Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

bana son wani tada rigima da maganganu. Idan ma wani abin ne, Janan ina da shaida ne? Koma menene, mutum ai kanshi ya yiwa. Don Allah kada ki bari ma Yaya yaji wannan maganar, Allah kadai yasan abinda zai yi akai. Ni na barwa Allah komi, na kuma yarda babu abinda yake faruwa face cikin yarda da izininsa. Don haka ki manta da maganar kawai".

Ta rausayar da kanta gefe guda, "to shikenan ai tunda haka kika ce. Zaki ci abinci?".
Ta watso min tambayar tana nufar kulolin dake ajiye a wajen wadanda yawanci abokan aikina ne na nan suka kawo min su, nasan duk don ta dauke hankalina daga kan zancen ne. Murmushi kawai nayi na gyada mata kai.




[Hello there! 😽].









*☆⋆45⋆☆*





Kwana na biyu ina hutawa a gadon asibiti. Bayan an tabbatar da lafiyata da komi, aka sallamomu muka koma gida. A ranar Janan ta koma Kaduna ina ta mata godiya.
Sai dana kara kwanaki uku ina kara hutawa, sannan na koma bakin aikina na kuma karbi girki. Rayuwa ta koma normal, mun maida komai bayanmu mun fuskanci gabanmu.

Zaune muke gabadayanmu a falon Yaya da misalin karfe tara na dare. Yanzu har Raheemah ta kan fito ayi hira da ita, kafin dare yayi kowa ya nemi makwancinsa kuma.
Na fahimci Yaya a mutum mai son karfafa zumunci da son kusanci ga iyalinshi, hakan yana kara min girmanshi da kimarshi da nake gani a cikin idanuna. Duk da cewa ta fanninsu, ba hakan suke so ba.

Na tashi na shiga kicin, fruit salad din dana hada yayi sanyi karara, na dauko forks guda hudu, na koma falon. A tsakiyarmu na ajiyeshi tare da ajiye cokulan masu yatsu, muka fara shan fruits din aka kuma cigaba da hira. Sai dai hirar kamar kowacce tata kawai take yi, idan Yaya yana hira da daya, baka ji biyun sun sanya baki sai dai su kalli TV ko kuma suyi shiru da bakinsu. Duk yadda yaso ya saka mu cikin hirar gabadaya abin gagara yayi, idan ma ya sanya bakin wata a cikin hirar ta danyi magana, sai ita dayar kuma tayi kim da baki, sai ta jira sun gama hirar sannan ta sako wata. Abin gwanin ban dariya, na dai yi ta kokarin makale tawa a ciki.

Duk da cewa a hakan ma ba karamin kokari yayi ba, tun da yanzu har mu kan zauna mu duka a waje daya ba tare da kaji kananan maganganu suna tashi ba. A ganina hakan kamar an fara daukar matakin farko kenan wajen hade kai.
Sai dai, tunda na dawo daga asibiti, wani shiru da matan suka yi su duka, yanzu babu bataccen girki idan nayi, Ameerah ta daina shiga dakin Yaya tunda safe, haka ita kanta Raheemah ta daina wannan yawan mitar tata. Jikina kawai yana bani ba daidai ba. Sai inji kamar shirun nan nasu, 'silence before the storm' ne.
Ko kuwa sun fara shiryuwa ne??.

Kadan-kadan Ameerah ta fara yatsina fuska, tun ana yi babu wanda ya kula har Yaya ya lura, ya kalleta cike da alamar tambaya, "lafiya, baki jin dadi ne?".
Duk sai muka juya hankulanmu kansu.

Ta girgiza kai a hankali, "cikina nake ji yana juyawa... Kamar zanyi amai...".
Tana rufe baki, ta tashi a sukwane tayi dakin Yaya, mu duka ukun muka tsaya muna kallon-kallo, kafin muka tashi da sauri muka bi bayanta.
Tana cikin bandaki tana ta kakarin amai, Yaya ya matsa da sauri ya tattagota suka dawo dakin, daga shi har mu sannu muke jera mata wanda take amsawa cikin jan numfashi. Muka rankaya muka koma falo muka zauna.

Muna zama ta fara wani kakarin da yatsina fuska, Yaya yace "wai wani abu yana damunki ne?".
Tana daga baki, sai cewa tayi, "ai ita warin kankana ne yake tada mata hankali".

Na daga girata sama cikin tsananin mamaki, Raheemah kam sai ta kama baki. Yaya yace in dauke farantin in maida kicin tunda mun gama shan fruits din. Ban ce komi ba na dauke kayan, a raina ina nanata ikon Allah kenan mai rike zariyar wando.

Na koma muka cigaba da hirarmu, har lokacin kwanciya barci yayi duk muka tashi. Na koma dakina nayi shirin barci, na koma dakin Yaya.

Cikin dare kawai sai karan waya muka ji, Ameerah ce wai cikinta ya dameta da ciwo. Nan muka nufi dakinta muka sameta tana ta birgima akan gado. Yaya yace min "ko kina da maganin ciwon ciki ne ki bata ta sha?".

Nan na koma daki na lalubo maganin boskafone na koma dakin bayan na biya ta kicin na dauko ruwa mara sanyi.
Nan na sameta kwance shame-shame a jikin Yaya. Ban ce musu komi ba, na mika mishi maganin, ya tallafo kanta zai bata maganin, nan tayi fir tace ba zata sha ba.
Yaya ya fara aikin lallashi, amma ta kafe.
Cikin nuna alamun gajiya da halinta yace "kinsan ba neman magani kike yi ba, zaki tado ni da tsakiyar wannan daren, idan ba zaki sha maganin ba zan tafi in kyaleki yanzu wallahi".
Sannan fa ta karba ta sha. Har wajen karfe hudu na dare muna kanta. Ni naki tafiya daki duk da sai da Yaya yace in tafi, ban san ko ciwon gaske take yi ko na karya ba. Sai da aka fara kiran assalatu sannan barci ya dauketa. Sai lokacin muka koma daki.

Bayan kwana biyu da yin haka, sai gata wai taje likita ya aunata ance tana da ciki. Nan suka hau murnarsu ita da Yaya, na bisu da addu'ar Allah ya raba lafiya. Wani abin mamakin shine, yanayinta sam bai yi kama dana masu ciki ba. Yadda take da, haka take yanzu, babu canjin komi a tattare da ita. Hakan yasa na fara tunanin anya ba cikin karya bane ba kuwa? Sai dai a yadda Yaya yake ta doki da rawar jiki akan cikin wannan, nasan ko giyar wake na sha ba zan fito in ce mishi ga abinda ake ciki ba. Don haka na kawo idanu na zuba musu, koma dai menene, nasan it's only a matter of time, zamu ga ciki dai ya bayyana ai ko?.

Ranar nan ina jinsu ita da Raheemah suna gabzawa, ranar Adi tazo gidan ta wuni, a cewarsu itama ta samu wani house of rep dake zaune anan Abujar har an sanya musu ranar aure. Ina tunanin Adin ce ta fada mata kamar ba cikine da Ameerah ba.
Sai gata ta tsareta a kicin, ta kare mata zagi tas, tace "kuma idan karyar cikine zamu zuba ni da mutum anan gidan mu gani. Haba, biri yayi kama da mutum! Ke da kike da ciki, maimakon ki dinga yin kiba ko rama, amma kina nan a yadda kike? To wallahi mu zuba don uban mutum, zamu ga karshen karya!".

Ta fita daga kicin din ta bar Ameerah tana ihun "tunda ita take bada cikin, ta riga ta san babu shi, ba sai ta fadawa Yayan ba?".
Ban ce musu komi ba ni kam sai kai dana dinga girgizawa. Su dai suka sani ai.

Ranar assabar a Kaduna na wuni, Yaya zai shigo su gaisa dasu Ummah, don haka nima na biyo shi. A gidan su Ummahn muka fara sauka, duk da sunyi murna da ganina, hakan bai hana su min fadan mai ya kaini fara yawo yanzu ba, jikina har yayi karfin da zan fara yawo ne? Nace musu lafiyata lau, na warke.
Bayan mun gaisa dasu na huta, na tafi gidan Janan. Nan muka wuni muna hira da hirar yaushe gamo.

Lokacin dana mata zancen cikin Ameerah, dariya ta dinga kyalkyalawa har sai data kifa daga kan kujera. Na bita da kallo ina dan murmushi duk da bansan akan meye take dariyar ba. Sai data yi ta isheta, sannan ta dago idanu taf da hawaye don dariya, tace "yanzu kuma Yaya ya yarda da wannan crap din??".

Nace "me zai hana shi yarda?".
Tace "haba, tun yaushe suke zarya wajen likitoci ana cewa kwayoyin haihuwarta basu da kwari? Wace kasa ce basu je ba akan wannan matsalar amma magana daya, ba zata iya conceiving ba. Kila dai Yaya mantawa yayi, ko kuma tsabar son yara ne yasa idanunshi suka rufe. Amma daga ma jin labarin da kika bani, ko rantsuwa nayi nasan ba zata taba ci na ba, cikin karya ne!".

Nayi shiru ina processing abinda tace, daga karshe na daga kafada, nace "kika san ko Allah ne ya dubeta da rahamar shi? Shi ikon Allah ai yawa ne dashi. Idan ma ba hakan bane, wannan matsalarta ce, ina zaune a gefe daya koma menene zai bayyana. Shi ciki ai ba'a boye sa, dole zai fito kowa ya gani".

Janan ta gyada kai, "haka ne kam. Allah dai ya rufa mana asiri bakidayanmu". Nace "ameen".

Da yamma da Yaya ya gama ziyararshi, ya biyo muka juya bayan sun gaisa da Janan da mijinta Almustapha. Ashe har Zaria yaje, sai a hanya yake fada min.
Kafin mu karasa gida sai da muka biya wani fast food joint, ya sai roll cakes, tarkacen hamburger, ice creams dasu chocolate, sakon Ameerah. Muna komawa na kwashi kasona na fada daki saboda girkin Ameerah ne ranar. Sai ya zama wadannan su muka ci abinci matsayin abincin dare, saboda apparently bata da karfin yin girki ranar.
Sai abin yazo ya zama kamar al'ada Yawancin ranakun girkinta sai dai Yaya yayo odar abinci.
Nace mishi me zai sa maimakon yayi ta asarar kudi wajen siyo abinci, mu dinga girka kayanmu duk ranar da taji ba zata iya yin girki ba? Sai cewa yayi idan aka yi hakan, za'a bata mishi tsari da dokar gidanshi. Da na matsa, sai yayi kici-kicin da rai, yace "wai idan ma na batar da kudin, kudina ne ko naki?".

Mamaki ya kama ni, na kama baki nace "daga maganar gaskiya? To Allah ya baka hakuri!". Na tashi na koma dakina.
Can kuma sai gashi ya biyo bayana, wai inyi hakuri, kawai yaga yana kokarin dauke mana wahala ne amma kamar bamu gani, maimakon mu mishi godiya, sai mu hau korafi, waye da waye, nan ma dai na kara bashi hakuri aka wuce wajen.

To rayuwar fa kenan, yau dadi, gobe akasinsa.
Kamar yadda duk kokarin mutum wajen kaucewa kaddarar data riga fata, duk gudunka da fata da burinka, baka da wani katabus akan abinda Allah ya kaddara. Shi yasa ita yarda da kaddara take da matukar kyau. Ko babu komi, kowani irin abu ne ya kan zo wa wanda ya yarda babu abinda yake faruwa a doron kasa face da izinin Allah, da sauki.

Gabadaya yinin yau a kasalance nayi shi, tunda na tashi da safiyar yau nake ji na ba daidai ba. Jikina yayi min nauyi, da kyar na dinga gudanar da ayyukan dana saba yi.
Zuwa yamma, abin ya kara tsanani da kamari. Ina zaune ina yin azkar din dana saba yi, idanuna suna likewa saboda wani azababben barci daya mamaye min idanu. Duk yadda naso in daurewa barcin nan, kasawa nayi. Ban san lokacin daya kwasheni ba anan.

Sai gab da magriba na tashi a firgice. Nayi salati ina jan addu'o'i a cikin raina, ban saba barcin yamma ba, kai barcin rana ma gabadaya ban cika yin shi ba, balle na bayan sallar la'asar.
Mutuwar jikina har tafi ta dazu, na lallaba na fada bandaki nayi wanka da ruwan dumi. Kasancewar bana yin sallah, sai na gyada jikina kawai na fito.

Washegari, na shiga gaida Yaya. Yana zaune a falonshi, matan nashi sun zagaye shi yana karin safe. Ameerah da har yanzu ciki bai fara turowa ba, an ci kwalliya ta kece raini, fuskarnan baka ganin komi sai kyallin foundation, concealer da eye shadow.
Raheemah ma taci tata kwalliyar babu laifi.

Na duka a gefenshi na gaida shi, bai ko daga kai ya kalleni ba, ya amsa ciki-ciki kamar wanda aka takurawa, yaci gaba da cin abincinshi. Babu tambayar 'ya kika tashi' ko kuma 'kin tashi lafiya?'. Wasu lokutan ma da yake cikin yanayi mai dadi, ya kan kara da 'da fatan kinyi mafarkina?'.

Sai ban kawo komi a cikin raina ba, na juya na gaida matan nashi da suma suka amsa ciki-ciki, su dama sun saba, don haka ban damu ba. Yaya ne dai da ba haka ya sabar min ba, duk sai naji abin yayi min wani iri. Amma zata iya yiwuwa ko bai tashi cikin dadin rai bane yau. After all, mu dukanmu mutane ne, we all have our moments.

Ban jima ba, na koma dakina na gama shiryawa nima na tafi asibiti. Aikin safe nake yi wannan satin.

Koda na dawo daga asibitin, kasa zama dam nayi. Jikina tun jiya nan bai dawo daidai ba. Ji na nake yi kawai kamar ba ni ba. Ranar sai dana juya gabadaya tsarin dakina duk don in dan ragewa kaina zaman banza da tunanika marasa amfani.
Har zuwa can yamma ina abu daya, nayi wanka na sanya wata doguwar riga single, na dauki wayata tare da zura takalmi flat a kafata na fita falo.

Raheemah na kicin tana kammala girki, na zauna akan kujera, na dauki remote na kunno wata tasha suna karatun kur'ani. Na kwanatar da kaina akan hannun kujerar ina bin karatun a nutse. A hankali naji nutsuwa ta fara shigata.

Ina nan har Yaya ya dawo daga wajen aiki. Na tashi zaune ina kallonshi cikin murmushi, "Yaya sannu da...".

Kafin ma in gama mishi sannu da zuwan, ya fada falonshi da sauri. Babu alamun ya kula dani a cikin falon da ya nuna, idan ma ya ganni din, ba karamin kokari yayi wajen share ni ba. Sai na bishi da kallo baki a dage.

Da dare kamar yadda aka saba, na tafi falon Yaya da niyar zuwa yin hirar dare. Suna zaune su duka ukun, Yaya da Raheemah suna hira, Ameerah kuma zaune a gefensu.
Na zauna a kusa da ita na musu sannu, Yaya da Raheemah suka yi shiru da hirar da suke yi suna kallona, babu wanda yace min ci kanki. Kafin suka komawa hirarsu.

Ko minti goma cikakke banyi ba, naji zaman wajen ya isheni. Yadda Yaya yayi kamar babu wata halitta a cikin falon face Raheemah kadai, abin ya sanyayar min da gwiwa. Ita kanta Ameerah din da idan da ne, duk wani motsi da zata yi zai yi ta binta da sannu, yanzu ko yunkurin tsoma baki tayi cikin hirar da suke yi, haka zaka ji yayi duf, sai kallo da zai yi ta binta dashi.
Da abin ya dameni, sai kawai na tashi na musu sai da safe don ba zan iya cigaba da zama a haka ba.


Wasa-wasa fa karamar magana sai ta fara kokarin zama babba. Shi kenan a wannan gidan yanzu babu wadda Yaya yake ganin tsakiyar kanta da gashi sai Raheemah kawai.
Lokacin da girki ya juyo kaina, sai dana kara raina kaina. Ranar Yaya bai shigo gidan ba sai can bayan isha'i. Na mishi sannu da zuwa ya amsa ciki-ciki, ya shige can kuryar daki.
Ban yi fushi ba, na bishi har dakin nace mishi ga abincin shi fa. Sai ce min yayi ai ya koshi.

Nace "ka ci abinci ne a waje ko kuma cikinka ne a cike?".
Sai ya dago ya kalleni fuskarnan a cune, "to wai idan ma naci abincin ko kuma na kasa ci, menene matsalarki? Cikinki ko nawa?".

Da yaga nayi shiru ina kallonshi ban ce komi ba, sai ya wawuri towel dinshi ya fada bandaki yana mitar duk na bi na tsangwame shi sai kace wani karamin yaro.

Na zabga uban tagumi har ya fito daga wankan ya sameni a yadda ya barni. Bai ce komi ba, ya fara shafa mai.

Nace mishi "Yaya, ko dai wani abu nayi maka ne? Idan ma haka ne, don Allah kayi hakuri. Ba da sani na nayi hakan ba".

Murya ciki-ciki yace "to ni nace ne kin min wani abu? Ko kuwa don dai shi mutum bashi da damar yace ya koshi da abinci, sai a hau tuhumar shi. Wai ni karamin yaro ne, iye?".

Gabadaya sai nake ga kamar Yayan an canza min shi da wani na daban. Wanda ban sani ba, wanda ban san komi nashi ba. Naji kwalla ta fara cika min idanu.

Sai ya dakata da abinda yake yi, ya kama baki yana kallona. Yace "to yanzu kuma me na miki da zaki sanya ni a gaba kina kuka?". Na girgiza mishi kai alamun babu komi.

Yace "abinci ne dai ko? Bari in zo in ci, shikenan?".
Na gyada kai ina dan murmushi, ina share kwallar data fara zubar min.

Bayan ya gama, muka rankaya zuwa falo, na zuba mishi abincin. Kadan yaci, hakan bai dameni ba, cin kadan din ai yafi rashin ci gabadaya.

Anan na barsu shi da matan nashi suna shan hirarsu. Har yanzu dai jiya i yau, bata sake zani ba. Ita kanta Ameerah na kula hakan ya dameta, bata fito fili ta fada bane kawai.
Dana koma falon, ban zauna ba, sai na shige can ciki nayi kwanciyata. Har Yayan ya shigo shima, ya gama duk abubuwan da zai yi, ya hayo kan gadon ya kwanta.

Ganin ya juya min baya ba tare da yace komi ba, yasa na gangara zuwa gefen daya kwanta. Nima na kwantar da kaina akan kafadarshi. Daga farko sak yayi kamar wanda lantarki taja, sai kuma ya saki jikinshi. Ana jimawa naji ya zame ya kara matsawa can gefe guda.

Wani irin makaki yazo ya takure min a cikin makoshina, wata kwallar ta sake ciko min idanu. Sai nima na juya mishi baya.

Zuwa can cikin dare na farka, na ganshi zaune a gefen gado, idanunshi kur a kaina kamar wanda yayi nisa cikin dogon tunani. Ban nuna alamun na farka ba, naci gaba da kallonshi ta cikin dan hasken dakin har barci ya sake kwasheni.






*☆⋆46⋆☆*





Har na fita daga girki na sake shiga wani, bata canza zani ba tsakanina da Yaya. Hankalina idan yayi dubu to a tashe yake. Wannan shine karo na farko dana taba fuskantar yace baya daga mijin aurena, bana kuma fatan hakan ta kara faruwa koda wasa ne. Yadda yake yi kamar duk duniya babu abinda yaki jinin ya gani kamar ni, shine yafi tayar min da hankali. Nan da nan nayi rama. Yanzu na samu yana cin abincina ba tare da bacin rai ba, sannan yana dawowa da wuri ranar girkina. Daga wannan shikenan, idan ma na samu ya amsa min gaisuwata da sannu, to naci sa'a.

Inda naji dadi daya ne, duk da dai ba abin jin dadi bane, ganin cewa ba ni kadai hakan take faruwa da ita ba, har da Uwargida Ameerah, duk da cewa dai ita yana dan daga mata kafa saboda cikin jikinta, amma dai babu gwara.
Hakan ya tabbatar min da cewa lallai da wata a kasa. Ta fannin addu'a da kula da jiki, ina iyaka kokarina dama, sai kara dagewa da nayi. Takanas na dauki kafa naje har Suleja wajen Malam Ali, da yake ya daina kawo mana rubutun da yake kai mana duk sati. Bayan mun gama gaisawa da mutanen gidan, aka min jagora zuwa inda yake karbar bak'inshi.
Mun jima muna hirar yaushe gamo, daga karshe dai na mike kafa na mishi bayanin abinda yake tafe dani, tun daga ranar da abin ya faru har zuwa yau.

Nan ya bani wasu addu'o'i yace in lazimci yin su, shima kuma yace zai dinga taya mu. Ya kara da cewa "ku matsalar ku ta yan boko, sai ku ce baku yarda da sadaka irin wadda ake rabawa yaranmu suyi ayi yanka da sauransu ba. Ita kuwa sadaka abu ce mai kyau, koda wani abu mummuna bai faru da kai ba, ta kan kiyaye mutum daga munanan abubuwa da dama, haka kuma tana tsare shi daga kambun baka, sihiri da sharrin jinnu. Baka san bakin mutane ba, akwai wasu zababbu a cikinmu, da idan suka yi mana addu'a zaki ga kamar da bakin yan amin suka yi ta, Allah ya karba. Shi yasa muke rarrabawa, saboda bamu san inda albarkar take ba".

Na gyada kai cikin alamun fahimta, nace "haka ne Malam. Muma din muna kwatanta yin hakan, amma zamu kara zage damtse in Allah ya yarda. Yanzu zan bayar da kudin sadakar kafin in tafi, in yaso sai ayi duk abinda yakamata dai".

Ya girgiza kai, "kada ki damu 'yar nan, babu abinda zai gagara da yardar Allah. Yaran nan namu ne, dan abinda ya rage kuma bai fi karfin aljihunmu ba, saboda haka za ayi duk abinda ya dace. Ke din ai diya ce a wajena, jinin Malam Audu tamkar jinina haka na dauke su".

Nayi murmushi nace "nasan da hakan Malam, amma duba da cewa sadakar tawa ce, me zai hana ka barni in bayar da kaina?".

Bayan je-ka-dawo dai, dole na sakar mishi, na mishi godiya tare da mishi sallama na tafi. A cikin gida nabi duk iyalan gidan da kyauta har ma da almajiran kafin na fita waje inda Balarabe direban gidanmu yake jirana, yaja muka koma gida.

Da yake aikin safe nake, sai na tashi da wuri tare da turawa Yaya sakon zan zo wajen Malam Ali wanda ya turo min da to kawai.
Akan hanya ya tsaya na sayi fresh fruits da vegetables, duk da ranar ba girkina bace, naji ina marmarin yin salad. Tunda na fara daukar albashina na daina jiran Yaya ya min, ko ya bani wani abu. In dai na ga babu abu kuma ina so ko kuma zanyi amfani dashi ranar girkina, bana kyashin cirewa in saya tunda dai Alhamdulillahi ina dasu, kuma shima Yaya Bilal din baya kyashin bude mana bakin aljihunshi. Wasu lokutan haka kawai zai kirgo kudi ya bamu, baya kuma banbancewa a tsakaninmu, duk da cewa ni ina daukar albashina, Ameerah ma kuma iyayenta na turo mata, amma hakan bai sa ya banbanta mu ba.
Kashi biyu na sanya Balarabe ya sayo komi, daya kawo nace ya dauki kashi daya shima ya kaiwa iyalanshi. Yayi ta godiya har muka karasa gida, ya zagaya da sauri ya bude min murfin motar na fito, ya biyo bayana da ledojin a hannunshi yana kara wata godiyar.
Yan aikin gidan na matukar girmama ni, kamar yadda nima nake girmama su, yawanci ko wani abu ya taso kafin kaji sun nemi Ameerah data kasance Uwargida sau daya sun nemeni sau goma, musamman idan wata bukata ce suke da ita wajen Yaya. Ban taba kyashin isar da sakonsu ba, tunda Allah yasa yana iyaka bakin kokarinshi wajen ganin ya kyautatawa mutane, kuma ya taimaka musu, meye a ciki idan na taimaka mishi ya cigaba da taimaka musu?.
Ranar nan Hasina wadda take mana wanke-wanke da shara, tace tana ta fadawa Raheemah ta taimaka ta yiwa Yaya tunin kudin albashinta, yace zai bata da wuri saboda aikin da za'a yiwa diyarta a hannu, amma har lokacin bai ce komi ba da alama ya manta. Tace ita fa tana zaton kamar bata fada mishi ba, don data sake mata magana sai ta hau ta da fadan wai ta takurawa mijinta. Nace mata kawai zan fada mishi da kaina. Sam ko sun kawo korafi kan wani halin rashin kirki da suka musu, bana biye musu mu ci namansu, yadda bana so ayi gulmata, nima bana yin ta wasu.

A bakin kofar falon muka tsaya na karbi ledojin hannun Balarabe saboda nan ne iyakacinsu da gidan, na tura kai na shiga falo. Karfe hudu na rana ta gota da kadan. Allah-Allah nake in dangana da dakina in cire uniform din jikina, in watsa ruwa ko naji sanyi a jikina saboda wani azababben zafi da ake zubawa yau.

Zaune a falo, Yaya ne da Raheemah sunyi jigum-jigum, sai wata Hajara cousin din Ameerah da take yawan zuwa gidan. Nayi sallama, suka amsa min cikin sanyin jiki, sai naji jikina ya kara yin sanyi, nace musu "lafiya kuwa?".

Hajara ce kawai ta iya amsa min, tace "Ameerah ce ta fadi a bandaki dazu, ana tunanin kamar ta samu miscarriage!".

Sai naji jikina ya kara yin sanyi, nace "Subhanallahi, ya jikin nata? Sun tafi asibiti ne?".
Tace "a'ah, ai family doctor dinmu tazo,

Please Login or Register in order to submit comment