Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tuni ya gigice, a cikin barci na ji sakonshi buɗe ido nayi naga Sadeeq a gigice akaina dumm gaba ya buga, jikina narawa nace.
"Ayya Mijina bani da lafiya wallahi bayana da cikina kayi min rai."

Ina bai masan inayi ba dan baki ɗaya ya kwarkwance min, kuka nasa ina cewa.
"Wayyo cikina, wayyo bayana na shiga uku na, Wallahi sadeeq zaka sake sawa a min wani aiki ka barni haka."

Ina baiji ba kuma bana tunanin yasan inayi bai sarara min ba sai da yaji shi a muhallinshi da yake ta fafutukar niman isa gurin rikeshi nayi gam tare da kifa kaina a kirjinshi ina shashekar kuka, sabida na gaji jikina yariga da ya sami hutun watanin, sosai ya gurje ni son ranshi haɗiye kukana nayi lokacin da naji ya ambaci kalmar da tafi kome tsada, ɗago kaina nayi ina kallonshi sake cewa yayi.
"Amrah Ina sonki I luv u, da duk rayuwata nake sonki karki min iyaka da kanki dan zan iya faɗawa wani halin..."

A hankali na kare matse jikina yanda zai kara zaucewa, aikuwa haka yayi amfani, toh ya aka iya an jima ba'a haɗu ba ranar da aka haɗu kuwa ai baza'a ganewa juna ba😉

Sai da naga ya iso inda ya dace nace.
"Ina sonka nima mijina."

Aikuwa yanq isowa ya ɗaukw wuta ya haɗa fuskana dashi yana sumbata sabida tsabar farin ciki sai da muka gama nasa mishi kuka bayana da cikina, dariya yayi yace.
"Magulmaciya sai da kika gama tsotseni tass zaki saka min kuka ina cewa har wani ruqurqune kikayi, kina amsar lollipop ba yarinya kinji kayan aiki sai wani sake jiki take taji yaro ɗanye jagaf ga kuruciya ga aiki."

Tsabar bakin ciki bansan lokaci da na wurga mishi pillow ba ina fara sabon kuka nace.
""Sai na faɗawa Inna wuro."

D'aga kafaɗa yayi yace.
"Yarinya Wallahi ce mata zanyi ince mata bina kike har da kuka na..."

Ai ɗayar fillow na wurga mishi zuwa yayi ya kamani muka shige banɗaki, ina kuka ina kome haka mukayi muka fito, niman kaya yayi zai sami na janyi jikina na kwanta biyoni yayi muƙa kwanta abinmu toh ai dama lalura yasa na daina ynz kuma tunda na amshi duty shiknn.


Washi gari ya rigani tashi nima dakyar na farka nayi wanka sannan naga ɗakin wayam har yayiwa ɗanshi wanka,

Fitowa nayi na ganshi da yaronshi kayan da ya ajiye min nasaka, doguwar riga gurinsu na isa na sumbaci yaron a goshi da kuma tu Uban kuwa na kwaɗa mishi harara na laifinshi na wajigani.

Karyawa nayi muka fara fita da kaya ana sakawa a taxi daga nan ya rufo gidan muka fito.

Muna isa airport aka fara kiran fasinjoji muka shiga layi muna, bayan wani lokaci jirginmu ya tashi zuwa Canada......



*Wani fata kake ko kike ga Sadeeq akan wannar tafiyar da Amrah ta bashi goyan bayan zuwa...*
🌺🌷🌷
*_DA CIWO A RAYUWATA_*
🌹🌸🌸

Na
Mai_Dambu
Wattpad:Mai_Dambu
       *WATA K'ADDARA🙆*
```😹Duk wanda ya karanta wannan pagen yayi shiru na minti 2```

     *_Wannan shafin sadaukarwane ga Ilahirin masoyan da ciwo a rayuwata a duk inda suke I heart you all_*

*Page E=Egg*

          Har cikin jirgin shi yake rike da yaron gaskiya na gaji hararanshi nayi karaf akan idonshi murmushi yayi cikin tsokana yace..
"Yarinya tabi ni a hankali in ba haka ba hmmn sau ɗaya nake nawa sai nasa wannan bakin kuka,."

Bugu na ksi mishi cike da takaici nace.
"Hammah kana cutata Allah na tashi ramawa zaka gane dani kake zance."

          Karshe maganar tare da murguda mishi baki, a nutsu yake kallon inda muke dan muna fisrt class ne, kafin na taya shi niman abinda yake dubawa sai jin bakinshi nayi a kan nawa bai kyale ni ba sai da ya cinye min bakina tasss,

     
  Sannan ya koma mazauninshi yana murmushi, bakina kamar zai fita sabida yanda aka min na horon maganar da nayi ne,

Ban kuma lakatarshi ba dan nasan nice zanta kayan kunya, baccin gajiya janyo kaina yayi na kwanta a kafaɗarshi duk ya haɗamu nida Abul ya kalleni ya kalle Abul, shi ɗaya ya haɗa garfe inda da waɗancan da suka mutu suna raye zaro ido yayi cikin murmushi yace.
"Kuma bazan fasa kashe arna ba ai koda zasu cika min gidana kuwa."
       Mugu ɗan masara😂.

          ****
   Tsabar niman magana irin na fauzan, bata bar kanta a guri ɗaya ba tashiga bin didigin wannan koramar, har takai kanta cikin ruwa wanda badan Allah yasota ba da babu labarinta,


Da imran yaji haka kaman ya daketa sabida tacika taurinkai.

****
Bacci Nanah ke sabida kwana biyu bata da lafiya, ga mustapha da ya addabi rayuwarta tun da safe yazo yake buga kofar gidan taki buɗewa hauka yayi ta mata, karshe da yagaji ya zauna a gurin ya cusa kanshi a cinyoyinshi yana kuka,

Haka ya wuni tun safe har dare bata buɗe ba kuma tana jinshi, hankalin Adda Kuluwa da Kawu Aminu ne ya tashi, sukayi ta nemanshi har suka iso gidan ganinshi a gurin yana gyangyaɗi suka isa guri tare da kiranshi "Musty!!!"
Mikewa yayi ya fashe da kuka, yana nuna kofar gidan buga kofar sukayi tare da kiranta, fitowa tayi ta buɗe tura kofar suka tare da shiga gida, cikin inda inda tace.
"Adda barka da zuwa Kawu ku zauna."

Basu zauna ba suka watsa mata mugun kallo tare da janyo ɗansu jikinsu Adda Kuluwa tace.
"Bayan kin lalata mana shine zaki koreshi ai yanda kika saba bashi haka zaki cigaba,"

Murmushi Kawu Aminu yayi yace.
"A'a ai natar aure ce zo mutafi Mustyna.'"

Kuka Mustapha yasaka yana ihu amma haka suka ja shi dan dole suka fito dashi.

Jikin Nanah yayi mugun sanyi dan dole ta koma ta kwanta badan taso ba,

***
Mun sauka lafiya inda muka tarda wanda zai kaimu masauki nagaji ainun har muka isa gidan wanda yake cikin wani estate yayi kyau gidajen muna isa ciki na zuɓe a kujera dan har ynz banyi lafiyan baya ba,


Dakyar na mike naje nayi wanka da alola nayi sallah can sai gashi da Abinci, namu na yan naija tuwon shinkafa miyar ganye ya ajiye min a wani warm ko mai ban shafa ba nafito na zauna nafara ci kallona yayi yana dariya wai.
"Irin wannan cin haka sai na faɗawa Inna wuro ci kike sosai dan ki tsotse mata jikallenta."

Ban iya kulashi ba har sai da naji nayi tam, sannan na ɗago manyan idanuna nace.
"Ni ban faɗa mata yanda kake raruke ni ba sai kai Allah kafita idanuna na rufe bani Abul yaci abinci.
Dan nima yanajin nace akawo shi take ya makale a jikim Uban ɗaga musu kafaɗa nayi na bar musu sauran abinci halinsu ɗaya da uba da ɗan, kamar yanda Uba bai damu da abinci ba idan ranshi bai so ba toh ai na Yaron yafi ma dan shi abinda yake ci daga tea sai risil halin, wani abincine da India da Larabawa sukeyi da alkama da madara, sai zuma suke sakawa a ciki shine abincinshi.

Kwanciya nayi ina mika sosai sabida bayana, lallaɓa ɗanshi yayi har yasamu bacci, dake yaron nada nauyin bacci shimfiɗashi yayi a kujera yashigo ɗakin,

Gaskiya jikina na ciwo na rasa yanda zanyi a hankali na soma kuka, a hankali ya hauro gadon ya zare min rigar jikina tausa yashiga min a hankali, ɓalle bra ɗina yayi a hankali yake bin duk wani lungu da sako najikina yana matsa min,kallon kwallar dake sauka min yayi yace.
"Sannu Baby akwai ciwo ko?"

Gyaɗa mishi kai nayi a hankali sannan na gyara kwanciyana, sosai yake lugwigwitani har barci yayi gaba dani, farkawa nayi na ga Abul a kusadani yana bacci sai yar takarda a gefenshi.

*Sannun kinji nafita ina appointment da Mr Muhammad take Care Muaa*

Frm Mr Lamiɗo
Murmushi nayi na duba agogon wayata, naga karfe biyu na rana tuna lokacin da muka shigo garin nayi, karfe huɗu na dare Allah sarki ko bacci kirki bai ba. Yafita niman nakanshi..


Lokacin da ya isa Officer ɗin tun daga bakin building ɗin ake binshi da ido har ya shiga cikin building ɗin, yana tafe yana gyara zamam netie ɗinshi hannunshi rike da jakarshi, saka yatsar hannunshi yayi ya gyara zaman madubin fuskarshi cike da kwarewa, take duk yan officer ɗin suka mike, suna mashi barka da zuwa yayinda wasu ke magana kasa kasa, dama mr Muh'd yana da wani ɗa ne mai kama da shi haka ko Adnan ne wasu suce a'a ai Adnan likitane, toh Ko Adil ne wasu suka ce ba adil bane dan shi ɗan kwallon kafane. Take ma'aikatar ya ɗauki kuskus, ana haka mr Muh'd ya iso kaman yanda Sadeeq ya shigo yana gyara zaman kwalar rigarshi da nitie ɗinshi kai babu abinda bayi ba, take yan officer ɗin suka shiga tafa mishi cike da mamaki yace.
"Mi nayi haka nasamu kambamawarku."

Daya daga cikin ma'aikatar yace.
"Kimanin shekaru sha bakwai da na fara aiki da kai ban taɓa ganin abinda ya burge ni kaman yanda ɗanka ya shigo haka kaima kashigo mana wannan abin yasa munka tafa maka."
Dariya yayi cikin jin daɗi yace.
"Toh amma ai Adnan ba mazani bane likitane Adil kuma ya gama karatu ya faɗa sport sai karqmar Y'ata itama tana karatunta na Mbs In Nurse wane a cikin yarna kuke faɗa."

Nuna mishi kofar office ɗin sukayi a hankali yake takawa jikinshi na wani irin sanyi tun daga tsakiyar kqnshi har tafin kafarshi da Sallama ya tura kofar, idanunshine ya sauka akan Sadeeq da yake gyara wani zane da akayi wanda matukar akayi gini kamar haka toh tabbas bazai haura shekara biyu ba zai zuɓe kuma anyi asaran rayuka knn cikin iyawa dukda yasami mutane a gurin amma bai ce musu uffan ba ya shiga gyarawa mutanen na binshi da ido, abinda da ba'a cire ba, ya cire musu misali garejin kasa, inda filin shakatawa, da kuma inda za'a ajiye na'ura yanq gamawa ya koma mazaunin take aka shiga tafa mishi toh ya za'ayi ɗan nagada nefa, abin a jininsu yake zanen.

Shigowa Mr Muh'd yasa duk suka mike binsu yayi yana mika musu hannu da ya ɗaura idanunshi akan Sadeeq ɗagoshi yayi ya rungumeshi dan wani mahaukacin soyayyar Sadeeq ce tasami mazauni a zuciyar Mr Muh'd.

Kaman zai zubda kwalla yace.
"About two days ago ina kokarin guba kurakuraina a wannan zanen ban gani ba kuma da nayi nszarin shi natabbatar za'ayi asara me yawwa Yaro nawa kake bukatq nakara maka a wanda na tura maka, babba damuwata girma nacin mani bani da magaji dan nima gadar zanen nayi yau gashi Allah ya kawo min ɗan baiwa Yaro daga wani yanki na duniya kafito."

Dariya mr Arfan yayi cikin barkwace yace.
"Mr Muh'd ai mun munzata ɗanka ne sabida kuwa yanda kukayi matukar kama, gashi Allah yayi mashi baiwa kamar taka, karka manta muna london ka taɓa gyarawa Professor David Mose gyaran zanenshi a lokacin muna dalibai yau kuma dubi ɗanka yazo ya gyara maka, dukda nasan Adnan da Adil amma wannan tsaginka ne,."

Kallon Sadeeq yayi yana dariya yace.
"Ai wallahi ba yanda kake tunani bane yau Adnan da Adil gare ni sai Autata amma ai haka ma ya bada ma'ana."

Nan aka zauna aka fara gabatar da abinda ya kawosu Mr Arfan daga Dubai yazo kuma ya biyo wani zane da Sadeeq yayi ne Mr Muh'd ya saya, toh ranshi ya biyawa xanen dan haka ido da ido yayi ciniki da Sadeeq ya riɓanya mashi kaso talatin akan na mr muh'd murmushi Sadeeq yayi sannan ya kalle Mr Muh'd cikin wani irin girmamawa yace.
"Ga Babana nan kuma mai gidana kuyi ciniki dashi dan ya rigada ya biyani hakkina."

Wani irin soyayyar Mr Muh'd Sadeeq yake ji dan bini bini yana kallonshi, cikin wani irin kulawa yake kallonshi a cikin haka mr muh'd yasha ruwa ya kware a gigice Sadeeq yazo kusadashi yana shafa bayanshi, sam bai taɓa tunanin bayan Iyaywnshi da Inna wuro da kuma ni da ɗanshi akwai wani wanda zai so kamar mr Muh'd ba,


Basu tashi a taron ba sai dare, ina ta zuba ido akan hanya, musaman naci gayu da wata doguwar riga purpule irin me roban nan daga kirjin a buɗe yake har kusan cikina, sai kuma tsagu daga cinyata har kasa, gyara gashina nayi da wani yar karamar gyale, na yafa wasan turare nayi a jikina sannan nasaka wani hill abin dariya ni danake fama da baya amma har da saka takalmi,

Fuskana kuwa zama nayi na mata makeove ina jiran zuwanshi, abincine dai ankawo mana ɗazun dan wani gidan abinci yar kasarmu yaje yabata kuɗi akawo mana can ya amso mana daga zuwanmu.

Da sallama ya shigo a yanga ce na ɗago kaina na rausaya dashi snnan na amsa a sanyayye, na mike na amshi jakarshi, kallon yaronshi dake kokarin saukowa daga kujera yayi, da sauri ya isa gurinshi ya ɗauke shi ya cillashi sama, janyo ni yayi cikin murmushi yace.
"Mrs Lamiɗo yau naga mai kama da mijinki.".
Tura mushi baki nayi nace.
"Ko ɗan kiss ɗin nan baka bar ni nayi maka ba kazo kana min wani funny story ai irin mijina suna dayawa my dear muje kayi wnka kazo kaci abinci."

"Toh ranki shi daɗe Papana yaci abincin kuwa dan naga sai shigewa jikina yake."

"Wannan yaron naka Allah bazan iya mashi ba yaki cifa." kaman zanyi kuka na kai karshen maganata,

Shiga mishi da jakar nayi naje na haɗa mishi ruwan wanka, sannan nafito, nasame shi yana bawa Abul abinci karba nayi nace.
"Hamma na jeka kayi wanka bari n karasa bashi."

Mikewa yayi banyi aune ba naji hannunshi ya shafo ni sai da muka kusan faɗowa daga kujeran kashe min ido yayi yace.
"Kaiiii Baby gal da sauranki."
Tafiya yayi yabar ni da mutuwar jiki dan aikarshi ya shiga inda ya dace.

Da wayo da dabara nabawa abul abinci yana shan ruwa yafara "Amama amama amama"

Yana leka kofar ɗakin zaro ido nayi nace.
"Love repeating again."..

Yaron kuwa ya cigaba da kiran Ubanshi dariya nayi na saɓashi sama muka nufi ɗakin muna zaune sai gashi yafito, kayanshi na mika mishi muka fito aikuwa yaron ya kwala ihu yana mika mishi Hannu tare da cewa.
"Amama Amama."

Dariya nayi nace.
"Kasa mi yake nufi yasan kiranka yake wai Hammana zai ce."

Waro ido yayi Yace.
"Wayyo Allah na yau nima nasan nahaihu ɗana yakirani.."

Daga yaron yyi sama yana cillashi, dakyarnafitar dashi yasaka kaya yafito nan yashiga bani labarin abinda ya faru. Office haka kawai naji nima raina yayi,har lokacin kwanciya yayi bayan abul yayi bacci, na,fito daga ban ɗaki ɗaure da towel.

"Adda Amra!!!" yakira suna na juyawa nayi na kalleshi nace.
"Hmm na'am faɗi cutarka."

"Kayya Yarinya baki da maganin cutata dan da zaran nayi magana zaki ce dr Inna wuro ta hana ko.?"

Murmushi nayi na kyaleshi rigata nasaka ta bacci, na haye gadon, ina shiga bargo nayi wurgi da rigar haka kawai a hanani sakewa, sama sama muka fara hira har nayi masa korafi ya saya mana kayan girki dan nagaji da cin abinci waje.

Gyaɗa kai yayi yana aiki da computersa bansan lokacin da yazo ya kwanta ba, sai farkawa nayi naji ni an zagayeni tare da turani jikinshi sosai gyara kwanciyana nayi tare da sumbatar kirjinshi,

"Baby Kwanta karki tada fitinar da kukanki bazai hana ba."
Da sauri na gyara kaina a kirjinshi dariya yayi yace.
"Matsoraciya kawai ko waya faɗa miki yanda ake gulma ai tunda kika fara sai anyi fa."

Shiru nayi naki kulashi dake yagaji sai ya kyaleni haka muka kwana da asuba na rigashi tashi kallon fuskanshi nayi a hankali na sumbaci goshinsa kafin na ankara naji bakinshi a wuyana, ware ido nayi zanyi magana yace.
"Shhh barni naji ɗuminki don Allah."
Ya na iya da Malam sadeeq yau duty ɗin nice a gaba, dan yaki juya ni kasanshi (Dama haka abin yake gaskiya bansan wannan tsarin manhajar ya haɗu ba sai da Hammana ya ɗaurani akai tare da bani haddarsu yanda ya dace)
Bayan wasu mintuna muka rungume juna muna sauke ajiyar zuciya.

Karfe bakwai duk muka fito, karyawa yana gama nashi na rakashi har bakin kofa tare da sumbatarshi,


Shi kuma ya sumbaci ɗanshi..


Zan iya cewa tun zuwanmu Canada bayi da lokacinmu saidare a daren muke fita sayayya har muka tanadi komi namu nagaji da cin abincin waje nima na soma dafawa mijina yana ci...
*Wata Kaddaran*
Watanmu guda sukayi tafiyan kwana uku, yana dawowa na rokeshi naje gidansu Meemah ashe wata kaddaran ce ke bibiyata, dakyar ya kawo ni gidan yace sai dare xai dawo, cikin farin ciki na shiga da Adil muka haɗu ihu yasaka sannan yazo ya amshi yaron Ammih ta rungume ni, take gidan ya kaure da murna nan muka zauna a falo Meemah ta sauko muka gaisa kallon Abul tayi cikin dariya tace.
"Amrah ke kuma sai ki haifi me kama dani, dubi yaron fa."

Tsam nayi ina kallon fuskarta a ruɗe na kalli abul sannan na hasko fuskar Sadeeq take na mike, cike da alajabi duk suka mike suna tambayana lafiya nace.
"Meemah lokacin da muka haɗu a macca waye kikewa Addu'a."

Shiru tayi tana tunowa jirine yake niman ɗaukarta babu shiri muka tareta ta zauna, kuka ta saka mana daga nan bata sake cewa kome ba.

Sai kallon yaron take wanda ya haye cinyarta ya kwanta, har dare inata jiran Sadeeq shigowar Adnan yasani mikewa sai da na lura naga ashe ba mijina bane zama nayi naja yarona jiki, kaman zai cinye ni haka yake kallona, ko ɗakinshi bai jeba yasani a gaba, shigowar drvn gidan yace ana kirana yasa na saɓi yaeona akafaɗa,

Nace.
"Meemah Abban Abul ya iso bari naje na shigo dashi."
Ina fita Adnan nabina magana yake min nayi banza dashi sai da ya bari mun fito haske ya fincikoni dani da yaron ya haɗani da kirjinshi kuma akan ido Sadeeq, ihu na fasa tare da kwace kaina na ajiye Abul na tsinke shi da mari amadadin yaji zafi saima dariya yake tare da kokarin sake rungume ni, "Hammnana kazo ka kwace ni, "

Kafin nayi wani yunkuri ya matse ni da motar Adil yana kokarin haɗa bakina da nashi,

Wani mugun naushi Sadeeq ya dannawa mishi wanda yaja ya sake ni da sauri na faɗa jikinshi, ina kuka jibgan dan banza yake amma dan taurin kai cewa yake.
"Amratuh tawa ce ko kashe ni zakayi kuwa sai na halatawa kaina aurenta."

Jan Sadeeq nayi dai dai lokacin da Daddy Ya shigo da motarshi, ina kokarin janshi ya juya ya kifa min mari har sau uku zan faɗi Adnan yayi maza ya tare ni na faɗa jikinshi ai lokaci guda Sadeeq ya sake rufe shi da duka bayan ya fauce ni a jikinshi kuka nake dakyar aka rabasu Jin furucin da Adnan yake yasa Daddy ko nace Mr Muh'd ya kife Adnan da Mari a lokacin su Meemah suka iso gani na a zaune daɓas yasa Ammih ta ɗago ni, nabi bayan Sadeeq ina kokarin mishi bayani amna ya juye afusace yace.
"Kije Na sak."
"Kul idan ka ɗauke ni a Aboki karka karasa kalmar matar rufin Asirinka ce tayi gwagwarmayya sabida kai kace zaka sake ta"

A hasale ya juya cikin tsawa yace.
"Nasaki Amratuh Yusif jama'are ni Abubakar Mustapha Lamiɗo taje ta zauna da kwartonta."..

Zuɓewa Meemah tayi a gurin sumammiya Mr Muh'd ko nace Daddy shima zuɓewa yayi kanshi nasarawa.....


Nikuwa zama nayi a gurin kamar doluwa wawuya mara hankali mikewa nayi nazo gabanshi ina kallonshi dariya nayi nace.
"Dama kasan bazaka iya rike ni ba ka lalara min rayuwa hmm auren shekara biyu da rabi na fito zawarci Allah sai ya saka min Sadeeq ka cutar dani fiye da kima kalalata min zuciya da sonka nagode, har zan juya na dawo idan sami damar kallon yarona ina kallon yaron na juya, banyi nisa da tafiyar ba jiri ya zubar dani a gurin Imran ma ya kalleshi yace.
"Itace fitilarka itace ganinka itace silar haɗaka da Iyayenka gasu can sune suka haifeka yau ka juya mata baya a sabida laifin da ba ita tayi ba wallahi Sadeeq tunda ka iya rabuwa da Amratu babu wanda bazaka iya rabuwa dashi ba na tafi sai ranar da kasan ciwon kanka zan dawo gareka..."

Kishi ya rufe mishi ido ko takan iyayen nashi bai bi ba Ammih takira motar asibiti..........


*Ina ma zan sami voting ɗari biyu a yau zuwa gobe nasake tattaro kundin Karamcinku na kara muku dan yau babu pagw biyu nagaji nima yan Whatsp ku karamin kwarin gwiwa da comments ɗinku tunda babu halin voter* 💋💋💋💋
🌺🌷🌷
*_DA CIWO A RAYUWATA_*
🌹🌸🌸

Na
Mai_Dambu
Wattpad:Mai_Dambu...

   *Madafa*

       Can't stop 😹😹😹

*Page=Fans*

        Lokaci guda motar asibiti har biyu suka nime shigowa Adnan ne yayi kaina kaman babu rauni a fuskarshi, yasa hannu xai ɗauke ni kenan  Sadeeq rike hannunshi yace.
"Kaii jahilin ina ne wallahi zan kasheka..." faɗa mashi da hargagi,

  Shi kuwa cike da giyar so yace.
"Mr Man indai akan Preety ne har ynx makabarta bata cika ba kagane nifa haka da yafaru gaba ta kaine wallahi na

Please Login or Register in order to submit comment