Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

batai bacci ba don jitakeyi kamar ta shiga ta sheka musu ruwa tafasassu, haka suka rika rayuwar kowace batason girkin yaruwarta yazo, sede bawani fada tsakaninsu kuma bawata jituwa tsakanin su,


khalil ko yana kan hanyar zuwa batsari kusan duk bayan kwana biyu itama hajiya tana lekawa ,kuma yakaita tawa musa godiya wanda se kawance ya kullu tsakanin mahaifiyar musan daita har suna kaiwa juna ziyara, jamila da lil khalil sunata shan wanka, inda zulai keta hada diyarta,

Yanzu inkaga khalil sam bazaka ganeshi ba gayu yakeci sosai ga hada to match color dinkunansa dede komai neat ,


acan niger fadila tayi missing ya omer sosai harta kwanta rashin lpy, yau gidan bakowa yara na islamiya da marece amma tafita suna baba babba yadawo yanufi dakinsu dubota da jiki yaji tana waya tana kuka,

Tana daga kwance "yaya omer Dan Allah kazo inbakazo ba bazan warke ba wlh kewarka ce tamin yawa ni inason ganinka kataho"

acan bangaren omer duk hankalinshi ya tashi jin masoyiya ba lpya yace "inanan zuwa my angel amma kirika cin abinci plsss inanan tafe gobe"

ta rage kukan tace "dagaske? "

Yace "eh inanan tafe nikaina in banzo naganki ba, ciwon zan kwanta"

Tace "thank you I love you yaya "

Yace "love you too angel"

Da marece ne gidan tsit kuma wayar ta nada volume har abinda yaya omer kecewa yaji, yajuya yakoma daki yanata girgiza kai yanzu de zamani ya sauya yara ba kunya kokadan soyayya Sun dauketa kamar rayuwa,

yanata tunani ya ciro waya a aljihu yakira abba abba ya dauka suka gaisa baba babba yace "ku shirya biki nanda 2wks don nabawa omer fadila nabashi ita kyauta zan mata lefe zan biya sadaki saboda naga dukkansu suna son junansu "

abba Farin ciki kamar me yayi ta godiya, sannan sukai bankwana yana sauri yaje yafadawa ummi taita murna shima ya omer da yaji Allah kadai yasan iya farin cikin da yashiga, yakira ta yafada mata segashi ta mike ta nemi ciwon tarasa ,

Daganan akafara shirye shiryen biki gidan da fahad yabasu me upstairs shi zasu zauna ciki abba yace yabashi kyauta, faseelat ma bakaramin dadi taji ba,

yanzu fahad dasauki don yana barinta fita ammafa don yazama dole ne,

Million daya fahad yaba omer gudumuwa yabasu abba da baba babba 500 thousands saboda bayada kudin sosai dan tunda yabiya kudaden nan account dinshi yayi low,

faseelat ma 500thousands taba kowa cikinsu kuma tadauki nauyin dinner dinsu sede fafir fahad yace banda ita ciki,

After 2weeks aka daura aure ran Friday Omer da Fadila Baffa da waseela,danrana daya bikin yakama,

da daddare faseelat ta kira omer a kofar gida don gidan be shiguwa saboda jamaa ,tabashi wani abu anyi rafin tana dariya tace "yaya kabawa fadila gobe da safe amma fa ba kyauta ta bace takace kuma karka buda ita zata buda "

yayi murmushi ya amsa yace "thanks sister"

Yatafi aka kai amarya kowa yatafi, omer ba dagin kafa suna gama salloli ya haye fadila yayita dirza tayi zam kunsan matan Niger bade dadi ba πŸ˜‚πŸ™ˆdon sunsan kayan mata sosai kuma Sun nakalcesu,

da yake miskili ne na karshe kodan ihunnan beba gum yake sede nishi 😬amma hakan behana shi bayan sungama ya rungumeta yana rarrashi ba, dakyar yashawo kanta ta hakura tai shiru ya kaita toilet ya gasa abinshi ,suka dawo suka kwanta Like da juna, dasafe yabata kyautar tana murna tabude dalleliyar waya iPhone 7+ ta rungumeshi tana murna da godiya, shima kallon wayar yayi tayi yana kara kaunar yaruwarshi.

bangaren su lady kuwa lokacin da Hussein yazo yataho da Hassan nashi da friend dinshi sutayashi fira, Hassan ya likewa safiyya abokinshi Rayyan yace umma salma ta mishi dukda de bata wani girma ba,

Fahad da yafadawa umma tace banda salma kiri kiri salma tace tanasonshi, daddy da kanshi ya tafi Egypt yakarayin bincike da temakon fahad, komi lpy lau sede rayyan nada mata kuma ko 1yr basuyi da aure ba, salma tace tanaso ahaka akasa biki nanda 1month,


yau amira nadawo wa school tafadawa faseelat zasu fara exam ran Monday, Aisha nakoya ma amira karatu don tanayin na 2,,3 '''4 wannan karan ta tare wurin faseelat ganin faseelat din nabakin kokarinta wurin koyamata yasa ta kyaleta, seda faseelat tai mata revision kaf karatun term din wani lokaci har 10 suke kaiwa sunayin karatun sannan su kwanta,

Amira nada kokari sosai tana fahimtar karatu musamman da faseelat ke mata da dubara anayi ana danyin abun dariya,


wannan yasa da akazo exam tayi kokari da akazo certificate itace tai na daya a class dinsu cikinsu 25 cifff ,

makarantarsu *salama Islamic institution* duk bayan week da Hutu sunayin speech and price given day wanda ake tara manyan mutane kasancewar me school din attajiri sosai kuma me suna,akanyi debate da yar drama a nishadantar da baki da iyayen yara da yaran su kansu, yadda sukeyi a debate yara zalla keyi don abun yafi kayatarwa a drama kau manya da yara, awannan karan harda amira cikin masu debate saboda takara wayo da kokari,

faseelat jitake kamar ita zatai debate din ta dage yi mata harta hardace sannan takoya mata yadda zatai movement awurin,

bayan hutu da kwana ukku sukaje sukayi rehearsal aka dauka harda amira itada wata se kuma maza yara biyu topic din shine *female education is more benefits and important than male education* malamin yakara koya musu da gyara musu inda ke bukatar gyara,

kowa ze sanya uniform amma su devators zasu saka personal school ce ke basu kaya masu kayatarwa su saka, akabawa amira white gownt gabanta ya dan dage baya ya zulbo da pink ta kalma partner dinta kuma black riga da red takalmi, mazan kuma jeans da riga daya yellow riga white jeans daya black jeans red riga, bayan da Akagama musu akameda kowa gida se kuma ranar speech din nanda 4 days ran weekend Saturday ,

amira tayi mugun hardace debate nata yazamar mata jiki,

faseelat ta kaita akamata saloon aka gyara mata kai akamata henna red color,

Kwanan Aisha ne gobe kuma 7 zasu fita suna dinner faseelat tace "hero gobe zan kai amira school "batareda yagane nufinta zataje attending din taron ba yace "Allah yakaimu "

Da safe dukkansu da amira da faseelat da murna sukatashi sunata shiri, shiko fahad yanacan Like da Aisha dan jiya basuyi barci ba dan ta rikitashi sunata bacci,

faseelat tawa amira wanka sunata labari tai mata kwalliya tasa mata gown dinta tai mata styling gashi wani ya kwanto a goshi sauran nabaya anyi parking da pink ribbon agaban gashin ta lika mata white clip me kwalliya white color yanata walkiya tasamata shoes dinta hills, tafeshe ta da turare,


Itakuma tasa material lace orange da kwalliyar baki jikinshi tasa black hijab har kasa lokacin 7 faseelat ta zauna amira tayi rehearsal agabanta gwanin shaawa faseelat ta rungumeta tanacewa "bravo dear haka zakiyi kamar yadda kikayi anan"

amira tadaga kai tana murmushi suka fita 7:30 suna cikin school din amma harsun samu mutane sosai faseelat taje tasamu gaba ta zauna amira kuma uncle dinsu yajata suka kara reahasal ,

8:30 speaker na school din yafara bude taro da addua,

mutane cike harda gwamna masari da matarshi, hjy bilkisu ministan ilimi ta jihar deputy gwamno da manyan masu mukamai da yan kasuwa,


bayan addua yafara yin godiya akan wadanda suka halarci wurin sannan wasu daga cikin malamai suka amsa speaker sukaiwa manyan baki welcoming sannan suka koma suka zauna,

Speaker ya amsa yace "as we all known in every speech and price given day some of the young students use to entertain and educate us with there debates ,it's like that today we have 4 debators 2girls,and 2boys the topic is female education is more important and benefits than male education ,our first debater is just 5yrs old ,ladies and gentlemen let's welcome amira fahad on the stage"

amira ta taho tana tako ta hau stage rap rap akadau tafi masu hoto na dauka masu vedio nayi abun burgewar ana kallon shirin live a nta news 24 da TVC news, Channel TV,,

kowa kwalliyarta kadai ta burgeshi kowa "wow, wow!! Beautiful girl,cutie etc "

Ba bata lokaci aka bawa amira speaker ta amsa ta Kalli faseelat dake gaba faseelat tai mata haka πŸ‘πŸ»da hannu, amira tasaki murmushi tafara

"before I proceed to.........






kubiyoni next page muji debate din amiraπŸ’ƒπŸΌ
➰➰➰➰➰
*RAGGON MIJI*
➰➰➰➰➰







By






*MAMAN MAMY*
*(SHALELE)*





✍🏽✍🏽 *GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION*✍🏽✍🏽✍🏽

We are bearer's of so golden a penπŸ–Š
We write assidiously perceiven no pain
So magical
Our creative golden penπŸ–Š
Be hold our words
A product of our penπŸ–Š
Savour our words
For it will cause you no pain.✍🏽


https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/





8⃣0⃣





*Manzon Allah (S. A. W) yace kurika nemawa yayanku tsari awurin Allah ga dukkan abunki,yakan dora hannu akan hassan da Hussein ya musu wannan adduar*πŸ‘‡πŸΌ

*U'IZUKUM BI KALIMATULLAHI TAMMAT MIN KULLI SHAIDANIN WA HAMMA WAMIN KULLI AININ LAMMA*
bukhari da Muslim


Fassara


*ina neman maku tsarin Allah da ayoyinsa gabadaya, daga dukkan shedani da abun cutarwa da kuma dukkan masu kambun baka*






"Before I proceed to my proceeding procedure, I will like to give honour to whom honour due to, by the acknowledgement of Mr. Chairman sir, the moderatore, Accurate time keeper, Distinguished,guest, ladies and gentlemen. Good day to you all.
My name is amira fahad, I stand here strongly to support the motion which state that; female education is better than male education.

First of all I will start with the saying of Prophet Muhammad (S. A. W) the truthful and truth worthy that said educating a single female is like educating the whole society,

What's education? education : is the basic terms of facilitating, learning, and acquisation of knowledge, skills, values, beleives, and habit.
Who is female?
Female: is the basic terms applied to member of sex that is biologically Distinguished from male.

With my following point, I want convince you, and for u to support and beleives my statement.
1_Improve health: educated girl or women are aware of the important of health and hygiene. Through health education there are aim to lead a health style.
Educated mother can take better care of both her self and her children.
2_Economic development and prosperity: education will empowered women to come forward and to contribute toward development and prosperity of the country.
3_Improved life: education helps a woman to live a good life. Her identity as an individual will never get lost. She can read and learn about her right. So our mother right will not get trodden down. The life or condition of women will improved alot, if we take a broad out look in the field of female education.
4_Diginity and honour: Educated women are now looked upon with diginity and honour they become a source of inspiration for millions of people (male and female) who make them their role models.
5_Justice: educated women are more informed of their right for justice, it would eventually lead to decline in instances of violent and injustice against women such as dowry, forced_prostitution, child marriage and female foeticide e.t.c.
6_Choice to choose a profession of her choice: educated women can prove be highly successful in the field of life. A girl child should get equal opportunity for education, so that she can plan to become successful doctor, engineer, nurse, air hostesses, cook, or choose a profession of her choice.
In this point I have question to ask, and I'm sorry for asking a such, Mr. Chairman sir will you be happy if your wife handed to a male doctor during birth to Take care of her?.
7_Elevate poverty: Women education is a pre_requisite to elevate poverty. We need to take equal durdel of the massive task of eliminating poverty. This would demand massive contribution from educated women. Their can't be match social and economic changes, unless girl and women are given their right for education.
A bonus Question for listeners: Will you give your child, wife, sister, fiancy( your wife to be) a right for education?

IN Conclusion: until the middle of nineteenth century girls and women were educated only for traditional house hold works, now society is witnessing certain some changes in the role status of women. There is greater emphasis on educating girls and women more than we educate boys and men.
Thank you all, for listening.

Tanayin abunne not that too fast amma da dansauri irin na kwarewar nan domin cikin 4mnt tagama, da muryarta me zaki ta yara tana dan yin bayani da hannu sannan tana yawo a stage din,

tana gamawa rap rap akadau tafi dama tuntanayi wasu ke dariya tayi masifar burgesu,

Takoma ta zauna, a gaba kusa da sauran debaters din,

speaker yakira sauran sukayi performing amma na amira is the best kuma tafi daukar hankali,

Acan gida su fahad suntashi sungama break suka koma falo Aisha ta kunna nta news 24 suna kallon taron,

Basu samu debate din amira daga farko ba amma ta burgesu fahad yakara rungume Aisha dake kan cinyarshi, ganin yadda take abun gwanin burgewa,

sam fahad besan faseelat bata gida ba don yanzu be cika shiga dakinta ba inba girkinta bane,


Aka kira sauran yara sukayi drama itama ta nuna amfanin ilimin macen ta yadda suka gabatar gida biyu ne daya me ilimi mijinta babu, Dayan gidan mijin me ilimi ita kuma babu ,segashi duk da mijin me ilimi yana bakin kokarinsa amma cikin yaran akwai masu shaye shaye da wadanda basuiya komai ba, itako gidan me ilimi yaranta tsaf domin kullum tana kula da karatunsu da tarbiyarsu,abunde yabada maana ankuma sha dariyar tabarar gidan namijin da yayanshi da matar,

Bayan nan aka kira amira akabata kyautar su dansu suka cinye ta amsa sannan suma opposing aka basu donsuma sun kokarta,

se akafara bada kyautar position and other things , har akazo class dinsu amira, itace tasamu kyautar best mark in Islamic and kuran itace the best awurin tsafta itace tai na daya itace tafi duk mates nata iya speak in English saboda yawo da sukai kasashe ,

Speaker yace "and we have amira fahad the best in English in Islamic and kuran, the neatest student and she take the first position in there class ,amira fahad! "ya kira sunanta,

amira tatashi ta hau step cabb gift 5 jere ringisss aka mika mata ta amsa tana murmushi anata daukar vedios da pic, duk wanda akabawa kyauta yakanyi godiya sannan yawuce,

Akabawa amira speaker da murmushi fuskarta ta kalli faseelat daketa jindadi tanajin dama diyarta ce amira, tace "Thank you all I'm very happy to have all this gifts but I don't deserve them, my step-mom is behind all my success she use to teach me after school, encourage me supporting me and give me all her time she love me so much ,she's the one that deserve them I want to donate all the gift to her as my gratitude ,thank you anty I love you "

mutanen wurin sunata kallonta da burgewa su na dariya,

Agida ko fahad yakara baza ido shida Aisha ko kishi kamar tajawota ta kulle bakin,

speaker ya amshi speakar yana murmushi yace "we invite her stepmother to come on the stage "

faseelat da tundazu take murmushi tana ware ido jin ankirata ta mike, masu vedios suka koma haskota,

fahad ya kalli Aisha da itama ta cika tai famm yace "dama faseelat bata gidannan waya bata izinin fita?"

Aisha da tacika da bakin ciki tace "yazaai nasani"

ranshi bace ya meda kallo gun TV din, sunata haskota har takai kan stage,

Amira ta mika mata gifts din da aka jera wuri daya, faseelat ta amsa tana kayataccen murmushi amira ta rungumeta,

mutanen wuri akadau tafi rap rap rap, masu hoto nata kara dallasu anata nuno su,

fahad ya janye Aisha ya mike tsaye yanajin balain kishi, kamar yaje ya jawota yace "faseelat nada hankali kuwa? "

Yafara zagayar falo, Aisha ma jira take amira ta dawo,

sannan su amira suka sauka daga stage din akaita bawa sauran yara kyautukansu,

Amira na rungume jikin faseelat dandanan an hasko gunsu wannan ke karawa zuciyar fahad wuta,

Har akagama basu kyautukan, sannan hjy bilkisu ta amshi speaker tai magana akan yadda abun ya burgeta kuma duk yaran sunyi kokari ta kuma yiwa amira kyautar 50k saboda ta burgeta ta kuma jinjina wa faseelat,
Me magana da bakin gwamna ya amsa yayi nashi jawabin ya kuma yiwa faseelat kyautar mota da kuma biyan school fees na ta harta gama school din,

fahad kamar yashako shi yakeji,

manyan mutane sunyiwa school din kyauta da kuma amira kusan 2millions tasamu,

Sannan akai addua akatashi nan kuma akafara daukar hotuna da yaran school din,

faseelat tasha hotuna da iyayen yara da wanda suka halacci taron harda mata manya sunata yaba mata kuma innace maku bakinta ya rufu bazaku yardaba ,

tuni akadauke hasko taron fahad kamar ya samesu can yanata zagayar falo rai bace, shiru shiru basu dawo ba,

Seda sukasha hotunansu sannan suka shiga mota faseelat na driving tanayi tana kallon amira tana murmushi tace "thank you daughter nagode da kyauta "dukda de na amira ne dan kyaututtukan daga text books da kudi computer yara da kuma digital kuran alkalam se kuma sabbin set na uniform gadagal taji dadin karayin fresh, jin dadin faseelat kawai yadda takirata da kalamanta,

amira tace "anty bansan irin son da nake miki ba inasonki sosai "

faseelat tace "thank you dear I love you too "

Se 12:30 suka isa gida Suna shiga gida suka fito suna murna ta kwashi gifts din ta bude kofa amira dagudu tai ciki ,

fahad dake tsaye yanata raba ido ya bita da kallon takaici taje ta haye Aisha,

faseelat na shigowa faraar fuskarta ta kau dan ganin yanayinsu,

a fusace fahad yaje yasha gabanta cikin fada yace"ashe dama bakida hankali bansaniba? Saboda kina mahaukaciya se kije taron da duk duniya ana gani taron maza da mata, kewace irin dakikiya ce wai? "

faseelat idanunta suka cika da hawaye tace "banje wurin dan kome ba sedan nakara karfafa gwiwar amira kuma na tambaye ka da izininka naje "


atsawace yace "tambayar banza kinsani sarai bazan bari kije irin taronba "


Aisha da amira nata kallonsu,


hawaye suka zubowa faseelat tace "to kayi hakuri danasan baka amince ba da banje ba "

ta gittashi taajiye gifts din akujera ta haye sama,

amira da tundazu tafara hawaye fahad yajuyo wurinta tunkan yaisa wurinta yace "ke kuma who ask you to call her name?"

Kafin yaiso gunta ta tashi ta ruga sama, yabi bayanta da harara da takaici,

Aisha da itama takejin mugun haushin amira tatashi tabita, nide narasa gane wa yafi jin zafin abun ita dashi don duk sun rikice,

amira tasamu faseelat nata kuka, duk kokarinta akan amira amma haushinta ma akeji maybe dabataje ba dabazata yi performing haka ba, amira tazauna tana tayata abun tausayi itada zaa yabamawa aimata kyauta danta kara kokari sema fada akemata,

suna cikin haka Aisha tashigo taja amira dakinta ta zauna tana kallon amira rai bace tace "gulmammiyar kawai ke u don't deserve them ur step mother deserve them ko? ke kilbabba sena dinke wannan shegen bakin inga ta inda zakirika wannan iskancin "ta rike bakin,

amira tanata kuka tasaketa tace "maza kije ki tube wadannan tsigaggun kayan munafuka kawai "

amira tafita dakin tashiga nata ta haye bed tana kuka,

se yazama su duka suna kuka while fahad da Aisha kishi kamar ze halaka su,


ba bata lokaci vedion amira na debate da inda take amsar kyauta suka watsu a media koina kashiga itace da faseelat anhada vedion 8mnt,da kuma hotunan amira dana faseelat a rungume,

fahad duk duniyar ta mishi zafi yashiga dakinshi yayi wanka yabar gidan donji yake kamar ya zane faseelat,

Aisha kasa tashi daura girki tayi tana kwance sema ta bude data sega vedion har a group dinsu na matan aljanna,haushi yakasheta sunata yabon faseelat anata yabon amira "wow Masha Allah dama diyata ce, kai yarinyar ta hadu, gaskiya kishiyar ma tayi ba karya kuma tayi kokari dama zaa samu kishiyoyi haka"

Wata datake da number Aisha tana ganin status nata tai replying "kamar diyar maman amira "

Aisha dake online tace "itace da kishiya ta faseelat "

Caiii yan group suka taso kowa na fadin albarkacin bakinshi wasu na yabon faseelat wasu na tunzura Aisha akan tabar bari tana daukar mata diya koda zata koyi wani abu gunta, ai ta iya ta koya mata mana .

Aisha takara hawa dole tasauka online din tai kwance kanta na ciwo zuciyarta na zafi dukda abun be burge fahad ba amma taji haushin yabonta da mutane keyi,

Kowa na dakinshi har laasar bawanda yaci komi, se 6 amira tatashi bacci ta tafi dakin faseelat,

Amira tace "anty dan Allah kiyi hakuri"


faseelat tace "bakomi amira kinci abinci muje in dafa miki indomie kici "

suka sauko kasa ta dafa mata indomei da kwai taci sama sama itako bataiya cin komi ba suka koma daki,


faseelat ce da girki amma taki tayi girkin bata tabajin haushin fahad ba irin yau kuma tasan kotayi baze ciba,

bayan Maghreb,

fahad suna tareda sabeer, sabeer yaganshi some how yace "lpy dude miye? "

Fahad yace "mtsssw I don't know meke damun faseelat tana abu like mad woman wai takwashi kafa taje taron speech na school dinsu amira abun haushin harda ita akan stage dan hauka wai amira takirata taimata kyauta "

sabeer yace "ai abun jindadi ne yarka tayi kokari, kuma kaga amira taji dadin zuwanta, ace ana speech dukkanku baku halarta ba aigwara dataje "

"ni nama ga pics da vedion se abun yaburgeni naji dama diyata da matata ne "

ran fahad ya baci yace "u see harkai shege kace haka mutane tsinannu nawa zasu ji shaawar matata? natsani wani ya kalli koda fuskarta ce "

Sabeer yanata dariya yace "let me show you something "ya bude insta segashi kusan mutum biyar da yake following sun dora vedion anata comments akai "wow brilliant girl"

"I love this woman inama ace matata ce shes beautiful with good heart"

"abun burgewa yarinyar nada wayo sosai har tasan tayi godiya "

"gaskiya su duka sun burge ba kamar matar data jajirce wurin ilimantar daita "

"Allah kabani family kamarsu "

"nimade I pray so Allah ya bata kamarta "

Fahad ya dauke ido akai yanajin mugun kishi,

Sabeer yace "zancen da aketayi kenan koina abun burgewa kai wlh kagodewa Allah "

fahad yace "u r mad, kana abu kamar ba namiji me kishi ba mtssww"ya shiga mota yakoma unguwarsu,

a masallaci yayi salla sannan yashigo ciki gidan tsit kamar bakowa aciki yazo ze wuce ya duba dining yaga wayam kuma yasan de yanzu basu isa cin abinci ba hakan yakara bata mai rai sosai wato faseelat batai girki ba? Ya tambayi kanshi ya jinjina kai yawuce dan dama baci zeyiba,

Aisha jin zuciyarta nata ciwo yasa tasha drugs nata da yoghurt ta kwanta ba jimawa se bacci,

su faseelat ko sunata kallo adakinta amma ita faseelat tunanin rayuwarta kawai takeyi tundaga gidan khalil zuwa yanzu, tunda tai aure daga wannan se wannan kuma tana bakin kokarinta amma duk a banza,


Faseelat ta dauko wa amira dudu milk tasha ita kuma tasha hollandia yoghurt suka cigaba da kallo,


fahad yanata duban hanyar faseelat amma shiru, tariga tasa ba masa tanabinsa shiyasa yayi kwanciyarsa yasan dukdare zatazo bashi hakuri Ammafa be dena jin haushinta ba akan abinda tayi ,

Karfe goma fahad dake zaune yana kallo ya meda farin wata TV don suna sanya labarai na BBC a Time din,

Alhaji dorikul bali shine megabatarwa ayau, acikin headline harda labarin amira ,

yace "a Nigeria zamuga vedion data yadu a dukkan kafofin sada zumunta inda yarinya yar shekara biyar da ta lashe kyautuka biyar ta yabi kishiyar mamarta "

Idanun fahad sukai jawur yarasa ina zesa kanshi,

har akazo kan labarin alhaji dorikul bali yace "a Nigeria karamar yarinya yar shekara biyar ta lashe kyautuka biyar bayan kyautar debate data lashe yarinyar mesuna amira tayi godiya kuma tayabi kishiyar mamarta wanan yaja hankalin duniya kanta, ga kadan daga cikin vedion "

aka dan hasko kadan daga cikin debate din inda take tambayar Mr chairman koze jidadi in aka damka Wa namiji matarsa ya amshi haihuwar ta ,se kuma complete inda take wa faseelat godiya har inda faseelat tafito ta rungumeta, alhaji dorikul bali yace "wannan abu ya kayatar ya dau hankalin mutane ,fiyeda mutane 2milion ne suka bude vedion ayau, domin abune dabaasa ba ganiba yanzu haka de yarinyar tana

Please Login or Register in order to submit comment