Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register



akan hanya fatouma takira wayarshi, yanagani yaki dauka dukda de yanason daukar,

Shikam yayi dubara tun kafin soyayyar shi da fatouma tayi nisa yafadawa radiya yana neman ta, abun yabashi mamaki don yayi tunanin zata rude amma cewa tai "Allah yasa alheri yabamu zaman lpy, dear ni bantaba sawa araina dani kadai zaka zauna ba kai mijin mata hudu ne sede dan Allah ka kamanta adalci tsakanin mu, karka fifita wata akan wata Allah yakara maka budi na alheri yabaka ikon rikemu"har yanzu bedena mamaki ba, kuma sonta yakara ninkuwa akan nada don yayi tunanin zata rikitashi wani girmanta yake gani, itada kanta ta amshi no din fatouma tana kiranta da yake fatoumar itama wayayyace ko radiyar bata kira ba ita seta kira don aganinta inde radiya batai kishi ba itada take gidanshi don me ita zatayi, wani lokaci idan suka samu matsala da fatoumar itake shiga ciki don fatoumar tacika jan aji da yawa da zuciya ko lokacin kiranta yayi be kira ba setai zuciya .

Wayar nata ringing radiya ta dauka tace "amarsu ko kinwa angon laifine? "

Fatouma tai dariya tace"bawani laifi anty nasan dan kina kusa shiyasa be dauka ba"

radiya tace "kode kode? "

fatouma tace "ihmmm bakomi anty ki gaishe shi"

Takashe wayar radiya ta kalleshi tace "donme bazaka dauki wayar ka ba don inanan watarana fa Agabana zaka shiga wajenta "

yayi murmushi yana shan round yace "baagabanki ba dear don baa gida daya zaku zauna ba, idan kuna nesa da juna zakufi zaman lpy amma in kuna tare zaai ta samun matsala,"

radiya tace "bawata matsala kaide tsarinka ne haka "

yayi murmushi yace "kwanciyar hankali nake neman mana"

Suna isa gidan basu samu Aisha ba se fahad dake kwance har lokacin,

sabeer yace "friend yakamata ka kokarta karika yin aikinka tunda bawani keyi ba asara kake ja wa kanka don sisi kamfani bazasu dauki asararta ba "

fahad beko kalleshi ba yagama surutanshi radiya nata kallonsu suka tafi,

Aisha ko tunda taje gidan mommy take kuka tana rokon mommy akan taje wurin alhaji rabiu su dawo da faseelat, mommy tace ba inda zata, tanata jin haushin aishar donme bazata barshi ya mutunba.


bayan 4days

tundaga ranar fahad bekara zuwa gidan mommy ko umma ba don beda lpy sosai har drip biyu ya sha, bacin alllurai iri iri, dukda ciwon yakanje gidan su faseelat amma besamun ganinta duk yabi ya rikice,

Faseelat ma bata barcin kirki da tunanin mijinta take kwana, Aisha ko tanata kunsar bakin ciki,



Yau akayi sunan jamila ansaka wa jariri sunan khalil hjy dakanta ta sa aka kawomata sa da raguna biyu daga cikinnata aka yanka rago daya na dangin jamila daya nasu sa na mejego, bawani taron suna akeba don ranar ne sadakar bakwai na khalil duk kayanshi da sauran tarkace an rabar, nanda kwana ukku zaa raba gadonshi,

jamila nanan tana cigaba da kukan rashin mijinta hjy kuma ta dangana se rarrashin jamila take,

da daddare bayan musa yazo khalil yafadamishi gobe zekoma gida, don inde bakunta ce kar tafi sati daya,

musa yace "malan khalil naji dadin zama da kai nakaru sosai danhaka nakeson mukulla zumunci muhada matanmu suma surika kawance "

khalil yace "nikaina naji dadin zama dakai kuma nakaru sosai, nagode da irin karramani da dawainiya dani da kukayi"

musa yace" goben da karfe nawa zakatafi? "

khalil yace "8:am"

musa yace "inba damuwa kabari har zuwa 10am sena kaika da kaina "

khalil yace badamuwa yayi godiya, khalil ya amshi number musa akan idan yayi waya zasu rika communicating don wayarshi bata hannunshi besani ba kota kone ko wani yasamu oho, ranar Sun kai dare suna fira sannan musa yatafi,

da safe khalil ya shirya karfe 10am suka kama hanyar shiga cikin gari,

agidan hjya kuwa su siyama da wasu dangin jamila sunata soye itako jamila tafito tai zaune cikin rana da zumbuleliyar hijabinta dan dukda ba takaba take ba amma kullum da hijab jikinta, tai zaune tanata tunani matan da kenan sunyi sunyi daita takoma daki ta musu shiru,

siyama ta shiga daki hjy nata rirrigar lil khalil daketa tsala kuka tafadamata hjy taba siyama shi tafita wurin jamila,

taje tasameta tace "haba jamila so kike ciwo yakamaki kinzo kinyi zaune acikin rana, se yaushe zaki hakuri ki sawa kanki dangana khalil de yatafi baze dawo ba"

Jamila na kuka tace "hjy be mutu ba khalil baze mutu yanzu ba kullum ina mafarkinshi ze dawo"

Hjy tajawota jikinta jamila ta kwantar da kanta akan kafadar hjy tana cigaba da kuka hjy tace "kiyi hakuri jamila ki daure ,ko tausayin danki bakiji bakicin abincin kirki yaki samun ruwan nono kiyi hakuri ki daure"

suna haka motar musa tafaka kofar gidan, khalil ya kalleshi yace "nagode sosai Allah yabiya "

musa yace "yiwa kaine Semun sake haduwa "

khalil yabude motar yafita, yanufi cikin gidansu,

kamshin nama ya kewaye gidan tun bakin kofa yanashiga ya hangi hjy rungume da wata me hijab beyi tunanin jamila bace sede yaga sunyi kama da jamilarshi har abayar,hjy bataganshi ba siyama ce ta lura dashi, jikinta na rawa tace "yaya khalil !!!"

yana tsaye hjy tadaga ido taga khalil tsaye, zuciyarta na harbawa tace "khalil kaine?dama baka mutu ba "

Jamila ta dago daga jikin hjy ta kalli gun taga khalil tsaye yana hawaye tanajin matsanancin farin ciki da gudu taje ta rungumeshi tasaki kuka, khalil ya rungumeta yafara kuka shima wanda kukan nashi na farin ciki ne naganinta da hjy da kuma tausayinsu,

yan soye duk suka fito suna murna hjy tai tsaye farin ciki be bari ta motsa ba,
Jamila ta dago daga jikinshi tana murmushi tana hawaye tace "nasani baka mutu ba inata fadamusu sunki yarda "

ta juya tace "hjy nafadamiki yaya ze dawo"

Hjy ta daga kai, jamila ta koma jikin shi ya janye ta ya nufi wurin hjy ya rungumeta yasaki kuka,

hjy na kuka tace "kayafemin khalil nasan ban kyauta maka ba kayi hakuri "

siyama de se hawayen farin ciki take ,

seda suka lafa, sannan khalil ya kalli siyama dake rike da jariri shide yasan batada ciki ya juya ya kalli jamila yaga wayam duk katon cikinnan babu,

farin ciki ya lullubeshi ya saki hjy yaje ya amshi khalil ya rungumeshi yana hawaye,

Ya dago ya kalli hjy yace "hjy dana ne wannan? "

ta daga mai kai ya kalli jamila ya sakar mata murmushi yace "thank you nagode miki da kika haifarmin aboki "

Dukansu sunata farin ciki suka dunguma daki jamila taje tai zaune kujera daya da khalil ta dora kanta akan kafadarshi, shi kuma yana rungume da lil khalil,

hjy ta share hawaye tace "khalil baka cikin motar ne? Ance dasunanka acikin list na fasinja wayoyin duk akashe munyi tunanin ka kone"

khalil yakara rungume danshi yace "ina ciki hjy, muna cikin motor wata mota tazo ta banki tamu nide nasan lokacin da muketa salati tundaga nan ban kara sanin inda kaina yake ba se jiya, mutumen da ya tsince ni yace a daji ya sameni kwance shine yake fadamin kowa ya kone seni kadai natsira"

hjy tace "alhamdulillah nagode ma Allah daya barminkai araye, Allah yaraya minkai dana,zanso naga mutumen da yayi jinyarka nai masa godiya"

khalil yace "shine yakawoni anan amma ya tafi, duk lokacin da kk shirya zan kaiki gidanshi"

ya kalli siyama ya sakarmata murmushi tana murmushi tace "yaya munyi kewarka sosai Allah yakiyaye gaba "

yace "amin "

Yasa hannu yakara matse jamila jikinshi, ta dago ta kalleshi ya sakarmata murmushi yace "ke baki missing dina ba? "

jamila tai murmushi siyama tace "itako tai missing naka kaganta nan kullum kuka baci basha tanata bawa lil khalil wahala, hjy itace kebata abinci abaki kuma bata wani cin me kirki "

Khalil ya kalli hjya yayi murmushi, sannan ya meda hankalinshi wurin jamila,

su hjy suka tashi suka basu wuri,

Khalil ya aje lil khalil a different kujera ya meda jamila kan cinyarshi yanata kallonta yace "yaakai haka dasaura time fa "

Jamila tai karamar dariya tace "I don't know inajin ance kayi accident sede naganni a labour room"

yayi dariya yace "shine kika fiddoshi yanzu, meyasa bakyacin abinci? Kobakisan awurinki zesamu nashiba ?"

tabata fuska tace " nasani bazan iya ci bane yaya, inasonka sosai bazan iya jure rashinka ba "

Yace "don't cry my beautiful wife,yanzu gani nadawo seki dawo cin abincinki kinji? "

ta daga kai ya saukar daita ya dora lil khalil kan cinyarta yace"kibashi yasha daganinshi baya koshi "yasa hannu ya zare mata hijab,

jamila tai dariya ta rufe fuska yace "kunyata kikeji ninefa wanda kikeyin tumbur gabanshi kina kukan dadi"

jamila ta harareshi tace "kai yaya nidin ce ke kukan dadi? "


Yace "kona tuna miki? "

tai dariya tace "inafatan baka manta naka kukan ba? "

Khalil yayi dariya yasa hannu cikin rigarta yace "ina zan mance bari na fiddo mishi da kaina in tayashi sha don nima nayi missing "

Jamila ta janye mai hannu ta fiddo nono ta dorawa lil khalil abaki, yakama yayita tsotsa,

khalil yayi ta kallonsu yana murmushi yana godema Allah daya bashi lil khalil,kan jamila Duke tadago ta kalleshi taga yakuramusu ido ta meda kanta kasa,

baai minty 30 ba sega hjy tashigo da kula tazo taajiye gabansu tace "khalil ka sauko kaci abinci, daganan kabawa diyata taci nasan tafi jindadin abincin "

Yayi dariya ya kalleta seyaga kamar ba hjyarshi ba yanayin maganarta,

hjy tafita tadawo da bowl shake da nama tace "khalil wannan fa ba naka bane na mejego ne itakadai aikin ka kabata kawai"


khalil yana murmushi yace "to hjy "

hjy tafita tabar dakin, khalil ya kalli jamila yace "kinzama yargatan hjy harkin amshemin fada"

jamila tai dariya tace "toyasan ranka nide kabani abincin yunwa nakeji "

Yace "angama gimbiya"ta aje lil khalil ta sauko suka rika feeding juna,



nanfa labari yabazu khalil ya dawo ba jimawa gidan hjy ya cika anata mata barka da arziki,shima khalil anata zo mishi jaje da murna,


Da daddare da khalil da hjya kadai suna zaune sunata labari gwanin shaawa har lokacin bacci yayi,

hjya tace "to khalil katafi dakinka ka kwanta sekuma in Allah yakaimu"

khalil ya sosa keya yace "hjy Dan Allah kibani aron diyarki ta tayani kwana "

Jamila ta fiddomai ido ta girgiza kai,

Hjya tace "khalil biki fa take kadeyi hakuri kaje ka kwanta "

yace "nasani hjy, Dan Allah kibari mukwana acan "

Hjya tace "tonaji zata tayaka kwana nayau kurum amma tunda matsa mata zakai gobe zan medata gida wanka "

ya zaro ido yace "hjy wlh ba abinda kike tunani bane amma na hakura natafi in kwanta basekin medata ba "

yatashi yafita, hjya tace" wa jamila kikara ba khalil yasha kikawo shi in goyashi se zuwa anjima na kwantar dashi karyagaji da kwanciyar yahanaki bacci "

jamila ta amsheshi takara bashi yasha tashige kurya tayi kwanciyarta,


Hjya ta dade goye da lil khalil wanda basu sauya ma suna ba tana ta tunanin rayuwa, sannan taje ta kwantar dashi gefen mamanshi tatafi ta kwanta,


Wanshekare khalil yashiga central ya samo yadiddika masu kyau ya kaiwa tailor dinshi yakuma jaddada masa kar ya masa tazarce dinki mekyau yakeso sede beson shape din yayi yawa,

Jin khalil yadawo mamansu jamila sukazo murna daganan kuma mamar ta taroki hjy tabata jamila tatafi daita badon komi ba donta gyara ta, ta haihu yakamata tasamu gyara na mussmamman kafin arbain,

Badon hjy taso ba ta amince da marece suka tafi jamilar nata kuka batasan tafiyar,

2days kadai ya rage baba babba yadawo amma fahad ganin 2days din yake kamar shekara,

Aisha de tazama yar kallo iyakarta jinya yayi ta sambatunshi yagama tanata hakuri,

Faseelat jini ya dauke har amfara salla kuma jiki ya warware sede idawa Wanda nasan dataga habibinta zata wartsake,takan dan fita ta taya ummi aiki, umma sunanan sunata zarya so daya taje taga fahad daganan bata sake komawa ba don yamatukar bata tausayi,

faseelat na zaune dubara tafadomata tai sauri ta dauko wayar ummi takira fahad sede duk layukanshi kashe tameda ma ummi wayarta rai bace,

Mommy tagaji daganin Aisha na wahaluwa taje tasamu alhaji rabiu sukai magana da baba babba yadawo zasuje bada hakuri,


fahad ne kofar gidansu faseelat da wasikarshi a hannu da wata leda cikinta da waya aciki, yazo yadade kofar gidan tsaye besan yaya zeyi sakonshi yaisa wurinta ba,

Yananan Mubarak yafito fahad ya mika mai hannu Mubarak ya mikamai nashi suka gaisa, sannan fahad yace "friend ka temaka ka kaiwa antinka wannan wasikar da wannan ledar batare da ansan ni nabada ba plsss "

Mubarak da tausayi ya mishi yawa yanaganin yadda faseelat ke wahala da yadda fahad keta zarya seya amsa,

Fahad yace "thank you"ya fiddo 5k yamika mishi,

Mubarak yace "kabarsu banada bukatarsu" yajuya yatafi,

fahad ya tabe baki shide sakon yaisa,

Bakowa tsakar gidan ya shiga dakin faseelat ya kaimata yace inji fahad da kwance take ta tashi zaune tana farinciki tace "nagode dan auta inasonka sosai "

Mubarak ya kalleta yajuya,

ta bude wasikar dake dauke da good hand writing na fahad tafara karantawa "honey ya jikinki?inafatan kin samu lpy ,honey I'm missing you nayi zarya amma bansamu ganinki ba, I'm not well bana barci banajin dadin rayuwata please kiyi bakin kokarinki harsu abba su hakura ki dawo mucigaba da soyayyarmu, nayi kewar komai naki inacikin wahala duk donke, inafatan kina kulamin da kanki ga waya nan kiboye zan rinka kiranki inajin koda muryarki ne don na dan samu sauki, ina kara baki hakuri akan kuskurena, I love you the love that words can't describe it miss you "

faseelat ta rungume takardar tana jin farinciki ta bude ledar ta zaro wayar tana cikin danna no dinshi zata kirashi, kiranshi yashigo waar da yayi mata setting a ringingtone tafi daukar hankalinta wakar umar m shareef *bazan iya rabo dake ba* tai shiru tana sauraren wakar tanajin kamar fahad ne keyi seda kiran yakusa tsinkewa ta dauka tai shiru , fahad beko bar kofar gidanba yace"i miss you honey I gone mad and crazy nagaji"

Ta kalleshi duk ya sauya hawaye suka cikamata ido tace "hero so kake kamutu katafi kabarmu why bazaka kwantar da hankalinka ba,dubi duk yadda ka koma dan Allah ka kwantar da hankalinka very soon zasu medoni kaji? "

Yace "honey bazan iyaba kidawo kawai I want you, dakin dawo gareni zan warke zan dawo dede just come back to me "

tace "I promise you zan dawo gareka karage punishing kanka for me please"

ya lumshe ido yace "I will try "se sannan yatsaya karemata kallo tana sanye da white shirt transparent ta matukar yi mata kyau yanajin kamar yakai hannu ya taba yace "I will go home kiboye wayar nan sena kiraki da anjima before nan kimin good bye kisss "


Faseelat tai murmushi tana jefa mai wani kallo taiwa hannunta kiss ta jefa mai, yayi dariya yace "thanks se nakira" yakashe wayar faseelat tai murmushi ta bi list na music ta kunno wakar tana saurare hardasu hawaye setaji kamar itada fahad ne,

Sunata wayarsu bawanda yasani for 2days wadda bata ragemusu kewa ba sekarawa don duk ji sukeyi kamar suyi kurciya su samu juna,

baba babba karfe hudu yashigo katsina direct gidansu faseelat yawuce, yana zuwa yashiga da sallama, ummi ta amsa tana mai sannu dazuwa ya amsa yace "ina diyata ya jikinta? "

ummi tace "tawarware ai"ta kwalawa faseelat kira,

faseelat tafito dasauri tana ganin baba babba ta duka kasa tana gaidashi ,

Baba babba ya amsa ya mata ya jiki tatashi takoma daki,

Baba babba yace "munyi magana da alhaji yace har yanzu be bata takardarta ba wai sunata rokon alfarma "

Ummi tace "aikuwa "

baba babba yace "seya saketa tunda beda mutunci, bawani hakuri da zebada miji meduka aiba miji bane faseelat batai saar miji ba gaskiya"


ummi tai shiru ,kamin ta rufe ido tabude sede taga faseelat tsugunne gaban baba babba tana hawaye tace "baba Dan Allah kuyi hakuri wlh kuskurene ba acikin hayyacin shi yayi ba dan Allah kumishi hakuri tunda yagane laifinsa"

ummi tanata fidda ido dan faseelat tai shiru amma ita batasan ma tanayi ba seda takai aya,

baba babba yasha mamaki ranshi ya baci sosai yace "ko kinki ko kinso se yabada takardarki marar kunya fitsararra,tashi kiban wuri kona mangareki wurinnan"

Faseelat tatashi tashiga daki tana kuka ummi tai shiru tanajin kunya, baba babba yace "ai gwara ya saketan wannan Allah kadai yasan azabar data kesha wurinshi tai shiru bari naje nasamu alhajin shigowata kenan nashigo ganinta "

ummi tace "Tom angode kwarai "yafita

ummi bata shiga dakin faseelat ba tawuce dakinta, ranta ya baci takuma kara jinjina rashin kunyar faseelat,

Baba babba shagon abba yawuce suka kara tattaunawa akan maganar dawasu abunda ya shafesu sannan ya tafi gida,

Faseelat na kuka takira fahad yana dauka tace "hero baba babba yadawo, yace dole seka sakeni Dan Allah komai zasuyi karka sakeni wlh inasonka inasonka sosai"

fahad dake kwance muryarshi very low yace "kiyi hakuri kinji yanzu zanje nasamu daddy zezo yasameshi ki kwantar da hankalinki bazan iya musu abinda suke so ba"

Yadan rarrasheta yakashe wayar, yatashi ya nufi gidan umma yasamu daddy da maganar daddy ya amshi address na gidan fahad bebar gidanba seda yaga baba babba yatafi can, sannan ya koma gida,

koda daddy yaje baba babba yana cin abinci seda akadau lokaci yana jira sannan baba babba yafito ya kalleshi don betaba ganinshi ba yabashi hannu suka gaisa,

daddy yakara gyara tsayuwa yace "nasan baka gane niba, ni kamar ubane awurin fahad don nike auren mamanshi,"

baba babba yayi shiru yana saurarenshi yanajiran yakai aya,

daddy yace "nazo bada hakuri ne akan laifin da fahad yayi da kuma rokon alfarmarku da kuyi hakuri kubari takoma dakinta a janye maganar sakinnan tunda yayi nadama kuma suna matukar son junansu"

baba babba yace "alhaji nasan de bazaka iya aurawa yarka mebugun mata ba, to nima hakane aguna bamusan halinshi ba mukabashi ita yanzu kuma da mukasan halinshi rabasu shine dede don watarana in abun yazo da karshen kwana seya kasheta, Dan Allah kayi hakuri kabar maganar komawarta wurinshi Allah yahada kowa da rabonshi"

daddy yace "ayi hakuri alhaji atemaka wlh yaron rayuwarshi ta tsaya cakkk yana bukatar temako aduba "

baba babba yace "da akwai yiwuwar yin hakurin da anyi since to bacin maganar duka ma yanada wasu problem din don bayason zumunci, yahana yanuwanta zuwa wurinta"

daddy ya fiddo ido jin wata sabuwa yace
➰➰➰➰➰
*RAGGON MIJI*
➰➰➰➰➰






By




*MAMAN MAMY*
*(SHALELE)*





✍🏽✍🏽 *GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION*✍🏽✍🏽✍🏽

We are bearer's of so golden a pen🖊
We write assidiously perceiven no pain
So magical
Our creative golden pen🖊
Be hold our words
A product of our pen🖊
Savour our words
For it will cause you no pain.✍🏽


https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/




7⃣7⃣





*page dinnakine soupnass ke kadai wlh don jindadinki nayi shi, nagode da kaunar da kikewa buk dina da dogon sharhi da kike me zafi nagode kwarai inayinki to the core*🥰





*Manzon Allah(SAW)yacewa sahabbai shin bana baku labarin abunda yafi salla da azumi da sadaka lada ba,se sahabbai sukace wane abune wannan ya maaikin Allah seyace sulhunta tsakanin mutane yafi salla da azumi da sadaka lada*

Sulhunta tsakanin friends, couple,yanuwa and others



*MANZON TSIRA (S. A. W) ME GASKIYA ABUN GASKATAWA yace zumunci yana sargafe ne asaman Al'arshi yana cewa ya Allah duk wanda ya sadani kasadashi duk wanda ya yanke ni ka yanke mishi* Imam bukhari




Yace "gaskiya be kyauta ba kuma mu bamusan haka na faruwa ba amma zai gyara da yardar Allah adeyi hakuri"

Baba babba yace"ina kara baka hakuri don gaskiya bazata koma ba duk namijin da beson zumunci ai ba miji bane"

Ba yadda daddy beba amma baba babba be hakura ba hakanan yajuya yatafi, fahad yakoma jin good news daddy ya rufeshi da fada,

Fahad yayi shiru har daddy yagama sannan ya tashi yafita yana shiga mota ya dukar da kai jikin sitiyarin motar yafasa kuka,

Umma de tagaji da ganinshi cikin hali ganin yadda yafita ta biyoshi waje tasamu yanata kuka, ta bude motar tashiga,

Fahad yanata kuka tace "kayi shiru son, nagaji daga ninka cikin kunci ka kwantar da hankalinka namaka alkawari kwanan nan faseelat zata dawo gidanka"

Ya dago fuska face face da hawaye yace "when and how? Kinaji fa abunda daddy yafada wlh umma sora kiris na mutu "

Umma tace "kabar cewa hakanan ni namaka alkawari zata dawo very soon ka dena kuka"

Yadan rage kukan yace "kin cefa alkawari? "

Tace "eh alkawari ne kuma soon zata dawo kaide kayi hakuri kadena damuwa kuma sabeer yace baka Aiki kuma baka zuwa ,yau dinnan kakoma aikinka inhar kanason nacika ma alkawarin ka "

Fahad ya daga kai yanajin dan sauki kadan,

Tace "gobe naga canji in kuma haka kakeso heart beat din taka tazo ta sameka a kanjame to,duk kabi kasusuce kai son anya ko mutuwa nai zaka shiga irin wannan damuwar? "

Fahad yayi murmushi ya duke, tace "ko kaifa kayi hakuri nadan lokaci kawai "

Ya jinjina kai sannan tafita, ya koma gida yabude system dinshi yadanfara aiki sama sama,

Da daddare daddy yakai umma gidansu faseelat bayan gaisuwa umma tace "nazone akan maganar fahad Dan Allah kuyi hakuri dan daddinshi yace yasamu alhajin kuma basu dedeta ba"

Ummi tace "zaya hakura kude cigaba da zuwa gunshin "

Umma tace "to nagode kwarai ina faseelat? "

ummi tace "tana cikin dakinta"

umma tace "bari naje naganta se nawuce"tafita ta shiga dakin faseelat ,

Faseelat na kwance tunda sukagama waya da fahad take kwance, umma tai sallama faseelat ta tashi zaune ta amsa,

umma taje ta zauna kan gadonta ta dafata tace "daughter kikara hakuri kinji very soon zaki koma dakinki "

faseelat tadaga mata kai tayi shiru,

umma taimata bankwana tafita,

awaje daddy Sun tattauna da abba shima de cemishi yayi suyita zuwa suna bashi hakuri,

Dasafe fahad yafita office, yana zuwa ko zaunawa beyi ba manager yakirashi ya fita yaje office dinsa ya zauna,

Manager yakureshi da ido sannan yace "meye dalilinka nakin yiwa company aiki munyi loosing contract da dama kasan konawa kasa company yayi asara? "

Fahad da yake har yanzu sama sama yace "I don't know, and don't care I will repay nasan da rules na company "

manager yace "u r not serious nawa gareka da kake ganin biyan kudin is not a problem, kudin sunkai 50 millions dollars "

fahad surutun manager yafara isarshi yace "I will repay all ur money back"

ya tashi yafita, manager yabi kofar da kallo yana jin matsanancin bacin rai,

fahad ya rubuta musu check ya basu yafita abinshi, bawai kudin is not much ba, sunada yawa to bayadda yaiya dole yabiya ,

tunda dugu dugu daddy yakoma gidan baba babba, yakara bashi hakuri amma bejiba sema rokonshi da yayi karya sake dawowa,

da marece alhaji rabiu yaje wurin baba babba shima yarokeshi baba babba yabashi hakuri ya tafi,

dukda alhaji yaroki daddy amma wanshekare seda yakoma, baba babba seyaji nauyinshi tunda zuwanshi na ukku kenan,

baba babba ya kalli daddy yace "ko a lahira wani nacin darajar wani, domin Allah yakan kankare zunuban bawa in yaranshi namashi addua yakara masa matsayi a aljanna, ana sanya iyaye wadanda suka haifi mahaddatan alkurani a inuwa albarkacin yaransu, wasu daga cikin yara kananu zasu ceci iyayensu a ranar kiyama,fahad yaci albarkacinku na hakura zata koma amma da sharadi se yazonan tareda waliyanshi da suka nema mishi aure agabansu yayi alkawarin baze kara dukanta ba kuma baze hanata zumunci ba in kuma yayi daya dagaciki to zamu kaishi kotu yabata sakinta "

daddy yace "insha Allah ze kiyaye kuma zamuzo din nagode da kamin alfarma "

baba babba yace "sekunzo "yajuya yashiga gida, tun kan hanya ya kira fahad yace yasameshi gida, ba bata lokaci yatafi acan daddy yasameshi,

daddy yafadawa fahad yadda sukayi, zufa taita karyomishi don besan komi zefaru nan gaba ba yanata de rokon Allah yarage mishi kishin amma dasaura,

Ba yadda yaiya yace "ya amince da hakan "

daddy yace "to inma kakara de ni baruwana ciki katashi katafi se zuwa gobe dasafe se kasame mu acan da karfe 9am"
Fahad yayi godiya yatashi yafita,


wanshekare da daddy da alhaji rabiu da kaninshi da fahad a sitting room na baba babba, sukadanyi gaishe gaishe da jajen abinda yafaru sannan baba babba yafadawa fahad sharadinsu, fahad yace ya amince agaban su,

baba babba yace "ga waliyanka nan duk sunji yadda mukayi idan har hakan tafaru karkai tunanin zata dawo gareka, yanzu zanyi magana da alhaji sekaje kadauki matarka ku koma gida "

fahad yace "nagode zan kiyaye"

suka rufe taro da addua suka tashi,

Yana shiga mota yakira faseelat yabata good new's taita murna tana tsalle shikam se aikin murmushi yake kamar yana ganinta,

ta waya baba babba yakira abba yafadamishi yadda sukayi abba yayi godiya sosai yace zasuyi magana da ummi sufidda ranar komawarta baba babba yace "eh amma karya

Please Login or Register in order to submit comment