Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

addua ta agareki , Allah ya kara maki dadin.....πŸ˜‚πŸ€­ kita zama tauraruwa awurin oga*



*FANS I'm sorry wani dan bayani da nayi abaya cewar faseelat tana da gadon khalil I'm sorry namanta romance ba sex bane πŸ˜‚ tunda be taba kusantar ta ba ko idda ma batada ita, inafatan kungane, sannan masu cewa haramunne fahad ya aureta to gaskiya ba haramun bane Sabida shi besan tana da aure ba kuma Allah baya kama bawa da lefin da besaniba kuma koda yasani aure be haramta tsakaninsu ba, sannan akwai masu cewa halak ne namiji yakarewa macen da yakeso kallo eh hakane amma seta suturce jikinta, mazhabobi da dama sunyi magana akan haka wasu suna ganin zata iya bayyana ado gareshi toni gaskiya nafi ganewa wadanda sukace bazata bayyana ado gareshi ba, sena fuska da tafukan hannaye da kafa,, kuma yawancin malamai suntafi akan haka, ga misali namiji yazo yana sonki se yazam yasan komi na jikinki to in yazo yafasa fa? Shikenan ya kalli banza? πŸ˜‚ kuma hakan mabudin aikata zina ne, to nide shawara ta yanmata ko gobe ne aurenki da namiji ki kame kamkam ta hanyar zumbula katuwar hijabinki komi kenan in an daura yagani, amma ki tabbatar bawani aibu kike boyewa ba wannan kam kin yi yaudara da zalunci , kuma inyagani komi na iya faruwa, Allah yasa mudace.*


*koda yaushe in anga kuskure amin magana plsss zan kasance me daukar gyara, haka ma kuna iya bani shawara, Nagode da irin kaunar da kukewa buk dinnan.*



Yana tuki yanajan tsoki, yarasa ina hankalinsa ya tafi harya kai hannu jikinta, ta madubi ya kalli siyayyar da yamata da suke aje a back seat yakara jan tsoki, ya fiddo waya yayi dialing number dinta tana ta ringing bata dauka ba cikin takaici yace "pick my call mana I want to apologize for my mistake"yakara dialing number din,

Faseelat nashiga gida ta fada kan bed tana kuka,cikin kuka take cewa "ya daukeni yariska ne kome? Daze tabani kamar wata matarshi, saboda inasonshi doesn't mean zan bari ya rika tabamin jikina "

Tana kukan tace "duk laifina ne da nake sonka sosai tunda kasan haka ai zakamin komi kaga dama don kasan bazan iya rabuwa da kai ba "

Tanaji wayarta na ringing bata dauka ba se kuka kawai take aganinta bama sonta yakeba jikinta kawai yakeso,

Ganin ya mata 3 missed calls bata dauka ba yasa ya aje wayar, direct kofar gidan sabeer yawuce ya mishi waya ya fito,

Yana shiga motar fahad ya dago da kanshi daga jikin sitiyarin motar yana kallon sabeer,

sabeer yace "mutumina lpya de? "

Fahad yaja tsoki mtswwww yana shafar sumanshi da hannu daya yace "ansamu matsala wlh"

sabeer yace "wace kalar matsala kuma?"

Fahad yace "daga gun faseelat nake, cikin kuskure muna fira na taba breast dinta, shine fa tai fushi tafita tana kuka nakirata fiye da 2 taki dagawa "

Sabeer ya fashe da dariya yace "kai meyasa kai haka ko Kasa aisha ce? "

Fahad ya daga mai hannu yace "please stop joking take it seriously "

Sabeer yace "gaskiya u have made a very big mistake, kaga yanzu setayi tunanin ko ba aurenta kakeson yi ba, wai kana aikinmi ma kayi haka? "

Ya hura iskar baki yace "bana cikin hayyaci na ne, ni tunda na shaki kamshin perfume dinta ma naji ni somehow gashi taci gayu, Allah nema ya takaita don jinayi kamar nai hugging dinta "

Sabeer ya fashe da dariya yace "plsss katafi dani wataran nima in shako irin perfume dinnan inji me kaji "

Fahad ya harareshi yace "bazako kataba jinshi ba, nide kawai kabani shawara "

Sabeer yace "yanzu ka tura mata text kabata hakuri kafada mata u didn't do that intentionally "

Fahad yace "bana tunanin zata hakura na lura taurin kai ne daita amma bari natura mata "

Sabeer yace "zata hakura mana tunda tana sonka kai de ka kula kar hakan ta sake faruwa "

Yace "OK I will try "

Sabeer yace "bari na shiga ciki se munhadu anjima "

Fahad yace "OK thanks "

Sabeer ya bude mota yafita,

Fahad ya turawa faseelat message,

Tana ta ajiyar heart ta bude message din "cutie I'm very sorry karki daukeni da wata manufa I don't did it intentionally, I just lost control ,kiyi hakuri ki dauki wayata, ina tsananin sonki cutie I'm ready to marry you ko da gobe ne, kimin hakuri I apologize for my misbehaving amma kisani ke kika rudar dani har nayi haka ,kuma I'm regretting forgive me please "

Tana karantawa setaji dan sauki aranta unlike b4 da takejin kamar zuciyarta naci da wuta,

Tanata bin message din ya kira ta vedio call ta dauka tana kwance,

Yana kallon fuskarta duk hawaye yayi fuskar tausayi yace "cutie I'm sorry kidena kuka "

Tai shiru kawai tana kallonshi yace "kinmin hakurin? "

Seda akadau minutes ta jijjiga kai alamun eh,

Ya lumshe ido ya bude yana sauke ajiyar heart yace "thank you very much "

Ta daga kai yace "talk to me mana "

Tai shiru yace "kince kin hakura kimin magana "

Tana turo baki tace "nayi hakurin shikenan"

Yace "I'm happy, wai dama cutie dina ustaziya ce bansaniba, ai da I'm about to hug you and give you a good kiss"

Tai dariya tace "just try it u will see "

Yayi dariya yace "I'm just joking, nayi miki shopping baki bari kin amsa ba, zandawo nakawo miki "

Tace "noo Nagode banaso kabarsu "

Yace "plsss mana bangaji da ganinki ba"

Tace "aa karka dawo"

Yace "to I will tomorrow "

Tace "aa bazan fito ba "

Ranshi ya baci yace "for god sake ya kkso nayi ne? Tunda nabaki hakuri ai komi yawuce kuma bawani abu zanmiki ba wani abu kawai zanbaki"

Cikin bacin rai tana ganin yama rainata tace "nace bazan fito ba ko dole ne? E ye "

Rai bace yace "saboda kawai na tabaki kike wannan abun amma ahaka kikaje kina bari wani ya kwana samanki, bakiji komi ba sedan tabawar da namiki itace tashin hankali "

ta kure shi da ido tana mamaki kuka ne yazo mata tace "kome zaka fada kafada amma bazan fito ba, ka daukeni yar iska ne? Da kake kiran dan tabawa?kuma naje nabari wani ya kwanta akaina din bama kwanciya yayi ba cinye ni yayi "

Idanun fahad sukai jawur yace "dan kinga ana sonki kike gayawa mutane magana bayan cutata da kikayi?kada kifito din nima bana bukatar ganinki useless girl "

Diff yakashe wayar ta kara rushewa da kuka saboda kalamanshi Sun mata zafi, tai ta kuka har tagaji kanta na ciwo barci ya dauketa.

fahad huci kawai yake fiddawa yana tada mota yakecewa "what she take her self? da zata rika medomin magana ni tsaranta ne? "

Yana tuki da hannu daya dayan kan bakinshi yana tunani yace "bazata fito ba,nitake fadawa haka it's okay duk ni najawo danake sonki sosai harma nadamu da son ganinki, yanata surutu har ya shiga gida aisha na ganin yanayinshi taja baya fuuuu ya haye Sama ya shige dakinshi ya kulle,aisha bata bishi ba don karta kai kanta karamin aikinshi ne ya wanka mata mari inta tsaya tambayarshi meke faruwa,


Faseelat taita barci har 2 dawowar Mubarak ne ya tadata yana tambayar "yaya ina abinci na? "

Idanu kumbure tace "banyi ba ban lpya kaina ke ciwo ka bari ishak ya dawo ya dafa maku ko taliya ce "

Cikin jin tausayi yace "sannu yaya amma ni yunwa nakeji "

Tace "jeka kitchen kaduba akwai sauran tuwo se kaci"

Ya juya yafita ta tashi tayo alwala ta kabbara salla cikin salla tana kuka take rokon Allah zabi in fahad ba alheri bane agunta Allah ya cire mata sonshi,

Har dare be kira ba itama bata kirashi ba cikin dare batai barci ba kwana tai salla da addua, shima fahad sama sama yayi barci tunanin faseelat ya hanashi barcin, seda ga baya ne yake ji be kyauta ba,


Da safe yayi ta kiranta taki dagawa yaja tsoki ya aje wayar,

Har akai kwana ukku bata daukar kiranshi har ummi ta dawo,

Gabadaya fahad so yake yaji muryarta saboda tafiya zeyi yanaso ya fadamata amma taki dauka wanda seda ta nuna jarumta sosai sannan take hakan don ji take kamar ta dauka inyakira amma take sharewa dan yagane itace yayiwa laifi,

ummi taga sauyawar walwalar faseelat ta Kasa hakuri yau da safe take tambayarta "mike damunki faseelat? Naganki sukuku tunda nadawo "

Faseelat ta kakaro murmushi tace "bakomi ummi "

Ummi tace "hmmmm"ta kyaleta Amman tasan da wani abu kam,


Karfe biyu na rana jirgin su fahad ze tashi karfe 1 saura ya tura mata message "cutie I'm sorry for everything that happened, nata kiranki Amman u ignored my calls, zan tafi Italy I will spend only 10 days there need ur prayer and remember that I love you ,take care of yourself bye "

Tana karantawa tafara hawaye tana jiran yakirata ta dauka itama she's suffering ,amma shiru be kira ba setayi niyyar kira zuciyarta seta bata shawara karta kira tajirashi ina har 2 be kira ba koda ta yakice shawarar zuciyarta ta kirashi har Sun daga, ta aje wayar tasa kuka don takaicin wahalar da kanta da takeyi gashi har ya tafi,

Shima yana cikin jirgi yana tunaninta, saboda he's wondering rashin kiranshi da tayi bayan karanta text nashi,

Faseelat na kwance tana duba pictures nashi da yanzu dasu take fira ummi tashigo, tana kallonta tace "ke tashi ubanwa ye akaganku dashi shekaran jiya?"

Faseelat tai wuf ta mike tana sadda kai tana mamakin yaakai ummi tasani bayan ranar ma bakowa unguwar tasu "

Ummi tace "dake nake magana "

Faseelat na inda inda tace "saurayi nane "

Ummi ta watsa mata harara tace "saboda bakida gaskiya seda nayi tafiya sannan kika gayyaceshi gidannan ko? Wato ni bama haushin fitar nakeji ba haushina mutane zasuyita ganin baki gama idda ba kike fita gun wasu tunda ba kowa yasan abinda ke faruwa ba yanzunnan daga fitata can gidan safiya take cewa wai ranar nan ta leko ta ganki zaki shiga mota, ina amfanin haka faseelat? Shi din waye shi saurayin naki? "

Tace "sunanshi fahad ga pic dinshi nan "
Ta nunawa ummi,

ummi ta amsa tagani tace "immm shi kinasonshi kenan? "

Faseelat ta daga kai ummi tace "Allah yasa alheri anshi nan"

tamika wa faseelat wayarta tafita,

Bayan su fahad Sun isa Italy be kira faseelat ba itakuma ko takira bata samu, faseelat takara shiga tashin hankali kar ya shareta don istiharar da takeyi setaji tana kara sonshima fiyeda da,

Shi ko fahad kyaleta yayi yabata lokaci amma da niyyar ranar da ya dawo zeje gidansu.


************************

Bangaren khalil lpya lau suke zaune da jamila har yasata islamiya tana zuwa kullum, yana iya kokarinshi wurin kyautata mata itama haka kuma yana hakuri da yarintar ta, maganar harka kau yanzu Sun zama yan hannu itama har magani yake siyomata yabata tasha suji dadinsu,
Kullum inbe shiga da leda ba inyadawo daga shago jamila zatai ta kumburi wani lokaci taita jaje har se yafita ya siyo mata wani abu, hjya ko tananan tana fama da haushi don duk jumaa se yakai jamila gidan, bayan antaso masallaci ya dawo su zauna su baje hira suna dariya, jamila ba ruwanta da wani taya hjya aiki intaga tanayi shi kuma be taba mata maganar ba,



Yau jamila tun tsakar dare take sheka amai gabadaya ta jigata, khalil na gefe yanata mata sannu yana zubda hawaye, saboda tausayi cikin kuka jamila tace "yaya ka temakamin cikina zafi "

Yace "kiyi hakuri kinji kibari 4 dede zamu tafi asibity kita innalillahi zaki warke"


tun karfe ukku da rabi ya mike ya daura mata zani don zindir tayi daurin zanen daban ita daban yasa mata hijab suka tafi asibity da temakon makwabciyar jamilan,

suna zuwa aka bata gado ana dubata dan tayi yaushi sosai, sukai mata tests,

Bayan tests din sunfito likita yakira khalil office yabashi albishir matar shi na dauke da ciki wata daya,

Khalil ya daga hannu sama cikin tsananin farin ciki yake fadin "alhamdulillah, alhamdulillah Nagode likita "

Likita yayi murmushi yace "Amma tana bukatar kulawa sosai saboda ta wahala yanzu zaku cigaba da zama anan hospital har taji sauki dan gudun matsala "

khalil yace "to mungode doctor Allah yasaka "

Ya tashi ya fita yana murna lokacin anata kiraye kirayen salla cikin zumudi yakira hjya, ganin kiranshi hjya dake zaune tana tasbihi ta dauka cikn faduwar gaba tace "lpya de khalil? "

Yana murna yace "ai ai muna asibity jamila ce ba lpya likita yace she's 1 month pregnant "


to bari muga ya hjya zataji,
Amma a next page 🀣



comment da yawa inkunason one more page in the night πŸ’ƒπŸΌ
[7/12, 11:01 PM] Maman Mamy: ➰➰➰➰➰
*RAGGON MIJI*
➰➰➰➰➰




By




*MAMAN MAMY*

*(SHALELE)*



https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/

✍✍✍✍✍✍✍
*~GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION~*
✍✍✍✍✍✍✍


*~❄We beare's of soon golden We writer's assiduously percieven No pain so Magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Our worlds for it cause u np pain~*



4⃣4⃣





*Dedicated to raggon miji fans group 1 inajin dadin comments naku wannan pagyn na wadannan zaratan matan ne*

*samira yahya*
*lady*😘
*F πŸ˜‰*
*Aisha kd*
*yanshana*
*jamila adam*
*Nana bilkisu*
*balkisu ishak....*
*husnah yar niger*
*maman zainab*
*halimatussaadiyya*
*mss L*
*yayana abin alfahari na*
*zainab*
*momyn abdul*
*asiya aliyu*
*se suwa ma ?πŸ˜‚kuna da yawa duk wacce bataji sunan ta ba ta jira a next page kuci gaba da comments πŸ’‹yanuwa*



Anata kara tambayata akan idda da takaba, na tambayi wani malami ga abunda yace πŸ‘‡πŸΎ


*_Idan Miji Ya Saki Mata Be Kusanceta ba Babu Idda a Gareta. Amma Idan Mutuwa Yayi Wajibi Ne tayi Masa Takaba Koda Kuwa Ranar Auren Ne Ya Rasu. Sannan Zataci Gado Cikakke._*




Hjya cikin farin ciki tace "alhamdulillah naji dadin wannan labarin Allah yabata lpy anjima kadan zanzo da gari yayi haske zantaho muku da breakfast "

Yana murna yace"nagode hjya se Kinzo "

ya kashe wayar ya koma wurin jamila da akawa alurar bacci ya zauna ya kamo hannunta ya rike yanajin tsananin son ta aranshi,

Karfe 7saura hjya tazo ta shigo dakin har lokacin jamila na bacci yana sadda kai ya aje hannun jamila,

Hjya cikin murna tace "ya jikinnata dasauki ko? "

Yace "eh dasauki tana bacci ne "

Hjy tace "to Allah yaraba lpya "

Yace "amin "yana sosa kai ta harareshi tana murmushi wato ko kunya ma bayaji yake amsawa da amin hmm,

Ta samu wuri ta zauna shima yayi zaune hjya tace "katashi ka tafi school mana lokaci na wucewa "

Yana sosa kai ba dan yaso ba ya tashi ya fita,

Hjy tabishi da kallo har ya fita tace "kaganmin Marar kunya nan zakaita zama tomiye amfanin zuwa na mtsww "

Karfe 10 jamila ta farka tana ya mutsa fuska saboda jinta weak,

Hjy tace "sannu jamila "

Jamila tazo tashi hjya ta temaka mata saboda ruwan dake shiga hannunta, tana yamutsa fuska tace "kubani abinci hjy"

Hjy ta jawo danwake data dafo ta bude kular ta dora kan cinyar jamila,

Jamila naganinshi ta yamutsa fuska ta dauke kai tana dade hanci tace "hjy farfesun kai nakeso, kibugawa yaya yakawo "

hjy ta dan harareta tace "to bari akirashi"

Takira khalil tafada masa, ko minti 30 baaiba se gashi da katuwar kula taff da naman kai maybe kan rago daya ne ya siyo duka don yasan abarshi daci bare yanzu da suka zama biyu , hjy na kallon ikon Allah ya zauna yana bawa jamila a baki tana ci yana mata sannu,

Hjy ta hadiyi miyau da niyyar a rage ta samu taci Amman tasss jamila ta cinye naman ta yabata ruwa tasha tabuga gyatsarta ta koma ta kwanta tana fidda nishi πŸ˜‚shi ko se sannu yake jera mata, shiyasa lokaci daya takara jibgewa ta mulla kibarta yo dadi take ci .

hjy cikin hadiyewa tace "ka kira gidansu kafadamusu? Kakira kafada musu susan abinda ake ciki "

Yace "Tom hjy "


ya dauki waya yabuga ma mahaifiyarta yafada mata jamilar bata lpya,

Wurin karfe 2 yan gidansu sukazo dubata seda laasar suka koma ,

hjy taga takaici yadda khalil yayi ta rawar kafa, kullum cikin tambayarta yake me xakici? Me kikeso ?wanda hakan ke bawa hjya haushi sosai, wani lokaci ma jamilar tai ta kuka tana cikinta shi ko yayi ta hawaye hjy taji kamar ta samishi kota,


Bayan 7 days aka sallamosu suka koma gida,

Kullum shike girki tana kwance tana baccinta yaci ya tafi gaida hjy sannan yawuce school ganin da hjy tayi yana makara tace yarika bari yanazuwa da daddre suna gaisawa,

Daganan yafara zuwa gaidata da dare, abun da yake ba hjy mamaki kullum se yazo da leda wani lokaci biyu har da ita wani lokaci guda daya su gama hira ya dauki abunsa yawuce, sosai takejin haushin shi gani takema kwara lokacin faseelat beyi rawar kai haka ba, itako wannan kullum cikin kwalkwalarsa take,

Se hjy ta fiddo da sabon salo in yazo da daren taita janshi fira har 10 wani lokaci ma har 11 ,tasamu fura ko gyada ko wani abu ya zauna suna ci suna fira,

yau ya shigo da katuwar kaxar da jamila tace a saimata akasha fira ya tashi tafiya ya dauki ledarshi,

Hjy takasa jure wannan tace "khalil shikenan de kazama bawa kulum cikin kashin kudi kake ita batasan babu ba? da zaace kullum se ka saimata nama, abunma be tsaya nanba yanzu de khalil jamila tafini agunka kafi sonta akaina,"

Cikin kwantar da murya yace haba hjya? Yazaki hada kanki da jamila kefa ke kika haifeni kikai duk wata dawainiya ta yazaayi na hadaki da wata, wlh hjy duk ranar da kikaga banyo muku leda biyu ba rashin kudi ne, kuma naga ita ga larurarta shiyasa, ya mazaayi na kwatanta fifitata akanki bayan nasan manzon Allah (S. A. W) yace" wanda ya fifita matarshi akan mahaifiyarshi yana tare da tsinuwar Allah data malaiku da ta mutane gabadaya, bazaa karbi aikinshi na farilla kona nafila ba harse ya tuba zuwa ga Allah ya kuma rika kyautata mata kuma ya nemi yardarta"

"wlh hjy kinfi kowa aguna matsyin ku ba daya ba, amma nagane kuskurena kuma zan gyara kiyi hakuri Dan Allah "


Hjy tace " nayi amma ka rage wannan rawar kan tsiyar ko nima haka kakemin rawar kan? "

Ya girgiza kai yace "Allah yabaki hakuri "

Tace "amin "yafita

Tace "shashasha gabadaya baya adana komi ciki ciki kawai yasa agaba ita kuma shegiyar taita bashi wahala "

Can zuwa ya shigo da rabin kaza ya ajiye mata ya mata seda safe tace "Allah yakaimu "ta jawo plate din tafara yagar kazarta tana "haka kawai ita ta haifamin kai da kullum abinda kake samu kanta zaya kare? "


Khalil na shiga gida ya iske jamila tsaye tagaji da jira, cikin rarrashi yace "kanwata amin hakuri nadawo daga gidan hjya mashin dina yayi faci"ya mata karya.

Tace"karya Kake wlh wai haka ake kasan kanada iyali Amman kaje kai zaune wurin hjy ni kabarni ni kadai, wani lokaci ma senayi barci zaka dawo nide wlh ana shiga hakkina "

Yana mata wani kalar kallo dukda beyi mamaki ba don ita bata wani tsayawa tauna magana takeyinta kuma bata barin abu cikinta setai magana, yace"nike karyar jamila? "

Tace "eh karantse faci kayi"

Yace "hmmm "

ya mika mata kazar ta yace "ga sakonki "yawuce,

Ta ansa tana maganganu Kasa Kasa ta dauko plate kitchen ta dawo falo ta bude sega rabin kaza,

Ta bata fuska ta dan iba ta meda miyau tabishi daki yana fitowa wanka kenan tasameshi tana ya mutsa fuska tace "ya naga rabin kaza? kasan de tamin kadan "

Yace "eh nasani kiyi hakuri da wannan banda kudine shiyasa "

yawuceta tabishi tana cewa "amma kasan de baa seda rabin kaza ko? Kawai kace hjy ta raba shine "

Ranshi ya baci ya juya ya zaro ido yace "eh hjy ta raba se meee "cikin tsawa

taja baya ganin yadda ya tasomata ta juya tana kunkuni, yaja tsoki ya saka rigar shi ya kwanta,

Wanshe kare da ze fita tace asiyo mata tsire yace "banda kudi "yayi hanyar fita

Tabishi har zaure tana bashi hakuri hardasu zukunnawa itade yasiyo ta samu taci, badan ita ba yace ze siyo albarkacin cikinta,


Bayan kwana ukku



yau tunda karfe 5 na asuba jirginsu ya sauka Nigeria, suna isa gida suka fara gyaren gidansu sannan aisha ta dafa masu indomei suka ci seda suka kashe arna bacci ya kwashesu,

Karfe 12 ya farka har lokacin aisha na barci a gaggauce ya diro yayi wanka shaf shaf ya shirya ya sauka kasa,

yaje ya bude jakar tsarabarsu ya fiddo wani akwati ya fice ya bude motarshi haryanzu kayanda yamata shopping sunanan ya fiddosu ya meda a motar da ze fita daita ya shiga motar yayi hanyar gidansu faseelat,


Faseelat ko jiya tata kiranshi bata shiga dan kwana goma yace ashe basu taso da wuri bane se yau,
Tagaji ta hakura Amma ta cika tai famm,



Tana daki tana charting dan yau gidansu hutun girki suke abba yasiyo fura da yoghurt da kwakwa daita zasuyi lunch dan sungaji da abincin,

Ummi na waje itako tana yankan farce yaro ya shigo gidan yace "ana kiran faseelat inji wani me mota "

Ummi tace "jeka ce gatanan zuwa "

Tamike ta leka ta window faseelat nata charting dinta hankalinta kaf yana kan wayar ummi na kallonta cikin zolaya tace "tsuntsuwar soyayya"!


Faseelat tadago tana zumburo baki ummi na dariya tace "ga tsuntsun soyayya can yazo yana jira "

faseelat tafashe da dariya tanajin dadi ta mike ba shafa komi ta jawo katuwar hijab dinta tasaka tafito tanawa ummi dariya tafita,

Ummi ta girgiza kai "ansamu wanda akeso inyazo zaafita ana dokin ganinshi "


faseelat nafita ta hangoshi tsaye bakin Ash din motarshi yana sanye da dark Blue Jeans da red shirt,

Bakaramin kyau yayi ba setaga har fari yakara sede yadan rame tundaga nesa take karemishi kallo ,shima yanata kallonta,

Tana karasowa kusa ta sadda kai,

Sheik kabir gombe yace πŸ˜‚su mata munafukaine tundaga nesa suke karemaka kallo da sunzo kusa su sadda kai,
[7/12, 11:01 PM] Maman Mamy: ➰➰➰➰➰
*RAGGON MIJI*
➰➰➰➰➰




By




*MAMAN MAMY*
*(SHALELE)*


https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/

✍✍✍✍✍✍✍
*~GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION~*
✍✍✍✍✍✍✍


*~❄We beare's of soon golden We writer's assiduously percieven No pain so Magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Our worlds for it cause u np pain~*



4⃣5⃣




*dedicated to Dr fatee the writer of matar bahausheπŸ’‹*





Tana zuwa tai tsaye ta sadda kai, yanata kallonta kamar yau yafara ganinta dariya taso kufcemishi ganin doguwar hijabin data saka abun dariyar abunda ake boyemishin de sunfito dan hijabin roba ce tsawonta yakara sa saman yayi shape,yana kara kallon tudun breast dinta yace "enter the car mana kinyi tsaye "

Ta dago tace "a, a daga nande "

Yana mata wani kallo yace "wlh zanzo in daukeki nasaki ciki da tsiya, gwarama kishiga"

Ta tunzuro baki ta bude marfin motar ta shiga, shima yabude yashiga yana kallonta yace"yanzu ni na zama abin tsoro kamar ba fahad naki ba "

Ta dago ta kalleshi tai murmushi, shima ya murmusa yana juyawa ya jingina jikin kofa dan yaji dadin karemata kallo yace "kinbani wahala cutie dan kinga inasonki da yawa ko? "

Ta harareshi, wanda hakan ya matukar birgeshi tace "munsha wahala, zakace kasan yadda nai missing dinka kuwa? Nasha kuka many times saboda shareni da kayi "

Abun ma yabashi dariya yadan shafi sajenshi ya kalleta yace "ke zakice haka? Kira nawa nai miki kikai ignoring dina dubi duk yadda nafada saboda tunaninki, kincika taurin kai tunda nabada hakuri ai shikenan amma se lokacinne ma kika kara hawa kawai dan na "se yayi shiru ya saki murmushi yana shafar kanshi da hannu ya dan kalleta yaga tanata watsa mai harara, yayi dariya yace "bada gangan nai hakan ba, nide inarokon ko hakan yafaru anan gaba amin hakuri, wlh kamshin turarenki kanshi rudani yake "

Ta balla mai harara "Allah karka kuma dan bazan daukeshi a kuskure ba tom "

Yayi dariya "kinganki ko, hmmm ki koyi hakuri dani shiyafi miki "

Ta turo baki gaba, yana dariya yana nuna setin breast dinta da hannu yace "harda jibgo hijab amma dukda haka ga yan albarkannnan sunfito gaidani "

Dasauri tadora hannu biyu saman breast dinta takare su, ya kwashe da dariya itako se kallon saman hannun take taga wai dagaske ne,

Ya sassauta dariyar yace "to yazakiyi ne tunda suna sona kome zaki sa se sunfito sede in a akwati zaki rika sakasu "

Ta zumburo baki tana so tayi kuka,

Yace "I'm sorry,im joking, nadena amman kicire hannunki plsss kibari ko daga cikin hijab din nasamu narika meda miyau na,"

Taki cirewa yace "kicire kigani wasa nake yi "

Ta zame hannun tana kallon gaban nata ashe dagaske yake sunfito tai sauri tameda hannuwan akai,

Ya dafe goshi

Please Login or Register in order to submit comment