Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ita, kwalla ne suka zubo mishi daga idanu wani wardrob ya buɗe, sai ga takardu sak irin wanda aka turowa Amratu,

       Komawa yayi ya zauna jikin window ɗakin diran tsuntsuwa a gabanshi ya gani, kura mata ido yayi take ta girgiza ta koma mace me suffar ɗan adam rabi tsuntsuwa.
            Murmushi tayi ta zauna akan iska tace.
"Ka kuɓutar da kanka, kuma ka kuɓutar da sauran ahalinka, Ka cire soyayyarshi a zuciyarka dan mutuwa zaiyi kaima zaka dauwwama a bakin ciki,."

   Dariya yayi yana kallonta yace.
"Been knn ce miki akayi shi ɗin lusarine, lokacin lalacewarku yayi karshen zalimcinku zai fara daga yau."

          Ihu tafasa tare da ɓacewa, rike wuyarta yayi da wani bulala, yajanyota zuwa, sai da suka lulla cikin gajire, kafin ya makata da kasa, ya buɗe wani keji ya wullata.
    Ya dawo gurin Daddy wanda ya jima da suma. Ruwa ya watsa mishi, yana farkawa ya sanya mishi barci yabar ɗakin.

             ****
   Duk mutanen gidan sun fito ganin ina kuka rungume da yarana, suma suka shiga zubda kwalla haka yazo ya rabani dasu.
      Muka fita kuka na saka mishi nace.
"Yarana!"
       "Daman dasu kika zo?"  ya wurga min tambayar girgixa kaina nayi, sannan nace.
"Amma wnn shiga hakkinmu kayi dan bana son rabuwa dasu."

      "Haba wanda ke cikinki fa? Da kuma wanda ke hannunki! Ina zaki kaisu?" ya sake jefa min tamvayar,
     Cikin kunar raina nace.
"Wai nikan laifin mi nayi ne? Da kake caɓa min gana son ranka, ɗazun ka ɗaga hannu zaka mare ni yanzun kuma bakaken magana masu zafi haka."

            Janyo ni yayi jikinshi yayi yana bani lallashina, har jirginmu ya tashi kuka nake, ga nur cikin wani hali haka nayita kokarin kula da yarinyar.

              ***Bayan tafiyarmu Kuka Meemah ta zauna tayi tasaka kuka, dakyar Inna wuro taja ta,zuwa ɗakinta tayi ta nasiha har tayi shiru.


Ga baki ɗaya gidan babu wanda yayi bacci cikin jin daɗi, tsabar damuwa tayi musu katutu.

****
Karfe goma nasafe muka sauka a lagos idan kaga fuskana kamar, an kwaɓa cincin wacce taji yist tsabar nayi kuka ina rungume da yarinyar shi kuma, yana rike da jakarmu, gurin sayan ticket yaje ya sayi na Yola, daga yanda yake magana nasan can zamuje.

Yana isowa ya amshi yarinya yace min,
"Sha ɗaya jirgin yola zai zo zan wucce can ke kuma zaki bi jirgin Bauchi ynx nan."

D'ago idanuna nayi wanda suka ja na zuba mishi murmushi nayi, sannan nace mishi.
"Babu inda zani ai gudu ya kare........"

Kuyi hakuri bana jin daɗin jikina ne.....
Follow#Mai_Dambu
🌺🌷🌷
*_DA CIWO A RAYUWATA_*
🌹🌸🌸
         
    _Himma bata ga ragu_
Na
Mai_Dambu
Wattpad:Mai_Dambu...
      *Gudu ya kare*
Not Edit👎
*Page=S...Sark'ak'yya*

A hankali ya tako gabana ya durkusawa yayi ya,duge kafarshi ɗaya yayi a kasa ya share min kwallar dake sauka a fuskana yace.
"A'a Hayati, kar muyi haka dake, tashi ga jirginku ya fara ɗiban mutane"
    
      Kukan da nasan bai da amfani na sake mishi nace.
"Dan Allah fa,"

            Motso da fuskana yayi tap ɗinshi kafin yace.
"Pls nace zanzo na dubaku."
    D'ago yayi ya rakani har cikin jirgin ajiye nur nayi na juya na rungume shi tare da sake kuka me taɓa rai nace.
"Karka manta damu, karka manta da Bayan da zaka bari, ga wani ma bansan mi zance mishi ba."
    Kai hannunshi nayi kan cikina nacigaba da kuka, janye jikinshi yayi yace.
"Ubangiji yana tare damu."
    Goshina ya sumbata kafin ya koma kan Nur ya sumbaceta k'in juyowa yayi balle naga kwallar dake bin fuskarshi, har zai fita ya tsaya ya juyo kaɗan yace.
"Karki kirani idan na matsu zan nimeku, sannan akwai Atm card, a jakarki da number cire kuɗi a asusun."
 
      Yana gama faɗar haka ya bar cikin jirgin kuka na cigaba har fasinjoji suka shigo,

                     Rungume Nur nayi ina shafa bayanta, har muka tashi daga lagos zuwa Abuja. A can muka sami jirgin bauchi mun iso bauchi ɗaya saura, Mubarak yazo ya ɗaukemu.

     Tunda muka shiga mota da muka gaisa ban kuma ce mishi kala ba har muka iso gida, s gaji nake ɗaga kafana na shiga palon baffa zuɓewa nayi na fashe da kuka, me cike da ruɗani tambayana suke amma ban basu amsa ba, sai danayi ya isheni sannan na buɗi baki na far musu bayani.
     Sun matukar razana jin irin abinda ya faru damu kuma bamu taɓa faɗawa kowa ba, karɓan Yarinyar Nenne tayi ta suka shiga ɗaki na cigaba damusu bayani.
D'ago kaina nayi cikin zubda kwalla nace.
"Baffa ina son shiga yola goba da safe."

     Murmushi yayi cikin nutsuwa yace.
"Allah ya kaimu, indai wannan ne mai sauki ne  amma Allah ya rufa asiri."

             ....
     Karfe biyu da rabi ya sauka a Yola, yana fitowa ya ɗauki jakarshi zuwa waje mota ya ɗauka zuwa, lamiɗo Estate.
            Har bakin get aka sauke shi ya ɗauki kuɗinsu yabawa drvn sannan ya isa bakin get ɗin zai shiga masu kula da get suka yo kanshi zuba musu ido yayi har suka karaso babban yace.
"Malam an san da zuwanka ne."
    Saka hannunshi yayi a aljuhunshi ya mikawa mutumin musu card ɗinshi.

        Kallon renin hankali mutumin yayi mishi sannan yace.
"Ai kaine the own estate ɗin wai toh ai oga bai faɗa mana zaka dawo ba dan haka kaje ka nime haɗuwa dashi."

         Ko kulashi Sadeeq baiyi ba ya buɗe get ya shiga mutumin ya cigaba da binshi yana rena mishi hankali kallo ɗaya Sadeeq yayi mishi ya juya,

                      Kaii tsaye gurinda ake ajiye motoccin, aiyukan gidan yaje ya buɗe inda Keys suke sannan, ya ɗauki wata mota ya nufi gidanshi.

         A get six ya hango wani mutum yana shiga dajin da sauri ya tsaida motar ya fita yabi bayan mutumin.

             Sai da sukayi tafiya me nisa sannan mutumin ya juya, yana kallon Sdeeq dake bin bayanshi.
               Da sauri Sadeeq ya isa gurinshi, yana isa yaga Imamun masalacin estate ɗin ne, ajiyar zuciya ya sauke kafin yace.
"Malam Hamza mi yashigo da kai wannan dajin?"

              Kan Imamu a sunkuye ne, bai ɗaga ba har sai da Sadeeq ya sake maimaita kalmar kawai ya ɗago kanshi, fuskarshi a zaizaye kama an zuba mishi ruwan b3, kwayar idanunshi fari sol, baya Sadeeq yaja, Malam Hamza yayita kyalkyalewa da dariya,

             Wani irin sura yakaiwa Sadeeq, ai kafin ya Isa ga Sadeeq Uwais ya makashi da kasa, take suka rungutsume da faɗa inda Malam Hamza ya koma kura, wani irin faɗa suke nafitan hankali cikin Ikon Allah Uwais ya naɗe kuran ya mikar da shi sai da yakarya mishi kasusuwa sannan ya cillashi gefe take, ya birbishi yabi iska.

      Girgiza jikinshi yaƴi a gaban Sadeeq ya mika mishi hannu ya mike.
"Ayya sannu, ai akwai tashin hankali a cikin dajin nan da baka biyo shi ba, muje na raka ka gida." Inji Uwais knn,

         Ajiyar zuciya ya sauke kafin yace.
"Zuwanka yayi amfani badan kai ba ai dabankai labari ba. Nagode"
         "Ba damuwa yiwa kaine."
       Haka sukayi ta taɓa hira har suka fito Sadeeq yashiga motarshi zuwa gidanshi.

           Koda yaje yaga kome a birkice, dan haka ya kintsa abinda zai kintsa kafin ya tattara kayanshi tsaf da na amfani ya dawo get, five kusada gidan Adda Mairo.

     Ya shiga gidn yasamu Uncle Hamidu cike da mamaki ya mike yace.
"Sadeeq kaine kuwa?"
          "Gani nan kawu ina raye ai."

    Murmushi yayi ya kira Adda mairo suka ganshi kafin kace me tuni an shiga faɗawa yan uwa da abokan arziki.
   
           Lokacin da Nanah taji labarin Zuwanshi ɗaukar Yarta tayi me shekara biyu da wani abu tazo har gidan tana haɗa ido biyu dashi jiknta yayi bala'in Sanyi kallon Babyn yayi ya mika mata hannu tabashi ita, ɗago kai yayi sannan yace.
"Kiyi hakuri bansan na tafi nabarki da cikina ba, ai ko ba kome nabarki da aiki."

        Sanin cewa Yarinyar ba yarshi bace kawai yasa tasake mishi, kuka janyota yayi ya shiga rarrashinta, hira akayi sosai inda suka tambayeshi Amratu yace musu tana nan lafiyarta lau da yaran.

Daga gida suka dawo shi da Nanah, yana ganin yanda, take ɗari ɗari dashi yasa janyota jikinshi.

****
"Alhaji ina ganin tunda yaron nan ya turo amratu zuwa gida ai yasan dalilin da yasa ina babu amfanin turata, tunda yace karta je wani abu ya faru da ita kaga ai ba'a yauka mishi ba." Inji Nenne knn,

Shiru Baffa yayi kanshi a sunkuye kafin ya ɗago yace mata.
"Nima nayi tunanin haka kiranta."

Ina zaune Nenne tashigo tasame ina bawa nur, abinci dake jikin da sauki tunda Nenne tayi mata hayaki tare da bata wasu maganin Islamic , shi kanshi hayakin Habbatul saudan ne da, sanya ta haɗa sai tafarnuwa.

Da kuma addu'a, tare da ita muka fito ina rike da Nur tana rike min da abincinta. Bayan na gaidashi kallona yayi cikin nutsuwa kafin yace.
"Amratu kiyi hakuri da abinda zance ki zauna a nan har mijinki yazo kamar yanda yace, karki je asami matsala kinga zai ɗaukemu dattawan banza."

Sunkuyar da kaina nayi kwalla suka zubo min gyaɗa kai nayi nace.
"Shi kenan baffa duk yanda kace haka za'ayi."
Kuma dana amshi maganarshi sai na hango fa'idar haka, domin masu niman shi zasu iya bibiyar al'amarinmu tunda idanunsu nakanmu. Haka na mike zuwa ɗakina nida Nur muka zauna hira nake mata tana kallona, can na kuna karatun alkur'ani take ta kwanta a jikina tana sauke ajiyar zuciya.

****
Bayan sallar Magrib yana zaune a bakin masalaci Malam Hamza yafito kallo kallon sukayiwa junarsu, take jikin malam Hamza ya ɗauki rawa da sauri ya nufi gidan Sadeeq ya rufa mishi baya har suka fara barin area gurin wata mota kiran sharon tazo da gudu tayi kan malam Hamza,

"Kaiiiiiii" Sadeeq ya kwala musu kira, Ina motar tayi gaba.

Da gudu yaje gurin da Malam Hamza ya ɗago shi jini ke zuba a hancin mutumin yace.
"Kayi namijin kokarin ganin bayan Kawun....."

Tarine ya sarkafeshi sosai ga jinin dake zuba daga hancinshi da kunenshi girgiza shi Sadeeq yayi yace.
"Waye a cikinsu."
Rike rigar Sadeeq yayi zaiyi magana take ya koma duk yanda Sadeeq yaso taimaka mishi dole ya bar gurin yaje masalaci ya ɗauko motarshi kafin ya isa gurin yaga motar nan ta dawo ta haye kan Malam Hamza da masifaffe gudu Sadeeq ya bisu, abin mamaki suka ɓace yanda baya hangosu dawowa yayi ya ɗauki malam Hamza zuwa asibiti koda yaje dakyar suka amshesi,

Shiru yayi yana tunanin waye ne a cikin kawunanshi yake bibiyarsu.
Fitowar likita cike da damuwa ya kalli Sadeeq yace.
"Kayi hakuri fa, mutumin da ka kawo ya mutu."

Cikin sanyi jiki ya ɗago kai, cike da damuwa ya mike yace.
"Ok nagode."

Bayan tafiyar likitan shima ya dawo gida inda yaje yasamu ana jajje malam Hamzan anan ya faɗa musu ya rasu, gawarshi tana asibiti.

Gidanshi ya koma ya sami nanah taci kwalliya, ko kallonta bayi ba ya shige ɗakin zama yayi a bakin gado yana tunani.

Dakyar yayi wanka da alola ya fito kallon miro yayi, cike da damuwa amma baiga kome ba.
Jallaɓiya yasaka ya gabatar da Sallar isha da kuma shafa'i da wutir,

Ya jima a zaune yana nazarin waye ne.

Jin iska tare da tawowar Turaren Imran yasa shi mikewa , ya zauna a bakin gado.
Har bayan awa guda yana jiran Imran kafin ya iso.
Sallama Imran yayi sannan ya zauna yana kallon Sadeeq yace.
"Baka sami kome ba? "
Girgiza mishi kai yayi, cike da damuwa.

Dukar da kanshi yayi cike da damuwa yace.
"Yau wani abu yaso faruwa sai Allah ys kawo min ɗauki ta sanadin Uwais, toh mutumin da ya mutu shi naganshi a gurin bayan mun fito sallar magrib ne kuma."

"Duk wanda yasan wani abinsu kasheshi zasu abinda na kasa fahimta shine, waye Inuwar nan" Inji Imran,
"Ni abinda na fahimta mutum ɗaya ne ke aiki da mutane,"

Ihun mace suka ji ta bayan gidan window suka leka. Ganin wasu kartin maza sukayi sun rufawa wata mace baya sun nausa dajin.
Da sauri Sadeeq ya juya Imran ya rike shi yace.
"Babu kowa sidabarune so suke su kasa maka hankali ka nutsu yanzun zaka sake ganin abin mamaki."

Dawowa yayi sai ga Malam hamza shime a guje, da kayanshi ko cirewa ba'ayi ba yace.
"Koma waye zai iya yin fiye da haka jibi kaje ka ɗauko Amratu, nan ne zaka fahimci mutanen sun wucce haka."

Zama yayi dafe da kanshi, yana nazarin maganar Imran.

Haka suka raba dare suna jiyo hayaniyar mutane suna kai kawoa gurin, amma basu fita ba dariya Imran yayi yace.
"Abokina kasan miyasa suke haka sabida, su buɗa maka kai matukar razana dasu sun gama da kai kuma bazasu barka ba sai sunga bayanka."

"Eh na gane haka kawai ina nazarin abine sabida kawai manta."

Haka suka raba dare da hiran karshe suka mike dan raya daren suna fara sallah kome ya tsaya cak.

****
Washi gari da wuri Sadeeq ya tashi ya shirya ya nufi masalaci shida Imran, bayan anyi sallah ne aka faɗi lokacin da za'ayi sallar gawar Malam Hamza.

Karfe tara akayi sallar gawar, kallon Kawu Aminu yayi sabida yaga yana mishi kallon mi kana raye ne dama.?

Murmushin baka sani bane Sadeeq yayi mishi. Har aka dawo daga makabarta ta wucce kamfaninshi inda yaga cigaban da kamfanin ya samu bai wani damu ba ya dawo na nasu ns haɗaka nan yaga kome ya taɓarɓare. Office ɗin Kawu Aminu ya shiga ya same shi ya kifa kanshi da table.
Tap ɗin table ɗin Sadeeq yayi da karfi ɗago kanshi yayi sukayi ido biyu da sadeeq wani irin takaici ne ya rufe shi cikin masifa yace.
"Da Allah ya ɗagaka daga masifa ya kaika inda zaka sami nutsuwa mi yasa ka dawo nan?, mi yasa Abubakar? Mi yasa bazaka zauna da Iyalinka a can ba kasake dawowa cikin masifa."

Mamaki goma da ashirin suka rufe Sadeeq kallon Aminu yayi cikin kokwanto yayi a ranshi yana nazarin abinda yake faɗa.
Ajiyar Zuciya ya sauke kafin yace.
"Ban fahimci mi kake nufi ba, Kuma abinda kake faɗa yana sani shiga ruɗani, nifa na dawo gidane bani da wani damuwa da abinda yake faru."

"Ka sani sadeeq kana ɓoye tsoronka ne kawai amma zamanka a nan akwai hatsari ka koma inda kafito Na haɗaka da Allah."
"Aikuwa babu Inda zani sai anyita ta kare dan bansan inda zan sake nufa ba koma waye yake bibiyata sai ya shirya dan na dawo za'ayita ta kare." Inji Sadeeq.
"Wai mi yasa ka cika taurin kaine haka nace ka koma inda ka fito." Inji Aminu,

"Idan na koma aikuma ba tsira kukayi ba daga sharrin sa waye ne haka kuke mishi tsoron mutuwa haka." Inji Sadeeq.

"D'aya daga cikinmu ne kuma....." Turo kofar akayi duk suka juya, Hamidu, da Junaid ne sai Bawa da Bilya, duk suka shigo Office ɗin lokaci guda Jikin Aminu ya ɗauki rawa, kallonsu Sadeeq yayi yana murmushi ya juya yaga yanda Aminu ya koma sai zufa ke karyo mishi sharaf a koma, kujeranshi suma niman abin zama sukayi.

"Kawu kayi shiru bayan kace min mi niman kasheni a cikinku yake aiga Yan uwan naka waye a cikinsu ?" ya wurga mishi tambaya duk a razane suka zubawa Sadeeq Ido taɓe baki yayi "toh koma Waye Shadow da zaran na kamashi da hannuna sai ya faɗi gaskiyanshi dan tauneshi xanyi ko kashinsa baza'a samu ba."
Har zai fita ya isa bakin kofa, sai yajuya yace.
"Ina Yaro akwai ɗaya daga cikinku da nake kiranshi da Ninu."
D'if kamar an ɗauke wuta haka office ɗin yayi, sake gyara murya yayi yace.
"Ai nasan ku baku manta ba Waye nake kira da Ninu."
Aminu Bilya ya nuna Hamidu, kai Aminu kanuna Junaid, bawa Ya nuna Aminu.
Dariya Sadeeq yayi yace.
"Haba kawunaina ya kuka ruɗe kaman nace ku kamomin Shadow nifa wanda nake kira da ninu nake nima."
Murmushi Hamidu yayi yace.
"Sadeeq kaida kayi abin ka manta sai mune zamu tuna maka."
"Kuma haka ne kawuna ni kaina na manta nabarku lafiya ku sha ruwan sanyi har da Shadow ya kurɓa amna ba irin wanda akewa Jini ba." Yana gama faɗa musu haka yayi waje abinshi.


Dukkansu fita sukayi zuciyarsu cike da zargin juna, amna wanda ya zame musu tashinhankali yafi su damuwa.

****
Dariya Sadeeq yake bayan ya kalli Imran yana bashi labarin abinda ya faru.

"Maganin biri kare maguzawa toh amma kasan mi yasa nace kayi musu haka, duk zasu tsargu har dashi shaiɗanin amma bari mu zuba musu ido kafin nan da wani lokaci.." Inji Imran.

"Eh nifa akwai abinda nake tunani akan Aminu."

"Kyaleshi ni dai ka muje bauchi gobe,"
Shiru Sadeeq yayi sannan ya ce.
"Mi yasa ka damu da muje can."

"Sabida ta sanadin haka zaka ɗauki haske sosai amma dole da wani abu dana shirya maka kai da Amratu kawo kunnenka.".... (Banda tsabar hassada shine baza'a barni naji gulmar ba can ta matse maku)

Zaro ido Sadeeq yayi ya cike da takaici yana kallon Imran ɓata rai yayi yace.
"Allah baxan iya ba nemi wani mafita kutt ni ɗin zaka janyowa bala'i."

Dalla mishi harara Imran yayi yace.
"Toh ragon maza ba kai kaɗai ba har da ita sai munje sai muji ta bakinta."0

Haka sukayi ta shirya nasu gadar zaren, har washi gari zuwa gidan kawunanshi yayi ya musu sallama.

****
Kwana biyu da bama tare na shiga damuwa, muna kwance da Nur wacce take bacci wajen Azahar sai ga Nenne tashigo da sallama mikewa nayi na zauna murmushu tayi sannan tace.
"Baban Nur ya iso kitashi ki haɗa mishi abinda zai ci."

Cike da jin kunyarta na mike zuwa kitchen zogalen da nace a dafa min na ɗauka na juye a katon roba na ɗauki kuskus, na juye akai kayan haɗin da zanci da zogale na juye amma ban saka tumatiri ba,


Maggi nasaka ns juye akan wuta bayan na yayyafa mishi ruwa.

Zoɓo na ɗauka na wanke sannan, nasa kanunfari citta rufe ya cigaba da duba dambuna. Buɗe firij ɗin nayi na ɗauko kifi na wanke tass shima na,zuba mishi kayan spices,

Qcumbe na ciro da Guave na wankesu na yanyanka na zuba a bleader na markaɗasu na, buɗe zoɓon nayi na zuba sannan a ciki na kashe wutar.

Na cigaba aikina a nutse har na juye dambu, na duba kifin shima da sauran kaɗan.

Kan zoɓon na koma buɗe turirin yafita haɗe da kamshin guave da qcumber, ajiyeshi nayi yasha iska, ina motsawa har ya fara huccewa, kankara najefa a ciki da tiara sai sugar ɗan kaɗan.

Na rufe, kifina na sauke na juye a kular biyu, sannan dambu ma haka bayan na gamasu nasaka akan wani tire na koma jikin zoɓona yayi sanyi taccewa nayi na sake farfasa kankaran na zuba a ciki ina gamawa na wucce ɗakina nayi wanka nida Nur na mana kwalliya.

Ita wani gown na yara pink da whiter nasaka mata, sai ban ɗin rigar,da takalminta irin kayan.
Ni kuma nasaka riga dazani sharoton ruwan goro, ɗinki yayi min ɗasss gyalena irin kayan na saka nafito falo naga baya nan, niman guri nayi na,zauna suna hiransu sai raba ido nake can mubarak yayi dariya sannan yace.
"Malama Adda kije ɗakin baki yaron nan yana ciki."

Pillow kujeran falon na jefa mishi cikin mita nace.
"Baffa kajawa Muba kune fa, ya zuba min ido."

"Kaiiii muba kwashe idanun da ka zuba mata." Inji Baffa,



Please Login or Register in order to submit comment