Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mijin fa"

        "Tir Allah ya sauwaka ba daini ba ina zankai wannan tsohuwar nifa burina na auri yarinya yar sha bakwai wacce zan moreta ta moreni ina zan kai guzuma irin wannan wllhi na aureta toh na shiga uku."

  Shi dai Imaran baice kome ba har suka fito waje.
             Tunda na shiga cikin gida gabana ke faɗuwa dan saura mintuna goma idanuna akan agogo har lokacin yayi.

      A falon baki yan uwan H.O.D ɗinmu ne suka zo akan an fasa tashin hankali bayqn sun gama bada hakuri sun fitane Ya Abbas ya fito sallamar mutane anan yake faɗawa ma'aikatan gidan haka kawai sadeeq yaji sun bashi tausayi riko hannun Ya Abbas Sadeeq yayi suka koma ciki, ya zuɓe a gabansu shiru yayi kafin yace.
"Idan bazaku damu ba a maida auren kaina da matukar nauyi a sallame mutanen da sukayi dogon tafiya haka dan shaida auren."

             Gyaɗa kai sukayi da yan uwan baffa sun amince fita akayi gurin ɗaurin auren aka ɗaura da Sadeeq Mustapha, abin yabawa mutane mamaki yanda al'amarin ya sauya farat ɗaya.

    Lokacin da labarin auren yaje mana cikin gida babu wanda yafl faɗa min sai wata kawatq takirani tana tambayata waye kuma sadeeq aka ɗaura aurena da shi.
     Fitowa nayi naji wasu nacewa.
"Allah ya biyashi yafitar damu kunya ai tunda ya aureta Allah sarki yayi kokari koma dan waye mutumin kirkine."

          Hannuwana nasaka akai na fasa ihu sosai kafin na zuɓe sumammiya, ruwa aka ɗauko ana zuba min amma ban farka ba, ɗakina aka maidani ana min fifita, har natashi da gudu na sauka agadon nafito waje falon Baffanmu ina kuka, nace.
"Baffa ka rufa min asiri karabani da wannan yaron mi zancewa kawayena kanin bayana nake aure don Allah ku sa shi ya sake ni."  

      "Shiru yayi na kallona kafin yace.
" Amratu kiyi hakuri kuma kiyiwa mijinki biyayya shine fatana dake yaron nan ya fiddamu kunya a gaban dubannin mutane karki zama mai butulcewa Ubangiji mana."

       Bansan mi yake faɗa ba anan dai na zuɓe asume, akayi asibiti dani ban farka ba sai dare duk yan uwana suna zaune ganin na farka suka yo kaina daka musu tsawa nayi nace.
"Wallahi karku zo kusadani indau bazaku rabani da wancan yaron ba."

  Take na shiga fisge fisge ina cire robar ruwan kowa yazo kusadani duka nakai masa,  har likitan tsoron taɓani suke, shigowarshi yasa yayuna suka fita takowa yayi har inda nake ya kama hannuwana ya murɗasu sannan ya haɗini da kirjinshi ya matseni a hankali yacewa likitan.
"Zo kuyi mata dress ɗin"

    Cikin hanzari suka shiga maida min abinda na cire sannan aka saka min alluran bacci, a hankali na shiga cewq.
"Wallahi sai ka rabu dani bana son wannan kaddararren auren naka mugu ɗan iska kacikani ni bana son ka kara taɓa ni banxa ɗan kauye."

      Bacci mai karfine yayi gaba dani, ban farka ba sai washi gari,

    Ina tashi aka cire min ruwqn naje nayi alola da wnka sannan nazo na gabatar da sallolina inayi ina kuka, shigowa yayi tare da sallama shida kanina mubarak, sai hira suke nan ya durkusa ya gaida Nenne sannan ta mike mubarak zai maida ita gida.
    Suna fita na ɗago idanuna nace.
"Mara zuciya kawai inka isa ɗan halak kasake ni nace inba haka sai nayi maka wulakanci a garin nan"

     Murmushi yayi yana gyara tsayuwarsa yace.
"Haka ko?"

     A fusace nace.
"Wallahi kanemi raina min hankali zan baka mamaki yaushe aka gama maka wanka da zaka fara tunanin aure, waton tashen balagarka ta motsa shine bari kanemi auren sa'ar yayarka ko, dubeka kai har kakai cikakken namijine a gurin"

        Tsura min ido yayi inata zaginshi da kiranshi yaro babu abinda ke ɓata masa rai kamar kalmar yaron nan.

            Da yagaji da rashin kunyanta zuwa yayi gabana ya tsaya, take na haɗiye bala'in da nake sakamakon make min baki da yayi aikuwa na fashe da kuka, sosai ko a jikinshi zama yayi a chair yana kallona nu kuwa tsakanina da Allah nake kuka na tare da cewa.
"Wallahi sai ka rabu dani."
        #Fiction
#Spirits
#Jinn
#Amsad......By Mai_Dambu
🌺🌷🌷
*_DA CIWO A RAYUWATA_*
                                  🌹🌸🌸


   Na
  Mai_Dambu
   Wattpad:Mai_Dambu

         Da sunan Allah Mai Rahama Mai Jinkai




Page D.

"Wallahi sai ka sake ni dubaka yaushe ka girma da har zaka iya rike mace guda nawa kake mi zaka iya bani dame zan kiraka mijina kana karamin yaro sai tsabar jaraba tsiya wallahi sai kasake ni."

Lumshe idanunshi yayi yana mai jin zafin maganata, dariyar Imran ce tasake harzuka shi ya kifa hannunshi akan fuskarshi imran yace.
"Zan baka guri ka nuna mata girmanka da irin darajarka don Allah ko sau ɗaya ne."

Tsaki yayi cikin ɗaga murya yace.
"Hmm daɗin abun rufa miki asiri nayi guzama dake wacce ko abinda yan mata suke takama dashi baki dasu shine zaki takura kanki ni sabida Mahaifinki na karɓr aurenki inba haka ba ɗan 28 zai auri guzuma mai shekaru kusa da kabari 30 da ɗauri fa gaskiya na cutar da kaina"

Mikewa yayi yazo har dai dai fuskana yace.
"Ni budurwa yar karama nike nima wacce kirjinta ke cike da ɗanyen yan matanci, kuma wacce kofarta yake tsuke babu alamar girma sun dafar da kofar ko daɗewar shekaru, kinga nifa wacce zan shafa kirjinta nasan na ɓata mace ba wacce zan shafa kamar na shafa kirjin kadangariya ba."

D'aga min gira yayi tare da kashe min idonshi ɗaya, tureshi nayi cikin ɗaga murya nace.
"D'an iska kawai mara mutunci."

Shiru yayi ya zuba min ido cike da mamaki dama zan iya zaginshi.
"Ni kika zaga? Kin manta da igiyar aurenki dake kaina ok ba dmw bari na nuna miki yanda ake rashin mutunci na kuma tabbatar miki ni ɗin ɗan iskane bugun farko."

Ya faɗa min,
Komawa yayi ya rufe kofar shigowa, jikina ne ya ɗauki rawa ina niman hanyar sauka a gadon gadangadan yayi kaina ihu da na fasa aikuwa ya saka hannunshi ya toshe min bakina, yana kallona sam bayi da niyyar min kome barazana ne kawai.

Matse ni yayi ya finciko ni daga gadon na sauko kasa, har ina bugewa, ya kalleni sama da kasa, yace.
"Nan kike zagina ashe bakin duk na bugine ki godewa Allah ni bani da ra'ayi akan mace irinki da yaƴ kinga shagali."

Shiru nayi cikin wani irin tsoro wallahi duk rashin kunyar da nake masa duk a bakine dan nasan loma ɗaya zaiyi dani takare min. Amma dukda haka bai hanani gunaguni ba inda nake cewa.
"Ni dai ka rabu dani kawai dan ba zan zauna dakai ba."

"Matsalarki ce ki zauna dani ko karki zauna dani amma kafin nan kije ki nemi izinin rabuwa dani a gurin Alhajinku sai idan yace na rabu dake shi knn dama nima inda wacce zan aura, yarinya karama wacce ko bata saka bra me soso ba akwai su ba karya.

Jan tsuka nayi na kuma ce masa.
"Ɓanxa mayen mata."

Wannan karan kan bakina ya murɗe da hannunshi har sai da yaga bakina ya fashe ya kyale ni, yana murmushin mugunta.

Wasa wasa sai gashi da zaran na zageshi zai buge min bakina har sai yayi jini, kuma yana kallona zanta kuka wallahi ko damuwa baya yi, sai dai yayi ta murmushi, sabida ganin ina kuka kwanana uku a asibitin city aka sallame ni nayi mamakin yands suka mike wani unguwa daban ba gida ba kusan mota huɗu suka rakoni, can madina quarts, inda wani katon gida mai ɗauke da gids Estate har guda takwas muna shiga yara suka taso suna masa Oyoyo Uncle sadeeq.

Fitowa yayi ya shiga ɗaga yaran ɗaya bayan ɗaya, sannan ya komo cikin motar ya mika musu, wata katuwar laida sai ihu suke da godiya,

Su Aunty Mom da su Aunty salma suka fito a hankali nafito nima, nabi bayansu sai Hajja kakarmu da Su Safina da fatima, da wasu daga cikin yan uwanmu muka shiga gidan,

A raina nace wow sabida haɗuwar falon nasan kusan zaɓina ne kayan ciki but yanayi tsarin falone ba ra'ayina bane dan har da gurin ajiye books kome na gidan ya haɗu,

Kallon Aunty mom nayi sannan nayi mata magana kasa kasa nace .
"Aunty Mom waye ya kama mishi wannan gidan dan naga bai da arzikin kama gida irin wannan? Allah yasa ba baffa bane"

Wani kallon banza tayi min kafin tace.
"Ki tambayeshi mana hm baki san waye kike tare dashi ba ko, wawuya kawai kibi a hankali dai."

Tura mata baki nayi sabida naji haushin maganar da tayi min,
. Haka suka gama ganin gidan sannan sukayi mana fatan alkhairi suka tafi, suna tafiya sai ga yaran gidansun shigo nan suka cika ni da surutu har ya shigo suka koma kanshi buɗe frij ɗin falon yayi ya ciro musu ice cream aikuwa suna amsa sukayi godiya suka fita a guje.
Tashi yayi ya shiga ɗaya daga cikin ɗakunan gidan wanda nag mubarak ya hanasu shiga ashe ɗakinshine shiga yayi ni kuwa kamar wacce aka dasani, a gurin bansan ta inda zanfara ba,


Bayan kusan minti talatin sai gashi ya fito sanye da kananun kaya, kallona yayi alamun mamaki sai ya basar ya ce.
"Daga wanca ɗaki zuwa wanca duk nakine wanca ɗayar kuma zaki iya ajiye yar aiki."

Tsaki nayi na mike nace.
"Dake kuma ance maka zaman gidanka nazoyi"
nabar masa falon zuwa ciki, ina shiga naga yanda aka narka min kaya a ciki kome na a haɗe yake, wanka na shiga nayi sannan na fito nayi sallah na saka riga da skirt na atamfa, dake rigar akwai bras cop ban saka bra ta ciki ba nafito abuna na shige kitchen.

Kayan abinci nagani ba kayan miya, tsaki nayi na daga indomie da bashashen kifin dake cikin kwalin da nagani,

Tun dana fito ban ganshi ba har dare sai gashi da nikiniki kayan danginsu kayan miya, ɗanyen namar saniya da na kaji, da wasu abubuwan bukata ya zuba min a kicin ya fito ya kalle ni, cikin sanyi murya yace.
"Don Allah taso ki ajiye kayan nan inda suka dace karsu lalace."

Shekeke na kalloshi kafin na mike naje kome na kintsa inda ys dace sannan na fito daga kitchen ɗin take away na gani da Habib yohgort ɗauka nayi na shige dasu ki cin na saka a freeza nafito abuna shi kuwa yana zaune ya juye tuwon dawa miyar kuka, da manshanu sai kamshi yake kallon abinci nayi nace a raina girkin Nenne ne wannan kwaɗayayye ya amso.

Haka muka cigaba da rayuwa a cikin gidan ni dashi kowa harkan gabanshi yake, idan ya gaji da sayan abinci sai yazo ya dafa da kanshi ana haka ranar sai ga mubarak yazo bansan yana falon ba Sadeeq ya shiga ɗakina daga bakin kofa yashiga bugawa, haushi da ya kamani na fito nace.
"Uwar me zan maka da kake buga min kofar ɗaki, ko ance maka naxo zamane da kai toh malam tun wuri ka juya."

"Kiyi hakuri abinci nake so nayi bakone" ya faɗa min cikin saukar da kai.
"Bazan girka ba kashiga ka girka muku ni ba baiwarku bace mara kunya kawai."

Karasowa mubarak yayi har inda nake ya zuba min ido cikin kaɗuwa yace.
"Adda Amrah ke ce kike wannan rashin hankali idan wani ya faɗa min bazan yarda ba. Mijinki kike faɗawa maganar banza haka toh Wallahi a kunnen baffa."
Rai aɓace ya bar gidan hararar sadeeq nayi kafin nace.
"Munafuki hankalinka ya kwanta ka shiga tsakanina da Yan uwana da iyayena."

Juyawa yayi jikikshi a sanyayye nima kirjina bugawa yake cikin damuwa amna can da natuna ba lallai bane Mubarak ya faɗa sai na cigaba da tsabgata karshe sadeeq waje ya fita yaje yaci abinci da ya tashi dawowa haka ya dawo dasu fresh milk da duk kayan ciye ciye, ya zuba a frij ɗinsa na ɗaki.

Bayan kwana biyu kwats sai ga Nenne da wasu daga cikin yan gidanmu har ɗaki ya bini ya faɗa min amma na tsagalgale shi da masifa har suna jiyo mu.

Aunty Mom ce ta mike tazo ɗakin tace.
"Sadeeq jeka abinka,"

Fita yayi ni kuwa kirjina ya shiga bugawa tana zuwa gabana ta kwasheni da mari sannan ta finciko hannuna tafito dani falon ta rufe ni da duka, wallahi babu wanda ya amshe ni sai shi da yake saka kaya zai fita nima musu abinda zasu taɓa kafin nagama girki, da sauri ya fito yazo ya kwace ni kamar zaiyi kuka ganin yanda take kifeni da mari, yace.
"Yanxun saboda Allah wannan dukar sai kace wata karamar yarinya kika samu ayya."
. Jana yayi ya kaini ɗakinshi dukda kukan da nake sai da nayabawa haɗuwarshi.....
🌺🌷🌷
*_DA CIWO A RAYUWATA_*
                                  🌹🌸🌸

   Na
  Mai_Dambu
   Wattpad:Mai_Dambu

         Da sunan Allah Mai Rahama Mai Jinkai

Page E.

      Ture shi nayi sannan na cigaba da kukana, hmm munafuki ko inda nake bai sake kallo ba yafita yabarni a ɗakin hakuri ya basu suma shi suka bawa hakuri  suka ce zasu tafi, har gurin motarsu ya rakasu ina hangosu ta cikin ɗakinshi juyawa nayi ina kallon ɗakin, cike da mamaki yanda ɗakin yake kome a nutse yake a ciki gadon ɗakine yayi bala'in mun kyau, kafin ya shigo nafita.

    Yana shigowa na tsaya tare da rike kuguna cikin masifa nace. "wani munafikin ne ya kai musu gulma"

          "Ga zahiri tunda kinyi akan idanunsu."
      Wnnar maganan da yayi ba karamin bani haushi yayi ba dan haka dayazo wuccewa ta gabana, nasa hannuna na finciko masa rigarshi har sai da ta yage, raina ya ɓaci dan haka bana jin zan iya kyaleshi.

     Shima da yake namiji ya gaza hakuri, juyowa yayi ya rike min wuyar rigana, inda ya caccumeni har da boons ɗina, ya kama rigar sai da ya kaita kasa, dan tsananin mugunta kuwa ya riko hannuna ya murɗa min shi baya har sai da na fasa ihu,  murmushi yayi yace.
"Ke nifa bani da, damuwa dake kece kika dami kanki nan da wata biyar aurena,zanyi bani da lokacin fitinarki."

      Sakeni yayi ya shige ɗaki sai lokacin na kalli ɓarnan da yayi min a raina nace *munafuki ya tqɓa min nono da wayo dama abinda yake sha'awar taɓawa kenan tir yaran ynzu da rashin kamun kai*

    Haka zamanmu ya cigaba da tafiya sam ba daɗi nina kafe sai ya sakeni ga rashin kunyar da nake masa shi kuma hidimar gabanshi ya isheshi

     Satina biyu da aure hutana ya kare, dan haka monday inada aiki da wuri na gama kome har miya nayi nasaka afirij abincine har dai banayi dashi dan babu wanda zai min dole idan nayi bakine nake bashi dake bai saba ba, sai yace shi ba ynx zai ciba.
        Haka na min dadi wallahi da mijin da nake sone da tuni yaga madaran luv.
              Hmm ina ruwan madam Amrah ranar monday na shirya  tsaf yana zaune a falo yana shan tea, sai gani nafito gyale na yafa akan doguwar rigar jikina,  ko inda yake ban kalla ba na wucce manta key motana nayi na ajiye kayana na koma kafin nashiga har yasa Imran ya ɗauko masa yakawo ya ajiye masa shi kuma ya saka a gaban remoteɗin tv nagama duba ɗakina babu keybabu dalilinshi,  fitowa nayi aikuwa idanuna ya sauka akan key ɗin bansan lokacin da bala'i ya ciyoni ba nazo kanshi na tsaya, zan ɗauka key ɗin yayi baya haka key ɗin yayita matsawa har kan cinyar Sadeeq sake ina cike da masifa sam banyi alakari da abinda ke faruwa ba sai naji ni a jikin mutum ko kallona baiyi ba, ina son mikewa amma kamar an danne ni, a jikinshi ɗaga kai nayi cike da masifa na nazubawa idanunshi ido, da hanzari nayi kasa da kaina wallahi tun da nake ban taɓa ganin, kwayar idanun ɗan naija ashe colour ba sai sadeeq cikin idanun kuwa har wani diz aka musu, sai kwayar tsakiyar itace mai ɗigon baki, kamar muna fuka na ɗaga kai da niyyar sake gani haka ne dai da sauri na mike tare da jan tsaki nace.
" Dan iska."

   Kasa kasa sarai ya ji,ni kawai baida niyyr magane ne,

      Daukar key ɗin nayi zan fita sai dana kai bakin kofa cikin isa da iko yace.
"Idan kika kuskura kika fita a gidan abakin..."

      "Yo banda abinka aina jima ina son gutsere auren karasa sai nafita daga nan nayi gidanmu"
Nace masa,

   Dariya yayi yace.
"Ai ba gidanku zaki ba aikinki zaki rasa har abada, sai kinsan yanda ake niman izinin miji idan mace zatayi abu."

    "Wallahi kayi karya Sadeeq aikin kan sai naje, banza malalaci mara zuciyar niman na kanshi idan... "

      Ban kai aya ba naji an finciko ni aka yi sama dani sai dakinshi, ban taɓa tunanin zai iya min wannan rashin mutunci ba koda ya jefani a gado fita yayi yabar ni a ɗakin. Har na awa uku kafin ya dawo ya buɗe ni sai gashi wani mugun tsoronshi ya kamani dan dole na sunkuyar da kaina.

    Tsawa ya buga min cike da ɓacin rai yace.
" Fitan min a ɗaki kafin na sauya miki halitta." tsabar tsoro a ɗakina nagama jin sauran maganarshi.

                ***
Kwana uku tsakani sai gashi yayi shirin tafiya, ban san inda zai je ba dan haka ban damu ba, yafito yace.
"Zanyi tafiya kwana uku zanyi kawai."

          Kuɗi ya ajiye min dubu talatin, cikin kunkuni nace..
"Ni me ya dame ni da tafiyarka aikina zan koma."

    "Allah ya baki sa'a da alamun kin kusan barin aikin knn".
          Ya faɗa min sannan yasa kai zai fita.
Aikuwa nace.
"Mugu Allah ya isa min."

    Bai damu ba, yayi tafiyarsa  sai zaman gidan ya isheni, haka na share wuni guda ina bacci da aiki. Har dare sannan na kuna tv na fara kallon Mbc 2 dama su ɗin mayun saka horror fim ne, dan haka idanuna yaki bacci,

              Zama nayi da niyyar kallon wani fim me suna the ring, a hankali aka fara fim ɗin babu tsoro can da fim ɗin yayi nisa aka fara wajen tsoro tuni na kashe tv na kashe wutar falon na koma ɗakina na kwanta, baccine ya fara ɗauka na sai naji karan tv a falo tashi nayi naje na kashe na cire socket ɗin,

     Na dawo na kwanta can har baccina yayi nisa sai naji tv nayi take tsoro ya kamani a hankali na,sauko da kafafuna nafito zuwa falon wasu irin fararen macizai nagani, a zaune a kujeran falon ina son yin addu'a amma na kasa, sai ma kasalar da ya sauko min da wani irin feelings a hankali idanuna ya shiga rufewa kamar zan zuɓe a gurin wani guguwa yayi sama dani sai ɗakina.

      Ina jin guguwar ta rikiɗe zuwa sufar maciji mutun, a hankali yake bin jikina yana faɗin.
"Amrahtuna da yardanki aka ci amanata, mi yasa kika amince da wannan auren kinsan yanda nake sonki kuwa mi zancewa Yaranki, Amrah karki tafi kibarmu muna bukatarki a rayuwarmu kinji."

    Gyaɗa kai nayi masa sannu a hankali ya shiga lasar jikina da harshensa guda biyu yana bin ko ina najikina yana motsawa, ji nayi abinda yake min yafi min daɗi akan kome mika nayi yasaka hannunshi duk biyu ya rungume hakarkarina tare da saka kanshi tsakiyar kirjina,  rawan da jikina keyi yasa ya cigaba da bin jikina yana lasa, buɗe ido nake sonyi amma na gaza dan dole na maida kai na kwanta bai fasa bin jikina ba, ni ma ban daina jin haka a jikina ba sai can naji yayi wani irin Ihu dakyar idanuna ya buɗo wani farin mutum na gani da fararen kaya ya kama macijin nan ya shakeshi, wura min isa mutum yayi bacci mai nauyi yayi gaba dani.

           Ban sake farkawa ba sai da na share kwana uku ina bacci ina farkawa da ihu nake tashi shafa min habbatul saudat da wasu haɗi ake sai na koma, bacci ina haka har nafarka ban tashi da ihu ko kuka ba, sai dai na tashi da sabon tsanar Sadeeq ne a raina, a hankali na fahimci a gida nake, gidan iyayena sosai naji daɗin haka,

         Tashi nayi na shiga ban daki nayi wanka da alola sannan nazo nasaka kayana, sallar dake kaina na sauke tare da addu'a jin muryan sadeeq yasa jikina ya soma rawa, kafin wani lokaci fatar jikina yayi fari sol,

           Kifawa nayi a gurin ina gurnani, yana shigowa ɗakin nayi wani irin tsalle na kai masa duka kafin na isa Imaran ya kare masa, yayi wani majjajwa dani ya makani da katifar ɗakin, take suka shiga shafa min magani.

      Ihu na fasa wanda yayi sanadin wautsina kome na ɗakin sai da suka gama shafa min magani sannan jikina ya fara dawowa normal,

              Baccine yasake gaba dani.

          A bakin rafin dunduma ta xube tana ihu da birgima sauran yan uwanta suka fito daga cikin kogon ramin da suke cikin tashin hankali Zarina tace.
"Fauzan mi yasa kika je gurin Umma a wannan lokaci ko baki ji Abbu yace kar wata taje ba  ya shiga tsakanin wanca mutumin da Umma ba, kina ci da zuci"

         " Hmm " Fatahiyya tace kafin ta juya ranta a ɓace,
      Rusaila ce tayi maza tasha gabanta cikin tashin hankali tace..
"Fatahiyya karki je kibar Abbu ya huta shima jikinshi akwai ciwo muyi hakuri Umma zata dawo garemu dukkanmu muna sonta dan haka kucire damuwar kome ai ynx babu wani shiri a tsakaninsu tunda Abbu ya zuba mata kiyayyar wancan bil adam ɗin umma zata dawo garemu."

      Kama fauzan sukayi suka sakata a cikin wani ruwa mai ɗauke da wasu irin jijjiyoyin da saiwowwen bishiya a ciki ta rikiɗe zuwa sufarta ta Whiter sneak.

       Sauran kuma kogonsu suka shiga cike da ɓaccin rai.....
        ***
  Kwana na uku kafin na warware, sai dai ina jin kewar wasu yara wanda bansan su ba, ko bacci nake sai nayi mafarkin gani da yarana har su huɗu duk mata,  nashafa kan wannan na rungume wannan ina tsaka da mafarkin, ko mahaifin yaran wani kyakyawan mijina yazo gareni, sai na farka toh idan na tashi bana sakewa wani magana a gidan sai anyi awa huɗu, ranar da abin yafi

Please Login or Register in order to submit comment