Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

cikin motar"

Hjya tafashe da kuka da shakakkar muryarta tace "khalil ya zama toka ya zaai aganshi,ashe kallon bankwana nayi mishi ayau, naso ya mutu yanajin dadi ba cikin kunci ba "

baban farida yayi sallama yashiga ciki,

kawu manu yace "ance ba gawar da ta kone, kode har yaisa batsarin shi?"

baban farida yace "a, a beje ba saboda yanzu mukayi waya da zulai tace beje ba "

hjya tace "khalil fa ya rasu shikenan banda kowa yanzu se siyama ba alhaji ba khalil "

Sukace "hakuri zakiyi hjya Allah yajikansu ya musu rahma "

Hjy ta kalli baban farida tace "ina siyamar? "


baban farida yace "suna asibity da jamila taji mutuwar se labour tataso mata "

hawaye suka zuboma hjy jin wadda ma yatafi biko tana cikin garin, se tausayin jamilar yakamata tanason khalil sosai, se hjyar taji yanzu ba abunda takeson gani se dan ko yar khalil ,

Tana share hawaye tacewa baban farida "mutafi asibitin "

Ta tashi ta dauko abayarta, ta fita su kawu manu da baban farida suka biyo bayanta, su hjya rabi ko suna zaune jingum jingum,

Baban farida ya budemata mota tashiga suka nufi asibity,

Suna zuwa siyama ta rungume hjy tana ta kuka se yazama hjyarce ke rarrashin siyamar, suna tsaye ba abinda sukeji se kukan jamila dake fitowa daga cikin labour room,



Fahad na isa gidan mommy yashiga jiki sabule ,ya fada kan kujera yayi zaune yanata tunani yanzu wane hali faseelat take ciki? zuciyarshi zafi kawai take for minutes sannan mommy tafito taganshi yanayinshi wani iri tace "lpy son naganka haka? "

yace "mommy amira bata lpy suna asibity tundazu "

mommy tace "subhanallahi tun yaushe? "

yace "tunda safe "

tace "shine se yanzu zakafadamin? "

Yayi shiru taja tsoki ta haye sama segata tafito da gyale da car key da jaka tazo zata wuceshi tafita,

Yace "mommy kitafin musu da abinci don haryanzu Aisha bataci komi ba "

mommy ta harareshi tace "tunda safe ace haryanzu bataci komi ba kai miye amfaninka ne dabazaka zo kafadamin ba in ita hankalinta ya dauku wurin jinya? Mtsswww "taja tsoki tafara kwadawa jummai kira, jummai tazo dagudu mommy tace "kingama dinner? "

Jummai tace "a, a amma akwai abincin rana kuma cikin warmer yake "

Mommy tace "daukomunshi dasauri"

jummai takoma tadawo da kula mommy ta amsa ta fita tashiga mota tai asibity,

Fahad nanan zaune dafe da kai yarasa yazayayi neman mafita yaketayi daga karshe yatashi yakoma kofar gidansu faseelat har lokacin kulle gidan yake yaja tsoki yanajin kamar yayi kuka ya bar unguwar,


mommy nashiga wurinsu Aisha amira ta rungumeta tana hawaye tace "mommy kitafi dani gidanki banison gidan daddy "


mommy tace "yi hakuri princess dake zan tafi kinji ko? Ki kwantar da hankalinki "ta kwantar da amira jikinta,

ta kalli Aisha dake koje koje tace "meya sameta?"

Aisha ta girgiza kai tace "zamuyi maganar after"

Mommy tace "okay kidaure kici abinci ko kadanne fahad yace bakici komi ba "

Aisha tace "banajin yunwa ruwa kawai nakeso "


Mommy tace "kibude jug gashinan ki zuba tea kisha amira nasa aka hadomashi itama ki zubamata "


Aisha tace "baride na zuba mata kibata ni zanfita nasamo mana drinks a reception "

Ta zuba tamikawa mommy ta dauki kudi ajakar mommy tafita,


Mommy tayi tayi amira tasha amira taki sema tafara rigimar ita anty "mommy ni anty nakeson gani ki kaini wurin anty"mommy tai shiru tana tunani dan tagano akwai abinda ke faruwa,


Su hjy na zaune sukaji kukan jariri yanata inyarrrr inyarrrr, hawaye suka zubowa hjya, dukda jamila ta haihu bata bar kuka ba nurses sukace ko ciwo takeji wani wuri batace musu komi ba tacigaba da kuka sunata fada itako bata fasa kukanta ba, suka shirya baby nurse tafito wurin su hjya dauke dashi,

duk suka tashi tsaye hjya hannunta har rawa yake wurin son ta amshi yaron, ta amsheshi ta bude fuskarshi yaron sakkkkk khalil lokacin da yana jariri, hjy se kuka ita kuka siyama kuka, Allah assamad khalil yatafi khalil yadawo, nurse tai tsaye tana kallonsu ganin suduka suna kuka ta juya takoma ciki,

Baban farida na tsaye ya rike hannu,

bayan mintoci aka fito da jamila aka medata rest room, su hjya sukabi zuwa dakin,

Jamila na kwance tana ta kuka suka shigo hjya ta mikawa baban farida jaririn ta matsa tariko hannun jamila tace "kiyi hakuri jamila, Allah yafimu san khalil shiyasa yadauki abunsa, "

fuska jage jage da majina da hawaye jamila ta kalli hjya tace "hjy kema kin yarda ya mutu? Wlh be mutu ba yana raye yananan zuwa baze tafi yabarni ba "

Hjya ta share hawaye tace "kiyi hakuri jamila kowa seya tafi can"


jamila takara fashewa da kuka, ko sanin me ta haifa ma batayi ba, hjy tasa hannu tana share mata hawaye tana rarrashinta,

Baban farida besan lokacin da hawaye suka zubomishita gefen ido ba, duniya kenan gashide wanda suke fada kanshi ya rasu dukansu suna kukan rashi yasa hannu ya share,

ana haka mamanta suka iso ,jamila takara wage baki tana kuka, duk dauriyar zulai seda tayi kuka,


gaf Maghreb faseelat ta farfado tana nishi ,idonta arufe ta tuno abinda yafaru tabude ido dasauri hawaye na zubarmata ta dafa cikinta dake ciwo, hawaye masu zafi suka kara zubomata,

ummi ta dafata tace "sannu faseelat ya kikeji?"

Se sannan faseelat tasan su ummi na wurin ta juyar dakai ga ummi abba,omer abul ishak da Mubarak harda baaba matar baba babba,

hawaye na cigaba da zubomata murya dishe tace "ummi cikin ya zube ko? "

ummi tace "kiyi hakuri haka Allah yakaddara"

Faseelat ta juyar da kai tana hawaye ,tana tuno yadda fahad ya rikice yarika dukanta kamar ba mutum ba, yanzu shikenan cikin ya tafi,

Ummi takatse mata tunani tace "bari na temaka miki kisha tea kokadanne "

faseelat ta girgiza kai tace "nakoshi ummi bazan iya cin komi ba"

Ummi tace"kidaure ko kinsamu karfi "

faseelat ta girgiza kai, dukkansu suka matso suna mata sannu ta rumtse ido bata amsa suba,

she wonder yaakai takenan ina fahad yaakai baya nan se su ummi kawai mike faruwa ne? Karde........zuciyarta tabuga da karfi, ta bude ido tace "ummi ina fahad? "

ya omer dake gefe zuciyarshi nacigaba da tafasa saboda halin da take ciki jin tana nemenshi yasa yaja dogon tsoki ya fita daga dakin,

Ummi rai bace tace"wane fahad kuma ke yanzu dan kina dakikiya ya nakada maki shegen duka daga farkowarki kifara tambayarshi wlh sunan fahad yafita daga bakinki ko natashi nai tafiya ta "

faseelat na hawaye tace "ummi waya kawoni nan?dan Allah kufadamin yana ina "

Ummi taja tsoki zatai magana abba yace "Dan Allah kibarta zafin ciwo ne bawani abu ba, kibari tadawo hankalinta sannan "

ummi ta tabe baki, faseelat ta cigaba da hawaye zuciyarta na harbawa tarasa gane meke faruwa,




Maghreb tayi musa da yazo duba gonarshi daga babbar riga, besamu yaje gonar bama seda aka kusa Maghreb don ya samu hadarin da yafaru, yagama abunda yake ya na cikin tafiya zuwa wurin da yayi parking motarshi yaga mutum sheme sanbal straight akwance acikin ciyayi,

Ya matsa wurin khalil ba alamun ko rauni jikinshi ya zukunna ya fara duba shi,

kamar wanda yayi bacci khalil ya tashi zaune, yana salati ya jujjuya kai gabas da yamma kudu da arewa ,sannan yadafe goshi yana jin kuwwar mutane da salati da mutane sukai tayi lokacin accident din,

musa ya dafashi yace "bawan Allah mekake anan yanzu da daddare? "

khalil idanunshi jawur zuciyarshi sanyaye yace "bansan yaakai nazo nan ba, nide nasan muna cikin mota, wata mota tahawo tamu daganan bazan iya tuna komi ba"

Musa yaja kabbara "Allahu akbar ,Allah me yadda yaso dama akwai ran da yafita a motocin can abun alajabi, bawan Allah lalle Allah nasonka daya barka da rai har zuwa yanzu domin acikin motocin bawanda ya fita duk sun kone "


khalil ya dago arazane, mutumen yace "eh duk sun mutu kaima ina mamakin ganin ka anan tunda yayi nisa da inda hadarin yafaru "

khalil yace "jinake kamar nayi bacci na farka amma nasan bakomi ne yasa Allah yatsareni ba se don yawan ambatonshi da nake kuma nakasance me kiyaye dokokinshi "

Musa yace "hakika wannan ba abun mamaki bane don ikon Allah yawuce mamaki azamanin manzon Allah (S. A. W) wata unguwa takama da wuta duk gidajen suka kone daakazo akafada ma sahabin daya daga cikin mutanen unguwar se ya karyata yace wlh banda gidana saboda bana fitowa gida harse nayi adduar da manzo ya koyar damu (fans namanta adduar) kuma ana zuwa akaga gidanshi lpya lau amma duk nakusa dashi akone,"

Ya cigaba da cewa" nan kusa akwai wani abokin mahaifina shide yakasance kullum baya manta karanta ayoyin karshen suratul tauba, lakadjaakum sau 7 koda yana tafiya yakan karanta ta koda besamu yin kowane azkhar ba yanayin wannan, se wani amininshi ya kawo mashi ziyara daga sudan shikuma abokin mahaifin nawa yana zaune a kaduna, bayan ya kwana se suka shirya suka nufi abuja don ziyarar abukkansu, tareda driver suke amma se abokin mahaifina yaamshi driving, kasancewar beiya dogon driving yake fara bacci suna cikin tafiya yafara gyangyadi dole yadawo gidan baya ya kwanta amininshi da driver suna gaba, baadade ba bacci ya daukeshi,yana bacci sukai accident koda yafarka sede yaganshi yashe a gefen titi mutane suna zagaye dashi bako kwarzane jikinshi, seyafada musu suna tare da yanuwanshi a mota, daaka bi daji ashe motar yankar daji tai taita tafiya tayi raga raga driver ya mutu yana ciki yayi jina jina, hankalinshi yatashi aka dukufa neman amininshi baagano amininshi ba se da akai tafiyar kilometers 25 sannan akaganshi kwance a mace cikin kungurmin daji, ya kidima sosai abun yabawa mutane mamaki, a kd akai janaizar amininshi da driver ana zaman gaisuwa wanda ina daga cikin wadanda ke gun anata jajanta lamarin sewani malami yake tambayar shi wace addua yayi ayau seyace "wlh ban karanta komi ba se lakadjaakum kafa 7 wanda kuma a riyadul janna nasamu falalarta hadisin da yakawota a rauda ta 18 ankarbo hadisin ne daga Muhammad bn abubakar cewa wanda ya lazimci karanta lakadjaakum ila akirul sura lam ya mut hadman wala garqan wala harkan wala darban hadid,shine na lazimceta kowane lokaci "

,malamin yace"hakika karshen suratul tauba kariya ce daga dukkan abun ki, nima zankara dukufa wurin yinta "


Musa ya cigaba dacewa daganan sena rike ta inayi danaji falalarta ,ban wata biyu da riketa ba zanje Lagos motar mu ta kife karamar macapolo ce amma bawanda ya fita seni nima cikin jini nake domin naji ciwo sosai "ya bude kafarshi zuwa bakin gwiwa wani katon tabo ya bayyana harda rami ajiki yace "kaga tabon da yakasa bacewa daga cikin tabunnan danayi a kalla anyi shekara biyar amma har yanzu be cike ba sede ina tafiya da kafata lpy lau duk dan temakon Allah "(it's true life story ya faru dagaske)

khalil yace"ina yawan karantata domin tana daga cikin jerin azkhar dake cikin littafi na sede bansan falalarta ba, hakika nagode ma Allah daya kareni domin koda mutuwa hutuce aguna zanso nakara rayuwa dan nakara aikata aikin alheri ,inada mahaifiya ita kadai ta ragemin inason na rayu har zuwa tsufanta zuwa lokacin da zata kasa yiwa kanta komi yazama nine me mata hidima don samun rahmar ubangiji da albarkarta dafatan Allah yabani wanda zemin haka nima"


musa yace "Allah ya yarda wane gari kake zan temaka maka nakaika duk da dare yayi "

khalil yace "cikin katsina nake idan har zaka temaka mun ba gida nakeso kakaini ba, don ina samun matsala da matata da mahaifiyata nasan in sukaji labarin mutuwa ta zasu saduda mahaifiyata zata sauko domin tana sona sonda takemin ne yayi yawa haryake kawo mana matsala take kishi da matata kamar kishiyarta, inso samu ne zanso na zama bakonka nawani lokaci sannan zan koma garinmu "

Musa yace "ba matsala nima zanso nasamu ladar bakuntarka, na tausaya maka Allah ya ganar da mahaifiyarka"



Khalil yace "amin nagode Allah ya baka ladar "

musa yace"amin ni sunana musa ina zaune babbar riga da matata da yara na uku "

khalil yace "ni sunana khalil ina zaune a layout matata yarinya ce aurenmu beyi shekara ba"

musa yace "masha Allah Allah yabada zuria dayyiba zamu iya tafiya "

khalil yatashi suka nufi motar musa suka shiga suka kama hanyar babbar ruga batareda kowa yasan khalil na raye ba.



ya Allah kajikan musulmai maza da mata ka musu rahma πŸ‘πŸΌ


*zakuji inata yiwa mamatanmu addua wata falala naji daga bakin sheikh daurawa cewa duk wanda ya nemawa muminai gafara zaarubuta masa lada adadin musulman da suka mutun , dukda de inayi akowace sallata domin nikan tuno da yanuwana da abokaina da suka rasu, to jiya kuma hatsarin nan yakara tadamin hankali har natuno garabasar nan shine nace bari nafada maku nasan akwai wadanda basu sani ba se sufarayi, Allah kakaramana ilimi*
➰➰➰➰➰
*RAGGON MIJI*
➰➰➰➰➰








By





*MAMAN MAMY*
*(SHALELE)*






✍🏽✍🏽 *GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION*✍🏽✍🏽✍🏽

We are bearer's of so golden a penπŸ–Š
We write assidiously perceiven no pain
So magical
Our creative golden penπŸ–Š
Be hold our words
A product of our penπŸ–Š
Savour our words
For it will cause you no pain.✍🏽


https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/





7⃣3⃣





*shafin nakine AISHA ALTO writer of SANA'ACE,da begenki arai na nayi typing inafatan zakiji dadin page dinnan nakine ke kadai uwargidan fahad🀣*



Har suka isa babbar ruga bawanda yace uffan dukkansu suna tunani daban, a kofar wani karamin gida suka tsaya duk suka fito waje, musa ya kalli khalil yace "nan shine gida na,muna zaune ne tareda mahaifiya ta "

Khalil yayi shiru yana tsaye musa ya shiga gida ba dadewa ya fito bakin gidan akwai kofar wani daki yasa key ya bude dakin yashiga few minutes yafito yacewa khalil "bismillah"

Khalil ya karasa ciki dakine karami da toilet aciki bakomai ciki se katifa da praying mat musa yace "nan shine masaukinka duk abinda kake bukata kamin magana "

Khalil yace "nagode sosai Allah yabaka ladar"

Musa yace "amin "ya juya ya fita,

Da fitarshi khalil yashiga toilet yayo alwala ya dawo ya shimfida carpet ya tada sallar laasar da Maghreb ,yana sallar yana hawaye yana tuno mutanen da suke tare a mota dukda shi yana gaba amma a bayanshi yanajin wata mata na waya tanafadin Sun kusa karasowa abata minty 10 kawai, da danta ahannu yanata kuka,sanda yagama sallar addua yayi ta masu akan Allah yajikansu ya musu rahma ,

Aisha ta dawo da drinks a leda tazauna tabude kwalin happy hour tadansha ta aje sauran, har lokacin amira tana ta kiran anty,

Mommy ta kalli Aisha tace "wai ina antin tata ita bazata zo dubata bane? "

Aisha ta yamutsa fuska tace "itama bata lpy tananan asibitin akwance "

Mommy tace "mtswww meyasa meta ne ita kuma? "

Aisha tace "I don't know me tamishi yayita jibgar ta ina shiga dakin na ganta cikin jini inaga tayi miscarriage abinda ya tsorata amira kenan har ta suma "

Mommy tace "amma naji dadi shegiya Allah yakara

Aisha ta girgiza kai ta nunamata amira da ido, mommy tai shiru,

amira tace "nide kukaini wurin anty inason naganta "

mommy tace "to zan kaiki wurinta kisha tea nikuma sena kaiki "ta dorawa amira cup,

Amira ta dan sha ta janye fuska,

mommy ta kalli Aisha tace "bari naje naga likitan inda yiwuwa se mukoma gida seya cigaba da zuwa yana dubata acan kamin ta warware "

Aisha tace "to "

Mommy ta dauki amira suka tafi office din doctor, ta zauna ta mishi magana yace ba matsala zasuiya tafiya mommy tai payment suka koma dakin, Aisha ta tashi suka shiga mota suka nufi gidan mommy,

Kafin su isa amira tai bacci suna zuwa mommy ta kwantar daita Aisha kuma tashiga toilet ta watsa ruwa,


Hawaye faseelat taketa yi don ma batada karfin yin kuka ,

ummi tagaji tace "shin ce miki akai ya mutu komi?"

faseelat tace "toyana ina?"

ummi tace "yananan zuwa ki kwantar da hankalinki "

Sannan tai shiru tana ta son taganshi don tsoro take karde sakinta yayi ,

Suna haka omer yashigo dakin faseelat tai sauri ta kulle ido, badan yadena jin takaici ba yace "faseelat ya jikinki? "

tai shiru saboda kunya dama he warned her amma bataji ba ga abinda yake gujewar yazo yana faruwa,haka akai ga auren khalil bata dauki shawararshi ba abinda yazatan kuma shi yafaru,

Ummi tace mishi "jiki kam aiba sauki kana ganin yadda take a kumbure, sonake jinin nan yakare in kamata in dan gasa mata jikin kotaji dama "


Omer yace "Allah ya sawwake "


Gidan sabeer fahad ya nufa yana parking yafito ya nufi gun sabeer dake waya da fatouma, sabeer naganinshi yace wa fatouma "pretty ga kanenki nan yazo bari nayi attending dinshi I will call you back"

yakashe kiran ya kalli fahad da yazauna a seat ya dafe kai ,sabeer yace "lpy de fahad naganka haka Very tensed? "

Fahad ya dago fuskarshi da tayi jawur yace "ina cikin tashin hankali sabeer kabani shawara plss "

sabeer yace "inajinka"

Fahad ya furzar da iska shikanshi haushin kanshi yakeji yace "something bad happened, kishi ya rufemin ido na doki faseelat hartayi miscarriage after I took her to hospital..."

sabeer yakatse shi yana fada "kana cikin hankalin ka kuwa? wane irin kishi ne da zesa ka bugi matarka har tayi bari? haba dude sekace baka waye ba ga hanyoyi nan birjik da zakai punishing nata seka tsaya ga duka saboda kajawa kanka raini agunta da iyayenta?"

Fahad ya dagamai hannu yace "please karka ce zakamin fada banzo wurinka don ka karamin tension ba nazo ne kafadamin mafita,in kuma fada zakamin sena tashi nai tafiya ta kobari bakai ba nakai numfashina ba "

sabeer yaja tsoki yace "badole nai masifa ba karika abu like mad person yanzu inajinka "

Shima fahad yaja tsokin bacin yana neman mafita da tafiyarshi zeyi, ya cigaba da cewa "after na kaita asibity nafita in duba princess dabata lpy se dawowa nai na tarar batanan yanuwanta sun dauketa naje gidansu many times a kulle "

sabeer yace"wow sunyi dede dasuka dauke diyarsu, kai kana tunanin kamar Aisha ce da kake jibga son rai dan tana kanwar ka? to yanzu de kaga da banbanci, seka jira hukuncin da zasu yanke "

fahad da tundazu yake kallon sabeer kamar ya kaimishi naushi, ya hadiye miyon bakin ciki yace "u r very stupid da kake tunanin ina hada Aisha da faseelat kowace da matsayinta in Kana bani shawara kabani in bazaka bayarba senai tafiya ta "

Sabeer ya janye hannunshi da yadora kan fuska yarage murya yace "gaskiya baka kyauta ba duk son da yarinyar nan ta nuna maka amma har kaiya mata haka "

fahad yace "I known, ya zanyi yanzu they took her bansan ina suka kaita ba nikuma inason ganinta inason sanin halin da take ciki "

Sabeer yace "dole kayi hakuri kaita zuwa har kasamu ganin mahaifinta kabashi hakuri sosai kila su hakura , don inajin tsoron kar su rabaku, saboda diyarsu tana da komai dahar wanda yafika zata iya aura "

Fahad ya dafe goshi yace "bazan iya rayuwa babu ita ba, she's my life, I'm regretting bazan iya bacci ba batare da nasan halinda take ciki ba ,ina son sanin halin da take ciki "se hawaye sharr sharrr

sabeer ya dafashi yace "kayi hakuri kabi komai asannu faseelat takace,ka kwantar da hankalinka kacigaba da zuwa gidannasu har kasamu ganin abban nasu sede sekayi hakuri bazan boyemaka ba duk mutuncin da suke ganinka dashi yanzu babushi "

fahad yayi shiru yana tunanin yadda ze tunkari abban nasu,

sabeer yace "amma dan Allah ka rika kiyayewa,karage kishinnan karika hadiye shi don gudun nadama "

Fahad ya share hawayenshi yace "thank you, nagode "ya tashi ya shiga motarshi yabar gidan,

Sabeer yabi bayanshi da kallo ya girgiza kai,


har bayan isha seda fahad yaje gidan har lokacin yana rufe, yajuya yanufi asibity yanaganin basanan yayi tunanin an sallame su ya nufi gida,


faseelat na nan tazuba ido jiran hero shiru babushi,hankalinta duk yatashi ,jinin na karewa ummi ta jona heater ta kamata suka shiga toilet, ta temaka mata ta tube se lokacin ummi taga tashin hankali jikinta duk bakin tabo ne ga kumburi da tayi, ummi takara hawa fiyeda baya, ta gasa ta tai mata wanka ta sauya mata kaya sannan takamata suka fito,

faseelat ta kwanta tana meda numfashi, ba dadewa abba yashigo da maltina da madara aka hadamata ,ummi ta tadata tabata don dole tasha sannan ummi ta kwantar daita ,

ummi ta kalli su abul da tundazu suna asibitin kamar masu azumi tace "yakamata ku tafi gida hakanan har tara tawuce"


Suka fita jikinsu a mace, ya omer ma ya masu seda safe yafita,
Ummi ta kalli baaba tace "baaba yakamata kitafi gida kihuta kema "

baaba tace "to Allah yakara lpy bari natafi "

ummi tace "a, a kijira alhaji ya kaiki "

abba yace "to inde ana bukatar wani abu ki kirani"

ummi tace "to insha Allah "

Abba yafita baaba tabi bayanshi yana cikin tafiya baba babba yakira ya dauka bayan sun gaisa,baba babba yace"ya me jikin?"

abba yace "dasauki zaace"

baba babba yace "Allah yabata lpy, da Allah ko mijinta yazo karka saurare shi ,ya saketa kawai "

abba yace "to Allah yasa haka shine mafi alheri"

Baba babba yace "amin"sukai sallama,

abba na ajiye baaba ya wuce gida,



fahad na zuwa gida besamu su Aisha ba yajuya ya nufi gidan mommy, yana zuwa ya zauna a kujera ya kwantar da kai jiki kanshi na mugun ciwo,

mommy tafito daga kitchen taganshi tabata rai tazo ta zauna, tace "yanzu fahad rayuwar da kazabar wa kanka kenan? matanka kamedasu kamar jakkai kaita bugunsu kamar dabbobi? "

Fahad hannunshi akanshi yace "mommy it's a mistake baason raina nayi ba "

mommy tace "idan de zakai hankali kayi idan kana dukan Aisha nayi shiru ita wagga iyayenta ba shiru zasu yi ba "

tatashi zata haye sama murya sanyaye yace "ina Aisha? "

mommy tace "tayi bacci katafi kawai gobe kazo ka dauketa, ita kuma amira anan zata zauna tunda kagama tsorata ta"
Ta juya ta hayewarta,

Fahad ya tashi yabar gidan, yakoma gida ruwa kadai ya iya sha ya shiga dakin faseelat yayi kwance kan bed dinta yanajin kewarta sosai, ya tashi ya bude wardrobe dinta ya dauko sleeping dress dinta ya rungume a kirji yana hawaye,


gidansu umma ma duk basu cikin walwala har 10 tayi umma taji bata iya bacci ta tashi ta nufi dakin lady, Lady na waya da Hussein dasuke matukar son juna yanzu, umma ta shigo lady takashe kiran ta meda hankalinta kan umma,

Murya sanyaye Umma tace"waikinsan gidansu faseelat ne? "

lady tace "eh nasani"

umma taji dadi tace "yawwa kitashi kisa hijab can zamuje yanzu bari naje na dauko mayafi na"

ta juya tabar dakin, Lady ta tashi ta dora after akan kayan baccinta tafito, umma tafadawa daddy suka tafi gidansu faseelat,

suna zuwa sukai parking suka fito suka tsaya bakin kofa sunata knocking, can zuwa abulkhair ya bude gidan unguwar dun dum dan babu nepa, sede hasken farin wata,yagade mata ne yayi tunanin kawayen ummi ne,

abul yace "inawuni "

Umma tace "lpy lau ya me jiki an sallamosu ne"


yace "dasauki suna asibity "

umma tace "wace asibity suke room nawa? "


Yace "turai, aminity ward room 9"


umma tace "to nagode sosai "ta kalli lady tace "mutafi asibitin "

suka juya suka tafi abul yameda gida ya rufe,

akan hanya suka sai kaza me dawafi da drinks suka tafi asibitin,

Bawani wahala suka gane dakin suka tura suka shiga da sallama bakinsu, ummi kadaice ta rage itama tana salla, da lady da umma hankalinsu bakaramin tashi yayi ba ganin halin da faseelat ke ciki,

idon faseelat akulle umma takarasa kan bed din dasauri tana kara ganin barnar da danta yayi,

jin kamshi na daban faseelat ta bude ido taga umma, tafara hawaye,

Umma tace "sannu faseelat Allah yabaki lpy"

Faseelat tariko hannun umma murya shake tace "umma! ya sakeni ko? "

umma tace"me kike cewa ne? Yazaai fahad ya iya sakinki yana sonki sosai baze iya rabuwa dake ba "

Tace "ban ganshi ba har yanzu bezo wurina ba, Dan Allah umma kikiramin shi inason ganinshi "

Umma tace "ki kwantar da hankalinki yananan zezo "tasa hannu tana share mata hawaye,

ummi da tundazu ta sallame tai shiru tana kallon gadon da faseelat ke kwance tanajin takaici kamar me,

lady ta matsa tace "sannu anty "

faseelat ta daga mata kai tana cigaba da hawaye,

ummi ta tashi tana linke carpet tace "sannunku da zuwa "

umma ta juya wurinta tace "ina wuni yame jiki Allah yabata lpy"

ummi tace "amin "

Itama lady ta gaida ummi, shiru dakin nawani lokaci sannan umma tace "Dan Allah ummi kuyi hakuri akan abinda fahad yayi baa cikin hayyacin shi yayi haka ba, shi kanshi yana cikin tashin hankali don koda yazomun da labarin kuka yakeyi ,nasan yanacan

Please Login or Register in order to submit comment