Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

su abulkhair suna ta tambayarta sede ummi tace bacci take ,

Har abba ya dawo gida bayan ishai ummi da abba suna daki suna fira while ishak abul da Mubarak na tasu firar, dan auta ya kasa hakura da rashin ganin ta ya leka dakinta tayi rubda ciki amma ba bacci take ba, abin duniya ne kawai ya sha mata kai, ganin idonta rufe yasa yaja mata kofar,

Dakin abba ya shiga ya samu ummi ya zauna gefenta "ummi kode ya faseelat bata lpy? Naga tundazu da rana bata fito ba yanzu naje dakinta na ganta kwance har yanzu "

Ummi tace "to bana ce maka bacci take ba? Ka tashi kaba mutane wuri "

Yace "to ummi kode a tado ta ni wlh gidan ba dadi da babu ita "

Ummi tace "kai kasani ai "


Abba yace "wai tun dazu bata fito ba? Kuma kika kyaleta haba Hjy kinsan fa ulcer na iya kamata "

"to ya kake so na mata? Ko so Kake naje na rarraso ta tunda na mata laifi "

Abba yace "yaro dan rarrashi ne in kika lallabata se ki shawo kanta amma bata haka ba, kinsan faseelat na da saukin kai ai "

"Alhaji kabarta kawai in yunwa ta kusa kasheta zata fito, nifa duk abinda nakeyi saboda ita ne yarinyar nanfa da kake gani kusan kullum se tayi mafarki, taya kake tunanin hankalina ze kwanta tana zaune gidannan gwara ai mata auren tun kan ai abun kunya "

Abba yayi shiru yana nazari,yace"eh ki de bita a sannu, wa ma ta gado inbake ba da jarabar tsiya in baayi miki 3 rounds ba baki koshi "ya ida yana dariya

Tace "eh naji din ai kai ma shine da har kake iya yin ukkun "

Suka sa dariya Mubarak fa yadade da barin wurin tunda aka korashi.

Ummi nata zuba ido faseelat zata fito cin abinci amma bata fito ba, se kuma tafara shiga damuwa.

Itako faseelat muguwar yunwa takeji ga, zazzabi da ya rufeta kwance kawai take tanata tunanin yadda zatayi rayuwa da khalil.

Can 12am samarin duk sunyi bacci ummi tafito daga dakin abba har zata wuce se kuma ta shiga dakin faseelat,

Tana kwance rubda ciki still ummi ta matsa "ke bana hanaki kwanciya haka ba?"

faseelat ta birkita ba tare da ta dago ba

Ummi tace "wai dani faseelat zaki fushi ?dan kawai ina fadamiki gaskiya? Ya kikeso nayi ne? So kike nabarki na zuba miki ido? Bayan ga hanya Allah ya kawo, haba faseelat wlh kinbani mamaki da har zaki bijirewa magana ta shi dake namiji ya amince da umarnin mahaifiyarsa, amma ke kinkasa ".

faseelat ta fashe da kuka tana sheshsheka ummi tace "aa kidena kuka faseelat bazan takura miki ba tunda bazaki iya aurenshiba shikenan gobennan zankira uwarshi in fadamata bakisonshi tunda burinki ki kunyatar dani, ni wlh daace kinada wanda kikeso da baabinda zesa na matsa miki amma keda bakida kowa ihhhhm? Dama ace ke lafiyayya ce amma kinada larura ki duba fa yanayinki faseelat, shikenan anfasa auren ki tashi kije kici abinci "

Ummi ta juya zata fita faseelat na kuka ta kira sunanta "ummi "!

Ummi ta waiwayo ta cigaba da cewa "Dan Allah ki hakuri baniso ranki ya baci karki fushi dani "

"bazanyi fushi da keba faseelat sede ki sani zaki sani cikin zullumi da tunani dan wlh inde ban aurar dake ba banida kwanciyar hankali "

Faseelat daga kwancen de take magana cikin rashin tunani tace "na yadda ummi zan aure shi inde zakiji dadi "

Ummi tace "dako kinfaranta min rai dan inada tabbacin bazaki kuka ba in Allah yaso"

faseelat tace "na amince ummi kuma kiyi hakuri da bata miki rai da nayi "

ummi tace "bakomi Allah ya miki albarka ki tashi kici abinci karkijawa kanki ciwo"


Faseelat tace "bazan iyaba ummi masassara nake tun dazu "

ummi tace "subhanallahi "tana hawa kan gadon ta fara tattabata gabadaya jikinta rau yake har kafafunta, ummi tace "sannu kinji bari na kawo miki magani "
Ta tashi ta fita wani kuka ne yazowa faseelat ita kanta tasan ta amsa ne kawai amma tasan haka zatai ta rayuwar hakuri harabada, tasa hannu ta share hawayenta yanzu de koba komi ta farantawa mahaifiyarta rai da tun tasowarta tana ganin yadda take fifita ta akan yanuwanta.

Motsin da taji yasa ta kara goge fuskarta ummi tashigo dauke da tray ta ajiye ta bude flask ta debo taliyar hausar da ta dafa da daddare ta dora kan bed ta debi ruwa ta ajiye sannan ta zauna bakin gadon tace "tashi ga abincin diyata "

Faseelat na ciza baki ta yunkura ummi taida tadata zaunen jikinta har kyarma yake saboda yunwa,

Ummi tafara bata abincin a baki da yake tana jin yunwa taci abincin sosai sannan ta bata magani ta koma ta kwanta se sannu ummi ke mata sede ta daga kai, tashi ummi tayi taja mata kofa tana mata seda safe.


ko bayan fitar ummi faseelat kuka ta rikayi ga bacci ya kaura cewa idanunta,
Ba abinda take tunani se fuskarshi da jikinshi tana tunanin yadda zasuyi rayuwa tare wuri daya gida daya daki daya gado daya.


Se asuba bacci ya dauketa, ummi na Gama azkhar taje ta gaida abba yake tambayarta jikin faseelat da yake wurinshi ta amso maganin tace dasauki ta fita dubota, tana shiga ta tada ta faseelat bude ido kawai tayi ummi tace "ya jikin "tana tabata faseelat tace "dasauki "

Ummi tace "naji haryanzu da fever din kitashi ki salla inje in hado miki tea kisha kisha magani "

Faseelat tace "I'm off"

Ummi tace "kinada pads ne? "

Faseelat tace "eh amma beda yawa "

"OK anjima zanba Mubarak yasiyo miki wata tashi kije ki kimtsa ko kinji dadin jikin "

faseelat tace "to "ta mike ummi taga har tangadi take ummi tace "zakiiya wankan kuwa "

Faseelat tace "eh "tafara bin bango ummi takamata ta kaita toilet sannan tai kitchen,

Da dai daya yanuwanta suka rika shigowa suna mata ya jiki kafin su bar gidan, shi ko Mubarak harda hawaye danba karamar shakuwa sukai ba daita.

Bayan tasha tea din da magani ta koma ta kwanta,

Can wajen 12pm ummi nata aikace aikacenta wani yaro yazo yace ana kiran faseelat .

Ummi ta danyi jimmm sannan tace "gatanan zuwa "

Yaro yaje ya kai sako

itako ummi tashiga dakin faseelat har lokacin tana bacci ummi tafara tapping dinta tana kiran sunanta faseelat ta bude ido, tana kallon ummin.

Ummi tace "ki daure kitashi ki dan kimtsa ga khalil can yazo "

Faseelat gabanta ya bada dudum, tasan datace bata iyawa ran ummi ze baci dan dole ta mike tsaye ummi tace "zade kiiya ko? "

Faseelat tace "eh ta jawo hijab har kasa ta saka ai gwara tajema ta kara ganinshi maybe jiya batai masa kallon tsaf ba.

Tana saka hijab din tafita ummi ta girgixa kai tana kallon yadda take tafiya a kasalance.

Faseelat na fita taganshi a.....




Next page loading........
[7/12, 10:58 PM] Maman Mamy: ➰➰➰➰➰
*RAGGON MIJI*
➰➰➰➰➰





By



*MAMAN MAMY*



https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
*~GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION💫💫💫~*


*~❄We beare's of soon golden We writer's assiduously percieven No pain so Magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Our worlds for it cause u np pain~*



6⃣




*Dedicated to SIS ZULAIHAT RANO*




a zaune kan roba-robar shi kallo daya tai mashi ta dauke idanunta, jikin bango ta jingina kanta na kallon sama ta cije baki saboda Marar ta data murda ,

Shi ko yana ganin fitowar ta ya mike tsaye yana gyara riga ganin ta jingina a bango tana ya mutsa fuska yasa shi jin badadi,

Bakomi yasa faseelat dauke kai ba se dan ganin kara jiya da yau, shadda ce jikinshi fara kall ya kawo farar hula akanta ga takalmi fari, wayaga balbela🤣
Shi gashi baki abin se ya dagule, itada tafito ganin canji se taga gara jiya, shaddar se sheki take tsabar fari.


Shi ko be samu ganin fuskar taba saboda kanta na facing up ganin Sun kusa minti ukku yasashi cewa "barka da fitowa"

Batare da ta sauke kanta ba ta dan juya shi ta zuba mai jajayen idanunta wanda suka kumbura saboda rashin barci da kukan da tasha ,

Yace "subhanallah, faseelat lpya kike? "

Ta juya sannan tace "ban lpya "

Cikin jimami yace"miyasameki?"

Tace "fever"tana tabe baki.

Yace "ayyyah "da karfi wadda tasa seda ta mike daga jikin bango saboda yadda gabanta ya fadi, Ya cigaba da cewa "Allah shi sawwake shi baki lpya "

Faseelat kamar ta dora hannu aka tasa ihu haka takeji, ashe ba karamar illa takeso taiwa Kanta ba ko magana be iya ba, shi ga bahaushe wani abinda ta dan lura dashi shine kamar maganarshi daga hanci take fitowa.

yakatse mata tunani da cewa "ga wannan"

Ta kai kallonta ga ledojin da yake miko mata, daya babba daya karama, dan dole ta mika hannu ta amsa can ciki ciki tace "Nagode"yayi kamar be jiba sema yace "dama zuwa nai mugaisa gashi bakya jin dadi yanzu ni zantafi se munyi waya ga waya nan da sim da komi "

Batare da wata murna ba ta kalli ledar hannunta ta yamutsa fuska.

Yace "se anjima agaida ummi "

ta juya kawai ta shige gida tana saka da warwara , yadda zata kuma ganinshi in ya dawo dan kullum kara gano muninshi takeyi.

tana shiga gida ummi tayi shimfida kan barandar gidansu kafafunta a mike tana huce gajiyar hidimar da tasha, ta je ta kwanta kan kafafunta,

Ummi tace "sannu faseelat kode mutafi asibity? "

Ta girgiza Kai ummi ta kai dubanta ga ledojin da suke zube ta jawosu tana fadin "shi ya baki wannan?"

Faseelat ta daga kai idonta na kawo ruwa batare da ummi ta dubeta ba ta Fara bude ledojin, daya cosmetics ne kawai ciki, danginsu perfume, Nivea lotion, roll on, powder irin big pack dinnan wadda Zaka samu su concealer da foundation, da janbaki duk a ciki, se lip gloss.

dayar kuma waya ce ciki me suna infinix hot 6, ummi tace "aaa!masha Allah Allah yasa alheri, faseelat kinga kaya ko? "

faseelat da duk abinda zaa daga wani kululu ke tokare mata makoshi tace "ihhhhm "

Ummi tace "to ga waya faseelat tunda wayarki tasamu matsala har yau alhaji babba be aiko da wata ba toga khalil ya hutar dashi "

faseelat ta mike tsaye zata wuce dakinta dantagaji da jin maganganun ummi, kawai wayar tafara ringing, ummi tace "zo zo gashi har ya kira ashe a bude take "

Faseelat takoma ta amsa kamar zatai kuka tashige daki tana shiga ta danna ta a key dif ringing ya tsaya ummi duk a tunaninta faseelat ta dauki wayar ne, kiran na yankewa shiru be sake kira ba faseelat ta tabe baki,

Ta haye gado tana tunanin rayuwar da zatayi nangaba,

Hannunta ta dora kan kirjinta taji yadda yake fat..fat ta fara hawaye.


khalil yana be koma gida ba se 2pm dan daganan school ya wuce,

Yana shigarda mashin dinsa yayi hanyar dakinsa Hjy saratu da ke alwala zatai salla tabar alwalar tana bin bayanshi da kallo har ya kusa shigewa Hjy tace "kai zonan khalil"

ya juyo yaisa wurinta dan slope din dakinta da take kai anan ya zauna tana kallonshi tace "lpya kake naga ka dawo haka kamar marar lpya? "

ya cire hular kanshi yana fifita yace "Hjy naje gidansu faseelat na sameta bata da lpya sosai "

Hjyar tace "ummm se akai yaya? "

yace "shine nakeji nima bani lpyan "

Hjy saratu tai kasake tana kallonshi shi kuma dagaske yake maganarshi ,Hjy tace "to Allah ya sawwake ,saboda bata lpya shine kake wannan yaushin? kamar ba namiji ba, tashi da Allah kaban wuri "

Memakon ya tashi se yace "Hjy yaushe zakije ganinta? "

ta banka mai harara "se ran da na shirya "

"to me ze hana kije yau? "

Cikin haushi tace "saboda ban ga dama ba "

Ze kara magana tace "aa da Allah kyaleni fita xanyi yanzu idan na dawo zan biya ingano tan "

yace "tom "ya mike zakadai -zakadai ya shige dakinshi, wata kan jiya daga jiya zuwa yau faseelat ta zama wani bangare na cikin jikinshi, ku jifa 😂kunsan irin su dasaurin shiga hannu ,

wayar shi ya fiddo a aljihu ya kara kiranta bata dauka ba faseelat lokacin ma batasan inda kanta yake ba dan gabadaya masassara ta rufeta tana cikin bargo tana kyarma lokacinma ummi na wurinta zaune tana jiran abba yazo su tafi asibity.

Koda kiran ya tsinke ajiye wayar yayi shi a kaidar shi baya missed call biyu, (audu ka'ida kenan)

Hmmm shifa ba ordinary mutum bane shi rayuwar shi daban take da yadda aka saba gani kude biyoni muji tasu salon soyayyar.

Au 😂nayi mistake, kaso a soka ai shine so, kaso a ki ka fa?shi kuma me zaakirashi?
[7/12, 10:58 PM] Maman Mamy: Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/LBBVKSXqmrj3oaalNYWqmS


➰➰➰➰➰
*RAGGON MIJI*
➰➰➰➰➰



By



*MAMAN MAMY*




https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
*~GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION💫💫💫~*


*~❄We beare's of soon golden We writer's assiduously percieven No pain so Magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Our worlds for it cause u np pain~*





7⃣





Dedicated to *SIS ZULAIHAT RANO*




Abba na zuwa ummi ta kama faseelat da temakon kaninta abul saboda ko tafiya bata iyayi ga zazzabi ga ciwon mara ga tension abun da yawa, har cikin mota akasakata, babansu yana da mota amma ta kwana biyu sede batayi tsufa can can ba ,yayan abba wanda sunansa salisu suna kiranshi baba babba ummi kuma na kiranshi alhaji babba mutum ne me kirki da arziki duk da de bawani arziki ne me yawa ba amma ba laifi tunda yana da zuciyar temakon yanuwan sa shi yakai su ummi hajji ya siya wa abba mota shine ya dauki nauyin karatun ya umar, kuma a gidansa yake zaune a Niger Republic din da yake shi alhaji salisun shima dan kasuwa ne yana yawan zuwa can shine yayi aure kuma yabar matar a can kasar.



Shi kuma abba tuni ya dena zuwa Niger din iyakar shi nan gida Nigeria duk da ummi can duk ilahirin dangin ta suke amma alhaji be bari ya zauna a wani gida ba se a gidanshi wannan kenan.


Asibiti suka kaita da zuwan su aka sa mata ledar ruwa, bayan allurai da aka mata,

Se bayan laasar ta farka likita ya shigo yana tambayarta mike damunta yanzu,

Jiki ba kwari tace "ciwon mara da nan "
Ta fada tana nuna setin zuciyarta likitan ya dan kura mata ido ta glass sannan yayi yan rubuce rubuce,

Ya juya wurin ummi da ke tsaye tanajin duk abinda ke faruwa yace "Hjy ire iren ciwon marannan inba aure akayiwa yaranba zeyi wuya ya barsu, sannan batun ciwon heart din rashin cin abinci ne da isashshen bacci wannan kesa ulcer ke kama mutum wuf daya, se akiyaye duk abinda na fada banda abu me tsami ko yaji ko mai da yawa arika bata abinci akai akai "ya juya bayan ya gama jawabin yana kara kallon faseelat,

ummi tace "insha Allah zaa kiyaye, kuma ankusa yin bikin ta ma "

Likitan ya Mike tsaye yana gyara ta kaddun hannunshi, shi da har ya fara tunanin ya samu ta ukku, matanshi biyu, ya killace a gida dukansu farare ne tass dan yanada gurin ajiye fararen mata kuma dukansu a asibity suka hadu daya ma kauye take daga amai da gudawa ya aure ta.
Fita daga dakin yayi yana fadin ,"Allah ya sawwake, "

ko da abba ya dawo hospital din samu yayi an sallame su dan lokacin kusan 6:40 ya biya Bill suka wuce gida.


Bakin wani pharmacy suka tsaya abba ya Shiga ya siyo magungunan da aka rubuta musu sannan suka wuce .

suna isa ummi takama faseelat suka fito har zuwa dakin ta ta kwantar daita malt da milk ta hado mata tasha tasha magunguna ta kwanta baadade ba bacci ya dauketa.

Can ana kiran sallan ishai se ga Hjy saratu kamar daga sama tana sallama ummi da fitowar ta wanka kenan ta amsa tana mata marhaba Hjy saratu ta shiga ummi tai mata iso har daki,

bayan sun gaisa take tambayar ummi ya me jiki?

ummi tace "dasauki dazunnan ma aka sallamomu daga asibity dan seda suka saka mata ruwa"

Hjy saratu tace "Abu beyi dadi ba Allah ya sawwake ya bata lpy ai tundazun naso zuwa se kuma na makara wajen fitar diyar kanwata ta haihu shine muka tafi suna tundazu inata so na taho se yanzu Allah yayi ina rokon Allah yabata lpy "

Ummi tace "amin"


Hiya saratu tace "tunda Khalil ya koma naga ne ba lpya ba dan kamar kwai ya fashe masa a ciki haka yayi "

Ummi tai dariya "khalil kenan ai dazun da yazo ya cika faseelat da abun arziki harda su waya a cikin kayan, Allah de ya kara budi na alheri "

Hjy saratu tace "amin amin,bari naje na dubata na wuce gida"

Suka mike suka fita zuwa dakin da faseelat ke kwance,
Har lokacin tana bacci ummi tace "bata tashiba kila cikin drugs da aka bata akwai na saka bacci ciki "

Hjy tace "to ni zanwuce Allah ya kara bada lpy "

Ummi tace "amin "

Ta na mata tattaki zuwa bakin kofa seda suka kai can ummi ta dawo ta shige daki ta'ida shiryawa, sannan tafito.


Ana gama isha'i duk suka hallara ummi takawo masu babbar cooler datake zuba musu abinci se plates da spoons suko sunbaje akan tabarma, kowa ya dibi nashi suka fara ci, Mubarak yace "ummi ni de nakoshi tunda yaya bata lpya"

Ummi tace "haba dan auta na, ka daure kaci ga faseelat can tana cin Nata itama "

Yace "dagasske ummi? "

Tace "eh kai sauri ka gama cika cikin ka se kaje wurinta yace to "yafara buga loma.


Su ummi basu dade da barin dakin ba tafarka ba laifi massaran ta sauka tun asibity ciwon ma ya lafa, sede ciwon da zuciyarta ke mata, baa jima ba taji wayarta na vibrate taja dogon tsoki kamar ba marar lpya ba afili tace "dan wahala"

Hjy saratu na'isa gida take bawa khalil labari tace "ashe haka faseelat ke jin jiki ?umminsu tace dazun har seda aka kwantar dasu asibity"

Yace "Hjy suna asibitin yanzu? "

Tace "a, a an sallamo su agida na samesu "

Ya tashi tsaye daga shi se jallabiya ga zungureriyar casbahar shi yana ja yace "bari na dawo hjy "

Hjy na kallonshi tace "kai dawo nan ina zaka? "

yace "yanzu zan dawo fa hjy gidansu zanje "

Tace "Kai baka da hankali da zaka je gidansu yanzu? "

Kawai ya juya "sena dawo "ya fice
Niko nace hjy barshi kinsan dogo dama be cika hankali ba 🤣🙊


Ya fidda babur dinshi yaja akan hanya ya tsaya wata supermarket ya siyi chivita da hollandia da malt da short cake da big biscuits gefen shagon ya siyi fruit irinsu orange, banana da pineapple

daya wuce gidansu, lokacin kusan karfe 10pm dan har Sun kulle gida ya yi parking machine dinsa ya fara kwankwasa gidan,

Be dade da fara kwankwasawa ba ishak ya fito bema sanshi ba hakanan yace masa "inayini "

Khalil yace "lpya lau, ya me jiki? "

ishak yace "dasauki "

Khalil yace "Allah shi kara afuwa, ga wannan ka kai mata "

Ya mika masa ledar ishak ya amsa yace "injiwa? Za a ce?"

Yace "khalil "

ishak ya juya yasaka sakata ya shiga cikin gidan abba da yake zaune shi ma yace "waye ne ?"

Ishak yace "yace khalil ne kuma yabada wannan yace abata "

Abba yace "kai ma ummi tana can wurinta

Ya juya zuwa dakin ummi kadai ya tadda tana gyara wa faseelat gado ita kuma tana toilet yace "ummi gashi inji khalil yace yana gaida me jiki "

Ummi tace "oh cikin darennan ya taso to kawo "

Ta amsa ta ajiye shi kuma ya fita baa jima ba faseelat tashigo dakin,

Wajen wardrobe dinta tawuce ta kimtsa kanta sannan ta dawo ta zauna kan bed.

Ummi tace "ga kayan marmari ankawo me zakisha? "

Faseelat tace "nakoshi ummi ruwan zafi kawai nakeso insha "

Ummi tace "to bari in je inhada miki amma ki tashi ga ayaba nan kici ko kadanne kinsan tana rage menstrual cramps "

Tace "to "

Ta amsa ta bare tana ci tana yamutsa fuska.
[7/12, 10:58 PM] Maman Mamy: ➰➰➰➰➰
*RAGGON MIJI*
➰➰➰➰➰






By *MAMAN MAMY*





https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
*~GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION💫💫💫~*


*~❄We beare's of soon golden We writer's assiduously percieven No pain so Magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Our worlds for it cause u np pain~*




8⃣




Dedicated to *ZULAIHAT RANO*




Lokacin da ummi ta dawo har faseelat taci biyu, mika mata tea din ummi tayi tana fadin "bansa sugar ba amma nasa miki citta da yawa saboda tana koro jini da wuri "

Faseelat ta amsa "Nagode ummi "

Ummi ta zauna tana kallon faseelat tace "dazun Hjyarsu khalil tazo kina bacci tana gaidaki da jiki "

Faseelat tai shiru bata ce komi ba,

Ummi tace "baki tambayi wanda ya kawo miki fruit dinnan ba "

Faseelat ta kurbi tea tace "nayi zaton abba yakawo "

Ummi tace "a, a khalil ne ya kawosu yanzu da darannan "

Kuts-kuts ta zubdo tea din bakinta wani kuma ya sarketa tafara tari,
Ummi tace "kibi a sannu mana inya miki zafi kibarshi ya huce tukun "

Faseelat ta goge gefen bakinta taajiye copyn tea din tai shiru tana mamakin wane irin mutum ne khalil itade ba sakarmishi fuska take ba sannan bawani sabawa sukai ba ballatana ya dinga yi mata wadannan abubuwan,

Ummi ta katse mata tunani da cewa "kind ace da miji faseelat alamu duk sun nuna haka yaro me kunya da tarbiyya, duk dade bansan halinsa ba amma ina mai kyakykyawan zato, Dan Allah faseelat ki saki jikinki sosai naga tunda yazo kike ciwo bansaniba ko hakanan kika amsamin amma baki son auren shi "

Faseelat tace "ummi gaskiya na amince ne saboda kawai kiji dadi ba dan inason shi ba "

Ummi tace "ai nangaba zakiso shi "

Faseelat tace "hmmmmm "

ummi tai dariya "kiyi magana mana nasan nangaba ko ance auren hadi akai muku mutane bazasu yarda ba danni nasan nabaki many lessons daga tasowarki zuwa yanzu Wanda ko bankara da komi ba sunisheki zaman gidan miji, kuma kina da komai da zakija hankalin namiji dashi inde har kinmeda hankali mallake namiji baze miki wuya ba ,zaki so shi ki haifa masa yara Kema kizama uwa me koyarwa kamarni"ummi ta'ida maganar da murmushi fuskarta.

faseelat batace komi ba batasan komi ze faru nan gaba ba amma bata tunanin zataso khalil ko ta so shi bawani so sosai ba, saboda tadan fahimci wasu abubuwa dangane dashi.

Ummi ta katse shirun da cewa "ga kayanda ya kawo ki dauki abinda kikeso na kaiwa yanuwanki sauran "

Faseelat tace "ni nakoshi ki tafi dasu kawai "

Ummi tace "to ki sha tea din kar yayi sanyi kuma "ta dauki ledar tai waje

Faseelat ta yi tagumi ji yadda komi ya jagule mata lokaci daya saboda kawai ummi ta kamata tana wankan janaba inda bataganta ba bazata matsa mata haka akan aure ba, faseelat sede taji hawaye Sun zubomata anata abubuwa kamar gobe ne auren why?

ita tai kanta haka ne haka Allah ya halicceta mata nawa ne irinta? Maza nawa ne Irinta suma haka iyayensu ke matsa masu akan aure ko se ita dantana ya mace tilo gun mahaifiyarta? Ta share hawayenta tana daga kai cikin zuciyarta tace bazan kara zubda hawaye na akan batunnan ba zanyi kokarin hakan.

(yo anya zata iya?)


ummi nafita ta kaiwa abba kayan ya gani tace "me zaabaka? "

ya dauki hollandia yace "wannan yayi "

Ta tashi su ishak nata fira abul na gefe yana duba handout ummi ta zauna tsakiyarsu tace "Mubarak kawo wuka"

Ya tashi domin daukowa,

Abul ya kalli kayan "wai ummi waye ya kawo kayan nan "

Tace "kubakusan antinku aure zatayi ba? "

Ishak yace "wannan kai "

abul yace "yaakayi ne"

Ishak yace "lokacin da na bude gida naganshi tsaye ya bani tsoro dogo ne sosai nazata ma aljani ne "

Ummi ta rumtse masa baki da hannuwanta tace "ubanka so kake ka kara tunzura yayarku"ta juya tana kallon wajen dakinta

Abul ya kece da dariya ,"ummi kibarshi ya ida mana"

Ummi ta harareshi "kayi dede Allah yayi maka albarka "

daya daga cikin sirrin ummi ko wane laifi zaaimata sede tace Allah yayi albarka bata taba cewa komi fiye da wannan sede harara.
Mubarak ya dawo da wuka hannunshi yana mita wai wukar can karkashin kwandon wanke wanke ya ganta ummi tace "to me kauda kayan bata lpya se inta tashi tukun "ta yanka kayan marmarin suka fara sha sunayi suna labari.


Hjy najin motsin mashin din khalil tafito waje seda yayi parking tace "kai dogore

Please Login or Register in order to submit comment