Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

a gani.. Sai dai son zuciya irin nata ya janyo mana yin rayuwar kunci da wulakanci a lokacin daya kamata ace munyi mabanbanciyar rayuwa.
Sai dai idan na sake duba hakan da wani ido na daban, son zuciya irin nata ne ya tseratar dani daga aikata mugun halin data aikata mana ga sauran abokanan zama na. Allah ya sani, ina da damar yin hakan, ina da fadar yin hakan, sai dai tunanin cutar da wani ta hanyar data cutar damu yakI ya zauna min, na kasa yin hakan. Idan na tuna zafin da naji, idan na tuna tsananin kunar da naji, idan na tuno darare da dama da nayi su cikin kuka da bakinciki da takaicin abinda matar nan tayi a gareni, sai inji ba zan taba iya aikata hakan ga kowa ba. Ba zan taba iya so wani yaji rabi-rabin abinda naji ba.

Sai dai ban hakuri daga bakin Ramata, abu ne da ban taba zaton zanji daga gareta ba, ban kuma shiryawa hakan ba.

Don haka naci gaba da kallonta kawai, har ta gama fadin abinda zata fada, ta juya ta fita daga dakin. Shiru ya biyo baya daga nan, ni da Maryam muka hau yin kallon-kallo, kafin na maida kallona ga kur'anin da nake karantawa.

Zuwa lokacin dana gama, gari ya gama wayewa, yara sun tashi suna ta shigowa gaisuwar safe. Sai lokacin na bude gwangwanin alewar eclairs dana kawo musu, bayan sun gama karba sun fita, sannan fa na koma barci. Ban tashi ba sai wajen karfe sha biyu na rana, shima wayar Yaya ce ta tada ni. Bayan mun gaisa dashi, na tashi na fita tsakar gida.

Babu kowa duk suna daki. Nan na fada bandaki nayi wanka. Sai anjima da yamma zamu tashi, hakan ya bani damar gudanar da duk wasu shirye-shiryena a nutse.

*

Kafin mu tafi na kira Aliyu dakina, na bashi kudi nace washegari ya raka Mamansu asibiti a dubata sosai. In yaso koma menene daga baya, zan kirasu inji.
Har bakin motarmu suka raka mu, Ramata har da kukanta tana ta godiya. Aliyu ya bude min bayan motar na shiga, ya maida ya rufe. Har lokacin kalma daya bata sake hada mu da Ramata ba, saboda ban san abinda yakamata in ce mata ba.
Yanzu da nake kallonta, ita da dan nata da a da, babu abin wulakantawa a wajensu kamar ni, abu daya ne yake min yawo a ka, 'lallai abinda ya baka tsoro, wata rana sai ya baka tausayi!'.

Muna first class ni da Yaya. Bayan jirgi ya gama lodi, aka fara sanarwar tashin jirgi. Kaina yana kan kafadar Yaya, hannuna na dama cikin nashi yana shafawa a hankali. Hankalinshi yana kan jaridar Vanguard yana karantawa.

Na lumshe idanuna a hankali kafin na bude su, ina kallon gajimare da muke ta ratsawa ta cikin tagar dake kusa dani. Na sauke wata doguwar ajiyar zuciya. Dana duba baya, shekara daya data wuce, ban taba zaton cewa yanzu war haka zan kasance akan kafadar mijina, Yaya Bilal, muna tsallaka Nigeria zuwa yin ibada a kasar Makkah ba. Idan na tuna gwagwarmayar da muka sha, da yadda abubuwa suka juye, har zuwa yadda aurenmu ya kasance, sai naji ina girgiza kaina kawai, hikimar Allah da ikonsa suna da ban al'ajabi.
Can kasar zuciyata, na kasa yakice wata murya da take mintsini na, 'shin ban ga aya ba?!'.

Yaya ya shafo kumatuna da bayan hannunshi, hakan yasa na bude idanun da ban san na rufe ba, na sauke su a kanshi. I can't help myself, duk lokacin da zan kalle shi, sai naji tali-talin yawon abubuwa a cikin cikina, tunanin how I've come to be this lucky yaki barina.

Yace "tunanin me kike yi ne haka, kin barni ina fama da takarda?".
Babu tunanin komi nace "kai!". Sau tari bana tauna maganganu irin haka kafin in furta su, Yaya Bilal has that effect on me.

Shi kanshi bai yi zaton amsar da zan bashi ba kenan, ya daga girarshi cikin mamaki, yana wani irin murmushi, "haba? Akan me?".

Na kara gyara kwanciyata a jikinshi, nace "ta yadda aka yi ka fara so na mana. Tell me, love at first sight ce, ko kuma sai a hankali?".

Yaya yayi shiru yana kallona kamar mai tunani, amma kuma har yanzu murmushi yake yi. Yace "kin tuna ranar farko da muka hadu dake?".

Nace "sosai ma. Ranar da kazo ka daukemu ni da Janan ka kaimu Kaduna, lokacin bikinka da Ameerah idan ban manta ba".
Ya girgiza kai, na kalleshi in confusion, "no? Ba lokacin bane?".

Ya jinginar da kanshi akan seat din, hakan ya kara bani damar sake makale mishi.
Yace "zaki iya mantawa, amma ni ba zan taba mantawa ba. How could I?". Yadda yayi maganar ne, yasa na daga kai na kalleshi. Idanunshi na kaina, cike suke da longing da ban taba katarin gani a cikin idanunshi ba.

"Akwai wata rana, da ban san dalili ba, kawai tsintar kaina nayi a cikin mota na tafi Funtua. Ban sani ba, tunanin Yaya Sa'a ne a cikin raina ko kuwa Janan? Na kasa mantawa. Sai dai duk wadannan tunanikan sun bi iska lokacin da nayi tozali da kyakkyawar halittar dana kusa bugewa da motata lokacin dana dora idanuna a kanta a karo na farko. Ban san cewa a take a lokacin tayi awon gaba da zuciyata ba sai da nayi nisa, nisan da ba zan taba iya dawowa daga inda na tafi ba har abada".

Kallonshi kawai nake yi cike da alamun tambaya don ban fahimci inda maganganunshi suka sa gaba ba.
Ya kalleni yana murmushi sosai, da alamu ba karamin dadada mishi rai abinda ya tuno yake yi ba, yace "kin tuna watarana da kuka shiga staff quarters ke da Janan siyan wani abu, meye ma sunan?".

Na zare idanu na kalleshi, mamaki kamar zai kashe ni, ta yaya ma aka yi na manta ranar?.
Watarana muka taba shiga cikin staff quarters, makotan gidan su Anty Sa'a a lokacin suna saida iloka, muka je saye. Ga takaicinmu muka samu babu, akan hanyarmu ta fitowa, muka ci karo da wani kare. Nan muka yi cak muna kallon-kallo dashi, yana shirin juyawa ya kara gaba, kawai Janan da dama tunda muka ganshi, ta fara rawar jiki, sai kawai ta dafe keya ta ranta ana kare. Shikuwa kare yace da wa Allah ya hada mu idan ba daku ba! Nan muka kafa tsere.

Tabbas, wannan rana itace ranar farko da muka fara haduwa da Yaya. Saboda kafin in san abinda yake faruwa, naji mota taja wawan burki, hakan ya tsorata karen ya juya a sukwane. Ni da Janan kuma muka tsaya muna maida numfashi kamar zamu amayar da kayan cikinmu.
Bayan mun gayawa Yaya dalilin daya kaimu nan, neman iloka, ya mana fada sosai. Washegari sai gashi ya dawo da iloka cike da bokiti. Daga wannan ranar duk lokacin da zai zo sai ya taho mana da ita.

Na maida kaina na kwantar a inda yake da ina murmushi, wani irin giddiness ya rufe ni, nace "wow! Lallai ka jima cikin tarkon so na. Amma me yasa baka taba fada min ba?".
Yace "kece dai baki taba fahimtar duk hints din dana dinga nuna miki ba".
Na kara daga kai na kalleshi, "wasu hints?".
Kafada kawai ya daga. Don haka nima na komawa previous position dina, wasu sake-saken naci gaba da yi.


*

Zuwanmu Makkah, da sabuwar soyayyar da muka kulla ta sanadiyar confession din da Yaya yayi a cikin jirgi. Hakan bai hana mu yin wasa ko sakaci da ibada ba. Sosai muka dage wajen ibada da addu'a babu wasa balle kakkautawa.

Kwananmu goma sha biyar a Makkah, mun je Madina ziyara kwananmu hudu muka sake dawowa, tuni mun fara shirye-shiryen juyawa gida nan da kwanaki biyar wanda zai yi daidai da washegarin ranar sallah.

Mun fito daga wata babbar mall ni da Yaya, tsaraba ce na fara hadawa. Hannuwanmu cike suke da ledoji masu dauke da tambarin mall din da suna. Muna fitowa hasken rana ya dalle min ido, wani irin jiri ya kwashe. Da ba don Yaya daya taro ni da sauri ba, da tuni na kai kasa.
Ya dubeni cike da kulawa, "lafiyarki lau kuwa? Na kula tun jiya kike jin jirin nan. Ko zamu je asibiti ne?".

Na girgiza mishi kai da sauri, "a'ah, ba wani abin damuwa bane. Ina ga yanayin weather dinne kawai".
Ya bini da kallo kamar bai yarda da abinda nace ba, kafin ya gyada kai. Mota ya tarar mana, muka hau muka wuce masaukinmu.

Magana ta gaskiya Yaya bai kula da kyau ba, tun muna gida nake irin wannan jirin sai dai bai kai irin wanda nake yi yanzu karfi ba. Gashi tunda azumin wannan ya kama ban sha azumi ko daya ba, tun ina jiran al'adata yau ko gobe, har na hakura saboda lokacin yin ya wuce.

Ina so in yarda da zuciyata da take rada min ko dai? Kusan kullum. Amma ina tsoron disappointment. Ina tsoron kada in sanyawa raina abinda bashi bane, daga karshe ni kadai zan ji ciwon hakan. Don haka na kasa yarda da zuciyata, duk da signs din da nake gani.
Musamman idan na tuna abinda likita tace lokacin da nayi bari, cewa saboda yadda cikin ya fita ta karfi da tsiya, mahaifata ta dan samu matsala. Saboda haka samun ciki a gareni zai yi wuya, ko zan samu to gaskiya ba a shekarun nan na kusa ba.
Abinda yake kara sanya min sanyin jiki kenan.





*☆⋆49⋆☆*




Washegarin ranar da aka yi sallah muka dira a Kaduna da yamma, nan muka kwana washegari muka wuce Zaria da safe. Kafin mu isa Yaya ya sa an share bangarenmu an gyara shi sosai. Tunda muka isa na lalubi gado nake zuba barci, sai can bayan azzuhur na tashi.
Nayi mika a kwancen da nake, kasusuwan jikina suna amsawa suna tuna min gajiyar dana kwasa a cikin yan kwanakin wadannan. Abu na farko daya fara zuwa raina shine abinci. Kada ma dai cikina da yake ta kugin yunwa yaji labari.

Na samu na mike da kyar na zauna tare da jingina da jikin allon gadon. Kamar tana jirana, ina tashi Anty Sarah ta turo kofar dakin ta shigo. Tayi murmushi ganina a zaune, nima na mayar mata da murmushin.
Tace "har kin tashi ne?".
Sai dana ja wata doguwar hamma na sauke sannan na amsa mata da 'ehh'.

Tace "sallah zaki yi kafin ki ci abinci ko kuwa?".
Na girgiza mata kai ina yar dariya, "barni dai in fara cin abincin. Irin yunwar da nake ji ai bana tunanin zan iya kara minti daya a zaune ba tare da wani abu ya shiga cikina ba".
Tayi yar dariya, "abincin yana falo, ko zan kawo miki shi nan ne?".
Na girgiza mata kai da sauri, "a'ah, ki barshi zan fito in ci. Bari in wanke bakina".
Ta gyada kai, "to shikenan. Ina falon", ta juya ta fita.

A hankali na zuro kafafuna daga kan gadon, sai dana dan tsaya a haka, jikina ya waye da jiri-jirin daya zame min jiki cikin wannan yan kwanakin, sannan na tashi tsaye. Na shiga bandakina da yake ta tashin kamshin freshner da antiseptic, na wanke bakina.

Falon na fita, kamar yadda tace, a falon na sameta zaune akan kujera. Rabi'ah na ta guje-gujenta a cikin falon. Ga kulolin abinci nan shirye a kasa an shimfida ledar cin abinci. Babu bata lokaci na zauna na fara zubawa, tun kafin in kai abincin bakina yawu ya fara tarar min a baki.
Anty Sarah tace "Yaya Bilal sun riga sun ci shi da Abban Mimah. Sun tafi can babban gida tun dazu". Kai kawai na gyada mata, yadda gabadaya hankalina ya tafi kan abincin da yake gabana ai bana tunanin zan iya saurarar komi.
Anty Sarah tayi murmushi ganin yadda na dage ina cin abinci hannu baka hannu kwarya, babu sassautawa. Zuba shi kawai nake yi kamar wadda aka ce za'a kwacewa. Tace "ci a hankali, kada ki kware". Na sake gyada mata kai.

Bata sake cewa komi ba, har na gama ci da shan abubuwan data ajiye min. Na ture kwanukan gefe tare da komawa na jingina bayana da kujera saboda jin yadda cikina ya cika tam.
Nace "ina Mimah kuwa?", tunda muka iso sai yanzu muka samu damar gaisawa sosai. Saboda mutane da yadda idanuna suke a rufe da barci lokacin da muka iso, a tsaitsaye muka gaisa.

Tace "taje gida weekend".
Bayan mun dan hiranta kadan, na tashi naje nayi sallah. Kafin in dawo har ta tattara kayan abincin dana bari.
Nace "da kin bari ma ai da na dauke".
Tace "babu matsala wallahi, meye a ciki?".

Na zauna akan kujera, wayata a hannu ina maidawa Janan sakon data turo min ina barci, bayan na tura mata muka cigaba da hira har take gaya min makota da wasu daga cikin 'yan uwan Yaya da suka zo min sannu da zuwa ina barci.
A hankali naji zuciyata ta fara tashi, kamar zan amayo da abubuwan da naci. Nasan ba zan samu lemun tsami a cikin fridge dina ba tunda mun jima rabonmu da gidan.
Na cewa Anty Sarah, "ko zan samu lemun tsami a wajenki? Zuciyata take tashi".

Anty Sarah ta kalleni cikin tunani, ko bata fada ba nasan ko tunanin me take yi. Nima sai ban tanka ba. Ta tashi ta fita, babu jimawa sai gata ta dawo da lemun tsamin.
Na karba na bare na fara sha. Kallona take tayi, kafin ta nisa tace "kin kuwa fadawa Yaya?".

Na kalleta cike da alamun tambaya, "na fadawa Yaya me?".
"Abin arzikin da muka samu mana", ta fada fuska cike da murmsuhi. Kai na girgiza mata.
Take murmushin kan fuskarta ya bace, tace "me yasa?".
Na daga kafada, "I just want to be sure. Bana son sanya mana rai akan abinda bashi bane".
Tace "wata alama kike son gani bayan wadda ta fito baro-baro a jikinki?".
Nace "na gansu nima, but we could be wrong!".

Tana shirin dawo min da amsa, aka turo kofar falon aka shigo. Duk muka maida kallonmu ga kofar, ganin Yaya Bilal sai duk muka ja bakinmu muka dinke, daga ganinmu kaga wadanda suka sha jinin jikinsu.

Yaya yayi kasa-kasa da idanu yana amsa sannu da zuwa din da Anty Sarah take mishi, idanunshi kafe a kaina, ni kuwa na kara lafewa a jikin kujera kamar wadda aka kama ta nannaga karya.
Yace "Allah dai yasa ba gulmata kuke yi ba?".

Anty Sarah tana dariya tace "haba dai Yaya, da girmanmu da komi? Kuma ma akan me zamu yi gulmarka? Kawai dai hirarmu ce muke yi irin ta mata".

Ya zauna akan kujera tare da ajiye bakar leda a kusa dani, yana yar dariya, "to ina zan sani ne? Na ga daga shigowata kun kame baki kun dinke bayan kafin in shigo naji kuna hira. Idan ban tsammaci gulmata kuke yi ba, me zan ce?".

Ta mike tsaye tana kade rigar jikinta, "to bari kuga inyi nan tun kafin magana ta zama babba. Na'ilah sai anjima".
Cikin dariyar da nake yi na amsa mata. Ta sa kai ta fita.

Tana fita Yaya ya kalleni, "har kin tashi daga barcin?".
Nace "ehh".
Yace "fatan gajiyar ta sakeki? Don gobe nake so mu koma Abuja. Nasan ayyuka sun tarar min, kema kuma suna jiranki".
Na gyada mishi kai, "zan iya maneji dai".

Yasa yatsa ya shafo kumatuna cike da tsokana, kamar wata karamar yarinya, "sarkin langwabu. Ban san yaushe kika zama alangwaba ba wallahi baby, kwanannan kin cika son jiki".

Na kuwa langwabe din, "kai Yaya!".
Yayi dariya tare da mikewa tsaye ya fara tunkarar daki, "ga fruits nan hada mana. Bari in rage kayan jikin nan nawa".
Ya wuce daki ni kuma na tashi na shiga kicin na dauko plate da fork.

Bayan anyi sallar la'asar, Yaya ya fita waje. Nima sai na kulle sashen nawa na tafi na Anty Sarah. Nan yan sannu da zuwa suka yi ta zuwa suna samuna har yamma sosai tayi. Muka shiga kitchen dinta muka dafa abinci. Anan muka yi dinner kafin muka koma sashenmu.

*

Sai wajen karfe hudu na yamma muka dauki hanyar Abuja, ko a wajen su Ummah bamu tsaya ba, kai tsaye can muka wuce.
Tunda garin Allah ya waye Raheemah take kiran wayar Yaya tana tambayar yaushe zamu iso? Akalla ta kira yafi sau biyar, yanzu ma muna daukar hanya sai data sake kira, yace mata yanzu muka taho. Cike da murnarta da doki tace "to Allah ya tsare hanya, Allah ya kawo ku lafiya". Yace "ameen".

Na bi wayar hannunshi daya ajiye bayan ya kashe wayar da kallo. Zuciyata na rada min wani abu sounds off da matar nan. Tunda muka bar gidan, kullum sai ta kira waya, ayi hira da ita faram-faram ayi sallama. Duk yadda zuciyata take rada min kan cewa kila ko tayi karatun ta nutsu ne, zuciyata ta kasa kwanciya da hakan. Nasan dai koma menene, tunda gidan zamu koma, idanunmu zasu gane mana.
Yaya bai ma kula da yanayin tunani dana shiga ba saboda yadda hankalinshi yake kan iPad dinshi, tun ma kafin mu koma gidan har ya fara aikinshi. Sai na maida kaina na kwantar akan seat tare da lumshe idanun, babu bata lokaci barci yayi awon gaba da ni.

Ban farka ba sai da muka shiga garin Abuja, sannan. Na gyara zamana ina taba bayan wuyana da naji ya dan rike. Yaya ya kashe hasken wayar hannunshi, da alama shima tunda muka dauki hanya bai ajiye wayar ba, ya bude gorar ruwan sona ya miko min. Babu musu na karba na kafa kai, sai dana shanye shi tas. Ya karba ya rufe gorar.

Balarabe yayi horn, maigadi ya taso da sauri ya bude gate din. Muka gangara da motar ciki, shi kuma ya juya ya maida gate din ya rufe kafin ya kwararo da gudu zuwa inda motar take kokarin yin parking. Ya budewa Yaya kofar motar yana ta zuba mishi ruwan sannu da zuwa, ni kuma Balarabe ya bude min. Duk muka fito daga cikin motar.

Su Balarabe da maigadi suna ta kokarin fito da akwatunanmu da tarkace daga booth, ni da Yaya kuma muka tasamma kofar shiga gidan.

Haka kawai naji gabana ya fara faduwa kamar ana buga ganga, muna tsayawa a kofar falon kuwa naji kaina yana wata irin juyawa kamar zan fadi.
Samuel wanda yake ban ruwan fulawowi da gyaran garden ya bazamo daga bayan gidan hannu rike da tsintsiya, da alamu shara yake ya taho gaisuwar ban gajiya.
Hakan ne ya dakatar damu daga bude kofar falon, muka tsaya suna gaisawa da Yaya. Bayan ya mana sannu da zuwa, ya juya.

Idanuna suka sauka akan matakalar dake manne da kofar wasu irin abubuwa kamar har da danko da lema, babu mamaki wani abu ne ya zuba a wajen. Da sauri na kira sunanshi, ya juyo yana kallona.
Nace mishi "don Allah dan sa tsintsiya ka share wajen nan, kamar yayi datti".
Babu musu ya matso tare da sanya tsintsiya ya fara shara wajen, "to Haji...".

Bai gama rufe baki ba aka turo kofar falon da sauri kamar za'a ballata, Raheemah ta fito a sukwane kamar wata sabuwar kamu tana ihun "kada ka share! Kada ka share!!".

Amma ina! Aikin gama ya gama, tuni ya gama sharewa.

Ta ja tayi turus, muna kallon-kallo. Mu na mamakin abinda ya sanyata yin haka, ita kuma fuska cike da alamun tsoro.
Yaya yace "lafiya?".
Ta kalleshi a dan firgice, kafin ta girgiza kai da sauri, "me? A'ah, babu komi. Dama turaren wuta ne na zuba a wajen".

Yaya ya karya kanshi gefe guda yana kallonta, kafin ya tabe baki, "well, to ina ma amfanin sanya turaren wuta a waje? Muje ko?".

Ya tura kai zuwa cikin falon na bi bayanshi. Strangely, babu wannan faduwar gaban da nayi ta ji dazu. Har Yaya ya gama shigo da kayanmu Raheemah na inda muka barota a tsaye. Sai da na kai akwatina daki na dawo daukar jaka sannan na ga ta shigo falon jiki a sanyaye.
A dan lokutan da muka yi bamu hadu ba, babu abinda ya canza daga jikinta. Ta sha kwalliyarta cikin wani tsadadden paper Swiss lace, daya daga cikin wanda Yaya ya dinka mana na sallah. Babu laifi kuma, sun matukar karbarta.
Kai tsaye dakinta ta wuce da sauri, kamar zata fadi, ni da Yaya muka bita da kallo cike da mamakin wannan halayya. Wa zai yi zaton irin tarbar da zamu samu kenan a yadda take ta faman dokin mu dawo dinnan?.
Yaya ya taimaka min na gama kai kayana daki, shi dama daga brief case dinshi babu abinda ya riko. Daga nan ya wuce dakinshi, ni kuma na fada bandaki don in watsa ruwa ko na warware gajiyar jikina.

Bayan na fito falo na sake fita. Ina zama, Yaya ya fito daga nashi falon sanye da jallabiya baka. Yadda fatar jikinshi tayi wani kyau, da yadda rigar ta bi jikinshi ta lafe kamar second skin, yasa ban san sanda na saki baki ina kallonshi ba har da karkace kai gefe guda. Yadda sajen fuskarshi ya kwanta mishi sosai...
Ban san ya iso kusa dani ba, sai dana ji iskan daya hura min ya sauka a fuskata, na lumshe ido ina murmushi yayin daya zauna a gefena da yake akan two seat nake.
Yace "wannan kallon fa baby? Na nawa ne kuma?".

Na kyalkyale da dariya ina jingina da jikinshi, "yanzu don na kalleka har sai na wani biya?".
Yace "ehh mana!".
Na daga kai na kalleshi, "halalin nawa?".
Shima ya kalleni, tare da sanya hannu yana dan jan hancina, "zakin baki ne zaki yi mun yanzu?". Na sake yin wata dariyar ina kara kwanciya a jikinshi.

Raheemah ta fito daga dakinta, ba kamar dazu da take a hargitse ba, yanzu ta warware duk da daga gani zaka fahimci cewa murmushin dake kan fuskarta bai kai can ciki ba. Lullube yake da damuwa.
Bakinta washe da murmushi kamar zai tsage biyu, "marhabun lale sannunku da zuwa. Ya hanya? Kun sauka lafiya?".

Bata nuna alamun tado zancen abinda ya faru dazu ba, don haka babu wanda ta tayar mata a cikinmu. Muka ce "lafiya lau".
Tace "abincin ku yana kan dinning, ko nan zan kawo muku?".
Yaya yace "sai na dawo daga masallaci".

Ta kalleni, "ke fa Na'ilah?".
Da fari kallonta nayi cike da mamaki da kuma alamun tambaya, banyi tunanin dani take ba. Da sauri na girgiza mata kai, "a'ah, nima sai anjima".

Ta zauna akan kujera dake gab data Yaya, ta fara tambayarshi abinda ya wakana yayin zuwanmu umrah, nan suka cigaba da hirarsu.
Ni kuwa kallo kawai nake binta dashi, mamakina ya kasa boyuwa. Shi kanshi Yayan nasan ba karamin kokari yayi ba wajen boye nashi. Bansan abinda ya tsirar da wannan sabuwar halayyar tata ba, koma dai menene nasan raina baya gaya min da dadi. Nasan hakan baya rasa nasaba da yadda na saba da halayyarta ta mita da tankawa duk wani abu daya dangance ni.

Ana kiran sallah duk muka mike, Yaya ya wuce masallaci, mu kuma muka wuce dakinmu.
Bayan nayi sallah na kunce tsarabar da nayi, na dauki turaren kaya, na miski da ruwan zam-zam na leka har dakin Raheemah na mika mata. Ta amsa da fara'arta tana godiya. Na jima a kofar dakinta bayan ta amshi kayan ta rufe kofarta ina kallon kofar, kafin na juya na koma dakina.

Abinci ma a tsaitsaye na ci shi saboda cikine a cike yake. Dambun kifi dana nama Anty Sarah ta hado ni dashi cike da wasu manyan plastic rubbers. Shi nake ta ci tunda muka iso abina.
Muna gama cin abincin na musu sallama na wuce dakina, nasan yau dai Raheemah ce take a turaka. Kayan jikina kawai na cire na saka na barci na kwanta. Ina kwanciya kuwa barci ya daukeni, ban tashi ba sai da asubahi da Yaya ya shigo ya tashe ni sallah.

Da wuri na shirya shiga asibiti. Jakata dam da kananun turaruka da robobin zam-zam na tsaraba. Ina kan dinning ina hada ruwan shayi, Yaya da Raheemah suka fito. Hannunta daya rike da jakar shi ta wajen aiki, dayan kuma ya sarkafo daya hannunshi. Na kauda kaina gefe ina kokarin danne wani abu mai daci da yake kokarin taso min. Idan nace bana jin irin haka a duk lokacin da naga wata daga cikin matan Yaya tayi kusanci dashi, kamar haka, kai koda bai kai haka ba, to nayi karya. Ina ji, sai dai karfin zuciya da tsananin iya danne zuciyar tawa ne yasa

Please Login or Register in order to submit comment