Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

,akunyace ya tura kofar ya shiga wayam ba faseelat basu ummi yabi gadon da kallo zuwa jinin dake sargafe ,ya karasa ya tura kofar toilet nanma wayam hankalinshi tashe yakaiwa abunda ake dannawa for emergency bugu ya dauki kara, duk yaburkice ko 1mnt baaiba doctor yashigo da nurses biyu, sukaga gadon wayam se fahad dake tsaye kamar mahaukaci,

fahad jijiyoyi amike yace "where's my wife? Ina matata where do you take her? "

Doctor da mamaki yagama cika shi yace "this is unbelievable, how will this happened in my hospital? "

Ya kalli fahad yace "I'm sorry sir bansan komai ke faruwa ba amma we have CCTV cameras all around the hospital zamu gano mike faruwa"

Fahad ya dafe goshi kanshi na mugun bugawa ,su ummi suka dauketa kokuwa? Yana ta tambayar kanshi,

Doctor yadafa shi yace "meet me in my office "

Yajuya yafita tareda nurses ,hawaye suka zubowa fahad yace "meyasa zaku dauketa? Ni yadace na kula daita"

Ya fita ya nufi office na likita,likita yanata duba computer abunda yafaru akofar dakin faseelat ya juya wa fahad computer yace "take a look at them do you know them or seen them before? "

fahad ya kalli computer omer ya fito dauke da faseelat ranshi yakara baci yace "he's her brother, but saboda me zaabari sufitar min da mata a asibity su suka kawota ?yama akai suka san we are here? bazan kara kawo patient a asibitin nan ba tunda it's not safety "

doctor yajawo computer gabanshi yayi rewinding lokacin da bello yakawosu kofar dakin ranshi ya baci yaja telephone ya kira number office dinsu bello ba dadewa sega shi ya shigo yanata hada zufa,

fuska tamke okato yanunawa bello computer yace "meyasa ka kira wadannan mutanen waya aike ka? meyasa ?"

bello yace "I'm sorry nasan yayanta ne banyi tunanin fadamishi ze zama matsala ba kuma nayi iya kokarina na tsayardasu basu tsaya ba "

fahad jiyake kamar yakaiwa bello naushi don haka ya tashi yafita ,

okato yace "meyasa baka fadawa securities ba? U r suspended kaje sena nemeka "


Bello ya fara begging "I'm sorry sir it's a mistake wlh danasan haka zata faru da bazan kira shi ba dan Allah kayi hakuri "

okato ya nunashi da yatsa cikin nuna gargadi yace "next time idan haka tasake faruwa zaka bar nan harabada,now leave "

Bello yajuya yafita yana yamutsa fuska cikin ranshi yanata regretting kiran omer,


Fahad nafita yashiga mota ya nufi gidan umma don besan ya zaiyi ba, a mota hawaye yake tayi duk lokacin da ya tuno ihunta da jinin da ya zuba seyaji hawayen tausayinta Sun zubomishi,

ya samu yaisa gidan umma suna zaune suna kallon film din su bosho munafikin mata sunata dariyar yadda yake fadawa hafsa idris cewa jamila nagudu wari take seya toshe hanci yake bacci saboda tusa, kwasar dariyarsu kawai suke hankali kwance ,ya shigo main falon wuji wuji dashi riga duk jini, dukkansu faraar dake kan fuskarsu ta gushe yaje wurin umma ya zauna kasa tana kan kujera yadora fuska akan cinyar ta yasaki kuka,

Umma tadora hannu ta tallabo fuskarshi zuciyarta na harbawa dasauri tace "meyafaru fahad jinin minene ajikin ka haka? "

yana kuka yace "umma I cheated myself na doki faseelat har tayi miscarriage "

umma dasu lady suka dau salati "innalillahi wainna ilaihi rajiun!"

Umma kamar zatai kuka tace "me tamaka da zaka dauki wannan hukuncin? Faseelat ce fa ur love meyasa zakai haka? "


Muryarshi na rarrabuwa yace "naga pic dinta da wani awayarta I tried my best nakasa controlling kaina shine na doketa"

umma tai shiru hawaye suka zubomata na tausayin baiwar Allah,

ya cigaba da cewa "na kaita asibity ,wani doctor yakira yayanta yafadamishi ina komawa nasamu Sun dauketa Sun tafi daita, ya zanyi ne umma? "ya cigaba da kuka,

Su lady suna hawaye suka tashi sukabar main falon,

Umma tasamu ta goge hawayen fuskarta tace "sunyi dede kuma Sun kyauta konice abinda zanyi kenan, banji dadi ba da dana yakasance mahaukaci me dukan mata ba don duk namiji me hankali bazaya iya daukar hannu ya daki matarshi ba ,bare faseelat yarinya me ladabi da biyayya me sonka me addini amma har kaiya cutar daita kayiwa kanka ai don bazaka taba samun kamar ta ba "

yana hawaye yace "umma Dan Allah ki temakamin kije ki basu hakuri wlh inasonta kishinta ne yasa nai haka"


umma tace "yo kishi haukane ko kai kadai ne me kishi aduniya? Saad daya daga cikin mubashshirina bil janna yace dazan kama wani akan shimfidar iyali na dazan sare shi da adda kuma ta wurin kaifin zansa se sahabbai sukaita mamakin kishinsa manzon Allah (S. A. W) yace shin kuna mamakin kishin saad ne? yace wlh ni nafishi kishi kuma Allah yafimu kishi gabadaya,bakai kadaine me kishi ba fahad amma ai kishi bekamata ya rabaka da hankalinka da imaninka ba har kayi kisan kai ko agadon ta kasameshi? kasan yaya suke daita ne? Shin kai baka daukar pic dasu lady dasu ramlat? , wai duka ne har ze zubar da ciki wlh fahad bakayi ba ni banda temakon da zan maka sede zan baka shawara ka koma wurin malamai kakara neman ilimi saboda da kanada ilimi wadatacce da baka aikata haka ba "

ta dauke kanshi tatashi zata haye sama ya waiwaya fuskarsa gwanin tausayi yace" umma tafiya zakiyi? "

Batare da ta jiyo ba tace"eh tafiya zanyi ko zaunawa zanyi na tayaka kukan katashi kabarmin gida "ta haye sama ranta bace,

wasu zafafan hawaye suka zubowa fahad dama anan kadai yake tunanin samun sauki kuma itama ta hau ya dade zaune sannan ya tashi ya fita ya nufi gida,


Yana zuwa ya danne horn bako dagawa baba tsoho na toilet yaji odar tayi yawa ko tsarki besamu yayi ba yafito da gudu yaja gate din dayake sliding ne,

fahad da kanshi ke jikin sitiyari ya dago yaja motar cikin gida,


Yakai kusan 15mnt zaune sannan yafito yashiga cikin gidan, dakin faseelat ya nufa zuciyarshi na harbawa tuno jinin dake kwance adakin,

dakin a bude yake yana zuwa yayi tsaye ya dafe kofa yasa sabon kuka dakin duk jini bakyan gani, ya karasa ciki yanata kukan yayi zaman dirshan gaban gudan tsokokin dake a wurin yana ta kallonsu yana kuka, yake tuno maganar faseelat "amma kasani cikinnan shine farincikina shi nake burin gani ayanzu nabaka amanarshi karka bari wani abu yasameshi"


da kuma inda take cewa "zan haifarma baby boy kasamu freind"

Kamar dan maye yafara magana "meyasa zaka zube?inason naganka araye banyi don na cutar da kai ba, katafi kabarta she love you ur her happiness and joy why zaka gujeta? it's just an accident meyasa bazaka hakura ba..." maganganun duk gasunan yadade yana sambatu, har yakai yayi kwance agun,

can zuwa yatashi yasamo leda ya sa hannu ya fara kwashe abinda zeiya kwasuwa yagama ya kulle ya ajiye gefe, ya cire shirt din jikinshi ya gogge abinda yasamu yafita ya dauko mofa yazo ya goge wurin sosai ya kuma sa fresheners duk da haka seda dakin yadauki kanni,

yafita yaje can garden yayi rami ya rufe ledan da rigar yadawo ya shiga toilet yasakarwa kanshi ruwa yanata meda numfashi, yana cikin cuda jikinshi ya tuno yadda yaja faseelat daga toilet din tana cikin cuda jikinta yakai wa bango naushi yanajin haushin kanshi, wayar faseelat ta fado mai arai yayi sauri yafito ya dauketa duk ta tarwatse baxata kara amfanuwa ba, ya budeta ya cire sim dinta wanda take chart ya dauko one of his phone yasa sim din, ya sake download wats app yayi restoring duk messages suka dawo ciki, yakoma cikin chart din ta da baffa beko bude pic dinba yawuce gaba don kar zuciyarshi ta tarwatse , faseelat da taga pic din tace "baffa kayi hakuri plss bansan yaakai nai missing contact dinka ba, ya gida yasu hjya da alhaji? ashe haryanzu kanada wannan pic din yayi kyau sosai "

Baffa yace "lpy lau suke ,badole kiyi missing no dina ba tunda kinyi aure 😬 thank God ansamin rana jiya nima zan angwance "

faseelat ta tura laugh emoji 😁tace "wai dagaske ?yaakai bansaniba "

Yayi dariya yace "young girl ,ai ummi dazakiji gunta batanan nasan kuma wannan miskilin baze kiraki yafada miki ba "


faseelat ta turamashi smiling face tace "namaka murna wacece ita takaini kyau ? 🀣"

yace "kedin me kyakkyawa ce ajin karshe"


faseelat tace "muganta in dagaske ne "


yayi dariya yace"banda sheri fa "

tace "Allah aa kawai inason ganinta "


seya turomata pic din wata black beauty jibgegiya kamataπŸ˜‚ me dogon hanci da wawakeken baki tana da ido she's cute de πŸ˜‚πŸ™ˆ,

Faseelat ta tura mishi "haba baffa wannan doshumar ina zaka ajiyeta πŸ˜‚"

baffa yace "kambuuuu matar tawa ce doshuma?"

faseelat tatura mai "sorry sorry 🀭"

yace "ke ni banason fararen mata ni fari ita fara abun will waste, nafison baka me kiba shiyasa seda na darje amma ai tanada kyau duba sosai inkuma Sheri ne sekitayi "

Faseelat takara kallon pic din itade awurinta batada kyau abun mamaki ma yabata yadda yake kyakkyawa amma wagga yakeso lalle so makaho ne,

Tace " Allah yasa alheri, gaskiya tana da kyau ka gaidata kafin musan juna"

Yace "wannan is not a villager wayayyace degree gareta akan microbiology awani hospital ma take aiki kibari gobe innaje wurinta zan kiraki vedio call amma ta wats app seku gaisa daita ki kara ganinta sosai Allah tahadu kuma tanada hankali"

faseelat tace "ihmmmmm Allah yakaimu naganta "


Daganan se chart da yaturo mata yau wanda bata ganiba,


"aljanah ya kk tashi? gani wurin waseela "

"zan kiraki yanzu"

Se kiran,

fahad yasa hannu yaita bugun kanshi yana hawayen danasani "why ban tsaya ida karanta messages dinba? "

"meyasa zata dauki pic dashi? don yana cousin dinta ai zeiya aurenta donme zata sakarmishi jikina "

Yanajin wani malolon bakin ciki a makoshi yace "ya Allah ka ragemin kishinnan na zauna lpy kasamin hakuri akan dangin ta, don ban kaunar naga tana muamala da kowane namiji"niko nace insun barmaka ita ko?

yatashi zuciyarshi na ciwo yasaka kaya ya tada salla har anyi laasar yayisu ahade, be taba adduar Allah yarage masa kishi ba segashi yau shine ke kuka yana rokon Allah yarage masa kishinsa,

yana gamawa ya tashi yafita direct gidan su faseelat ya nufa amma gidan akulle don duk suna asibity,

yadade yana kallon kofar sannan yajuya ya nufi asibity,

A asibity amira ta farko a firgice, Aisha ta riketa tana rarrashi amira tana kuka take cewa "ina anty? Ni kikai ni wurin anty "suna haka fahad ya shigo ya karasa bakin gadon dasauri yana fadin "sannu princess "

amira naganinshi ta rumtse ido tai gum zuciyarta na harbawa don matsanancin tsoronshi takeji,

Aisha dake hawaye ta kalleshi,

Ya riko hannun amira yace "princess open ur eyes it's me ur dad "

gaf-gaf hannun amira ya dauki rawa, takara rumtse idonta yanzu in akwai abinda batasan gani befi daddinta ba,

Aisha ta zare hannunshi tana hawaye tace "katashi kafita bata son ganinka tsoron ka takeji karka karasa rikitamin ita"

Yayi kasake yana kallonta yace "u r lying "

Ya meda hannu ya riko amira yace "amira it's me ur beloved dad"

amira tafasa kara idanunta a kulle wadda tasa seda fahad yasaki hannunta, amira na kuka tace "I don't want to see you stay away from me"

ya fiddo ido waje "amira nine fa dad dinki bakison gani na inyi nesa dake? "

amira tace "mommy please take me to big mom house I'm scared here,"

Aisha tace "Dan Allah kafita kabarmu, badole taji tsoronka ba yadda kake dukan mu tana gani tanaji dan Allah kafita "

Fahad ya tashi yafita yanata tariyo maganganun umma da amira, wai his daughter da kullum take cewa she love him itace ke cewa yayi nesa daita ,ya shiga motar shi yayi zaune yakasa ma hawaye se zuciyarshi dake kuna,


yadade zaune sannan ya nufi gidan mommy dan yafada mata amira ba lpy,kokadan beda niyyar fadamata abunda yafaru amma yasan she must heard it,


har lokacin faseelat bata farfado ba daga baccin da take, dukkansu tun safe har yanzu bayan laasar ba wanda yakara sawa cikinshi komi,



itako jamila gidan siyama tawuce tana ta kuka tafadawa siyama abinda tayi tace dan Allah taje tabata hakuri,bataso su mama suji siyama shiru tayi kawai jin abinda hjy keyi da tsiyar da jamila tayi,

seda mijinta yayan mamar jamila yadawo cin abinci sannan siyama tafadamishi abinda jamila tayi tace anjima ze kaisu su bata hakuri,

Ranshi ya baci yakira jamila ya rufeta da fada "ke dan uwarki saboda yana kai dare be dawo ba shine zakije kiwa hjy wulakanci, ke wlh a aljanna kike in kikaji matsalolin uwayen mazan wasu sakarai shasha hakanan zaki rusa mana zumunci, kika ma kanki wlh in kuma so kike ki zama karamar jawara to tashi kiban wuri "jamila ta tashi tana kuka tafita,

Cikin kwantar da hankali siyama tace "kayi hakuri yarinya ce nangaba ko ance tayi bazata yi ba,Allah yasa hjyar ta hakura "

Tai shiru tana tunani don tasan hjyar ma bata kyauta ba kuma zatai mata magana koba yau ba ,


Motarsu khalil tayi nisa da tafiya sunkusa kai batsari tunda yashiga counter dinshi kawai yake latsawa yana lazimi dede gadar wani kauye kurmiyal wata mota ta kwacewa wani driver tazo tabanki motar su khalil karfen da yakare gadar ya balle duka motocin suka afka cikin gadar akife , suna fadawa suka kama da wuta gabadayansu,

Kafin mutane su taru mutanen ciki tuni sun kone koda mutane sukazo bakajin sautin komi se fasss! Dasss!! Tatasss!!! Jikin mutane na fashewa, mutane sunata zuba kasa da ruwa kafin motar kashe gobara tazo , daga katsina zuwa kurmiyal akwai yar tafiya don sunfi kusa da batsari,shiyasa abun yadauki mintoci

wutar bata mutu ba har yan kwana kwana sukazo aka kashe wutar ,

ranar yan kauyen kurmiyal sunga tashin hankali tsoron Allah yakara shigarsu wadanda suka manta da Allah ranar Sun tunadashi sun koma agunshi, ga warwakin sunyi baki kirin wasu Sun fashe wasu Sun kwarkwarje wasu hanji awaje, yara, jarirai, maza, mata, samari da yanmatasa,

kusan rai 15 don waccan motar j5 ce,

ba jimawa police suka zo aka daukesu zuwa matuary kafin asamu danginsu dukkansu sun mutu kurmusss,


dandanan gidajen radio suka fara baza labarin,

Hjya aminiyar radio tana zaune tana sauraren radion taji hadarin gabanta yayi mummunar faduwa, tai sauri takashe radion,

Ba arziki tana rawar duwawu ta shiga daki tana haki ta dauki waya takira mamar jamila,

Mamar jamila dabatasan abinda ke faruwa ba ta dauka da sallama hjy batako amsa ba tace "khalil yaiso nan? "

mamar jamila tace "a, a khalil bezo ba da yataho.... "bata ida magana ba wayar ta sullube daga hannun hjy,

Ta zame kasa zaune saboda kafafunta daketa rawa, ta dora hannu akai tafasa kara "nashiga ukku nabani na lalace wayyo Allah khalil dina ya mutu ya tafi yabarni"hawaye kamar famfo suke zubarmata ihun da take ta rafkawa yasa seda makwabtan ta suka shigo gidan suka rirriketa suna tambayar baasi,




Allah sarki rayuwa in Allah yaso cikin kiftawar ido se kaga duniyar ta zama empty , mutum ba abakin komi ba amma munsamu duniya mun shan take ko tunanin mutuwar ma bamayi kamar anan zamu dawwama,mun manta kiyama munata tsiya,ya Allah ka kyautata rayuwarmu kasa mucika da imani kasa muyi kyakkyawan karshe amin,






*ya ubangiji ina rokon ka kajikan dukkan musulmai maza da mata ka musu rahma kajikansu domin kai mai rahma ne me jinkai*😭😭😭
➰➰➰➰➰
*RAGGON MIJI*
➰➰➰➰➰








By






*MAMAN MAMY*
*(SHALELE)*




✍🏽✍🏽 *GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION*✍🏽✍🏽✍🏽

We are bearer's of so golden a penπŸ–Š
We write assidiously perceiven no pain
So magical
Our creative golden penπŸ–Š
Be hold our words
A product of our penπŸ–Š
Savour our words
For it will cause you no pain.✍🏽


https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/







7⃣2⃣





*SHAFIN mommyn mufeeda da me dambu inajin dadi yadda kukasance daga cikin mabiyan buk dina ina kuma jin dadin comments naku thanks*



*yaruwa kinayin azkhar din safiya da marece kuwa? Koko aiki da son kwanciya barci ko saurin kunna data suna hanaki yi? Da kinsan falalar yinsu dako kina gudun ceton rai zaki rikayin su,in kuma kinsan falalarsu why kike sanya? Ko mantawa dasu? Azkhar suna haska rayuwa, yana sauya mummunan abu zuwa alheri, kariya ce daga sharrin kowane abu, yana kawo arziki dajin dadin rayuwa,yana gyara zuciya,yana kusantar da mutum ga ubangiji, yana kai mutum zuwa aljanna,shin me zesa kiyi sanya da yinsu? gasunan da yawa masu saukin karantawa se dumbin lada da falala, Dan Allah murika yin azkhar karmuyi sanya dasu don neman kusanci da kariya awurin ubangiji, duk abinda mukeyi mu daure murika yin azkhar dinnan koda muna kitchen ne, ko a mota going to office ko a school ko ina sau da dama Allah ya janyemiki sharri sanadin azkhar wanda ke baki sani ba, kinemi littafin azkhar a book shop's ki kara samun wasu ki hardace kitayi insha Allah zakiji dadinsu kuma zaki samu natsuwa*


*yaruwa kinada riyadul janna fi azkharul kitabu was sunna kuwa?littafi ne da ya tattara azkhar da adduoi wanda baakawosu hakanan ba seda akafara rubuto hadissan da aka samosu da wadanda suka ruwaito, acikinshi akwai adduoi da yawa wadanda wlh zakiji dadinsu an tattara duk adduoin dake cikin alkurani a littafin da kuma sunayen Allah kyawawa wadanda idan an rokeshi dasu yana amsawa wanda sukazo a alkurani me girma wanda suka jerosu tun daga fatiha to nas, ga kuma manyan adduoi a bayansu wanda Allah yake amsa addua in akayi su , na rungumi riyadul janna naji dadinshi matuka,idan bakidashi ina me baki/ka shawara ki nemi riyadul janna zaki samu biyan bukata kuma zakisamu kusanci da Allah (S.W).zaki sameshi a kasuwanni wurin masu littattafai ko bookshops wallafar yusuf bin Ismael ,bangonshi da hoton lambu da flowers,nasan beda tsada ada bansaniba yanzu kiyi kokari ki mallakeshi don bukatarki, bakin cikinki,ko damuwarki zasu yaye,zaki godemin kede kinemi naki ki runguma*



Cikin gigicewa Hajiya take ce musu"nabani khalil dina ya mutu yayi accident ya mutu"

Matan suka dauki salati jikinsu yayi sanyi domin khalil mutum ne har mutum yana girmama mutane bazaka ce ga abokin fadanshi ba yana da hakuri uwa uba yawan ibada,

Hjy tace "hjya rabi Dan Allah kuce be mutu ba, be mutu bako? Nasan baze mutu yabar niba bandashi cikin motar wlh babu shi"

matar daakace ma hiya rabi ta kalli abokiyar zamanta tace "hjya zaliha ki kira alhaji kifada mishi yafada ma manu naji labarin accident din yanzu inajin radio se suje su dubo indashi se suanso gawar ai mishi sutura "

Zaliha ta juya dasauri ta shiga gida ta dauki waya ta kira mijinsu tafada mai yayi ta sallallami yace "yanzunnan naji labarin accident din bari nakira manun donni ina jibia amma yanzunnan zan kamo hanya "

ya kashe kiran ya kira manu, kawu manu ya girgiza ba bata lokaci ya tafi gidan kaninshi suka nufi matuary dauko gawa,


zaliha ba bata lokaci ta dannawa siyama kira ,siyama na kitchen wayar ta keta kara yaranta duk sun tafi islamiya jamila ta dauko wayar ta kawomata ta juya ,

siyama ta dauka takara kunne da sallama a bakinta,

Zaliha tace "siyama nice hjya zaliha ki taho gida khalil yayi accident ya rasu hjyar ku kuma bata lpy"diff takashe takoma gidan hjya dasauri,

Siyama zuciyarta ta rika harbawa dasauri hawaye suka rika zuba a fuskarta masu zafin gaske,

Tai cikin daki tana kuka, jamila dake zaune tayi tagumi taga siyamar tashigo tana kuka ta tashi tabita ciki siyama har tazira hijab jamila tana ta kallonta tace "anty lpy kike kuka? "

siyama tafashe da kuka tace "yaya khalil ne yayi accident ya rasu "

kamar saukar guduma jamila taji maganar ta yanke jiki tafadi,

Siyama tai kanta tana kuka tana kiran sunanta "jamila! Jamila kitashi Dan Allah "

Mijinta babban mutum ne idan ya dawo aiki a kofar gidanshi yake zama wurin har yazama majalisa cika yake da maza,

siyama ta tashi tafita waje dagudu bata tsaya koina ba se gaban mazan dake gun ta kalli mijinta tana kuka cikin tashin hankali tace "baban farida jamila ta fadi "

yace "subhanallahi ! "ya tashi yayi cikin gidan dasauri, siyama tabi bayanshi,

Yana shiga ya samu jamila a sume da sauri ya bude fridge ya dauko ruwa masu sanyi ya sheka mata su a fuska,

jamila tasaki ajiyar zuciya ta bude ido wuf tatashi zaune tafara hawaye" anty yaya na ya rasu? Ya khalil dina fa"?

siyama daketa kuka tace "ya rasu jamila "


Marar jamila da tunda tafarko take murdawa kadan, ta murda da karfi ,jamila ta dafe ciki da kugu tafara kuka tana nishi zufa tarika karyomata ta koina,

Baban farida yace "siyama me kike fada ne?"

siyama tace "yanzunnan aka kirani akace yayi accident ya rasu "

Baban farida yace "innalillahi wainna ilaihi rajiun!!!! ...

karar da jamila tayi ne ya katseshi,

"wayyo Allah marata zata balle wayyo kuguna "

dashi da siyama suka rirriketa baban farida yace ma siyama "dauko min keys dina mutafi asibity"

Siyama ta saketa tana kuka tatafi dauko keys, shima idonshi jawur ya dauko jamila suka fito siyama ta bude mai yasa jamila baya tashiga yajasu suka nufi asibity, tsakanin jamila da siyama bazaka gane wake nakudar ba don dukkansu kuka suke riris,


baban farida har kyarma yake wajen tuki dakyar suka isa Medical Center aka amshi jamila akashiga daita,

siyama ta cigaba da kuka zuciyarta kamar zata fito duka yaushe sukai rashin alhaji yanzu kuma khalil,

baban farida ya rungumota jikinshi yana rarrashi,

ba jimawa wata nurse tafito wurinsu tana sauri tace "patient da kuka kawo labour take ayi sauri akawo kayan haihuwa "tajuya takoma dakin,

baban farida ya zaunar da siyama akan seat ya fita anan bakin asibitin yasiyi kayan haihuwar ya koma ciki dasauri,

Ba jimawa nurse tafito ta amshi kayan hankali tashe yace "ta haihu ne?"

nurse din tace "a, a dasauran lokaci kumata addua "takoma ciki dasauri,

wayar baban farida tadau kara yana dubawa yaga mamar jamila ce, kamar kar yadauka ya dauka ya kanga akunne ,

acan bangaren tace "yaya kuna lpy kuwa dazun maman siyama ta kirani tana tambayar khalil ko yazonan bamu gama waya ba takashe wayar yanzu naji labarin accident da akayi ahanya shine hankalina ya tashi nace bari nakira "

Murya dishe yace "harda Khalil acikin accident din, yanzuma muna asibity jamila labour take "


maman jamila dake zaune ta mike tsaye tana salati tace "Allah yajikanshi, Allah yabata lpy nan bada jimawa ba zamu taho "takashe kiran tafara neman layin mijinta yana dauka tafada mishi ba jimawa yazo gida suka kama hanyar kt,

Shiru shiru jamila bata haihu ba, hankalinshi duk da baa kwance yake ba yayi ta maza yacewa siyama tajira zeje yadawo,

yanufi gidan hjy,

Hjya tabi ta rude tayi sambatu har muryarta ta shake dole tai shiru tana ta kuka batsayawa, matan dake wurinta sunata bata hakuri, hjy rabi tafara mata nata waazi "haba hjy kinaso kinuna Allah be kyauta ba komi? kituna fa Allah ne yabaki shi kuma ya amshi kayansa meyasa bazaki hakuri ba? Kiyi hakuri kita innalillahi wainna ilaihi rajiun ki kuma cigaba da mishi addua ita yake bukata a yanzu ,insha Allah yanzu khalil ba abinda yakeso fiyeda akaishi makwancinsa inamishi kyakkyawan zato kiyi hakuri Allah seyabaki ladar hakurinki, ko kuma kita kuka da surutan har Allah yayi fushi dake, hjy bayau akafara miki mutuwa ba ina iyayenki ina mijinki? duk kin hakura donmi yanzu bazaki hakuri ba? kuka dole ne amma ba irin yadda kike ba kiyi hakuri Allah yamishi rahma "

hjya ta cigaba da kukanta danbata jin wani waazi yanzu,



kawu manu sunje matuary mutane da yawa wadanda abun ya rutsa da yanuwansu ,har akazo kan su kawu manu aka tambayi sunan khalil suka fadi acikin list na fasinja harda khalil a motar su shidda ne ,

dandanan aka shiga dasu ciki akafara zaro maza daga lokokinsu ba kyangani abun, basuga khalil ba, abun yabasu mamaki ga sunanshi amma babushi dan sandan da kenan yace "to gaskiya kila babushi a motar don motocin duk sunyi ragaraga kaida ka gansu kasan ba ran daze fita daga ciki kuma ba gawar da tazama toka donba kasusuwa kuma wurin ba wasu gawarwaki awaje munyi screening sosai kuje kukara bincikawa ko kafin accident sun saukeshi wani gari "

su kawu manu suka fita suka nufi gidan hjya,

hjya na zaune tayi lakwas ko mutuwar alhaji bata girgizata haka ba, suka shigo suka zauna,

ta dago tace "manu ina gawar khalil? Ko gawar tashi ma bazan samu gani ba? "

manu yace "se hakuri hjy, Allah kadai yasan komi munje acikin gawarwakin ba khalil kuma dasunanshi acikin list na passengers ,kila babu shi

Please Login or Register in order to submit comment