Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mata ido , tana cije lip's ta shanyesu tana jin tsanar faseelat aranta,


a bed ya direta suna kwance sunata firar soyayya da wasa aka kira salla, fahad ya mike ya shiga toilet yin alwala, faseelat tai murmushi tana kallon kofar toilet din ya matukar burgeta baya wasa da salla da Ankira yake tashi,

tana kwancen ya fito yabita da kallo duk ya harmutse mata gashi tana ta kallonshi with smiling on her face ya sakarmata murmushi ya bude wardrobe ya dauko dadduma,

yana cikin shimfidawa faseelat ta kira sunanshi "Hero !!!"

ya dago ya kalleta tana lumshe ido tace "dik yau bakaje masjid ba "

yayi murmushi yace "ban cika zuwa masallaci ba, mutanen unguwar nanma haka duk yawanci suna sallarsu agidane"

faseelat ta tashi zaune tace "hero kasan yawan ladar da kake missing kuwa? Ai salla a masallaci tafi ta gida lada saboda ko tafiyar da kake kafin kakai masallacin lada ake rubuta maka,

bari nabaka labarin banu salimata a zamanin fiyayyen halitta (s. A. W) hadisi ne ingantacce yayi bayani akansu su sunyi nisa da masallaci se suka so su dawo kusa da masallacin saboda samun sauki........
ﻭﻋﻦ ﺟﺎﺑﺮٍ ﻗَﺎﻝَ : ﺧَﻠَﺖِ ﺍﻟﺒِﻘَﺎﻉُ ﺣَﻮْﻝَ ﺍﻟﻤﺴْﺠِﺪ، ﻓَﺄَﺭﺍﺩَ ﺑَﻨُﻮ ﺳَﻠِﻤَﺔً ﺃَﻥْ ﻳْﻨﺘﻘﻠُﻮﺍ ﻗُﺮْﺏَ ﺍﻟﻤَﺴْﺠِﺪ، ﻓَﺒَﻠَﻎَ ﺫﻟﻚَ ﺍﻟﻨﺒﻲَّ ﷺ ﻓﻘﺎﻝَ ﻟَﻬُﻢْ : ‏« ﺑَﻠَﻐَﻨﻲ ﺃَﻧَّﻜُﻢْ ﺗُﺮﻳﺪُﻭﻥَ ﺃَﻥ ﺗَﻨْﺘَﻘِﻠُﻮﺍ ﻗُﺮْﺏَ ﺍﻟﻤَﺴْﺠِﺪ؟ ‏» ﻗﺎﻟﻮﺍ : ﻧﻌﻢ ﻳَﺎ ﺭَﺳﻮﻝَ ﺍﻟﻠَّﻪِ ﻗَﺪْ ﺃَﺭَﺩﻧَﺎ ﺫَﻟﻚَ، ﻓﻘﺎﻝَ : ‏« ﻳﺎ ﺑَﻨِﻲ ﺳَﻠﻤَﺔَ ﺩﻳﺎﺭَﻛُﻢْ ﺗُﻜْﺘَﺐْ ﺁﺛﺎﺭُﻛُﻢْ، ﺩﻳﺎﺭَﻛُﻢْ ﺗُﻜْﺘَﺐْ ﺁﺛﺎﺭُﻛُﻢْ ‏» ﻓﻘﺎﻟﻮﺍ : ﻣَﺎ ﻳَﺴُﺮُّﻧَﺎ ﺃَﻧَّﺎ ﻛُﻨَّﺎ ﺗَﺤَﻮﻟْﻨَﺎ . ﺭﻭﺍﻩ ﻣﺴﻠﻢ

_An Kar6o daga *Jabir* Yace: Akwai Wani Fili a Gefen Masallaci. Sai *Banu Salama* Sukaso Su Zauna Kusa da Masallacin. Sai Labarin Ya Isa Ga *Manzon Allah*. Sai Yace Dasu: *“Labari Ya Isomin Lallai Kunaso ku Dawo Kusa da Masallacin?”* Sai Sukace Eh Hakane! Ya *Manzon Allah* Sai Yace: *“Yaku Banu Salama Ku Zauna a Gidajenku Za'a Dinga Rubuta Muku Ladan Duk Taku Daya da Zakuyi”*. Sai Sukace: da Hakan Bai Faranta Mana ba da Mun Kasance a Gefensa (Masallacin)._

se suka janye fasa dawowa gefen masallacin saboda surika samun wannan ladar.

akwai wani hadisi kuma da aka rawaito daga bukhari.....

ﻭﻋﻦْ ﺃَﺑﻲ ﻣﻮﺳﻰ ﻗﺎﻝَ : ﻗﺎﻝَ ﺭﺳﻮﻝُ ﺍﻟﻠَّﻪِ ﷺ : ‏« ﺇِﻥَّ ﺃَﻋْﻈَﻢ ﺍﻟﻨَّﺎﺱِ ﺃَﺟﺮًﺍ ﻓﻲ ﺍﻟﺼَّﻼﺓِ ﺃَﺑْﻌَﺪُﻫُﻢْ ﺇِﻟﻴْﻬﺎ ﻣﻤْﺸًﻰ ﻓَﺄَﺑْﻌَﺪُﻫُﻢْ . ﻭﺍﻟَّﺬﻱ ﻳَﻨْﺘَﻈﺮُ ﺍﻟﺼَّﻼﺓَ ﺣﺘَّﻰ ﻳُﺼﻠِّﻴﻬﺎ ﻣَﻊَ ﺍﻹِﻣﺎﻡِ ﺃَﻋْﻈَﻢُ ﺃَﺟﺮًﺍ ﻣِﻦَ ﺍﻟَّﺬِﻱ ﻳُﺼﻠِّﻲ ﺛُﻢَّ ﻳَﻨَﺎﻡُ ‏» ﻣﺘﻔﻖٌ ﻋَﻠَﻴْﻪِ

_An Kar6o daga *Abi- Musa* Yace: *Manzon Allah* Yace: *“Lallai Daga Cikin Mutane wanda Yafi samun lada me girma Acikin salla, Wanda Yafisu Nisa Wajen Tafiya. Wanda Yake Jiran Sallah Har Sai Ya Sallaceta tare da Liman Yafi Wanda Idan Yayi Sallar Yake Bacci Girman Lada”*._

```{Bukhari da Muslim Suka Ruwaitoshi}```

Faseelat ta sakar mishi murmushi tace nasan zakaso ace kasamu lada mafi yawa,

Shiko yayi sororo yana kallonta cikin burgewa,

ta cigaba da cewa ,ba iyakar nan ladar ta tsaya ba, bayan kagama samun ladar tafiya se kuma ladar sallah acikin jam'i,manzon Allah (S. A. W) yace

صلاة الجماعة،ثفضل صلاة الفذ بسبع و عشرين درجة.

رواه البخاري و مسلم


Cewa salla acikin mutane tafi sallar mutum daya da lada ashirin da bakwai,

Tai narai narai da fuska cikin ladabi tace "hero nasan daga yau zaka rika gaggawar tafiya masallaci dan nasan bazaka bari wannan dumbin ladar yarika wuceka ba",

fahad da dadi ya gama cikashi yanda faseelat take ta kawo hadissai yace "insha Allah honey daga yau sallar Jam i bazata wuce ni ba thank you for showing me the best path "

faseelat tana murna tace "Nagode da ka amince Allah ya amshi ibadunmu "

yayi murmushi yace "amin "

ta yunkura ta tashi da kyar ta dauko mishi jalabiya ta zo tasaka mishi yanata kallonta tana gama samishi tace "Tom don't forget to include me in ur duas "

cikin jindadi da murmushi kan fuskarshi ya lakuci kuncinta yace "mar'atussaliha"ya juya yafita.


tasaki murmushi ta lumshe ido tasauke ajiyar zuciya from yesterday to now soyayyarshi takara shiga cikin jinin ta wadda tare daita take duk numfashi tanajin kamar ta shekara dashi kamar ma bazata iya rayuwa inbabu shi kusa ba ,

ta juya tana takawa asannu tashige toilet tayo alwala tazo ta tada salla, tana gamawa ta dauki alkurani tafara karantawa tafijin dadin karatun القران bayan Maghreb ko da asuba .

ko megadi yayi mamakin ganin fitar fahad da jalabiya da alamun zuwa masallaci, acan masallaci fahad yana sallar wani dadi da natsuwa nashigarhi lalle salla nakarawa mutum natsuwa, duk dade masallacin be cika ba amma akwai yan mutane ba laifi (that's what's happening a yawancin unguwar masu kudi they are not going to masjid Allah ,majority of them ana kiran salla suna kara shigewa cikin bargo ba kamar sallar asuba sauran salloli ko duk agida ,wasu ma sede ta jumaa) 🤣

Bayan an sallame sosai ya daga hannu yana adduar samun zaman lpy acikin iyalinshi da rokon yin adalci don baai nisa ba amma he's dying for faseelat ya shafa ya tashi ya fita a hanya sunata musabaha da jamaa makwabtansu masu attending salla wasu sundade basu haduba ma , (gaskiya fahad ka kwaso lada) 🤣

tunda ya doshi dakin faseelat yakejin kiraarta cikin murya me dadi tana karanta suratul mulk da ta saba karantawa duk dare wani lokaci ko ba kurani ko tana aiki tana karantawa , fahad yayi tsaye bakin kofar yana saurare murmushi kawai yaketa saki ,bawai basa karatun bane aa sunayi akan dade baai ba, kuma muryar faseelat is different saboda yadda take bawa kowane harafi hakkinshi da yadda take karatun da tajweed,

ya tura kofar ya shiga da sallama bakinshi, faseelat ta dago tamai murmushi ta amsa sallamar ta cigaba da karatu, da yayi zaune yanata kallonta he then decide to join her suka cigaba da yi atare,

Aisha da tafito daga daki bayan tayi tata sallar zataje tai masu dinner taji karatunsu ta kara matsawa sosai ta dan saurare su jin sunayi ne atare kishi ya taso mata taja dogon tsoki tace "mtswwwww wani sabon salo, himmmm kingama munafuncinki kibarmin mijina wlh "
Ta sauka Tawuce kitchen, duk jikinta ya mutu Allah da zataje bp test da jininta se yakai 190 and some things, cikin rashin kuzari ta dafa musu indomei da kwai ta juye a cooler ta kai kan dining tareda forks da plates ta haye ta shige daki,

da kwanciya tayi tanata wrong tunani kome ta tuno tai sauri ta tashi ta dauko kuraninta dake can saman wardrobe da kura jikinshi don anyi 2 months bata duba ba ta bude tafara nata karatun in a sweet and low tone nata (dakyau😂)tanayi tana kuka

kiran ishai yasa su faseelat dakatawa atare sukaiwa annabi salati da yin ربنااتنا في الدنيا حسنة وفي الآخرة حسنة وقناعذاب النار

Da subhanakallahumma wabi hamdika nashhadu an LA'ilaha illa anta nastagfiruka wa natubu ilaik, suka shafa,

atare kowa na kallon juna suka sakarma juna murmushi, fahad ya tashi ya shige toilet ya sauyo alwala badan tashi ta kareba a, a don kara samun lada da tsarkake gabbai ,

ya fito yana tsane ruwan da tawul cikin sauri don yaji anata hayya alassalah 😃

har yakai kofa ya rike handle yajuyo,
faseelat ta daga mishi hannu tanamai bye ya daga mata yafita zuwa salla.
[8/5, 6:09 PM] +234 815 712 7134: ➰➰➰➰➰
*RAGGON MIJI*
➰➰➰➰➰






By






*MAMAN MAMY*
*(SHALELE)*





https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/


*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*




*~We are bearer's of so golden pen🖊~*

*~we write assidiously perceive no pain~.*

*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*

*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*




5⃣9⃣





*Dedicated to sweetie I mean my kawalliya, my bestie here's ur page again enjoyed*




Itama tashi tayi tayo alwala tayi tata sallar ,bayan tagama tayi shafai da wuturi ta gama addua ta tashi tana linke carpet ya shigo rike da hannun amira,

Faseelat ta juyo tana murmushi tace "sannu da zuwa hero"

Kallonta Kawai yake bece komi ba, amira ta janye hannunta ta tafi wurin faseelat,

Faseelat ta cire hijab taajiye ta dauki amira tana kallonta tace "princess ya akai? "

Amira tace "anty I'm hungry "

Faseelat ta fiddo ido tace "ba magana princess najin yunwa dafatan de kinyi salla? "

Ta daga kai "nayi tareda mommy "

Faseelat tace "alright muje kici abinci diyar mommynta "

Fahad nata kallonsu faseelat ta fara takawa dakyar dauke da amira ahannu, fahad na dariya yaisa wurinsu yace "daughter taho karki karasa mommy she's not well "ya ansheta

Amira tai fuskar tausayi ta kalli faseelat tace "ayya sorry anty daddy na duka yake har mommy yana duka tai ta kuka when I heard ur crying nace mommy tazo for your rescue setace kindena kukan but she's scared........."fahad ya rufe mata baki ya kakaro murmushi yace "muje kici abincin sarkin surutu"

Ya kalli faseelat yace "muje honey queen muci abinci"ya mika mata hannu

Faseelat da take ta kallon fahad dan samm bata ganeba abinda zuciyarta ke bata shine kila tanajin screaming dinsu ne, tana murmushi ta saka hannunta anashi suka fita ,

Amira nata surutu da faseelat ,sukaje suka zauna kan dining Table faseelat sede tai dariya can zuwa ta dago suka hada ido da fahad daketa kallonta ta dena dariyar ganin irin kallon da yake mata ta sadda kai kasa tana gyara gashinta, be dena kallonta ba

amira tace "anty sarve me plsss"

Faseelat ta dago tai murmushi ta tashi ta bude kular ta zuba mata a plate tasa fork ta mika mata, bajira amira tafara ci sede tsakura kawai take duk kukan yunwar nata,

fahad yatashi ya hau sama don it's about 20 mnt Aisha bata fito ba,

Yana tura dakin ya shiga yaganta kwance dukunkune tanata ajiyar heart don tasha kuka ,

Cikin sauri yaisa wurinta ya haye gadon ya dora kanta ajikinshi yanata taba jikinta ko da zafi amma babu,

Cikin tashin hankali yace "heart beat meyasameki meyasa kike kuka? "

Ta lumshe ido can ciki ciki tace "kaina ke ciwo sosai da zuciya ta "

Fahad ya zaro ido cikeda tausayinta yace "sannu heartbeat meyasa baki kirani ba tundazu da na kira doctor since, sannu bari nakira likita "

ya daga wayarshi da niyyar kiran doc,

Aisha tace "no kabari zansha magani ba se ka kira doctor ba "

Fahad da hankalinshi ya gama tashi yace "kina wasa da lpyarki ne?idan ke zakiiya hakurin zama da ciwon ni bazan iya hakurin ganin ki cikin ciwo ba cos nima I'm feeling the pain "bajira ya dannawa doctor faith kira, after few ring ta dauka,

Tace "hello sir "

batare da ya amsa ba yace "my wife is not well plss come and check on her "

faith tace "I'm coming right now "
Ta kashe kiran .

Fahad ya jingina kai jikin bed din ya rumtse lips yariga yasan abinda ke wahalar da Aisha kishi ne kawai ke cinta, ya dora hannu yana shafa smooth hair dinta yace "Aisha dan Allah inarokonki ki kara hakuri akan na da, karki sawa kanki damuwa ciwo yakama minke ,nasan it's not easy kirika ganin mijinki tareda wata amma ki daure, Aisha inasonki sosai bazan iya hadaki da kowa ba, cos u r a sister, wife , mother of my daughter and my lover ke ta dabance bekamata kinasa wa kanki damuwa don duk wacce zanso bayanki take, Aisha u r my heartbeat duk bugun da zuciyata takeyi da sonki yake fita, ki kwantar da hankalinki kwanciyar hankalinki shine nawa "

Aisha ta rike hannunshi fuskarta akanshi tace "yaya bazan iya jurewa ba I can't endure hearing yours screaming doing sex with someone else, last night I'm sleepless, kokadan barawon bacci be dauke niba, taya ma kake tunanin hankalina ze kwanta inaganinka da wata Kana bata desame kulawa da kakebani I can't take it "hawaye suka gangaro daga idonta makoshinta a bushe saboda zuciya,

Fahad ya rumtse ido yanajin ba dadi it will hurt alot seeing your Husband with another girl showing her so much love, zuciyarshi tafara harbawa da karfi cikin dauriya ya fara sharemata hawaye yace "insha Allah that will not going to happened again, I'm so sorry my beloved wife "

ta dora hanninta akan nashi da ke kan fuskarta ta danyi murmushi tace "I love you "

Yayi karamin murmushi ya mata kiss a forehead,

Faseelat sunata shan labari da amira taji door bell ta tashi taje ta bude, taga mace Krista sede da kayan aikinta ahannu daganinta likita ce,

Faith tace "hi I'm doctor faith I'm here to check on Mr fahad wife "

Faseelat tace "ok" tabata wuri tashigo

Faith da ba bakuwa bace ta haye sama tana dialing no fahad,

Fahad ya dauka tace "I'm here sir "

Yace "OK come to the third room "


Faith tana dubawa taisa kofar dakin tai knocking yace "come inside "

Ta shigo ya sauka daga kan bed din, doctor tazo tana duba Aisha tai mata yan tambayoyi Aisha ta bata amsa,

Faith ta fahimci damuwa ce tawa Aisha yawa tace "madam se kina cire damuwa aranki kina mantawa da abu komi girmanshi damuwa bazata sauya kome ba kuma ba itace zata maganin problem naki ba ki kula ur health is your everything "
Aisha ta daga kai alamun taji.

Faith ta girgiza kai ta dauko jotter ta rubuta drugs ta bawa fahad,

Ta tashi tafita,

Faseelat tana zaune kan dining din tana ta tunani faith tazo Tawuce ta daga mata hannu "good night madam"tafice


fahad ya koma kan bed din ya zauna yana mata kallon tausayi yace "sannu heart beat bari naje na siyo miki drugs din "

Aisha tace "OK take care "

Ya tashi ya fita yana saukowa ya zagaya kan dining faseelat daketa tunani amira nata zuba ita kadai, ta dago ido ta kalli fahad,

Ya karasa isa kusada ita ya duka ya mata kiss a cheek yace "I keep you waiting ko? Aisha ce ba lpya just eat ur food ni zanje nasiyo mata drugs "

Faseelat tace "ayya sorry Allah yabata lpya "

Yace "amin sena dawo "yana kallonta

Tace "Allah ya dawomin da kai lpya"

Yace"amin"ya sakar mata murmushi ya juya ya fita,

Yana fita ta tashi dama abincin bewani burgeta ba ta kama hannun amira suka shiga dakin Aisha, tana kwance still,

Faseelat tace "ashe bakijin dadi anty Allah yabaki lpya "

Cikin tsawa Aisha tace "da Allah fitarmin a daki karki kuskura ki kara shigomin daki munafukar banza kuma ta Allah ba taki ba komin tsiyarki bakiisa ki ja dani ba donna miki fintinkau"

Faseelat ta tabe baki tace "Allah yabaki hakuri "

Ta juya still da hannun amira anata ta fita,

Aisha taja tsoki tana jin zafi a zuciyarta da yadda zuciyarta ke raya mata zatai da ta kasheta ta huta,

Faseelat ko abin be dameta ba wanda ya dakeka dan yafadama irin wannan ai bakomai bane, suna shiga daki tayowa amira wanka suka fito amira tace tana da assignment ta dauko faseelat na nuna mata tawuce toilet seda ta gasa jikinta sosai da sosai sannan tai wanka tafito tasaka sleeping dress dinta ta feshe jikinta da perfumes bayan tayi wankan humra tazo suka cigaba da karatu da amira,

Bayan fahad ya dawo shi da kanshi ya hadowa Aisha tea tasha yabata magani yamata kiss sannan ya mata seda safe ya fita,

Yana tura dakin faseelat kamshin yan agadez😃me tada shaawa ya bugi hancinshi ya lumshe ido ya ida shiga cikin dakin daga faseelat har amira sunyi bacci ga littafi da school bag din amira gefe, yayi murmushi yaje ya dauki amira ya kaita dakinta ya dawo, ya shiga yayi wanka ya fito yayi shafe shafenshi ya saka boxer dinshi ya kashe haske ya haye gadon yajawo faseelat ya rungume,


Suka fara bacci Aisha ma tasamu bacci, can cikin dare jarabar fahad ta motsa faseelat na bacci taji bakinshi acikin nata ta bude ido tana kallonshi ta cikin duhu yadda yaketa kissing dinta yana kara matsa breast dinta, ta meda ido ta lumshe wato duk jarabarta akwai wanda ya shanyeta, da tayi shiru kamar tana bacci fahad da yarika mata wasa mewuyar fadi dandanan ta haukace tana kaimishi kisss takoina tana yamutsarshi itama, she was thinking yanzu bazeyi zafi ba amma yadda fahad ke abun ba tausayi a zauce, dole seda ta rika kukan neman temako shi kuma yana ihun dadi ,

Kukanta ne ya tada Aisha daga bacci ta tashi zaune tana saurarensu shi yanafadin "honey dadinki yayi yawa zaki kasheni ke ta dabance I love you nabaki komi nawa........ "

itakuma faseelat na kuka tana kiran "ummi kizo mutuwa zanyi kasheni zaiyi, Dan Allah hero kabari zafi....... "

Aisha ta hade kai da gwiwa ta saki kuka me cin rai "


Fahad seda yawuce 40mnt sannan yayi releasing ya kankameta yana sa mata albarka ,itako tana ta kuka don zafin da takeji yayi yawa, dakyar ya rarrashi kayanshi ya dauketa suka tafi toilet ya gasa ta sosai sukayi wanka ya daukota suka dawo suka kwanta,

Suna rungume da juna Se ajiyar zuciya takeyi ,yace "honey I'm sorry yakusa dena zafin I'm sure gobe idannayi bazaki ji zafi ba "

Ta harareshi tace"se ka gama min illa karika cewa sorry bayan baka bina Ahankali se kaita abu kamar zaka cinyeni duka "

Yayi dariya yakai hannu kan kugunta yana shafawa yace"naji bazan kara yi kamar zan cinye kiba, amma sede ki rage dadi don inde kina haka ba abinda zaa fasa"
ta turo baki takara shigewa jikinshi sosai don tanajin dadin hakan ,dede kunenta yace "ummi kizo plsss ze kasheni mutuwa zany..." ta rufe mai baki da hannu tana dariya,
firar masoya suka cigaba da yi sunata dariyarsu bayan wani lokaci bacci ya daukesu,

Aisha ma ta dade tana kuka gaff asuba bacci ya dauketa,

Kiran farko na asuba ya tada faseelat dukda ba gaf suke da masallacin ba amma anaji, ta bude ido ta janye jikinta a hankali ta sauka ta shiga toilet tayo alwala tafito,

Har lokacin fahad na bacci seda ta shimfida carpet tasa hijab sannan taje tafara masa waiwayi a kafa, can cikin bacci yaji hakan ya bude ido ya zubasu kanta,

Ta sakar mai murmushi tace "assalatu khairun minan nawm"

Yana murmushi ya dafe kai ya kalleta yace "akwai sauran time fa, inada alarm ze tayar dani "

faseelat tace "harfa anyi kiran salla na farko gashi kuma masallaci zakaje "

Ya langabe kai yace "fisabilillahi cikin duhunnan masallaci zaki turani? ko tausayi na bakiji "

Faseelat tai murmushi tace "Hero bawai bana tausayinka bane ladar fita masallacin nakema kwadayi bare ta asuba is special ,akwai wani hadisi da yayi magana akan sallar asubar wanda abu dawood da turmuzi suka ruwaito......
ﻭﻋﻦ ﺑُﺮَﻳﺪَﺓَ  ﻋﻦ ﺍﻟﻨَّﺒِﻲِّ ﷺ ﻗَﺎﻝَ : ‏« ﺑﺸِّﺮﻭﺍ ﺍﻟﻤَﺸَﺎﺋِﻴﻦَ ﻓﻲ ﺍﻟﻈُّﻠَﻢِ ﺇِﻟﻰ ﺍﻟﻤﺴَﺎﺟِﺪِ ﺑِﺎﻟﻨﻮﺭ ﺍﻟﺘَّﺎﻡِّ ﻳَﻮْﻡَ ﺍﻟﻘِﻴﺎﻣَﺔِ ‏» ﺭﻭﺍﻩ ﺃﺑُﻮ ﺩﺍﻭﺩ ﻭﺍﻟﺘﺮﻣﺬﻱ

_An Kar6o daga *Buraidah* Daga Annabi Yace: *“Kuyi Bushara GA Masu Tafiya Cikin Duhun Dare Zuwa Masallaci da Haske Cikakke Ranar Alqiyama”*._

"kuma kasan ranar alkiyama duhu ne wanda mutum baze iya ko ganin tafin hannunsa ba, sukuma masu zuwa salla cikin dare manzon Allah (S. A. W) yace ayi musu bushara bazasu ga wannan duhun ba ,shine nake maka kwadayin samun wannan hasken mijina " ta langabe kai ta kamo hannunshi,

fahad yayi murmushi yace "Nagode *maratussaliha* inajin dadin gyaranki gareni ko da yaushe kikasance me nunamun mafificiyar hanya nikuma zanbi insha Allah "

Faseelat ta yiwa hannunshi kiss tace "thank you for understanding "

Fahad ya turo baki yana nuna cheek dinshi yace"u supposed to do it here fa instead "

Faseelat tana dariya ta yaye bedsheet din jikinshi tana fadin "zaka makara sekayi sauri "

Ya tashi yana mikar shakiyanci ya shige toilet,

Faseelat tai dariya ta girgiza kai ta hau carpet ta kabbara sallar rakatanil fajr,

Seda yayi brush yayi alwala yafito lokacin har tagama tana zaune tana azkhar tayi sauri ta gyara shimfidar carpet din zuwa gicce,

Ya saka jallabiya ya juyo yaga ta gyara carpet, yace "what ? Again "

Tai murmushi tace "nufi na kayi rakaatanil fajr kafin katafi inkaje inbaa kabbara ba sekayi tahiyyatul masjid kafin atada sallar "

Fahad yayi murmushi yace "angama ranki shi dade "ya kabbara sallar 3mnt ya gama ya tashi ya fita zuwa masallaci megadi de nashan mamaki koshi yasan anyi amarya,

Bayan tagama salla ta zauna tayi azkhar wadanda suka samu ta tashi ta nufi kofar Aisha,

Aisha nata bacci jin ba ko motsi faseelat ta fara knocking, Aisha ta san dakin bude yake cikin jin haushi tasan bewuce faseelat tace "waye?"da karfi,

Faseelat tace "anty ni ce dama cewa nai anyi salla "

Aisha taja dogon tsoki tace "sannu diyar liman jikanyar sheikh"

Faseelat batama tsaya jinta ba ta wuce dakin amira, amira da se bakwai, 8 take tashi wani lokaci ko sallar batayi, faseelat ta tasheta itada kanta ta kaita toilet tai mata alwala Tawuce daita dakinta,

amira tai salla faseelat ta dauko kurani tana kallon amira tace "princess wace sura kike? "

amira makarantarsu akwai ta hafeez bayan bokon kuma suna hadda tace "suratul fajri "

Faseelat tace "OK kingamata? "

Amira tace "a, a anty muna aya ta 15 zamu tashi ta sha shidda, "

Faseelat tace "OK yanzu zamuyi murajiar na baya se mu cigaba "

Suka fara karatun har ta 15 sannan faseelat ta dora mata,

Suna cikin karatun fahad ya shigo, abun really surprise and impress him yayi tsaye yanata kallonsu cikin burgewa be saba ganin amira a irin wannan time dinba suko basu dena karatun ba ,

da yanata sauri ne yazo yakara wa faseelat gajiya se kuma ya samesu ahaka ,

Cikin farin ciki ya juya ya nufi dakin Aisha,

Aisha faseelat tabar wurin amma ita batadena banbami ba "shegiya laanannar Allah wai wadda ke bin namiji da aurenta itace zatazo tana nunamun musulunci, fara me bakar zuciya...... "taitayi har ta gaji sannan ta tashi tai sallar tagama ta dawo ta kwanta gabadaya zuciyarta ta mata nauyi so kawai take ta fadawa mommy problem nata, ta dauki waya ta kirata, mommy da tai salla takoma ta kwanta bacci me dadi ya dauketa don itama bawani baccin kirki take yi ba ta dauka murya dishe ,

Aisha tace "mommy nabani faseelat zata kwacemin miji, mommy duk ya rude akanta wlh mommy bani lpya, jikina duk ya mutu baniya komai "

Mommy tuni bacin idonta ya kau taja dogon tsoki tace"banza sokuwa har seki tsaya bakin cikin kishiya ya kashe ki? Bayan fahad ba yayinki ya dena ba dan batan basira seki kwance taita yin yadda taso kenan? To bari kiji kitashi ki wartsake kifita ki kane kane da gidanki sede in ita ta tare daki, in kuma kikai sanya ita taita yadda taso ki kumshe dakin sakarai kawai, da batasan miya dace ba, ga saudat can da kishiyoyi amma ko maganar su batayi don ta masu fintinkau duk tsoronta suke se ke babbar banza se ankoya miki, seki tashi kifara hidimarki inkin ga dama "diffff takashe kiran,

Aisha tai tsit tana nazari batajin fadan mommy dan kotayi fada tana fadin mafita, tana niyyar tashi fahad ya shigo,

ta sakar mai murmushi ya meda mata hannunshi biyu acikin riga,

Tana kallonshi tace "good morning sweetheart "

Yaida isa kusa da ita ya zauna ya taba wuyanta yace "how are you feeling today"

Tace "better naji sauki "tana marmara ido

Ya sauke ajiyar zuciya yace "alhamdulillah I'm happy "

Aisha tadora hannu tana shafa sajenshi tace "thanks I missed you "

Ya lumshe ido yace "me too "

Ta sauka akan bed din tace "I'm going to the kitchen "

Yace "OK thanks you muje nima I want to sleep "

Suka fita tare,

faseelat naganin amira ta haddace don tana da kokari seta tashi tabarta tatafi kitchen don yin girki ita kuma amira ta cigaba da karatun,

Faseelat nashiga kitchen tai tsaye tana nazarin abinda zatai, ta yanke shawarar yin grilled fish da vegetable sandwich and black tea,

Shaf shaf tafara aiyukanta, Aisha na saukowa taji kamshi ta rike kugu ta shiga kitchen din taga faseelat daga ita se short tight trouser da armless riga tana ta aiki bako kallabi,

Aisha tabi bayanta da kallo cikeda kishi da balai tace "banza marar kamun kai mtswwwww "tana ta ballamata harara,

Faseelat ta juyo ta sakar mata murmushi ta kalleta up and down ta koma ta cigaba da aiki Dan bata da lokacinta ,

Aisha taja tsoki ta fita ta koma daki kamar zata fashe taita zagaye haushi takeji bataso fahad yaci abincin can,

Fahad na komawa ya samu amira nata karatu ya wuce ya haye gado ya kwanta,

Amira da kejin bacci ta tashi ta cire Arabian hijab din jikinta ta haye kan gadon ta matsa can kusa da babanta,

Fahad daketa kallonta yakara jawota jikinshi yace "har angama karatun?

Please Login or Register in order to submit comment