Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tatacciyar madarar hollandia da gasasshiyar k'afaffiyar kaza. Kamshinta ya hade dakin gabadaya, cikina ya fara juyawa saboda yunwa, amma na kasa motsawa. Ina kallo yayi amfani da wuka karama ya yanka kazar ya zuba a cikin plate, ya kuma tsiyaya madarar a cikin kofunan biyu.

Sai daya gama, ya dago kanshi ya kalleni. Nayi sauri na kauda kaina daga kallonshi da nake yi.
Yace "ba zaki ci bane?".
Nayi shiru ina kallonshi kamar ba zan ce komi ba. Bai sake ce min uffan ba, yayi bismillah ya fara cin abin shi.

Da naga uwar bari, sai na silalo daga kan gadon a hankali kamar wadda kwai ya fashewa a jiki, na lallaba na zauna a gefenshi.
Ina kallon murmushin daya saki a hankali, na turo baki gaba. Ya turo min plate din kusa dani da kofi daya. Kaina a kasa na fara ci bayan nayi bismillah.
Shirun da duk muka yi ni dashi, babu mai motsin kirki a cikinmu shi ya cika min ciki, sai kuwa taraddadi daya kara cika min ciki.

Na kara tsiyayar madarar dake ajiye a gefenmu bayan na shanye wadda ya zuba mana. Ina kallonshi yana cin namanshi hankalinshi kwance, har ya gama. Lokacin nima na shanye madarar dana tsiyaya.
Ya zari tissue ya goge hannunshi, tare da kokarin fara hada kan kayan. Da sauri na riga shi fara daukar kayan, nace "uhm, ka bari zan hada".

Bai ce komi ba, ya dai sakar min kayan, ya tashi ya nufi hanyar bathroom dina. Na bishi da kallo cikin sanyin jiki, haka kawai naji ina tausayawa kaina. Haka tawa rayuwar auren zata kasance kenan?.
Na dauki kayan dai gabadaya na fita zuwa kicin dasu. Na wanke plates da kofunan, sauran kazar da bamu kai ga cinyewa ba, na nade a foil paper na saka cikin fridge. Sannan na koma dakin.

Wayyo faduwar gaba! Zuciyata tayi wani irin bugawa lokacin dana ganshi kwance dai-daya akan gadona, ya dago daga kan wayarshi ya kalleni da alama cikin mamaki ganin yadda naja tunga na tsaya kyam, kamar wata wadda taga wani abin tsoro. Sai dai bai ce komi ba. Ni wannan silent treatment da yake bani ya fara bani tsoro kuma maimakon haushi.
A hankali ya kauda kanshi ya maida kan wayarshi kamar ma bai ganni ba. Ni kuwa naci gaba da kafewa a tsaye a wajen. A kalla nafi minti goma a wajen har sai da naji kafafuna sun kage. Har ya gama latsa wayarshi, ya kashe hasken tare da ajiye wayar a kan bedside drawer.
Ya kalleni yace "idan kin gama, ki kashe wutar dakin". Daga haka ya juya min baya.

Na kara wasu mintunan a tsaye ina kallon bayanshi, kafin daga karshe na yanke shawarar wannan tsayuwar da nake yi anan babu abinda zata kare ni dashi, ga barci da gajiya da suka dabaibaye ni. Idan kuma ba so nake yi inyi barci a tsaye ba, ina bukatar wajen da zan kwantar da hakarkarina.

Na lallaba na kashe wutar dakin, a hankali, cikin sanda na taka zuwa kan gadon kamar mai tsoron a kamata, na kwanta a gefen gadon nima na juya mishi baya. Na sake yin addu'ar kwanciya barci tare da lumshe idanuna. Sai dai wannan karon babu alamun yin barci a cikin idanuna, zuciyata cike take da tsoron abinda zai je ya dawo. Ban san lokacin da barci ya kwashe ni ba. Cikin dare na farka na jini kwance luf akan kirjin Yaya, ban san ko ni ce na gangara wajen da yake ba ko kuma shine ya gangaro inda nake ba, ban kuma damu da in janye jikina ba. Sai ma kara lafewa da nayi, saboda a lokacin ji nayi kamar duk duniya babu abinda ya kai kirjin Yaya Bilal dadin kwanciya sai dumi.

Lokacin dana tashi, ni kadai ce kwance a tsakiyar gadon. Sai kuwa tarin fululluka a gefena da ban san yadda aka yi suka zo wajen ba.

Dan hasken da dakin yayi da kuma motsi da naji a bandaki ya tabbatar min da cewa Yaya yana can. Na juya na kalli agogo, karfe biyar babu mintuna goma, asubahi ta riga tayi kenan. Daidai lokacin da naji karan bude kofar bandaki ana fitowa, nayi sauri na koma na kwanta kamar mai barci.
Ina kallon Yaya yazo ya tsaya a gefen inda nake yana kallona ta idanuna dana dan lumshe.
Ya jima a tsaye yana kallona, har dai naji kallon ya isa haka nan, na danyi motsi. Da sauri naga ya ja da baya, na bude idanuna a hankali na sauke su a kanshi.

Ya wani yi kici-kicin da fuska har yaso ya bani dariya, kamar ba shine ya gama kare min kallo ba yanzun nan.
Yace "lokacin sallah yayi". Na gyada mishi kai tare da tashi zaune, shi kuma ya juya ya fita daga dakin.
Bayan ya maida kofar ya rufe, na sauka daga kan gadon ina yin mika, strangely feeling good and relaxed. Kamar wadda ta samu dadadden barcin data jima bata yi ba. Na shiga bandaki na dauro alwala na fito na tayar da sallah.

Ina nan a zaune har gari ya gama yin haske, Yaya Bilal bai dawo dakin ba. Wani barcin na sake komawa. Sai karfe tara na safe na tashi.

Wanka na fara yi, cikin kayana na fiddo wasu riga da wando na Pakistan na sanya. Na bade jikina tun daga kafa har kaina da turare. Show glass babba guda aka cika min da kayan kamshi iri-iri yan asali irin na mutanen Bare-bari, dama su ba baya ba. Kamshi mai dadi da sanyayar da zuciya. Na dauki gyalen na nada a kaina, na fita falo. Lokacin karfe goma na safe. Babu kowa a falon, kamar yadda naji babu hayaniya a cikin gidan.

Tunda na tashi cikina yake kiran yunwa, na duba kicin da dinning table ko Janan ta shigo da abinci lokacin da nake yin barci, naga wayam. Ina shirin juyawa in koma daki in dauko wayata in kirata, kofar dakin Yaya ta bude.
Ya fito, da alama shima wankan yayi. Ya sanya wandon jeans navy blue da farar rigar top wadda ta dan kama kirjinshi. Sai bada kamshi yake yi. Ya zauna akan kujera yana lalubar remote ya kunna talabijin.

Na duka har kasa na gaida shi, ya amsa yana wani fuskewa. Na girgiza kai a hankali, wannan basarwa ta Yaya Bilal na kasa gane kanta balle dalilinta.

Yace "miko min abinci".

Nayi shiru ina muzurai, ya kalleni cikin mamaki. "Abinci nace!".

Yadda yayi maganar cikin rashin alamun wasa, yasa naji jikina ya dauki rawa cike da tsoro, nace "ai.. uhm... Da naga ana kawowa kwana biyu sai banyi ba".

Ya dago ya kalleni sosai, "to ita wadda take yi girkin, tare aka kawo ku da ita ne ko kuma zata kare ne wajen girka miki abinci? Banda ma rashin tunani, a kawo ki gidan aurenki, ki zauna kina jiran wata ta dafa abinci ta kawo miki? Lalaci kenan ko kuma duk cikin rashin so ne!?".

Na daga kai da sauri, kuma cikin kaduwa na kalleshi. Shima kallona yake yi, fuskarshi babu alamun nadamar abinda ya fada. Sai a lokacin na fahimci dalilin hade fuskar da yake tayi. Naji wata kwalla ta cika min idanu, a hankali nayi kasa da nawa kan.
Na daga baki da kyar, nace "kayi hakuri... Bari in dafa maka yanzu". Na tashi cikin sanyin jiki, na shiga kicin.

Tsayawa nayi a tsakiyar kicin din ina share hawayen da suka fara zarya a fuskata, wace irin rayuwar aure ce haka muke yi ni da mijin aurena?. Sai dana dan nutsu, sannan na fara dube-dube ina neman abinda yakamata in dafa mishi mai sauki.

Da yake kicin din shake yake da kayan abinci kala-kala, sai na shiga store na dauko ledar cous-cous. Na bude fridge da yake shake da vegetables da abubuwan gwangwani, na ciro abubuwan da nake bukata. Fridges din guda biyu ne, daya na kayan miya, nama da sauransu, dayan kuma na ruwa da soft drinks.
Cikin sauri nayi vegetable sauce, na dafa cous-cous din, tare da hadawa da ruwan shayi.

Na zuba mishi komi, na dora akan tray na fita na kai mishi. Yana nan zaune a inda yake, na hada komi a gabanshi, na koma gefe na zauna.

Kasa ya sauko, ya dauki cokali zai fara ci, sai ya dakata ya kalli inda nake.
Yace "ba zaki ci ba ne ke?".
A hankali na girgiza mishi kai.

Yace "me kika ci?".
Ban ce komi ba, na sake girgiza mishi kai.

Yace "to matso maza ki sa hannu ki ci, bana son zama da yunwa".
Na matsa a hankali kusa dani, na dauki wani cokalin nima na ci. Wannan karon ma har muka gama babu wanda yayi magana a cikinmu, ya tashi ya kwashi wayoyin hannunshi daya ajiye a kan center table, yace min ya fita.
"Allah ya tsare", kadai na iya ce mishi. Yasa kai ya fita.

Bayan fitarshi na maida kayan kicin nazo na zauna ina kallo cikin rashin dadin rai. A haka Janan ta shigo ta sameni. Zuwanta ne ma ya dan sanya na saki jikina, muka shiga hira da ita. A bakinta ne naji ashe Yaya da kanshi ya cewa Anty Sarah kada ta kara turo mana da girki nan. Nayi kwafa a cikin raina, amma ban ce komi ba.


*


Yau ma ana yin sallar isha'i ta tsere sashen Anty Sarah. Ashe a can ta kwana jiya ma, wai Raheemah rufe mata kofa tayi. Na jinjina girman al'amarin, nace 'Allah ya kyauta', tace ameen.

Yau tun kafin in kwanta Yaya ya dawo. Na kai mishi abincin dana girka mishi, ya ci ya tashi ya tafi dakinshi, ni kuma na dauke kayan. Na koma daki nayi shirin barci, na kwanta.

Ina jin lokacin daya shigo dakin har ya kashe wuta, yazo ya hayo kan gadon ya kwanta shima, ban motsa ba.

Lokacin da naji ya matso zuwa tsakiya gadon, hannunshi yana ratsawa ta kan ruwan cikina, kanshi kwance akan kafadata, ji nayi kamar an tsayar da duk wani gudun jini a jikina. Nayi sak, hatta da numfashina sai daya tsaya cak.

Cikin wata irin murya, kamar ba ta Yaya Bilal din dana sani ba, yace "amarya ta!".

Naji wasu irin emotions a cikin raina kala-kala, iri-iri, har na rasa da wanne zan ji. Idanuna suka ciko da hawayen dana rasa dalilin su, murya a cushe, kamar zan fashe da kuka, nace "amaryar da ake fushi da ita?".

Ya sake janyo ni cikin jikinshi sosai kamar zai balla ni biyu, yace "to Na'ilah ya kike so inyi ne kam? Kiri-kiri fa haka kika fito kika nuna duk duniya baki da makiyi kamata, kika ki aurena, saboda tsabar rashin so ma har suma kika yi fa da kika ji labarin an daura miki aure dani ba wani ba. To ya kike son inyi? In dinga binki sawu da kafa, duk da rashin son da kika nuna min? Anya Na'ilah, anya baki so kanki da yawa ba kuwa?".

Na hadiye wani yawu daya tarar min a baki, nace "wa yace maka na tsane ka?".

Yace "ko baki fada ba Na'ilah, yadda kika badawa idanunki toka kika ki aurena kadai ya isa ya tabbatarwa da mutum cewa baki so na. Ba wannan ba, tunda abinda ya faru ya riga ya faru, me zai hana ba zamu bar abinda ya faru a bayanmu ba, mu fuskanci gaba? Mu fara rayuwar aurenmu ta hakika? Don in fada miki, aurena dake babu saki. Idan ma zaki hakura ne, ki hakura. Ba ki tunanin jan aji da yawo da hankalin ya isa haka?".

Na turo baki kamar yana ganina, "wa yace maka jan aji nake yi?".

Ya kara matsoni jikinshi, kanshi yana kara nutsewa a cikin gashin kaina, yana kara shakar daddadan kamshin da yake yi.

Muryarshi bata fita sosai saboda yadda ya gashin kaina ya rufe mishi baki da fuska, yace "nace miki rashin so, kin ce ba haka ba, shima jan ajin kin ce ba haka ba. To menene? Tsabar so ce, uhmm??!".

Na daga baki da niyar bashi amsa, hannunshi da yake kan ruwan cikina ya fara zana circles, jikina ya dauki rawa kamar ana kada min mazari, na rasa muryar maida mishi martani.

A hankali naji ya juyo dani, hannunshi daya yana shafa gefen fuskata zuwa bayan wuyana, kafin ya hade bakinmu waje guda. Na lumshe idanuna a hankali, savouring the moment.

Zuciyata tayi nauyi, tunanina yayi nisa, babu abinda nake ji kuma nake fahimta a lokacin sai Yaya Bilal kadai da abubuwan da yake min, da kuma abubuwan da suke haddasa min a jinin jikina.

Zuwa can naji komi ya tsaya cak, kamar da can babu abinda yake faruwa. Na bude idanuna a hankali, na daga kaina da niyar ganin abinda yake faruwa.

Sai dai abinda naci karo dashi ne ya bani mamaki, ta wani bangaren kuma yaso ya sanya ni kyalkyalewa da dariya.

Yaya Bilal barcinshi yake shaka tsakaninshi da Allah akan kirjina, har da jan minshari!.









#F.W.A




*☆⋆37⋆☆*





Da asubah Yaya Bilal ya tashe ni, ban ma san lokacin da barci ya dauke ni ba jiya. Ya fita masallaci, ni kuma na dauro alwala nayi sallah ta.
Yau bai tsaya a waje ba, gari yana fara yin haske ya dawo cikin dakin. Ina zaune ina lazumi ya shigo, ya koma kan gado ya nade, ni kuma naci gaba da lazumi na. Ina gamawa kuma kicin na shiga, na hada breakfast mai kyau, na gyara ko'ina ya fito fes, sannan na koma daki. Har yanzu Yaya barci yake yi.

Na shiga bandaki da niyar yin wanka, kafin in fito Yaya ya bar dakin. Bayan na fito, na shafa mai, yar hoda da man lebe, na janyo wata doguwar rigar buba ta atamfa na sanya. Na bade jikina da turare kamar ko yaushe na fita falo.

Har yanzu Yayan bai fito ba, don haka na zauna akan daya daga cikin kujerun falon ina jiran ya fito. Kafin ya fito dinne na kira Maryam wadda naga missed call din da tayi min jiya da dare yau da safe, muna cikin hira da ita kofar dakin Yaya ya bude, na juya na kalleshi lokacin daya leko daga ciki.
Yace "kawo min abinci na nan Na'ilah".

Muka yi sallama da Maryam, na dauki kayan na wuce dakinshi. Yana tsaye a gaban mirror yana fesa turare a jiki na shiga, ya ajiye kwalbar turaren, ya matso ya karbi kayan hannuna ya ajiyesu a can gefe. Na koma kicin na dauko babbar ledar cin abinci nazo na shimfida, sannan na zauna na hau zuba abincin.

Ya gama abinda yake yi, yazo ya zauna, na tura mishi abubuwan dana zuba gabanshi. Sai daya zauna sosai sannan na gaida shi, ya amsa min fuska da walwala da fara'a, hakan ya sanyaya min zuciya kwarai.

Ina kokarin zuba nawa abincin, ya katseni, "dauki cokali ki sa mu ci wannan, idan mun cinye sai a kara. Ko ba zaki ci dani bane?".

Nayi saurin girgiza kaina, "ni ban ce ba", na dauki cokalin nasa na fara ci, Yaya yayi dan murmushi.
Shiru tunda muka fara cin abincin, babu wanda yayi magana.
Zuwa can yace "an riga an gama komi, a can Abuja zaki yi internship dinki. Ina fata babu matsala?".

Da sauri na girgiza mishi kai, nace "a'ah, babu. Nagode".
Yace "meye na godiya kuma? Kunshin hannunki yayi kyau matuka". Ya canza akalar hirar tamu.

Na dan saci kallon hannuna na hagu dake kan cinyata. Ni kaina da kunshin yake hannuna yana burgeni sosai, don ya tsaru ne.
Ban tantance ba naji ya kamo hannun nawa cikin nashi, na kalleshi a dan kunyace, amma shi ko a jikinshi. Ya cigaba da cin abincinshi a nutse, kamar babu abinda ya faru.
A hankali nayi kokari na zame hannuna daga nashi, sai dai ina maida shi inda yake da, naji ya sake janyo shi. Wannan karon kyam ya rike idanuna cikin nashi kamar wanda yake challenging dina akan in sake janye hannun, sai nayi kasa da nawa idanun, na kuma kyale shi. A haka muka gama cin abincin.
Nayi tsam na tashi, na fara hada kan kayan na kai kicin. Na tsaya na wanke su ma ajiyesu a inda yakamata, sannan na koma falo. Na dauki remote na kunna tv ina kallo har Yaya ya fito cikin shirin fita.

Ya tsaya a gefena yana daura agogon hannunshi, "zan fita, nasan sai zuwa dare zan dawo yau don haka kada kiyi abincin rana dani. Babu wata damuwa dai ko?".
Na girgiza mishi kai.

Ya sanya hannu ya dago habata yadda muke kallon juna ta cikin ido, kallon tsakiyar idanunshi ba abu bane mai sauki, ji zaka yi kamar an sanya sarkoki an daure duk wasu gabban ka masu motsi, yayin da a gefe guda kuma zaka ji kamar an dauko wani dutse ne an aza maka aka, ka kasa motsi.

Yace "wai kin koyi rashin magana ne yanzu ko kuma rowar muryarki kika fara ne? Kodayake, har da laifina ma. Saboda ba'a sayi bakin ki bane ba ko?".
Nayi saurin girgiza mishi kaina ina dan murmushi, ya sake girgiza kanshi, "uh uh?!".
Nace "a'ah, ba haka bane".

Sai lokacin ya sakeni, yace "to ko ke fa? Ki dinga hana ni jin muryarki, baki san muryarki tana da dadin saurare bane?".
Ni na rasa ta ina Yaya Bilal ya zama frank and blunt ba, ko kuwa dama can haka yake?. Ina shirin bashi amsa wayata dake gefena ta shiga yin kara, kafin in kai hannu in dauka, Yaya ya riga ni. Ya kalli sunan mai kira, ya kalleni girar sama data kasa a hade.

"Waye kuma wani Hamza cm?", ya tambaya cikin hade fuska.
Nace "classmate dina ne", tunda aka daura min aure nake samun kiran waya daga yan ajinmu da muka gama makaranta dasu suna taya ni murnar yin aure.
Bai ce komi ba ya kashe karan wayar, ya saka ta cikin aljihun rigar shi. Yace "bari in fita".

Na mike na mishi rakiya har bakin kofa, nace "Allah ya tsare, a dawo lafiya".

Yace "ameen baby na, sai na dawo".
Ya wuce, ni kuma na maida kofar na rufe ina murmushi kamar wata kuntacciya. Damn, why does it feel so good to be his baby again?!.

Bayan ya tafi, gidan na rufe na tafi sashen Anty Sarah. Janan da Mimah na falo suna karin safe lokacin dana shiga, Anty Sarah kuma da alama tana daki.
Muka gaisa dasu, Janan ta min tayin abinci nace na koshi, na nemi waje na zauna ina kallo har suka gama. Nan Janan ta dawo wajena muna hira da ita, har Anty Sarah ta fito daga dakin Yaya Jameel, Yaya Jameel din yana bayanta hannunshi dauke da Rabi'ah.

Muka gaida su, suka amsa, Yaya Jameel din yana ta tsokanata har dai ya fita. Anty Sarah ta zauna muka cigaba da hirarmu.
Sai da azahar sannan muka koma bangarena ni da Janan. Bayan na dafa mana abinci mai sauki, muka ci. Janan ta tafi karbo min dinkin data kai mana, ni kuma naci gaba da zama anan har ta dawo.

Dinkunan sunyi kyau matuka, tace "sauran sai dai ko zuwa ranar juma'ah ne ko asabar aje a amso miki, na yiwa Is'hak magana zai je ya amso miki".

Na gyada mata kai cikin daukewar hankali lokacin dana daga wata riga, na hangame baki da hanci cikin mamaki, nace "meye haka nake gani wannan Jan? Wannan show me din ai yayi yawa".

Tace "ke ja can! Wani irin yawa kuma? Ba mijinki zaki yiwa kwalliya dasu ba?".

Ban kulata ba na tashi na hau gwada kayan. Na cire wata doguwar riga da tsabar tsagar da aka yiwa hannuwanta, baka banbanceta da vest sai idan kaga dogayen lebatun da aka mata, na ja tsaki, nace "gaskiya baki kyauta min ba Janan, wannan ai bata min kaya kawai kika sa aka yi ba wani abu ba".

Janan tayi murmushi, tace "kada ki damu matar Yaya, zaki gode min ne nan gaba".

Haka dai na hada kayan naje na shirya su cikin wardrobe, sai dai bani da niyar sanya su a cikin raina koda kadan. Kawai na riga na gama rayawa raina asarar kaya da kudin dinki Janan tayi.

Na koma falo muka cigaba da hirarmu ni da ita, har yamma tayi, Is'hak da zai kaita gida ya mana sallama da yake yau zata koma gida. Na rakata har bakin motar muka yi sallama da ita cike da kewa da kauna.
Anan muka hadu da Mimah itama tazo mata sallama, naja hannunta muka koma sashena, na kunno mata cartoons tana kallo, ni kuma na shiga kicin na fara hada dinner.

Da dare sai ga Yaya Bilal ya dawo da sabuwar waya kar a kwalinta, da sabin sims guda biyu.
Nace "ita fa waccan wayar tawa?".

Bai ko kalleni ba, yana ta tura abincin dana girka mishi, yace "nayi kyauta da ita!".

Na turo baki gaba kamar zanyi kuka, nace "amma fa akwai lambobin mutane da dama da zan rasa, kuma za ayi ta kirana ba'a samuna!".

Yace "manufar hakan kenan ai dama, ba zai yiwu in zauna in rabbe hannu a kirji ba ina kallo wasu gardawan kawai na kira min mata ba. Ban yarda ki ba kowa lambar wayarki ba sai wanda ya dace, kina ji na?".

Duk da na jinjina wannan karfin iko da mallaka, hakan bai hana ni amsa shi ba, nace "to, nagode, Allah ya kara budi".

Ko baiyi tunanin zan amince cikin sauki ba ne? Ya kalleni cikin mamaki, kafin yayi murmushi yace "yauwa baby na, ko ke fa?". Muka cigaba da cin abincinmu.

Bayan mun gama, ya wuce dakinshi zai watsa ruwa a cewarshi, ni kuma na koma dakina nima. Nayi brush, na fito na sanya kayan barci, nayi shafa'i da wutiri, sannan na kwanta.
Ban jima da kwanciyar ba sai gashi ya turo kofar dakin ya shigo. Ya kashe wutar dakin tare da hayowa kan gadon da nake, ya janyo ni cikin jikinshi.
Gabana dukan uku-uku yake yi, musamman lokacin da naji ya fara aika min nauyayan sakonni a cikin sassan jikina. Sai da tafiya tayi nisa, ni a kaina na fara fita daga hayyacina, naji tausassan sautin minshari yana tashi a kusa dani. Sai dai wannan karon, ban samu kaina da darawa kamar jiya ba, daga kai nayi ina kallonshi cike da mamakin abinda yake faruwa. Wani abu a tattare da wannan lamari just seems off.


*


Wasa-wasa abin dariya fa yake neman juyewa ya zama abin kuka. Kullum haka abin yake kasancewa, wani abin mamaki ma shi Yayan kamar bai san hakan tana faruwa ba. Saboda washegari normal zamu tashi ni dashi, babu wata alama ta ya tuna abinda ya faru a daren daya gabata a tattare dashi. Damuwa ta fara lullubeni, tunani ya fara addabata, tabbas akwai wata a kasa. Sai dai kafin in tono abinda yake a kasan, har ranar Lahdi ta zagayo, ranar dana fita girki, ranar da zamu koma Abuja kuma.

Ranar tun da safe na gama hada duk wasu kaya da zan tafi dasu. Duk wadanda yakamata mu yi sallama dasu, mun riga mun yi.
Karfe hudu Yaya ya leko yace min in fito zamu tafi, tun dazun aka fitar da kayan dana riga na shirya. Su kuma kayan dakin na samu manyan ledoji na lullubesu saboda kura.

Na fito tare da kulle kofata, na saka makullin cikin jakata.
Na leka sashen Anty Sarah na sanar da ita zamu wuce, ta saba Rabi'ah a kafadarta muka fito ni da ita.
Yaya Bilal da Yaya Jameel suna tsaye a gaban motar suna tattaunawa, muka tsaya anan gefensu muna jiran Raheemah ta fito. Sai yau kannen nata suka hada kan kayansu suka tafi. Da safe naga ana ta fita da kaya da tarkace, kusan zaryarsu biyu. Wani saurayin Salame ne yake ta zaryar kai kayan da dawowa ya lodi wasu. Na fito daga sashen Anty Sarah da safen, naci karo dasu sun fito kowacce na jan akwati kamar zasu je ci rani. Suna ta kwashewa mai motar albarkar saboda ya tsaida su suna ta jiran shi, suka daka min harara lokacin da suka ganni, ni kuwa na daga kafada na wuce abina.

Sai da muka kusa yin mintuna biyar muna jiranta a wajen, har sai da Yaya ya kai ga kiranta ya tunatar da ita muna jiranta fa, amma babu ita babu alamunta.
Yaya ya shaka, ya bude min gaba tare da umartata akan in shiga mu tafi, Yaya Jameel

Please Login or Register in order to submit comment