Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

daga suman da yayi da ihu ya farka yayi waje da gudu yayi cikin daji tsirara yanata zunduma ihu da alama brain dinshi tasamu problem,bukkar kuwa ta ruguje ,


Basukai bakin titi ba ya saki hannunta ya watsa mata kayanta batare da ya kalleta ba ya tafi yanata kuka zuciyarshi na ciwo,

Aisha ta durkushe awurin tana kuka me sauti,


Yashiga mota yana tuki ahankali yanata hawaye wannan shine babbar jarabawar rayuwarshi his beloved wife tareda wani,idanunshi naganin bijibiji ya nufi gida,


Tanata kuka numfashinta na season ta dauki kayanta tasaka ta shiga mota ta nufi gidan momy tanata kuka zuciyar ta na harbawa da karfin tsiya, gudu taita shararawa batako kallon gabanta ,


Fahad yana isa gida ya fito kanshi na juya ya tsaya bakin kofa yana niyyar bude kofar,

Faseelat datasha wanka tayi gayu cikin doguwar riga, tana falo ta mike kafa tanashan Ovaltine tana kallon sunna TV shirin (don iyali) taji anata kakaniyyar bude kofa ta tashi dakyar ta dauko remote ta bude kofar ,

Fahad ya shigo yana layi kamar ze kife kanshi nata juyawa,

Faseelat ta zaro ido waje ganin jikinshi duk jini ga halinda yake ciki ,tayi wurinshi hankali tashe tana "innalillahi wainna ilaihi rajiun ,innalillahi wainna ilahi rajiun!!!!!"

Kafin ta kai ya zube kasa ,ta isa wurinshi ta zukunna tana kuka,"hero Dan Allah katashi meya faru?"tanata jijjigashi ,

Ganin fa baya motsi yasa tafara lalubar aljihunshi ta jawo wayarshi takira doctor ,tana kuka take fadamishi hankali tashe yakamo hanya,tai zaune wurin tameda kanshi jikinta tanata kallon busashshen jinin dake ga hannuwanshi,tana kuka,


Aisha nashiga gida tafito tana layi domin ciwo biyu ne take daukedashi donko mararta ba abinda takeyi se murdawa tundazu,tatura kofa tashiga main falo nasu tana shiga ta zube a sume ,jini yafara gangaro mata from virgina,

Ramlat dake falon tana kallo tayo kanta tana kuka ,ganin jini yana zubomata yasa tadunga kwalawa mommy kira ,mommy tafito dasauri jikinta na rawa ,ganin Aisha acikin yanayin ya rikitata batako tsaya dubata ba ta dauko veil da keys ta sungumi abarta tana ta kuka tasata a mota Su ramlat suka shiga ta nufi asibity da high speed,

Faseelat tana ta kuka doctor yazo takasa mishi kome doctor ya yayyafamishi ruwa ya farko da tari ya dafe heart da hannu yanajin matukar ciwo ,doctor ya dubashi sosai shima yakamu da ciwon zuciya kuma jininshi yahau sosai,


He ask faseelat takawo katifa tatashi ta fiddo katifa dakyar ta shimfida ,doctor
Ya temakawa fahad yamedashi akan katifar fahad nata hawaye masu zafi ta gefen ido ,docton yafita don siyo magani da drip daze samishi,


Asibitin okaton aka kai Aisha nurses suka amsheta suka fara bata temakon gaggawa,Su mommy na waje sun hade kai suna kuka su duka ukkun,

Dakyar suka samu ta dawo da numfashi shima ba normal numfashi ba kirjinta nata yin sama tana jawo iska amma dukda haka "yaya" take kira,shima jinin dakyar suka samu yatsaya,

Akasamata jini da abinda ze temaka mata wurin numfashi bayan sun mata allurai d.s, suka fito daita tana sheme kan bed akamedata rest room,
Su mommy nabiye Suna kuka,


Nurse tace mommy tabiyota office tabita tanata hawaye ,

Nurse tace"Hjy anyi raping yarinyanki har takusayin miscarriage zuciyarta takara kumbura jini yahawo akan heart nata ,dole se anbata good care sannan asamu aceto rayuwarta tana cikin a lot of pain ,yakamata arika mata abinda takeso da Wanda zesa taji dadi"

Mommy ta fiddo ido tanata memeta rape a brain dinta bakinta na rawa tace"doctor rape ?cikin ya zube kenan ?"

Doctor tace "nooo yana nan sede sean kiyaye movement nata da komi,domin motsi me karfi ma zeiya affecting nasa Allah yabata lpy"


Mommy tace"thank you "
Ta tashi tafita takara lekawa dakin taita kallon fuskar Aisha tana tambayar kanta raping ?kasa hakura tayi tai dialing number fahad ,

Taita ringing sannan faseelat ta dauka tana kuka ,Mommy tace"kibashi wayarshi ?"

Cikin kuka tace"mommy baya lafiya sosai gashinan kwance anasa masa drip "

Mommy takashe wayar tana tunani barkatai batasan lokacinda Aisha zata tashi ba kuma tanason sanin abinda yafaru ,tabar su Sadiya wurin tafita ta nufi gidan fahad,


Doctor yasawa fahad drip da alllurai ciki hadata bacci amma baccin yaki daukarsa saboda karfin jininshi idonshi lumshe ba abinda yake gani se bad moment na dazu,doctor ya ajiye masu magunguna yafita,shimade besan miye ke faruwa ba ganin duk jini jikinshi with out tiny wound kuma,

Bayan yafita faseelat Takara matsawa kusadashi tasa hannu tana share mai hawayen dake fitowa daga gefen idonshi,

Tana kuka tace "meyasameka hero ?I want to know hankalina ya tashi sosai,jikinka duk jini Aina kasamu jini?"

Makoshinshi na ciwo hawaye masu zafi nakara zubomasa zuciyarshi nakara bugu dakyar ya bude ido ya riko hannunta yace"faseelat Aisha ta cuceni ,ta cuci rayuwata ,meyasa zatamin haka?ina tsananin sonta da kishinta ,ina kokarina wurin kyautata mata amma taci amanata"

Faseelat nata hawaye tace "me anty ta maka? Anty bazata iya cutarka ba tanasonka fin yadda takeson kanta"

Zuciyarshi na zafi kuka na shirin kwacemishi yace"my Aisha awurin boka ,naga Aisha da idona ta sakarwa boka jikinta yana sex daita"yafashe da kuka,

faseelat ta girgiza wannan yasa zuciyarta ta ringa bugawa fat fat!!! ,brain dinta tarika tuno face din innocent Aisha dabata cika hayaniya ba,hawaye suka kara gudu a fuskarta ,

Muryarta na rawa tarika girgiza kai tace"anty bazatai haka ba ,hero anty bazata iyayin wannan mummunan laifin ba"

Yana kuka yace "but she deed it ,me too i don't belief myself I thought it was a dream amma dagaske ne ,Aisha kwance dawani suna lalata ,my heart is burning like hell"


Tafashe da kuka tace"wace irin kaddara ce tafadawa anty? yamazaai anty tayi hakan"

Yayi shiru yanata hawaye murya shake yace "ba kaddara bace son zuciya ne ,tanaso ta haramta abinda Allah ya halattamin ,Aisha batasonki bata kaunar koda hada ido dake nima bataso narika kulaki itace tayimin asiri for all this time itace tasaki cikin kunci faseelat...."

Faseelat tanata kuka tace"banso haka yafaru tsakani na da anty ba ,nabata hakuri na mata biyayya but taki hakura nasan namata laifi I deceived her amma yakamata ta yafemun nasan dole tarika tuno abinda namata shiyasa naita kyautata mata ko zata mance amma bata manta ba, kamata hakuri hero kamata uzuri anty nada kishi saboda tana tsananin sonka kayafemata plsssss"

Yace" I divorced her banason ina ganinta banason tuno komi nata arayuwata I hate her"

Yarika tari sosai dole faseelat tai shiru tana mai sannu,tameda kanshi a kan cinyarta tana shafar sumarshi tana cewa "kayi hakuri hero ka medo anty yar uwarkace nasan bazaka so kaganta cikin wani hali ba ,batada lpy duk saboda sonka kamata hakuri Allah nason masu hakuri masu yafiya in an musu laifi"

Shiru kawai yayi idanunshi a lumshe she will not understand his feeling ,

Tayi shiru tana tunani all this thought anty ce tai charming dinshi meyasa zatabi son zuciyarta da rudin shedan ,hawaye suka zubomata inama batasan fahad ba inama suna nan tareda anty a kawaye ,

Door bell ne yakatseta ,ta ajiye kanshi tatashi ta dauki remote ta latsa mommy tashigo gidan a harmutse dakaganta zaka gane tasha kuka ,

Tazo ta zauna kusada fahad jin kamshin mommynshi yasa yakara rumtse ido hawaye na zubarmishi ,

Mommy tabi hannunshi da jini ya bushe ajiki da kallo ta riko hannun tameda kallonta kan fuskarshi tace "son meyafaru ne?meyasameku kuduka ?"

Yayi shiru zuciyarshi na zafi sosai,

Idon mommy jawur tace "kafadamin plsssss meyafaru ?Aisha taje gida ta sume tana bleeding munje hospital doctor tace anyi raping dinta amma cikinta be zube ba, kafadamin abinda yafaru plsss son"

Kirjinshi yakara dokawa da karfi jin tanada his child acikinta tayi sex da wani, yaronshi yasha sperm na katon arne daniska ,ya fashe da kuka numfashinshi na sarkewa zuciyarshi nata ciwo,

Hawaye suka zubowa mommy tace "plssss kadaure kafadamin nasan komiye ke damunku yayana "

Kamar ana rura wuta a makoshinshi dakyar yace

"mommy Aisha ta cuceni da cikina jikinta tabawa boka jikinta ,mommmy I caught them red handed suna sex"yacigaba da kuka,



Mommy ta saki hannunshi ta rufe baki zuciyarta na bugawa daf daf!!!!!

Batasan lokacin da tadora hannu akai ba ,tacigaba da hawaye ,cikin zuciyarta take magana " yanzu Aisha komawa tayi wurinnan ?seda takoma meyasa bata nemi shawara ta ba ?",

Bakinta na rawa tace "kayi hakuri son kayafemata "

Yana hawaye yace "I forgive her mom, amma bazan iya cigaba da zama daita ba,i divorced her ,I don't love her anymore"

Mommy ta fiddo ido waje tace "meyasa zakai hukunci da gaggawa yakamata kayafemata kodan cikin jikinta ,taci albarkacin shi "

ya girgiza kai yace"banason ganinta mommy banason kojin sunanta I hate her ,taya zaniya zama daita?"

Ya share hawaye yace"I wish brain dita zata manta komi da sena iya barinta amma bazan taba mantawa ba ,bazan taba manta zaluncin datamin ba"

Mommy ta dafe kai tana neman mafita ,

Faseelat na gefe tana hawaye da regretting shigowa cikin rayuwarsu,


Mommy ta tashi ta kalli katon cikin faseelat ta matse baki ta juya tabar gidan takoma asibity ,tanata tunani dajin haushin Aisha ,

Har lokacin Aisha bata farko ba ,ta zauna gefenta tanata kallonta ,zuciyarta takusa bugawa anya idan taji fahad ya saketa anya zuciyar bazata ida bugawa din ba?

Se karfe 11 drip yakare shida kanshi ya cireshi ,sunci kuka harsunyi shiru faseelat takamashi yana dafe da zuciyarshi suka hau sama ,

ta cire masa kaya suka shiga toilet yayi wanka yazo ya kabbara salla daga zaune yanayi yana hawaye,


Itama faseelat alwalar tayi tai sallar ishai tanata rokon Allah yadedeta tsakanin Su yasawa fahad hakuri da dangana,

Bayan tagama tabashi tea yasha yasha drugs ya kwanta yanata tunani ,

Yunwa takeji taje ta karasa sanwar da Aisha ta bari ta zauna a kitchen din taci, tana ci tana kuka tagama takoma sama ,

Tayo wanka tazo ta kwanta kusa da fahad dayake ta kallon pop na dakin,


Karfe 1 na dare Aisha tafarka tana tuno abinda yafaru ,tarika kuka tana sheshsheka,

Mommy dake zaune ita kadai tace "Aisha meyasa kikayi haka meyasa kikabiyewa shedan ?yanzu da cikin jikinki ya zube fa?"

Jin ciki yasa zuciyarta bugawa da karfi tafara aman jini gulama gulama, tabaki ta hanci ,

Mommy tai kanta tana kuka tana kiran sunanta ,ta latsa switch na kiran doctor,

Ba jimawa doctor da nurses suka shigo aka fidda mommy daketa kuka waje suka cigaba dabata temakon gaggawa,don ceto rayuwarta.



*Hey fans ya kuke I know buk din yadena maku dadi but I'm sorry tun baya nabaku hakuri kuma yanzu ma nakara baku, wasunku suna cewa banyi adalci wa Aisha ba,wasu nacewa sunsa buk din anyi shine akan cin amanar aure da faseelat tayi ,ko daya baga wannan lessson din kadai yatsaya ba,yakamata arika fahimtar writers arika kuma bari mukai karshen novels sannan afara hukunci ,daace raggon miji a labarin faseelat kadai yatsaya daya kare tuntuni amma nasa wannan labarin domin in fadakar da mutane bawai don yamaku dadi ko akasin sa ba ,kowace cikinsu tanada tata kaddara da jarabawar ,kadan daga cikin lesson da naso ace an fahimta*👇🏼

1_illar auren dole ,daace faseelat tanason Khalil da kila tayi hakuri tacigaba da zama dashi ahakan,

2_illar rashin biyawa mace bukata,komin addinin mace shedan naiya yin galaba akanta komin kiyayewarta,

3_illar cin amana faseelat tayi regret sosai akan abinda tayiwa Khalil segashi kuma takara fuskantar desame problem ,na asiri,

4_illar yada sirrin mijinki aishace tabude kofa da har faseelat tai shaawar mijinta,

5_illar bugun mace ta yadda fahad yarasa mutuncinshi awurin dangin faseelat ,kuma yayi asarar gudan jininshi,

6_yafiya yakamata mukasance masu yafewa juna amma Aisha takasa yafewa faseelat,

7_illar zafafa kishi da rashin hakuri ,kungade yadda Aisha tasha wahala awurin fahad dan rashin boye kishinta,

8_ illar bin son zuciya da rashin hakuri da yarda da kaddara,sune suka kai Aisha halaka hartaje wurin boka,

9_illar nuna fifiko da miji keyi ,shine yake kai wasu matan a halaka ,

10_ da illar son zuciya ta yadda Umma ta yadda danta saboda soyayya ta wulakantashi itama Allah ya jarabceta,

11_ gashi muna kan gabar nadamar da Aisha zatayi da wasu darussa masu zuwa a gaba,kuma nasan akwai wasu abaya wadanda wasu sun fahimcesu,

Kodayaushe kirika tuna Allah da kuma ranar hisabi,kisani kome kike yana kallonki mekyau ko marar kyau,


Aisha batana shan wahala bane danta yada sirrin gidanta what I mean the only result shine kwace mata mijinda akai shine yazama horonta kome zance?shine yazama izinah,kuma shima yada sirrin ai laifi ne, akwai hadisin da Muslim ya ruwaito cewa zaa munana mazauninsu saboda fayyace sirrin shimfida,


Faseelat wahalhalun da tasha shine yazama nata result din na fira dawani da aure, wasu nacewa bata wahala ba,aikuwa taga rayuwa,

A_Kishigo gidan dake da kishiya ma wahalane don sekin dage da addua,

B_Duka tasha jibga wurin fahad koshima ba wahala bane? dukda yanasonta be hanashi jibgarta ba,Khalil kuwa be taba ko dungurinta ba,

C_she lost her baby koshima ba jarabawa bane?

D_wulakancin su anty salma shima ,yana ciki agidan Khalil waya taba yimata?

E_asirin data baro shi aka karayi anan can tai zaman 8month,nan tayi 5 shima ba jarabawa bane?

Da kuma wasu dazata fuskanta nangaba,ainasa kam ta jarabtu itama,

Daga bikin su faseelat zuwa time din asirin Aisha anyi 5month? ba aiba, kenan Aisha batai hakuri ba ,tunda gashi ba tai Wanda faseelat tayi ba,

Wannan buk din baze zama silar rugujewar aure ba se Wanda Allah ya kaddara mutuwarshi ga masu cewa haka ,wai tunda faseelat taji dadi wasu sesuyi, INA dadin dame ta tsira? da soyayyar mijince kawai ta tsira,

Kina zaune da mijinki baya biyamiki bukata sekiyi hakuri in zakiiya in bazaki iyaba seki nemi ya sakeki dan gudun fadawa halaka ,

Amma kirika tuna bakisan kuma ina zaki shiga ba ,can din ba irin waccan matsalar? idan zakiyi hakuri seki ta masa addua Allah yakara masa karfin gamsar dake,kina kuma nusar dashi ,


Ina bawa fans na Aisha hakuri 🙏🏻Ku cigaba da bin buk din koba dan itaba ,zaku amfanu da wasu darussan ,kuma na warwaremaku badan watsa sirrin miji take wahala ba ,sannan inkun lura itama mijinta na sonta, dukkansu halinsu zaku diba ,nagode da zafafan sharhi na ba akyauta maku ba naji haushi naji dadi domin gashi nakara wayarmaku da abinda baku ganeba Allah yasa Ku fahimta thanks
➰➰➰➰➰
*RAGGON MIJI*
➰➰➰➰➰

*(musulmin novel😂)*






By






*MAMAN MAMY*
*(SHALELE)*




https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/


*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*




*~We are bearer's of so golden pen🖊~*

*~we write assidiously perceive no pain~.*

*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*

*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*



8⃣8⃣





*dedicated to my fans*





*07063721063*
*Duk wacce taga gyara ko kuskure ko barna ko tanason wani magana dani, whats up me direct to wannan number very simple thanks*


*I'm sorry a rubutun jiya Wanda nayi na Arabic ansamu typing errors wannan ya farune saboda matsalar wayata da bangane kanta ba na rikita mata kwakwalwa da kuma yin abu daka batare da dubawa ba ,na rubuta surar da ayar inkin natsu zakiga gyaran ,nobody above mistake bareni I'm just a learner yanzu muke koyo,u know a single mistake can change a word or meaning*





Sunfi 30mnt awurinta sannan suka samu kanta suka kara auna mata drip da allurai harda ta bacci ,mommy na waje tana ta share hawaye suka fito takutsa kai cikin dakin tana cigaba da hawaye ,yanzu ita ya zatayi ne?

Bacci ne yakwashe faseelat shiko fahad be runtsa ba,

Karfe 3am faseelat dake bacci tatashi saboda jin kukan fahad acikin bacci,

Ta bude ido se hangoshi tayi akan carpet ya kalli gabas yanata kuka kamar karamin yaro,

Tatashi zaune hawaye cikeda idonta na tausayin mijinta,ta sauka taje wurin shi ta zauna ta jawoshi jikinta tana hawaye tace "kayi hakuri hero dan Allah kadena kukannan haka kasawa zuciyarka hakuri kadauki kaddara"

Fahad na kuka yace" I love her so much ,ina sonta sosai meyasa tayi min haka?ya zaniya cigaba da rayuwa batareda ita ba ?"

Yanata kuka yace "farko I lost amira yanzu kuma bazan iya cigaba da zama da Aisha ba ,yazaai namanta Aisha a rayuwata ,faseelat ina cikin tashin hankali"

Faseelat tasa hannu tana share mai hawaye tace "zaka cigaba da zama da anty zaka yafemata ,ka roki Allah ya mantar dakai abunda kagani"

Yace"noo sede nai addua Allah yq cire min sonta a rayuwata u know me well kishina yayi yawa wlh bazan iya kallonta ba a matsayin mata kona medota bazan iya mata adalci ba"

yaja numfashi ya cigaba da cewa"dama nafisonki a raina I was trying ne nake hakura da nuna maki so saboda ita ,yanzu bazan iya hadaki daita ba the girl that cheat on me tabawa wani kato jikinta ,abinda yafi dagamin hankali shine jinina dake jikinta tanada cikina taje tai zina dawani kato, faseelat Allah Aisha bata tsoron Allah "

Faseelat tace "stop saying that tana tsoron Allah tabari ne shedan yayi galaba akanta ,kayafemata koyane nasan anty bazata sake ba ,manzon Allah (S.A.W)yace ba abinda Allah zekara wa wanda aka zalunta kuma yayi hakuri face daukaka da girma ,kayi hakuri hero kadawo da anty,"


Ya share hawaye yace"plsss kidena maganar Aisha agidannan I want to forget all about her domin shine dede ,kitayani da addua Allah yakara sanyayamin zuciyata domin tanamin zafi inajin wani iri "

Tace"nadena ka cire damuwa kabar tunanin abun plsss kaga baka lpy inkuma so kake abun yayi affecting cikina shikenan"


Yayi shiru yana kallon cikinta yanzu ba abinda yafi jindadin kallo sama dashi ,


Memakon Su kwanta se alwala sukayi suna gayawa ubangiji bukatunsu,

Shi he is praying Allah ya cire mai son Aisha ya tsare masa jininsa,while ita faseelat tana rokon Allah ya shiryarda Aisha ya gafarta mata ya dedeta masoyan,


Har akayi asuba sannan suka kwanta bacci ya kwashesu,

Tun asuba anty salma tazo asibitin ,hankalinta tashe ,

Mommy na zaune take bata labari "salma Aisha batajin magana Aisha seda takoma gun bokannan Ashe son nabiye daita ya kamasu suna zina,salma ni yazanyi ne yanzu? ciki ne da Aisha gashi son ya saketa kuma bana tunanin Aisha zata iya rayuwa babushi bata iya sati batare dashiba bare rabuwa ta dundun"

Anty salma tace"yo anty ta inda akahau tanan zaa sauka samun wani bokan zamuyi a mantar dashi abinda yafaru akara masa sonta shida kanshi ze medata "

Mommy tasaki baki tana kallonta tace"salma bazan kara ziyartar wurin boka ko Malam ba ,yanzu bayan asara me zuwan yakaramin naje nabada kudina aiki lokaci kadan yatsaya gashi ita Aisha ancita a banza ba biyan bukata ,shawara zakibani wadda zata fishsheni don insamu Aisha ta fiddashi aranta shikuma nasan yadda zanyi dashi"

Anty salma tace"to idan tasamu sauki seta koma gidana da zama kinga zata dena ganinshi kuma zanyi bakin kokarina wurin ganin ta mantashi,Allah de yabata lpy"

Mommy tace"amin amma Aisha tasaka rayuwarta cikin wani hali batayo hali na ba kwata kwata donni bansamu namijin da nai maso haka ba don baruwana ko auren ko rabuwar"

Anty salma tace "yaran yanzu akwaisu da kwallafa soyayya just kiyi mata addua amma inajin tausayinta"

Mommy tace "dole ne"


Karfe 7 Aisha tatashi tabude ido tarikabin dakin da kallo anty salma,da mommy da Sadiya sukayo kanta,

Hawaye na zubar mata zuciyarta na mata zafi tace"ruwa mommy kubani ruwan sanyi zuciyata ciwo sosai"

Anty salma ta fiddo ruwa a fridge ta matsa tatada ta tana bata,

Ta dansha tabari jin bawani sauki shan ruwan da takeyi,

Ta medata ta kwantar daita,mommy tace"sannu Aisha Allah yabaki lpy"

Hawaye na zubarwa Aisha tace"mommy yaya ya sakeni ko? Ina yaya dan Allah mommy kubashi hakuri wlh bazan iya rayuwa in babushi ba ,ku kiraminshi dan Allah "


Mommy tai tagumi tana kallonta,
Anty salma tace "kiyi hakuri Aisha be sake kiba kuma kinsan baze zo dubaki ba yanzu kibari adan kwana biyu ze hakura"

Aisha tafashe da kuka tana danasani tace"mommy I cheat myself nacuci kaina da kaina wlh mommy ko yaya yamedani baze soni ba nasan yanzu ba wacce ya tsana sama dani,mutuwa zanyi mommy kutayani addua Allah yagafartamin nasani nan dawani lokaci zani mutu"

Kowanensu yanata hawaye Sadiya tace"anty kiyi hakuri zaki cigaba da rayuwa in Allah yaso kicire abun aranki kuma kita istigfariii Allah zeyafe miki"

Aisha tajuyar dakai ta cigaba da kukan nadama ,mommy ta zuba tea akatada ta zaa bata ta kauda kai tace"banaci banajin yunwa kubarni dan Allah"


Mommy tace"toshi cikin naki bakison yarayu ne?ki daure kici abinci don shima yayi kwari "

Hawaye masu zafi suka zubowa Aisha tace"mommy I'm regretting plsss forgive me ban dauki shawaranki ba ,ban tsaya dogon tunani ba nabiyewa shedan yanzu mommy what of in inada cuta wayyo Allah na"

Mommy tace "bakida ita bakida wata cuta aysha ki sawa ranki hakuri ko kinsamu lpy ki cigaba da renon cikinki"

Dan dole Aisha ta dansha tea din ta dauke kai,


Yunwa ce tatada faseelat daga bacci tara saura ta sauka kasa kamar taci babu tabude fridge ta daga robar nutri yoghurt ta banbameta ta shige kitchen dasauri abincin jiya ta dumama a oven ta zauna ta cinyeshi tasss ,

Sannan tatashi ta soyawa fahad kwai da dan Irish da plantain kadan ta kai kan dining da ruwan tea ta shiga toilet tai wanka tasaka blue duguwar riga me adon baki ajiki dankwalinta baki ,bawani makeup don daka ganta tana cikin tashin hankali, ta sauka tafara goge inda yakamata agyara agidan, dakyar tagama tana zufa sannan ta zauna a palon tanashan iska,

Se 10 saura fahad yatashi yanata ya mutsa fuska kanshi na mugun ciwo ya shiga toilet yayi abinda zeyi yafito yasaka kaya ya fito daga dakin ,ba inda idanshi yafara sauka se dakin Aisha ,idanunshi sukai jawur yawuce ya sauka kasa jiki mace,

Faseelat na ganin yafito ta tashi tsaye tana mai kallon tausayi ,

Yazo ya zauna kan kujera ya rumtse ido ,

Faseelat taje gefenshi ta zauna tace"kayi hakuri hero kazama me daukar kaddara me kyau ko akasinta,ka daure kaji mijina ,banason wani Abu yasameka "

Ya daga kai kurum tace"muje nabaka abinci sekasha magani ka kara hutawa "

Ya lumshe ido yace"banason ci kibarni plsss"

Tace "tom nima nakoshi kowa ya hakura da abincin"

Ya riko hannunta yace "hey kefa kinsan problem naki karki wahalarmin da babies dina plsss eat ur food"

Tace"tonaji kaima sekaci tukun kadaure "

Ya daga kai ,ya tashi yana rike da hannunta suka tafi dining, tunda ya tunkari wurin yake kallon seat na Aisha dana amira ,

Yaja seat ya zauna yakurawa seat din Aisha ido ,faseelat tafara zubamai tana hadiye hawayen idonta don itama abinda yake fado mata kenan,


Yana tuna lokacin da suke cin abinci awurin suna feeding juna time amira na da rai da time dabasu haifi ko amira ba yaduke jikin table yana kuka zuciyarshi na zafi ,

Faseelat ta ajiye zuba abincin ta duke itama tana kukan tanata kuka take cewa" meyasa nashigo rayuwarku meyasa nakamu da sonka? ina dorawa kaina alhakin komi saboda ni anty tai haka,dama bansan anty ba dama kome yadawo baya"tana kuka mecin rai,

Fahad ya dago da hawaye kan fuskarshi yana kallonta yace"kidena cewa haka u r my wife shiyasa hakan tafaru idan da batasanki ba maybe ba yadda zaai muhadu"

Ta dago tana kuka tace"look at the house bakowa saini yazanyi in manta baya yazan in manta rayuwarmu dasu anty "har numfashinta na daukewa ,

Fahad ya goge hawayenshi ya matsa gunta yafara gogemata hawayen yace" kidena kuka ,haka Allah ya kaddara ze faru ,barin gidan zamuyi donmu manta rayuwar da mukayi dasu kiyi hakuri kinji "ya cigaba da share mata hawaye,

Tai shiru tana kallonshi sotake tace mai yayi hakuri Su zauna don atunaninta ze sauko watarana amma abinda take gani yasa takara ganewa baze hakura yamedo Aisha ba,


Ya debo abincin ya kai fork bakinta ta kauce ta ansa tarika bashi yanacin abincin kamar madaciya,

Beci sosai ba ya dauke kai tacigaba daci tana ajiyar zuciya,

Fahad ya fiddo waya yakira sabeer yanason yabashi sako to office don se bayan week ze koma aiki,

Suna zaune a falo TV kashe sunyi zugum kowa yana tunani ,sabeer yayi knocking ta tashi tarufe kai taje tabude ,

Sabeer yashigo da faraa yace" amarya bakya laifi "

Tai yake, tace"ina kwana"

Yace"lpy lau "yana kallonta

Tajuya ciki sannan yashigo shide he love faseelat shaawarta ma ce yasa ya auro fatouma dan Suna kama amma they're different fatouma zuciya tana iya sati tana fushi in ta gadama ,shiyasa yafison radiyarshi itakuma Jan class amma bata saurin hawa ,


Daace lpyar fahad lau dabaa bunda ze hana ya zage sabeer tasss saboda kallonda yake mata,

Ta zauna gefen fahad shiko yazauna kujerar dake facing nasu fuskokinsu duk ba annuri sema jawur dasukayi,

Yana raba ido yace" lpy kuke ko?meyafaru?"

Fahad yace"lpy lau" ya mikamai wata small laptop yace "kabawa manager banjin dadi senan da week zancigaba da aiki"

Sabeer ya zaro ido yace"amma kasan hakan naiya jawo maka problem kuma wane irin ciwo ne wannan?"

Fahad yace"kayi yadda nace kabashi kuma ciwon zuciyane da bp shikenan"

Sabeer be yadda ba ya kalli faseelat yace"faseelat mike faruwa ?naga kamar anyi mutuwa nasan ba ciwo ne problem dinba"

Tai shiru kanta kasa fahad yace"ni zaka tambaya ba itaba kuma nabaka amsa plsss leave

Please Login or Register in order to submit comment