Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ana shigowa dasu, dayake dama alhajinsu khalil yayi retire shine yabude babban supervision store da kudin retire nashi.





da Faraa abba yashigo gida ummi na masa sannu da zuwa tace "wai lpy kake ta faraa "

Yayi dariya "surukanki har sunzo sun tafi "

Tace "eh se akai yaya? "

Yace "uban diya har yasaka rana nan da 3month ran Friday "

Ummi farin ciki ya lullubeta tace "to Allah yasa alheri "

faseelat na kitchen tanajin abinda suke fada lokaci daya cikinta ya juya ji Kake kululululu, ta tashi da sauri tatafi kewaye tafara fetsa zawo,
[7/12, 10:58 PM] Maman Mamy: ➰➰➰➰➰
*RAGGON MIJI*
➰➰➰➰➰





By



*MAMAN MAMY*



https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
*~GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION💫💫💫~*


*~❄We beare's of soon golden We writer's assiduously percieven No pain so Magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Our worlds for it cause u np pain~*




1⃣2⃣



*dedicated to sis zulaihat*





Shikenan yanzu tagane kowa baya sonta har shima baba babba baya sonta, ta dauki mintuna kafin tafito,

Su abba ko shigarta kewaye ba su gani ba dan Sun riga sun shige daki,

Faseelat wani dutse ne ya tsaya mata awaya, tana tuna firarsu da khalil ta jiya, wai ya mata missed call daya da safe be sake kiraba se dare, ana cikin fira yake tambayar ta wai bata ga missed call dinshiba? Tace tagani amma daya ne yace dayan ai, ai ni bana missed call biyu innayi daya ba bukatar insake maybe Wanda na kira yana busy "

Tace "ko? "

Bakaramin haushi maganar shi tabata ba, dazun da safe ma yakira bata daga ba, tariga tayi alwashin seta sakashi ya rika mata many missed calls.

Lokacin da khalil yaji labarin bakaramin farin ciki ya shiga ba wanda yakasa boyuwa ko da akan fuskarsa ne,

Hjy saratu ta banka mai harara tajin haushi tace "seka fara shirin biki bawai yin wata hidima ba "

Ya sosa kai "ai Hjy lefe ne kawai aiki na kinsan abba ya dade da bani wani gida da yagina can a layout fenti kawai zaayi se kantoci "

Tace "eh dukda haka lefen da Kake gani bakomi ba se yazama aiki, kai lefe fa yana cin kudi sosai ,dan haka yanzu kameda hankali kawai akan abinda ke gabanka "

Yace "to Hjy "ya tashi ya fita, tace "shashan banza kawai kamar anmasa bushara da aljanna ko kunya bayaji mtsssw"

Shi ko dakinshi yawuce ya ciro wayarshi yayi dialing number faseelat,

Faseelat na kitchen stew ma ce take soyawa wayar na hannunta tana chart ya kira, harta tsinke baa daga ba, ya ajiye wayar Ahankali murmushin dake kan fuskarshi Ahankali ya bace, gashi so kawai yake suyi magana, yace "bari na bari zuwa anjima"

Faseelat naganin kiran ya tsinke tace"kasake kira in abun ya matse ka "

Ta koma charting dinta, kawai se ga maman amira ta turo a group "slm yanuwa inamaku bankwana zamuyi tafiya ni da mijina zuwa Cyprus, se Allah ya mana dawowa I'm going to miss you "

Ta tura ma group din da tasa akasa ka faseelat,sega best wishes Nata shigowa, wasu naturo zamuyi missing naki muma da alamu ta dade da sabawa da yan group din, tun ranan da sukayi saving contact na juna basu kara magana PC ba sede a gaisa a group,

se faseelat ta bita prvt "anty tafiya zakuyi ne? "

Maman amira ta tura mata "eh faseelat gobennan around 4am zamu tafi tareda mijina "

Faseelat tace "amira fa? "

Tace "wurin momy nakeso mu barta nima nadan huta, inde daddynta ya bari"

Faseelat tace "anty kitafi daita mana "

Maman amira tace "ai duk takare dole mutafi Daita dan daddynta bana tunanin zeiya 3wks batare daita ba "

Faseelat tatura smile emoji tace "yanzu se yaushe knan? "


Maman amira tatura "2 to 3 months only "

Faseelat tace "zanyi missing naki anty"

Maman amira tace "ki dena kira na anty kila ma kin girmeni "

faseelat tai dariya tace "yakamata ko insanki "

batare da bata lokaci ba maman amira taturo mata pic dinta a kasam sa ta rubuta "my name is aisha, I'm just 23 years old married with one girl name amira "

Faseelat na bude pic din ta tsaya kallonta kyakkyawa ce black beauty gajera ce amma baso saiba bata da kiba inde kaganta Zaka iya cewa shekarata 19 Daganinta tana jindadi, ko kayan jikinta Sun isheka kallo,

Bata gama kallon Nata ba taga Anturo wani ta bude kasan sa an rubuta "baby amira "
Ta tsaya kallon yarinyar yar 3yrs fara fesss irin farinnan ba ja ba gashegen kyau tana sanye da gownt fara tasha twisting, bakaramin burge faseelat yarinyar tai ba, tawani rike kugu ta sunkuya harda su turo baki gaba faseelat tace "duniya inda ranka kasha kallo yaran yanzu da zamananci ake haifarsu jibi yadda tai wani style "har cikin ran faseelat taji tanason amira, faseelat ta tura "wow maman amira kibani amira mana inasonta sosai "

Aisha tace "hmm faseelat da se me wannan diyar ya daureki, zande baki aro "

Faseelat ta tura dariya "nide wlh inasonta kunyi kyau sosai, amma duk da haka kingirme ni sunana faseelat b maaruf shekaru na 21 "

Ta tura hoton ta,

Ta tashi tafara zuba miyar da take soyawa a cooler dan tuni ta sauketa har ma tafara kamu, tana juyewa ta bude wayar,

Ga reply din maman amira "faseelat kina da kyau sosai inama ni ce ke danaji dadi Kindace a komi ko a suna "

Faseelat ta tura mata "Nagode sosai maman amira se anjima ko kuma ince Allah yamedoku lpya"

Maman amira tace "amin mommyn amira "

faseelat bata iya tura komi ba saboda kiran khalil da ya shigo, tai rejecting abun yabashi mamaki ko second baaiba wani kiran ya shigo faseelat ta fashe da dariya "kai da kace baka kira biyu yanaga haka? "

takara datse kiran khalil besan lokacinda yakara kiranta ba ta dauka ta yamutsa fuska tai shiru,

Yace "haba faseelat mi yayi zafi da zaki rika rejecting kira na?"

faseelat ta murguda baki "bakace bakayin missed call biyu ba? shine na ke gwadawa, ashe abun naka bame daurewa bane "tai dariyar rainin hankali.

Yayi shiru "ba da wata manufa nai wannan maganar ba faseelat ,baki fahimceni bane"

Faseelat tace "na fahimta mana "

Yace "to kiyi hakuri in missed call din ne kikeso kinsamu shikenan? "

Tace "bansaniba"


Yace "to Allah yabaki hakuri se anjima"

Ya kashe kiran kiran ta ma yayi ya fadamata abun farinciki amma tasako wannan batun.


maman amira kau itama sauka tai tunda tagama rabawa duniya cewar zasuje Cyprus dukda ba zuwanta waje na farko bane,


A sannu lokaci ke tafiya abubuwa masu dadi da marar dadi na faruwa har anyi wata daya dasaka baikon su khalil gaba daya yangidansu faseelat bawanda be saba da shiba dukda de bai cika sakin fuska can-can ba,

Faseelat kau gyara takesha daga sama har kasa, to da anyi na banza ma bare yanzu me dalili,

Lefe Nata haduwa har ansiyi akwatuna anata zuba duk abinda ya samu akwati 6 ne setin hello Queen, Hjy bata nuna komi dan itama burinta ta fita kunya dan tana daga cikin masu zuwa ganin lefe gidaje inbe yiba aita surutu.


Bangaren soyayyar khalil da faseelat kau abunde ba cigaba firarsu a waya bata wuce 2mnt saboda besan firar da zasuyi ba, be iya tsara mace ba sam,
Inkuwa zuwa yayi to befi yayi 20mnt ba kusan rabin lokacin duk kan kallonta yake tafiya.

Yau ya kirata zezo danhaka tafito tana hadamasa abinda zeci dan ummi ce ta koya mata yi masa girki da drinks in zezo.
[7/12, 10:59 PM] Maman Mamy: ➰➰➰➰➰
*RAGGON MIJI*
➰➰➰➰➰



By



*MAMAN MAMY*



https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
*~GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION💫💫💫~*


*~❄We beare's of soon golden We writer's assiduously percieven No pain so Magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Our worlds for it cause u np pain~*




1⃣3⃣



*Dedicated to ALL RAGGON MIJI FANS*




Kuma hakan bakaramin dadi yakemasa ba dan sakin jiki yake yaci abincin sa wanda hakan bakaramin mamaki yake bawa faseelat ba,



Gaba daya ummi tayi tayi faseelat tabar shiga kicin saboda gyaran jiki da ake mata, faseelat taki ita bazata iya kwanciya ba mahaifiyarta kuma na aiki,

Dole ummi ta siyo gas cylinder yanzu dashi faseelat ke girki, saboda gyaran da faseelat ke samu har wani damshi damshi da maiko fatar keyi,gashi ta kara haske yanzu kam faseelat kamar fitila ce .

Gas din tadora shaf shaf tai masa alkubus da stew, tun jiya da daddare ta bada ishak ya siyo mata banana, garin Katsina garin manoma zeyi wuya ka nemi wani naui daga fruit ka rasa ko da wane lokaci gasunan bakin titi suna wali,

Banana milkshake take so ta masa, shaf shaf ta Gama ta zuba a jug tai arranging abincin a dakin ummi dan yan zu har cikin dakin ummi suke fira.

Da yake khalil yafi zuwa da safe yau ma duk da be fadamata ba tasan bewuce yazo karfe 11 ko 12 ba.

Tana fitowa wanka ta zauna bakin madubi tana kallon kanta, kumatunta ta dan latsa tasaki murmushi, "wlh ni me kyau ce dubi yadda na kara haduwa "

Tace "bari de natsaya na tsantsara kwalliya saboda gudun raini kullum yana gani na ba makeup aise ya rainani "

Ta zauna ta tsantsara kwalliya uban ubansu ta saka doguwar riga baka ganin doguwar rigar dankwalinta na da girma se bata saka hijab ba, ta yafa gyalen rigar, ta tsaya gaban madubi ta jujjuya .

Tana cikin juyawa ummi ta shigo dakin tana ganin abinda take, se tai dariya tace "to gashi can yazo seki fita karyaita jiranki"

faseelat ta dauko turare ta kara feffesawa sannan tafita zuwa dakin ummi.


Tunda ta tunkaro dakin kamshi ya sanarwa khalil faseelat na gab da shigowa dan haka ya kurawa kofar ido, tana tafiyarta normal amma shi awurinshi kwarkwasa take, har ta zauna kan kujera.

Ta sadda kai sannan ta dagoshi a hankali ta Kalle shi, duk lokacin da yake mata irin wannnan kallon bakaramin haushi yake bata ba, ta dauke ta ja gyalen sama sama ya rufe mata rabin fuska,

Cikin sanyayyar muryarta tace "sannu da zuwa "

yayi firgigit tareda gyara zama, kusan 2mnt sannan yace "na sameki lpya?"

Ta yamutsa fuska "lpya lau "

Yace "ya hidimomi "

Tace "suna wurinku "

"mu suwa "

Tace "ku manya "

yayi dariya "to yayi "

Shiru na wani lokaci, sannan faseelat tace "ga abinci nan bismillah"
Tai zauniyyarta dama ba ita keyin serving dinshiba, yadanyi danne dannen waya sannan ya zuba, milk shake din a copy tunda yakafa seda ya shanye yaajiye, ya jawo kular abincin alkubus goma ne a kular saboda shikadai taiwa, ya zuba guda biyar ringis ya zuba miya gefe, Cas...cas..cas karar cokali ne kawai ke tashi, faseelat kau dukewa tai tana charting da wayarta, ya cinye biyar dinnan tas, ya sake juye biyar din, suma tass ya cinye ya kara tsiyaya madarar a cup ya shanye sannan yabuga uwar gyatsar sa wadda tasa faseelat dagowa ta Kalli kulolin gabanshi kular alkubus bude take alamun bakomi ciki, ta kalli jug din taga yafi half, ta daure fuska.

Shiko ba ruwanshi handkerchief ya fiddo daga aljihu ya goge bakinshi, tare da furta "alhamdulillah, gaskiya girkin yau yafi karfinki nasan bake kikayiba ummi tayi "

Tace "ihhhhm" ta yatsina hanci sama tana mai kallon wawa.

Ya jawo wayar shi ya lallatsa bayan minti biyar ya medata aljihu ya kalleta "ni zanwuce se na sake waiwayo "ya ajiye mata bandir din 100 guda daya.

Tace "to yayi "

ya mike yayi hanyar fita yanata mata kallon bankwana, har yakai kofa yaji tace "Allah yakiyaye"

ya waigo yayi murmushi wanda yasa bakinsa kara fadi ya juya yafita, faseelat tace "kam wlh daace bakinka haka yake da ko kasuwa aka kaika bazaka siyuba.

yana fita ummi ta shigo dakin, tana kallon faseelat, faseelat ta mike tsaye, zata fita ummi tace "wai duk ya cinye alkubus din ina tunanin in ya rage inzo inci naji kamshi Nata tashi lokacin da kina girkawa"

faseelat tai dariya "waccan wawan ze rage sa ne? Ya cinye shi tass, ga sauran madara nan yabar miki ki dan kora, wlh natsani namiji me yawan cin abinci kamar mace ai mata akasani da ci, kuma shi ba kunya gidan surukai yasaki jiki ya tande plate "

Tunda take magana ummi ke hararta sede da yake ta juya mata baya bata gani ba.

Ummi tace "amma faseelat baki da daa, ya kikeso ki meda kanki kina girma kina kara rashin wayau, haka zaaimuku auren kije kitamishi yadda kika ga dama? To wlh kibari tun kan kishiga gidanshi, yo inama laifinsa da kika samu yaci, da beci ba ai bazakiji dadi ba kema."

Cikin ran faseelat tace "da yaci da kar yaci uwarsu daya ubansu daya " amma a fili ta langabe kai "Allah yabaki hakuri ummi "

Tai sauri tabar dakin ummi tabita da harara "shashasha kawai wadda batasan ciwon kantaba, yaro nata miki hidima ke kina wulakantashi"taja tsoki taje ta dauki kudin da yaajiye tai daki,


bayan sati biyu, faseelat ce rike da troly tsakar gida ta rungume ummi tana kuka, ummi ma hawaye take can zuwa ummi ta banbareta daga jikinta, tace "haba faseelat kamar yarinya kinata kuka harnima kinsa nayi kukan ni wlh bacin yan hade -haden da nakeso amiki aida bazaki tafiyar nan ba, kiyi hakuri mana "

Ta goge mata hawaye sannan tace "ki gaida min so dijen da su ammah, ki tabbatar kin zagaya dangi kinmusu bankwana kafin ki dawo "

Ta daga kai ta juya ishak ya anshi trolyn suka fita tana rike da auta Mubarak.

Gidan baba babba suka rakata zasu tafi Niger kanwar ummi ce ta ce taje can su gyarata gyaran ze dauki lokaci shiyasa zasu tafi yanzu ,su ishak na ajiye kayan suka juya danbasu son ganin tafiyarsu, kiran khalil ne yashigo wayarta, ta share hawaye ta dauka tai shiru,
Yayi sallama bata amsa ba, can zuwa yaji ajiyar zuciya, yace "faseelat kuka kike? "

Tai shiru yace "dukafa wata daya ne"

tai shiru shima dauriya kawai yake maganar da yakemata, can zuwa yace "ganinan zuwa muyi bankwana, kina gidan baba babban? "

Tace "eh "

Yace "ganinan zuwa yanzunnan"

Ta datse kiran matar baba babba wadda suke kira baaba tace "amarya, amarya ki adana kukanki se ranar da zamukai ki gidan miji sannan, "

Faseelat tadan fadada bakinta, sega kiran khalil har yazo, ta tashi tafita, yana ganin fuskarta tai jawur ya bata fuska kamar zeyi kuka "kiyi hakuri mana faseelat,"

Faseelat ta daga kai yace "ga wannan inkinje kinyi amfani dasu "

ya mika mata wata leda ta amsa tadan leka cikinta sweet -sweet ne kala -kala se wasu yan dubu -dubu dunkule kila sunkai ashirin ,

Ta rufe tace "Nagode, ni zanwuce kar baba yafito "

Yace "to Allah yakiyaye "

Tace "amin "ta juya ta shige cikin gidan, tuni idanun mazaje yacika da hawaye ya samu yayi ta maza ya shanye su, ya dade tsaye sannan ya tafi.

Be dade da tafiya ba baba babba yafito daga sashensa cikin shirinsa, ya kalleta "diyata harda kuka canma ai gida ne "

Ta dukar da kai yace "to tashi mu wuce "
Lokacin kusan karfe 10am na safe suka dau hanyar niger.



Faseelat a niger........





Team khalil on top 🤪
[7/12, 10:59 PM] Maman Mamy: ➰➰➰➰➰
*RAGGON MIJI*
➰➰➰➰➰



By




*MAMAN MAMY*




https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
*~GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION💫💫💫~*


*~❄We beare's of soon golden We writer's assiduously percieven No pain so Magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Our worlds for it cause u np pain~*




1⃣4⃣



*This page is all for you sweetie*




*ina godiya ga masoya na, ina ganin sharhinku kuma inajin dadi, insha Allah zakuji dadin labarinnan dan bamuyi komi cikin shiba domin akwai doguwar tafiya a gaba, faseelat na gaida masoyan ta all over the world, khalil kuma yace a fada maku akwai ga garumar walima kuma yana gayyatar ku zuwa daurin aure*.




Tafiya ce me dan tsayi ga wanda be saba yin ta ba,

suna tafiya, baba babba yanata dan janta da labari yace


"faseelat wace color ce best color taki? "

Tai murmushi tace "brown "

Yana kallon titi yace "kin tabbatar? "

Tace "eh baba"

Yace "to ba matsala dama dan asiyo miki kayan daki irin kalar da kikeso dan inaga duk lokacin da zaai wannan bakinan naji ance wata daya zakiyi "

Tace "eh "

Yace "Allah yakaimu, ai hakanan ma kike kuka nasan omer yana can yana murnar zuwanki "

Tai shiru itafa bata kaunar dan karamin abunda ze rabata da ummi ko da na kwana ne.


Bayan laasar suka isa,

Wow Niger garin buzaye garin rakumma garin sahara lol ,

direct gidanshi ya wuce yayi parking faseelat tafito tana kara kallon garin rabonta dashi kusan she Kara daya kenan,
Batare da tabi kan trolynta ba tai gaba da sauri zata shige cikin gidan,

Baba babba yace "zo zo faseelat dauki akwatinki ki wuce dashi ciki "
Se sannan ma ta tuna da wani akwati ta dawo ta dauka tai cikin gidan.


Tana sallama yaran dake nan suka ruga wajenta suka rungume ta ,tana ta raba ido taga fadila bata ganta ba, sega ammah ta fito jin hayaniya tana faraa tace "sannunku da zuwa amarya "

Faseelat tai murmushi "ina wuni ammah"

ammah tace "lpy lau ya gajiyar tafiya ?ki shigo ki ci abinci kiyi salloli "

Faseelat "tace ina su fadila da husnah? "

ammah tace "ai suna islamiyya amma nan ba da jimawa ba zaki gansu "

"yaya omer fa? "


Ammah tai dariya "yana school shima yakusa dawowa kishigo ki huta mana inje in kula da mijina nima "

faseelat tai dariya taja trolynta zuwa cikin dakin ta zauna kan kushin, ammah ta kawo mata abinci a plate tafita, faseelat ta tashi ta shiga toilet ta yi bawali ta wanko hannu sannan tafito ta zauna ta bude plate din shinkafa da miya da salad ce, tasaka cokali tana ci a sannu,


Bayan tagama ta yo alwala ta kabbara salla, dayake kasaru tayi shiyasa bata dauki lokaci ba, ta dade tana addua,

Sallamar fadila ne ya katseta, fadilan tana ta jindadi ganin motar babansu kuma mamansu tace tareda faseelat zaya zo,

Dasauri faseelat tafito dagudu fadila ta rungumeta "oyoyo yar uwa "


Faseelat tai breaking hug din ta Kalli fadila sama da kasa tace "yar uwa Kin girma hardasu kidayar dangi akafara "

Fadila ta bata fuska "da ya kike so ne? "
Ta harareta shigowar husna yakatse faseelat suka rungume juna suna murna, sannan suka shige daki.

bayan kamar 15mnt omer yashigo gidan da sallama,aikuwa faseelat da gudu tafito ta rungume shi se kuka,

Ba karamin kashe mashi jiki tayi ba da kukanta, a sannu ya dagota yana goge mata hawaye, "miye na kuka kuma? Ki shiru plsss kukanki na daga min hankali "

tai shiru tana ajiyar heart yana tallabe da fuskarta yana kallon kwayar idanunta yace "kinyi kyau kanwata "tai murmushi kawai ya Saki fuskar ya kama hannunta zuwa dakinshi,

Tana zaune ya rage kayan jikinshi ya rage daga shi se singlet da wando jumper ya shiga toilet din dakin ya yo brush yadawo ya zauna cin abinci yana ci yana kallonta itama shi take kallo kullum de bazata gaji da yabon danuwanta ba yayi a kowane Fanni, ya katse shirun da cewa

"yasu ummi da auta?"

Tace "lpya lau suke, suna gaidaka "

yace "ai ummi takirani jiya tace zakizo in kula dake "

tai shiru yace"kitashi ki shirya mutafi gidan dijen "

Ta tashi tsaye ya dago ya kalleta har tafita ya girgiza kai a zuciyarshi yace "tunda bazaki bi shawara ta ba ai shikenan "

he have been advising her ta je ta fadawa baba Babba bata san auren amma taki a karshe ma Cewa tai tafara son khalil din ,shiyasa ya kyaleta,

Yana Gama cin abinci ya tashi ya watso ruwa ya shirya suka tafi gidan dije shi da ita da fadila,

Suna isa dije se murna take takawo masu abinci tai nan tai nan, su omer da fadila suka barta suka koma gida a tare, domin shi omer tuni Sun dedeta da fadila wadda dama can tasu tazo daya.


tun daren ranar akafara gyaren faseelat taff,ko sati baaiba takara jin shaawa ta mata yawa, abun mutum baze yarda ba domin har zuba takeyi kamar me mensis, nasan wasu zasu ga cewar novel ne kawai amma it's happening wlh dan wani lokaci irin wannan yanayin harda ciwon mara yake Saki,

Kiri-kiri faseelat bacci nason ga gararta saboda shaawa, itaba abun ta dau azumi ba tunda shaye-shayen da take wasu ma dasu take breakfast, dubarar da tayi shine tadena zama ita daya kullum tana like da fatoum wadda tama girmeta, bata aikin komi tunda taje,


*Bayan 3wks*


Lefe ya Gama haduwa hjy ta kikkira danginta da abokanta da makwabta ganin lefe, ba lefi lefen yayi kyau kuma de anyi kokari wajen kala 45 bag 5, 10 shoe's include bathroom slippers, 6 hijab, kaya de sunyi.

Mutane dodo-dodo ake zuwa ganin lefen dadi kam yakashe hjy domin ita macece meson ace komi Nata yafi na kowa,

bangaren su ummi kuwa tuni anje angano gidan faseelat matsakaicin gida ne, ciki da falo da toilet se waje kitchen store da toilet na waje da dakin khalil falle daya, tsakar gidan beda girma sosai se get dake makale da bangon gidan,


Baba babba yariga yabada kudin yimata furnitures se nanda 10days zaagama kitchen plaza kawai yaje yace ahada mishi all kitchen material, aka hada yana zaune ya Kalli kayan yace akaro, irinsu food flask da jugs set 5, aka hada kayan kusan million daya ba abinda babu har su gas toaster oven d. s.

Ya bada ATM aka cire, suna da motar kai kaya danhaka har kofar gida aka kai kayan aka zubasu a old garage nashi kafin ran jere.


Khalil kau sukan dan taba waya da faseelat amma ba sosai ba saboda rashin lokaci dabata dashi, gaskiya yayi missing dinta dan kullum da tunaninta yake barci.



Bayan sati,


yau faseelat shirin tafiya kawai take, gashi motar haya zata hau dole ta fita da wuri yanzu kusan 7am tana fitowa daga dakin tana kiran "dije.. Dije! Na shirya" sega ya omer

Yana kallonta yadda ta canza yace "zuwa nai muyi bankwana, zan wuce school ne kigaida ummi,Se nashigo daurin aure "

Bata iya bashi amsa ba ta bishi da ido, ganin ranshi bace yake, seta fara tuhumar kanta mima yasa ta fadamishi bata son auren gashi tabarshi cikin tunani, danuwa kenan me hana kansa sukuni saboda matsalar dayan danuwan.

Baffa dan yayar ummi shi yakaita tasha yanata tsokanarta wai ta kode tai kamar aljanna karta je ta tsorata mijinta.


Yana kai ta suka dau hanya,

motarsu ta samu matsala a hanya ga shi cikin daji, sukayi cirko cirko suna jiran su samu wata.


Da kyar suka samu ana daukarsu da dai daya wannan yasa se Maghreb taisa, se murna kowa yake,

harta kwanta kiran khalil ya shigo kamar karta daga se kuma ta daga, ya mata ban gajiya ta kashe.

Washe gari aka kai lefe gidan baba babba mutane suka fara zarya biyadin ma biyadin.

Seda yayi kwana biyu aka kaishi gidansu faseelat, ko kadan lefen be mata ba ,ba English wears ko daya se tarin atamfofi kamar me, haka de taje takai dinki.


yau saura kwana goma auren, kamar daga sama sega wata kawar hjy da suka dade basu haduba, bayan gaishe gaishe, kawar wadda ake kira rakiya tace naji ance danki zeyi aure "

Ummi tace "eh abu yazoma sauran kwana bakwai, "

rakiya tace "naji ance diyar hjy asiya ce wadda ke can kofar durbi wadda kukaje hajj tare "

Hjy ta washe baki "aiko haka abun yake"

Rakiya tace "kina aikinmi, Zaki hada jinin ki da nasu asiya, tobari infadamiki asiya ko kara ta aje alhaji maaruf be tsallakewa nasanta sosai munyi zama unguwa daya kafin su tashi, tariga ta mallakeshi, cewa ma akai danginsu wani lakani garesu inde aka kusancesu to shikenan Sun mallake mutum se yadda sukace, ke mi zaki hada jini da yan niger? Kinsan su da tsirface tsirface da shan kayan matan tsiya kamar danshi aka halicce su, aiba hakanan suke ba "

Hjy tsoro ya da baibayeta jikinta har kyarma yake yi saboda tashin hankali ,tace "aiko wlh dole afasa aurennan, muddin ina numfashi bazaai aurennanba kawai? Wlh rakiya tunda yaronnan yaje ganinta shikenan ya sauya ashe har an fara asirce shi wlh bazeyiwuba sam "

ta jawo wayarta ta kira alhaji,yana dauka tace "alhaji kataho gida ba lpya "


hularshi kawai yasaka ya nufi gida a 360....
[7/12, 10:59 PM] Maman Mamy: ➰➰➰➰➰
*RAGGON MIJI*
➰➰➰➰➰




By



*MAMAN MAMY*




https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
*~GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION💫💫💫~*


*~❄We beare's of soon golden We writer's assiduously percieven No pain so Magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Our

Please Login or Register in order to submit comment