Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

nake a gajiye, barci bai taba isata ba, wanda nafi danganta hakan da gajiyar mota.

Sailu kuwa tunda muka zo ta fada kicin ta hau girki, nan da nan gida ya bade da kamshi. Ina so inje in tayata yin girkin, amma kwata-kwata na kasa motsawa. Wani irin barci ne ya fara fuzgata ba tare dana shiryawa hakan ba.

Sailu ta fito daga kicin, ganina a kwance yasa ta dakata tana kallona, Malam da Abul-khairi suna ta wasan su a tsakiyar falon. Na dago kai a dan galabaice ina kallonta, tace "wai lafiyarki lau kuwa? Tunda muka dawo kika wani langwabe a kan kujera kamar wata mara lafiya?"

Nace "wallahi nima ban sani ba, ina ga kamar gajiyar hanya ce har yanzu bata sake ni ba".

Ta kyalkyale da dariya, "hahh, ina ruwan ba sabon shiga ba! Idan ma zaki warware ki san abinda yake damunki, ki mike. Ko in zo inyi palpating dinki ne?".

Na tashi zaune da kyar, "palpat... me??", na zaro ido, "ba fa haka bane, bani da komi, da gaske".
Ta gyada kai tana dan murmushi, "kada ki wani gaya min ba haka bane, duk ga alamu nan sun bayyana a jikinki?".

Nace "kin dai san wannan abin fannina ne ko? To bani da komi da gaske".
Tace "to ai shikenan, kada dai ki koma barci don an kusa kiran sallah". Ta koma kicin, nima haka nan na tashi na bita kenan din ko jikina ya dan warware.

Kwana na biyar cur anan, sannan na musu sallama na tafi. Wannan karon motar Kaduna muka wuce kai tsaye, sai wajen karfe hudu muka shiga cikin Kaduna. Jikina yadda kasan an yi min dan banzan duka haka nake ji, ban taba jin wuyar tafiya ba sai yau.

Direban gidan su Ummah yaje ya dauko ni daga tasha zuwa gidan. Nan na samu tarba mai kyau daga wajensu. Su Firdausi suna makaranta, aka kaini dakinsu nayi wanka da sallah, sannan naci abincin da aka kawo min. Saboda gajiya ma ban iya cin komi ba, na koma na baje anan kusa da kayan.

Sai da Yaya ta leko sannan na tashi da kyar, ganin yadda nayi daidai yasa tayi dariya, tace "ki koma kan gado mana ki kwanta, kwanciya a kasa ba dadi, ga sanyin tiles. Ke kuwa yanzu sanyi zai iya cutar daku a halin da kike ciki", ban fahimci komi take nufi da mu ba, na tashi na koma kan gadon na kwanta dai.

Washegari a gidan Janan na yini. Itama tunda na isa, zancenta daya, na harbu. Duk yadda naso in fahimtar da ita akan ba haka bane, kin yarda tayi.

Tana dariya tace "wai ki hakikance akan abinda baki gwada kin tabbatar da gaske bane ko ba haka bane? Ni naga abinda na gani, ke dai da idanuwanki suka rufe kika kasa ganin komi, sai kije kiyi tayi".
Na kada mata idanu sama, na dauki kankarar da ta dalilinta ne maganar ciki ta taso, na kai baki ina harararta, "sai kuci gaba da lakaba min abinda bani dashi ai, ku zaku yi disappoiting din kanku!".
Tace "to ai shikenan, zamu gani".

Sai da nayi sallar la'asar sannan na mata sallama, muka wuce Abuja.









*☆⋆43⋆☆*




Saboda tsabar gajiya washegari ko asibiti kasa zuwa nayi. Yini nayi cur akan gado, ga yunwa da take ta rarakar min ciki amma na kasa samun kuzarin fita. Sai yoghurt da maltina nayi ta durawa a cikin cikina wadanda na jera su a cikin firjin, har sai da naji kamshinsu yana neman sanya ni amai sannan na kyalesu.

Sai can da yamma sannan na iya tashi, wani abin mamaki kuma babu gajiya balle ciwon jiki, sai lokacin nayi wanka, na dauki wata doguwar riga yar Saudiya, ruwan madara na saka a jikina. Nasan lokacin Yaya ya kusa dawowa daga wajen aiki, ranar Raheemah ce take yin girki.
Falon Yaya na wuce, wayar hannuna a hannuna. Sai da yammar nan sannan naga tarin kiran dana rasa da sakonni, tunda na dawo wayar take cikin jaka, ban daga ta ba sai yanzu.

Yaya Bilal naso in fara kira ganin kiranshi har sau uku, da sakonshi da yake tambayar lafiya ban dauki wayarshi ba? Sai dai ina zama, sai gashi ya fado falon. Da alama yau ya tashi da wuri daga wajen aiki.
Na mishi sannu da zuwa, daidai lokacin da Raheemah da Ameerah suka shigo suma kusan a lokaci guda. Ya amsa yana kokarin cire neck tie din shi, "lafiya nayi ta kiran wayarki baki dauka ba?".
Nace "gajiyar hanya ce ta hana ni ko motsi yau wallahi, sai yanzun nan na gani".
Yace "ok", ya shiga daki, Raheemah ta bi bayanshi, Ameerah kuma ta samu waje ta zauna.

Babu wanda yayi magana a cikinmu, ni Janan ma na kira da naga nata missed call din, muka sha hirarmu da ita har sai da Yaya ya fito zai tafi masallaci, sannan muka yi sallama. Nima dakina na wuce da niyar yin sallar na bar su anan.

Sai da naji motsinsu a babban falo sannan na fita nima.
Yaya na zaune akan kujera, su kuma sun sanya shi a tsakiya. Sai naja kujerar dake fuskantarsu na zauna.

Raheemah tana bude kwanon abincin, wani kamshin kifi daya bugo min hanci, ba shiri na ja da baya ina yatsina fuska. Wani irin yawo naji diyan hanjina suna min a cikin cikina.

Kwana biyu na kula yanzu tana kokarin zubawa Yaya abinci da kanta ba kamar farkon dawowarmu ba. Ko kuwa don taga daga ni har Ameerah ba ma barinshi ko ruwa ya zuba da kanshi? Ita dai ta sani.

Sai dana bari duk suka zuba nasu, ina kallo Ameerah tayi wancakali da nata plate din, ta tsoma cokalinta a cikin abincin Yaya. Na jinjina kai kawai tare da jan plate nima na fara zubawa kaina. Macaroni ne jollop, da ya sha kifi da nama sai lemun exotic na abarba da kwakwa, da ruwan gora. Duk yadda nayi ganin cewa na hana warin kifin nan damuna, kasawa nayi, don haka abincin ma kadan na zuba kawai. Idan da ba don yunwar da nake ji bama, babu abinda zai saka ni cin abincin nan. Haka nan dai na cije baki na kai cokalin farko bakina. Tun ma kafin in saka shi a bakin nawa, wani irin amai ya tuko ni kamar me.

Da sauri na ja kujerata baya na tashi cikin sauri na fada bandakin dake nan cikin falo, ina shiga na fara amayar da duk abubuwan dake cikin cikina.
Yaya daya biyo bayana da sauri, ya fado bandakin shima. Shi ya taimaka min na tashi saboda yadda nake jin gabadaya gabban jikina sun kasa motsi ga wani jiri da ciwon kai. Ya taimaka min na wanke bakina, ya gyara wajen dana bata sannan ya tallabo ni muka koma falon. Matan nashi na zaune, suka biyo mu da kallo har ya kwantar dani akan kujera.
Ya juya ya kallesu yace "Raheemah miko min ruwa".

Bata ce komi ba, ta dauko gorar ruwa daya ta tashi ta kawo mishi. Ya tallabo ni na dan tashi zaune, ya kafa min gorar a baki, dan kadan na sha na koma na kwanta. Ya rufe gorar ya ajiye, ya dafa kaina da tunda muka fito nake dafe dashi.
Murya cike da damuwa yace "me yake damunki ne? Dama baki da lafiya ne?".

Na girgiza kai a hankali, "a'ah, ciwon kai ne dai nake ji kadan, da alamu na gaji ne da yawa".

Yace "me zaki ci to, zaki iya cin abincin in kawo miki wani?".
Gabadaya na rasa kuzarin yin magana, kai kawai na iya girgiza mishi.
Yace "to me kike son ki ci?".
Nan ma na sake girgiza mishi kai, ya dan yi frowning, "kin san ba zan taba barinki ki kwana da yunwa ba ko baby? Ki fada min abinda kike son ci idan na dafawa ne sai a dafa miki".

Nayi shiru ina tunanin abinda zam ce mishi amma kuma ji nake kamar duk duniya babu abinda zai iya shiga cikin cikina yanzu. Ya fara jero sunayen abinci kala-kala, har da su Chinese da Italian, daga karshe dai nace mishi salad.

Ya shafa kaina har yanzu damuwar fuskarshi bata bar shi ba, yace "bari yanzu a siyo miki, sannu kinji?". Na gyada mishi kai, shi kuma ya tashi ya dauki wayarshi. Ban san me yace ba, na dai ji yana maganganu kasa-kasa, yana gamawa ya dawo kusa dani ya zauna. Ba ayi minti talatin ba, aka kawo salad din a cikin take away, na tashi zaune shi kuma ya zauna a kusa dani. Da kanshi ya dinga bani, na kuma samu naci da yawa.

Ina gama ci, na tashi nace mishi zan wuce daki in kwanta, nan na musu sallama, yana biye dani har zuwa dakina. Da kanshi ya taya ni sanya kayan barci sai da yaga na kwanta sannan ya kashe min wutar dakin. Babu jimawa barci ya dauke ni.
Washegari na koma bakin aikina.


*


Kwanana biyu da dawowa, a hankali na fara lura da canje-canjen da jikina yayi. Misalin yadda fatar jikina tayi wani irin smooth da taushin da karya mutum yake yace na mayuka ne, ga wata kasala da nake yawan ji, yawan barci da jin yunwa duk da dai bana wani zabar abinci. Da dai sauran canji da na kasa kawar da kai daga garesu.

Na fara tunano maganganun su Sailuba da Janan, da irin assumption dinsu. Amma na kasa yarda da hakan.

Na fito daga bandaki jikina daure da towel, da kuma dan karami a hannuna ina kafar da lemar jikina. Na tsaya a kusa da doguwar mirror din dake cikin dakin, ina ganin ilahirin jikina tun daga tafin kafata har kaina.

A hankali na kai hannu na shafo shafaffe kuma damammen cikina da yayi kamar ba yanzu na gama dura mishi abinci ba. Saman hancina, kumatuna da kuma kasan habata sun fara fitar da wasu kananun fararen abubuwa, su kuma ba kuraje ba, (blackheads), lokaci zuwa lokaci na kan yi su, amma sai a halin da nake cikin stress, damuwa, ko kuma lokacin sanyi. Sai dai yanzu ba sanyi bane, bana cikin wata damuwa kuma ko stress, saboda haka fitowarsu a fuskata a halin yanzu, abin mamaki ne. Cikin wadannan tunanikan na kammala shiryawa. Na fito da uniform dina da suke a wanke a goge, na saka.

Ina cikin gyara zaman hijabita a jikina, Yaya ya turo kofar dakin ya shigo hannunshi rike da brief case dinshi.
Yace "kin gama shiryawa?", nace "ehh, nayi zaton har ka tafi ne?".

Yace "a'ah. Yau direban ba zai shigo da wuri ba, muje in sauke ki ko?".
Ba musu na dauki jakata na rataya, muka jera ni dashi muka fita. Ya tsaya na rufe kofar dakina, sannan muka wuce. Ina ganin Ameerah tana lekenmu ta tagar dakinta lokacin da muka wuce, Raheemah kuma tana falo a zaune kamar wadda take jiran Yayan.
Da yake yau Ameerah ta fita daga girki, ni kuma na amsa, nasan ba lallai sun hadu ba.

Tana ganin fitowarmu ta tashi tsaye, a tsaitsaye ta amsa gaisuwar dana mata, ta kalleshi, "kasan bikin Haleemo next week ne ko?".

Ya kalleta cikin nuna alamun rashin damuwa, yace "sai aka yi yaya kuma?".
Tace "dama ina so ne inje in amso dinkin dana kai mana, daga can kuma zan shiga kasuwa in sayo wasu kayayyaki".

Ya gyada mata kai, a lokaci daya kuma yana daga kafa ya fara tafiya, "sai kin dawo to!". Ganin haka nima yasa na bi bayanshi.

Da sauri ta biyo mu, "bani da ko kwandala fa, kuma kudin dinkin da yawa".

Ya dan dakata, kamar ba zai ce komi ba, kafin yaci gaba da tafiya, "babu cash a hannuna, zan turo miki idan na karasa office".
Babu godiya kamar wadda ta bashi ajiya, ta juya ta koma ciki, mu kuma muka fita.
Har ya kaini asibiti yanayinshi ba irin wanda ya shigo dashi bane yau da safe duk sai naji na damu. A haka dai ya ajiye ni ya wuce.


Bayan na tashi daga asibitin, na tsaya a wani babban pharmacy anan cikin asibitin. Nayi zarya a wajen tafi sau ashirin, daga karshe dai na tattaro duk wani kwarin gwiwata na shiga ciki. Na sayi abinda zan saya, sannan na wuce gida.
Ina zuwa ko hutawa ban yi ba, na dora musu abincin rana. Ni ko ci ma banyi ba, kankanar dana siya a kofar asibiti, ita na yini ina sha abuna.

Sai dana gama duk abubuwan da zanyi, sannan na fada bandakina na rufo kofar.
Gabadaya jikina rawa yake yi lokacin dana bare ledar teat strip din dana siya a pharmacy, na sakata cikin kwalbar dana dauki sample din fitsarina, na tsaya cikin rawar jiki ina kallon tsinken kamar ina jiran yayi magana.

Ina tsaye, har na kula da canjin da abin yayi. Na dauko shi tare da dubawa.

Ban san lokacin dana koma jikin bangon da nake tsaye ba na jingina. Na kasa yarda da abinda idanuwana suka gani, da gaske? Ya Allah, ko dai mafarki nake yi?.

Ban san iyaka lokacin dana dauka anan ba, har sai dana ji karan turo kofa an shigo dakin, ina jin Yaya yana kwala min kira, amma na kasa motsawa balle in amsa mishi. Daga karshe dai ya turo kofar bandakin ya leko.

Ganina a haka, ya rikice. Da sauri ya saki kofar ya fado bandakin, ya tallabo ni cike da matsananciyar damuwa, "baby, lafiya, me ya faru ne?". Ya jero min wadannan tambayoyi.
Amma na kasa motsawa har yanzu. A hankali na daga hannuna da yake rike da tsinken awon, na mika mishi.

Ya amsa, fuskarshi dauke da alamun tambaya da mamaki, "menene wannan kuma?".

"Positive... positive...", kadai na dinga fada ina nanatawa kamar wani karatu.

Ina ga a hankali ya fara fahimtar abin, saboda daga baya naga ya kamoni yana jijjiga ni cikin zakuwa, "me kike son fada min ne baby? Are you...??!", muryarshi ta katse ya kasa cewa komi, yayi gyaran murya tare da sake cewa "...cikina? baby...?".
A hankali na hau daga mishi kai alamun ehh.

Rasa bakin magana yayi, sai kallona daya tsaya yana yi. Mun jima a haka, kafin daga baya ya daga ni sama cak, sai gani ina shawagi a sama yana juya ni. Ban san lokacin da muka fita daga bandakin ba, sai dana ji ni a tsakiyar gadona.

Ya janyoni cikin jikinshi ya kankame, jikinshi yana masifar rawa kamar ana kada mishi mazari, "baby da gaske? Da gaske kina dauke da cikina? Ya Allah, me zan ce maka ni kam? Ya Allah... Ya Allah...".

Nayi shiru ina saurarenshi yana sambatun godiya ga Allah ina ta murmushi.
Ya dago yana jero min tambayoyi, "me kike so? Me zaki ci? Kina marmarin wani abu? Ki fada min duk abinda kike so baby kinji?".
Na girgiza mishi kai, "barci nake ji".
Da sauri ya hau gyara min wajen kwanciya, ya kwantar dani akan gadon tare da sanya bargo ya rufe ni, "kiyi barcinki kinji? Sannu baby na...".
Ina yada kai akan filo, barci ya dauke ni.

Washegari wayar Janan ce ta tasheni daga barci, daga nan nasan babu wanda bai ji labarin samuwar cikina ba.

Da alama matan nashi kuma basu sani ba. Idan ma sun sani ni ban ga alama ba. A ranar Raheemah ta tafi wajen bikin Haleemoh, sai tayi kusan sati biyu lokacin an gama bikin sannan zata dawo. Gida ya rage daga ni sai Ameerah da Yaya.

Yadda yake lallashina, yana riritani, yana nan-nan dani kamar wata karamar yarinya, Ameerah da kanta ta cafko da wani abu a kasa, da kanta ranar naji tana tambayarshi lafiyata lau kuwa? Shi kuwa yace mata cikine dani. Tunda muke da matar, sai ranar ne naga bacin ranta. Ranar ko dan murmushin yaken data saba yi, kasawa tayi. Da kyar ya iya kakaro sautin "Allah ya raba lafiya", ta tashi daga wajen da sauri.

Wata tafiya ta kama Yaya zuwa Niamey, wani bincike da aka tura su wajen aikinshi. Da kyar ya iya tafiya ya barni, a cewarshi sai dai mu tafi tare, ni kuma nace mishi a'ah, da kyar dai ya tafi da har yace ya fasa zuwa sai dai wani daga wajen aikin yaje a madadinshi, na dai samu ya tafi da kyar.

Yana barin gidan, itama Ameerah ta janyo akwati ta bar gidan, daga gani dama jiran ya tafi take yi. Gida ya rage sai ni kadai.






*☆⋆44⋆☆*





Satin Yaya daya da tafiya, sai gashi ya dawo. Babu sanarwa kawai sai ganinshi nayi a cikin gidan.
Lokacin ina kwance ma a falonshi, kallo nake yi da plate cike da dambun nama a gabana ina ci, ban ma san lokacin da barci ya dauke ni ba. Ji nayi kawai ana shafa gefen fuskata a hankali.
Na bude idanuna da suka yi nauyi, na sauke su a kanshi a nutse. Mamaki ya kama ni, a yadda muka rabu dashi a jiya ta waya, sai gobe da safe sannan zai dawo. Cikin mamakin na fara kokarin tashi zaune, yayi sauri ya maida ni na koma na kwanta, "uhm uhm koma barcinki abinki, I'll join you in a bit".

Sai lokacin na kula da suits din dake jjikinshi da kuma akwatun kayanshi da yake ajiye a gefe, da alama ko daki bai karasa ba.
Ya tashi ya ciccibi akwatinshi ya shige daki. Bayan tafiyarshi kuma sai na kasa komawa barcin, na tashi zaune da kyar ina hamma da mika. Idanuna suka sauka akan agogo, karfe daya na ranar Laraba. Kamata yayi ace Ameerah ce kuwa da girki ranar tunda ranar daya tafi girki ya fita a hannuna.

Na tashi na zauna akan kujerar tare da daukar filo na rungume naci gaba da cin dambun nama na ina kallo.
Zuwa can sai gashi ya fito sanye da kayan hutu, jar rigar T-shirt mai buttons da bai yi buttoning duka maballan ba, ya bar guda biyu na sama, hakan yasa ake iya hango fara kar din singiletin daya sanya daga ciki. Sai ya sanya car-go pants baki, na kuwa daga baki na bishi da kallo cike da burgeni din da yayi.

Zama yayi a gefena yana dan murmushi, "kada dai ace na tashe ki?".
Na girgiza mishi kai a hankali, idanuna manne da talabijin inda suke nuna film din 'Gentleman', "ko kadan, dama can ba wani barci bane. Ya hanya Yaya?".
Yace "Alhamdulillahi, mun iso lafiya lau, shine kawai".

Na dan turo baki gaba, "kuma shine baka fada min zaka zo ba?".

Ya janyo ni cikin jikinshi yana yar dariya, "kada fa kice zaki fara yi min rigima yanzu. Ganin mun gama muhimman abubuwan da suka kaimu, yasa na baro sauran a baya na taho. Na kasa jira har sai gobe kafin in ganki. Ya baby na, baya takura ki dai ko?". Na girgiza mishi kai.
Yace "yau baki leka asibiti bane? Naga kamar morning kike yi wannan satin ko?".

Nayi hamma tare da kara komawa cikin jikinshi na langwabe, shi kuwa ya kara rike ni, nace "sister Hanifa taga ina ta layi saboda barci, shine tace in taho gida kawai zata kula min da nawa aikin".

Ya shafa sumar kaina, "ta kyauta gaskiya, ki tuna min idan muka hadu da ita nan gaba in mata godiya sosai. Wai ina Ameerah ta shiga ne, ko barci take yi? Naji dama tana cewa kwana biyun nan ta cika yin barci".

Nayi shiru ina muzurai don ban san me ya kamata in ce mishi ba, bana so yaji mutuwar sarki a bakina. Ganin yadda nayi shiru ina kallonshi, yasa ya fara dube-dube kamar wanda yake neman wani abu.
"me ya faru ne? Ko bata jin dadi ne?".

Naga dai duk wani boye-boyena babu abinda zai sa ko ya hana, Ameerah dai bata gidan, Yaya kuma gashi nan a gidan, idan ma nace zan kareta zata iya karewa in kwana a ciki, tunda babu ranar dawowarta.

Nace "bata fada maka ranar da zata dawo bane?", Allah ya gani, banyi don in hada su ba, don dai babu yadda za ayi in kaucewa hakan shi yasa.

Yace "ban gane bata fada min ba, ina ta tafi, kuma yaushe?".
Na dago na kalleshi, haka kawai naji tausayinshi ya ratsa ni. Ban ga amfani, ko dalilin da zai sa haka kawai mata ta bar gidan aurenta ba tare da ta nemi izini daga mijin aurenta ba, akan wane dalili? Kodayake, rashin tsoron Allah yayi karanci a zukatan mutane a yanzu. Rayuwar auren an maidata kamar wata wasan yara, matan aure basa girmama mazajen aurensu. Gani suke yi kamar yan kananun abubuwa kamar tambayar miji zuwa anguwa wani kankanin abu ne. Bayan babbar magana ce, kuma babbar matsala wadda idan muka yi da wasa, zata iya kaimu wuta. Balle kuma, fita unguwa har ki kwana ki wuni a wani waje can daban? Shi mijinki yana can ya bude baki da hanci, yana tunanin ya baro ki a gida a zaune, cikin tsarewar bangon gidan aurenki, ba tare da yasan abinda yake faruwa ba. Ko tunanin yanayin rashin tsaro da wannan duniyar tamu take ciki bata yi, idan ace wata matsala ta samu, misali hatsari ko kidnapping Allah ya kiyaye, me zata ce mishi; me kuma zata cewa Allah?.

Nace "ai kamar tun ranar da ka tafi itama ta tafi, bata dawo ba har yanzu".

Rubutaccen mamaki ya zanu a fuskar Yaya, ba karami ba kuwa. Bai ce komi ba sai kai da ya girgiza, yace "ok!". Sai dai daga jin yadda yayi maganar kasan cewa ranshi yayi matukar baci.
Nima ban samu na iya cewa komi ba saboda bani da abin cewar, sai kawai na kara kwanciya a jikinshi. Muka cigaba da kallonmu ni dashi, babu wanda yake iya magana a cikinmu, sai sannu da yake yawan jefo min a duk lokacin da na motsa.

Sai da aka kira sallar La'asar sannan muka tashi, kafin ya fita ya umarceni da in sama mishi abinda zai ci kafin ya dawo. Bayan nayi sallah, na shiga kicin na dafa mishi abinci mai kyau, daya dawo muka ci tare. Shi ya dauko laptop dinshi ya fara aika bayanai akan ayyukan da yaje yi a Niamey, ni kuma na zauna a gefenshi.
Anan ne Maryam ta kira ni daga gida, mun jima muna hira da ita, har su Anty Alawiyya da su Kulsum sai da muka gaisa dasu. Tunda labarin cikin nan ya same su, kusan kullum sai munyi waya dasu, ko su ko Janan. Ummah ma da Yaya kusan kullum muke yin waya dasu, kullum maganarsu daya, yadda zan kula da kaina da dan cikina, abinda ya kamata in ci da wanda bai kamata in ci ba, kulawar da muke samu daga wajensu ni da abinda ke cikin cikina ma kadai ta isheni, balle kuma ta wajen uban gayya, Baban baby na.

Karfe shida ta dan gota na yamma, lokacin da muka ji an shigo cikin falon. Lokacin mun koma kasan carpet din falon, har yanzu Yaya yana fama da rubutu a laptop dinshi, ni kuma nayi matashin kai da cinyarshi. Ayaba ce a gefena ina barewa ina ci, shima idan na ci na kan kai wata bakinshi ya ci.

Ameerah ta shigo da waya sarkale a kunnenta tana amsa kira, hannunta mai rike da wayar rataye da jaka, dayan kuma yana jan karamin trolley.
"... Yanzun nan na shigo gida fa ko daki ban karasa ba. Idan na huta zan kirak...", ta kasa karasa maganar da zata yi sakamakon ganin Yaya zaune ya zuba mata idanunshi.

Bata san lokacin da wayar hannunta ta zame daga hannun nata ta fadi a tsakiyar dakin ba, tayi sak kamar wadda aka kafe da wani abu a wajen.
Da kyar sautin "baby....!!", ya fita daga bakinta. Daga ganinta kasan cewa ta rikice, ta kuma tsorata da ganin Yayan a gida.

Yaya yayi zaune very calm and collected, yana kallonta yadda kasan ranshi ba a bace yake ba. Ganin babu wanda yayi yunkurin ce mata kala, yasa ta durkusa ta dauki wayarta data fadi, ta tashi tsaye tana kallonmu fuska dauke da wadataccen murmushi kamar ba ita bace aka kure tayi satar hanya ba. Tace "baby... Banyi zaton cewa yau zaka dawo ba ai, ya hanya? Yaushe ka da...??".

Yaya yayi saurin

Please Login or Register in order to submit comment