar munafuka haka nafito ita ɗaya a falon, sai muryansu Ihsan da nake ji acan ɗakin Wasansu wuf na wucceta zuwa ɗaki wanka na shiga nayi na fito sai gata.
😳 Kallona tayi yayinda Ruwa ke ɗiga a jelar gashina ina kokarin tsame gashin, ɓantaran goranta tayi tana taunawa tunda naga haka cikina ya bada kululu, a raina nace na shiga uku da tijaran Inna wuro.
Shekeke ta kara😒 kallon towel ɗin da na ɗaura, tace.
"Amarahhhh wato da nace zan kwato miki yancinki a gurin buba shine kika kai mishi kanki dan baki da Haji ake cewa ko zaure, Innalillahi Anya Buba bai baki bita zai zai ba, naga jaraba kinje ya rarukeki hankalinku ya kwanta toh tattara kayanki ki koma ya cigaba da ɓaɓɓakeki😒"
Ta fita nata masifa shima ta sauke mishi.
'Buba dama wannan shine kidnafin ɗin ɗan banza ka ɓata min yar mutane maza kaje ka ɗauke min ita da gani, kuma ia nan daku jarababbun wofi."


Kamar yanda ban kulata ba haka shima bai kulata ba sai ma mikewa da yayi ƴaje ya kwaso min kayana, muka bar ɗakinta sai sababi take ga gidan ba kowa,, ciki ya shiga da kayana yazo ya same ni akan kujera, ina kwance duk jikina ciwo suke, biyoni yayi ya ɗaga ni, sai ya zauna ya ɗaura kaina a cinyarshi yace.
"Har ynx baki ce min kome ba akan kaina nidai bana son kalmar rabuwar nan sabida ni nafi kowa dacewa dake."

Lumshe idanuna nayi sakamakon wasan da yake min da gashina, abinda na lura a rayuwar aure shine dole muyiwa juna uzuri, kuma mu ɗauki kome ba kome ba sai Allah ya bamu nasaran akan abokan zamanmu, ɗabi'ar ɗa namiji da halayarshi kundine guda wanda da,zaran ka fara buɗewa sai karasa wane zaka ɗauka kabar wani.

Matukar kace a rayuwa bazakayi hakuri da abokin zamanka ba toh aiki ya sameka babba dan kafin wani lokaci na fara maka lissafi da aure, koda yake Suma mazan batayan baya bane idan dai wata ce take tare da sadeeq tuni sun rabu dukda shekaruna gashi na zabtare kaso mai girma a cikin shekaruna, namai da kaina like 18yrs na ɗauke duk wata lalurashi, abinda nasan koda kuɗi aka bani bazanyi ba, yau ina mishi badan kome ba sai dai dan bashi girmanshi, da Allah ya bashi akaina wani lokacin nakan jinjinawa kaina idan na,zauna ina zuba mishi shagwaɓa da kiriniya, kuma yana biye min.

Ynx ma akan cinyarshi nake na fara zillo kamar zan faɗa sai yayi maza ya tare ni yana kallona tura mushi baki nayi cikin ɗanye halin danayi course a gurin Inna wuro, nace.
"Ni...fa"
Kallona yayi sannak yace.
"Ke fa me?"
"Bacci nake ji"
Shiru yayi yana kallona a nutse can ya sauke numfashi yace.
"Toh Adda kwanta."..
Ware idanuna nayi akanshi na mikw daga cinyarshi kankantar da idanuna nayi cike da tsiwa nace.
"Gatari ne ba Adda ba, karka kara kirana da wannan sunan."
Mikewa nayi zan bar falo ya janyoni na faɗa kanshi kallon fuskana yayi cike da murmushi yace.
"Toh naji hayatina bazan kuma ba kinji ko basan mi nake ji akanki ba amma kacokan rayuwata mallakarki ce."

Tsareshi nayi da ido, ina nazarin abinda idanuna yake hangowa, nace.
"Ada kace nike sarafa zuciyarka yau ka ambace ni da rayuwarka Abubakar tsoro kake bani, don a kullum sauya min launi kake kaman awainiya, nafi karkata tunani akan nice nake hauka akanka ba kai kake akaina ba, wani shashi na zuciyata tana tunatar min da cewa kai ɗin wani abu zaka cima akaina. Koma dai me nene karka manta, soyayyar da na nuna maka, Sadeeq koda bana raye karka wulakanta min Yarana."

Cizon lips ɗina nayi cikin kokarin rike kukana nace.
"Several time ina tambayar kaina Anya na dace dai kuwa, dan gani nake kaman kana zaune dani ne akan dole babu yanda ka iya dani shi yasa baka ganin girmana kake iya wulakantani, Sadeeq!!! Alfarma ɗaya zan nimaa gurinka koda zaka rabu dani karka rabani da Yarana dan na wahaltu akansu koda zaka guje ni karka rabani dasu, dan nafi kowa sannin ciwonsu, Sadeeq bansan wani irin yanayi nake ji ba amma ko yaya ne zanso na kara faɗa maka
Ina sonka ina kaunarka kayi hakurin zama dani a duk yanayin da nake, idan kuma na koma ga mahaliccina karka manta dani karka manta da bayana koba yau ba zanso kasake maimaita min kalmar Ina sonki dukda bani da darajar samunshi."

Ina gama faɗar haka na mike zan bar falon janyo ni yayi ya zaunar dani akan cinyarshi yana kallon idanuna da yanda nake saukar da kwalla, can kasar makoshinsa yace.
"Sai da nasami shekara biyu ina mafarkin wacce take niman na taimaka mata, dazaran na taimaka mata sai naga tajani zuwa ga Haske, ashe kece zan bawa lokacina amma bansan wani haske zaki jani ciki ba, hasashena na farko haɗani da iyayena kin kunna min fitila lokacin da nake cikin duhu Amratu idan nace ina sonki ai nayi karya ne basonki bane a'a ke ɗin kaunace guda dan so yana tashi kaunarki a jinina take."..

Haka mukayita musayan kalmai har Inna wuro tashigo ganina akan cinyarshi mikewa xanyi ta maka min harara tare da tauna goronta tace.
"Jarababbu Harijai haka zaku tabbata, kuna mnne da juna sai kace kalangaru a jikin bango, zaki wucce ki mana abincin rana tunda ayu ya sakaki a ɗaki ke kuma matar ayu kina like dashi wato, idan na kintata dai dai, bashi kaɗai yake barbaranki ba har dake fito muje mayu kawai zanga karshe zama a cinya ai."

Ban gama jin mi zata ce ba nayi gaba abuna shima biyo ni yayi muka fara aikin amma shi ba aikin bane ya kawoshi dan rungume ni yayi ta baya ina aiki hannunshi na rike da waist ɗina, can ta leko cike da mamaki tace.
"Buba kaci kwal ubanka fita min kabar yar mutane tayi aiki."

Juyawa yayi yana shafa fuskarshi yace.
"Inna wuro kishinki yayi yawa, matata ce fa,ko sokike naje wajen wasu matan n..."

"Na shiga uku na lalace kaiiiiiiii Buba Anya da aka zo rabon kunya an tuna dakai kuwa, wato idanunka sun kara buɗewa kasaba ganin masu ɗan diros suna yawo agabanka shi yasa bazaka dinga jin kunyata ba dan uwaka awa nawa kukayi a ɗaka, inma abincine ai yaci ace ka koshi har da gyatsa amma dake kun zamewa kanku yan barbara......"




Yaseen Inna wuro zata sheke min sauran dariyana

Idan nagama Hidiman gida na kuma taɓoku idan ban gama ba kuyi hkr zuwa Monday Insha Allah
🌺🌷🌷
*_DA CIWO A RAYUWATA_*
🌹🌸🌸

Na
Mai_Dambu
Wattpad:Mai_Dambu...
*Al'amarin Ubangiji*



Page=Q...Qwai


D'agowa yayi cike da zolaya yace.
"Wai ke Inna wuro miye matsalarki damune ba hali muyi rayuwa knn sai ya zama damuwa Allah zanyi kidnapping"

Shiru tayi tabar kitchen ɗin shi kuwa yazo ya rungumeni muka cigaba da aiki yana tambayana mi nike yi ina faɗa mashi har na gama, muka jera a table, leka su Nur nayi abin mamaki Abul da Ihsan suna can suna wasa ita kuma nur, tana gefe tajuya bayanta. Zuwa nayi na juyota arazane na koma baya na fasa salati da karfi take kamaninta suka sauya, tare da Inna wuro suka shigo ina ganinshi nayi bayanshi a tsorace jikina na rawa nace.
"Abban Abul yarinyar nan ba mutum bace."

D'ago idanunta tayi wanda sukayi wani rolling, har sadeeq ɗin sai da ya mike tsaye tsabar firgita takama dariya sosai tana tashi kamar ana ɗagata, yarinya me shekara ɗaya da rabi, wani irin dariya tayi kafin tace.
"Kunyi kuskuren sanin wacece ni, domin na jima a jikin yarku, nima turoni akayi, na zauna idan kuka matsa kasheta zanyi hhhhh ni ba Aljana bace ni demons cee kuma an bani damar ruguza ahalinku baki ɗaya, amma sabida kana tare da wani banza can yasa na gaza aikina, nice na shiga jikin kaninka, bayan ya karbi aikin kasheka hhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhh."
Luu yarinyar tayi zata faɗi cikin sauri naje ta faɗi a jikina kuka nasaka nace.
"Sadeeq Miye Laifin Nur a cikin matsalarku nidai kar acutar min da y'ata shi yasa nake jin bakon yanayi a jikina ashe akwai matsala ne Wayyo Allah na."

Kamshin Imran yaji ya fita da mugun gudu, har zuwa lambu dake cikin gidan zuɓewa yayi a kasa yana kallon Imran dake zaune akan kujeran da aka tanadesu dan hutawa, kallon Sadeeq yayi zuciyar shi cike sa tausayinshi yace.
"Been knn tana daga cikin manyan matsafar ifiritai, kafira ce tana daga cikin jinsin mugayen aljanu."

A raunane sadeeq yace.
"Wani laifi Yarinyar tayi? Gabar ba da ita aka fara ba mi yasa sai da ita a cikin."

"Sabida ta haɗa abubuwa guda biyu na iyayenta, kaman yanda ruhinku keda karfi hak nata keda karfe, ita ɗayanta ta kwashin abubuwan da kuke ɗauke dashi, kai katara ɗaukaka da kwarjini,Nasara da buɗi, soyayyar mutane yana zagaye daku , ita wa zai samu wannan damar ya kyaleta, ka kwantar da hankalinka ina cikin gidan nan, zuwa lokacin da Ubangiji zai buɗa mana hanyan"

Cikin tsananin damuwa ya zuga hannuwanshi akanshi, yace.
"Dole na tashi."

"Kafara shiri haka nake son mazajena angon Amratu da Inna wuro kataki D'an Mustapha Uban Mustapha na gaida Baban Nur da Ihsan Yayan Saminu Yayan Hauwa, Bauna saniyar sake sarki kake adawa sarki kake a gari, Ina gwani ga nawa ina namijin duniya Ga Abubakar ɗina Ina mazajen suke gashi nan zuwa gareku dodon makiya nagaida wanda amakiya suka gaza baiyana kansu a gareshi karamin yaro da babban zuciya tashi maxa kanemi yardan Allah sa maza gudu, ubangayya kake kai kaikaɗan zugane Yawwa Aminin kwarai."

Juyawa Sadeeq yayi ya faɗa jikin Imran ya fashe da kuka yace.
"Kwararramin gwiwar da kake Aminina yayi yawa,."

Dukar kafaɗar Sadeeq Imran yayi yace.
"Idan da zumma toh akwai aiki jeka Amratu tana jiranka."

Sallama sukayi sadeeq ya dawo cikin gida, yana zuwa ya amsheta zuwa ɗakinshi irin magungunar da yayi min amfani dashi ya rubuta yasake fitowa da ita a kafaɗarshi yabawa Adil da suka dawo suka sami labarin kuɗi yayi da takardan yaje ya sayo mishi magani.

Can sai ga Adil ya dawo ya bashi a falon ya haɗa ya bata tasha ya shafa mata,

****
A haka rayuwarmu ta cigaba da tafiya cike da damuwa, da farga ga, har aka sami wata biyu a wannan watan na fara wasu mugayen mafarkai, wanda suke curkuɗe da ababen ban tsoro haka zan tashi na zauna ina kallon Sadeeq dan kusan akanshi nake mafarkan ana cewa na rabu dashi, shi kuma zai raye daren da bautar Ubangiji.

Yau ma a dame nakwanta dan na fara tsoron mafarkan, ina kwance ya shigo ya zauna can muka fara raya daren tare da wani shafin kauna na musamam, munyi nisa a zungure juna na fara jin amai, da wani irin karni da wari, aikuwa na shiga kela aman dakyar ya janye daga jikina muka shiga ban ɗaki wanka nayi na fito, nazo nasamu yana gyara gadon ɗaukar fillow nayi na kwaɗa mishi, cikin mita nace.
"Wallahi pure love kana cutata ove wani cikin ka sake lika min, Allah yasa daya ne dan haka nayi fama da cikinsu Abul kuma dis month circle ɗina yaki zuwa kusan wata guda har da kwanaki."
Sama nayi anyi dani cike dafarin ciki yace.
"Yar mata kina karɓan zungura da kyau, kwanta ki huta."

Dariya nayi na kwanta yana fitowa har barci yayi gaba dani, sallah ya gabatar addu'a yafara barci mai nauyi ya sauko mishi dakyar ya kallama ya hawuro gadon yayi min addu'a ya kwanta shima yayiwa kanshi.

Karfe ɗaya caf na dare, wanda yayi dai dai da farawa wani mafarki, muna kwance wani yaron da bazai wucce shekara biyu yazo ya tashemu tashi mukayi dani da Sadeeq ɗin, a hankali muke tafiya har zuwa bakin get six, shiga dajin mukayi tayi har wani fili babba daga nesa muka tsayawa wasu mutane ne agaban wani gunki me sifar kura, jikinsa na mutum, mace da namijine suke shiga jikin juna a hankali inuwarsu ya fita daga jikinsu ya haɗe guri guda,

Dukkansu a tuɓe suke tsiraransu suna zaga wannan gunkin.

A hankali suka ɗauki wani akwati suka nufo mu, ɓoya mukayi, sai da suka tafi muka bi bayansu a har bakin wannan koramar, bamu gansu ba sai motar da take shigowa cikin gurin, faci motar tayi suka tsaya me motar yafito ya fara gyara motar inda ta ciro wani taya zai saka gurnani yaji a bayanshi yana juyawa yaga wata katuwar kura, kafin yayi wani yunkuri ta bangajeshi fitowa matar shi tayi, yace mata.
"Hadiza koma mota ki ɓoye wannan takardun ki saka nomber ma'ajiyin." sunyi maganar cikin harshen germany ne,

Da sauri ta koma motar tayi yanda yace kallon Sadeeq tayi cikin kuka tace.
"Ya Ubangiji Kaine masanin fili da ɓoye Ya Allah ga D'ana Allah kare min shi daga sharrin masu sharri."

Ajiye Sadeeq tayi ta buɗe kofar tace.
"Baban Daddy karka fito kaji ko."

Fita tayi taga suna jan Mijinta da gudu ta rufa musu, kwale kanta akayi ta faɗi har filin da suka jasu daga nan suka fara wasu irin magana har wani tsawa da walkiya ya baiyana take, wani abu suka cire a jikinsu suka ɗaure suka saka a cikin akwatin, sannan suka ɗagasu suka ce.
"Mustapha da Hadiza kushiga duniya mun muku iyaka da mahaifarku har abada."

Cilla wani kirciya sukayi sama take Mustapha da Hadiza suka mike suka bishi a guje, bakin koramar matar da namijin suka dawo inda suka jefa akwatin A ruwa, suka ɗaura mishi dutse sannan suka kawo wasu irin halittu suka jefa su a ruwan, daga nan suka ɗauki yaron suka kawo shi cikin gidansu dake karshen garisuka wurgashi, hannu ya mika yana kuka yace.
"Uncleeeeeeee Mommy Daddyyyyy."
Jefa mishi kwai yayi ya fashe take wasu irin abubuwa suka fara fitowa ihu yaron yayi Yace.
"Uncleee Nuniiiiiiiii"

Rike kofar yayi yayinda ya xaro mishi Ido. A gigice ya farka tare da dafe goshinsa yana salati, Imran yagani........


Kaiiii Jama'a na gaji wallahi
🌺🌷🌷
*_DA CIWO A RAYUWATA_*
🌹🌸🌸

Na
Mai_Dambu
Wattpad:Mai_Dambu...
       *Akwai lauje cikin...*

Page=R..Ra'ayi
 
    Mik'ewa ! yayi jikinshi na rawa ya buɗe jakar kayan aikinshi ya ɗauko pencil da wani farin takarda ya shiga zana hoton yayi ya yaga yayi ya yaga.

      Rike hannunshi Imran yayi yana girgiza kanshi, sannan yace.
"Babu lokacin wannan aikin koma waye zaka samu sauran amshoshinka a can dan haka ka shirya kawai, kai da ita kubar musu Yaran a nan Hafsat zatazo ta zauna dasu."
   
        Girgixa kanshi yayi cike da damuwa yace.
"Imran bazan iya tunkaran Amratu da maganar tafiya naija ba! Numfashi ya sauke kafin ya cigaba da cewa.
"D'an kwanciyar hankalin da na samu da ita yasa na kara fahimtarta kuma nasan wacece bazan iya tafiya ni ɗaya na ba?"
       Karshe maganar yayi da tambayar Imran tare da tsare shi da idanu shi da sukayi ja.

         "Kaii ne fa miji! Sannan itace matar, matukar kana son dakatar dasu sai da ita. Abinda zan faɗa maka yanzun haka ɗan uwanka ya isa garesu, kuma dole ya taimaka musu Sadeeq tafiya da Amratu yana da alfanu ka duba lamirina na abokinka" Sauke numfashi yayi sannan yadafa Sadeeq, yace.
" Baka ga kome ba, dan kome na nan kwance zasu iya juya maka tunanin kowa na kusada kai Amma Allah ya fisu, idan ka yanke hukunci ina tare da kai amma karka manta kaine kake aurenta ba ita ke aurenka ba. Sai an jima Aminina."

       Cike da damuwa ya mike zuwa banɗaki ya watsa ruwa sannan yayi alola yafito.
     
   Sallah ya tada baiyi sallama ba sai da yaji wasu masalatai suna kiraye kirayen Sallah.
     
     Zama yayi da kyau ya cigaba da Addu'a, har aka shiga sallah shima ya mike yayi yana idarwa ya tadani, wanka da alola nayi nazo na gabatar da sallah, zama mukayi a gurin muna azkar, rana na fara fitowa muka koma, gado jikinshi na raɓe na kwanta yajanyo ni muka cigaba da barci.

             Zagaye nake a gaban wasu mutane, fuskarsu a lulluɓe, daga ni sai rigar baccina fari amma abin mamaki ya rine ya koma ja, kallona mace tayi tace.
"Zamu baki zaɓi ko rayuwarshi ko na Y'arki duba ki ganta can."
    Juyawa nayi naga Nur ce a kwance ansa kanta a tsakanin wani abu za'a datse wuyarta, mik'ewa nayi zanje gurinta suka dawo dani, kallona namijin yayi, yace.
"Idan Mustapha da Sadeeq suna raye sunanmu mabarata, sannam itama wancan ta gaji abinsu, ki fanshi rayuwar y'arki dasu."

             Wani kofi suka kawo fari me ɗauke da jini, wanda suka ɓolla cinyar Nur suka kawo min fuskana, zasu ɗura min. A firgice na tashi ina salati wayam naga ɗakin baya ciki, hijab ɗina nasaka nafito da sauri zuwa ɗakinsu.

  Duk sun hallara falon har da Yaran amma babu nur ko kallonsu banyi ba na shige ɗakin kwance take,  ita ɗaya sai juyi take tana nishi, ina zuwa na ɗagata sama jini na gani daga cinyarta, wani bakin tsuntsune ya dira a window ɗaki ya jefa min wata jar takarda, mikewa nayi jikina na rawa naje har gaban takardan na ɗauka, ina warwarewa na naga rubutu kamar haka.

     *_Bama rantsuwa akan abinda zamuyi kuma bama fashin aikatawa ki duba, jikin yarki mun warka da ita wannan shine gargaɗin farko."

                            *Shadow*

     Dafani akayi a firgice na fasa ihu tare da, ja baya Sadeeq ne a tsaye, gurin nur na koma babu jini babu almarshi, mantawa nayi da abu a hannuna, jin wani mugun zafi yasa na yarfe ina dubawa naga kunar wuta.

    "Ya Allah" abinda na iya furtawa kenan na ɗauki nur zuwa ɗakinmu, kuma yana biye damu.
            Man habbatul sauda na ɗiga me ɗauke da addu'o'i abin mamaki take gurin yayi baki can wani hayaki ya tashi, yabi iska kwalla ne masu zafi suka zubo min.
        
Tashi nayi na ɗauki nur zuwa falo, duk sun gama cin abinci zasu tafi aiki, shan gaban Daddy nayi cikin rawan murya nace.
"Miye kayi musu ne hka? Mi yasa fansarsu bai tsaya akanka ba..."

     "Amaratuuuuu." Sadeeq ya kirani da karfi.
       D'aga hannuna nayi alamun ya dakata min.

          "Mi yasa suke niman rayuwar Y'ata  da namijina."

           "Kee Amra ya isheki haka mahaifina ne fa." Sadeeq ya tadaka min tsawa.

           "Ai toh me yake ɓoyewa, ka bincike shi akwai abinda yake ɓoyewa."
       Raɓa gefenmu Daddy yayi ya wucce har ya kai bakin kofa yace.
"Young lady xan baki shawara karki saka kanki a bincike ko ki saka wani Sanin Wasu abubuwan na da wuyar faɗuwa, mafi alkhairi kaja bakinka kayi shiru."

    Ajiye nur nayi zan bashi da gudu sadeeq ya dawo dani ya ɗaga hannunshi, kallon cikin idanunshi nayi nace.
"Try it"
         Sauke hannunshi yayi ya dunkule ya shiga naushin bangon gurin, har sai da na rike hannun, a fusace ya fauce yace.
"Yau zamu bar kasan nan har da Yaran."
               A gigice nace. "Babu inda zani. Kaima nimanka suke ruwa a jallo."

   "Dani dake waye mijin." cike da tsiwa nace.
"Matsalarka ce amma baxanje ko ina ba."

          Dawo dani bayayi zuciyarshi na zafi yace.
"Kina kure nifa."
      "Ai nafi son naga fusatarka toh kaji kana zuwa sunanka matacce dalla malam cikani." na kwace rigana na ɗauki y'ata zuwa ciki ɗakina.
        Tausayi Yarinyar ta bani, akan me ita da bada cin nanin ba amma nanin zata cita.

         Har dare ban leka waje ba, suma sauran yaran dawowa sukayi gurina duk na lulluɓesu, a jikina, kuka nasaka ina kallonsu.
   . Jikin nur ne yayi sanyi na kalleta naga Idanunta na haurawa Sama, bansan lokacin da na fashe da kuku ba, ɗaukar yarinyar yayi daga cinyata ya fita da ita, har ɗakin Daddy ya dire mishi ita yace.
"Daddy Ga Nur nan na kawo maka ita, bansan mi yasa ake niman fansa da ranta ba."

             "Abubakar Sabida naki biya musu bukatarsu na mallakawa F.R Baba filin shi kuma ya rigada ya kafa cibiyar shan jininshi a gurin, tare da taimakon na kusadani."

                "Toh meye na sakani a cikin husumiyarku, bani. Ba har Yar cikina tashiga Yau jirgin karfe sha biyu zan bi zuwa lagos, zan tafi da Ita kai kuma ka,zauna kaci abinda ka tara."
   Juyawa yayi zai fita Mahaifin ya riko shi, cikin tashin hankali yace.
"Idan zafi yayi zafi a sahara, toh ko ruwa ka kai bakinka, zaka ji shi tankar wuta ce, karka saka kanka a uku dan fitarka bazai zama da sauki ba, tsalle ɗaya ake a faɗa rijiya sai anyi dubu....."

   "Kenan na zauna ina gudun hijira sabida makiyana hhhh ji min Papa, toh ai ba damuwa ka naɗe hannun kana gudu nima bari na naɗe hannun mu cigaba da zabga gudu. Ko mutuwa nayi bana fatar tashi a rago balle kuma ina raye."

   Har ya isa bakin kofa ya juya yakalle Nur yace.
"Addu'a zaka mana na fatan nasara ita kuma gata nan a gurinka ka tuna da Mahaifiyarta."

   Yana gama faɗar haka ya fita daga ɗakin,

   Fita yayi daga cikin yayiwa drvn magana ya fito da mota zamu tafi. 
      Yana dawowa ya gamu da Imran yace.
"Kabar sauran yaran ka tafi da nur ɗin."

        "Shi knn" yace mishi,

      Koda ya shigo kayanmu ya shiga haɗawa har da na nur, ina kallonshi, Daukar Abul yayi ya fita dashi zuwa ɗakin Inna wuro sannan ya dawo ya ɗauki. Ihsan ya kaita ni kuma yana shigowa yace.
"Zaki iya tashi mutafi."

      Mik'ewa nayi na ɗauki hijab ɗina muka fito, ajiye kayan yayi a bakin kofa kafin ya koma ɗakin Daddy, ya sameshi a jikin window.
      "Sosai idanu suka rufe akan wasu ababen rayuwa, wasu sukanyi kokarin rufe gaskiya bayan sunsan bata rufuwa, a koda yaushe mutanen duniya sukan bibiyeka ne dan karfin ikonka ko ɗaukakarka, abin takaici a cikin kashi ɗarai da suke kambama Al'amarinka fuska uku garesu wanda zai zo da fuska biyu shine saukakken makiyi masu fuska uku, al'amarunsu da wuyar ɗauka, koda wasa karka ɗauki ɗaukaka ko Suna a wata maudu'i ta burge a duniya, ɗauke shi duniya Me yayi , me wuccewa ne. Yarona ina maka fatan.alkhairi."

        Sam ya gaza fahimtar wannan juyayyar maganar da mahaifinshi, kawai yarshi ya ɗauka yayi waje da

Please Login or Register in order to submit comment