Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

nake iya kauda kaina gefe guda.

Nan suka ja kujera suka zauna. Bayan mun gaisa, Ameerah ta zubawa Yaya nashi abincin. Ni kam ina gama ci, na dauki jakata na musu sai anjima. Sai dai tun kafin in kai ga tashi tsaye Yaya ya tsayar dani. Yace "bari in gama sai in sauke ki".
Ban ce komi ba, na koma na zauna. Again, nayi zaton zata yi magana ko wani abu, nan ma ta bani mamaki da naji tayi shiru. Bai ma dauki wani lokaci ba ya gama cin abincin, nan muka mike muka fita.

A asibiti bayan na gama gaisawa da duk wasu wadanda muke gaisuwar mutunci, ganin babu aiki sosai yau a ward din yasa na yiwa ofishin Dr. Anita tsinke. Bayan mun gaisa da ita a mutunce kuma cike da girmamawa, na yi mata bayanin duk wasu signs da nake gani a jikina. Bayan tayi min wasu tambayoyi da kuma gwaje-gwaje, ciki sati biyar ya bayyana.

Ba karamin mamakinta ta nuna ba, cikin jijjiga kai tace "Allah kenan! Wannan abin mamaki da me yayi kama? A yanayin yadda kike dinnan, ban taba zaton zaki iya daukar ciki a cikin shekaru biyu masu zuwa ba wallahi. Kai congratulations!".

Nayi murmushi ina jina kamar ina yawo a sararin samaniya. Duk da cewa nayi zargin haka, amma na kasa yarda da abinda naji yanzu gaskiya ne.
Tace "sai dai you'll have to be extra careful gaskiya, saboda cikin jikinki yana bukatar kulawa da takatsantsan. Kin fahimce ni?".
Na gyada mata kai. Nan ta zauna ta kafa min dokoki, irin ayyukan daya kamata in dinga yi, da wadanda yakamata in guda, irin abubuwan daya kamata in dinga ci, da dai sauransu. Nan na mata sallama na wuce pharmacy na sayi magungunan data rubuta min. Throughout jin jikina nake kamar ba nawa ba. Da an dan motsa kadan, sai in kai hannuna saman cikina ina shafawa.
Lokacin tashi yana yi, na koma gida.

Bayan na ci abinci na cire uniform dina, na zauna a gefen gado ina tunanin ta yadda zan sanarwa da Yaya maganar wannan cikin. A haka har barci ya dauke ni, sai wajen karfe hudu na tashi.
Nayi sallah na fita waje don samawa cikina abinda zan ci. Babu kowa a falon, sai dai daga jin sautin muryoyin dake fitowa daga dakin Raheemah, nasan baki tayi.
Na bude fridge na ciro fresh fruits da yoghurt na koma dakina. Har Yaya ya dawo ban fita ba.

*

Fiye da kwana uku kenan, amma na rasa ta yadda zan isar da sakon cikinnan wajen Yaya, na kuma rasa dalilin da yasa na kasa din.

Safiyar ranar juma'ah, na gama shirin tafiya wajen aiki. Na fita falo da dan saurina ganin cewa naso in makara yau.
Yaya na zaune akan kujera yana latsa wayarshi, babu alamun Raheemah wadda take yin girki yau, babu alamun kayan kari.
Na dan yi turus, kafin na karasa kusa da Yaya na zauna tare da gaida shi.
Ya amsa yana bina da kallo, nasan yadda na murmure da wata irin kiba dana fara yi ne yake kallo yana mamaki. Bai kai ga amsawa ba Raheemah ta fado wajen kamar an jefota. Tun kayan barcin jiya ne a jikinta bata cire ba. Kanta babu dankwali, gashin kanta ya cure waje guda.

Taje gaban Yaya tayi tsaye har da kama kugu, duk muka bita da kallon mamaki.
Cike da tsiwa da alamun dibar albarka tace "Bilal!".

Ba Yaya kadai ba, ni kaina sai dana bude baki na bita da kallon mamaki. Bana tunanin ko Ummanmu tana ambatar sunanshi haka balle ayi maganar Yayye ko kannenshi, ayi zancen matar aurenshi. Nasan kila dai abokanshi na kiranshi haka.

Ya kalleta a dage, "lafiya?".

"Lafiyar kenan, lafiya ce ta kawo haka. Sakina zaka yi!". Ta furta hakan cikin saurin murya da mazarin jiki kamar wadda take shaking.

Yaya yace "ban gane ba? Ke lafiyarki lau kuwa? Me ke damunki ne?".
Tace "ka ga bawan Allah, ba wasu maganganun banza na tambayi ka min ba, idan kana son arzikin kanka, to kawai ka miko min takardata in kara gaba. Dole ne? Nace auren naka dole ne wai?".

Saboda tsabar mamaki Yaya kasa magana yayi, kawai zama yayi yana kallonta, kamar yadda nima na sankame a zaune.

Tace "ni fa bani da lokaci kaji? Ka sallameni don Allah".
Yaya yace "ba zaki zo kai tsaye ba kawai ki ce in sallameki, akan me? Akan wani dalili?".
Tace "saboda na gaji da zama da kai, zama da kai haukata zai yi. Kawai ka sake ni, ka sakeni nace!!". Zuwa yanzu karaji kawai take yi. Tana rufe baki ta juya zuwa dakinta a sukwane, bata jima ba ta dawo hannu rike da takarda, ta jefa mishi jikinshi, "maza maza rubuta min in wuce Malam".

Wani abu yayi snapping a jikin Yaya, kamar wani wanda aka yi possessing, kawai ya dauki takardar da biro ya hau rubutu, ko sauraren ihun kada ya aikata abinda ba'a so a aikata a cikin aure da nake mishi bai yi ba. Yana gamawa ya mika mata, ta warta tana karantawa cikin yatsina fuska.

"Saki biyu? Karya kake wallahi, wallahi sai ka cike min shi. An gaya maka wata tsiya nake kwasa a gidanka da zata sanya ni son dawowa gidan? Kai yau fa idan baka sallameni ba wallahi sai ayi yakin duniya a cikin gidannan! Kaji ma wani rashin mutunci!". Ta hau wasu maganganu marasa kan gado da ma'ana.

"...Dama boka sai da yace kada in bari iska ta share wannan maganin, wannan shegen tsinannen mai sharar wannan yazo ya share shi. Dama sai da yace kaikayi koma kan mashekiya ne, kaina zai dawo muddin bata tsallaka shi ba. Saki uku yakamata ka mata, ni me yasa ba zaka min saki ikun ba?".

Yaya ya tashi tsaye a hankali yana fuskantarta, "me kika ce? Me kike nufi?".

Ta kwashe da wata irin mahaukaciyar dariya kamar wata mahaukaciya, "to ina ruwanka da abinda nace? Abinda za ka damu dashi shine karashen saki na. Kasan wani abu? Boka ya bani wani magani yace in jika shi ya kwana uku, sai in tace in ba waccan sakarar matar taka data kunshi ciki, tana wani daga kai sama tana tutiya ita zata haifi magaji..."
Ni da Yaya muka zare idanu muna kallonta, saboda nasan inda maganar ta nufa. Bata damu da yadda muka yi ba taci gaba,
"kasan me nayi? Sirinji na sayo na zuki ruwan maganin, nawa mangwaron da zata sha allura. Hahhha!". Ta sake wata dariyar. Tuni kwalla ta gama wanke min idanuna.
"Sakara, ina kallonta har wani rawar jiki take yi zata sha mangwaro, bata san cikinta zata fitar ba!".

Na kai hannu bakina na rufe cikin kokarin danne kukan daya taso min, ita kuwa taci gaba da sheka dariyarta.
Karan marin da Yaya ya zuba mata, sai daya karade falon gabadaya. Yace "dama kece kika zubar min da cikina? Kodayake, I've had my suspicions tun daga farko. Saki kike so ko? To kije na karasa miki sakin na uku, meye amfanin zama dake dama? Tunda na aureki na rasa walwala a cikin rayuwata, ban ma san dalilin da yasa na aurekin ba, amma hakanan nake hakuri ina zama dake. Kuma abu dayan da yake sanya ni farinciki ki ce zaki raba ni dashi? Ki fitar min daga gida yanzun nan, kada ki kuskura in dawo gidannan in same ki don wallahi sai na wulakanta ki. Kada kuma ki daukar min ko allura daga cikin kayana!!".

Yaya ya fita daga cikin falon da sauri kamar wanda zai tashi sama, ya barni sarkafe a tsaye ina kallon Raheemah da take ta dariya babu kakkautawa babu alamun zata daina.
Sai gashi kuma ya dawo, "kin san me? Fitar min daga gida yanzun nan, kada ki kuskura ki sake dawowa!".

Sai lokacin ta dakata da dariyar da take yi, "yo dama ko baka ce ba fita zan yi. Gidanka da kayanka din banza dana wofi?". Ta shige dakinta ta fito da gyale a hannu daya, purse da waya a hannunta daya.

Yaya ya saka ta a gaba kamar wata barauniya har bakin gate, sai data fita daga gidan sannan ya juya yana gayawa maigadi kada ya bari ko jingina da gate din gidan tayi balle ta kai ga shiga. Maigadi da rawar jikinshi yace "an gama Alhaji!".

Kawai sai ta zube kasa ta fashe da kuka, kukan ihu bayan hari, kukan nadama da bata da amfani. Tana ba Yaya hakuri, wai don Allah yayi hakuri ya maidata, sharrin shaidan ne. Yaya ko kallonta bai kara yi ba, ya ja hannuna zuwa cikin motarshi ya tada. Maigadi ya bude mishi gate ya fita a sukwane, muka wuce Raheemah tsugune anan, crying her heart out.




Wajen aikin su Yaya muka wuce. Kai tsaye ofishinshi da yake hawa na goma sha biyu muka wuce. Muna shiga ya dauki land-line ya kira secretary dinshi yace tayi oda din abinci. Ya zauna akan kujera yana maida numfashi.

Tashi nayi tsam na koma kusa dashi na zauna, na kamo hannunshi na rike a hannuna ina shafawa soothingly. Gabadaya ya ma kasa magana, mun jima a haka, kafin ya iya daga baki. Maganganu suka fara fita daga bakinshi kamar ana turo su, duk akan yadda Raheemah ta cuce shi ne.
Ban ce mishi komi ba sai hakuri kawai da nake bashi har ya dan nutsu, nace mishi "ka daina blaming dinta, abinda Allah ya kaddaro dole sai ya faru babu makawa, babu kuma tsumi balle wata dabara ta mutum. Raheemah ta saka min magani ko bata saka ba, dole cikin jikina ya fita tunda Allah bai kaddaro zai taka kasa ba. Don haka ka daina damun kanka don Allah, don't beat yourself for it".

Ya kalleni, "for real baby? How are you this calm? Da kunnenki fa kika ji abinda tace, ita ta zubar mana da ciki. Kin kuma ji abinda likita tace, that ba lallai ki iya kara samun wani cikin ba cikin lokutan nan".

Murmushi na sakar mishi mai sanyaya zuciya, na kamo hannunshi na dora a saman cikina, nace "saboda shi Allah ba azzalumin bawa bane, baya kuma dorawa rai abinda ba zata iya dauka ba. Yasan abinda yake cikin zuciyoyinmu, ya kuma fimu sanin cewa muna bukatar ganin sanyin idaniyarmu a gabanmu...".

Nayi shiru ina kallonshi, ina jiran yayi calculating din abin da kanshi. Ba'a jima ba kuwa ya gama tarawa da ninkawa, ya kalleni, "kina nufin..?".

Na gyada mishi kai a hankali ina murmushi, gefe daya kuma ina danne kwallar data ciko min ido.
Bakinshi rawa yake, da kyar ya iya kakaro kalmar "how... wata..?".
Nace mishi "sati biyar".

Daga nan bai ce komi ba, sai janyo ni cikin jikinshi da yayi ya rungume. Ba sai yayi magana zan san yana cikin tsananin farinciki ba, saboda na sani, wani farincikin yafi karfin ka daga baki ka bayyana shi, saboda duk kokarinka da iya bayyana abu, farincikin nan ba zai taba iya bayyanuwa ba. Halin da Yaya yake ciki kenan a halin yanzu.

Sai da aka kawo abincin da yace a kawo, sannan ya zameni daga jikinshi, yadda ya maida ni cikin kujerar ma ya ajiye kamar wani kwai kadai yasa na bi bayanshi da kallo cike da murmushi, kaunar mijina tana kara dabaibaye ni.
Ya amso abincin ya dawo, da kanshi ya dinga bani abincin nan har na koshi. Daga nan kuma muhawara muka hau tafkawa akan gida zan wuce in huta ba wajen aiki ba, da kyar na samu na iya fahimtar dashi lafiyata lau, kuma zan iya zuwa wajen aikina. Sannan fa ya saka ni a gaban mota ya kaini har ward dinmu, bayan dogon bayanin in kular mishi da kaina fa da baby, ya juya ya tafi. Ya barni da su sister Hajara da suke ta sheka mana dariya.

*

Janan tafi minti biyar tana ihu da shewa, har sai dana kai ga kauda wayar daga kunnena kafin ta kai ga kassara min ji na ina zaman lafiya. Sai data gama ihun murnar, sannan kuma ta hau zuba hamdala, "kai Alhamdulillahi, Allah na gode maka! Yau ina zan kai farinciki a cikin rayuwata?! Finally, Allah ya raba mu da bakar kaska, zamu huta dai. Gari ya waye dukan duhu na yayewa!!". Ta karasa maganar da take yi cikin sautin wakar gari ya waye.

Hakan yasa na saki dariyar da ban shirya ba. Na dawo gida daga wajen aiki. Duk da cewa ba yau na saba dawowa na tarar da gidan babu kowa ba, sai dai wannan karon da banbanci. Wannan karon nasan cewa komin dare babu wadda zai dawo, zan ci gaba da kasancewa ni daya, ban sani hakan ko abin murna da farinciki bane a gareni ko kuwa na jajantawa?

Janan itama tayi dariyar, "Malama kada ki fuske mana, nasan ran nan naki yau fari tas kamar likkafani".
Nace "ke fa baki da kirki wani lokacin wallahi, likkafani seriously?".
Ta kwashe da dariya. Ina tunanin yau dai ba za'a samu yin hira mai ma'ana da ita ba, don haka nace mata taje taci gaba da abinda take yi kawai.

Tace "shine don wulakanci ranar nan kika ce wai baki da ciki?".
Nace "waya fada miki ina da ciki ne?".
"Dalla can, an gaya miki zancen duniya yana buya ne? Zancen cikinki ai ya gama zagaye gari da dangi yanzu, har yaron goye yasan da maganar".

Na girgiza kai kawaI, na manta ba'a maganar sirri da Yaya, musamman wadda ta danganci wannan.
Nace "to naji, je ki cigaba da soyawa maigidanki cin-cin, nima abinci zan zo in dafa mishi".

Ina jin tana guna-gunin wai kada in mata gorin miji fa, na kashe wayar kawai ina dariya.








☆⋆50⋆☆
Finale





Watanni goma sha uku kenan bayan haka, na samu kaina tsaye a kofar gidan a can cikin unguwar Tudun Wada cikin Zaria. Gida ne kadaran-kadahan, amma zaka fi saka shi cikin jerin gidajen ya-ku bayi. Gabadaya gine-ginen unguwarma haka take, kwata, bumps, ramuka da bola sunyi yawa a wajen.

Muhaaseen, diyata mai kimanin wata biyar dana haifa watanni biyar da suka wuce, tana sakale a kan kafadata gefen damana. Sunan Mamata marigayiya taci. Hannunta rike gam da gululun kwalliyar dake jikin jakata tana ja tare da yin wakokinta na yan yara wadanda basa taba kin kawo murmushi kan fuskata. Yanzunma murmushin nake yi a tausashe, kauna ce ta uwa da d'iya Allah ya sanya mana, ko a halin da take ciki na yarinta, ta sanni sosai. Na kara sakin wani murmushi a karo na barkatai, tare da manna mata sumba a gefen kumatunta. Tana jin motsi na tayi saurin juyo da fuskarta, tare da kamo lebbana tana tsotsa, na saki dariya a hankali, gefe guda kuma ina kai hannu ina kara buga kofar gidan.

Bayan wasu dakikai, har na fara tunanin kila ko babu kowa a gidan. Ina shirin juyawa kenan, naji ana taba kofar da daga gani wani katon abu aka sanya daga ciki aka tokare saboda yanayin yadda kofar ta nuna, taga jiya da yau sosai, babu alamun zata iya daukar kwado ko makulli daga ciki.

Wata siririyar bakar mata ta bude kofar, muka tsaya muna kallon-kallo da ita. Yadda ta zare idanu tana kallona cikin wani yanayi mai kama da mamaki da kuma tsoro da shock yasa na kara kallonta sosai, a zuciyata ina tunanin ko na santa?.

Murya na masifar rawa ta ambaci sunana, "Na'ilah?!".
Sai a lokacin ne fahimta ta saukar min, nace "Raheemah ce?".
Tayi kasa da kanta a kunyace, kafin ta dago tace min "shigo mana!". Ba musu na daga kafa na bita cikin gidan.

Kwanaki masu yawa da suka wuce, lokacin da naje Kaduna haihuwa, nake jin labarin hatsarin daya aukawa Raheemah din da 'yan'uwanta a hanyar Nijer. A cewar wadda take bada labarin, mahaifiyarsu a take ta rasu, su kuma sun samu sun fito da kyar, rabin jikin Salame ya kone da wuta, Raheemah kuma Allah ya takaita ta fita ba tare da wasu munanan raunuka ba sai tsagewar kashi da kurjewa nan da nan kawai.
Mummunan hadari ne motar golf din tayi da wata babbar motar mai, Allah ne kadai ya nuna ikonsa da har wasu suka iya fita da rai.
Tun a wancan lokacin naso zuwa yi musu gaisuwa kwarai, Allah bai nufa ba. Sai yanzu da muka shigo Zaria jiya ni da Yaya. Wani babban aminin Babansu ne tun yarinta yayi rashin lafiya har aka kwantar dashi a asibiti. Bayan an sallameshi ne Yaya yace zai zo ya duba jikin nashi ya kuma ga 'yan'uwa, nima na nuna sha'awar ina so in biyo shi. Ko babu komi nima na jima rabona da Zaria.

Can ainihin gidansu na Hanwa na taba zuwa, aka ce min ai tun bayan rasuwar mahaifiyarsu suka koma wajen mahaifinsu da zama. Don haka na juya akalar tafiyar tawa na taho nan, da kyar da kwatance na karaso. Wai don ma mahaifinsu ba boyayyen mutum bane a unguwar.

Tana tafe ina binta a baya, yanayin gidan kawai da suturar jikinta nake karewa kallo, tabbas, babu wanda zai kalli Raheemar dake gabana yanzu yayi tunanin hadata da Raheemar baya. Wato kawai a duk halin da mutum ya tsinci kanshi a rayuwa, ya godewa Allah ne.

Dakin data kaini yafi kama da akurki maimakon falo, babu komi a ciki sai tarkacen kaya iri-iri, daga kwanukan abinci, bokitai, kayan wanki, gasu nan dai birjik kudaje na bi abin babu kyan gani. Ta dauko wata yamutsattsiyar tabarma ta shimfida min a tsakiyar falon, na zauna ina kara kallon wajen.

Tsayawa tayi kikam a kaina tana kallona tana faman susar kai kamar mai fama da kwalkwata, "me ya kawo ki nan wajajen?".

Sai lokacin na maida kallona kanta, "naji rasuwar Momcy ne shine nazo muku gaisuwa. Ya hakuri? Allah ya jikanta".

Maimakon ta amsa min kawai sai naji ta saki dariya, "hahhh.. Su Momcy fa lokaci yayi, hmm!". Ta wani ajiye numfashi. "Ai in gaya miki, labarin wani zazzafan malami muka ji acan cikin Nijer, shine fa muka kama hanya muka tafi. Muka je ya bamu magunguna, wanda zai sa Bilal ya sake ki ya manta dake da cikin jikinki ni kuma ya maida ni, ita kuwa Halimo ta karkato hankalin wannan shegen tsinannen mijin nata kanta, kawai ba sai muka ci karo da motar mai a hanya ba? Sakaran direba kawai, yana ta wa Momcy surutu akan ta bashi lambar wayarta ya hada mu da motar. Dan iska!". Ta ja tsaki kafin ta kwashe da dariya.

Ni kuwa da nake ta binta da kallo cike da mamaki, na sake ware idanu ina kallonta. Dama naji Janan tace wai ance tun bayan rabuwarsu da Yaya, kamar kwalwarta ta tabu haka take, ban tabbatar ba sai yanzu. Ta kalli Muhaaseen da tunda muka shiga gidan ta makalkaleni, haka take duk lokacin data ganta a gaban mutanen da bata sani ba.

Ta zare ido, "laa, wannan ce diyar da kika haifa? Amma fa kyakkyawa ce!". Ta kai hannu kamar zata dauketa, yarinyar tayi saurin kara makalewa a jikina, ni kuwa na sanya hannu na kara riketa tsam a jikina, a can kasan raina ina cewa Tubarkallah. Duniyar yanzu baka san bakin mutane ba.

Ganin na riga na gama yin abinda ya kawo ni, ga wani irin wari da yake tashi a cikin falon da yake kokarin tasar min da zuciya, yasa na mike tsaye ina cewa "bari mu tafi, sai anjima".

Tace "da wuri haka?".
Na kalleta cikin rashin abin cewa, idan na tsaya mai hakan zai kareta dashi?

Tace "to shigo ki duba jikin Salame mana".
Bata jira nace komi ba ta tunkari wata kofa, cikin sanyin da jikina yayi na bi bayanta.

Ina shiga dakin nayi baya da sauri, wannan warin da nake ji a falo sama-sama ya bugo ni full force. Sai lokacin na fahimci daga inda warin yake fitowa. Daga inda nake na hango Salamen kwance acan kuryar dakin kamar kayan wanki akan shimfida, rabin jikinta lullube da mayafi inda aka sakaya private parts dinta.
Naji wani irin tsoron Allah ya kamani a lokacin, lallai shi dai mutum ba a bakin komi yake ba a wajen Allah.
Kamar yau ne fa, suka tareni suna min dibar albarka a cikin gidan aurena, akan mijin da nake aure. Yanzu dana duba baya, lallai ba karamin lokaci bane ya wuce, amma kuma a cikin kaina sai nake ganin kamar yau hakan ta faru.

Da kyar na iya karasawa kusa da ita, da alama ma barci take yi. Itama gefenta kwanuka ne birjik a ajiye, wasu ma daga ganinsu ba karamin lokaci suka dauka anan ba.
Nace "har an sallameku daga asibiti ne?".

Tace "ina fa! Koro mu suka yi saboda babu kudin gado dana magunguna. Ni kuwa nace aikin banza kenan, muka maidota gida. Ai yanzu maganin gargajiya ma ake mata. Shima kwana biyu dai an daina bata ma".

Na gyada kai a hankali, ina so in kara watso mata wata tambayar, amma bakina ya kasa budewa, don haka na dinke bakin nawa kawai na mike tsaye. Ina ji Raheemah ta biyo bayana tana wasu surukai dana kasa fahimtar abinda take cewa, na dai tsinci sunan Salamen da kuma zagin da take dankarawa.

Na kara rike Muhaaseen sosai ina kokarin sanya takalmina, wani zagi data saki ne yasa na daga kai na kalleta cikin mamaki. Tace "kan ubar nan!! Wannan shegen hadadden takalmin fa? Zai yi dubu nawa? Kai, wallahi dama ki bani shi in dinga kwalliya dashi abina".

Ni yanzu tsoro ma take bani kuma, yadda tayi tsaye a kaina tana watso min hakoranta da tsabar rashin wanki yasa suka yi wani yalo-yalo, gani nake kamar a kowane lokaci zata iya kawo min mazga. A karo na farko na fara tambayar kaina tsautsayin daya kawo ni nan. Musamman idan na tuna ta yadda ma aka yi Yaya ya barni na zo gaisuwar nan.

Ban ce mata komi ba, na tunkari kofar fita da sauri, ta biyo bayana. Muna gab da kofar gidan hayaniyar yara ta kusantomu, ihu kawai kake ji da kururuwa.
Haleemo da itama babu banbanci tsakaninta da Raheemah, duk da ita suturar jikinta da yar dama-dama akan ta Raheemah, ta fado gidan hannu rike da fararen manyan plastic bokitai da sauran shinkafa da tarin kabeji a ciki. Tsinin dake cikinta zaka fara gani kana dora idanu a kanta.

Waka da shewar da yaran suke yi ta kara yawa,
_'Yar iska taki zaman aure, daga talla sai yawon iskanci!_
_'yar iska tayi cikin shege...!_

Ita kuma tana korarsu da kayan hannunta tana dankara musu zagi da tsinuwa, har dai Allah ya bata sa'a ta shigo gidan ta maida kyauren ta rufe da sauri tare da daukar wani gingimemen dutse ta jingina da jikin kofar.

Tana juyowa ta kallemu tayi turus! Ta kalli Raheemah tace "wannan fa wacece?".

Raheemah din ta watsa mata harara da sauri, "to uwar yan tsegumi, ina ruwanki da bakuwata?".

Ta tabe baki, "jibeta sakara kawai, banza mai tabin kwakwalwa, to sai me don kinyi bakuwa? Daga gani ma kuskuren gida tayi ba wajenki tazo ba don daga gani bata yi kama da irinki ba".
Raheemah ta tunzura da abinda tace "na dai gode Allah, duk da tabin kwalwar tawa dai ban je nayi cikin shege ba!".

Ta daga baki kamar zata yi magana, sai kuma ta fasa, tayi cikin gidan tana "oho miki dai, mahaukaciya".

Ba shiri na kama dutsen nan na janye da sauri na fita daga gidan, Raheemah ta sha gabana tana wasu yan soshe-soshe.
"To Hajiya Na'ilah, na gode ko? Yaushe zaki sake dawowa? Gashi kin zo ko ruwan sanyi ba'a baki ba. Nasan ba zaki iya shan ruwan randa ba, ni kuwa bani da ko sule balle ko na fiya wata ne a sayo miki".

Ganin take-taken bata da alamar rabuwa dani don wasa da kuma abinda take hinting, yasa na zage jakata na ciro kudin da ko kirga su banyi ba, na mika mata. Ta warta kamar wadda take tsoron zan kwace ta jefa su cikin rigarta. Sai data tabbatar ta boye kudin sannan ta juyo ta hau zuba min godiya, tana lissafo abubuwan da zata sayo taci dasu ta hana 'yan uwan. Ban kara cewa komi ba na juya da sauri, ina ji kamar ma in sheka da gudu.

Please Login or Register in order to submit comment